Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sakayya Complete Hausa Novel by Aisha Aliyu Garkuwa

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   74 / 140

219K to 222K   out of 417.8K words

ya fara zazzaga mata abin dake zuba kamar an buɗe Famfo rufe bakinta tayi abin na bin gefen bakinta yana zuba bata sha ganin haka yasa boka Kar'uzu toshe hancinta bakinta ya fara ɗurawa.
Atake ta fara haɗiye wa got-got-got yakai kimanin minti ashirin yana matsa mata saida yaga cikinta ya ciko tukunna ya barta Atake tayi wani irin gyatsa.

Acan Falon Hajiya Lami kuwa tsaye take Atsakiyar falon cikin sanyi ta kalli Agogon dake manne Atsakiyar falon dake nuni da ƙarfe 8:00am baki ɗaya ta fara shiga damuwa gashi ta daina jiyo koda sautin Kukanta ne da sauri tabi shawarar zuciyarta tare da fita ta nufi BQ tana isa ta tura ƙofar falon shiru ba kowa sai Farantin abinci dake kan Centre table kai tsaye Bedroom din ta nufa kana ta tura ƙofar ɗakin ta shiga Idanunta suka sauƙa akan Boka Kar'uzu dake zaune akan gado tsirara hannunsa riƙe da jagularsa d yana kaɗawa har lokacin bawai ya gaji da ita bane kawai dai ya haƙura ne.
Cikin sauri ta maida Idanunta kan Samira dake kwance tsirara tana maida numfashi da gudu ta nufi kanta cikin tsanananin tashin hankali tace.
“Samira!, Samira!!, Samira!!!.
Wayyo nashiga uku! Boka Kar'uzu kaddai ta mutu!?”.
Cikin ɗaga sautin murya yace.
“Ba abinda ya sameta kada ki taɓa ta³ yanzu nan zan haɗa mata magani maza kawo min ruwan zafi”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh”, Kana ta fice da gudu tana isa kichen ɗinta ta ɗauko Flaks din ruwa zafi kana ta dawo tare da miƙa masa still suna yanda ta barsu Buɗe Flaks din Yayi tare da tsiyayan ruwan amurfin Flaks din.
Hannunsa ya ɗaga sama Atake wani ƙullin magani ya faɗo kan hannunsa budewa yayi tare da juyewa acikin ruwan zafin Flaks din.
Zare ido Hajiya Lami tayi cike da mamaki ganin yanda ruwan ke ta farfasa ahannunsa.
Miƙewa yayi tare da isa kan Samira ya ɓude ƙafafunta.
Cikin sauri Hajiya Lami ta kalli fuskar Samira da hawayen azaba ke zuba kana ta kalli gabanta daya canza siffa ya wani irin kumbura.
Boka Kar'uzu kuwa ruwan maganin ya dinga ɗiba yana shafa mata a wurin raunin sannu Ahankali Samira ta fara sauƙe Ajiyar zuciya tana jan numfashi kamar ƙiftawa da Bismillah ta Mike ta zauna tare da kallon Hajiya Lami.

Cike da tausayawa Hajiya Lami tace.
“Sannu Samira”.
Numfashi Samira ta fesar kana tace.
“Yawwa”.
Kallon Samira Yayi tare da ƙurawa gabanta Ido kana ya lashe wangamemen laɓɓansa yace.
“Ina yake miki ciwo!?”.
Girgiza kai tayi tare da faɗin.
“Babu”.
Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauke tare da cewa.
“Bari in kawo muku abinci kuje kuyi wanka tukunna”.
Boka Kar'uzu kuwa Girgiza mata dugujejen kansa yayi kana yace.
“A'a ba yanzu za tayi wanka ba sai anjima inaso wannan abin ya bubbushe ajikinta domin shine mahaɗin aikin dan yadda yake ƙyalli a jikinta haka Modibbo zai rinƙa ganin ƙyallinta kuma dole shi da kanshi zai nemota”.
Cikin sanyin Murya Hajiya Lami tace.
“Toh yanzu sai yaushe Samira bakya jin yunwa ne?”.
Girgiza Kai Samira tayi kana tace.
“Mommy bana jin yunwa”.
Wata mahaukaciyar dariya ya fashe dashi wanda yasa Hajiya Lami da Samira saurin Kallonsa cikin wata murya yace.
“Kinsan abinda na bata tasha kuwa?.
Na bata abinda babu namijin da ya isa bata tasha na bata abinda babu ita babu yunwa har na tsawon sati in dai zan cigaba da bata wannan ba dai taci abinci dan yunwa ba saidai ta buƙaci abinci dan kuzari”.
Kai Hajiya Lami ta gyaɗa still Idanunta na Kan Samira.

Cikin tsawa yace.
“Ki fita ki bamu waje zamu ɗaura daga inda muka tsaya”.
Ya faɗa tare da kamo hannun Samira.
(Wa'iyazu Billah lalacacciyar uwa mai lalatacciyar tarbiya da ƙeƙyasashiyar zuciya).
Daga wannan rana haka Boka Kar'uzu ya cigaba da lalata rayuwar Samira Amma dake Hajiya Lami lalacacciyar Uwa ce da ba Allah da Manzonsa a ranta bare digon imani bata damu ba acikin kwanakin Hajiya Bunayya ta kawo musu ziyara sunanta hira, harda murnar gwara da suka canza Naseer da Jameel dan da shi suka riƙa gashi na ya rasu.

Kana tun ranan da Samira ta shiga ɗakin bata fita ba duk wani abu da suke buƙata Hajiya Lami na kai musu Boka Kar'uzu kuwa ko yaushe yana manne da ita yana addabarta a haka har ya cika satinsa da yace saida yayi gyaran kwana uku sannan ya koma gidansa bayan komawarsa da kwana biyar Baban Samira ya dawo.


*LITTAFIN SAKAYYAH DAI NA KUDINE KO KIN GANSHI A WASU WURAREN DA BA WURINA BA TOH NA SATANE KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI BABU HAƘƘIN WANI A GANKI LITTAFIN SAKAYYAH 1K NE KACAL DUK DA YAWANSA DA DAƊINSA DUBU ƊAYA NEFA KACAL, ki biya dubunki ɗaya ki karanta maimkyau ba sallake-sallake babu kin samu wasu PAGE ɗin baki samu wasuba ki karanta abinki one by one tura kuɗin samun damar karantawa ta asusuna na GTBank. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 sai in tura miki karanta lfy lafiya. Mu guji yaƙin wani duk ƙanƙantarsa domin na watan nan dai na Allah ya isane atoh*


*Jauro Yaya*
Hajja Nana ce zaune da ƙoron Abincin agefenta yayinda Dije da bata daɗe da zuwa ba ke zaune gefenta cikin sauri Hajja Nana ta miƙe tsaye jin tsayuwar mota aƙofar gida kallon Dije tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace.
“Ya naji kamar ƙaran mota?”.
Kai Dije ta gyaɗa tare da miƙewa kana tace.
“Nima Hajja Nana haka naji kamar ƙaran Mota”.
Cike da zaƙuwa tace.
“Maza je ki duba waye ne?”.
Kai Dije ta gyaɗa tare da fita tana ganin motar tayi dariya tare da ɗaga sautin Muryanta tace.
“Laaa Hajja Nana Baffa Jimeta ne”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Masha Allah dan albarka ya ɗauki abin da muhimmanci ne”.
Anutse Baffa Jimeta ya shigo cikin gidan.
Cikin sauri Dije ta shimfiɗa masa tabirma ya zauna suka gaisa ba daɗewa baki daya ƙannenta suka shigo.
Bayan sun gama gaishe-gaishe Hajja Nana ta kalli Baffa Jimeta fuskarta ɗauke da murmushi tace.
“Kazo kenan?”.
Kai Baffa Jimeta ya gyaɗa cike da ladabi yace.
“Nazo Hajja Nana”.
Murmushi tayi tare da gyara zamanta kana tace.
“Kazo batun Khausar ko?”.
Jinjina kai yayi cikin sanyin murya yace.
“Ai dole na inzo domin cika Umarnin ki”.
Kallon ƙannenta tayi cikin alamun jin daɗi tace.
“Toh Idan Allah ya kaimu gobe da safe zamu tafi can”.
Ahankali ya gyara zamansa sannan yace.
“Toh shikenan Allah ya kaimu lafiya”.

Da daddare Misalin karfe 7:30 malam Arɗo da Abba ne zaune acikin mota Kallon Abba dake tuƙi Malam Arɗo yayi tare da sauke ajiyar zuciya kana yace.
“Insha Allah yau zamuje mu isar da nufin Mu”.
Jinjina kai Abba yayi cikin sanyin Murya yace.
“Insha Allah yau zamu ida Wasiyyar Jameelu na sai muji abinda mahaifin yarinyar zai faɗa”. daga nan suka nufi gidan Ummi

Washe gari da safe Misalin ƙarfe tara Hajja Nana da Baffa Jimeta tare da Malam Liman suka isa gidan Lamiɗo kai tsaye Sashen Mommy ta nufa Dije na biye da ita.
Malam Liman da Baffa Jimeta kuma suka nufi falon Lamiɗo.

Cike sauri Mommy dake shirya dining table ta juya jin Sallamar Hajja Nana cike da girmamawa tace.
“Hajja lale marhaba kece”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da faɗin.
“Wallahi kuwa”.
Murmushi Mommy tayi tare da miƙewa bayan sun gaisa ta nufi dining table ta kawo musu Flaks din tea da soyayyan ƙwai da buredi da kuma ɗumamen tuwon shinkafa miyar taushe ta ajiye musu sannan ta basu waje dake basuyi breakfast suka taho nan suka ci.

Bayan sun gama Mommy na murmushi tace.
“Amma kunyi saurin isowa”.
Kai Hajja Nana ta gyaɗa tana gyara zaman Flaks din tace.
“Eh ai bani kaɗai bace da Malam Liman da kuma Baffa Jimeta muka zo akan dai Maganar Auren Khausar dana miki ne”.
Khausar dake zuba chips afaranti tayi saurin kallon Hajja Nana babu walwala atare da ita tace.
“Wai dan Allah Hajja Nana mena tsare miki ne arayuwar duniyar nan?”.
Kallonta Hajja Nana tayi cikin sassauta murya tace.
“Ni ba abinda kika tsare min, kawai dai gata nake so na Miki domin Aure shine rufin asiri da kuma gatan ƴa mace, sannan ga ɗan uwanki zai riƙe ki da Amana da gaskiya”.
Ta dire ayar mgnar tare da murmushi ta kallon Khausar data tsareta da ido kana ta sassauta murya ta cigaba da cewa.
“Ga Babansa ma munzo tare, dan in muka gama magana ma, shi yau zai wuce mu kuma motar Kasuwa zamu hau kawai”.
Kallonta kawai Khausar keyi Muryanta na rawa tace.
“Wai dan Allah Hajja Nana Meyesa kike min haka ne?.
Agaskiya ni banason abinda kike min?”.
Taɓe baki Hajja Nana tayi tare da tsira mata ido tace.
“Ko bakyaso dole sai anyi”.
Cikin sauri Khausar tace.
“Wallahi Ni dai baza ayimin dole ba”.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe da alamun ɓacin rai ta kalli Khausar tace.
“Wai Khausar Meyesa haka ne bana son abinda kike min fa banaso kifa kiyayi kanki ki barni inji da abu ɗaya”.
Dai-dai lokacin Lamiɗo ya shigo falon tare da zama aƙasa kana cike da ladabi ya Marabci Hajja Nana.
juyawa yayi ya kalli matarsa tuni ya gano ɓacin ran dake fuskarta kawai kawaici takeyi shiyasa bata nunawa amman wani lokaci ma daɗi takeji in Khausar na titse kakartata.
Anutse ya gyara zamansa kana yayi ƙasa da kansa cike da ladabi da kuma mutuntawa yace.
“Addah Nana yanzu mukayi magana da Alhj Muhammadu da kuma Malam Liman mun gama magana dasu”.
Murmushi Hajja Nana tayi tare da jinjina kai kana tace.
“Yawwa sun maka bayani ko?”.
Jinjina kai yayi cike da ladabi yace.
“Eh sunyi min”.
Miƙewa Khausar tayi tare da kallon Dije tace.
“Dija mu tafi”.
Numfashi Lamiɗo ya fesar kana yace.
“A'a Khausar zauna”.
Kai ta gyaɗa tare da komawa ta zauna kana ta sunkuyar da kanta ƙasa hawaye na ciko mata ido.

Ahankali Lamiɗo ya sake yin ƙasa da kansa kana yace.
“Toh Hajja Nana naji abinda yake tafe daku, akan batun Khausar da ɗan Uwanta Aliyu”.
Cikin sauri Khausar ta ɗago kanta tare da kallon Lamiɗo sai kuma tayi saurin sunkuyar da kanta hawaye na kwaranyo mata kana zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi.
Ahankali Abba ya cigaba da cewa.
“Ni babu wata matsala daga gareni, duk da da akwai ƙanina ɗan Yafendo na dake son Khausar tun tana ƙarama, toh amma sawun giwa ya take na raƙumi, abinda kuke ce shi za ayi domin koda inada power akan Khausar kun fini ƙarfi”.
Sai kuma ya ɗago kansa tare da kallon Hajja Nana data tsaresa da ido Ajiyar zuciya ya sauƙe kana ya cigaba da cewa.
“Amma Koda batun Naseer bazai kau da batun ku na kawo na Naseer ba, duk da cewa bamu ji ta bakin yarinya ba duk da naga alamun ta dai-dai-ta da ɗan Uwanta tun da yanzu bana ganinsu da Naseer”.

Ya kare mgnar tare da kallon Khausar da tayi ƙasa da kanta fuskarta cike da hawaye numfashin ya ɗan fesar kana yace.
“Sannan ba aji ra'ayin Khausar ba, domin yaran yanzu ba ayi musu dole sabida haka ya kamata aji ra'ayin Khausar idan tanason.
Ɗan Uwanta tofa sawun Giwa ya take na raƙumi idan kuma Naseer take so tou sai mu nemi al'farma a wurinku”.
Ƙankance ido Hajja Nana tayi kana ta shiga girgiza ƙafanta tare da kallon Lamiɗo tace.
“Lalle kam kamar yanda ka faɗa haka ne, sawun Giwa ya take na raƙumi, sannan batun so kuke ɓata ƴaƴanku mu da ai sai dai a aura maka ko kana so ko baka so, kuma hakan be hana zaman lafiya ba”.
Ahankali Lamiɗo ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa da tausashi harshe yace.
“Ai zamani ne ya sauya Hajja Nana Da da yanzu ba ɗaya bane amman yanzu bari muji ta bakinta”.
Ya kare mgnar tare da gyara zamansa ya fuskanci Khausar cikin tausasawa yace.
“Khausar”.
Murya na rawa ta amsa, yayinda tuni hawaye ke kwaranya.
Mommy kam numfashi mai nauyi ta fesar tare da kauda kanta ranta cike da tausayin yarta.
Shi kuwa Lamido cikin kulawa yace.
“Ki dena kuka Khausar kada ki damu ki gaya min cikin mutun biyu Aliyu Dan uwanki da Naseer wa kikeso, kada kiji tsoro kinjiko Mamana gaya min”.
Jin hakane yasa Khausar ɗago kanta ahankali zuciyarta na cike da wani irin masifaffen rauni murya na rawa ido na kwaranyar da hawaye ta kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Abba Ni dai bana sonsa”.
Cikin sauri Hajja Nana ta kalli Khausar tare da ƙankance Ido a faɗace tace.
“Don Ubanki to Naseerun kike so dangin Mayu!?”.
Sassayan kuka Khausar ta saki tare da cewa.
“Nikam shima bana sonsa”.
Kusan a tare Mommy da Hajja Nana da Lamiɗo duk suka kalleta.
Cikin tsawa da masifar isa da iko Hajja Nana tace.
“Toh wa kike so?, sannan me kike nufi ?,wa zaki Aura?, tunda kince bakyaso Aliyu ba kyason Naseerun?”.
Shiru batace komaiba, sai kuka.
Ganin haka yasa Lamido yin gyaran murya cikin Muryar lallashi yace.
“Toh wa kikeso Manana?”.
Kukan ne ya fara tsanantan mata kana a raunace ta ƙara sunkuyar da kanta.
Afusace Hajja Nana tace.
“Toh dan ubanki wa zaki Aura? Wa kikeso?”.
Cike da sanyi murya na rawa tace.
“Ni dai akwai wanda zan aura?”
Mommy kuwa da sauri ta kalli Khausar wacce tunda aka fara magana bata ce Uffan ba cike da mamaki tace.
“Khausar dawa ye kike soyyayya ban saniba wa kike so wa zaki Aura!?”.
Ahankali Khausar ta gyara zamanta tare da sun kuyar da kanta ƙasa kana tace.
“Ni Moddibo nake so”...!





*LITTAFIN SAKAYYAH DAI NA KUDINE KO KIN GANSHI A WASU WURAREN DA BA WURINA BA TOH NA SATANE KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI BABU HAƘƘIN WANI A GANKI LITTAFIN SAKAYYAH 1K NE KACAL DUK DA YAWANSA DA DAƊINSA DUBU ƊAYA NEFA KACAL, ki biya dubunki ɗaya ki karanta maimkyau ba sallake-sallake babu kin samu wasu PAGE ɗin baki samu wasuba ki karanta abinki one by one tura kuɗin samun damar karantawa ta asusuna na GTBank. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 sai in tura miki karanta lfy lafiya. Mu guji yaƙin wani duk ƙanƙantarsa domin na watan nan dai na Allah ya isane atoh*

By
*GARKUWAR MARUBUTA*SAKAYAH

35

Zare ido Hajja Nana tayi cike da matsanancin mamaki al'ajabi haɗi da alhini.
Tayi salati tare da tafa hannu.
Muryanta na cike da mmki, takaici, haɗi da fusata ta cigaba da cewa.
“Ohh Allah ya kawo mu ƙarshen duniya, yarinya babu tsoron Allah bare aje ga babin kunya ki dubi tsabar Idona ki kuma dubi tsabar idon Mutumin dake matsayin Mahaifinki, sannan ki dubi tsakar idon Mahaifiyarki kice wai wane kike so!”.
Cikin raunin Khausar tayi ƙasa da kanta tana mai rumtse idonta tana jin wani irin yanayi mai cike da rauni azuciyarta.
Wani shegen kallo Hajja Nana ta watsa mata cikin tsananin fushi da ɓacin rai tace.
“Wanene shi Moddibo? wani gantalellen yadine Moddibon? shin inane tushensa su waye ne Asalinsa dame yafi ɗan uwanki da har kika zaɓe sa kika ƙyale ɗan Uwanki dame yake taƙama!?”.
Ta ida maganar tana me tsare Khausar da ta ɗan ɗago kanta fuska cike da rauni, ita Hajja Nana da idanun fusata ta banka mata harara.

Ita kuwa Khausar ahankali ta sake sunkuyar da kanta ƙasa batare da tace. Uffan ba yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke tsuma.
Cikin sanyi Lamiɗo ya sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi tare da jinjina kansa kana ya maida kallonsa kan Khausar da kanta ke ƙasa.
Mommy kuwa cikin yanayin mamaki da yadda maganar tazo mata abazata ta tsirawa Khausar Ido tana maimaita abinda Khausar ta faɗa aƙasan ranta.

Girgiza kai Hajja Nana tayi tare da juyawa ta kalli Mommy tare da sakin kuka kana tace.
“Yanzu Aysha Ina magana kema kinyi min banza, baza ku bani amsaba, wato ni zaku mayar gantalalliya ga tsohuwar banza tana magana dole ku shareni tunda kun mayar dani bansan abinda nake ba”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Khausar cikin matsanancin ɓacin rai da kuka tsufa tace.
“Yanzu abinda kika zaɓawa kanki kenan Khausar!?.
Yanzu abinda zaki yimin kenan? Kice ba kyason ɗan Uwanki?. Wannan dangin Mayu da kika ce bakyaso ai ban damu ba amma ki dubi tsabar Idona kice bakyason jininki ɗan uwanki yaro mai mutunci da kamala?”.
Mommy, Lamiɗo, da Dije baki ɗaya Idanu suka zubawa Hajja Nana suna kallon yadda take kukan tsakaninta da Allah Khausar kuwa still Kanta na ƙasa ita kadai tasan abinda take ji.

Cikin fushi da tsawa Hajja Nana ta kalli Khausar data ƙi ɗago kanta tace.
“Waye shin dame yafi Aliyu?.
Wato dai ya tabbata babu tsoron Allah acikin waɗannan tsayayyun idanun naki, banda lalacewa da taɓarɓarewar tarbiyarki shin har kina da bakin da Iyayenki na maganar aurenki zaki sanya naki aciki da masifar tijara?”.

Cikin sanyi Khausar ta ɗago kanta, tare da buɗe idanunta wanda tuni suka sauya launi daga farin madara zuwa jan rushi, cikin rauni ta kalli Hajja Nana dake zazzaga bala'i kamar ba gobe.
Sai kuma ta lumshe idanunta kana ta buɗe, amma ko ƙala bata ceba.
Afusace Hajja Nana dake kuka tace.
“Maza ki daina kallona da wannan.
Fitsararrun idanunki dake tsaye kamar Nonon maza tunda kin shafawa Idanunki baƙin kwalli, adole gaki ƴar tijara.
Ohoɗijam kai ni wallahi tallahi billahil-azem tunda nake ban taɓa kallon abinda ya gigitani ya ratsa ƙwaƙwalwa ta irin wannan maganar taki ba!”.
Sai kuma ta sanya bakin zaninta tare da sharce hawaye da yar majina still tana kuka tace.
“Yanzu Khausar me kike nufi dani?, kina nufin Baffanki da yayi tattaki tun daga Adamawa yazo nan yazo abanza mu taso tun daga Jauro yaya da sanyin safiya munyi a wofi kenan?.
Ki dubi tsabar Idanun mu saboda baki da kunya kice bakyason Jikana sannan ki dubi tsabar idon Baffanki kice bakyason.
Ɗansa bayan shi zai bada Aurenki?”.
Kasa ɗago kai Khausar tayi ta kalleta sabida wani irin abu take ji azuciyarta yayin da hawaye suka shiga bin kuncinta.
Mommy Kam ta gumi tayi baki ɗaya kanta ya kulle da lamarin ta rasa ta yanda zata fara misalta abin.

Lamiɗo kuwa ganin yanda Hajja Nana ke kuka haiƙan ƙadaran tana surutai yasa ya sassauta muryarsa tare da cewa.
“Dan Allah Hajja Nana kiyi haƙuri ki daina wannan kukan”.
Saurin ɗaga masa hannu tayi still tana kuka tace.
“A'a barni idan banyi kuka ba me kake so inyi tunda Allah ya haɗani da gantalalliyar jika dake son kunyatani a Idanun duniya anya yarinyar nan tana da hankali kuwa kodai akwai abinda ke damun aƙwaƙwalwar , hegiya fitsararriya”.
Cikin rauni da alamun damuwa Khausar ta ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kalli Hajja Nana muryanta na rawa cikin sanyin tace.
“Dan Allah ni. Ki daina zagina Hajja Nana ki daina Sheganta ni ke kinfi kowa sanin cewa niba Shegiya bace kuma ki daina

74 / 140

Chapters