Author : Aisha Aliyu Garkuwa Category : Free Novels Online (Read & Download)
saka da alkhairi”.
Hannunsa Malam Arɗo ya riƙe bayan ya mike suka fita kai tsaye bangaren ƴan primary suka fara shiga Ajinsu Ramadan da Raudat yaran na ganinsa suka miƙe cike da farin ciki suna cewa Moddibo Moddibo Kusan a tare Raudat Ramadan da wasu ɗalibai uku suka ce Moddibo ina Malam Jameel munyi kewar ku bakwa zuwa.
Lumshe Idanunsa da yaji suna masa zafi da zaran an ambaci sunan J ɗin sa zuciyarsa zata buga da masifar ƙarfi tsayuwar sa ya gyara agaban ajin tare da cewa.
“Ina ɗaliban Malam Jameel?”.
Baki ɗaya yaran suka ɗaga hannu suna tsalle tare da cewa gamu nan Moddibo ina yake munyi kewarsa bakwa zuwa yanzu, dan Allah kace yazo muna san ganinsa.
Kasa furta komai Moddibo yayi hakan yasa ya jingina bayansa da jikin bango yayi ƙasa da kansa yasan yanda J ɗin sa ke son Yara da kuma wasa da su wanda a ra'ayinsa baison koyar da yara amma saboda yanda J ɗin sa ke son Yara Yasa yake shiga koyar musu ganin haka yasa Malam Arɗo yayi gyaran murya Atake duk yaran suka nutsu tare da tsirawa Malam Arɗo ido.
A hankali Malam Arɗo ya sauƙe tare da faɗin.
“Kuna jina?”.
Kai suka gyaɗa masa.
Ya sauƙe numfashi tare da cewa.
“To zaku yiwa Malam Jameel din ku addu'a Allah ya bayyana shi?”.
Aruɗe yaran suka ce Malam Jameel ya ɓata ne?."
Kai Modibbo ya gyaɗa musu cike da damuwa.
Cikin zare ido Raudat tace.
“Malam Jameel din mu ya ɓata kuma to ina yaje?”.
Ramadan kuwa miƙewa yayi tare da zuwa gaban blackboard ɗin cikin yanayin damuwa sosai ya riƙe hannun Moddibo da har zuwa lokacin Idanunsa ke lumshe yace.
“Moddibo ina Malam Jameel ɗin mu yaje dan Allah ka kira wayansa kace ya dawo Muna so sa”.
Kasa cewa komai Moddibo yayi sabida zulumi.
Gyaran murya Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Kuyi masa addu'a Allah ya bayyana shi idan kunyi sallah kuyi addu'a Allah ya bayyana Malam Jameel sannan ku faɗawa iyayenku suma suyi masa addu'a Allah ya karesa ya kuma dawo dashi cikin aminci da salama”.
Hawaye Ramadan ya fara zubdawa tare da cewa.
“Toh Malam zamuyi masa addu'a zan faɗawa Mommy da Addah Khausina suma zasuyi masa addu'a Allah zai dawo dashi”.
Ahankali Moddibo ya shafa kansa tare da cewa.
“Yawwa Ramadan kuyi masa addu'a ayanzu babu abinda Malam Jameel yake buƙata awajen mu face addu'a”
Cikin rauni sosai yaran suka ce zamu yi masa.
Cikin sanyin jiki Malam Arɗo da Moddibo suka fita zuwa bangaren Secondary bayan sun fita anan suka shiga ɓangaren na naziri saida suka gama zagaye ko wani aji suna sanarwa Ayiwa Malam Jameel addu'a Ubangiji Allah ya bayyana shi cikin tashin hankali ɗalibai suka shiga masa addu'a.
Bayan sun fito Moddibo ya nufi hanyar gate
Cikin kula malam Arɗo yace.
“Moddibo baza ka shiga office din ku ba?”.
Kai ya girgiza tare da cewa.
“Um-um bazan shiga ba zan tafi bazan iya zama babu J ba”.
Ya faɗa tare da ficewa yashiga motarsa kai tsaye gidan Abban M Jameel ya nufa bayan yayi Parking ya fito tare da shiga falon bakinsa ɗauke da Sallama A inda ya fita yabar Abba anan ya dawo ya sameshi zaune still wayarsa na gabansa ya zubanusu Ido da alama tun bayan fitarsa ko motsawa baiyi ba.
Ahankali Abba ya ɗago kai tare da zuba masa ido cike da tausayinsa baki ɗaya ya rame ya canza idanunsa sun sake girma da ja kana idanunsa sun faɗa, Ahankali Moddibo ya ƙaraso ya zauna agefensa aƙasan Capet Cike da tausayawa Abba yace.
“Aliyu ba kayi wanka ka sauya kaya ba”.
Siririn tsaki Moddibo yaja tare da yin ƙasa da kansa kana yace.
“Abba har yanzu basu sake kira ba!?”.
Kai Abba ya Girgiza tare da cewa.
“Har yanzu basu sake kira ba gani nan ina zaune tamkar gadin waya nake sai tsumayin kiransu nake amma basu kira ba, amma yanzu ka samu kaje kayi wanka ka samu kaci abinci”.
“Abba banajin yuwa”.
“Ya zamuyi Aliyu idan kaima baka ci abinci ba ai faduwa zakayi. Insha Allah addu'ar mu bazai bar Jameelu ya ta gayyara ba”.
Sai ya kuma maida kallonsa kan Hajiya Karima data shigo wacce ita ma baki ɗaya tayi sanyi ahankali yace.
“Ki zubawa Aliyu sbinci”.
Kai ta gyaɗa tare da nufar dining ta ɗauki Plate ta zuba masa jollof fice da yaji bushesh-shen kifi da namar kaza ta kawo masa.
Moddibo kuwa hannu ya daga mata alamar kada ta ajiye masa ganin ta ajiye yasa ya maida kansa jikin kushin ɗin ya jingina tare da lumshe idanunsa yace.
“Ina ma ace tare suka ɗauke Ni da J da yafi min farin ciki ina rayu dashi aduk inda yake duk halin da yake ciki ace muna tare wallahi da yafi min farin ciki akan rabani da Jameel da sukayi”.
Kallonsa Abba yayi cike da tausayawa wannan shine karo na farko arayuwar sa da yaji Moddibo ya kira Complete sunan M Jameel cikin raunin murya yace.
“Toh ya zamuyi Aliyu ka daure kaci abinci”.
“Abba ba zan iya cin abinci ba”.
Cikin rarrashi Abba yace.
“Haba Aliyu ka naso kasake sa kamu cikin damuwa ne rashin cin abinka dai dai yake da yiwa kan ka illah, wanda bazan so hakan ba dan Allah ka daure kasa wani abu acikin ka”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Toh Abba abani tea”.
Miƙewa Hajiya Karima tayi ta nufi dining kana ta haɗa masa tea cup ɗaya ta kawo masa ahankali ya karba tare da kaiwa bakinsa da ƙyar ya iya shan rabi ya ajiye Cup ɗin.
Abba bai tilasta shiba dan shima akaran kansa yasan ba zai iya saka komai acikin sa ba baya ga tea ɗin da yake sha dan raya kai, cikin sanyin murya yace.
“Aliyu kaje ɗakin Jameelu kayi wanka ka sauya kaya”.
Girgiza kai yayi cikin rawan murya yace.
“Abba bari in je gida saboda nabar Innayi ita kaɗai tun safe sannan na barta cikin damuwa”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh Aliyu ka gaisheta”.
Yana isa gida yayi Parking tare da wucewa Bedroom ɗin sa, kai tsaye toilet ya shiga tare da sakarwa kansa ruwan sanyi sai alokacin ya lura da Dick ɗin sa daya kwanta luƙui tamkar bai taɓa tashi ba tsanananin fargaba da tashin hankali da yake ciki yasa ya kasa tantance shin shi ɗin wani irin halitta ko kuma wanne irin jinsi ne shin shi ɗin namiji ne ko mace baisan matsayin da yake ba bare kuma ace sha'awa baki daya Dick ɗin sa ya kwanta tamkar babu wani abu mai suna sha'awa daya taɓa ji cikin sanyi Jiki ya gama wankan tare da fitowa ya shirya cikin Jallabiya kana ya fesa turare kai tsaye sashen Innayi ya nufa.
Misalin ƙarfe 5:00pm da wasu Mintuna bayan antaso Amakaranta motarsu Ramadan na shiga harabar gidan tayi Parking Ramadan ya ɓude tare da ficewa da gudu.
Acan falo kuwa Mommy da Khausar ce zaune suna kallon TV cikin tashar Nat geo well Suna kallon namomin daji Ramadan ya shigo tare da zama gefen Khausar kana ya langwaɓar da kansa tare da cewa.
“Addah Khausi”.
Hankalinta na kan wasu irin halittun ruwa tace.
“Na'am Ramadan”.
Cikin muryan rauni yace.
“Addah Khausi wai Malam Jameel ya ɓata”.
Cikin sauri ta kallesa tare da riƙe hannunsa kana cike da mamaki tace.
“Malam Jameel ya ɓata kuma!?”.
Kai ya gyaɗa mata kana yace.
“Eh Addah Khausi Moddibo da Malam Arɗo su suka shiga ajinmu suka faɗa mana Malam Jameel ya ɓata ba asan inda yake ba”.
Cike da mamaki da kuma al'ajabi Khausar tace.
“Ha'a wace iriyar magana ce wannan Malam Jameel ya ɓata ba'a san inda yake ba!?”.
Mommy kuwa cike da mamaki take kallon Ramadan kana tace.
“Ramadan ka tabbatar kuwa?”.
Kafin yace wani abu Raudat ta shigo da kuka fuskarta jage-jage da hawaye kana ta zauna kusa da Mommy tare da cewa.
“Wallahi Mommy wai ya ɓata!”.
Da sauri Mommy ta ɗauki wayarta dake hannun kujera kana tace.
“Gashi kiramin Umminsa”.
Amsar wayar Khausar tayi still da mamaki atare da ita tace.
“Eyyy aikuwa Jiya naga miss call ɗin Asma'u bana wajen daga baya kuma da nazo ina ta kiranta bata ɗaga ba”.
Dai-dai lokacin Hajiya Bunayya ta shigo sanye da hijabi har ƙasa kana ta zauna kusa da Khausar dake laluɓo number Ummi ya zama na sun sa Ramadan Atsakiya kasancewar kujeran 2sitter ne.
Bayan Mommy ta amsa Sallamar ta tace.
“Hajiya wai kinji abinda yaran nan suke faɗa wai Malam Jameel ya ɓata!”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh dama baki ji bane aini tun jiya da yamma Aminu ke faɗa min wai yaji Amasallaci ana cewa ayi addu'a Allah ya bayyana ya kuma tsaresa ashe dama ba kiji ba?”.
Kai Mommy ta.
Girgiza fuska cike da damuwa tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Wallahi ban jiba Subhanallah ya Salam Ubangiji Allah ya tsaresa”.
Hajiya Bunayya kuwa ahankali ta saci kallon Mommy sai taga idanunta nakan Khausar data maƙala waya akunnenta cike da dabara ta sake murza turaren dake hannunta kana ta fito dashi ta ɗaura akan Ramadan tana shafa masa aranta kuwa fari fess tana cewa Alhamdulillah wannan turaren dai na samu na shafa masa saura kuma gobe in faɗawa Boka Kar'uzu na shafa masa turaren.
Khausar kuwa jin Asma'u tayi Picking call ɗin yasa cikin sauri tace.
“Asma'u”.
Cikin wata dashash-shiyar murya mai cike da rauni Asma'u tace.
“Na'am Khausar”.
Cikin alamun damuwa Khausar tace.
“Asma'u wai me nake ji?”.
Cikin muryan kuka Asma'u tace.
“Khausar an sace Yah Jameel yau kwana biyu kenan kusan na uku ba Yaya Jameel ba labarinsa”.
Atsorace Khausar ta dafe hannunta aƙirji kana tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n ansace Yah Jameel Kuma?”.
Kai Asma'u ta gyaɗa hawaye na bin kuncinta tace.
“Eh”,
Cikin sanyin murya tace.
“Ubangiji Allah ya bayyana shi aduk inda yake Allah ya fito mana dashi”.
Ameen Asma'u ta amsa tare da katse kiran.
Kallon Mommy Khausar cikin tashin hankali tace.
“Mommy wallahi da gaske an sace sa”.
Girgiza kai Mommy tayi tare da cewa.
“Ya Salam wallahi bamu sani ba barin idan Abbanku ya shigo zan tambaye sa muje muyi wa Umminsa jaje Ubangiji Allah ya bayyana shi Allah ya tsaresa aduk inda yake”.
Khausar kuwa kasa tsaida hawayen ta tayi cikin Muryan kuka tace.
“Ameen Mommy Ameen ya hayyu ya ƙayyum Allah ya bayyana Malam Jameel har kwana biyu kuma!?”.
Ta gumi Hajiya Bunayya tayi tare da marairaice fuska kana tace.
“Hakane kam wannan duniyar ta zama abin tsoro idan kana fama da talauci ka banu idan kayi wadata ɓarayi da ƴan Kidnapping su hanaka kwanciyar hankali da nutsuwa Allah dai ya kyauta”.
Ta faɗa tare da miƙewa ta fice ranta fess.
Baki ɗaya Wunin wannan ranan haka Mommy da Khausar suka yita cikin jimami da fargaba musamman Khausar ta gagara tsaida hawayen ta.
Moddibo kuwa yana fita daga sashen Innayi mota ya shiga tare da nufar gidan Abba yana isa ana kiran maghariba tare da Abba suka shiga Masallaci suka gabatar da sallah.
Acan ɓangaren Mommy kuwa bayan an idar da sallar Isha'i ta sanarwa da Lamiɗo suna san zuwa yiwa Ummi jaje nan yace ba damuwa ta kira Khausar da Hajiya Bunayya su fito bayan sun fito da kansa yayi Driving ɗinsu zuwa gidan Ummi.
Bayan sun isa.
Mommy ce agaba sai Khausar sai kuma Hajiya Bunayya bakinsa ɗauke da Sallama suka shiga dai-dai lokacin kuma maƙotansu suka fito.
Zaune suka samu Ummi kan 2sitter tana riƙe da Kur'ani Idanunta sun kumbura sun ƙanƙance yayin da Asma'u ke zaune gefenta hannunta riƙe da Carbi.
Cikin sauri Khausar ta ƙarasa kusa da Asma'u tare da riƙe hannun ta kana tace.
“Asma'u da gaske wai dagaske ansace Yah Jameel!?”.
Cikin zubda hawaye Asma'u ta gyaɗa mata kai kana tace.
“Khausar da gaske ansace Yah Jameel tun randa kikazo ya maida kin nan, har yanzu babu labarin sa yanzu kusan dare na uku kenan za ashiga”.
Khausar ma cikin zubda hawaye ta damƙe hannun Asma'u tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Kallon Ummi Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Ayyah Ummin Jameel Ashe abinda ya faru kenan toh Ubangiji Allah ya tsare Allah ya bayyana shi”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da faɗin.
“Ameen ya Allah Nagode”.
Mommy kuwa kafaɗar ta ta dafa kana tace.
“Ba komai Ummin Jameel kiyi haƙuri ki daina kukan nan ki riƙa yi masa addu'a Insha Allah Ubangijin zai bayyana shi”.
Cikin sauri Ummi ta share hawayenta kana tace.
“Nagode Mommyn Khausar Nagode³”.
Cike da tausayawa Mommy ke sake ƙarfafa mata guiwa.
Ahankali Khausar ta juya tare da kallon Ummi cikin Muryan kuka tace.
“Ummi Allah ya bayyanar da Yah Jameel insha Allah ba zasu samu nasarar cutar da shiba zamu tayi masa addu'a Allah ya karesa”.
Miƙewa Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Bari mutafi Alhj na jiran mu awaje yace a gaidaki".
Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.
“Nogeda Allah ya saka”.
Sannan suka fita a coumpund suka haɗu da wasu matan sun shigo yiwa Ummi jaje bayan sun koma gida.
Baki ɗaya Khausar ta kasa nutsuwa kafin ta kwanta taje tayi alwala kana ta ɗauki Kur'ani tana ta karatu tare da tawassali dashi da niyyan Ubangiji ya bayyana M Jameel aduk inda yake.
Misalin ƙarfe goma na dare kamar lokacin da aka dauke M Jameel Moddibo dake gefen Abba ya miƙe da niyyar tafiya Akuma dai-dai lokacin wayar Abba dake gabansa ta hau ruri.
Atare Abba da Moddibo suka kalli wayar cikin sauri Abba yayi Picking call ɗin tare da kaiwa Kunnensa.
Daga ɗaya ɓangaren akace Alhj Bashiru mahaifin Jameel ko!?”.
Cikin sauri Abba ya gyaɗa kai tare da cewa.
“Eh nine nayi ta kiran layinku baya shiga”.
Cikin fusatacciyar murya Mutumin yace.
“Dama ce maka mukayi idan ka kira zai shiga?”.
Girgiza kai Abba yayi tare da faɗin.
“A'a to menene sharaɗin ku na biyu kaga ban faɗawa kowa ba!”.
Cikin bauɗaɗɗiyar murya Mutumin yace.
“Kuɗin fansa zaka biya shine sharaɗin mu na biyu”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da cewa.
“To nawa kuke buƙata?”.
Kai tsaye mutumin yace.
“Milion ɗari biyu”.
Atsorace Abba ya dafe hannunsa aƙirji kana ya zare ido cikin tsanananin firgici yace.
“Milion ɗari biyu!?”.
Atare Hajiya Bunayya da Moddibo da maganar ya dakesu suka haɗa baki atare wajen cewa.
“Milion ɗari biyu?”.
Cike da gadara Mutumin yace.
“Toh idan ba zaka bada ba sai ka shirya karɓan gawar ɗan ka!”.
Cikin sauri Abba ya Girgiza kai tare da cewa.
“Kuyi hakuri dan Allah dan darajar Annabi kada ku kashe wayar”.
Cikin Yanayin ɓacin rai Mutumin yace.
“To ai mun riga mun faɗa muku abinda ake buƙata idan ka shirya gobe zamu sake kiran ka muji ko ka shirya”.
Yana gama fadar haka ya katse kiran...!
By
*GARKUWAR MARUBUTA*SAKAYAH
29
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*LITTAFIN SAKAYYAH NA KUDINE KO KIN GANSHI A WASU WURAREN DA BA CIKIN GROUPS NA DANA BUƊE NA SAKAYYAH BAto na satane, 1k ne kacal kuɗin littafin SAKAYYAH yar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, kiyiwa Allah da Manzonsa ku dena fidda min littafina, in dai kin san kin sayane dan ki turawa wasu, dan Allah ki gaya min in mayar miki da kuɗinki🙏🏻🙏🏻Dan Allah nace ba dan niba*
Isrnejny. Moddibo kuwa cike da mamaki da tsoro ya maimaita 200 Millions asaman laɓɓansa, he can't believe or imagine zasu iya tambayar wannan maƙudan kuɗin how cames kidnapper zasu tambayi kuɗin fansa kamar sun sace ɗan shugaban ƙasa.
Rintse idanunsa yayi tare da cije labɓansa na ƙasa lokaci ɗaya jijiyoyin kansa suka tashi sukayi ruɗu-ruɗu dasu.
Dafe kuncin Hajiya Karima tayi da hannunta duka biyu kana ta kyale baki tare da cewa.
“Ohh Allah ya kawo mu wani zamani ka haifi ɗa sannan wasu ƙartin banza da wofi su saka kasa ke sayan sa bafa Millions biyu ba, Ba ashirin ba, Ba hamshin ba, Ba ɗari ba, har Millions ɗari biyu sai kace abin Masifa ko dan sunyi zaton Jameel ɗan Aliko ɗan Gwate ne, shi, ka haifi ɗa kasha wahalar ciyar dashi shayar dashi tufatar dashi biya masa makaranta sannan ace ka sake siyan sa”.
Dafe kai Abba yayi da duka hannunsa biyu baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake kar-kar-kar tamkar mazari yayin da idanunsa suka kaɗa sukayi jawur tamkar garwashi.
Dai-dai lokacin Hajiya Turai tashigo baki ɗaya tayi zuru-zuru da ita. Idanunta sun kaɗa sunyi jawur dasu ganin halin da Abba ke ciki yasa tace.
“A'a Alhj Lafiya Subhanallah”.
ta faɗa tare da nufar Bedroom ɗin sa ta da buɗe drawer ta ɗauko naganinsa ganin alamar hawan jinjinsa ne ya tashi tare da manna waya akunnenta bayan kamar second uku tace.
“Hello Dr Muktar dan Allah kazo yanzu ina ganin kamar hawan jinin Alhj ne ya tashi”.
Cikin raunin murya Abba ya ɗago kai ya kalleta tare da cewa.
“A'a ki bari ba sai Dr yazoba, ki bani maganin kawai”.
Kai ta gyaɗa kana cikin sauri ta zuba masa ruwa a glass cup ta miƙa masa tare da bara masa maganin karɓa yayi ya afasu abakinsa ya haɗiye.
Sannu a hankali ya fara maida numfashi sama-sama yana jin bugun zuciyarsa tare da sarawan da kansa keyi ya fara raguwa amma still hannunsa na dafe da kansa.
Ɗago Idanunsa yayi tare da kallon Moddibo daya zuba masa Idanu kana ya kalli gefen damansa Hajiya Turai ce durƙushe Idanunta cike da hawaye lumshe idanunsa yayi kana ya shiga tunani kwata-kwata kuɗin dake cikin account ɗinsa tsuran kuɗi, gaba da baya Million Sha biyu ne wanda yake tunanin da sun cika Ashirin zai bawa M Jameel saboda ya habɓaka Company daya bashi, da ƙarfi ya sake rintse idanunsa tare da dafe kansa tuno wa da yayi acikin Million Sha biyu ma akwai cikon kudin hajji nashi da na matansa da zai cika ta, baki ɗaya tunaninsa ya tushe ina yasan zai fara kai kadaransa asiya masa su cikin gaggawa kuma da daraja sannan abashi kuɗin cikin tsanananin tashin hankali yace.
_“Ya Ilahi ya lillahi ya mujibud da'awati ya hayyu ya ƙayyum bi rahma tika astaghisu lahaula wala ƙuwwata illa billahil aliyul azim”_.
Abin da yake maimaitawa kenan asaman laɓɓansa.
A hankali Moddibo ya matsa kusa dashi cike da tausayawa yace.
“Colm down Abba ka nutsu ka kwantar da hankalin ka everything will be fine by the grace of Allah”.
Cikin sauri Abba ya riƙo tsintsiyar hannun Moddibo tare da cewa.
“Aliyu Why should I find 2 hundred Millions?”.
Aliyu mai zan fitar in sayar dashi cikin gaggawa in Samu kuɗi?.
Aliyu bani da ko Million ashirin acikin account ɗina,kaji kuɗin da suka kira fa”.
Kallonsa kawai Moddibo keyi cike da tausayinsa Cikin raunin murya Abba ya cigaba da cewa.
“Aliyu kwanan nan na cire kuɗi na siya filin nan kuma shima gaba ɗaya filin dana siyeshi 25 Million ne da ace suna nan kaga kuɗin akwai ɗan gwaɓi ahannu na”.
Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da sake damƙe hannun Moddibo