Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sakayya Complete Hausa Novel by Aisha Aliyu Garkuwa

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   85 / 140

252K to 255K   out of 417.8K words

in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.


Da ƙarfi yayi baya ya zame luuuuu yana faɗin.
“JJJ”.yana rufe bakinsa ya sume.
Ɗaya daga cikin perciens dake zaune a reception ne yayi saurin miƙewa tare da kallon Moddibo dake kwance babu numfashi atare dashi yace.
“Dr Jameel ya suma fa”.
Ya faɗa tare da ƙara sawa kan Moddibo cike da damuwa yace.
“Bawan Allah!,Bawan Allah!!”.
Ina ko motsa wa Moddibo baiyi ba.
Juyawa Dr Jameel Yayi tare da kallon security cikin fushi yace.
“Kun sanshi?".
Atsorace security ya kalli Moddibo dake kwance kana ya kalli Dr Jameel Murya na rawa yace.
“Wallahi Sir munyi iya bakin ƙoƙarin amma mun kasa motarka na shiga shima ya shiga da ganin yanda yake tuƙi yasa nayi ƙoƙarin hanasa badan na kauceba bige ni zaiyi”.
Ɗaya matar dake tsaye cikin tashin hankali tace.
“Dr dan Allah katemaka min ƴata na cikin hatsari katemaki Rayuwar ta”.
Jin haka yasa ya juya tare da take step zuwa inda Office dinsa yake mutumin dake tsaye kan Moddibo yayi saurin Kallonsa cike da damuwa yace.
“Dr Jameel suma yayi fa a duba al'amarin sa shima yana bukatar temakon gaggawa”.
Tsayawa Dr Jameel Yayi ya rasa shin me zaiyi cikin raunin matar dake biye dashi tace.
“Dr ƴata dan Allah”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana ya kalli sauran Norses ɗin yace.
“Ku kula dashi”.
cikin sassarfa ya nufi Office ɗin sa yana shiga ya cire Jacket ɗin sa ya maƙala ajikin kujera ya fita kai tsaye Theater room ya nufa yana shiga ya samu angama shiryata kawai shi ake jira Atake ya fara aiki cike da tsananin ƙwarewa da iyawa na cikakkun likitoci ya fara mata C'S.

Acan ɗakin da Moddibo ke kwance kuwa baki ɗaya Norses ɗin sunyi iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin numfashinsa ya dawo amma abin ya faskara da alama ya tafi suma da wani ɗan ciwone dake tare dashi.
Dr Jameel kuwa sai bayan awa ɗaya ya fito daga Theater room Agajiye ya fito domin mata biyu yayiwa Cs ɗin, Norses na biye dashi abaya tsaye ya hango Mahaifiyar Yarinyar atsaye abakin wajen kallonta yayi tare da sakar mata da murmushi kana yace.
“Alhamdulillah ancire yaro yana lafiya kuma Insha Allah itama tana lafiya”.
Cikin sauri matar ta sauƙe ajiyar zuciya kana da murmushi afuskarta tace.
“Alhamdulillah”.
Dai-dai lokacin Norses suka turo gadon matar na kwance akai wani Corridor suka nufa yanayin tsarin asibitin komai na musamman ne, ɗaya daga cikin Norse da sukayi Operation ne ta fito rungume da jariri kana ta miƙawa matar dake tsaye da murmushi afuskarta tace.
“Alhamdulillah ga Baby boy nan lafiyarsa ƙalau”.
Murmushi matar tayi kana tace.
“Alhamdulillah Allah Nagode maka”.
Dr Jameel kuwa kai tsaye Office din sa ya nufa cikin sauri Norse dake kan Moddibo ta ɗago ta kalli Dr Jameel da alamun damuwa afuskarta tace.
“Dr har ka fito?”.
Kai ya gyaɗa mata alamar Eh.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Sir Wallahi har yanzu fa mutumin bai farfaɗo ba Dr kazo ka dubasa nayi ƙoƙari Inje in Samu Dr Mubarak ya dubasa to kuma already ya tafi”.
Numfashi ya fesar kana yaja siririn tsaki Ido ya zuba mata kana yace.
“Ina Dr Eshaa?”.
Cikin sanyin murya tace.
“Itama bata nan tun Azahar ta fita tace suna da biki”.
Dafe kai yayi kana yace.
“Kenan ba Dr acikin asibitin?”.
Cikin sauri ta girgiza kai tare da cewa.
“A'a akwai perciens ne sunyi yawa akansa shiryasa nace basai na masa magana ba bari inzo wajenka”.
Tsaki yaja kana yace.
“Toh”,Yana ƙoƙarin sauƙa ɗaya daga cikin Norses da sukayi C'S ta kallesa cikin wani narkakkiyar murya tace.
“Sir”.
Cak ya tsaya tare da juyawa ya kalleta wani irin juya masa Idanu tayi tare da kashe masa ido kana ta hura masa kiss.
Dogon numfashi yaja tare da ƙanƙance Idanunsa kana ya narkar da muryarsa yace.
“Ohhh My Baby kasheni kike sonyi ko?”.
Bai jira cewar taba ya juya ya nufi ƙasa yabi bayan Norses data kirasa kana ita kuma wacce ya kira da Baby ta biyo bayansa.
Yana shiga ɗakin da Moddibo ke kwance ya tsaya ya zuba masa ido yana karewa fuskar bawan Allah da karo na farko kenan arayuwar sa ya fara Kallonsa, sai dai tabbas komai nashi baida banbanci dana Ibrahim, toh shin waye shi din.
Ɗaya daga cikin Norses dake ɗakin ne tace.
“Sir ataima ka mishi ya daɗe da suma fa yanzu kusan awa ɗaya da rabi kenan fa yana sume”.
Nunfashi ya fesar tare da sunkuyowa kansa cike da tsantsar ƙwarewa da iyawa da kuma bijinta na ainihin ƙwarerren Likita wanda yasan aikinsa In and Out ahankali ya kamo tafin hannunsa ya fara murzawa kana ya kamo tafin ƙafarsa yana murzawa yana danna jijiyoyin tafin ƙafarsa yana murzawa da sauri ya kai kimanin minti goma yana murzawa kafin ya koma murza jijiyoyin bayan wuyansa ahankali ya sunkuya kansa ya ɗaura bakinsa akan hancinsa ya fesa masa numfashin tare da zuƙo nashi ahankali.

Hannu ya miƙawa Norse dake gefensa cikin wani salo ta ɗaura tafin hannunta akan nasa ta riƙe tana murzawa.
Ahankali ya juya ya kalleta kana cikin wani shu'umin murya yace.
“Ruwa zaki bani ba hannun ki ba”.
Yanayin da yayi magana kaɗai zai tabbatar maka da cewa shi ɗin shu'umin Namiji ne na ƙarshen zamani mai cike da shu'uman da sanin barikanci.
Kai ta gyaɗa kana ta fita kai tsaye Office ɗinsa ta nufa ta ɗauko masa goran ruwa ta dawo ta miƙa masa karɓa yayi kana yasa atafin hannunsa ya watsawa Moddibo ruwan da ƙarfi dogon numfashi Moddibo yaja kana cikin wata raunan'niyar murya yace.
“Ummi naga J ɗin mu Ummi J ɗinmu bai mutu ba Ummi ga Jameelun ki bai mutu ba”. Yayi mgnar da larabci kasancewar dashi ya sume a bakinsa.
Baki ɗaya ido Norses ɗin suka zuba masa musamman wacce Dr Jameel ya kira da Baby wani irin kallo take bin ilahirin jikinsa dashi musamman Lips ɗinsa da yake tattarewa yayi pinch dashi.

Dr Jameel kuwa ahankali ya ɗago Ido ya kalleta cikin wani narkakkiyar murya yace.
“Ya dai Baby wani irin kallo ne wannan kada fa ki cinye sa yana kwance agadon asibiti”.
Sai alokacin ta lura da kallon ƙurullan da take bin Moddibo dashi numfashi ta fesar kana ta narkar da murya tace.
“Masha Allah kaga madaran kyau babu algus ga haiba da kamala”.
Harara ya watsa mata cikin muryarsa dake ɗauke da kishi yace.
“Ya fini ne?”.
Kallonsa tayi kana ta kalli Moddibo tace.
“Hmmm in dai kyaune da ƙasaita ya fika sai dai kuma ai kaine nawa kuma jaruntarka na sani”.
Ɗaya Norse data kirasa ta watsa masa Harara kana ta taɓe baki.

Moddibo kuwa ba tare daya dawo hayyacinsa ba ya cigaba da cewa.
“Ummi ga Jameelun ki ki daina kuka Abba ga J ɗina na gane J ɗina”.
Maganar Moddibo da Dr Jameel yaji shi yasa ya janyo hankalin sa ahankali ya sunkuya da kansa daidai kunne Moddibo yace.
“Ikon Allah”.
Moddibo kuwa Jin sautin Muryan ma sak ta J ɗinsa akunnensa yasa sannu Ahankali ya fara buɗe idanunsa domin ba zai taɓa mantawa da muryarsa ba akan Dr Jameel da har zuwa lokacin ke durƙushe kansa ya buɗe idanunsa cikin wani irin sauri ya yunƙura ya zauna Atsakiyar gadon kana ya janyo Dr Jameel ya fashe da wani irin kuka yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa.
Lokaci ɗaya kuma jikin Norses dake ta faman rawan kai da zumiɗin ganin kyawunsa jikinsu yayi masifar sanyi ganin yanda Kamilin mutum kana Matashi mai jini ajiki ke kuka Dr Jameel ma Baki ɗaya jikinsa ya mutu ganin yanda mutum dake kiranshi da J ke kuka tamkar mace.

Cikin rauni da tarin damuwa kana da kuka da yaci ƙarfinsa ya cigaba da cewa.
“Alhamdulillah Allah Nagode maka Ubangiji ya cika min burina Allah na gode maka dama J kana raye?”.
Ya ida maganar tare da janye jikinsa daga na Dr Jameelu ya tallafe kuncinsa still hawaye na bin fuskarsa kana muryarsa na rawa yace.
“J”.
Cikin sauri ya sake Rungume Dr Jameel Araunane yace.
“Ummi! Ina kike? Yau ina Abbana? Ummi ina kuke ga J ɗina Ummi J ɗina bai rasu ba Ummi gawar wani aka nuna mana akace J ne Ummi J ɗina bai rasu ba Ummi”.

Dr Jameel kuwa cikin sauri da tsoro ya janye jikinsa daga na Moddibo kana ya nuna sa da yatsa muryarsa na rawa yace.
“Bawan Allah ni ban sanka ba nifa ba J ɗinka nan da kake faɗa bane”.
Miƙewa Moddibo yayi ido cikin ido ya kallesa kana yace.
“J nine kake cewa baka sani ba!?,A.J ɗin ka nefa”.
Ya ida maganar kana baki daya ilahirin jikinsa rawa yake yayinda maransa ke cigaba da damƙarsa cikin rauni ya kalli Dr Jameel daya zuba masa ido kana yace.
“A.J ɗinka nefa Amma kake cewa baka sani ba”.
Ajiyar zuciya Dr Jameel ya sauƙe tare da fesar da numfashi cikin gaskiya da gaskiya yace.
“Wallahi ban sanka bani ban taɓa ganin ka ba”.
Cikin tsanananin tashin hankali tsoro da kiɗima Moddibo yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n J kaji tsoron Allah ka daina rantsuwa nine kake cewa baka sani ba J Moddibo kane fa Jameelu Nine zaka ce baka saniba!?”.
Cikin yanayin rashin fahimta Dr Jameel ya Girgiza kansa kana yace.
“Wallahi ban sanka ba ni ban taɓa ganinka ba”.
Araunane Moddibo ya tsira masa idanu kana yace.
“Baka Sanni ba J kace baka taɓa kallona ba?”.
Ya ƙarasa maganar tare dasa hannu ya shafa jikinsa jin babu waya yasa yayi saurin kallon Dr Jameel yace.
“Ina wayata?”.
Araunane ya sake kallon yace.
“J naji baka sanni ba domin Ni Aminine daya cancanci ka wurgar ko? to amma J Ummi fa Ummi ma baka santa ba?”.
Kai Dr Jameel ya girgiza kana yace.
“Wacece Ummi kuma?”.
Zare ido Moddibo yayi Aƙiɗime yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n J Ummi mahaifiyar kace baka sani ba!?”.
Ahankali Dr Jameel ya sunkuyar da kansa ƙasa kana ya ɗago ya kalli Moddibo yace.
“Ni kuma Mahaifiyata?,Gaskiya dai inaga wannan kana da Lalurar ƙwaƙwalwa!”.
Cikin sauri Moddibo ya zauna abakin gadon ya dafe kansa da hannu bibbiyu muryarsa na rawa yace.
“J ni kake cewa ina da matsalar ƙwaƙwalwa yayi kyau J shin wani irin laifi muka yi maka aduniya da muka cancanci irin wannan hukuncin agareka me muka yi maka mai tsanani da zaka hukunta mu ta wannan hanyar”.
Kallonsa kawai Norse din keyi cike da tausayawa.
Cikin rauni ya cigaba da cewa.
“J Ni kake jifa da kalmar cewa ƙwaƙwalwa ta ba ɗaya bane, to koma ƙwaƙwalwa ta takasance tana da matsala J rashinka akusa damu ne da kalmar da aka faɗa mana cewa ka rasune ya jefamu cikin wannan halin”.
Kallon ikon Allah kawai Dr Jameel yake kana yana kallon yanda hawaye ke bin kuncin Moddibo.
Cikin sanyi da rauni Moddibo ya cigaba da cewa.
“J sannan koda na kasance mai taɓin hankali katari da gawarka da akayi da gawarka akace ka rasu shiya jawowa ƙwaƙwalwata matsala!”.

Ahankali Dr Jameel ya matsa kusa dashi Asanyaye yace.
“Bawan Allah ka nutsu ni bansan kaba ban san mekake nufi ba”.
Cikin fushi Moddibo yace.
“J ƙarya kake”.
Miƙewa Dr Jameel yayi tare da ɗage kafaɗa yace.
“Ok toh shikenan”.
Ya ƙarasa maganar tare da ficewa Norses suka mara masa baya.

Cikin sauri Moddibo ya mike ya fita kai tsaye wajen motarsa ya nufa ya ɗauki wayarsa ya dawo reception din ya kunna wayarsa dake ɗauke da hotonsa dana M Jameel ya nuna masa kana yace.
“Yanzu wannan ka mantani ai gaka gani”.
Kallon fuskar wayar Norses ɗin sukayi Wacce Dr Jameel ya Kira da Baby tayi saurin buɗe baki cike da Mamaki ta kalli Dr Jameel kana tace.
“Iyee Dr da gaske fa kaine”.
Harara ya watsa mata kana yace.
“Kuma dai baku da hankali”.
Ahankali Moddibo ya juya da fuskar wayarsa nan yaga takwas tara cikin sauri yace.
“Yah salam banyi maghariba banyi Isha'i ba”.
Sai alokacin Dr Jameel ya tuna da batun sallah kallon Moddibo yayi da duk kiɗima da ruɗu kana da gigita dake jikin mutumin amma ga mamakinsa sai ya juya ya nufi Masallacin dake cikin Hospital Kai tsaye Tap dake wajen Moddibo ya nufa ya ɗaura alwala har zai shiga Masallacin ya tsaya ya juya tare da kallon Dr Jameel da still Idanunsa ke kansa.
Kai ya jinjina muryarsa na rawa yace.
“Yayi kyau J nine kake cewa baka gane ba zan shiga Masallaci in faɗawa Ubangiji duk abinda ke damuna”.
Ya ida maganar tare da shiga Masallaci nunfashi Dr Jameel ya fesar kana shima yayi alwala ya nufi masallaci.

Yana shiga Masallaci yayi maghariba da Isha'i yana idarwa idanunsa suka sauƙa kan Moddibo daya tsira masa ido.
Cikin sanyin murya da rauni Moddibo yace.
“J Nine kake cewa baka gane ba”.
Kai Dr Jameel ya Girgiza cikin gaskiya da gaskiya yace.
“Wallahi bawan Allah Ni bansan kaba ban kuma gane kaba kadena cemin J Ni sunana Jameel”.
Cikin sauri Moddibo ya katsesa kana yace.
“Aina sani dama sunan ka Jameel ne”.
Dr Jameel kuwa jin wayarsa na ringing yasa ya Mike ya fita kai tsaye cikin Hospital ya nufa duba matar daya mata Theater Yana shiga Moddibo yabi bayansa bayan ya gama duba ta yafita ya kalli Moddibo kana yace.
“Yanzu ko inda zanyi aikin ma sai kabini har ciki?”.
Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.
“Eh dole sai na bika J”.
Cikin alamun gajiyawa Dr Jameel yace.
“Toh kabarni mana ina sarara”.
Kai Moddibo ya Girgiza cikin tsaresa da ido yace.
“Ai tsakanina da kai babu sararawa sai lokacin dana danƙa ka ahannun Ummi da Abba”.

Siririn tsaki Dr Jameel yaja kana ya juya yabar wajen kai tsaye Office ɗinsa ya nufa dai-dai lokacin Baby ta shiga.
Tana shiga ta tsaya daga bayansa bayan ya zauna akan kujera cike da salo ta sanya tafin hannunta tashafa sajensa zuwa kan Lips ɗinsa.
Cike da shu'uman ci ya lumshe Idanunsa cikin wata narkakkiyar murya mai tarwatsa lissafin mata yace.
“Ohhhh My Baby don't kill me. Cikon Office muke fa, mu tafi gida Please I need you”.
Shagwaɓe Murya tayi tare dayi masa fari da ido tace.
“But Dr Ina da Nightduty”.
Wani kallo ya bita dashi yana shinshina wuyarta kana yace.
“Toh yanzu yakike so inyi”.
Ido ta kashe masa tare da ɗage gira tace.
“Duk yanda kace haka za ayi?”.
Cike da tsanananin Mamaki Moddibo ke kallonsu Aruɗe yace.
“J wacece wannan kuma kasan abinda kake yi kuwa?”.
Cikin tsawa ya kalli Baby kana yace.
“Ke ki sake shi baki da hankali ne?”.
Juyawa Dr Jameel Yayi tare da kallon Moddibo Up anda down Cike da takaici yace.
“Ya dai bawan Allah Meyesa kake shige min rayuwa da ƙudundunai ne?,Ko kuma dan kaga bansa security sun jefa ka waje bane?Ina ruwanka da ita?”.
Araunane Moddibo ya kallesa kana yace.
“J baka da hankali ne J mekake yi haka? Shin wace rayuwa ka jefa kanka aciki J?”.

*Gembila*

Acan Gembila kuwa adai-dai wannan lokacin Mommy ce zaune abakin gadon Khausar yayinda Khausar da Asma'u ke tsakiyar gadon cikin dariya Mommy ta gyara zaman wayar dake kunnenta kana tace.
“Yau dai Ummi kiyi haƙuri nice na hana Asma'u dawowa kuma Khausar ce ta hana dan Allah kiyi haƙuri ki barta ta kwana, kinsan abokin kuka shi ake faɗawa mutuwa”.
Murmushi Khausar tayi tana kallon Mommy.
Still Mommy na Dariya tace.
“Shiyasa nace bari in kiraki in Faɗa miki kuma ɗazu nayi ta kiran wayarki yana shiga ba'a ɗauka sai yanzun”.
Acan ɓangaren Ummi kuwa murmushi tayi cikin yanayin sakin fuska da jin daɗi tace.
“Laa bakomai ai lokacin da kika kira ina tare da Babansu ne kuma nabar wayar aɗakina muna tatauna batun Khausar ne sai yanzu dana shiga ɗaki naga miss call ɗinki na kira”.
Murmushi Mommy tayi cikin jin daɗi tace.
“Toh Nagode Insha Allah zamu kwana gobe zata dawo”.
Khausar dake gefe tayi ƙasa da murya kana tace.
“Mommy kice mata dan Allah goben ma sai da daddare zata dawo zamu sake yini”.
Dariya Ummi dake jiyo sautin muryar Khausar tayi kana tace.
“Ai kwana ya isa basai anyini ba”.
Karɓan wayar Khausar tayi tare da langwaɓar da kai tace.
“Dan Allah Ummi idan mun kwana mu yini”.
Murmushi Ummi tayi tare da gyara rikon wayar tace.
“Ku kwana dai sannan kuzo da wuri Ina son tattaunawa dake”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana tace.
“Toh Ummi”.
Sannan ta katse wayar.
Miƙewa Mommy tayi kasancewar girkinta bisa duk kan Alamu cikin shirin tafiya side ɗin Lamiɗo take kallon Khausar tayi kana tace.
“Toh kizo ki rufe muku ƙofa”.
Kai suka gyaɗa atare suka miƙe da Asma'u suka bi bayanta kana suka rufe kofar.

Zama Asma'u tayi akan 2sitter kallonta Khausar tayi ta shafa cikinta kana tace.
“Asma'u mai za muci ne?”.
Kai Asma'u ta girgiza kana tace.
“Wani abinci zanci Khausar bayan kinsan Maganar daya kawoni nake so muyi amma tun yamma kin ƙi ki zauna muyi”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi cikin sanyin murya tace.
“Shiyasa nake so mukwana kinga yanzu ma Mommy Bata nan zamu sake muyi maganar mu”.
Jinjina kai Asma'u tayi tare da cewa.
“Toh shikenan”.
Ahankali Khausar ta shafa cikin tace.
“Gaskiya yunwa nake ji kema kuma naga ɗazu bakici abincin sosai ba”.
Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe kana tace.
“Toh shikenan muje kichen ɗin muga mai zamuyi”.
Suna shiga kichen Asma'u ta buɗe freezer Khausar kuwa na tsaye gefenta ganin ɗanyen kifi yasa Asma'u juyawa ta kalli Khausar kana tace.
“Toh muyi Marghi special mana”.
Kai Khausar ta gyaɗa cike da gamsuwa tace.
“Toh shikenan muyi”.
Suna aikin suna taɓa hira cikin awa ɗaya suka gama kana suka soya chips aplate Asma'u ta zuba musu sannan Khausar ta zuba musu Tea cup biyu afalo suka zauna suna ci suna kurɓan tea suna cikin ci suka ji Knowking ahankali Khausar ta kalli ƙofar tace.
“Waye”.
Haiydar dake tsaye yace.
“Nine”.
Kurɓan tea Khausar tayi tace.
“Toh lafiya har mun rufe kofa zaka zo kana mana Knowking?”.
Murmushi yayi kana yace.
“Naji ƙamshi yana ta buɗewa ne ta ko ina shiyasa nasan wani abu kuka girka Ni dai Ku sammin kawai yunwa nake ji dan nayi dogon hira”.
Hararan ƙofar Khausar tayi tare da cewa.
“Shegen kwaɗayi mutum yana nan da hanci kamar Mage duk abinda akayi baka ciki ma sai an baka”.
Dariya Asma'u tayi tare da miƙewa tashiga kichen ta ɗauki Plate ta zuba masa sauran kana ta buɗe ƙofar ta miƙa masa har ta juya yayi saurin cewa.
“Toh ni baza abani shayin bane”.
Harara Khausar ta watsa masa kana tace.
“Ohh Haiydar kinga Ni Ko Asma'u da ba kin fara bashiba”.
Murmushi Asma'u tayi tare da juyawa ta koma kichen Haiydar kuwa gwalo yayiwa Khausar kana yace.
“Oho dai abani”.
Miƙa masa Asma'u tayi bayan ta zuba.

Bayan sun kammala Asma'u tace.
“Khausar mu dan watsa ruwa mana”.

“Eh to ki fara shiga".
Cewar Khausar dake gyara zamanta.

Miƙewa Asma'u tayi tare da tattare Plate ɗin ta kai kichen kana ta dawo ta watsa ruwa bayan ta fito Khausar ma tashiga ta watsa tana fitowa ta bude Siff ta ɗauka musu sleeping dress riga da wando masu duhu ta miƙawa Asma'u ja sannan ita ta sanya fari.
Kai tsaye falon suka fito Khausar ta kunna Tv ta rage Volume Anutse Asma'u ta juya ta kalli Khausar kana cikin sanyin Murya tace.
“Khausar”.
Ahankali Khausar ta

85 / 140

Chapters