Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sakayya Complete Hausa Novel by Aisha Aliyu Garkuwa

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   91 / 140

270K to 273K   out of 417.8K words

bai samu yayi shi ba a lokacin rasuwar, baka jin sautin komai acikin ɗakin, face Shesh-sheƙan kukan su dake cigaba da wanzuwa aƙalla sun ɗauki kimanin minti goma sha biyar suna kuka batare da wani yayi yunƙurin rarrashin ɗan uwansa ba.
Cikin dauriya da ƙoƙarin son hana kansa kuka kana da shesh-sheƙa Jalaludeen ya ɗago tafin hannunsa mai masifar sanyi tamkar wanda aka ciro acikin dusan ƙanƙara ya manna aƙirjin Moddibo daya ke jiyo bugun zuciyarsa, cikin rauni yace.
“Kayi haƙuri Mouley haƙiƙa munyi rashi mai girma.
Munyi rashi mafi ciwo azuciyarmu. Kayi haƙuri Aliyu kaya femin tsawon lokaci baka ganni ba ina cikin haramine! shiyasa baka ganniba”.
Lumshe idanu Moddibo yayi wasu hawaye masu masifar zafi suka zubo akuncinsa yayin da sanyin tafin hannu Jalaludden ke ratsa zuciyarsa Jalaludden kuwa cikin raunatacciyar murya ya cigaba da faɗin.
“Saboda na shiga inayin I'itiƙafi tsawon lokacin nan shiyasa kuma koda na fito munyi tafiya nida Kakana munje ƙasar Sin shiyasa baka ganni ba bansan Jameelu yashiga wannan hali ba bansan Jameelu ya rasuba Mouley”.
Sai kuma ya fesar da numfashi mai zafi tare da cigaba da faɗin.
“Sai jiya Juma'a ne naje Taraba domin kai muku ziyara, kasancewar na daɗe ba muyi magana ba yasa na shirya muku Surprised sai dai kawai ku ganni, toh ina isa gidan innayi na nufa, naje gidan Innayi na samu babu kowa sai na wuce gidan Ummi”.
Kallonsa kawai Moddibo keyi hawaye na cigaba da silala daga idanunsa.

Cikin rauni Jalaludden yace.
“Acan na samu Innayi suna hiran. Jameel ya rasu kuma na tsinkayi cewa kana ƙasar Morocco, nazo ƙasar Morocco na bibiyi al'amarin ka har na gane cewa kana cikin Fadar Rabat!”.
Kuka ne yaci karfinsa cikin kuka kamar ƙaramin yaro ya cigaba da cewa.
“Mouley munyi rashi.
Jameel ya tafi ya barmu Allah yajiƙan Jameel Allah yayi mishi rahma!”.

Cikin sanyin murya Moddibo yace.
“Amin Ya Allah. Amman nayi mamaki rashin jinka Jalaladdeen ina ka shiga, tsawon lokaci ba ɗuriyarka. Na shiga matsanancin damuwa Jameel ɗina ya ɓace tsawon lokaci, bamu sameshi ba.
Naso ace kana kusa damu kayi mana amfani fiye da amfanin da kayi mana abaya ka faɗa mana inda J.yake”.
Kai Jalaludden ya girgiza still hawaye na kwaranya daga idanunsa ya riƙe hannun Moddibo kana yace.
“Bana kusa Aliyu, sannan kuma koda ina kusa muma kanmu jinnu. Ubangiji bai sanar damu gaibu ba Aliyu,
da ace Allah ya sanar damu ilimin gaibu ko a inda nake zan iya sani da zan faɗa maka, amma Allah bai sanar damu gaibu ba.
Sanin gaibu sai Allah kaɗai bansan haka zai faru da Jameel ba.”
Numfashi Moddibo ya fesar kana ya dafe goshinsa da hannunsa na dama tare da faɗin.
“Tabbas munyi rashi mafi girma ban taɓa sanin ya ɗaci da zafin mutuwa yake azahiri ba har sai da na rasa J ɗina, mutuwar J mutuwa ce da bazan taɓa mancewa ba. Sannan bazan daina jin zafi da raɗaɗinsa ba har sai ranar dana koma ga Ubangiji na!”.
Kai Jalaludden ya gyaɗa kana yace.
“Sosai ma kuwa Aliyu, amman haƙuri zamuyi, domin babu abinda Jameel yafi buƙata agaremu yanzu face addu'a addu'ar mu”.
Kai Moddibo ya jinjina tare da cewa.
“Zan cigaba da yiwa J ɗina addu'ar samun rahamar ubangiji har zuwa numfashina na ƙarshe”.
Haka suka kwana suka yini suna hira.

Washe gari da safe koda Sarki Youseef Mouley da Didi suka shiga wajen Moddibo suna tare da Jalaludden sai dai su basu da ikon ganinsa kasancewar bai bayyana musu kansa ba,
ko Moddibo ba ma asiffar mutum yazo masa wanda sukayi karatu dashi.
Bayan fitansu ya kalli Moddibo yace.
“Kana kama da Mahaifinka”.
Da mamaki Moddibo ke kallonsa kafin ahankali yace.
“Mahaifina ko?”.
Kai Jalaludden ya gyaɗa Fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Eh Mahaifinka mana, shin ban taɓa faɗa maka cewa kai ba ɗan Nigeria bane, har kaita dariya kana tambayata to kai ɗan ina bane?”.
Kai Moddibo ya jinjina tuni lokacin suna Jami'atul Madina bayan sun fito daga darasi suna shan shayi Jalaludden ke sanar masa.
Still da murmushi afuskarsa ya cigaba da faɗin.
“Har kace min kai ɗan ina ne nace kai ɗan Morocco ne, kace ba haka bane.
Amma ni nasan hakane saboda nayi bincike ne akan Innayinka na kuma fahimci haka”.
Zazzafan ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe cikin tsira masa idanu yace.
“Kenan kana nufin nan ƙasatace?”.
Murmushi Jalaludden yayi ta gyaɗa masa kai kana yace.
“Sosai ma kuwa ƙasar kane, tsatsonkane, Mahaifarkane. Wa'annan kuma Mahaifanka ne”.
Cikin girmamawa lamuran Ubangji mabuwayi gagara misali Moddibo yace.
“Ya Salam shin taya akayi wanna al'amarin yakasance ya akayi abin ya faru a haka, abin ne yazo min tamkar amafarkaina na yau da kullum”.
Gyara zama Jalaludden yayi tare da faɗin.
“Kada kayi mamaki,Ka cire al'ajabi da mamaki acikin lamarin Ubangji ya wuce mamaki. Kai dai kawai kayi godiya ga Allah”.
Ahankali Moddibo ya motsa laɓɓansayace.
“Alhamdulillah Allah kulli halin”.

Kai Jalaludden ya jinjina haka suka cigaba da hira kafin daga bisani Jalaludden ya kalli Moddibo da murmushi afuskarsa yace.
“Sannan kuma akwai al'amarin da naje na samu ranan juma'a ya kasance amma bazan faɗa maka ba sai ka ganin da idonka”.
Ware idanu Moddibo yayi kana ya langwaɓar da kai tare da cewa.
“Jalaluddeen nawa dan Allah ka faɗa min mana”.
Ƴar dariya Jalaludden yayi wanda ya bayyanar da fararen haƙoransa yace.
“Ok naje na samu Ummi ta shiga damuwa sosai akan tsawon kwana uku kenan tana kiran wayar ka amma bai shiga har Abban Jameel yazo da kanshi dan Maganar dana samu suna tattaunawa da Innayi kenan”.
Lumshe idanu Moddibo yayi yasan dole hakan zai kasance rashin jinsa awaya zai ɗaga musu hankali musamman Innayi da Ummi shima Abba sai dai kawai yayi dauriyar maza.

Da murmushi Jalaludden ya cigaba da cewa.
“Ya faɗawa Innayi shima ya kira wayarka baya shiga tsawon kwana uku kenan, amma kuma Innayi sai dariya take tana ce musu kada su damu kawai afara shirin kawo maka”...
Sai kuma yayi shiru tare da yin mgnar zuci. Alhamdulillah gwara da ban faɗa masa ba saboda naji suna faɗin cewa Moddibo bai san anyi masa Aure ba..

Ɗan ware idanu Moddibo yace.
“Ana shirin kawo min me?”.
Buɗe hannu Jalaludden yayi kana yace.
“Kai dai ana shiri kawai abinda naji sun faɗa kenan”.
Langwaɓar da kai Moddibo yayi cikin Muryansa mai cike da sanyi yace.
“Kai dai Jalaludden baza ka faɗa min ba kawai”.
Kai Jalaludden ya girgiza kana yace.
“Um-um iya abinda naji kenan, kasan na faɗa maka bansan gaibu ba Allah ne kaɗai mafi sanin gaibu”.
Kai Moddibo ya jinjina cikin gamsuwa da maganarsa yace.
“Toh shikenan”.

Washe gari Litinin ya kama kwanan Moddibo biyar kenan acikin Masarautar Mouley.
Misalin ƙarfe tara na safe Moddibo ne zaune acikin tangamemen Falon kamar yanda ya saba ko yaushe yaji an buɗe ƙofar falon anutse ya ɗaga kyawawan idanunsa tare da kallon ƙofar.
Idanunsa suka sauƙa akan.
Didi da Sarki Youseef Mouley sai wani kyakykyawan Matashi mai masifar kama dashi kallo ɗaya ya masa ya fahimci shine Ibraahim ƙaninsa ne da Didi ke yawan bashi labarinsa duba da kamannin dake tsakanin su. Sai kuma Lalla Khadijah da Lalla Hafsat, sai ƴar auta Rahama.
Ibraahim kuwa yalwataccen murmushi ya sakar masa domin shi yakasance mutum ne mai fara'a da son Mutane kana da abin dariya

Suna haɗa ido da Moddibo ya ƙara fara'ar fuskarsa kana ya tafi cikin sassarfa ya rungumeshi yana mai jin farin ciki da nutsuwa agaba ɗaya ilahirin jikinsa cike da shauƙi ya ɗago kansa kana yace.
“Yaya zance maka? Ko kuma Usaini? ko kuma Hassan ɗina?”.
Moddibo kuwa lokaci ɗaya ya tsinci kansa da ƙaunar yaron aransa rungumesa yayi kana cikin ɗan sakin fuska yace.
“Koma me ka kirani dashi zan amsa”.
Sai kuma suka sake rungume juna yayin da ƙaunar junansu ke ratsa ko wani lungu da saƙon dake jikinsu...
Cikin tsanananin so da ƙauna Lalla Khadijah tace.
“Kai Ibraahim ka sakeshi haka mana”.
Kalla Hafsat dake ruggume da ɗiyarta ce tayi dariya tare da zama tana kiciniyar bawa baby nono, tace.
“Ai dai kam ya maƙaleshi kamar ya fimu sonshi”.
Didi da Abualeey kam kallonsu kawai suke cike da jin daɗi mata misaltawa.
Rahama kuwa cikin tura baki ta harari Ibrahim cikin yanayin tsamar saƙo-da saƙo tace.
“Ai shi haka yake ga yadda ya maƙaleshi kamar shine auta”.
Cikin jin daɗi Abualeey yace.
“Toh mu zauna dai kafin ai ta yiwa Ibraahim ƙorafi”.
Shiko Ibraahim signal yayiwa Rahama tare da cewa.
“Ai shi nawane ni kaɗai ba dama cewa kike nine bani da ɗan uwaba toh Allah ya dawo min da ƴaƴana dama yafi Yayunki kyau”.
Lalla Khadijah ce ta ɗan zuggure ƙayarsa.
Ɗan tsalle yayi tare da
ɗago kansa ya kallin Moddibo kana yace.
“Kaga abinda suke minko ko Yah Aleey”.
Murmushi Modibbo yayi tare da ɗan janye jikinshi gefe yana mai kallonsu ɗaya bayan ɗaya yakejin sonsu da ƙaunarsu na ratsa mishi zuciya.
Shi kuwa Ibraahim baki ya ɗan tura tare da cewa.
“Kayi haƙuri ɗan uwana”.

“A kan me?”. Modibbo ya jefa mishi tambayar.
da sauri yace.
“Sabida rashin dawowata da wuri, sabida ranar da kazo ranar na tafi Turkiyya dan daga nan muke kai musu dabino, toh nike wakiltan lamarin, koda Lalla Hafsat ta gaya min ji nayi kamar inyi fiffige in dawo gashi naga dan ban dawo da wuriba kamar kafi sonsu a kaina”.
Dariya sukayi baki daya.
Sai kuma duk suka tsagaita tare da zubawa Modibbo ido ganin yadda yake dariya tare da shafa kan Ibraahim dan ganinshi yake kamar Bashir.
Didi kuwa da su Kalla Hafsat murmushi dukeyi ganin yadda ya jawo Ibraahim ya ruggumeshi yana mai cewa.
“Waya ce maka nafi sonsu, suda zasu koma gidajensu su barmu tare”.
Cikin dariya yayi musu gwala.
Rahama kuwa ɗan rawa tayi tare da faɗin.
“Ni dai muna tare”.
Shi kuwa Ibraahim
juyowa ya kalli Didi da Abualeey tare da cewa.
“Dan Allah Didi ku aurar da ita ta bar mana gida mu sake".
Baki ta tura tare da cewa.
“Ba ruwanka da ni”.

Didin kuwa fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi ta kallin ƴaƴan nata dake zaune reras agabanta kana tace.
“Alhamadullah Allah na gode maka da ka cika min farin cikin ahlina”.
Kai Abualeey ya jinjina tare da faɗin.
“Masha Allah”.
Ibraahim kuwa
janye hannunsa dake cikin na Modibbo yayi kana ya juya tare da kallon Alƙibla yayi Sujudur Shukur.
Kana ya ɗago tare da komawa gefen Moddibo ya zauna still fuskarsa ɗauke da ƙayateccen murmushi ya kalli Sarki Youseef Mouley tare da faɗin.
“Abualeey Addu'ar mu ta karɓu Ubangiji ya dawo mana da Yah Aliyu alokacin da bamuyi zato ba sannan ba muyi tsammani ba sai nake ji kamar gaba ɗaya burikana na duniya aka gama cika min dan ganin ɗan Uwana kuma gudan jina”.
Kai Sarki Youseef Mouley ya gyaɗa kana yace.
“Tabbas kuwa domin babu abinda ya gagari Ubangji Allah da kansa yace mu roƙeshu zai amsa mana. Domin shi addu'a ba'a gaggawa dashi”.
Moddibo kuwa cike da tsananin so da ƙaunarsu dake ratsa ko wani magudanan jinin jikinsa yace.
“Tabbas kuɗin kun kasance min. Garkuwa ne atare dani ina jin ajikina babu abinda zanyi face godiya ga Allah daya haɗani daku kafin na koma garesa”.
Haka suka cigaba da hira tsawon lokaci ganin suna shirin tafiya yasa Moddibo ya sunkuyar da kansa ƙasa kana yace.
“Ayyah Abba dan Allah Ina bukatar wayoyina akawo min su”.
Murmushi Sarki Youseef Mouley yayi kana yace.
“Kada ka damu za'a kawo maka wayoyinka dan suna hannu na”.
Cikin sauri da mamaki Moddibo ya kallesa tare da faɗin.
“Abba toh a taimaka min dasu Ummi, Innayi, da Abba zasu nemini, musamman ma Innayina zata shiga damuwar rashin jina?”.
Kai Sarki Youseef Mouley ya girgiza kana yace.
“Kada ka damu In sha Allah babu komai rashin ɗaukar wayar yana da muhimmanci, da amfanin da zaiyi Kankane yace kada a ɗauki wayar shiyasa ma ban kawo maka ba”.
A ladabce Moddibo yace
“Abba zasu shiga damuwa saboda zasuji tsoro kada abinda ya faru da Jameel nima ya faru dani”.
Cike da kulawa Sarki Youseef Mouley yace.
“Wanene Jameelun naka?”.
Idanunsa ya lumshe tare da buɗewa kana yace.
“Ai wannan Dr Jameel ɗin dana biyo, da fari ina bibiyarshi a zatona J nane sabida tsananin kamar da sukayi”.
Nan ya shiga basu labarin Jameel da duk abinda ya faru dashi.
Ya ɗaura da faɗin.
“Shiyasa lokacin da naga wannan Dr Jameel baki ɗaya na ɗauka cewa Jameelu na ne saboda kamanninsu yayi yawa, hatta maganarsu, tafiyarsu, muryar su babu abinda ya raba su sai dai ɗabi'unsu ya samu bambanci dana Jameelu na”.
Cikin raunin murya da tunowa da Jameelunsa ya basu cikekken tarihin abotarsu.
Sosai suma suka tausayawa masa tare da yiwa Jameelun fatan samun rahamar Ubangji kana ya cigaba da faɗa musu cewa aikine ya kawo sa kamfanin Baban Jameelu.
Cikin fesar da numfashi Ibraahim yace.
“Allah sarki Yah Jameel Allah ya gafarta masa”.
Cikin sanyi Moddibo yace
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Lalla Khadijah ce ta gyara zama tare da fuskatarsa kana a mutunci tace.
“Da fari dai kaga iya mu yamune cikin mahaifiyarmu da wasu daga cikin amintattun fadane, suka san da isowarka wacce dole labarin ya bazu cikin Faɗa, to Alhamdulillah zan haɗa taro na musamman damon gabatarda kai a tsakiyar family'nka wato zuriyar sarki Aliyu Mouley, wanda zuriyace ta tun kakannin Abbanmu da kuma kakanninmu, mu da kuma iyayenmu da ƴan bappanayenmu dama goggoninmu, in Sha Allah zayi tarone na musamman dan dan haka ka shirya fuskatarta idanu mabanmanta. Alhamdulillah na gamsu da nitsuwarka zuwa yau kuma na fahimci kasan komai na tsarin al'adunmu da nake mamakin yadda akayi ka sansu”.
Da sauri Kalla Hafsat tace.
“Ke kuwa Lalla Khadijah ya za'ayi ya rayu da jakadiya kiyi tunanin akwai wata al'adar da bazai saniba”.
Murmushi Modibbo yayi domin shi dai innayi bata taɓa alaƙantashi da labarin fadaba, sai dai yasan komai na fadar ne a cikin mafarkansa.
Abualeey ne ya gyara zama tare da cewa.
“Zuwa yanzu mun gama shiryawa komai na taron”.
Haka dai sukaci gaba da tattauna lamurran.

Washe gari ranan Asabar misalin ƙarfe uku na yamma Jirginsu Innayi yayi landing a _Rabat Sale international airport_.

Suna sauƙa a airport motocine na alfarma guda biyar suka zo ɗaukar su bisa jagoranci Dr Ahmad abokin Abban Jameel.
Mota ta farko Dr Ahmad ke driving yayin da Abban Jameel ke gefensa daga can baya kuma Innayi ce tare da Hajja Nana da kuma Khausar.
Motar dake bima sa kuwa Ummi ce da Hajiya Bunayya sai kuma ƙanwar Momyn Khausar Aunty Hajara, sai Haiydar da yake gaba gefen direba.
Yayin da mota ta uku kuwa Asiya, Asma'u ce tare da Dija. Sai Aunty Ruƙayya ƙawar Mommy
Motar dake bayansa kuwa Baffa Jimeta ne da matarsa Hajiya Umma, kana da Babbar Ƴar sa mai suna Aunty Hawwa .
Yayin da motocin ke tafiya ajere cikin nutsuwa bisa Jagoranci Dr Ahmad
Bayan sun shiga cikin gari sun nufi unguwar Ben slimane, cikin sauƙe numfashi Innayi ta fesar da numfashi tare da buɗe Idanunta ta kalli cikin garin da tsarukan da kuma gine-gine suka sauya alamar garin ya sake samun cigaba fiye da da.
Cikin sanyayyar murya me cike da kewa da kuma bege ta kalli Dr Ahmad dake driving kana tace.
“Mubi ta unguwar El'gara sai mu ɓullo ta cikin Ben Ahmad dan Masarautar Rabat zamu nufa”
Cikin wani amintacciyar murmushi Abban Jameel ya juya ya kalleta kana yace.
“Kai tsaye kuma?”.
Kai ta jinjina kana tace.
“Eh can zamu nufa shine abinda yafi da cewa”
Still Idanunsa na kanta yace.
“Amma da ya kamata mu fara isa masauƙi mu huta tukunna!”.
Numfashi ta fesar tare da faɗin.
“A'a ai acan ya dace muyi hutun”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Toh shikenan”.
Shi kuwa Dr Ahmad juya akalar motar yayi, kana suma saura suma mara mishi baya.
Nan suka ci-gaba da tafiya cikin nutsuwa still motocinsu na jere.

Suna isa ƙofan Gate na farkon Masarautar Rabat ganin motoci ajere yasa cikin Sauri Hadiman dake bakin gate ɗin mutum biyar suka miƙe biyu suka tsa gefen damar motan biyu gefen hagun motar kana ɗaya ya tsaya agaba.
Cikin nutsuwa da yanayin jikin girma Innayi ta sanya hannu ta buɗe murfin motar kana ta fito yayin hannunta ke riƙe da wani abu kamar murfi kolbar Vaselin sai dai bisa ga alamu ginannene kana anyi sa da hatimin Masarautar.
Wanda ke kusa da ita ta miƙawa.
Karɓa yayi ya duba kana yayi saurin kallon fuskarta sai kuma ya juya ya miƙawa na gefensa shima ya karɓa ya duba.
Da wani irin sauri suka ɗaura hannunsu asaman ƙirjinsu kana suka sunkuyar da kansu alamar girmamawa.
Kai ta jinjina musu.
Kana cikin sassarfa suka juya tare da buɗe musu Gate ɗaya daga cikinsu ya tsaya abakin Gate yayin da sauran huɗun suka marawa moticin baya cikin sassarfa suna isa Gate na biyu ɗaya daga cikin masu binsu yayi saurin buɗe musu Gate ɗin suka shiga kai tsaye har harabar fadar suka isa, suna isa sukayi Parking atare.

Acan motarsu Hajiya Bunayya kuwa Haiydar wani irin zazzafan ajiyar zuciya ta sauƙe mai nuni da zallan mamaki kana ta kalli gabas da yamma kudu da Arewa wani irin daular duniya da suka shiga wanda ya kamata akirasa da Aljannar duniya cike da al'ajabi ta maida idanunta kan Ummi kana tace.
“Toh nan kuma ina muka zo haka”.
Lallausan murmushi Ummi ta sakar mata kana tace.
“Nan gidansu Moddibo muka zo gidan Mahaifinsa”.
Dariyar sheƙiyanci Hajiya Bunayya ta saki tace.
“Kai lallai wannan ta tsuniya yawa ne dashi nan ɗin ne gidansu Moddibo?”.
Kai Ummi ta jinjina tare da faɗin.
“Toh ki zuba ido ki gani”.
Baki ta taɓe tare da yiwa Ummi wani kallo kana tace.
“Caɓ amma Ummin Jameel banyi zaton haka daga gareki ba da girmanki”.
Ta ida maganar tare da ƙyalƙyalewa da dariya ita baki ɗaya ma maganar dariya yake bata yo ai ko amafarki Moddibo bai isa ya kasance jinin wannan ahali ba mutumin da ake kyautata zaton ɗan shegene.
Ummi kuwa da mamaki ta kalli yanda take dariya kana tace.
“Kina mamaki ne?”.
Hajiya Bunayya kuwa cikin taɓe baki tace.
“Sosai ma kuwa ai ba mamaki ba harda Al'ajabi na haɗa Moddibo fa”.
Sai ta kuma fashewa da dariyar sheƙiyanci data tuna wai Ummi tace nan gidansu Moddibo ne.
Kai kawai Ummi ta girgiza batare da tace Uffan ba tana mai bin baki ɗaya ilahirin gidan da kallo.

Acan Motarsu Asma'u kuwa cikin zumuɗi da ganin tsantsan kyawu da tsaruwan gidan Dija tace.
“Ehyeh”.
Asiya ma kallon coumpund ɗin tayi cike da shauƙi tace.
“Wowwww Masha Allah kaga wani daular duniya”.
Asma'u kuwa dogon numfashi taja tare da fesar wa tare da faɗin.
“Toh Masha Allah wannan al'amari da ban mamaki yake”.
Motocin kuwa re ras suka tsaya.
Fadawan dake tsaye bakin Fadar kuwa cikin sauri suka nufo motocin wanda aƙalla sun kai biyar isowarsu yayi dai-dai da fitowar Innayi daga motar.
Sarkin ƙofane idanunsa suka sauƙa akanta cikin sauri ya mutsi-stika Idanunsa kana ya sake kallonta sama da ƙasa cikin al'ajabi da mamaki tu'ajubi yace.
“Innare Jakadiyar Gimbiya Ruƙayya?”.
Murmushi Innayi tayi kana ta gyaɗa masa kai tare da faɗin.
“Eh”.
Duk da yawan shekaru kuwa sun gane juna
Cikin wani irin sauri ya juya tare da nufar cikin Fada yana shiga ya durƙusa agaban Sarki duk da

91 / 140

Chapters