Author : Aisha Aliyu Garkuwa Category : Free Novels Online (Read & Download)
mata biyu duk sun girma Hakeem ɗan Lalla Hafsat ya Auri Fatma ƴar Dija Haiydar kuma ya Auri Ruƙayya yarinyar Rahama.
Alhamdulillah rayuwa ta cigaba da tafiya tamkar yanda ake buƙata.
Bayan anyi biki an watse.
Ahankali Khausar ta shirya cikin shiga ta alfarma sai baza ƙamshi take sanye take cikin wasu tausasan rigar bacci masu masifar kyau da santsi idan ka ganta zaka yi zaton yau akayi Aurenta duk da cewa sun Aurar da ƴaƴan su amma tana da kyakkyawan jiki wanda Babu wanda zai ce ita ta haifi wannan yaran ga autarma Eeman an zama manyan ƴan mata wacce ba abinda ya bari na mahaifiyarta har rawan kan.
Anutse ta tura ƙofan bedroom ɗin ta ta shiga idanunta suka sauƙa akan Moddibo daya sake zama magidanci baza kayi zaton ya wuce 45years ba saboda kyawun jikinsa nutsuwa, jin daɗi kwanciyar hankali sun sake wanzuwa acikin rayuwarsu yana ganinta ya buɗe mata hannunsa anutse ta ƙara sa tsakiyan tare da faɗawa jikinsa ya mata wani Amintaccen runguma ahankali yake cusa yatsun ƙafansa aƙasan nata ganin haka yasa ta ɗaura ƙafafunta asaman rumfar ƙafansa anutse ya riƙa tafiya da ita har yaje bakin kofa yana isa ya rufe ƙofar saurin kallonsa tayi tare da cewa.
“Yah Mu'allim ya zaka rufe ƙofa”.
Goshinsu ya haɗe waje ɗaya still ƙafafunta na kan nasa yace.
“Um Minha Vidaa (My life) rufe wa zamuyi saboda kada _Aysha Aliyu Garkuwa_ ta shigo ta samu abin rubutawa Fan's ɗinta”...
Acan gidan Dr Jameel kuwa Asma'u ce zaune tare da ƴaƴanta wa'anda ta haifa bayan ta haifi Ishmah ƴaƴa maza guda biyu wanda ɗaya an yiwa Moddibo ta kwara suna kiransa da Moddibo sai takwaran Abban Jameel suna kiransa da Abba ahankali tace.
“Yah Moddibo”.
Anutse ya kalleta cike da girmamawa yace.
“Na'am Ummina”.
Tana gyara zamanta tace.
“Yaushe zakaje Nigeria ne?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ummi kwanan nan dai nake son zuwa amma nafi son mu tafi da Abba idan ya gama exams ɗinsa”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh ba matsala nima dama nayi kewar Ummina idan yaso zamu tafi tare”.
Dr Jameel dake gefe yai mata wani kallo mai cike da so kauna yace.
“Nima ɗin dani za'a je saboda nayi kewar Abbana da Ummina”.
Hira suka cigaba dayi mai cike da farin ciki da ƙaunar junansu...
Acan bangaren Ibraahim rayuwa tayi musu daɗi da matarsa.
Haka bangaren Asiya ma Alhamdulillah rayuwa na tafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali ɗan ta ya Auri ƴar Amina da suka haifa da tsohonta...
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya hankali ya kwanta ya kowanne ɓangaren...
_TAMAT BIHAMDULILLAHI..._ Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Na godewa Allah daya bamu aron rai da lfy da lokaci da dama ya nuna mana forkon littafin nan lfy tare da aramana daman ganin ƙarshensa lfy dani daku masu karatu. Toh Alhamdulillah. Yah Allah mun gode maka, muna kuma neman yafiyarka da gafararka da rahamar ka, Yah Allah ka yafe min kurakuran dake cikin wannan littafin ka shafe zunubaina kayi min gafara da rahama da jinƙai dani da masu karatu. Abinda mai dai-dai Ya Allah ka haɗamu a kan ladan, ya Allah ka nuna mana forkon wanda zan fara lfy da ƙarshensa duk lfy, ya hayyu ya ƙayyum kasa al'ummar Annabi su amfana da alkhairan dake cikin littatafai na ka tsaresu da sharrin dake ciki.
*Yafiya! Yafiya!! Yafiya!!!*
*Ina mai neman yafiyarku makarantan littatafai na, mace ko namiji babba ko yaro wacce muka taɓa mgn da ita da wacce bamu taɓa mgn da ita, na kusa dani dana nesa. Wala Allah akwai abinda nai Miki ko nai maka ko cikin rashin sani ko ajizanci ko kuma yanayin gajiyawa da raunin ɗan adam ki kuma yanayin ɗan fusatan lissafi ko gaza danne fushi, Ka! Ku! Ki! Haƙuri ku yafe min, kuyi min azurun na fama da yawan jama'a, ni na yafewa duk wacce taimin abu cikin rashin sani, Amman wlh ban yafewa masu fitarmin littafina su tura a wasu groups ɗin ba domin misali ka bawa ɗan uwanka mutum ɗaya biyu wannan da banner da turawa a groups mutum dari ko sari biyu ko uku ku dari hudu ai wannan kai kankama kasan me sunanka madadin samun wani suyi Murmushin group a kuma kwashi zunubi*
*Littafin Sakayya dai kowa ya sani na kuɗine, in ma kin ganshi a wani wurin to na satane kika karanta 1k ne kacal, 0661110170 GTBANK Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki ta Whatsapp number na 09097853276. In tura Miki littafin complete Kisha karatun ki ba haƙin kowa a kanku*
*Gareku masu son kayan mata ko turarukan wuta da kulacca da su Humra a wannan no ɗin ne zakuyi min mgn 08069423567 in kuma kuɗi zaki tura to ta account in na na Jaiz bank zaki tura. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta Whatsapp number na na 08069423567, in haɗa Miki kayanki in tura Miki shi duk state da kike nama lfy fata lfy*