Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sakayya Complete Hausa Novel by Aisha Aliyu Garkuwa

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   84 / 140

249K to 252K   out of 417.8K words

sabbi ana ta haɗa su ga manyan-manyan AC dake aiki kana ga sanyin garin dake sauƙa wajen ya ɗauki sanyi baki ɗaya aiki suke gadan-gadan babu kama ƙafar yaro da alama nan da Kwanaki biyar za'a haɗa komai gashi an dakatar da aikin komai sai sabbi dake aiki Saboda sabunta Injina da akayi Ma'aikatan na ganinsa suka nufo sa suna Cikin harshen larabci suke masa Barka cike da mutuntawa da kuma girmamawa shima sannu yake musu yana yaba aikin da suke.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan wanda yake shine Babba yace.
“Alh aiki na kyau yanda ake buƙata insha Allah nan da kwana biyar za'a gama daddasa Injinan da za'a gama aikin”.
Kallon yanayin wajen Moddibo yayi kana yace.
“Masha Allah abu yayi kyau sosai”.
Kai Engineer ya Jinjina kana yace.
“Sosai ma ai saboda ansamu zaƙaƙuran ma aikata kuma baki ɗaya cikin kwanaki Ukun nan da aka dakatar da buga Abaya's,Veils,Jakankuna da Takalma *BASJAM”.*
Ahankali Moddibo ya lumshe Idanunsa Aransa yace Allah sarki Abba gashi ya haɗa sunan sa dana J ɗina a Company sai dai bashi da ikon aiki a Company Engineer ya cigaba da cewa.
“Baki ɗaya har abin ya fara ƙaranta zuwa ƙasashen da ake kaiwa danma ansamu antanadi masu yawa suna zaune amma Alhamdulillah aikin zaiyi gaggawa tunda ansamu zaƙaƙuran ma'aikata”.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa saboda sanyin da wajen ke dashi kana yana jin yanda Kasan mararsa ke murɗawa ahankali ya ɗaura tafin hannunsa na dama akan maransa ya danna sai kuma ya cije Lips ɗinsa na ƙasa cikin dauriya ya kalli Engineer tun jiya ya kwana da ciwon cikin kana har yau bai lafaba na awa ɗaya mai kyauba da zaran yayi minti talatin zai sake murɗa masa ahankali ya cije Lips ɗinsa kana yace.
“Abu yayi kyau Allah yatemaka insha Allah nan kusa zamu kammala akoma bakin aiki a cigaba da aiki gadan-gadan”.

Ya ida maganar tare da juyawa ya nufi gefen dama wanda office, Office ne awajen wani Corridor ya shiga tare da buɗe makeken Office da yafi sauran kyau da tsaruwa sosai Office din ya haɗu table ne kansa ɗauke da system da takardu sai flowers kana daga jikin bango kujera ce mai juyawa daga gaban table ɗin kuma kuma jeru biyu ne sai Cottons sky blue da fari daga gefen dama Ac ne daga ɗaya gefen kuma tamkar falo ne manyan kujeru ne guda bakwai suma Sky blue sai Tv Plasmer ajikin bango da frigde sai kuma showglass dake ɗauke da kofuna ahankali ya ɗauki remote din AC yaƙara gudu duk da kuwa sanyin da ake stugawa yayin da zufa ya shiga tsats-tsafo masa agaba ɗaya ilahirin jikinsa kana maransa na cigaba da murɗawa jikinsa sai zufa yake karyo masa rintse idanunsa yayi da ƙarfi jin yanda mararsa ke murɗawa tamkar zai fita ahankali ya zauna kana ya ɗaura kansa akan Center table dake tsakiyar falon ya lumshe idanunsa sai kuma yayi saurin buɗewa kana ya lashi busassun laɓɓansa baki ɗaya jikinsa ya fara rawa jin yanda maransa ke dunƙulewa yana tsikarinsa cike da damuwa da rauni ya soma faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Kana yaja wani numfashi me nauyi ya yunkura da niyyar miƙewa ji yayi bashi da kuzarin da zai iya tsayawa ji yayi tamkar an haɗa maransa da bayansa ana dinkewa ga wani irin harbawa da zuciyarsa keyi da Masifar ƙarfi kwanciya yayi akan 3sitter yayi rub da ciki baki daya ilahirin jikinsa rawa yake ga zufa dake tsats-tsafo masa tamkar babu Ac saboda yanda azabebben ciwon cikin ke gallazarsa yakai kimanin minti talatin yana murƙususu akan kujera kafin ya fara lafawa sannu Ahankali ya fara maida numfashi yana fesaewa.

*Gembila*

Asma'u kuwa ta daɗe tsaye aƙofar gida bata samu Adaidaita ba jin kiran sallar La'asar yasa ta juya da niyyar koma gida tayi Sallah kuma sai tasamu adaidaita shiga tayi tana isa gidan Kai tsaye falon Mommy ta shiga bakinta ɗauke da sallama zaune ta samu Khausar da Haiydar tana riƙe da hannunsa tana yanke masa Farce.
Haiydar kuwa kallon Khausar yayi kana yace.
“Nifa ki kula kar ki yanke min hannu”.
Hararansa tayi sai kuma ta cigaba da yankewa kana tace.
“Tunda dai baka iya ba kona yankekama kai ka jawa kanka”.
Ta ƙarasa maganar tare da sauke Idanunta akan Asma'u data gama shiga falon da sauri ta sake masa hannunsa tare da miƙewa da sauri ta Rungume Asma'u cike da farin ciki tace.
“Oyoyo Asmeey ta”.
Zare ido Haiydar yayi tare da yarfe hannunsa yace.
“Wayyo ta yankeni Wayyo ya tsana”.

Da sauri Mommy ta fito daga Bedroom ɗinta Idanunta akan Haiydar tace.
“Lafiya kuwa”.
Yarfe hannu Haiydar yayi kana ya Marerece fuska yace.
“Mommy ki kallafa Addah Khausi ta yanke min yatsana daga kallon Asma'u”.
Langwaɓar da kai Asma'u tayi kana tace.
“Ayyah Haiydar Sorry sannu bata sani bane”.

Hararansa Khausar tayi tace.
“Rabu dashi ƙato dashi tunda dai har yanzu bai iya yanke Farce ba sai dai in yanke masa aikuwa nata yanke masa hannu”.
Kallonta Mommy tayi kana tace.
“Wato ma da saninki kika yanke sa?”.
Cikin sauri ta girgiza kai tare da langwaɓar da kai tace.
“Wallahi Mommy ban sani ba ganin Asma'u ne yasa na tashi da sauri ashe na yanke sa”.

Kai Mommy ta gyaɗa tare da kallon Haiydar tace.
“Sannu Babana mu gani”.

“Mommy Ummina tace in gaisheki”

Jinjnna kai Mommy tayi kana tace.
“Ina amsawa”.
Hannun Asma'u Khausar taja suka shiga Bedroom ɗinta suna shiga Khausar tace.
“Fisabillah baki zoba sai yanzu ko dai kwana zamuyi?”.
Zare ido Asma'u tayi kana tace.
“Mu kwana kuma wa zai taya Ummina aiki da safe?”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi sai kuma tace.
“Don Allah Asmeey mu kwana zan kira Ummi mu roƙeta”.
Kai Asma'u ta girgiza kana tace.
“A'a keto muje mu kwana mana”.
Ware ido Khausar tayi tare da sanya dariya tace.
“Caɓɓ lallai kam”.
Murmushi kawai Asma'u tayi kana ta zauna abakin gadon.
Khausar kuwa fridge ta buɗe ta ɗauki Plate ta sanya Faro water da Ayaba ta mikawa Asma'u.
Karba Asma'u tayi tana ɓare Ayaban tace.
“Ke dai bakya rabuwa da Ayaba aɗaki kina nan kamar biri”.
Murmushi Khausar tayi kana tace.
“Wallahi kuwa Ina son Banana yana min daɗi”.
Jinjina kai Asma'u tayi tare da faɗin.
“Ai lallai dai kam”.

*Morocco*

Aɓangaren Moddibo kuwa haka yaita fama bayan minti talatin cikin yake sake Murɗansa yana kallon gari yayi duhu maghariba ta kawo kai har wasu massallatai sun fara kiran sallah amma ya kasa miƙewa saboda yanda ciwon cikin ke kartansa jin ciwon ya lafa yasa ya miƙe tare ya fita yaga wajen shiru alamar duk ma aikata sun tattafi sai securities da mai bawflowes ruwa kasancewar karfe biyar da wasu Mintuna ake tashi ma tsaye wajen motarsa yashiga yaja ya fita a gate one.
Ya miƙe titin ya fito gate ɗin La riva restaurant dake Opposite da Company yazo Dai-dai wajen Traffick sun tsaida shi saboda sauran motoci da suke wucewa ahankali yasa hannunsa ya dafe fuskarsa ta gefe yatsunsa na dafe da kuncinsa ya tsansa ɗaya kuma na cikin bakinsa kana ya fito da fuskarsa ta wajen motar yana ɗan shan Iska jikin katangar Company sa yana shaƙan iskar bishiyar dabino dake zagaye da Company wanda ta ko ina sune da gudu yaga wata mota ta gilma ta gabansa wacce ta fito daga gefen yamma zata yi gabas kana shi kuma yana gefen kudu ne idan ya samu dama zaibi arewa ganin wulgawar motar yaga fuskar J ɗinsa ne aciki cikin sauri ya zare Idanunsa sakamakon kallon fuskar J ɗinsa aciki Motar cikin wani irin sauri ba tare da anbasa hanya ba ya figi motar ya karya kwana yabisa har ya kusa bige wata mota.

Da mugun gudu yake bin motar kana ga cunkoson ababen hawa kasancewar maghariba ta kawo kai ƴan kasuwa sun taso ga kuma ma'aikata sun tattaso daga Office kowa na burin komawa gida wasu kuma na ƙoƙarin su samu masallacai dan kada su rasa jam'i hakan yasa cunkoso yayi yawa ga kuma duhun gari gudu yake yana bin bayan motar ga kuma cun kuson motoci da suka taresa ya cusa ta nan yaga antaresa baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake tun lokacin daya zare idonsa har yanzu bai maidasu daidaiba saboda idanunsa sun gane masa Allah ya nuna masa fuskar Jameel ɗin sa ne yasani Koda amagagin mutuwa yake ya tabbatar fuskar Jameel wulgawa daya zaiyi ya gane yasani wannan fuskar Jameel ɗinsa ne baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake kana yana maimaita kalmar Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n yana cigaba da dannawa motocin gabansa hon baki daya mutane Kallonsa suke wasu kuma na cewa wannan kam lafiyarka ina zakaje haka kamar zaka tashi sama shidai haka ya cigaba da tafiya ya kutsa tanan ya kutsa tacan garin hakane ya bigewa wani motarsa mutumin na cewa Kai lafiya amma ina tuƙi kawai yake da gudu baki ɗaya hankalinsa baya jikinsa wani mai Napep ne ya tare gabansa madadin ya kalli gabansa amma baki ɗaya idanunsa na kan motar daya yaga J ɗinsa aciki yana samu ƙaramar ɗin ya kauce masa ya cigaba da bin bayan motar yanda yake gudu da masifaffen ƙarfi haka zalika motar da yake bi ɗin ma take gudu hakan yasa yasake tabbatarwa kansa J dinsa ne kenan gudunsa yake ko kuma yaya ahaka suka isa wani roud about nan yaga ya ɗauki hanyar da zata sa dashi da flyover gudu yake da ƙarfi haka shima wancen ke gudu duk da gudun da yake amma ya kasa kamo wancan motar saboda shima gudun yake ga kuma motoci dake tsakaninsu amma yana iya hangosa kasancewar be wuce motoci biyu zuwa uku bane agabansa sunzo daidai kan Flyover yasamu yabi sama Shima Moddibo cikin sauri yabi sama kasancewar ba cunkoso sosai numfashi mai karfi ya sake kana ya hau kan Flyover yabi sana kafin ya isa tsakiyar Flyover shi kuma wannan har ya sauƙa ya ɗauki hanyar Unguwar Mellila shima Moddibo cikin sauri yabi wannan hanyar tafiya kaɗan sukayi yaga motar ta wuce wani asibiti cikin gudu shima ya wuce tafiya kaɗan suka ƙara yaga motar taja kwana adai-dai wani tamfatsetsen gini mai masifar kyau da girma bisa duk kan alamu asabiti ne saboda sunan dake manne asaman ginin idanunsa ya ɗaga yaga sunan dake manne ajikin ginin *Youssef Mouley Hospital*.
Mai motar kuwa yana danna hong aka buɗe masa gate yashiga kafin ya juya akalar motarsa ya ƙarasa wajen kuma a maida gate din ana ƙoƙarin rufewa da wani irin sauri ya danna hancin motarsa cikin gate din.

Cikin sauri securities dake bakin gate din suka taso suka yo Kansa.
Shi kuwa mutumin cikin motar tuni yayi Parking ya buɗe motar ya fita da sauri Norses biyu suka biyu bayansa suna faɗin.
“Welcome Sir”.
Security din kuwa kan Moddibo suka nufa suna faɗin.
“Lafiya kuwa?”.
Shi kuwa Moddibo gadan-gadan ya nufi kan security din da sauri suka kauce masa yana shiga yayi Parking kana ya fito da sauri security suka yo kansa suna faɗin.
“Lafiya kuwa?”.
Bai tanka suba yabi bayan mutumin yana cewa.
“J!,J!!,J!!!,”.
Shikuwa Mutumin gaba yayi Norses na biye dashi jin hayaniya yasa ya juya ya kalli bayansa gani yayi Moddibo ya nufo kansa yana cewa.
“J”.
Security kuwa ƙoƙarin riƙesa suke suna faɗin.
“Malam lafiyar ka kuwa ina zaka je?”.
Cikin sauri Moddibo ya hankaɗesu kana cikin fushi yace.
“Ka matsa min anan ka bani hanya, J!J!!”.
Wata matace ta fito daga cikin Hospital din ta ƙaraso kusa da wannan mutum kana tace.
“Dan Allah Dr Jameel kayi sauri kaceci rayuwar ƴata tana cikin hatsari”.
Jin haka ne yasa Mutumin da takira da Dr Jameel ya juya ya nufi cikin asibitin.
Moddibo kuwa da gudu yabi bayan Dr Jameel da already ya shiga cikin reception tamkar wani zautacce haka ya dawo baki daya bashi da wani cikakkiyar nutsuwa Akuma dai-dai lokacin yaji cikinsa ya sake kartawa da masifaffen ƙarfi da gudu ya nufi kan Dr Jameel yana cewa.
“J!,J!!,J!!! Ina zaka je”.
Afusace Dr Jameel ya tsaya tare da juyawa yace.
“Wai lafiya Malam Security ku fita dashi mana me kuke jira ha'a ya zaizo yana mana ihu yana firgita mana marasa lafiya”.
Baki ɗaya Norses da sauran mutanen ido suka zubawa Moddibo.
Cike da girmamawa security yace.
“Yallaɓai munyi ƙoƙarin korinsa amma yaƙi tafiya sai turemu yake”.
Juyawa Moddibo yayi jin J ɗinshi na mgn da larabci wai a koreshi, da sauri ya buga hannunsa aƙirjin Dr Jameel Cikin juya harce zuwa larabcin yace.
“J ni kake cewa akaro?,J nine fa A.J ɗinka ni kake cewa akaro?”.
Cikin fushi Dr Jameel ya fincike hannun Moddibo ajikin rigarsa yace.
“Ka sakeni wanene kai a ina na sanka kaji yanda kake ihu kana gigita mana mutane”.
Ya ƙare mgnar yana yiwa Modibbo wani irin kallo mai cike da tarin mmki da kuma son nazartan abubuwa da yawa musamman kamaninsa.
Shi kuwa Modibbo Cikin rauni da tsanananin tashin hankali da azabebben ciwon ciki Moddibo ya sanya tafin hannunsa ya dafe maransa muryarsa na rawa yace.
“J Nine fa J A.J ɗinka kake cewa baka gane ba Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n J nine yau kake cewa baka sani ba?”.
Akuma dai-dai lokacin cikinsa ya sake murɗawa da masifaffen ƙarfi cike da ɓacin rai Dr Jameel ya Kalli security kana yace.
“Ku fitar min dashi”.
Norses ɗin kuwa cikin alamun damuwa suka ce.
“Dan Allah Dr muje ka duba matarnan”.
Juyawa Dr Jameel Yayi Moddibo kuwa ganin haka yasa Cikin wani irin rauni ya kallesa muryarsa na rawa kana numfashinsa na fusga yace.
“Jameelu nine fa aduniya Koda baza ka gane kowaba amma Ni da Ummi da Abba bamu cancanci kamanta damu ba kuma ko me yafaru da kai aduniya Ni dai da Ummi da Abba bamu cancanci ka ce baka gane muba A.J dinka nefa”.
Yana gama faɗar haka ya yanke jiki yayi baya...

*Zakusha Typing errors dan banyi editing ba, wani wurin zakuga kalaman a baude ko baibai*

By
*GARKUWAR FULANI*SAKAYYA

40

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number'n nayine, ko kuma a'a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan*
Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.
INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah

84 / 140

Chapters