Author : Aisha Aliyu Garkuwa Category : Free Novels Online (Read & Download)
akai yaita zunɗuma ihu koda zaiji sanyin Aransa baki ɗaya lips ɗin sa rawa suke idanunsa sun sauya launi zuwa ja jijiyoyin goshinsa sun tashi yayin da goshinsa ke tsata-tsafo da zufa.
M Jameel kuwa lura da yanayin da yake ciki da yayi yasa ya miƙe tare da nufar kichen kamar ko yaushe ruwan Tea da lemun tsami da kuma zuma ya haɗa masa kana ya fito ya miƙa masa tare da cewa.
“Gashi kasha”.
Ba musu Moddibo ya sanya hannu ya karɓa domin baya cikin yanayin da zai iya musa masa ahankali yakai kofin bakinsa tare da kafa kai ya shanye saboda yanda yake ji ajikinsa.
Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe kana cikin sanyin murya yace.
“Tun da kasha ka kwanta Insha Allah zaka ji sauƙi bari zanje gidan Ummi anjima zan dawo bazan daɗe ba”.
Kai Moddibo ya gyaɗa masa still Idanunsa alumshe M Jameel kuwa key mota ya ɗauka tare da ficewa kai tsaye gidan Ummi ya nufa.
Yana isa yayi Parking Cike da nutsuwa ya buɗe Murfin motar ya fita tare da duba agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa dake nuni da ƙarfe 5:15 lumshe idanunsa yayi kana ya buɗe tare da nufar cikin Falon bakinsa ɗauke da Sallama shiru falon ba kowa sai dai komai akimtse kana ga ƙamshin tularen wuta dana Room freshner dake tashi, Murmushi yayi Aransa yace.
“Allah sarki Ummina ba dai tsafta ba”.
Numfashi ya fesar tare da nufar kichen inda yake jiyo motsinta.
Tsaye yasame ta a kichen ta tuƙa tuwo tana kwashewa aleda cike da so da ƙauna yace.
“Ummina”.
Juyawa Ummi tayi fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi ta kallesa kana tace.
“A'a yaushe kashigo?”.
Yana ƙara sa shiga kichen ɗin yace.
“Yanzu Ummina”.
Juyawa Ummi tayi tare da leƙa bayansa”.
Dariya yayi kana yace.
“Nasan wa kike nema ai”.
Murmushi tayi kana tace.
“Eh to ai ban gan shi bane naga Hussain banga Hassan ba”.
Cikin sanyin murya yace.
“Yana gida Ummi yau yana ɗan jin zazzaɓi ne shiyasa bamu zo tare ba”.
Girgiza kai Ummi tayi cike da tausayawa tace.
“Subhanallah Ubangiji ya bashi lafiya Allah ya sawwaƙa mishi”.
Ahankali M Jameel yace.
“Ameen”.
Kana ya matsa jikin kular yana ƙoƙarin budewa yace.
“Ummina yau me kika girka mana ne?”.
Murmushi tayi kana tace.
“Tuwo ne”.
Wara ido yayi tare da cewa.
“Miyar me za kiyi mana Ummi?”.
Tana ƙoƙarin wanke nama ta kallesa kana tace.
“Miyar taushe zanyi”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“A to asamana nama da yawa”.
“Toh Babana za'a saka”.
Ta ida maganar tare da ɗaura naman akan gas kana ta yanka albasa tare da sanya Maggi, citta kamafari ta rufe.
M Jameel kuwa Attaruhu, Albasa,Tattasai ya haɗa ya wanke tare da gyarawa kana ya ɗauko blander ya zuba.
Kallonsa Ummi tayi kana tace.
“Ka bari fa da yaji kada yashiga Idon ka”.
Kai ya girgiza tare da cewa.
“A'a Ummi kibari in tayaki nima yau na samu ladan da Asma'u ke samu dana iyama ni zan miki girkin nan”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ai dai kam hakan ma Nagode yayi Allah yayi albarka Ubangiji ya tsareka daga sharrin duk kan abinƙi kuma ai kafin Asma'u samun lada in sha Allah”.
Kallonta yayi kana yace.
“Ameen Ummina”.
Ummi kuwa buɗe tukunyar tayi tare da zuba mai kana ta zuba jejjegen da M Jameel Yayi a blander.
M Jameel dake gyara kifi banda ya juya ya kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi ya yau naji gidan Shiru ina Asma'u da Bashir”.
Tana ɓare Maggi tace.
“Sunje gidan Goggon su takwarar Asma'u”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Ayyah shiyasa yau naji gidan shiru sun barki ke kaɗai to Malam fa?”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Ai dai kam Malam kuma yaje wata rugar Fulani nan kusa amma sai gobe zai dawo acan zai kwana”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Ashe dai yauma kam zan ta yaki ɗebe kewa gidan nan”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ai dai kam ko zamu kwana ne?”.
Ahankali ya juya ya kalleta tare da cewa.
“Da nafi kowa farin ciki Ummina ace zan kwana gida ɗaya dake”.
Murmushi Ummi tayi batare da tace komai ba.
Ana kiran sallar maghariba suka gama dai-dai lokacin kuma Asma'u da Bashir suka dawo atare, alwala M Jameel Yayi kana Bashir ma yayi hannun Bashir ya riƙe suka tafi masallaci su kuma sukayi alwala tare da gabatar da Sallah.
M Jameel kuwa koda suka idar da Sallah basu dawo ba saida sukayi Isha'i sannan suka fito.
Asma'u kuwa Anutse ta fito daga Bedroom bayan ta idar da sallah kusa da Ummi ta zauna kana tace.
“Ummina Ayyah yau aiki ke kaɗai”.
Kallonta Ummi tayi kana tayi murmushi tare da cewa.
“Ina kuwa nayi aiki Ni kaɗai Yayanku yazo ya tayani yau shiya mana miya ma”.
Wara ido Asma'u tayi tare da sakin murmushi kana tace.
“A lallai kai ashe yau zamu sha miyar Yaya kenan”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da faɗin.
“A sosai kam zaku sha miyar Yaya Jameel”.
Atare M Jameel da Bashir suka shigo tare da zama.
Gnin shigowarsu yasa ta miƙe tashiga kichen kular tuwon ta ɗauko kana ta koma ta ɗauko Plate-plate ta dawo Ummi ce ta karba ta sakawa M Jameel kana ta zuba masa miya agefe sannan ta zubawa Asma'u da Bashir.
Ahankali M Jameel ya kalli Ummi kana ya kalli Asma'u da Bashir sai kuma ya kalli tuwon Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Toh Ummi muci tare mana musamu ladan cin abinci tare”.
Ɗagowa Ummi tare da kallon sa kana tace.
“Kuma dai”.
Cikin wani irin yanayi ya gyaɗa mata kai kana yace.
“Allah kuwa Ummi”.
Kallonsa ya mayar kan Asma'u tare da cewa.
“Asmeey jeki ɗauko Tray babba ki kawo mana”.
Kai Asma'u ta gyaɗa kana tace.
“Toh Yaya Jameel”,.
Sannan ta miƙe ta shiga kichen ɗin ta ɗauko Babban faranti ta fito dashi tana ƙoƙarin juyewa yace.
“Kawo in zuba mana”.
Murmushi Asma'u tayi tare da faɗin.
“Yah Jameel da kan ka kabari zan zuba mana”,
Girgiza kai yayi kana yace.
“A'a Asma'u kawo in zuba mana bana so ki wahalar da kanki”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Laaa Yah Jameel ka jika Allah zanyi mana”.
Lumshe Idanunsa yayi tare da saurin dafe ƙirjinsa kana ya buɗe Idanunsa tare da Kallonsu ɗaya bayan ɗaya tare da cewa.
“No Asmeey ki bari in zuba mana kaɗai”.
Saurin Kallonsa tayi tare da miƙa masa Plate ɗin.
Murmushi yayi tare ɗaukar Plate ɗin tuwon ya zuba musu akan babban farantin kana ya ɗauka ya ajiye musu Atsakiyar su tare da kallon Bashir yace.
“Ɗauko Mana drinks”.
Kai Bashir ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh”,Kana ya miƙe ya ɗauki Plate ya ɗebo drinks da swan water ya ajiye musu.
Ya zauna sai ya zamana M Jameel da Ummi na facing juna Asma'u da Bashir ma na facing juna sai ya zama sunyi Cycle plate din na tsakiyar su.
Ummi kuwa shiru tayi tare da zubawa M Jameel Ido Batare da tace komai ba kana tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa azuciyarta wanda takasa sanin na menene hakanan ta tsinci kanta da Kallonsa acikin kwanakin nan.
Ahankali M Jameel ya janyo kular miyar tare da ƙara musu namar da bandan kifi kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Hayya kuci yau zakuci miyar da baku taɓa ciba irinta ba dan ni nayita ko Ummi?”.
Ya faɗa tare da ɗago kai sai yaga baki ɗaya Idanun Ummi na kansa faɗaɗa Murmushin fuskarsa yayi tare da cewa.
“Kai Ummina ya dai?,Ai gaskiya na faɗa”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“A gaskiya ka faɗa kam”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Toh Ummi kici mana”.
Dariya Ummi tayi tare da girgiza kai kana tace.
“A'a kai da kayi dai ka fara ci muga result ɗin da fuskarka zai bayar kafin mufara ci”.
Wara ido yayi tare da kallon Asma'u da Bashir da suma Kallonsa suke,
“Toh ɗan Auta fara ɗana mana muji”.
Kai Bashir ya gyaɗa kana ya gutsiri loma ɗaya yakai bakin sa lumshe ido yayi tare da haɗa yatsunsa hannu biyu alamar jinjina kana yace.
“Kai amma miyar tayi daɗi gaskiya Yah Jameel na baka Award”.
Murmushi Ummi tayi tare da kallon M Jameel da Yayi wani irin kyau na ban mamaki tamkar wanda aka sanya shi a inji aka sake ƙenƙesashi ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Uyummm toni nayi bashi ba”.
Dariya M Jameel Yayi wanda ya bayyanar da Fararen haƙoransa kana yace.
“Toh na yarda Ummi mu duka biyu mukayi”.
Murmushi Asma'u tayi tare da kallon M Jameel kana tace.
“Aikuwa Yaya Kayi ƙoƙari sosai amma muci kada yayi sanyi”.
Kai suka gyaɗa atare kana lokaci ɗaya suka sanya hannunsu akan tuwon tare da kai tuwon bakinsu lokaci ɗaya suka kalli juna tare da sakin murmushi.
M Jameel kuwa murmushi ya saki tare da lumshe Idanunsa kana yace.
“Ina ma ace zamu kasance ahaka ko yaushe mu riƙa zama tare nuna cin abinci atare da nafi kowa farin ciki”.
Asma'u da takai nama bakinta ta kallesa kana tace.
“Yah Jameel zamu kasance atare mana Insha Allah”.
Kai ya Girgiza tare da cewa.
“Dole wataran fa zan barku sai dai ku zauna ku uku kuci abinci ba tare dani ba”.
Cikin sauri suka kallesa Bashir yace.
“A'a Yaya Jameel mai yasa zakace haka insha Allah zamu kasance atare”.
Ummi kuwa Kallonsa kawai take.
Murmushi M Jameel Yayi tare da kurɓan drinks kana yace.
”Dole wataran zan barku zanyi tafiya gari mai nisa wanda zan kasance Ni kaɗai acan batare da kuba nasan zanyi kewar ku kamar yanda zakuyi nawa tunda Abba ya dage dole zan koma Marrocco”.
Kai suka gyaɗa tare da sauƙe ajiyar zuciya kana suka ci gaba da cin abinci batare da wanin su ya sake magana ba sai dai lokaci zuwa lokaci yakan kallesu tare da sakin murmushi.
Wayar M Jameel ne ya karaɗe wajen da ruri ahankali ya ɗauka tare da sakin murmushi kana yayi Picking tare da Sallama.
Daga ɗaya ɓangaren kuwa cikin sanyin murya Moddibo yace.
“J ina ka tsaya na jika shiru ko abinci banci ba, sannan kasan bani da lafiya ko dai har yanzu kana gidan Ummi ne?”.
Murmushi M Jameel Yayi tare da gyara zaman wayar akunnensa kana yace.
“Ayyah sannu A.J Please kaci abinci sannan ka sake shan maganin dana haɗa maka Insha Allah ina hanya”.
Lumshe idanu Moddibo yayi tare da sakin ajiyar zuciya kana.
“Toh shikenan sai kazo kace ina Gaishe da Ummina”.
Murmushi M Jameel Yayi tare da kallon Ummi dake sauraron duk abinda suke faɗa kana yace.
“Zata ji”,daga haka ya katse kiran.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Ohh ina ga dai wannan ko kunyi Aure gida ɗaya zaku zauna bakwa iya minti talatin batare da kunga juna ba ko kuma kunji muryan juna”.
Murmushi M Jameel Yayi kana yace.
“Ai dai kam dole watarana arabu”.
Jinjina kai Ummi tayi,tana murmushi kana suka cigaba da cin abincin.
Bayan sun cinye tuwon farantin M Jameel ya Kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi aƙara mana yau ina jin daɗin abinci ina so inci³ incika cikina dan ban sani ba sai kuma yaushe zan sake ci”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“A'a to ai ko yaushe ma kakeso ai zaka zo kaci”.
Lumshe Idanunsa yayi tare da buɗe su akan Ummi kana yace.
“Toh Ummi kwanan nan zamu fara batun aikin nan kinga in dan na tafi Marocco ai bazan dinga samun ciba”.
Kai ta jinjina tare da faɗin.
“Ai in dai nan da ne ba nisa bane dashi idan ya kama sai inmaka miya da komai duk zan aika maka dasu idan yaso saika na sawa a fridge”.
Murmushi Yayi tare da cewa.
“Hmmyyym Ummina Allah ya ƙara miki nisan kwana mai amfani Allah ya barmu tare”.
Jingjna kai tayi tare da faɗin.
“Ameen Babana Allah ya ƙara maka nisan kwana inga har jikokin ka”.
Murmushi yayi tare da kallonta kana yace.
“Hmmm Ummina kenan.
Kin ko san in sha Allah ƴata ta farko sunanki zan samata,
Na kuwa tabbatar zata ga soyayya ko ƙuda bazan bari ya taɓa ta ba”.
Kallonsa Ummi tayi tare da cewa.
“Jamiluuu na”.
taja sunan tana murmushi haka nan take jin daɗin kiran sunan sa.
Bayan sun kammala cin abincin Asma'u ta miƙe tare da tattare Plate ta Kai kichen M Jameel kuwa da kansa ya mike ya ɗauki kular abincin ya kai kichen Ummi kuwa Kallonsa ta riƙa yi cike da so.
Bayan ya ajiye ya fito, woje ya nufa yana cewa
“Bari in ɗauko abu a mota".
Toh Ummi tace kana ta meda hankali kan tv.
Jim kaɗan da fitar da ya shigo riƙe da kwalayen waya masu kyau.
Ƙirar Samson, kana ya dawo ya zauna gefen Ummi Asma'u da Bashir suka zauna daga gefensa gyaran murya yayi tare da fuskantar Asma'u kana yace.
“Ga woyoyinku nan Asma'u yau dai na cika alƙawarin ko”.
Cikin tsananin jin dadi Bashir ya ruggumshi, yayinda Asma'u kuwa Ummu ta ruggume.
Cikin son juna suka rinƙayi mishi godiya tare da fatan al'khairi.
Murmushin jin dadi yayi tare da shafa kan Bashir kana yace.
“Asma'u yanzu ke wani irin makaranta kike so?”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Yah Jameel duk makarantar da ka zaɓa min ina sonta ina farin ciki da ita”.
Jinjina kai yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.
“Zan kuwa zaɓa miki wanda ya dace dake Insha Allah naga keda ƙawarki kusan ra'ayin ku ɗaya ko yaushe amman wannan karon an samu akasi ita Jenouelist take fata naga ke kuma likitanci kike son karanta”.
Kallon Bashir yayi tare da cewa.
“Kai kuma wani irin Makaranta kake so?”.
Murmushi Bashir yayi kana yace.
“Duk wanda ka zaɓa min Yaya”.
Lumshe idanu M Jameel Yayi tare da cewa.
“Insha Allah kuwa zan zaɓa maka ina ganin Law zaka karanta zaifi dacewa da kai”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana ya tsira musu ido tare da cewa.
“Asma'u”.
Kanta ta ɗago tare da cewa.
“Na'am Yaya”.
Anutse ya kalleta cikin yanayin nutsuwarsa da alamun rashin wasa yace.
“Kinga ke ƴa macece ita rayuwar duniyar nan duk i da ƴa mace ta tsinci kanta ta tsare mutuncinta da darajar ta shine abu mafi daraja ki kiyaye tarbiyyar da muka sha wahalar baki nida Ummi kada ki kunya tamu kada kisa ta baƙin ciki”.
A hankali ya sauƙe numfashi tare da gyara zamansa kana yace.
“Saboda ke ƴa macece ke mukafi taraddadi akan ki kinga yanzu ga Bashir amma bana ta raddadi akansa kamar ke mace”.
Asma'u kuwa ƙasa ta sakeyi da kanta batare da tace komai ba sai wasa da yatsun hannunta da take yi.
lumshe idanunsa yayi kana yace.
“Burina da fatana inga mun kasance gida ɗaya muhalli ɗaya wallahi akanki da Bashir da kuma Ummin mu yasa nake so inyi Aure inga muna tare”.
Sai kuma ya kalli Bashir da shima yayi ƙasa da kansa kana yace.
“Ina so inga lokacin tafiyarku makarantar kana inga lokacin dawowan ku a idona sannan insan kalar mutanen da kuke mu'amala dasu".
Sai kuma ya juyo ya kalli Asma'u cikin yaƙini yace.
“Na yarda da ƙawancen ku da Khausar saboda tana da tarbiyya duk da kuwa tana da rawan kai”.
Numfasa yayi tare da kallon ta kana cikin raunin murya yace.
“Asma'u ki kula da rayuwarki sannan kisan irin mutanen da zaki dinga alaƙa dasu idan kuma har Aure kike so Asma'u ki faɗa min idan yaso idan kikayi aure sai ki cigaba da karatun ki agidan mijinki kada ki ɓoye min ki faɗa min komai ki ɗaukeni tamkar ƴar Uwarki mace”.
Cike da kunya Asma'u tayi ƙasa da kanta tare da girgiza kanta kana tace.
“A'a Yah Jameel nikam karatu zanyi”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Kin tabbatar ba Aure kike so ba sannan babu wanda kike so?”.
Cike da kunya ta girgiza masa kai tare da faɗin.
“Yaya Jameel Ni kuma wazan so kuma babu wanda ke zuwa gurina”.
Dariya M Jameel Yayi tare da kallonta kana yace.
“Mun shiga uku Ummi kadde ƙanwar tawa baƙin jini take dashi?”.
Murmushi Ummi dake aikin Kallonsu tayi tare da faɗin.
“Ba wani baƙin jini kawai dai dake tana kiyaye kanta ne babu wanda ke kawo mata wargi”.
Jinjina kai yayi tare da dai-dai-ta nutsuwarsa kana yace.
“Toh shikenan Asma'u tun da dai kin bani tabbacin karatu kike so daga nan harki kai digir-gire ki gama har ki taka duk kan matakin da kike so nayi al'ƙawarin zan taimaka miki da duk kan ƙarfina da kuɗina muddin ina numfashi zan tsaya miki”.
Kallon Bashir yayi tare da cewa.
“Sannan kai kuma Bashir zaka karanci fannin Law tunda kana da ilimin addini ina da yaƙinin zaka tsaya akan gaskiya duk runtsi duk wuya kada Kabi bayan ƙarya ka kasance mai al'ƙawarin da rikon amana aduk inda ka tsinci kan ka”.
Jinjina kai Bashir yayi kana yace.
“Yah Jameel Insha Allah Nayi alƙawari zan kasance ayanda kake fata”.
Hira suka cigaba dayi sosai irin wanda suka ɗauki tsawon lokaci basuyi irin saba wanda har dare yaraba basu lura ba.
Ahankali Ummi dake murmushi ta daga kanta Idanunta suka sauka akan agogon dake manne abango wanda ke nuni da ƙarfe sha biyu da minti goma,Cikin sauri ta kalli M Jameel tare da cewa.
“Jamilu”.
Anutse ya ɗago ya kalleta tare da cewa.
“Na'am Ummina”.
Ta sauƙe ajiyar zuciya tare da Kallonsa kana ta sake kallon agogon zuciyarta na bugawa tayi saurin dafe ƙirjinta kana tace.
“Ka kalli time fa”.
Cikin sauri M Jameel ya juya Kalli agogo tare da kallon Ummi kana...!
Cikin sakin fuska yace.
“Ummi yau anan zan kwana”.
Cike da mamaki Ummi ta juya ta kallesa, domin tunda Allah yasa tayi aure agidan mahaifin Asma'u bai taɓa kwana ba, sai dai yakan zo aduk sanda yaga dama, a hankali ta sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Anan zaka kwana?”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Eh zan kwana Ummina”.
Kallon Ummi Bashir yayi cike da farin ciki ya langwaɓar da kai kana yace.
“Ayyah Ummi ki barshi kinga yanzu ma dare yayi ki gani fa sha biyu hadda kwata dare fa ya riga da yayi nisa”.
Cikin sanyin murya me ɗauke da farin ciki Asma'u tace.
“Gaskiya dai kam mu kwana kawai Yah Jameel, yau nayi matuƙar farin ciki zamu kwana agida ɗaya Allah ya nuna mana ranan Aurenka mu kasance atare na har abadan”.
Murmushi M Jameel yayi tare da shafa sajensa kana ya tsira musu ido tare da lumshe idanunsa, a hankali ya sauƙe ajiyar zuciya kana yace.
“Asmeey zamu kasance atare in sha Allah zanyi Aure kana zaku kasance gida me kyau da na al'farma da kwanciyar hankali, ni kaina bansan kamannin gidan ba amma na sani gida ne mai masifar kyau da ɗaukar hankali zan riska in sha Allah”,
Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da lumshe idanunsa kana yaci gaba da cewa.
“Wanda kowa ke burin samu, in Sha Allah zan sameshi, domin inaji ajikina na kusa isa wannan gidan kafin ku iso zan kasance cikin farin ciki amma idan ina tare daku zanfi farin ciki na zai fi nin kuwa”.
Cikin yanayin sanyin jiki ya tsira musu ido su duka ukun.
Ummi kuwa idanu ta zuba masa ko ƙyaftawa ba tayi wani irin yanayi takeji azuciyarta, wanda takasa tantance na menene.
Asma'u kuwa murmushi tayi tare da Kallonsa kana tace.
“Yaya Jameel Allah ya baka mace ta gari wacce zata kula da Ummin mu tamkar yanda kake kulawa da ita sannan ta ƙaunace mu tamkar yanda kake ƙaunar mu”.
Murmushi yayi kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.
“Insha