Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sakayya Complete Hausa Novel by Aisha Aliyu Garkuwa

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   58 / 140

171K to 174K   out of 417.8K words

wata zuciyar tace kasani ko yazo suna tare da Innayi suna can suna ƙus-ƙus atake ya amince da abinda zuciyarsa ya raya masa cikin mutuwar jiki ya nufi ƙofan falonsa tare da buɗewa.
Wani sanyayyan iska ya hurasa ahankali ya ɗaga kansa sama gani yayi hadari ya fara haduwa sai walƙiya dake haskawa can ƙasa alamun yanzu hadarin ya fara, garin ya danyu duhu sakamakon rashin wuta ga kuma hadarin,
ahankali yabi sararin samaniyar da kallo ganin yanda hadarin yayiwa garin zobe kana aƙasan ransa yace to kodai wannan hadarin ne ya hana J zuwa sai kuma yace to kodai yana ɗakin Innayi ya faɗa yana taka step ɗin ahankali.
Cikin sauri Innayi ta haske masa ido da touch light mai masifar haske cikin han zari ya Janye hannuunsa dake danne da J ɗinsa ya tare Idanunsa dashi saboda hasken touchlight daya haska masa ido.
Cike da kulawa Innayi tace.
“Moddibo ya dai lafiya ina zuwa Atsakiyar adaren nan?”.
Ahankali ya sake sakƙowa daga kan step ɗin tare da jingina bayansa da jikin filan barandarsa, kana hannunsa na dama na kan flowes dake gefe yace.
“Kece fa kike ganinsa tsakiyar dare ne, dudu shabiyu da rabi ne fa yanzu”.
Kallonsa tayi tare da cewa.
“Tsakiyar dare ne mana Moddibo yanzu fa ƙarfe shabiyu harda rabi ai tsakiyar dare ne, to amma me kafito yi lafiya dai ko?”.
Cikin sanyin murya yace.
“J ne har yanzu bai zo ba kuma ya fito akan zai zo ma ya kirani awaya kan cewa yanzu zai shiga wajen Abbansa ya masa saida safe ya fito, kuma har yanzu bai iso ba sannan nata kiran layukan sa basa shiga”.
Ya ida maganar akasalance.
Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe tare da cewa.
“Toh dan bai zoba Moddibo ai ba abin tashin hankali bane, kaga yanayin wannan hadarin daya haɗu zai iya hanasa zuwa wataƙil daya shiga wajen Abban nasa zaice dare yayi kuma ga hadari ya bari sai gobe”.
Da sauri ya katseta da cewa.
“To ai Innayi wayarsa bata shiga fa”.
Saurin Kallonsa Innayi tayi tare da cewa.
“Ka kira layinsa duka?”.
Kai ya jinjina mata.
“Eh na kira layukansa duka fa basa shiga”.
Cikin yanayin bacci ta kalli Moddibo tare da sakin hamma kana ta aro Jarumtaka tare da cewa.
“To ko dai network ne?”.
Lumshe Idanunsa yayi tare da Girgiza mata kai kana yace.
“A'a ba network bane cemin akeyi akashe kuma fa Innayi J baya kashe wayarsa, ko zai kwanta komai yaya kuma nasan wayar J baya rasa caji”.
A hankali Innayi ta rufe idonta jin kamar tsinkewar zuciya ya ziyarci ta.
Amma sai ta daure kana tace.
“To amma kaga jiya ma kace min wajen Umminsa ya kwana to ko dai yauma yaje canne ne ya kashe wayarsa dan kada kayi ta kiransa?”.

Jinjina kai yayi tare da faɗin.
“Ok ba mamaki fa bari na kira Ummi”.
Cikin sauri Innayi ta kallesa tare da cewa.
“Aƙarfe ɗaya saura zaka kirasu?”
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Eh Innayi in dai har wurin Ummi yake nasan yanzu zasu ganshi kamar takwas na dare ne, saboda nasan yanzu suna hira ba suyi bacci ba.
Kai Innayi ta gyaɗa tare da gyara tsayuwar ta kana tace.
“Toh shikenan ka kira”.

Dearling number Ummi yayu.
Acan ɓangaren Ummi kuwa kwance take yayin da idanunta ke lumshe cikin tsananin tsinkewar zuciya da kasala jin rurin wayarta yasa ta miƙe firgice cikin yanayi sanyi sanya hannunta na dama ta janyo wayar tare da ƙurawa screen ɗin Ido sunan Moddibo ke yawo.

Cikin sauri tare da rawan jiki tayi Picking call ɗin tare da kaiwa Kunnenta batare data amsa Sallamar daya mata ba tace.
“Babana Lafiya?”.
Cikin ƙoƙarin danne damuwarsa yace.
“Ummi lafiya ya naji kamar kin razana?”.
Ahankali ta koma ta jingina bayanta da jikin kushin ɗin tare da lumshe idanunta kana cikin wata raunan'niyar murya mai cike da kasala da tsoro ta fesar da numfashi tare da cewa.
“Gaba ɗaya ma ai. Arazanen nake Babana”.
Moddibo kuwa cikin kasala da mutuwar jiki ya yaja numfashi tare da fesar wa kana yace.
“To Ummi me yafaru?”.
Buɗe Idanunta dake lumshe tayi tare da dafe ƙirjinta da still yake bugawa kana tace.
“Ban saniba amma gaba ɗaya ina jina wani irin gani nan dai kamar mara lfy, kuma ba zance ga abinda yake damuna kai tsaye ba”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.
“Toh amma Ummi lafiyar ki lau?”.
Kai ta gyaɗa masa kamar yana gabanta kana tace.
“Lafiya ta ƙalau,Amma Babana lafiya ka kira yanzu?”.
Numfashi ya sauke tare da lumshe idanunsa kana ya sake jingina bayansa da jikin step ɗin tare da cewa.
“Eh lafiya lau babu komai dama zan tambayeki ne ko dai J yazo yana wurinki ne munyi dashi tun ɗazu akan zai zo har yace min gashi ya fito amma zai sallami Abbansa ne kawai ya taho”.
Sai kuma ya lumshe idanunsa tare da cijan lip ɗin sa na ƙasa kana yace.
“Amma har yanzu be taho ba, inata jiran sa ko ƙofar gida bamu rufe ba, shiyasa nace bari na kira koya biya wajenki, da yake jiya ma nan ya kwana!?”.
Rumtse ida nunta tayi da masifar ƙarfi k cikin wani azabebben tsinkewar zuciya da faɗuwar gaba ta buga hannunta na dama aƙirji tare da cewa.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n. Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan min_
bai zo ba kuma yace maka zai zo?
Abbansa kaɗai zai Sallama?”.
Gyaɗa kai Moddibo yayi tamkar yana gabanta kana cikin raunan'niyar murya mai cike da sanyi yace.
“Eh Ummi”.

Cikin wani irin yanayi na taraddadin zuciya da rauni Ummi tace.
“Ya Ubangiji Allah ka dubeni da Idon Rahma. Ya Allah ka tsare wannan bawan naka, aduk inda yake Alfarman Annabi da Alkur'ani”.
Jin salatin da kuma yanayin da Ummi tayi Magana cikin firgici ya farkar da Asma'u, Bashir da Malam Ahmad Aruɗe Asma'u ta miƙe tare da dafe kanta da taji yayi masifar sarawa ta sauƙa daga kan gadon.

Acan ɗakin Bashir kuwa Hasbunallahu wani'imal wakin ya furta tare da sauƙa ƙasa kusan atare suka fito falon ko wannensu zuciyarsa na bugawa da kaso tamanin cikin ɗari.
Moddibo kuwa cikin sanyu da ruɗu yace.
“Ameen ya Allah Ummi ameen ya rabbil Izzati”.

Cikin zulumi Ummi ta runtse Idanunta kana tace.
“Amma Babana ka kira Abbansa mana”.
Numfashi Moddibo ya fesar tare da kallon Innayi data tsaresa da ido cikin yanayin razani yace.
“Eh Ummi nayi tunanin kiran Abbansa amma sai nace bari na fara kiranki tunda jiya yazo na, sannan Ummi nasan J baya kashe wayarsa rashin shigar wayarsa nema yafi damuna!”.
Girgiza kai Ummi tayi yayinda ruwan hawaye masu masifar ɗumi suka cika kwarmin Idanunta kana cikin raunan'niyar murya tace.
“Tabbas baya kashewa ka kira Abbansa kaji”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Eh dama zan kirasa amma Innayi tace ko Abbansa ne ya hanasa zuwa ganin hadari”.

A hankali tace.
“Anya?,Ka kira sa dai”.

“Amma yanzu dare baiyi ba Ummi”.

Cikin sauri tace.
“A'a ka kira Babana ka kira Abbansa ɗin duk yanda kukayi ka kirani ka sanar min”.
“Toh”.
Moddibo yace kana ya katse kiran.

Asma'u da Bashir kuwa zuru-zuru sukayi da ido domin suna iya jiyo sautin muryar Modibbo.
Durƙusa wa Asma'u tayi tare da toshe bakinta kana tashiga.
Girgiza kanta tare da cewa.
“Ya Allah kada ka jarabcemu da abinda baza mu iyaba ɗaukaba Allah ka tsare Yaya Jameel aduk inda yake ya Allah kada ka bari wani abu na cutarwa ya sameshi”.
Cikin raunin murya Ummi ta kalleta Atake taji wasu hawaye masu masifar ɗumi sun zubo kuncinta.
Ahankali Malam Ahmad da jikinsa yayi masifar sanyi ya ƙarasa kusa da Ummi.

Moddibo kuwa yana katse kiran ya shiga contact tare da fito da Number Abban M Jameel.
Kana ya Kalli Innayi cikin sanyin murya mai cike da tashin hankali yace.
“Kin gani ko Innayi baya can. J baije gidan Ummi ba. Innayi ina J ya tafi bayan yasanar dani cewa zai taho”.
Lokaci ɗaya wani masifaffen tsoro da tashin hankali ya ziyarci Innayi wanda ta kasa ɓoyewa har hakan ya bayyana asaman fuskarta dake nuni da tsantsar ruɗu.
Cikin dakiya da kuma nuna masa babu komai insha Allah ta gyara tochligt dake hannunta kana tace.
“Ka dai kira Abbansa muji wataƙil yana can tare dashi hadarin ne ya hanasa fitowa”.
Kai ya gyaɗa mata tare da dearling number Abban M Jameel yana jin yanda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da masifar ƙarfi yana bada sautin dif-dumm-dif dumm.
Abba dake kwance kan 3sitter Idanunsa arufe bacci ya fara fusgarsa yaji suwwan wayarsa Atsakiyar kansa afirgice ya miƙe tare da zama kana ya duba screen ɗin wayar nan yaga sunan Moddibo na yawo cikin rawan jiki yayi Picking.
Atare Abba da Moddibo sukayi Sallama.
Ahankali Moddibo ya sauƙe numfashin tare da ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa kana yace.
“Wa'alaikum Salam Abba”.
Cikin yanayin firgici da ruɗu Abba ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Na'am Aliyu ya akayi?”.
Numfashi Moddibo ya fesar kana yace.
“Lafiya Abba”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da jingina bayansa da jikin kushin kana yace.
“Ya gida kowa lafiya dai?
Jameelun yaƙara so yana lafiya ko?”.
Lokaci ɗaya zuciyar Moddibo ya buga da masifar ƙarfi kana yayi saurin dafe ƙirjinsa tare da cewa.
“Abba baya gidane”.
Wani irin azabebben bugawa zuciyar Abba yayi kana yace.
“A'a bakwa tare ne tun 10:15 ai ya sallameni yace min zai taho wurinka”.
Moddibo kuwa da sauri ya rumtse idanunsa tare da dafe jikin step ɗin yana mai jin kansa na masifar sarawa tamkar zai rabe gida biyu cikin raunin murya yace.
“Abba tun ƙarfe 10:15 ya fita kuma yace wajena zai zo? Abba tun ɗazu fa nake jiransa ko ƙofar gida bamu rufe ba har yanzu J bai zoba sannan fa nata kiran layukan basa shiga”.

Cikin tsananin razani da tsinkewar zuciya Abba ya miƙe tsaye kana yace.
“Aliyu mai kace?”.
Araunane Moddibo da Idanunsa ke juyawa ya dafe kansa kana cikin sanyin murya yace.
“Abba na yita kiran layinsa baya shiga”.

A ruɗe Abba ya miƙa tsaye tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n to lafiya Aliyu?”.
Girgiza kai Moddibo yayi tare da gyara tsayuwar sa kana yace.
“Toh Abba kuma yace waje na ɗin zai taho?Abba J bai zoba bafa”.
ya ida maganar cikin raunin murya mai cike da tsantsar tashin hankali.

Atake zufa ya wanke wa Abba jiki duk da iskar dake kaɗawa d ƙarfi ya haɗiye wani abu mai ɗaci kana yace.
“Ko dai gidan Ummin sa yaje”.
Da sauri Moddibo ya girgiza kansa muryarsa na rawa yace.
“Um-um Abba baya can yanzu nayi waya da Ummi itace ma tace in Kira ka Dan ni Ina tunanin dare ma yayi bazan kira ba”.

Cikin tsinkewar zuciya Abba ya nufi ƙofar falon Hajiya Karima da sautin muryansa ya farkar da ita tayi saurin fitowa daga Bedroom ɗin Aruɗe ta kallesa kana tace.
“Lafiya Alhj?”.
Girgiza kai Abba yayi tare da cewa.
“Jameelu ba agansa ba wai baije wajen Moddibo ba sannan baije wajen Umminsa ba”.
Da sauri ta dafe ƙirjinta kana tace.
“Ba agansa ba kuma gashi yanzu ƙarfe ɗaya”.
Kasa cewa komai Abba yayi ya nufi ƙofa da sauri.
Tare da cewa.
“Miƙo min key mota”.
Cikin sauru tabi bayansa tare da Kallonsa ganin Gajeren wando da single ne kaɗai ajikinsa yasa tace.
“Toh yanzu ina zaka je adaren nan??”.
Cikin raunin murya yace.
“Karima ina zanje kike tambaya ta? Jameelu na fa baya gidansu Aliyu sannan baya gidan Umminsa to ina Jameelu yaje kinsan waye Jameelu da in dai baya nan yana gidansu Aliyu ko gidan Umminsa tabbas da akwai abinda yake faruwa”.
Cikin sauri ta juya tare da komawa Bedroom ta dauƙa Masa Jallabiya da key mota kana ta sanya hijabinta ta fito tare da miƙa masa.

Karba yayi yana tafiya yana saka jallabiyar kana ya nufi inda Motarsa yake ya shiga cikin sassarfa tabi bayansa yana shiga mazaunin Driver itama tayi saurin buɗe gefen mai zaman banza ta Zauna.
Kallonta yayi tare da cewa.
“A'a ki koma”.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“A'a Alh ya za'ayi in barka ka tafi kai kaɗai muje dai”.
Kai ya gyaɗa batare da yace komai ba ya figi motar.
Suka tafi bayan mai gadi ya buɗe masa ahankali ya fara bin hanyar Yana dudduba gefen titin kana cikin sanyin murya yace.
“To ko dai motarsa ta samu matsale ne?”.
Girgiza kai Hajiya Karima tayi kana tace.
“Idan ma motarsa ta samu matsala Alh ai saidai ya kira akawo masa wata”.
Kai ya jinjina still Yana cigaba da Driving ɗin yayin da zuciyarsa ke cigaba da bugawa da kaso Cassa'in cikin ɗari suna cikin tafiya har suka isa gidan su Moddibo.

Moddibo dake tsaye coumpund ɗin har zuwa lokacin ya gagara koda ƙoƙƙwaran motsi yayi saurin kallon gate ɗin ganin hasken mota Itama Innayi dake tsaye tayi saurin bin wajen da kallo zuciyarta na cigaba da bugawa.
Cikin sauri tare da rauni yace.
“Toh waye wannan ko dai motar J ne?”.
Ya faɗa tare da nufar gate ɗin Innayi kuwa ido ta zuba masa har ya buɗe gate.
Moddibo kuwa yana buɗe gate din idanunsa suka sauƙa akan motar Abba.
Cikin sauri ya ƙarasa jikin motar tare da cewa.
“Abba kaine?”.
Jinjina kai Abba yayi asanda ya ƙarasa fita daga motar kana cikin raunin murya yace.
“Eh Nine Aliyu ina tsammanin Jameelu yana nan to idan ba nan ba ina Jameelu zai je adaren nan.
Amma anya ka bin cika baya gidan Umminsa ba wasa take mana ba?”.

Girgiza kai Moddibo yayi cikin mutuwar da jiki da rauni yace.
“A'a Abba baya can tunda nayi magana da Ummi kuma yanzu da muka gama waya da kai ma na kirata nace baya can itama kuka fa takeyi”.
Cikin ruɗu da rashin sanin madafa Abba yace.
“Toh kazo muje can ɗin mu duba may be ko motarsa ta ɓaci ahanya can ya nufa”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da faɗin.
“To bari in ɗauki motata dan nasan Innayi ma bazata zauna ita kaɗai agida ba”.
Ya faɗa tare da shigewa cikin gida kai tsaye falonsa ya nufa ya ɗauki key sannan suka fito da Innayi acikin motar.
Motar Modibbo ce ta shiga gaba na Abba na biye da ita tuƙi kawai Moddibo yake amma baki ɗaya baya cikin nutsuwarsa.

Acan gidan Ummi kuwa tunda Moddibo ya sanar mata M Jameel baya gidan Abba hankalinta yayi masifar tashi ta fito coumpund ta tsaya tana kuka yayinda Asma'u da Bashir ke taya ta cikin tsanananin kaɗuwa.

Cikin rarrashi da nasiyya Malam Ahmad ke tausanta dasu Asma'u.
Cikin sauri Ummi ta ɗaga kanta ganin hasken motoci abakin gate ɗin gidan su.
Aruɗe ta kallesa tare da cewa.
“Ka kalli hasken mota Malam ko dai Jameelu ne?”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ki kwantar da hankalin ki Fatima dan Allah ki nutsu Insha Allah babu komai, ba abinda zai samu Jameelu”.
Kai ta girgiza kana tace.
“A'a to ai naga hasken mota ne”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da riƙe hannunta ganin yanda ta firgice kana yace.
“Toh bari naje na duba naga ko waye ne”.
Kai ta girgiza kana cikin raunin murya tace.
“A'a to muje dai”.
Kai ya gyaɗa tare da yin gaba kana tabi bayansa Malam Ahmad na buɗe ƙaramar ƙofa yaga motar Moddibo daf da bakin gate Dai-dai lokacin Moddibo ya buɗe Murfin motar ya fito.
Cikin sauri Ummi ta kallesa tare da leƙa motar dake bayansa kana tace.
“Babana”.
Cikin sanyin murya yace.
“Na'am Ummi J bai zo nan ba dagaske?”.
Cikin muryan kuka ta girgiza kai kana tace.
“A'a bai zo bafa Babana idan yazo ya za ayi in ɓoye muku”.

Cikin mutuwar jiki Abba ya buɗe Murfin motar tare da fita kana ya kalli Ummi da hawaye ke bin kuncinta yace.
“Fatima”.
Saurin Kallonsa Ummi tayi tare da cewa.
“Abban Jameel”.
Cikin yanayin tashin hankali yace.
“Da gaske Jameelu bai zoba?”.
Kai ta gyaɗa Masa still Hawaye na bin kun cinta tace.
“Bai zoba kuma nata kiran wayoyinsa basa shiga”.
Cikintashin hankali da ruɗu suka haɗa baki wajen furta.
_“Innalillahi Wa'inna Ilahi rajiu'n Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha”_.
Cikin sanyi Moddibo ya kalli Abba da idanunsa suka sauya launi saboda tashin hankali kana yace.
“Abba mu koma ta hanyar gidaku mu duba ko dai motarsa ta samu matsala ne ko kuma yayi hatsari ne?”.
Kai suka gyaɗa cikin sauri Ummi ta juya tare da kallon Moddibo kana tace.
“Bari na ɗauko hijabina muje tare”.
Bata jira jin abinda zasu ce ba ta juya da sauri ta koma tare da ɗaukan hijabinta ta fito coumpund ɗin kallon Asma'u da Bashir tayi wanda har zuwa lokacin suna cikin ruɗani, cikin Muryan kuka tace.
“Asma'u ku kula da kanku zamu duba hanya ko Allah zaisa mu gansa”.
Cikin sauri Asma'u tace.
“Ummi zamu biku”.
Girgiza kai Ummi tayi tana tafiya tace.
“A'a ku zauna kada ku fito”.
Daga haka ta fice Malam Ahmad na ƙoƙarin ɗauko mota Moddibo yace.
“Ummi kuzo ku shiga motata kawai”,

Kai ta gyaɗa kana tashiga bayan motar kusa da Innayi.
Malam Ahmad kuwa a gaba, kana suka fara tafiya koda da irin tunanin da yake Aransa duk wani inda suke tunanin mota zai iya maƙalewa ko kuma hatsari sun duba amma babu M Jameel da motarsa babu dalilinsa har unguwar su Abba suka koma amma still Babu shi babu dalilinsa.

Cikin yanayin gajiyawa da ɗimuwa Abba ya buɗe Murfin motar ya fito kana Moddibo da sauran ma duk suka fito.
Cikin raunin murya me nuni da razani Abba yace.
“Gashi mun biyo har nan ma amma baya nan, to mu gwada zuwa asibiti mu duba ko dai yayi hatsari ne ko yaya”.
Cikin raunin murya Moddibo ya Girgiza kai kana yace.
“Abba hatsari kuma? Ai da hatsari ne da munga mota kuma da ankira mu”.
Kafin Abba yace wani abu Innayi ta kalli Moddibo tare da cewa.
“Eh muje dai asibitin saboda Kore shakku”.
Jinjina kai sukayi tare da shiga motar kana suka nufi Asibitin.
Ahankali Moddibo ya kalli Innayi kana yace.
“Toh wani asibitin zamuje kin san dai bawasu manyan asibiti muke dasu ba”.
Cikin sanyi malam Ahmad yace.
“Mu fara zuwa babban asibitin idan yaso sai mu duba sauran daga baya”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da nufar babban asibitin Abba na biye dasu.
Suna isa suka tarar da gate din asibitin arufe kasancewar har biyu tayi,sauran asibitin suka shiga zagayawa amma ko wanne arufe in sun buga an buɗe musuma in sun shiga bashi ba lbrinsa.
Cikin han zari Abba ya cewa Moddibo su nufi Private hospital ɗin Abba haka kuwa akayi.
Suna isa Moddibo ya sauƙa tare da nufar cikin Hospital kana ya tambayi Norse dake aiki ko M Jameel yazo suka ce a'a juyawa yayi ya shiga motar kana suka ci-gaba da nemansa.
Wasa gaske fa babu Jameel ba dililinsa ba motarsa, gaba ɗaya sun shiga ruɗu da zulumi gamida tsoro.

Misalin ƙarfe uku hankalin su ya kai ƙololuwa wajen tashi baki ɗaya sun cika da damuwa zuwa wannan lokacin sun tabbatar ba lafiya domin M Jameel baya yawo sannan Gembulan ba wani babban gari ne da keda charking point ba bare su kai report.
Moddibo kuwa banda tasbihi da kiran sunan Allah babu abinda yake Aransa yayin da kasala da mutuwar jikinsa ke ƙaruwa fiye da farko kana ga hadarin da zuwa yanzu yayi gangami asama da alamar ruwa na gab da sakƙowa, dan tuni aka fara yayyafi.

Abba kuwa tunda suka

58 / 140

Chapters