Author : Aisha Aliyu Garkuwa Category : Free Novels Online (Read & Download)
yarda da motar nan ba, dan ko can Rugar da suje adaren ranan akwai abinda ya faru”.
Ajiyar zuciya ta saki tare da rintse Idanunta kana ta cigaba da cewa.
“Haka nan naji na tsargi motar duk da bani da tabbaci sannan still yauma. Kaga tazo ta tsaya mana abakin makaranta Indai tazo ka sake ganinta ka sanar min ko kuma ka sanarwa Malamai”.
Jinjina kai Baba mai gadi yayi tare da cewa.
“Toh shikenan insha Allah ”.
Kai ta gyaɗa tare da buɗe ƙaramin gate ta koma cikin makaranta tana koma suka haɗu da M Jameel na ƙoƙarin zuwa office.
Da Mamaki M Jameel ya kalleta kana yace.
“Daga ina kike Khausar kaddai yanzu kika zo?”.
Kallonsa tayi tare da girgiza kai tayi kana tace.
“A'a tun ɗazu nazo na gama Peper nama shiyasa na fito”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“To mai kika je yi awaje?”
Murmushi tayi tare da cewa.
“Wani abu naje na ɗan duba?”.
Gyara tsayuwarsa yayi kana yace.
“Wani abu kika je dubawa bayan kinsan doka da ƙa'idar makarantar nan, in anshiga ba'a fita yanzu kiyi laifi idan ansaki kaɗe ɗankwali kice rayuwar bauta kike baki da cikekken ƴanci ko?”.
Ƙasa tayi da kanta tare da cewa.
“A'a wata mota ce muka gani nida Baba Mai gadi”. Dai-dai lokacin kuma ta hango Moddibo ya fito daga corridor da zai sada ka da office ɗin su zare ido tayi cikin sauri ta juya tare da hawa step ɗin class ɗinsu.
Murmushi M Jameel Yayi tare da girgiza kai Dramer Moddibo da Khausar na sanyashi nishaɗi.
Khausar kuwa na haurawa ta samu Asma'u ta fito tayi submitted Booklet din ta ba daɗewa kowa ya fito sannan suka tafi.
Motar na parking Khausar ta fito dai-dai lokacin Mommy ta shigo tsayawa Khausar tayi har Mommy ta ƙaraso kusa da ita.
Kallon ta Khausar tayi tare da cewa.
“Mommy daga ina haka naga kamar kin fita Unguwa?”.
Kai Mommy ta gyaɗa mata kana tace.
“Eh Khausar na fita Unguwa naje gidan Aunty Asiya ce yau ta haihu Allah ya sauƙeta lafiya”.
Wara Ido Khausar tayi cike da farin ciki tace.
“Laaaa Mommy Aunty Asiya ta haihu? Mai ta haifa Mommy?”.
Jinjina kai Mommy tayi tana tafiya tace.
“Ta haifi ƴa mace”.
Jinjina kai Khausar tayi tare da faɗin.
“Masha Allah bari nayi wanka naje na duba Baby”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da cewa.
“Ai dai kam ya kamata dama anats cewa wai yarinyar na kama dake”.
“Dani kuma Mommy?”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da zama akan 2sitter tana cire hijabinta tace.
“Eh toh da Raudat take kama Raudat kuwa kinga dake take kama shiryasa kowa ke cewa Jaririyar kamar Khausar ²”.
Murmushin fuskarta ta faɗaɗa kana tace.
“Aikam bari nayi wanka Inje inga mai kama dani”.
Ta ida maganar tare da wucewa Bedroom akan beside drawer ta ajiye tarkacen hannunta kana ta cire Uniform ɗin ta ɗaura towel tashiga toilet.
Tayi wanka tana fitowa ta zauna gaban Dressing mirrow tare da shafa Lotion ɗin ta, kana ta sanya dogon rigar material Sky blue ta yane Kanta da baƙin gyale, sannan ta feshe jikinta da turaruka masu daɗin ƙamshi ta fice.
Mommy dake zaune a falo ta kalleta tare da cewa.
“Khausar ko abinci fa baki ciba?”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“A'a Mommy sai na dawo”.
“Adawo lafiya”.
Anutse ta fita tafiya kaɗan tayi ta isa gidan mutum uku kawai ta samu aɗakin.
Kusa da Aunty Asiya dake mata murmushin ta zauna tare da cewa.
“Aunty Asiya ina baby?”.
“Gata nan”.
Ta faɗa tana nuna mata matar dake gefenta.
“Masha Allah, wata tana kama da niko? Allah ya raya mana”.
Murmushi Aunty Asiya tayi tare da faɗin.
“Ameen Khausar ga Baby”.
Da sauri Khausar ta karɓe ta tare da cewa.
“Bari inga mai kama dani”.
Ta faɗa tana zubawa Jaririyar Ido farace sol da ita ga wani yalwataccen gashi daya kwanta asaman goshinta kana girar tama da yelwataccen gashi bakinta yayi pich da dogon Eyelashes.
Da sauri Khausar ta ɗago kanta da murmushi afuskarta tace.
“Aunty Asiya wallahi kam Baby kam tayi kyau Masha Allah”.
Jinjina kai Aunty Asiya tayi tare da cewa.
“Aikam dake take kama, wai Gimbiya Dadu tace idan kinzo kitso ina yawan kallonki shiyasa na haifi me kama da ke”.
Baki Khausar ta taɓe tare da cewa.
“Uhm Ita kuma duk duniya akwai wanda yafi ta kallona ne?”.
Murmushi Aunty Asiya tayi, Khausar kuwa Jaririyar ta miƙa mata tare da miƙewa kana tace.
“Bari in tafi Aunty Asiya Allah ya raya”.
Karɓar Jaririyar Aunty Asiya tayi kana tace.
“Toh ki Gaishe da Mommy da gajiya”.
Amsawa Khausar tayi da cewa.
“Za taji” kana ta fice.
Bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon zaune ta samu Mommy a inda ta tafi ta barta kusa da Mommy ta zauna da murmushi afuskarta tace.
“Wallahi Mommy Jaririyar muna kama nima naga kamar mu”.
Jinjina Kai Mommy tayi tare da ajiye wayarta kana tace.
“Nima gaskiya naga kamar ku sai naga kamar lokacin kina Jaririya, kuma haka Raudat ma take shiyasa ake ganin kamar dake take kama”.
Veil dake kanta ta janye tare da cewa.
“Ai dai kam”.
Miƙewa tayi tare da cewa.
“Mommy bari na ɗauko abincina”.
Kai Mommy ta gyaɗa mata sannan ta wuce kichen ɗin.
Bayan kwana shida; Alhamdulillah a yau ne su Khausar suka rubuta Final Exam ɗin su cike da tsananin farin ciki ko wanne ɗalibi ya fito daga hall da suka rubuta Exam ɗin, cikin tsanananin farin ciki Khausar ta nufi jikin tap ɗin ruwa tare da buɗe wa ta cika wani ƙaramin Bocket kana ta nufi kan Asma'u dake tsaye.
Rungumeta tayi tare da sheƙa musu ruwan tace.
“Thank God My Asmeey Alhamdulillah yau mun taka matsayi na farko a fannin karatun mu”.
Cike da farin ciki Asma'u da jikinta ke ɗigan ruwa ta kalleta kana tace.
“Sosai kuwa Khausar mun godewa Allah”.
Baki ɗaya ɗaliban haka suka ringa jiƙa jikinsu da ruwa cike da matsanancin farin ciki kasancewar an hanasu penday yasa suka shiga jiƙa jikinsu.
Khausar kuwa kallon Samira sani da itama jikinta ke jiƙe tayi tare da miƙa mata hannu kana tace.
“Assalamu Alaikum, Alhamdulillah yau kam abinda ya haɗa ya raba”.
Hannunta Samira Sani ta riƙe tare da murmushin gefen baki sai kuma ta watsa mata Harara dama can ba wani haushin Khausar take jiba tunda Moddibo ba wani kulata yake ba sai dai yadda tafisu ƙwazone ke bata haushi.
Acan ɓangaren Malamai kuwa baki ɗaya sun hallara a inda suka tanadar dan yin taro Moddibo ne kaɗai baya wajen bayan duk ɗalibai sun hallara.
M Jameel ya miƙe tare da hura Microphone kana yace.
“Assalamu Alaikum warahmatullah Wabarkatuhu”.
Baki ɗaya Suka amsa da. “Wa'alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu”.
Yayi gyaran murya tare da cewa.
“Da farko amadadin dukkan malamai da shuwagabannin wannan Makaranta muna taya ɗaukakin Ɗaliban wannan makaranta murnan kammala jarrabawar su na gama makarantar.
Allah ya bada sa'a Ubangiji ya baku ikon fitowa da sakamako mai kyau”.
Baki ɗaya wajen suka amsa da.
“Ameen”.
Tsayuwarsa ya gyara tare da cewa.
“Insha Allah shugaban makaranta zai bada Award da hannunsa ga dukkan ɗaliban da suka cancanta Malam Bismillahi”.
Miƙewa Malam Arɗo yayi tare da karɓan Microphone ɗin kana yace.
“Ina taya ɗaukakin Ɗaliban wannan makaranta ta *AL,ANSAR Academic School* murnan kammala karatun su na matakin farko Allah ya Albarkanci karatunki Ubangiji ya ɗauka ku aduk inda kuke”.
Baki ɗaya suka amsa da.
“Ameen”.
Gyaran murya yayi tare da cewa.
“Zamu miƙa award ga ɗilibar da tafi ko wacce ɗaliba.
Hazaƙa da tsafta”.
Baki ɗaya wajen sake nutsuwa yayi dan jin wacece wannan.
“Khausar Usman Abubakar Lelewal itace ɗalibar da tafi ko wacce ɗaliba Hazaƙa da kuma tsafta”.
Atake wajen ya kaure da kabarra masu taya ta murna irin su Asma'u da Aunty Ruƙayya nayi yayin da masu baƙin ciki irinsu Samira da sauransu keyi.
Cike da nutsuwa Khausar ta miƙe tare da ƙara sawa ta amshi Award cike da tsananin farin ciki.
Gyaran murya Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Ɗalibar da tafi ko wacce ɗalibai Nutsuwa da biyayya itace Asma'u Ahmad”.
Cike da farin ciki Asma'u ta miƙe tare da ƙara sawa ta amshi Award ɗin ta haka aka kira sauran mutum uku aka basu Award .
Cike da farin ciki Khausar ta koma gida kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da cewa tana cikin farin ciki zaune take afalon hannunta riƙe da bowl na Fruit Salat.
Haiydar ne yashigo falon bakinsa ɗauke da Sallama kallon Khausar yayi tare da cewa.
“Addah Khausi Uncle Naseer yana kiranki afalon Abba”.
Murmushi tayi tare da ajiye bowl din Fruit Salat ɗin kana tace.
“A'a lallai kam ina zuwa”.
Murmushi Mommy dake zaune gefenta tayi tare da cewa.
“Yau kam Alhamdulillah gidan nan muna cike da farin ciki Khausar an gama Secondary school tare da samun Award”.
Miƙewa tayi tare da cire hijabin Uniform da har zuwa lokacin yake jikinta wurgi tayi dashi tare da faɗin.
“Yau kam nayi hannun riga da Uniform daga yau nayi bye bye da uniform, shiyasa ko aiki banason aikin da zai kasance min da Uniform, daga yau na wurgar da Uniform aduniya shiyasa Insha Allah Jenouelist zan zama in dinga zaƙulo gaskiya aduk inda yake ”.
Murmushi Mommy tayi tare da cewa.
“Toh Allah ya taimaka Ubangiji ya cika miki burinki”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Ta faɗa tare da shigewa Bedroom kana ta cire Uniform ɗin ta tare da shiga toilet ta sakarwa kanta shawer bayan ta gama wankan ta fito Lotion ta shafa tare da sanya doguwar rigar atanfa mai golden kana tayi ɗaurin ture, ta feshe jikinta da turarukanta masu daɗin ƙamshi kana ta fice. Jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin kai tsaye falon Abba ta nufa bakinta ɗauke da Sallama.
Lumshe Idanu Naseer dake zaune kan 2sittee yayi tare da zuba mata idanu yana shaƙan daddaɗan ƙamshin turaren yace.
“Congratulation My Khausi yau kin gama makarantar ki, nayi matukar farin ciki abubuwa na tafiya yanda ya kamata”.
Murmushi Khausar tayi cike da farin ciki ta jinjina masa kai.
Ahankali Naseer ya ɗauko Flowers dake jikin wata leda anyi wrapping ɗinsa tare da ɗauko kwalin waya iPhone tare da tarin Choculate ya miƙa mata.
“Ga gift ɗin Graudion ɗin ki”.
Wara Ido Khausar tayi tare da kallon Uban gift ɗin cike da tsanananin farin ciki ta ɗago manyan Idanunta tare da kallon sa kana tace.
“duka wannan na wane?”.
Kai ya jinjina mata tare da faɗin.
“Yes My Wife duka naki ne”.
Langwaɓar da kai tayi kana tace.
“Mommy ta hanani riƙe waya tace sai na gama Secondary school duka ko lokacin da muke Ss duk abinda zanyi da waya tace sai dai in karɓi nata yanzu kuma kaga”.
Saurin katseta yayi tare da cewa.
“Ai me ai kun gama kin manta yau kukayi final Exam”.
Jinjina kai tayi tare da cewa.
“Eh haka ne fa Uncle Naseer”.
Murmushi yayi tare da faɗin.
“Kada kice komai kawai kice Allah yamin Albarka, ya mallaka min ke Insha daɗin zama dake”.
Shiru tayi tare da ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta.
Miƙewa yayi daga kan 2 sitter da yake zaune ya dawo gabanta ya zauna aƙasan rock ɗin daya mamaye ɗakin kana cikin narkar da murya yace.
“Naga yau kina cikin farin ciki?”.
Kai ta gyaɗa masa tare da cewa.
“Sosai ma kuwa Uncle Naseer”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da narkar da murya kana yace.
“Nima ki sani cikin farin ciki mana”.
Tana wasa da yatsun hannunta ta ɗago kanta tare da cewa.
“Toh me kake so in yimaka?”.
Karyar da murya yayi tare da faɗin.
“Ki cika min alƙawarin da kika ce zaki yimin, kince sai kinyi shawara nan da kwana biyu amma yau kusan kwana goma kenan da yin maganar mu kullum idan na tambayeki, sai kice baki yi tunani Ba dan Allah yau dai kiyi min”.
Cike da farin cikin kammala karatun ta da kuma nasaran data samu ta kallesa tare da cewa.
“Nayi alƙawari Uncle Naseer duk abinda kake so zanyi maka matuƙar bai saɓawa addinin Musulunci ba”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da gyara zamansa kana yace.
“Naji daɗi My Khausi, Khausar ɗina ina sonki My life is nothing without you, you are my World”.
Kallonsa kawai take Amma batace Komai ba.
Ahankali ya sanya hannunsa acikin aljihu tare da ciro wani farin ƙyalle fari ƙal yana fitar da wani irin ƙamshi mai masifar hawa kai tare da birkita lissafi, ƙyallen ya miƙa mata ba tare da ta karɓa ba ta tsaida Idanunta akansa kana tace.
“Wannan kuma na menene?”.
Langwaɓar da kai yayi tare da cewa.
“Ki karɓa mana”.
Girgiza kai tayi tare da faɗin.
“Toh ka faɗa min na menene sai na karba”.
Marerece Murya yayi kana yace.
“Ki karɓa mana zan faɗa miki ai ba dai kinyi al'ƙawari ba?”.
Kai ta gyaɗa tare da karɓa..
Murmushi yayi tare da shafa sajensa kana yace.
“Ki shin shina ƙamshin mana”.
Kai ta girgiza tare da jan siririn tsaki asaman laɓɓanta kana tace.
“Haka ma yayi dan inajin ƙanshin yana hawa kai!”.
Zama ya gyara tare da cewa.
“Allah ko?”.
Matsar da ƙyallen tayi daga jikinta saboda irin ƙamshin da yake fitarwa mai masifan hawa kai.
Anutse ta ɗago manyan Idanunta dake lumshe ta kallesa tare da cewa.
“Toh Uncle Naseer mai zan maka da wannan ƙyallen?”.
Matsowa kusa da ita yayi har gwiwan ƙafarsa na taɓa yatsun ƙafa ta cikin wata siga ya karya murya tare da faɗin.
“Khausar kinyi min al'ƙawari ko?”.
Kai ta gyaɗa tare da cije lips ɗin ta kana tace.
“Eh nayi al'ƙawari”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kallon ƙofan falon kana yace.
“Kuma na faɗa miki cewa sirrine tsakanin mu dake”.
Kallon farin ƙyallen tayi tare da juyawa ta kallesa kana tace.
“Eh nasani”.
Sauƙe numfashi yayi tare da fesar da iska daga bakinsa kana yace.
“Sannan kinsan na faɗa miki cewa ci gaban mu ne. Ni dake da kuma ƴaƴan da zamu haifa?”.
Jinjina kai tayi tare da cewa.
“Eh nasani ka faɗa min mana”.
Langwaɓar da kai yayi tare da narkar da murya kana yace.
“Zan faɗa miki amma da farko ina so ki.
Sirrinta min dan nasan duk duniya babu wanda zan roƙa ya min inba keba”.
Aƙage ta kallesa tare da faɗin.
“Toh ina jinka ka faɗa min menene?”..
Kallon fuskarta yayi tare da sakin ajiyar zuciya kana ya sunkuyar da kansa.
Idanu Khausar ta zuba masa tare da kallon yanda ya sunkuyar da kansa ƙasa sannan tace.
“Ka faɗa kawai”.
Ɗago kansa yayi cikin sigar rauni yace.
“Kinyi al'ƙawari ba zaki faɗawa kowa ba ko?”.
Jinjina kai tayi tare da cewa.
“Nayi al'ƙawari bazan faɗa ba”.
Sauƙe Ajiyar zuciya yayi tare da faɗin.
“Kin tabbata?”.
Aƙage ta gyaɗa masa kai batare da tace komai ba dan tagaji da wannan tambayar tasa.
Iska ya furzar daga bakinsa kana yace.
“Khausar nasan dai tuntuni kin daɗe da fara period ko?”.
Cikin sauri tayi ƙasa da kanta cike da mamaki da kuma kunyar tambayarsa.
Ya shafa ƙyeyarsa tare da karyar da murya kana yace.
“Ya kikayi shiru?”.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Babu komai”
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da tsira mata idanu kana yace.
“Ki faɗa min gaskiya tsakanin ki da Allah nasan dai kin daɗe da farawa?”.
Ƙin cewa komai tayi sai ƙasa data sake yi da kanta.
“Ki faɗa min gaskiya kiyi haƙuri na haɗa ki da Allah”.
Still Nan ma shiru tayi Zuciyarta na bugawa.
Zama ya gyara tare da faɗin.
“Nasan dai kin fara tabbas”.
Ataƙaice ta gyaɗa masa kai.
Zare Ido yayi tare da cewa.
“Yauwa Alhamdulillah
kin fara period din ko?”.
Kai ta gyaɗa fuskarta babu walwala tace.
“Eh”.
Sajensa ya shafa tare da cewa.
“Alfarma to nakeso kiyi min”.
Gyara zamanta tayi tare da ɗago kanta kana tace.
“Toh wace iriyar alfarma ce zanyi maka?”.
lumshe idanunsa yayi tare da buɗe su akanta kana yace.
“Bance ki bani kuɗi ba, ban kuma ce kibani ranki, ko lafiyarki ba, kuma bance ki mallaka min kanki ba, kawai abinda nake so ki sammin Period ɗin ki”.
Atsorace ta zare Idanunta tare da ɗago kanta kana cike da mamaki tace.
“In san maka Period Kuma Uncle Naseer? Kamar yaya ban gane ba”.
Tayi mgnar jikinta na rawa kana ta miƙe cike da tsoro tana ja da baya.
Da sauri ya ɗaga mata hannunsa cikin sassauta murya yace.
“Karki manta fa kinyi al'ƙawari zaki sirranta min maganata, kuma shiyasa na faɗa miki dan nasan cewa zaki siririn ta min ki zauna mana kiji”.
Ya ƙare mgnar yana kuma yin mgnar zuci.
“Wannan yarinya sirri baya kamata da wuri, duk da ta shaƙi ƙamshin turaren nan amman ga yadda take min gardama”.
Yayi mgnar cikin ƙoƙon zuciyarsa dan baiyi zaton zata iya musa mishiba.
Ita kuwa Khsusar kallonsa tayi jikinta na rawa ta girgiza kai tare da faɗin.
“Toh ai ban fahimci mai kake nufi bane! wannan wace iriyar magana ce? me hakan yake nufi kenan?”.
Marerece Murya yayi da alamun damuwa yace. “Dan Allah dan darajar Annabi Muhammad (S.A.W) kiyi shiru kar kuyi magana da ƙarfi kiyi magana ahankali zaki fahimceni”.
Lokaci ɗaya tashin hankali ya bayyana afuskarta cike da tsoronsa tace.
“Toh mai zanyi maka?.
Kai ya langwaɓar tare da karyar da kai tamkar mai shirin fashewa da kuka yace.
“Nasan kina Period”.
Cikin fusata da yanayin tsoro tace.
“Ni ka daina maimaita min wannan maganar”.
Matsota yayi tare da cewa.
“Dole in maimaita Miki wannan maganar tunda abinda nake sone kuma kikayi al'ƙawarin zaki yimin!”.
Girgiza kai tayi still jikinta na rawa tace.
“A'a ai ko al'ƙawari idan abu yafi ƙarfin ka ba zaka yiba zaka janye sa”.
Cikin sauri ya kalleta tare da cewa.
“No baifi ƙarfin kiba Khausar bafa cewa nayi kiyi min komai ba, idan Period ɗinki yazo kika fara kawai zaki ɗauki ƙyallen ne sai kisa shi agabanki madadin kisa Pad Idan yayi awa ɗaya sai ki cire kisa min aleda zanzo in karɓi abuna shine kawai abinda nake so Khausar abinda kaɗai nake sofa”.
Ya ida maganar cikin yaudara murya tamkar zai fashe da kuka.
Ya cigaba da cewa.
“Kuma kada ki manta al'ƙawari kika yimin kuma baifi ƙarfin ki ba sannan ba kanki nace kibani ba”.
Cike da mamaki take Kallonsa cikin yanayin damuwa da alamun tsoro ta zare Idanunta kana tace.
“To me zakayi dashi Uncle mai zaka yi dashi wannan wani irin abune?, Wannan wace iriyar magana ce zaka ce min haka Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Cikin sauri ya riko tsintsiyar hannunta tare da Marerece fuska kana yace.
“Ki yiwa Allah da Annabi ki nutsu Khausar kar ki manta cewa kinyi min al'ƙawari.
Kuma wallahi idan kika faɗawa wani zan miki abinda ba kiyi tsammani ba!”.
Cike da fushi da kuma tsoro tace.
“Toh me zaka yimin tukunna?”.
Karyar da murya yayi tare da saurin dai-dai-ta nutsuwarsa kana yace.
“Zanyi fushi dake”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da sakin murmushi har tayi zaton ko wani mugun abu zai mata tura madaidaicin bakinta tayi tare da cewa.
“Nidai gaskiya banyi al'ƙawari ba Uncle tsoro nakeji, amma tukunna mai zaka yi dashi?”.
Ɗan hararanta yayi tare da cewa.
“Ke dai me ruwanki? Maganin abu zanyi da shi maganine ance sai na samu Period ɗin zanyi maganin?”.
Kallonsa tayi still zuciyarta na cigaba da tsinkewa tace.
“Wani irin maganine wannan wanda saida period ɗin mace za'ayi shi?”.
Wani irin kallo ya watsa mata kafin ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Magani ne kawai nace miki magani zan haɗa amma kamar baki yarda dani ba inada matsala ne ke dai in Zaki yimin