Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sakayya Complete Hausa Novel by Aisha Aliyu Garkuwa

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   72 / 140

213K to 216K   out of 417.8K words

kafin ya tun kari lamarin mu kuma bamu da sahihiyar Hujja dan haka mu barwa Allah lamarinsa”.
Jinjina kai Asma'u tayi tare da gyara zaman ta tace.
“Makama ɗaya muke da shi batun Khausar”

Cikin zurfafa nazari Moddibo yace.
“Kin tabbata Asma'u zata bamu haske kan batun?”.
Kai ta gyaɗa masa kana cikin gaskiya da gaskiya tace.
“Na tabbatar Yah Moddibo”.
Kallon Ummi dake Kallonsu yayi kana cikin ƙarfin gwiwa yace.
“Ummi”.
Cikin sanyi da tausayinsa tace.
“Na'am Babana”.
Cikin alamun samun nasara da jin daɗi yace.
“Ummi zamu fara bincike”.
Kai Ummi ta gyaɗa kana cikin wani irin yanayi tace.
“Nikam ina tsoro Babana ina tsoron kada kaima Azo acutar mana da kai ina tsoro kada wani abu ya sameka kawai abar maganar nan”.
Cike da mamaki da kuma sanyi Moddibo yace.
“Ummi tayaya”.
Girgiza kai Ummi tayi kana tace.
“Babana Abar Maganar kawai”.
Kai ya gyaɗa mata sannan suka dauka wani hiran sosai kowannen su ya samu nutsuwa sosai sukaji damuwar suya fara raguwa kaɗan sai bayan da Moddibo yayi sallar maghariba kafin yayiwa Ummi Sallama ya tafi.

Bayan Sallar Isha'i Malam Arɗo ne zaune gaban Abba wanda baki ɗaya ya rame yayi wani iri dashi.
Kallonsa Malam Arɗo yayi kana yace.
“Toh Alh kaji yanda akayi kuma shine abinda ya kawo ni”.
Jinjina kai Abba yayi cikin yanayin sanyinsa yace.
“Nima nasani Jameelu ya faɗa min”.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da faɗin.
“Masha Allah abu yazo da sauƙi kenan”.
Jinjina kai Abba yayi kana cikin sanyi yace.
“Ba matsala Insha Allah zuwa jibi zamuyi kokari muyi maganar”.
Kai Malam Arɗo ya gyaɗa tare da cewa.
“Ayyah Jameelu Insha Allah zamu cika masa burinsa tunda har yayiwa Amininsa zaɓin mata yayi fatan ya haɗa wannan Auren kafin ya tafi zamu cika masa burinsa da izinin Ubangiji zamuyi ƙoƙarin cika wasiyyar daya bar mana”.
Kai Abba ya gyaɗa cikin sanyi ya gyara zamansa tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Insha Allah zan tsaya akan lamarin sannan zanyi iyakacin bakin ƙoƙarina ganin ancika masa duk kan wasiyyar daya bari”.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da jinjina kai yace.
“Insha Allah babu damuwa idan Allah yakai mu jibin zanzo ba matsala”.
Godiya Abba ya masa sannan Malam Arɗo ya masa Sallama ya tafi.

Bayan kwana biyu: Moddibo ya fito daga gida jikinsa sanye da Gezner fari soll yayin da kansa ke sanye da hula tangaran baƙa yalwataccen sumar kansa irin na Fulanin Usul yana kwance aƙeyarsa fuskarsa tayi fayau manyan Idanunsa na lumshe yayinda jikinsa ke fitar da sanyayyan ƙamshin tularen Oud Khareem kai tsaye gidan Ummi ya nufa bakinsa ɗauke da sallama ya shiga coumpund ɗin Abaranda ya hango Asma'u na Morping Jin ƙaran buɗe ƙofa yasa Asma'u ta juya ganin Moddibo yasa tace.
“Yah Moddibo sannu da zuwa ka iso mana”.
Ahankali ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Ummin fa naji gidan shiru?”.
Tana matse mopan dake hannunta tace.
“Bata nan”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Ke kaɗai ce agida?”.
Girgiza kai tayi kana tace.
“A'a Bashir na ciki?”.
Kai ya gyaɗa tare da gyara zaman hular dake kansa kana yace.
“Ina Ummi taje?”.
Ahankali ta jinginar da Moper kana tace.
“Ummi ta tafi asibiti saboda kwanan nan ciwon kai yana yawan damunta taje adubuta”.

Cike da kulawa da kuma sanyi yace.
“Subhanallah toh Allah ya sawwaƙe”.
Ahankali Asma'u tace.
“Ameen”.
Moddibo kuwa gyara tsayuwar sa yayi cike da nutsuwa da kuma sanyi yace.
“Asma'u zo muje ki rakani gidansu.
Khausar akwai tambayoyin da nake so nayi mata”.
Kai Asma'u ta gyaɗa cike da jin daɗin hukuncin da yake son ɗauka tace.
“Toh Shikenan Yah Moddibo bari in kira Ummi in Faɗa mata”.
Cikin sauri ya girgiza mata kai kana yayi ƙasa da muryarsa yace.
“A'a kada ki faɗawa Ummi, zata hana mu binciken idan kika faɗa mata zata hana amma yanzu kiyi sauri muje kafin ta dawo yanzu zamu dawo”.

Jinjina kai tayi tare da faɗin.
“Toh shikenan”,Sannan tashiga ta dauki Maroon hijabinta har ƙasa kana ta kalli Bashir dake karatun wani littafi na addini tace.
“Bari muje gidan su Khausar nida Yah Moddibo”.
Ta Ida maganar tare da fitowa.

Miƙewa Bashir yayi tare da fita kana yace.
“Laa Yah Moddibo Sannu da zuwa”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Yawwa Bashir koda Ummi ta dawo kada ka faɗa mata can mukaje kace gidan Innayi muka je”.
Ahankali Bashir ya gyaɗa masa kai kana yace.
“Toh shikenan Yah Moddibo sai kun dawo”.
Suna fita suka shiga mota kana Moddibo yaja suka tafi.

Acan gidan Lamiɗo kuwa cikin sauri Khausar ta fita daga side dinsu ta nufi sashen Gimbiya Bunayya tun kafin ta ƙarasa shiga tace.
“Ummah!, Ummah!!Ummah!!!”.
Daga ciki Hajiya Bunayya tace.
“Na'am”.
Khausar na karasa shiga tace.
“Ummah Raudat tashigo?”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa kana tace.
“Eh tashigo”.
Ƙarasa shiga Khausar tayi tare da Hararan Raudat dake ɓuya tace.
“Raudat kizo muje in miki wanka amma sai wani bauɗewa kikeyi tun ɗazu kina ta gudu”.
Maƙale ka faɗa Raudat tayi tare da tura ƙaramin bakinta tace.
“Ni dai na faɗa miki bana son wankan nan akwai sanyi”.
Cikin rarrashi Khausar tace.
“To ai da ruwan ɗumi zan miki”.
Girgiza kai Raudat tayi tare da tura bakinta tace.
“Ni dai Banason gaskiya”.
Ganin tana son ɓata mata lokaci yasa Khausar ta shiga tare da janyo hannunta tace.
“Maza wuce muje in miki zan baki waya kafin fito kiyi game”.
Bubbuga kafa Raudat tayi cike da Shagwaɓa tace.
“Addah Khausi Ni dai ki ƙyaleni bana so”.

Ahankali Khausar tayi ƙasa da muryanta tace.
“Harda Game ɗin bakya so?”.
Ware Ido Raudat tayi tare da ƙyalƙyala dariya kana tace.
“Allah dagaske Addah Khausi zaki bani?”.
Murmushi Khausar tayi tare da lakace mata hanci tace.
“Eh”.
Suna shiga Bedroom ɗin Raudat ta zauna gefen gado sannan Khausar ta mika mata wayar bayan tasa mata game ɗin _Subway surf_ ta bata murmushi Raudat tayi kana ta fara buga game ɗin.
Khausar kuwa dogon rigar jikinta ta cire tare da ɗaura towel iya ƙugunta ta shiga toilet.

Akuma dai-dai lokacin Moddibo yayi Parking afarfajiyar gida dai dai nan Lamiɗo ya fito da motarsa ganin Moddibon yasa Lamiɗo yayi Parking din motarsa ya fito cikin sauri Moddibo ya ƙarasa kusa dashi tare da basa hannu sukayi Musabaha cike da kulawa Lamiɗo yace.
“Moddibo bar kadai ya gida ya kuma Ƙarin haƙurin rashin Jameelu?”.
Cikin sanyin Murya Moddibo yace.
“Alhamdulillah hakuri mungode Allah”.
Cike da kulawa Lamiɗo yace.
“Allah ya gafarta masa ayi ya masa addu'a”.
Cikin sanyin yace.
“Ameen Mai Martaba Nagode.
dama munzo wajen Khausar ce”.
Cike da kulawa Lamiɗo yace.
“Toh ba matsala Asma'u ku isa”.
Ahankali Moddibo yayi ƙasa da kansa tare da cewa.
“A mai Martaba baza'a a bari daga nan ba”.
Girgiza kai Lamiɗo yayi kana yace.
“Ku shiga ba matsala bari na kira Aysha in Faɗa mata”.
Hannu ya sanya a aljihunsa tare da ciro wayarsa yayi dearling number Mommy tana ɗagawa yace.
“Aysha ga baƙi Moddibo da Asma'u zasu shigo”.
Cike da kulawa Mommy tace.
“Toh ba damuwa su shigo mana”.
Katse wayar Lamiɗo yayi tare da yi musu Sallama kana ya shiga motarsa ya fita.
Moddibo da Asma'u kuwa suka nufi sashen Mommy suna isa bakin barandar Moddibo ya tsaya Asma'u ta ƙarasa shiga falon tare da cewa.
“Assalamu Alaikum”.
Shiru falon ba Kowa sai dai ko ina tsaf-tsaf kana ga ƙamshin dake tashi. Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe tare da nufar Bedroom din Mommy tana cewa.
“Mommy!, Ta ƙarasa tare da shiga Bedroom din Mommy dake sanye da hijabi tace.
“Asma'u kun ƙara so Ina Moddibo?”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh amma yana waje”.
Mommy na zama gefen gado tace.
“Toh kice masa yashigo mana ya zaki barshi atsaye”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh Mommy”.
Sannan ta juya tare da fita falon ta leƙa ƙofan Falon cikin sanyin Murya tace.
“Yah Moddibo wai kashigo”.
Ahankali ya ɗago kansa tare da buɗe Idanunsa dake lumshe yace.
“Toh”.
Sannan ya shiga falon da komai ke kintse yana fitar da sanyayyan ƙamshin ahankali ya zauna akan 1sitter dake fuskantar ƙofar Bedroom din Khausar.

Asma'u kuwa juyawa tayi tare da kallon Moddibo kana tace.
“Yah Moddibo bari in sanarwa Mommy ka ƙara so”.
Bata jira amsar saba ta nufi Bedroom ɗin Mommy.

Khausar kuwa ahankali ta fito daga toilet tare da juya kanta yalwataccen sumar kanta dake jiƙe ya mannu da wuyanta da kuma gefen fuskarta dake da damshin ruwa fararen cinyoyinta masu haske da santsi na ɗauke da damshin ruwa.
Ware Ido Raudat dake Game tayi tare da kife wayarta akan gadon kana ta dira tare da ficewa da gudu saida ta isa kofar Bedroom din kafin ta tsaya.
Cike da mamaki Khausar ke kallonta kana tana tafiya ahankali tace.
“Raudat ina kuma zaki je?”.
Tura baki Raudat tayi tare da juya Idanunta tace.
“A ni dai Banason wankan nan da kwai sanyi”.
Sake baki Khausar tayi wato ita Raudat zata yiwa wayau, ɓata fuska tayi tare da cewa.
“Aikuwa baki isa ba kisa in. Baki wayata kiyi game sannan yanzu kinga na fito kice zaki gudu”.
Gwalo Raudat ta mata tare da fita da gudu.
Ware ido Khausar tayi tare da bin bayanta da gudu dariya Raudat ta ƙyalƙyale dashi tare da nufar hanyar fita sai kuma ta karya kwana ta nufi Bedroom ɗin Mommy.
Khausar kuwa garin zata karya kwana ta nufi Bedroom din Mommy santsin ruwan dake ƙafarta da kuma santsin tlyes ya jata tayi baya Suuuuuu ta faɗi a ƙasa kana towel ɗinta ya since ya zame yayi ƙ...!



Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA.


By
*GARKUWAR MARUBUTA*SAKAYAH

34

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*LITTAFIN SAKAYYAH DAI NA KUDINE KO KIN GANSHI A WASU WURAREN DA BA WURINA BA TOH NA SATANE KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI BABU HAƘƘIN WANI A GANKI LITTAFIN SAKAYYAH 1K NE KACAL DUK DA YAWANSA DA DAƊINSA DUBU ƊAYA NEFA KACAL, ki biya dubunki ɗaya ki karanta maimkyau ba sallake-sallake babu kin samu wasu PAGE ɗin baki samu wasuba ki karanta abinki one by one tura kuɗin samun damar karantawa ta asusuna na GTBank. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 sai in tura miki karanta lfy lafiya. Mu guji yaƙin wani duk ƙanƙantarsa domin na watan nan dai na Allah ya isane atoh*

Towel din na sincewa ya zame yayi ƙasa, manyan caɓɓullenta masu haske da sheƙi suka bayyana a fili, yayinda ita kuwa ta zame tayi ƙasan cikin jin zafi da raɗaɗi ta guiwowinta da suka bugu tayis ɗin ta runtse Idanunta cike da raki tace.
“Washhh! Allah Mommy na”.

A can cikin daki kuma
Kallon Asma'u Mommy dake ninke kaya tayi kana tace.
“Asma'u ki kai masa abin taɓa wa yanzu zan fito”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh Mommy”.
Kana ta fita.
Moddibo kuwa baki daya abinda ya faru akan Idanunsa ya faru cikin wani irin yanayi ya ware manyan idanunsa dake ɗauke da launin Ja akan tantsama-tantsaman caɓbulenta da suke tsaye cirko cirko dasu masu masifar haske da sheƙi kana kansu sunyi ja sai sheƙi da ɗaukar ido suke haka zalika har ramin cibiyar ta yana ɗan iya hangowa.
Atake yaji zuciyarsa da A ɗinsa sunyi wani irin harbawa da masifaffen ƙarfi tamkar zasu fito waje ya taka rawa.
Cikin wani irin sauri ya matse ƙafafunsa da masifan ƙarfi kana ya shiga ƙoƙarin rintse idanunsa da don janyesu daga kan abinda ke ƙoƙarin tafiya da nutsuwarsa da kuma numfashinsa amma baki ɗaya ya kasa janye Idanunsa dake kan manyan caɓɓullen ta dake neman zautar dashi bare yayi nasarar kawar da kansa.

Akuma dai-dai lokacin idanun Asma'u data fito yanzu suka sauƙa akan Khausar dake kwance ƙasa cikin sauri ta nufi kanta tana faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n sannu Khausar”.
Khausar kuwa jin Muryar Asma'u yasa tayi saurin ɗago kanta Atake Idanunsu suka sarƙafe dana Moddibo daya wani irin zuba mata mayatattun idanunsa da suka sake canza launi ko ƙyiftawa ba yayi sai lips dinsa da suka fara rawa kar-kar.
Cikin wani irin yanayi na tsananin kunya da zafi Khausar tayi saurin janye Idanunta daga nasa ta mayar ganinta dai-dai inda ya tsiwara Ido cike da masifaffen kunya ta rintse Idanunta ganin yadda ya tsare.
Ƙirjinta Ido musamman saman Nipples ɗinta da sukayi ja suna tsaye cir dasu tamkar zasu tsole masa ido.
Asma'u kuwa na ƙarasawo tayi saurin sanya hannunta tare da ɗagota kana tace.
“Subhanallah Khausar sannu”.
Cikin wani irin karfi mai haɗe da kunya Khausar ta janyo towel ɗin sama tare da miƙewa da gudu ta koma Bedroom ɗinta yayin da zuciyarta ya cigaba da bugawa da masifaffen ƙarfi kana gaba ɗaya ilahirin jikinta na rawa babu kalmar da take maimaitawa face Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n, jingina bayanta da jikin wodurob tayi cikin tsanananin kunya da takaici gami da tsoro still jikinta na cigaba da rawa.
Asma'u kuwa bayan Khausar tabi ganin yanda ta jingina da jikin wodurob baƙi ɗaya ilahirin jikinta na rawa yasa cikin sanyin murya Asma'u tace.
“Sannu Khausar”.
Kallonta kawai Khausar keyi.
Asma'u kuwa murmushi ne ya subce mata ganin yanda gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa, sai kuma ta tuna yanda. Moddibo ya zubawa Khausar ido yana kallon Breast ɗinta tamkar wani zautacce sai kuma ta tuna yanda jikin Khausar ke rawa yana wani irin tsuma bisalamu gani take kamar mafarkine haka ne yasa Asma'u sakin.
Dariya tare ƙyalƙyalewa har tana dafe gefen cikinta, kana ta cigaba da ƙyalƙyala dariya tana nuna Khausar da hannu.

Khausar kuwa Ido ta zubawa Asma'u madadin haushin dariyar da Asma'u ke mata da ji ciwon guiwowinta keyi ta sinci kanta da zubawa Asma'u ido kana aranta tace Allah sarki Asma'u rabon da inga dariyar ki haka tun kan a sace Yah Jameel sai yau, hakan yasa ta gyara tsayuwarta tare da sake ɗaure towel ɗinta da kyau Asma'u kuwa dariya ta cigaba dayi harda hawaye da zaran ta tuna yanda Moddibo ya kafe kirjin Khausar ɗin da ido da kuma yanda Khausar ta zare ido sai ta sake ƙyalƙyalewa da dariya.
Cikin sanyin murya me ɗauke da tsoro da kuma kunya tace.
“Kin gama dariyar!?”.
Kallon ta Asma'u tayi still tana riƙe da cikinta kana da murmushi afuskarta tace.
“Ikon Allah lallai Yah Moddibo Yayi farin gani”.
Harara Khausar ta watsa mata tare da tura bakinta kana tace.
“Ɗan Iska kawai harda wani tsayawa ya tsura min ido sai kace maye, wato ya samu gani na bati ko? toni dai Yaseen ban yafe ba ato”.
Dariya Asma'u ta kuma ƙyalƙyalawa dashi ganin yanda Khausar tayi kicin-kicin da fuska kana har zuwa lokacin jikinta bai daina rawa ba.
Ahankali Khausar ta zauna gefen gado tare da kallon Asma'u da har zuwa lokacin fuskarta ɗauke da murmushi tace.
“Tukunna ma wai meye kawoshi gidan mu har cikin falon Mommy na!?”.
Zama Asma'u tayi agefenta tare da cewa.
“Wajenki yazo”.
Wani kallo Khausar ta mata tare da ɗage girarta na dama tace.
“Wajena kuma lallai ya kama tashar da ba Passenger. Dan wallahi babu inda zan fita ya samu damar ƙare min kallo dan yanzu ko ariga ya gani nasan zai iya siffanta kamannin su”.
Wani sabon dariya Asma'u ta fashe dashi tare da faɗin.
“Um-um Fattanah banda dai sharri kallon second nawa ya musu da har zaki ce zai iya siffanta wa a'a kin manta drawing zaiyi kamar ba shiba”.
Duka Khausar ta kai mata cikin Sauri Asma'u ta kauce tare da cewa.
“Ke kuwa abin kallo ya samu ai dole abawa Ido hakkinsa”.

Anutse Mommy ta fito daga Bedroom tare da kallon Moddibo da har zuwa lokacin Idanunsa ke kan inda Khausar ta faɗi cike da kulawa tace.
“Maraba Moddibo”.
Jin muryan Mommy ya ratsa dodon kunnensa yasa yayi saurin lumshe idanunsa da sai yanzu ya samu dawowa nitsuwarsa matse jikinsa yayu tare da jan ajiyar zuciya kana ahankali ya fesar da wani numfashi mai Masifarr nauyi mai ɗauke da wani irin yanayin na tsananin matsuwa.
Kana cikin sanyi ya sake sunkuyar da kansa ƙasa yayin da ya sake matse muhallinsa da yaji yana neman fallasashi cikin sanyun murya yace.
“Ina yini Mommy ya gida fatan mun same ku lafiya? Ya hakurin rashin Ramadan”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da cewa.
“Lafiya lau Alhamdulillah haƙuri ya zama dole”.

“Allah ya jinƙasa da rahama”.

“Amin ya Allah, ai Lamiɗo ya gayamin kunzo ta'aziyar ne kuka samu labarin Jameel shiyasa baku isoba”.
Cikin nitsuwa yace.
“Eh”.
Sassayan numfashi Mommy ta fesar kana tace.
“Ya karin haƙurinmu.da wajensu Ummi?”.
Kansa a ƙasa yace.
“Alhammadullih. Ummi na lafiya tace ma agaisheki".
Mommy kuwa kallon falon tayi tare da Kallonsa kana tace.
“A'a Ina su Asma'u kuwa?”.
Cikin sauri Raudat dake tsaye bayan Kushin tace.
“Mommy Adda Asma'u tana ɗaki Addah Khausi kuma tana ta dariya”.
Jin haka yasa Mommy ta ɗaga sautin Muryanta tare da cewa.
“Asma'u”.
Cikin sauri Asma'u ta fito tare da cewa.
“Na'am Mommy”.
Ahankali Mommy ta kalleta tare da cewa.
“Asma'u kinzo kin bar baƙo shi kaɗai ko ruwa baki kawo masa ba?”.
Cikin sauri ta nufi hanyar kichen tare da cewa.
“Toh Mommy bari na kawo masa”.
Ta faɗa tare da shiga kichen ta buɗe fridge kana ta ɗauki Plate tasa masa ruwa da exotic ta fito ta ajiye masa agabansa kallonta Mommy tayi tare da cewa.
“Ina khausar kuma?”.
Satan kallon idon Moddibo Asma'u tayi sai taga hankalinsa na kan inda Khausar ta faɗi har yanzu bai cire idoba, cikin ƙasa da murya tace.
“Mommy khausar fa tace baza ta fito ba!”.
Kallon mamaki Mommy tayi mata kana tace.
“Ha'a baza taxo ta Gaishe da Malamin su ba kuma?”.

Kai Asma'u ta gyaɗa tare Da yin ƙasa da kanta tace.
“Eh Mommy faɗuwa tayi kuma taji ciwo a Ƙafarta”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh bari Inje in ganta”
Anutse Mommy ta nufi ɗakin bakinta ɗauke da sallama ta shiga a inda Asma'u ta barta azaune anan Mommy ta shigo ta sameta bata ko motsa ba.
Ahankali Mommy ta zuba mata ido ganin yanda ta lumshe Idanunta tare da rungume hannunta aƙirji har zuwa lokacin towel ne ajikinta kana zuciyarta na cigaba da bugawa da masifar ƙarfi cikin sanyi murya Mommy tace.
“Khausar baza ki fito ki Gaishe da Malamin kuba”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da Shagwaɓe murya kana tace.
“Mommy faɗuwa fa nayi kuma naji ciwo aƙafa na bazan iya fita ba”.
Girgiza kai Mommy tayi tare da ɓata fuska kana tace.
“A'a sai kin fita ya za ayi Malamin ki yazo kuma kice baza ki fita ki Gaishe sa ba kema kinsan bai dace ba! Kuma ma ta'aziyyar Ramadan yazo mana fa”. Ta faɗi hakan dan ita a tunaninta gaisuwar Ramadan ɗin yazo musu.
Saurin Kallonta khausar tayi tare da yin Rau-rau da ido Muryanta na rawa tace.
“Don Allah don darajar Manzon Allah (S.A.W) Mommy ki bari ba sai nafi ta ba. Ni dai gaskiya bana son fita Mommy kawai ki barni ai mun gaisama fa”.

Cikin tsira mata ido Mommy ta jingina bayanta da jikin ƙofar kana babu walwala afuskarta tace.
“Kin tabbata?”.
Kai ta gyaɗawa Mommy ba tare da tace Uffanba saima ƙasa da tayi da kanta

72 / 140

Chapters