Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sakayya Complete Hausa Novel by Aisha Aliyu Garkuwa

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   45 / 140

132K to 135K   out of 417.8K words

in samu lafiya in kuma baza kiyi min ba shikenan dama can aikinsa inada ciwon kai ko?”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da jinjina kai kana tace.
“Eh nasani toh shine ake cemin saina samu yanzu idan kika samin a farin ƙyalle, da daddare in zan kwanta ne zangoga shi asaman goshina ance insha Allah daga ranan na rabu da shi kenan”.

Sanyayyar Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da lumshe Idanunta kana tace.
“Tsakaninka da waye?”.
Ahankali yace.
“Tsakanina da Allah Wallahi dagaske na faɗa miki. My Khausi Magani zan haɗa kuma kinsan duk sanda ciwon kan nan ya tashi kamar zan mutu”.
Khausar kuwa jinjina kai tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana tace.
“Toh shikenan ba damuwa insha Allah zanyi maka”.
Ta faɗa tare da juyewa ta fice bayan ta dauki ƙyallen.

Tun da Khausar ta koma ɗaki ta rasa meke damunta baki ɗaya ƙamshin ƙyallen na damunta ahankali ta buɗe drawer ta ɗauki leda ta jefa ƙyallen aciki sannan tasake saka wani ledan saida ta ninka masa laida biyar sannan ta fita bakyard ta ajiye sai asannan ta samu nutsuwa baki ɗaya ƙamshin ɗaga mata hankali yake.

Bayan kwana biyu Ya kama yau ne ake sunan Aunty Asiya misalin ƙarfe goma Mommy, Hajiya Bunayya, Amina, Raudat, Ramadan duk suka tafi sunan Aunty Asiya gidan ya rage saura Khausar ita kadai kasancewar. Mommy tace da ita dai idan ta dawo zata je dan kada abar gidan.

Khausar dake zaune a Bedroom ɗin ta tayi saurin miƙewa jin muryan Asma'u afalo atare Asma'u da Haiydar suka shigo falon da alama daga koyon Machine ya dawo saboda hannunsa dake riƙe da ƙaton L, kwanciya yayi akan 3sitter tare da kunna TV bayan sun gaisa da Asma'u, Khausar kuwa cike da farin ciki ta rungume Asma'u.
Ahankali Asma'u ta janye jikinta daga na Khausar kana tace.
“Ya naji gidan shiru kamar ba kowa?”.
Kai Khausar ta jinjina cikin sanyin murya da alamun damuwa atare da ita tace.
“Eh babu kowa sunje gidan Aunty Asiya yau sunanta, nima so nake inyi wanka sai Inje in duba su. Mommy nake jira baya ga haka ma jikina duk amace yake”.
Ta ida maganar lokacin da suka shiga ɗakin ƙaramin fridge dake ɗakin Khausar ta buɗe tare da ciro Friut ta ɗauki Plate akai ta zuba mata kana ta ajiye mata agabanta.

Cike da kulawa Asma'u tace.
“Khausar ya dai na ganki Asanyaye kamar akwai abinda ke damunki?”.
Girgiza kai Khausar tayi tare da cewa.
“Babu komai Asma'u kici Fruit”.
Kallonta Asma'u tayi tare da girgiza kai kana tace.
“A'a Taya zan sha Friut baki faɗa min abinda ke damunki ba?".
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da faɗin.
“Wallahi Asma'u wani Abu ke damuna, yake kuma bani tsoro nasha faɗa miki al'amarin Uncle Naseer.
Yana bani tsoro kince ba haka ba ko to kinji abinda ya faɗa min kwanaki”.
Atake ta kwashe dukan yanda sukayi da Naseer ta faɗa mata“.
Atsorace Asma'u ta dafe ƙirjinta tare da cewa.
“Kai Khausar kada ki yarda ki sanya Period ɗinki akan wannan ƙyallen ki bashi muka san mai zaiyi dashi ke har kin yarda dashi”.
Girgiza kai Khausar tayi cike da damuwa ta langwaɓar da kai kana tace.
“Nasan yana da ciwon kai, amma baki ɗaya ban yarda cewa maganin ciwon kai zaiyi dashi ba”.
Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe kana tace.
“Gaskiya kar ki yarda ki kiyaye”.
Cike da damuwa Khausar tace.
“Toh yanzu ya zamuyi?”.
Gyara zama Asma'u tayi tare da faɗin.
“Gaskiya dai kam Khausar kada ki yarda kisa jininki akan wannan ƙyallen, hakan ma bazai yuba mukasan me yake nufi dashi, kika san me zaije ya aikata dashi ai haka baza ta yuba?”.
Lumshe idanu Khausar tayi kana tace.
“Toh shikenan ai dama bazan saba”.
Mommy ce tashigo tare da ɗaga labulen bayan tayi sallama.
Amsawa suka yi kana cike da ladabi Asma'u ta gaishe da Mommy.
Cikin sakin fuska Mommy ta amsa tare da tambayarta yasu Umminta.

Kallon Khausar Mommy tayi tare da cewa.
“Khausar ki ɗauki Plate da Spoon ki Kai gidan Aunty Asiya”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh”,Juyawa Mommy tayi ta fice.
Miƙewa Khausar tayi tare da cewa.
“Asma'u muje ki rakani”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da miƙewa direct kichen ta nufa ta tare da ɗaukar Plate da Spoon suka fita kai tsaye gidan Aunty Asiya suka nufa.

Ahankali Asma'u ta zubawa raguna biyu dake rataye a coumpund ɗin ido, da alama na suna ne duk angama gyarasu an cire kayan cikinsu ana jiran su tsantsame.
Har suka shiga cikin gidan suka kai Plate ɗin baki ɗaya hankalin Asma'u na kan ragunan dake coumpund ɗin bayan sun fito Asma'u ta kalli ragunan cikin sanyin murya ta kalli Khausar tare da cewa.
“Khausar ga dama ta samufa”.
Da sauri Khausar tace.
“Wacce damar”.
Cikin yin ƙasa da murya Asma'u tace.
“Dauko ƙyallen nan zamuyi muzo musaka jinin wuyan ragon nan”.
Jinjina kai Khausar tayi cike da gamsuwa tace.
“Ƙwarai kuwa Asma'u muje mu ɗauka”.
Cikin sauri suka fice cikin sa'a koda suka shiga basu samu Mommy a falon ba tana toilet. Haiydar kuwa baya nan kai tsaye backyard suka nufa Khausar ta ɗauki ƙyallen a inda ta ajiye sannan ta since.
Da sauri Asma'u ta kawar da kanta gefe jin yanda ƙamshin jiki ya bugeta.
Cikin ya mutse fuska tace.
“Kai Wannan wani irin ƙamshine mai tada hankali ba daɗin ji”.
Baki Khausar ta taɓe kana tace.
“Hmm nima dai haka naji”.
Ahankali suka juya suka fita kai tsaye gidan sunan suka nufa Baba Mai gadi dake zaune yace da.
“Hajiya Khausar ya gida?sai yanzu kika leƙo?.
Murmushi tayi tare da cewa.
“A'a ɗazu ma nazo bamu ganka bane”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Ayyah wataƙil na zagaya ne”.
Cikin sa'a babu kowa a coumpund ɗin kallon Khausar Asma'u tayi cikin ƙasa da murya tace.
“Kinga mai gadi na kallonmu sai munje dai-dai wajen ragon zan durƙusa kamar takalmina ya tsinke ke kuma saikiyi saurin daddalan jinin ajiki”.
Kai Khausar ya gyaɗa suna isa wajen Asma'u ta tsugunna tana taɓa ƙafarta.
Khausar kuwa cikin sauri ta matsa jikin ragunan ta ciro ƙyallen cikin leda sannan ta manna ƙyallen ajikin wuyan ragon dake ɗigar da jini kaɗan-kaɗan sannan ta sake dan dala tayi haka har sau uku ajikin wuyan ragon cikin sauri tace.
“Asamu'u nayi mu tafi”.
Miƙewa Asma'u tayi suka nufi ƙofa,Baba mai gadi yace.
“Ya dai Asma'u ta kalmin tsinkewa yayi ya kuka tafi baku shiga ba?”.
Murmushi Asma'u tayi tare da cewa.
“A'a kawai dai na ɗan gurɗene naji ƙafar na yimin ciwo sannan mun manta ɗauko abinda Mommy ta aiko mu mukawo”.
Daga haka suka fice daga gidan.
Kai Baba ma gadin ya jinjina musu,
Tare da juyowa, cikin gidan,
Wani irin zazzaro idanu waje yayi cike da tsanani tsoro da mamaki Baba Mai gadi ya buɗe baki da ido da hanci duka gani, cikin raguna biyu dake rataye ɗaya ya ɓace ɓat......!




*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276,*




*By*
*GARKUWAN MARUBUTA*SAKAYAH

21

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Isreg'o. Cikin tsananin tsoro da mamaki Baba mai gadi ya juya gabas da yamma,r kudu da arewa acikin coumpund ɗin gidan amma babu mutum babu dalilin mutum, cikin tsananin kaɗuwa da ganin wannan abin al'ajabin yace.
“Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n. Cikin abinda bai wuce second ɗaya ba ace babu rago babu dalilinsa, kuma abu ayanke bawai da ransa ba bare ace ya gudu”.
Cikin kaɗuwa ya nufi cikin gidan tare da cewa.
“Ya Ilahi mai ya faru”.
Duk ya burkice ganin abin yake tamkar mafarki dai-dai lokacin da mai gidan ƙanin Lamiɗo yake fitowa.
Aruɗe Baba mai gadi yace.
“Alhaji ragunan biyu suna ɗaure amma yanzu naga ba ɗaya”.
Kallon Mamaki Alhj Musa ya masa tare da cewa.
“A'a ragunan biyu yanzu kuma babu ɗaya ƙafa ragon yake dashi Malam Idi?.
Aruɗe Malam Idi yace.
“Wallahi tallalahi Alhj da gaske yanzu-yanzu ragonan yana nan amma yanzu ya ɓace babu shi babu dalilinsa”.
Tsayuwa Alhj Musa ya gyara tare da cewa.
“Toh ragon ƙafa zaiyi ina zai shiga?”,.
Malam Idi daya gama shiga tashin hankali yace.
“Wallahi da gaske Alhj”.
ya faɗa tare da juyawa ya fice daga gate ɗin ganin su Khausar basu yi nisa ba yasa ya saki Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Khausar!, Khausar!! Kuzo”.
A tsorace Khausar da Asma'u suka jiyo atare kana suka haɗa baki wajen faɗin.
“Ya dai Baba mai gadi”.
Hannu ya ɗaga musu tare da cewa.
“Kuzo dai”.
Cikin rawan jiki da tsoro Khausar tace.
“Lafiya?”.
Cikin ƙasa da murya Asma'u tace.
“Mun shiga uku kad dai ya gane?”.
Da ƙarfi Khausar ta haɗiye wani abu mai ɗaci tare da cewa.
“A'a Insha Allahu ma bai gane ba”.
Suna isa bakin gate ɗin yace.
“Khausar kushigo”.
Ƙara sa shiga sukayi zuciyar su na bugawa da mugun sauri.
Kallonsu Baba mai Gadi yayi tare da kallon Alhj Musa kana yace.
“Dan Allah dan Annabi ba ragunan biyu suna nan ba, har kuka tsaya kusa dasu suna ɗaure ba?”.
Atsorace Khausar ta gyaɗa masa kai kana Muryanta na rawa tace.
“Eh”.
Da sauri Baba mai gadi ya sake kallon wajen tare da cewa.
“Kawai ina zaune fa kamar abin wasa kamar amafarki kamar a Tv naga rago ɗaya ya ɓace”.
Khausar da jikinta ya fara rawane tace.
“Ya ɓace kuma?”
Cikin tashin hankali Asma'u da Idanunta sukayi zuru-zuru ta dafe ƙirjinta tare da faɗin.
“Ya ɓace kuma dai?”.
Jinjina kai Baban mai gadi yayi tare da cewa.
“Wallahi kuwa kun fita kenan ina juyawa naga ragon nan ya ɓace Khausar abin nan abin mamaki fa ina kuma kun gansu?”.
Shi dai Alhj Musa na tsaye ya harɗe hannunsa aƙirji yana sauraransu cike da al'ajabi.
Cikin tsananin tsoro mamaki da al'ajabi da kaɗuwa gami da kiɗima Khausar ta kalli Alhj Musa kana tace.
“Wallahi kuwa Baba ƙarami muma munga ragunan nikam mafa akusa dasu na tsaya. Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n yau mun shiga uku Meye faru ya akayi haka?”.
Jin hayaniya yasa mata dake cikin gida suka fara fitowa suna tambayar abinda yafaru duk wanda yaji rago ya ɓace sai yashiga cikin mamaki da al'ajabi.
Baba mai Gadi da abin ya tsaya masa arai ya kalli mutanen dake wajen tare da cewa.
“Wallahi ganin Idona ragon nan ya ɓace ɓat kamar a Film kuma babu kowa a farfajiyar gidan Khausar suna fita abin ya faru ina juyawa naga sun ɓace ɓat!”.
Atsorace Khausar ta jinjina kai tare da cewa.
“Wallahi kuwa Muma yanzu muka gansu mun samu ragu nan nan aɗaure”.
Ana haka Mommy tashigo nan ta samu labarin rago ya ɓace nan suka shiga jajantawa.

Khausar kuwa hannun Asma'u taja suka fice bayan sun fita Asma'u ta juya ta kalli Khausar tare da cewa.
“Khausar”.
Juyawa Khausar tayi tare da haɗiye wani abu mai Masifar ɗaci tace.
“Asma'u”.
Asma'u taja dogon numfashi kana tace.
“Khausar da kece zaki ɓace fa. Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n”.
Khausar kuwa da jikinta yake rawan jitayi Idanunta sun ciko da hawaye cike da alhini tace.
“Asma'u mun shiga uku”.
Cike da rawan jiki suka ƙarasa gida kai tsaye ɗakin Khausar suka nufa tare da zama a ƙasa Capet ɗin duk sunyi zuru-zuru dasu kallo ɗaya zaka musu kasan cewa suna cikin ɗimuwa da tashin hankali mara misaltuwa.
Cikin rawan murya Khausar ta kalli Asma'u tare da cewa.
“To yanzu kam Uncle Naseer me yake nufi dani? Dama tsafi zaiyi dani, kenan Uncle Naseer ma tsafi ne Asma'u? ba kingani ba dama ni sam ban yarda da shiba, tsoronsu nake dama Gimbiya Dadu ya take bare kuma ƙanwarta mun shiga uku dama tsafi zaiyi dani Asma'u shikenan da kashe ni suke sonyi?”.
Cikin raunin murya Asma'u tace.
“Khausar wannan abin ya gigita ni na rasa ta yanda zan fassara shi”.
Ta gumi sukayi yayin da zuciyarsu ta cigaba da bugawa tsoro da tashin hankali ya bayyana atare dasu lokacin ɗaya zazzaɓi ya fara dirarwa Khsusar.

Ba jimawa Mommy ta dawo kai tsaye ɗakin Khausar ta shiga tana cewa.
“Ohhh Allah mai iko an duba fa ƙasa da sama babu ragon nan babu dalilinsa an duba ko ina babu shi ya ɓace!”.
Murya na rawa Asma'u tace.
“Mommy muma fa mun gansu”.
Mommy kuwa ahankali ta maida kallonta kan Khausar da jikinta ke rawa duk ta ruɗe cike da kulawa tace.
“Khausar ya dai?”.
Kuka Khausar ta fashe dashi tare da yarfe hannu kana tace.
“Mommy zan faɗa miki Mommy zan faɗi gaskiya”.
Kallon Mamaki Mommy tayi mata kana tace.
“Meya faru Khausar?”.
Cikin kuka sosai Khausar tace.
“Allah Mommy Zan faɗi”.
Zama Mommy tayi gefensu kana tace.
“Wai meke faruwa ne Asma'u”.
Cikin ƙoƙarin tsaida hawayen Khausar ta riƙe hannun Mommy acikin nata, kana ta zayyane mata duk yanda sukayi da Naseer da kuma shawarar da Asma'u ta bata sannan ta ɗaura da cewa.
“Mommy kuma nice ɗazun na dandala ƙyallen akan wuyan ragon, har muka ji tsoro kar Baba mai gadi ya ganmu kuma Allah wanda na shafawa ƙyellen ne ya ɓace”.
Aruɗe Mommy ta saki salati tare da sanar da ubangiji.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n. Hasbunallahu wani'imal wakil. La'ilah ha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal Zhalimin. Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha_. Ohh Khausar am nashiga uku wannan rayuwa har ina Khausar kin tabbatar?”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Wallahi tallahi Mommy da gaske ne”.
Ta faɗa tare da cusa hannunta ƙarƙashin gado ta ciro mata ƙyallen data ajiye da niyyar idan Naseer yazo zata bashi”.
Cikin raunin murya tace.
“Mommy kingani Mommy kin gani ko wallahi shine ƙyallen”.
Jinjina kai Mommy tayi tare da kallon ƙyallen da ƙamshinsa ke bugun kanta kana tace.
“Nashiga Uku ni Aysha wannan masifa har ina?”.
Asma'u kuwa ta gumi tayi ganin abin take tamkar almara.

Khausar na share hawaye tace.
“Mommy ina dai yanzu kin gani kinga zahiri Mommy inaga yanzu kam zaki iya yarda su Mayu neko?”.
Girgiza kai Mommy tayi cike da jimami da kuma al'ajabi ta kalli Khausar tare da cewa.
“Toh su sukayi ko shi Allah am nashiga uku ba'a shaidar halin ɗan mutum”.
Girgiza kai Asma'u tayi kana tace.
“Nikam wallahi Uncle Naseer ya bani Mamaki duk da rawan kansa ban taɓa zaton zai aikata irin wannan abin ba”.
Ta gumi Khausar tayi duk abin duniya ya isheta Hausawa sunyi gaskiya da suka ce Mutum mugun Icce.
Ganin yanda suka ruɗe da al'amari yasa Mommy dai-dai ta nutsuwarta tare da cewa.
“Kar ku damu ku cigaba da addu'a domin addu'a takobin mumunice, sannan kada ku faɗa wa kowa wannan maganar ya zama sirri atsakanin mu”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Asma'u kana tace.
“Asma'u Allah ya miki al'barka, kin cika ƙawar kirki duk inda ake neman ƙawar arziki kin kai.
Allah Ubangiji ya Al'barkanci rayuwar ku ya kuma kare ku aduk inda kuke”.
Haɗa baki sukayi wajen faɗin.
“Ameen”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe kana tace.
“Wannan magana ya zama sirri atsakanin mu, kada ku fadawa kowa daga. Ni sai ku sai kuma Ubangijin daya halluccemu shi kuma Naseer zamu ga manufarsa.
Za muga iya gudun ruwansa sannan daga yau Khausar koda ya kira ki baza ki sake zuwa inda yake ba ko dai kina son shi!?”.

Zaro ido Khausar tayi cikin sauri ta shiga yarfe hannun tare da Girgiza kai kana tace.
“Allah Mommy bana sonshi, na tsane shi bani bashi har abada, me zanyi da matsafi ni dai bana sonshi Wallahi bana sonshi”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da kallon su kana tace.
“Toh shikenan ki kwantar da hankalin Allah ya tsare ku ya muku zaɓi da maza na gari, wannan ma ai addu'a ce tasa asirinsa ya tonu Allah ya ƙara tsaremu baki ɗaya ku kara riƙo da addu'a in sha Allah duk sharrin mai sherri sai dai yaga gadon bayanmu”.
Atare suka amsa da.
“Ameen”.
Haka dai akayi suna aka watse kowa na al'ajabi da ta'ajjadin ɓacewar ragon suna.

Acan gidansu Moddibo kuwa M Jameel zaune tare da Innayi Moddibo kuwa na tare da Malam Arɗo bai dawo ba.

Anutse M Jameel ya ɗago kansa tare da kallon Innayi dake zaune ta tanƙwashe ƙafafunta cikin sanyin murya yace.
“Innayi”.
Ahankali ta ɗago kanta tare da cewa.
“Na'am”.
Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe kana yace.
“Innayi ni ko badan kar kice ina bincikar ki da tuhumar kiba.
Da zance da Allah Innayi ina ne asalin ƙasar ku tunda nan dai garin naji labarin zuwa kuka yi dan Allah Innayi ki faɗa min inane asalin garinku sannan, wai kwata-kwata mahaifin A.J bashi da dangi ne? Sannan Ina dangin Mahaifiyarsa”.
Ido Innayi ta tsira masa tana jin bugun zuciyarta na ƙawura.
M Jameel kuwa cigaba yayi da cewa.
“Sannan dan Allah kiyi haƙuri kada ranki ya ɓaci shin ke kakarsa ta wajen auwace ko kuma kakar sa ta wajen Uba ne?”.
Kallonsa kawai Innayi keyi tana jijjiga ƙafarta.
Ajiyar zuciya M Jameel ya saki kana yace.
“Dan Allah Innayi ki faɗa min ina son insan wannan abin kada ki ƙi faɗa min ke ta wani gefe ne kika kasance.
Kaka agaresa sannan kuma akwai abubuwa da dama da suke ɗaure min kai ina so insan su Innayi, idan har baki faɗa min suba Wallahi zan rayu da ƙumfa dan Allah ki faɗa min kada in mutu baki faɗa min ba”.
Sanyayyar Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kallon M Jameel kana tace.
“Aaa to mutuwan nan Kam Jamilu am ai tana kan kowa, sannan ni tsohuwa ma ban ce kar in mutu ban faɗa muku ba, sai kaine zaka ce kar ka mutu ban faɗa maka ba!”.
Langwaɓar da kai yayi tare da karyar da murya cikin son karya logonta da batun zai mutu dan yasan bata son jin hakan yace.
“Ni dai ki faɗa min”.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Jamilu bana son tone-tone ne Jamilu abar kaza cikin gashinta fa yafi, sannan kuma babu amfanin tone-tone da faɗe-faɗe!”.
Zamansa ya gyara tare da cewa.
“Innayi Ni dai inaso shi tone-tonen nan da faɗe-faɗen nan ina so afada min waye ne A.J Ina son insan Abu akan Abokina kuma Aminina ina so insan komai akanshi”.
Sauƙe numfashi tayi tare da kallon M Jameel kana tace.
“Toh nayi maka al'ƙawari ni kuwa zan sanar maka da komai in. Allah ya yarda zan faɗa maka abinda ya sawwaka duk da cewa bakomai zan faɗa maka ba”.
Jinjina kai yayi kana yace.
“Toh Innayi nagode amma ranan yaushe zaki faɗa min”.
Shiru tayi alamar tunani sai kuma tace.
“Duk ranan dana shirya zan faɗa maka sai kazo kai kaɗai”.
Jinjina kai yayi tare da cewa.
“Toh shikenan Innayi Nagode sosai”.
Bayan sun sake taɓa hira ne ya mata Sallama ya tafi.

Da daddare Misalin ƙarfe takwas Naseer ya shiga gidansu bayan yaje ya gama sharholiyarsa kai tsaye falon mahaifiyarsa ya nufa zaune ya samu Mahaifiyarsa da Yayunsa mata guda biyu dawowarsu daga gidan sunan kenan basu daɗe ba.
Zama yayi tare da gaishesu suka amsa cikin sakin fuska.
Aunty Hindu ce ta kallesa tare da cewa.
“A'a yau fa mun ga abin al'ajabi agidan Yaya Musa

45 / 140

Chapters