Author : Aisha Aliyu Garkuwa Category : Free Novels Online (Read & Download)
kallon kurillaba.
Shi kuwa numfashi ya fesar tare da cewa.
“Ya za'a yi ki tarawa sheɗan Mafaka ajikin ki?No wonder shiyasa kika cika rawan kai ashe muhalli kikayi ibilis a jikinki”.
Bakinta ta tura tana kallon yanda yake matse mata hannu.
Shi kuwa Moddibo cikin sanyin murya ya cigaba da cewa.
“Shiyada duk rashin ji da neman mgn duk kece a gaba ashe-ashe muhalli kika tarawa sheɗan agangar jikinki. Toh kiji da kyau, ko kiyanke faratun nan ko kuwa idan na tashi da kaina zan haɗa da ƴan yatsunki in yanke kana na wurgawa karnuka su cinye”.
Cikin yanayin tsoronsa da sanyin murya tace.
“Dan Allah ka sake min hannuna zafi fa yake min”.
Sake matsawo kusa da ita yayi tare da faɗin.
“Bazan sake ba”. Da sauri tace.
“Afwan”.
Cikin kasala yace.
“Sai kinyi al'ƙawarin zaki yanke farcen”.
Da sauri ta gyaɗa masa kai cikin narke fuska tace.
“Nayi al'ƙawari zan yanke amma zan bar ɗaya”.
Fuska ya ɗaure tare da faɗin.
“Ban yarda ba duka zaki yanke”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Na yarda zan yanke toh ka sake min hannu”.
Wani irin murmushi mutanen dake wajen sukayi yayinda wasu ke binsu da kallon sha'awa.
Asma'u kuwa hannu ta miƙawa Dije dake gefenta suka tafa cikin yanayin farin ciki Dije tace.
“Asmeey kinga wata Madarar soyayya kamar a Indi'a muke, lallai na yarda cewa Ustazan nan sunfi kowa iya soyayya”.
Kai Asma'u ta jinjina tana mai binsu da kallon sha'awa yayin da aranta take musu addu'ar samun dawwa-Mam-miyar farin ciki tace.
“Ai kam ko tattabaru bazasu gwadawa su Khausy zama da junaba, kinaga wani irin mayataccen kallon da Yah Modibbo keyi mata, ko me yake gaya mata?”.
Da sauri Aseeya tace.
“Sai Allah gashi dai tun ɗazu suketa wani ƙus-ƙus ji Khausar yadda take lumshe ido”.
Dariya sukayi dukansu
Zakariyya kuwa cikin sarawa salon Modibbo ya ɗan sunkuyo daf da kunne Moddibo kana yace.
“Dan Allah ka riƙa tunawa, cikin mutane da kuke.
Na lura gaba ɗaya ka zauce ƙa kauce hanya baki ɗaya, ka wani gigice daga ganin yarinya kana ƙoƙarin taɓarewa acikin tsakiyar taron al'umma duk kuma wani narkewa”.
Khausar kam kanta na ƙasa Zakariyya kuwa cike da sheƙiyanci ya cigaba da cewa.
“A cikin Family fa kake ba cikin falonku kuke ba”.
Shi kuwa Modibbo Numfashi ya sauƙe mai nauyi A ransa yace.
ohhh ni Aliyu na lura Zakariyya magana ne abakinsa shida. Dr Jameel sai dai Allah ya shirye su.
Hannunsa na dama yasa ya damƙe nata da ƙarfi, sai ya zama na kamar sunayin musabaha ne.
Sai kuma yayi shiru tare da rintse idanunsa da sanya haƙoransa ya cije gefen lips ɗinsa na ƙasa kana ya sunkuyar da kansa ƙasa, wani irin abu yake ji tun daga tsakiyan maɗigan ƙwaƙwalwar kansa, har zuwa tsakiyar tafin ƙafarsa, lokaci ɗaya yaji gangar jikinsa ya fara tsuma baki ɗaya jikinsa ya fara tsuma amma ta ciki yanda babu wanda zai fahimta sai shi...
Ibraahim ne ya tsugunna kansa tare da faɗin.
“Bismillah Yah Aleey, Continue”.
Jin muryan Ibraahim yasa ya fesar da sanyayyan numfashi sai alokacin ya fara dawowa hayyacinsa.
Ahankali ya buɗe Idanunsa da suka kaɗa sukayi Jawur ya kalli Khausar yana mai jan wani dogon numfashi da ɗan ƙarfi ya sauƙe numfashin kana ya ɗago idanu ya kalleta.
Da sauri ta fito da idanunta waje ganin yanda ƙwayar idanunsa suka sauya launi baki ɗaya.
Khausar kuwa ahankali tace.
“Ayyah kasake min hannu na zafi”.
Numfashi ya fesar tare da sakin hannu kana ya kamo yatsunta.
Didi dake tsaye ta dauki wani ƙyalle me kyau kamar farko ta miƙa masa karɓa yayi kana ya goge mata tafin hannun zuwan ƴan saffa-saffa yatsunta.
Rahma kuwa kaskon turaren wuta dake fitar da wani Masifeffen ƙamshi ta miƙa masa.
Ƙamshin da ya fara gigita masa tunaninsa lokaci ɗaya ya fara jin wani irin yanayi yana game masa gangar jikinsa da ruhinsa baki ɗaya.
Kaskon turaren wutan ya ɗaura akansa kasancewar gindin Kaskon nada faɗi sai ya kamo hannayenta ya kife akai.
Ahankali hayaƙin turaren wutan ke ratsa yatsunta yana buga fuskanta.
Mai busa Algaita ne ya cigaba da busawa dare da haɗawa da kirari.
Sarkin Zaƙi kuwa hura Microphone yayi tare da cewa.
“Idan akwai ƙanin Amarya ko ƙanwar amarya ta fito, ta amshi kaskon bisa al'adarmu”.
Cikin sauri Haiydar dake ta faman Video ya miƙe ya fita kana ya zare Kaskon turaren wutan kasancewar haka Al'adarsu take.
Shi kuwa Haiydar sunkuyowa kan Khausar yaui tare da faɗin.
“Kai Addah Khausi kunyi kyau.
Kinga yanda kika zama kamar wata acikin taurari baki ɗaya ke kike haska wajen nan”.
Kallonsa tayi cikin yanayi gajiya, sai kuma ta ɗan hararesa kana tace.
“Dole mana kace haka tunda ni kaɗai ce ƴar Uwarka”.
Murmushi yayi kana cikin gaskiya da gaskiya yace.
“Wallahi ba haka bane Addah Khausy kinyi masifar kyau fa”.
Ya ida maganar tare da miƙawa Jakadiya Kaskon.
Jakadiya kuwa da ido ta yiwa Moddibo alamar ya tashi ya koma kan kujera.
Kai ya gyaɗa tare da komawa mazauninsa.
Haka ma Didi da yayunsa suka koma wajen zamansu...
Sarkin Zaƙi kuwa cike da rakaɗi yace.
“Alhamdulillah da wannan al'adar tamu mu kazo ƙarshen wannan taro na yau, sai kuma gobe idan Allah ya kaimu bisa dai da lafiya, za'a fitar da Aleeyu Youseep Muhammad Mouley atsakiyar fada, domin gabatar dashi atsakiyan Fada a matsayinsa na sarki mai jiran gado”.
Daga nan aka tashi kasancewar ƙofofine da dama cikin falon, yasa lokaci ɗaya duk aka fita cikin nutsuwa batare da wani cunkuso ba duk da kuwa yawan mutanen.
Acan ɓangaren Innayi kuwa cikin sauri ta nufi wajensu Moddibo tare da riƙe hannun Khausar ta juya.
Moddibo kuwa baki ɗaya Cousing Brother's ɗin sa ne suka riƙa bashi hannu suna rungumesa cike da ƙaunarsa tare da gabatar mishi da sunayensu da dangatakar su.
Shima cikin yalwataccen farin ciki yake rungunarsu.
Kafaɗarsa Zakariyya ya dafa tare da faɗin.
Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N 09097853276, in tura miki ki karanta abinki salamun Salam.
By
*GARKUWAR MARUBUTA*SAKAYAH
47
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Assalamu alaikum mutanan arziki masoya kamshi ma abota kamshi Amaren kamshi masu jargon kamshi Yammata wadanda sukasan darajar kamshi ni Aysha Aliyu Garkuwa na kawo muku tallan wasu Amintattun turarukana masu matukar kamshi da Kama jiki
Masu saukin farashi sannan ga biyan bukata
Yarhjya_incense_and_more
Ta shirya tsaf domin ta gwangwajeku da Turaruka na alfarma
Farar khumrah
Bakar khumrah
Turaren Wanka
Oil 6ml 1
Oil 12ml 1
Turaren fesawa 100ml 24 hours guda 1
Duka Akan 8k kacal
Sannan kayanta suna tafiyane da guarantee duk wacce tasiya taji babu kamshin nan na alfarma ko kuma basuda lasting to tayi alkawarin mayar muku da kudinku
Wannan garabasar zata kare on 5th September insha Allah
Ku hanzarta ku mallaki naku domin kayan yarhjya babu Danasani a cikinsa saidai kuyi alfahri da siyan kayanta
Account number 1419787445 Amina Umar usman access bank
Kitura evidence of payment to
08092664954
Kuyi saving number TA domin ci gaba da ganin Turaruka Kala Kala
Normal price
Bakar khumrah 1500
Farar khumrah 2k
Turaren Wanka 1500
Oils 6ml 800
Oils 12ml 1500
Turaren fesawa 100ml 3500
Turaren fesawa 50ml 2k
Kayanmu available ne a koda Yaushe
Akwai turarukan wuta na jiki na Kaya Dana daki duka sai Wanda kika zaba
“Kazo mu koma ciki Maghriba tayi muje muyi alwala mu tafi masallaci”.
Cikin gamsuwa ya gyaɗa kai,
Ibraahim kuwa hannun Moddibo ya riƙe tare da faɗin.
“Yah Aleey daga yanzu zaka riƙa zuwa jam'i yanda kake buri da fata da marari”.
Sanyayyan numfashi Moddibo ya fesar kana yace.
“Alhamdulillah, dan babu abinda nafi bege kamar zuwa sallah jam'i da kuma Innayi na”.
Ya ida maganar tare da bin bayan Ibraahim suka fara tafiya.
Tuni ƴan Uwa sun fiffita falon ya rage babu mutane sai ɗaɗ-ɗaya.
Innayi dake riƙe da hannu Khausar ta nufi wajensu Ummi tare da faɗin.
“Kuzo mu koma masauƙinmu sai kuma gobe idan Allah ya kaimu, za'a cigaba da hidima”.
Sheikh Jabeer kuwa da kansa ya nufi inda su Abban Jameel ke zaune yace.
“Kuzo mu tafi Maghriba ta ƙara to”.
Kai suka gyaɗa kana suka miƙe suka bi ta ɗaya ƙofar suka tafi.
Moddibo da su Ibraahim kuwa a hankali suke tafiya cikin nitsuwa auka shiga Corridor da zai sada su da falon Side da suke.
Su Khausar kuwa sun fara haurawa kan steps din.
Asma'u ta juya da sauri ta kalli Ummi tare da faɗin.
“Ayyah Ummi bari inje na gaida Yah Moddibo in faɗa masa saƙon Bashir”.
Ƴar dariya Ummi tayi kana tace.
“Bismillah keda ɗan Uwanki”.
Kai ta gyaɗa cikin sauri ta juya ta nufi wajensu Moddibo tana faɗin.
“Yah Moddibo! Yah Modibbo”.
Moddibo kuwa Already sun riga sun shiga falon da Dr Jameel ke ciki.
Shi kuwa Dr Jameel jiyo motsinsu ne yasa ya sassauta murya cikin wani irin yanayi da yake ciki bisa ga duk kan alamu hirar batsa suke awayar cikin lumshe idanu yace.
“Please Baby kiyi haƙuri muna cikin wani Uzuri ne fa na Fada”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ok bye bye Amma please kazo Ina jiranka, kasan cewa kwana biyu bamu haɗu ba ina kewarka”.
Ta ida maganar tare da katse kiran.
Dr Jameel na miƙewa su Moddibo na shiga....
Cikin yanayin takaicin halayyarsa Zakariyya ya maka masa harara tare da cewa.
“Wallahi kai dai kam Jameel kayi asara, komai aka shirya da kai da zaran mace tashiga ciki saita ware ka cikin mu, musamman wannan shegiyar Baby na rasa yanda zanyi in raba ka da ita”.
Moddibo dake jinsu ne ya girgiza kai kana yace.
“Alhamdulillahi kaima kenan abin na damunka Zakariyya?”.
Kai Zakariyya ya gyaɗa yana mai cigaba da hararan Dr Jameel dake murmushi yace.
“Sosai ma kaga an tsara fitan nan dashi amma dayake shi Mamajone mayen mata, ni wlh ban na lura da lokacin daya zame ya dawo ciki ba, sai da muka shiga na gane baya tare damu”.
Sai kuma Moddibo yayi saurin juyawa jin muryan Asma'u na cewa.
“Yah Moddibo”.
Da murmushi afuskarsa yace.
“A'a Asma'u”.
Asma'u kuwa idanunta ta zare tare da ɗaura hannunta ɗaya akai kana ta buga ɗaya hannunta a ƙirjinta tare da faɗin.
“Yah Jameel”.
Tayi maganar idanunta na kan Dr Jameel dashi ma ita yake kallo.
Cikin sauri Moddibo ya juya ya kalli Asma'u sai kuma ya juya ya kalli Dr Jameel.
Cikin yanayin kaɗuwa, mamaki, Al'ajabi ta fara takowa har ta isa gaban Dr Jameel ta tsaya cikin sarkewar murya ta furta.
“Yah Jameel”.
Kallonta Moddibo yayi tare da girgiza kai yace.
“A'a Asma'u”.
Cikin ficewar hayyaci ta ɗaura hannunta akai tare da faɗin.
“Ummiiii kizo ga Yah Jameel”.
Sai kuma tayi baya luuu idanunta sukayi sama.
Cikin wani irin sauri Dr Jameel da tun time data kira sunansa ya zuba mata idanu yana kallon ƙiranta da kuma yanda Ubangji ya ƙawata surarta, lokaci ɗaya yaji wani irin yanayi da bai taɓa jin makamancin sa ba akan ko wacce irin mace da yake mu'amala da ita karon farko yaji wani irin tsarkakekken soyayyar ta ya mamaye masa zuciya.
Azabure ya nufe ta ganin saura kaɗan takai ƙasa ya tallafota jikinsa ta faɗa kan ƙirjinsa asume.
Faɗawa jikinsa da tayi yasa ya koma baya ya faɗa kan kushin ya zauna, hannunsa yasa ya tallafo fuskarta sai kuma ya ɗaga kansa ya kalli Moddibo kana yace.
“Suma fa tayi”.
Cikin Sauri Moddibo ya riƙe tsintsiyar hannunta cikin yanayin damuwa yake faɗin.
“Asma'u”.
Ina tuni ta samu kallon Ibraahim yayi kana yace.
“Ibraahim ka miƙo min ruwa”.
Dr Jameel kuwa kallon Moddibo yayi cikin wata kasalalliyar murya gami da shauƙi yace.
“Ya dai kake shiga hurumin daba naka ba, ya ina matsayin Dr sannan ta suma ajikina kake cewa amiƙo maka ruwa”.
Wani kallo Moddibo ya mata tare da watsa masa harara kana ya buga masa tsawa da faɗin.
“Kai Mahaukacin ina ne ya yarinya zata suma sannan ka tsaya kana maganar sai huruminka wani irin hurumi kake dashi a kanta, idan zakayi abinda zata farfaɗo kayi ka wani maƙale yarinya atsakanin cinya haukane akan ka”.
Kallon Moddibo yayi tare da juya idanunsa kana yace.
“Kamar ya kake cewa haukane akaina Ni naga matar Aure”.
Cikin tsawa da hararansa Moddibo yace.
“Koma yayane yanzu kayi abunda yarinya zata farfaɗo”.
Ahankali Zakariyya ya tsugunna kansa tare da bubbuga kumatunta yana kiran sunan da yaji Moddibo na kiranta da.
“Asma'u³”.
Hannunsa Dr Jameel ya janye kana ya ture gefe tare da cewa.
“Dakata Zakariyya nasan kai Likita ne amma wannan ba hurumin ka bane Saboda wannan hiruminane”.
Alalace Zakariyya ya banka masa harara tare da faɗin.
“Mayen banza mayen wofi, wato daga ganin Yarinya itama ka ɗaura ƙolafacinka da kwadayin ka akanta”.
Araunane ya ɗago kansa ya kallesu baki ɗaya cikin yanayin gaskiya da gaskiya yace.
“Wallahi ban kalleta da idanun da nake kallon sauran ƴan matan da nake mu'amala dasu ba, na kalleta ne da wasu irin idanu masu matuƙar daraja domin ita mai darace da mutunci”.
Tsaki Moddibo yayi cikin hasala da abinda Dr Jameel keyi ya karɓi goran ruwan da Ibraahim ke miƙa masa ya watsa mata afuska amma bata farfaɗo ba.
Langwaɓar da kai Dr Jameel yayi tare da faɗin.
“Dan Allah kar ka jiƙamu Ni nasan yanda zanyi in farfaɗo da abuna”.
Moddibo kuwa cikin mamaki ya zubawa Dr Jameel idanu yana kallon ikon Allah da karfin hali.
Cikin lumshe idanu Dr Jameel da har zuwa lokacin yake rungume da Asma'u ya sunkuyo da kanta.
Da wani irin azabebben sauri Moddibo ya riƙe ka sa fuskarsa babu walwala yace.
“Wallahi kada ka kuskura, Idan ka yarda ka kuskura Ni nasan abinda zanyi maka hauka ne akan ka? Ko kuma kayi tunanin itama irin ƴan matan da kake rayuwa dasu ne da zakayi ƙoƙarin kai bakinka kan nata?”
Hannunsa biyu ya haɗa kana yace.
“Dan Allah kayi haƙuri Moddibo na rantse da Ubangijin daya busa min numfashi bana kallon wannan Baiwar Allah Asma'u amatsayin matar da zanyi lalata da ita”.
Sai kuma ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa kana ya cigaba da cewa.
“Idanuna suna kallonta ne amatsayin matar Aurena, kuma uwar ƴaƴana wallahi bawai kissing ɗin ta zanyi ba ya kuke maidani kamar Bunsurune zanyi ƙoƙarin dawo mata da numfashinta nefa”.
Still babu walwala atare da Moddibo ya gyaɗa kai kana yace.
“Ok”.
Dr Jameel kuwa cikin lumshe idanu ya sunkuyar da kansa kanta kana ya ɗaura bakinsa kan hancinta yana hura mata numfashi.
Asma'u kuwa ahankali taja wani dogon numfashi tare da faɗin.
“Ummi wallahi Yah Jameel ɗin mu bai rasuba ga Yah Jameel ɗin mu na ganshi da rabshi”.
Sai kuma ta buɗe Idanunta ganinta kwance acinyar Dr Jameel cikin sauri ta yunƙura ta zauna tare da faɗa wa kansa ta rungumesa yayin da take kuka mai tsuma zuciya kana tace.
“Yanzu dama Yah Jameel baka mutu ba, aka kawo mana gawar wani akace ka mutu?”.
Kasa ƙara sa Maganar tayi saboda yanda kuka yaci ƙarfinta kana kallo zaka san daga ainihin zuciyarta maganar ke fitowa.
Lokaci ɗaya tausayin ta ya mamaye baki ɗaya ilahirin zuciyar Dr Jameel hannu ya ɗago da niyyar rungumeta.
Da sauri Moddibo ya buge hannunsa.
Shi kuwa Dr Jameel zafin bugun da Moddibo ya masane yasa shi saurin mayar da hannunsa yana yarfawa sai kuma ya kalli fuskar Asma'u dake cigaba da kuka yace.
“Asma'u Wayyo Allana Yayanki zai kashe Ni kafin komai ya kankama”.
Moddibo kuwa ahankali ya kira sunanta cikin girma da kamalada da zame mata matsayin babban wanta kana jagoro kuma uba yace.
“Asma'u”.
Ahankali ta juya ta kalli Moddibo sai kuma ta maida kallonta kan Dr Jameel ta sake rungumesa.
Ganin haka yasa Moddibo saurin fin cikota daga jikin Dr Jameel ya tsaidata sai kuma yace.
“Zo ki zauna anan”.
Ya faɗa tare da zaunar da ita akan Kujeran cikin yanayin nutsuwarsa da tuno yadda J ɗinsa ke killacesu da basu kariya akan kamilallun mazama bare irin Dr Jameel a hankali yace.
“Asma'u ki buɗe ido ki kalleni da kyau”.
Idanunta ta buɗe da tuni hawaye suka kwaranya ta kalli Moddibo.
Cikin fesar da numfashi ya gyara zamansa tare da cewa.
“Wanene Ni awajenki?”.
Cikin raunin murya tace.
“Yah Moddibo Yah Jameel”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Menene matsayina awajenki?”.
Still idanunta na zubar da hawaye tace.
“Tamkar uba kuma tamkar Yaya Jameel”.
Zazzafan Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.
“Toh kiyi haƙuri da abinda zan faɗa miki, Dr Jameel ba J ɗina bane mai kama dashi ne kawai, nima nashiga irin yanayin da kika shiga lokacin dana fara ganinsa”.
Kai Asma'u ke girgiza wa tare da cewa.
“Wallahi Yah Moddibo ban yarda ba Yah Jameel ne”.
Cikin rauni ya kira sunanta da faɗin.
“Asma'u”.
Ahankali ta ɗaga ido ta kallesa cikin sanyi Murya yace.
“Na taɓa yi miki ƙarya ne?”.
Cikin wata raunatacciyar murya ta girgiza masa kai tare da cewa.
“Yah Moddibo baka taɓa yimin ƙarya ba, amma wallahi bazan yarda da abinda kake faɗa ba”.
Ta ida maganar tare da miƙewa ta nufi Corridor data shigo tana gudu tana cewa.
“Ummi Ummi”.
Ahankali Moddibo ya koma ya zauna tare da ɗaura hannunsa duka biyu ya dafe kansa.
Ya tabbar kafin Asma'u ta yarda cewa wannan ba ɗan uwanta bane za'a ɗauki lokaci.
Sai kuma ya ɗaga kansa tare da kallon Dr Jameel dake ƙoƙarin binta yana kiran Asma'u asanyaye yace.
“Ka dawo ka zauna saboda bazata saurareka ba.
Wallahi Ni kaina zuciyata bata gama yarda min cewa ba J ɗina bane kai.
Kawai jikina da zuciyata tana gamsuwa da cewa Kai ba J ɗina bane”.
Sai kuma ya lumshe idanunsa da yake jin ruwan hawaye na tsats-tsafowa kana ya cigaba da cewa.
“Saboda yanayin lalacacciyar ɗabi'ar da kake yi na tabbatar kuma babu abinda zaisa Ummi, Asma'u,da Bashir su yarda cewa ba kai bane J sai In har sun fuskanci mummunan ɗabi'unka da halayyar ka da yanayin ka na neman mata shine kaɗai zaisa su yadda”.
Sai kuma ya sanya bayan hannunsa tare da goge hawayen da suka saƙƙo asaman kuncinsa kana ya cigaba da faɗin.
“Saboda J ɗina Amintaccene mai Aminci mai kamala ne mai mutunci ne, kuma tsarkakekkene bai kasance yanayin makamancin ɗabi'unka ba”.
Tunda Moddibo ya fara magana jikin Dr Jameel yayi bala'in sanyi, ganin maganar da Moddibo keyi daga ainihin zuciyarsa ke fitowa kana yana jin magan-ganunsa nada muhimmanci da kuma ƙarfi kana yana ganin yana da yaƙini da gamsuwa.
Cikin mutuwar jiki ya koma ya zauna karo na farko arayuwarsa daya fara jin tsananin ƙyamar kansa da kansa akan ɗabi'unsa na neman mata.
Lokaci ɗaya ya riski kansa da wani mummunan tsinkewar zuciya saboda har ƙasan ransa Allah ya jarabcesa da son wannan yarinya daya gani wacce ake kira da Asma'u.
Wacce ita kuma take masa kallon ɗan uwanta wanda zuwa yanzu ya fahimci komai nasa yana mata kama da ɗan Uwanta ne daya rasu.
Hakanan ne yasa zuciyarsa ya cika da tsoro da taraddadi anya Moddibo zai lamunce abashi Auren Asma'u ayanda yake nuna tsananin ƙyamarsa akan halayyarsa na zina...
Kansa ya riƙe da