Author : Aisha Aliyu Garkuwa Category : Free Novels Online (Read & Download)
fito da wanda kike so, tun kafin kakar ki tazo ta buwayemu da batun Aurenki.
Kinga dama ta ajiye target ne kina gama Secondary school magana ya ƙare za azo ayi miki aure”.
Ajiyar zuciya ta sauƙa kana ta cigaba da cewa.
“Idan kuma kinƙi baki da hujjar da zaki ƙi Auren Aliyu, dole kibi zaɓin ta dan haka ma gwara ki tsaida zuciyarki kisan me kike ciki don in duniya duk zasu taru babu mahluƙin da zai hana batun wai kin gama secondary School za'ayi miki aure, tunda har Hajja Nana ta rantse, dan haka gwara kawai ma ki tsaida zuciyarki, ki fidda mijin da zai iya barinki kici gaba koda kinyi aure, kuma da fidda wanda kike sone, zamu samu hujjar nuna mata kinada wanda kike son”.
A hankali Khausar ta janye idonta daga kallon Mommy kana tace.
“To amma ni gaskiya ba zanje.
Falon Gimbiya Dadu ba”.
Ɓata fuska Mommy tayi babu walwala atare da ita tace.
“Maza ki wuce kije idan ita kura ce to ta cinye ki”.
Miƙewa Khausar tayi badan ranta yaso ba sai dan ganin yanda Mommy ta ɓata rai yasa ta ɗauki hijabinta dake fitar da ƙamshi sanya kana ta fice.
Acan ɓangaren su Moddibo kuwa zaune suke aɗakin Innayi shi da M Jameel bayan sun kammala cin abinci Anutse ya miƙe tare da kallon Innayi da suke magana da M Jameel ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Innayi saida safe”.
Kallon sa M Jameel da mamaki afuskarsa yace.
“Zaka je ka kwanta fa kace?”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Eh”.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare da faɗin.
“Ok nima zan tafi gida”.
Ahankali Moddibo ya buɗe Idanunsa dake lunshe kana yace.
“Mu kwana anan mana tunda har ƙarfe takwas tayi”.
Girgiza kai M Jameel yayi tare da miƙewa kana yace.
“A'a ina so Inje gida”.
Kallon yanayin fuskarsa Moddibo yayi tare da cewa.
“Dan Allah mu kwana mana”.
Ataƙaice M Jameel yace.
“A'a tafiya zanyi”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauke tare da cewa.
“Toh shikenan ni zanje in kwanta”.
Ya Ida maganar tare da ficewa.
Da kallo Innayi da M Jameel suka bisa har ya ɓacewa Kallonsu.
Moddibo kuwa yana shiga falonsa yayi saurin yarfe hannunsa tare da jan tsaki tare da jan numfashi kamar wanda yaci yaji lokaci ɗaya lips ɗin sa suka kama rawa cikin yanayin damuwa ya dafe kansa tare da cewa.
“Ya salam³,Wannan wani irin al'amari ne meke mai wuyar ɗauka haka?”.
Cikin mutuwar jiki ya wuce kichen tare da ɗaukan Cup ya ɗauraye ya zuba ruwan Tea kana ya yanka lemun tsami ya matse sannan ya zuba zuma ya kafa kansa ya shanye tass, ajiye Cup ɗin yayi ya fita zuwa Bedroom ɗin sa yana shiga ya kwanta ko minti ɗaya baiyi da kwanciya ba yayi saurin miƙewa ya zauna cikin sauri ya sake komawa ya kwanta tare dayin ruf da ciki cikin wani irin yanayi yasanya hannunsa duka biyu ya danne mararsa saboda wani masifaffen harbawa da yakeyi.
Acan ɓangaren Gimbiya Dadu kuwa cikin sanyi jiki Khausar ta buɗe ƙofar falon tare da Sallama tana shiga ta...!
*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki littafin 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, kana in saki a Group ɗin da zanke posting nashi, yar uwa koda kinga LITTAFIN SAKAYYAH A WAJE TO na satane, in dai kin san baki biya kadama ki karanta.*
*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*
Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.
Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.
Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.
GARKUWAR MA'AURATA
*By*
*GARKUWAN MARUBUTA*SAKAYAH
20
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Ujnr. Tana shiga ta sauƙe numfashi ganin babu. Gimbiya Dadu, falon shiru ba kowa sai Uncle Naseer dake zaune kan 3sitter yana riƙe da system akan cinyarsa da kuma wayarsa.
Yana ganinta yayi saurin rufe system ɗin kana ya zira wayarsa acikin aljihu tare da tsira mata idanu afili ya furta.
“Wowww Masha Allah kinsha kyau My Dear”.
Batare da tace komai ba ta ƙara sa shiga falon tare da yiwa kanta masauƙi akan 1sitter.
Tsuke fuska yayi tare da zuba mata idanu kana yace.
“Meyesa ba zaki zauna akusa dani ba My Khausi?”.
Kallonsa tayi da lumsassun idanunta kana da alamun bacci acikin Muryanta tace.
“Unclr Naseer nan ma yayi”.
ta ƙarasa maganar tana mai lumshe Idanunta.
Ido ya tsira mata yana kallon yanda ta lumshe sexy Eyes ɗin ta miƙewa yayi tare da dawowa kusa da ita ya zauna a hannun kujeran, yana shaƙan daddaɗan ƙamshin turarenta, Khausar kuwa jin alamu sa akusa da ita yasa tayi saurin buɗe Idanunta dake lumshe kana ta miƙe da niyyan barin wajen.
Cikin hanzari ya sanya tafin hannunsa dake ɗauke da zoben azurfa ya riƙe nata yana binta da wani mayataccen kallo.
fuskarta ta yamutsa cikin ɗaure fuska kana da rashin walwala tace.
“Me haka Uncle Naseer?”.
Langwaɓar da kai yayi tare da tsaida idanunsa cikin nata kana ya karyar da murya tare da faɗin.
“Guduna zakiyi?”.
Kai ta girgiza masa tare da lumshe Idanunta jin bacci na fusgarta kana tace.
“A'a ba gudunka nake ba kawai dai ai baidaceba”.
Karyar da muryarsa yayi tare da yi mata kallon Up and down kana yace.
“Toh ki zauna anan ni dodone, ko kuma cinye ki zanyi mai yasa kike min haka ne Khausar”.
Kai ta girgiza tare da gyara hijabinta kana tace.
“Bai dace bane Uncle Naseer haka baiyi ba ni ka sakar min hannu”.
Wani kallo ya watsa mata kana yace.
“Bazan sakar miki hannu ba”.
Ya ida maganar yana latsa mata hannu tare da yi mata tafiyar tsutsa.
Cikin fushi ta.
Fisge hannunta tare da galla masa harara kana tace.
“Ni gaskiya banason abinda kake min banaso sam”.
Ta Faɗa tare da juyawa zata bar masa falon.
Da sauri ya miƙe tare da shan gabanta kana ya durƙusa akan gwiwoyinsa tare dasa hannunsa duka biyu ya riƙe kunnensa cikin wata. Sanyayyar murya mai cike da lallashi ya zuba mata ido tare da cewa.
“Na tuba dan Allah kiyi haƙuri, bazan ƙara ba Insha Allah, ki gafar ceni kinji My dear.
Dan Allah Dan darajar Annabi Muhammad (S.A.W) kiyi haƙuri ki koma ki zauna naji Ni zan zauna a ƙasa”.
Jin haka yasa ta saki ajiyar zuciya tare da komawa ta zauna.
Murmushin gefen baki ya saki tare da miƙewa ya zauna aƙasan Capet mai taushi dake malale Atsakiyar falon tare da yin tagumi kana ya tsira mata Idanu, tare da saki ajiyar zuciya langwaɓar da kai yayi kana yace.
“Khausar ina sonki, ya zanyi idan har kikayi fushi dani rayuwata ba zata yimin daɗi ba. Duniyar nan zata yimin duhu matuƙar dai kikayi fushi dani, hankalina ba zai kwanta ba.
Kada ki mancefa na yarda nabi duk dokan da aka samin nacewa kada in sake inyi miki maganar soyayya har saikin kammala Secondary school, ni Kuma na kammala karatuna”.
Ajiyar zuciya ya saki tare da fesar da numfashi kana yace.
“Bisa wannan sharaɗin aka hanani koda jin Muryan kine Koda na Kira Mommy mun gaisa baza ta baki mu gaisa ba, haka nayi ta dakon soyayyarki azuciyata, duk tsawon shekarun nan da nayi a India ina ɗauke da dakon soyayyarki Khausar, Ina son ki³ kinsan tsawon shekara shida ba wasa ba I miss you, I really love you Matata, kece farin cikina kece sirrina kece duniya ta Khausar will you Marry me?”.
Ahankali tayi ƙasa dan kanta har ga Allah batasan mai zata ce dashi ba.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Khausar zaki Aureni!?”.
Lallausan tafin hannunta tasa ta rufe fuskarta batare data bashi amsa ba.
Shi kuwa Naseer murmushi ya saki kana yace.
“Nagode My Khausi”.
Domin shi duk azatonsa kunyarsa da kuma rufe fuskar da tayi sonsa take.
Cikin Sanyayyar murya mai taushi da kulawa ya kalleta kana yace.
“Kece Sirrina duk abinda zanyi aduniya dole ke sirrina ce, dake zanyi shi abubuwa biyu ne suka dawo dani ƙasar nan Khausar,
akwai mahaɗin abinda ya dawo dani ƙasar nan sai kuma burin mallakar ki da fatan kasancewarki mallakina na har abada”.
Cikin sanyin murya mai ratsa zuciyar duk wanda ya saurara tace.
“Uncle Naseer kace Ubangiji ya mana zaɓi msfi al'khairi, duk abinda muke so aduniya mu barwa Ubangiji zaɓi kaji ko Uncle Naseer”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Naji Nagode amma ina da wata alfarma da nake so in nema awajenki shin zakiyi min shi?”.
Cikin sanyi da alamun bacci a idanunta tace.
“Eh Uncle Naseer in baifi ƙarfina ba zanyi maka shi”.
Gyara zamansa yayi tare da cewa.
“Kinyi alƙawari?”.
A hankali ta buɗe Idanunta sosai akansa kana tace.
“Toh ai ban sani ba yafi ƙarfina ko baifi ba”.
Langwaɓar da kai yayi tare da cewa.
“Baima fi ƙarfin kiba Khausar. Insha Allah bai fi ƙarfin ki ba zaki iya ba abune na kokuwa ko dambeba sannan ba mugun abu da zai saɓawa Addinmu bane".
Ajiyar zuciya ta saki kana tayi murmushi tare da cewa.
“Allah dagaske!?”.
Ka ya jinjina mata kana yace.
“Eh dagaske”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan Uncle Naseer”.
Idanu ya tsira mata tare da faɗin.
“Kinyi alƙawari zakiyi min!?”.
Wara manyan Idanunta tayi tare da cewa.
“Bana so ina ɗauki al'ƙawari bansan kuma menene bane!”.
Cike da manufa ya karyar da murya tare da cewa.
“Ni dai nafi son kiyi min al'ƙawari, zaki te maki rayuwata, da kuma cigaban mu, da Kuma jin daɗin ki kinji ko Khausar, saboda jin daɗina da jin daɗin ki nakeso muyi wannan abin kuma wannan sirrin mu ne amatsayin ki na matata dan ko mahaifiyata bata san wannan sirrin ba!”.
Nan-nauyan ajiyar zuciya Khausar ta saki Idanunta akansa tace.
“Toh wannan wani irin sirrine ka faɗa min mana”.
Kai ya Girgiza tare da cewa.
“A'a har sai kinyi al'ƙawari zaki min abun zan faɗa miki”.
Girgiza kai tayi kana tace.
“Yaya Naseer bana so in maka al'ƙawarin da ban sani ba ko bazan iya ba”.
fesar da iska mai sanyi yayi tare da kallonta kana yace.
“Zama ki iya”.
Kallonsa tayi ganin yanda ya marairaice yasa ta saki Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Toh shikenan sai nayi shawara”.
Da sauri ya kalleta tare da cewa.
“Shawara kuma da waye zakiyi shawara? bana faɗa miki siririn mu bane! Sirrina ne dani dake kasancewar abu ɗaya zamu kasance, zaki kasance matata kuma uwar ƴaƴana kece zaki kasance ruwa mai kashe min ƙishina”.
Sauƙe sanyayyar Ajiyar zuciya tayi tare da faɗin.
“Toh shikenan sai nayi tunani”.
Langwaɓar da kai yayi tare da cewa.
“Zuwa yaushe?”.
Shiru tayi alamar tunani sai kuma tace.
“Zuwa gobe ko jibi”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan ba damuwa Allah ya kaimu muyi hira mana”.
Marairaice fuska tayi kana tace.
“Ayyah Uncle Naseer bacci nake ji”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Toh shikenan muje inda rakaki”.
Batace komai ba tashige gaba yana biye da ita, tare da zubawa ƙugunta idanu saida ta shiga falo sannan ya koma ya shiga motarsa ya wuce gida.
Acan ɓangaren Moddibo kuwa awannan dare haka ya kwana cikin mawuyacin hali saboda wani azabebben yanayi dake damunsa sai. Wajajen ƙarfe uku da rabi wani irin bacci mai shegen daɗi ya ɗauke sa.
Can cikin baccin nasa ya fara wani irin bahagon mafarki, ganinsa yayi tare da Khausar, suna kwance akan gado ɗaya cikin wani irin ni'imtaccen bargo fari ƙal mai masifar taushi, kana babu komai a jikinsu yana rungume da ita hannunsa na dama nakan yalwataccen sumar kanta mai ƙamshi da sheƙi yana shafawa, yayin da ɗaya hannun ke kan caɓullenta yana murzawa.
Cikin Sanyayyar murya mai cike da shagwaɓa Khausar ta sakar masa wani irin narkekken kuka tare da cewa.
“Tsoro nake ji nikam bazan iya ba Moddibo kabar ni bazan iya ba”.
Shi kuwa Moddibo karyar da murya yayi cikin tattausan murya mai cike da salama yake lallashinta.
Ƙarfe huɗu dai-dai ya farka sakamakon kiran sallar assalatu da akayi miƙa yayi tare da furta.
_“Alhamdulillahi lazi ahyana bada amatana wa'ilaihin nushur”_.
Kana ya tashi zaune yana kallin Boxes ɗinsa da ya bada damshi alamar yayi ta liking.
Cikin sauri ya furta.
“Ya Salam Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n nashiga Uku”.
Da sauri ya miƙe tare da dafe kansa kana yace.
“Innalillahi Wa'inna ilahi rajiu'n, shin wannan wace irin Masifa ce mai nacin tsiya da bibiyata, madadin abin nan yayi baya kullum sai gaba-gaba yake yi, yanzu abin har yakai matakin mafarkin yarinyar nan nakeyi wannan wace irin rayuwa ce? In banda ma rashin kunya da raini ya za'ayi yarinyar nan ta biyoni har cikin bacci na”.
Sake kallon boxes sa yayi dan tabbatar wa still gani yayi zahiri ya jiƙe da yarinyar amafarki, cike da tafasan zuciya ya shafa Dk ɗin sa dake bayyana zalamarsa duk da cewa yayi liking.
Amma bai nitsuba ba zama yayi abakin gado tare da dafe kansa da hannu biyu ji yake tamkar ya fashe da kukan takaici.
“Tabbas da ace mafarki na zama gaskiya to da sai na sumar da yarinyar nan, ta yadda har abada bazata sake zuwan min ba”. yayi mgnar a sama lips inshi.
Ahankali kuma sautin muryanta yashiga dawowa cikin kunnensa tana cewa.
“Tsoro nakeji bazan iya ba Moddibo”.
Wani dogon tsaki yaja kana cikin wani irin fushi ya miƙe tare da lumshe idanunsa tabbas badan amafarki bane da sai yayi maganin yarinyar.
Toilet yashiga tare da wanka kana ya ɗaura Al'wala duk zuciyarsa babu daɗi bayan ya shirya ya tafi masallaci.
Bayan kwana biyu kamar ko yaushe Anutse Khausar ce ta fara miƙewa kana tayi submitting ɗin Booklet ɗin ta yayin da sauran ɗalibai ke cizon gindin biro sosai Exam ɗin Nahwun ya basu wahala ahankali. Khausar ta fita tana lumshe Idanunta duk da cewa ta saba answering questions kafin abasu amsa amma na yau ya wahalar da ita ajikin Up stair ta tsaya tare da ɗaura hannunta akan step ɗin sama kana ta zu bawa farfajiyar makarantar Ido, sanyayyan iska na kaɗata tsayuwar ta da kamar minti biyar wata baƙar mota tazo ta faka ta bada baya.
Cikin sauri ta zare Ido tare da kallon number motar cike da mamaki da al'ajabi ta mitsika Idanunta tare da sake kallon number motar cikin rawan murya tace.
“Wannan Motar Again?”.
Tabbas wannan shine motar da tagani a Jauro Yaya a lokacin da suka tafi Rafi dasu Dija still, kuma aranan aka kashe Baffa Umaru tabbas kamannin motar da kuma Number ba zasu taɓa ɓace mata ba to amma mai yazo yi amakarantarsu.
Kallon motar ta sake yi still Yana tsaye cikin sauri ta fara taka step ɗin tana haɗawa bibbiyu har ta sauka kana ta nufi gate.
Da sauri Baba Mai gadi ya miƙe tare da cewa.
“Khausar ina Zakije?”.
Kallonsa tayi tare da cewa.
“Saƙo zan amsa awajen masu wancan motar”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Kinsan dokar makarantar nan bata bari idan anshiga afita amma kina amsa ki dawo”,
Kai ta gyaɗa tare da ficewa shi kuma yabi bayanta.
Ahankali ta tsirawa number motar Idanu kana cikin sanyin jiki ta nufi motar.
Mutanen dake Cikin motar kuwa sam basu lura da ita ba saida taje gab dasu suka lura da kamar tana leƙa su ne, kana ga dukkan alamu Idanunta na kan Plate number motar cikin sauri suka ɗaga glass ɗin motar dake ƙasa.
Khausar kuwa cikin sauri ta nufi gaban motar dan ganin fuskokin su waye ne, mutumin dake zaune a mazaunin Driver ne yayi saurin figar motar da mugun gudu suka tafi.
Cike da mamaki Khausar ta dafe kuncinta tare da cewa.
“Ha'a to meyesa haka?”.
Anutse ta juya bayanta jin Muryan Baba mai gadi na cewa.
“Toh ya kuma ba abinda suka baki suka ja mota da gudu haka suka tafi?”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kallon Baba mai gadi kana tace.
“Agaskiya bansan suba fa, amma dai na taɓa ganin motar acan Rugar mu shiyasa yanzu na saƙƙo inga shin wannan motar ce ko kuma watace, kuma na gane motar ita ɗin ce, kuma awannan ranan ma dana gansu haka suka gudu”.
Kai Baba mai gadi ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh Allah yasa dai lafiya?”.
Nan-nauyan ajiyar zuciya ta saki tare da furzar da iska mai zafi daga bakinta kana tace.
“Ka kula gaskiya Baba mai gadi, ka kula duk sanda kasake ganin wannan motar ka faɗa min”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Toh shikenan amma ai kalar motoci da yawa taya zan gane wannan?”.
Sauƙe numfashi tayi tare da faɗin.
“Aina riƙe number”.
Bata jira cewarsa ba ta janyo biron dake kanta tare da yagar ƙasan Qautions paper ta rubuta masa number tare da miƙa masa kana tace.
“Gashi ka riƙe duk sanda ka sake kallon tazo bakin makarantar nan, ka faɗa min ni ban