Author : Aisha Aliyu Garkuwa Category : Free Novels Online (Read & Download)
min kama da wani sai dai na rasa da waye yake min kama ina ta tunani na rasa ganowa sabida gaba ɗaya lamarin shi ɗauremin kai yadda yake ta nuna ya sanni”.
Sai kuma ya ɗan fesar da numfashi tare da gyara zamansa kana ya cigaba da cewa.
“Na rasa dawa yake min kama baki ɗaya abin ya kwanta min akaina, sai yau da muka zo nan naga na kalli Fuskar Abualeey, sai na ga suna tsananin kama, sai kuma na tuni Ibraahim ashe dasu yake min kama kai kamanninsu da Ibraahim ya ƙazanta Didi shin wanene shi”.
Cikin wani irin yanayi na tsananin al'ajabi da tsuman zuciya. Didi ke sauraransa yayin da ƴaƴanta Lalla Khadijah, da kuma Lalla Hafsat mahaifiyar Hakim wacce take aure a Mexico wanda zuwan kakansu Sheiyk Jabeer Nuruddeen Gwadabe Joɗa, ne yasa su zuwa dan ganawa da kakansu.
Ido suka tsira Dr Jameel cikin son fahimtar wani abu.
kana hadiman Didi kuwa dake can gefe sunkuyar da kansu sukayi
Dr Jameel kuwa ahankali ya cigaba da faɗin.
“Sannan kuma ashe ban sani ba yana bibiyata, har muka shigo gidan nan”.
Nan ya kwashe komai tun daga haɗuwarsa da Moddibo har zuwa yau ya sanar mata...
Kana ya ɗaura da cewa.
“Sannan kuma Didi ɗazun da Abualeey ya kirani kan inzo in duba jikin Rahma ciwon cikinta ya tashi. Ashe ban sani ba yana biye dani sannan kuma shigowar da zamuyi *Rinƙas* ya ƙwace ya shigo cikin Masarauta Didi.
zakisha mamaki idan kika ga yanda yake sarrafa Dokin nan”.
Lokaci ɗaya Lalla Khadijah da Kalla Hafsat suka kalli juna, kana suka juyo cike da mmki suka kalli Didi.
Da bugun zuciyar ta ya sake nunkuwa fiye da kaso tamanin cikin ɗari.
Cikin fesar da numfashi ya cigaba da cewa.
“Kuma kinfi kowa sanin mutum biyu ne ke kaɗai ke iya, sarrafa Rinƙas, ko Ibraahim baya iya zuwa ko kusa dashi.
Amman shifa kai tsaye ya fuskanci dokin. Didi wlh al'amarin mutumin yayi masifar ɗaure min kai fiye da yanda kike zato”.
Didi kuwa tun daga lokacin da Hakim ya faɗa mata yaga mai kama da Ibraahim zuciyarta ke bugawa har zuwa yanzu da Dr Jameel ya dasa ayar mgnar, cikin sauri ta juya ta kalli Lalla Khadija da Hafsat, sai kuma Rahma data fito yanzu ta kwanta gefenta Lalla Hafsat tana damƙe cikinta.
cikin sauri Hafsat da idanunta ke waje ta kalle Didi kana tace.
“Didi”.
Murya cike da sanyi da bugawar zuciya Didi tace.
“Na'am”.
Sai kuma suka shiga kallon juna alamar maganar ta ratsasu.
Dr Jameel kuwa batare daya lura da yanayin da suke ciki ba ya cigaba da cewa.
“Allah Didi kamannin nasu har ya ƙazanta kamanninsa da Ibraahim is too hight har Abualeey da kansa abin ya jijjigasa kin kuwa ga Fada? yana shiga fa sai da kowa ya tashi tsaye”.
Didi kam kallonsa kawai take bako ƙyaftawa shi kuwa Dr Jameel cigaba da cewa.
“Kinga Jabeer bin Jabeer shima sosai yayi mamaki saboda naji yana cewa wai sun haɗu dashi ajirgi, dan sai cewa Abeey yake, Abeey ka ganshi ko babu abinda ya raba shi da Ibraahim kamannin yayi yawa, nacema zan faɗawa Didi kace kar in faɗa mata hankalinta zai tashi, gashi yanzu yazo har inda take Abeey wlh jininmu ne. Haka yake ta faɗa yana can yana ruɗe”.
Cikin sauri da yanayin zabura Didi ta miƙe tare da kallon Jakadiyarta da kanta ke ƙasa kana tace.
“Jakadiya maza je ki duba idan Mai Martaba na nan. Kice Ina son ganinsa cikin gaggawa. In kuwa yanada uzuri a fada, ina fatan ayi min iso”.
Cike da girmamawa Jakadiya ta gyaɗa mata kai kana ta furta.
“Toh”.
Sai kuma ta juya cikin sauri ta juya ta fita Ahankali ta riƙa ratsa tamfatsa-tamfatsan falon har ta isa bakin ƙofar fadan wayam ba kowa alamar duk an watse.
Cikin Sassarfa ta juya ta koma falon domin sanar mata...
Acan ɓangaren Moddibo kuwa jin ana ƙwala kiran sallar Maghriba yasanshi motsa laɓɓansa yashiga bin kiran Sallar kana yayi addu'ar da Manzon Allah (S.A.W)ya koyar sai kuma ya furta.
“Ya Salam, shin Mutanen nan me suke nufi dani, suna nufin ba zanyi Sallah acikin jam'i ba?”.
Ahankali ya juya idanunsa akan wannan Corridor dake gefen damansa cikin nutsuwa yabi hanyar yayi tafiya mai ɗan tsayi ya hango wasu ƙofofi guda biyu gefen hagu da dama ahankali ya murɗa ƙofar dake gefen dama.
“Ya Salam”.
Ya furta asaman laɓɓansa ganin wani tsarerren falo ahankali ya taka ya shiga ciki.
Sai kuma ya ɗan jujjuya kai, ƙofar dake kusa dashi ya nufa.
Wanda bedroom ne a hankali ya murɗa ya shiga.
Ƙofar bathroom ya sake murɗa yashiga, alwala kana ya fitowa.
Jujjuya ya kai yayi cikin sa'a yaga darduma a shimfiɗe a wata ƴar kusurwa awajen alamar ana sallah awajen anutse yayi sallar Maghriba awajen kana ya cigaba da addu'oi har aka kira Isha'i, bayan ya idar ya fito falon farko da aka fara ajiyesa.
Yana isa Idanunsa suka sauƙa akan dining da aka jera abinci kala-kala sai kuma ya juya kanshi hanyar shigowa nan yaga wasu hadimai guda uku maza suna tsaye.
Ganinsa yasa sukayi saurin sunkuyar da kansu ƙasa kana suka ɗaura hannunsu aƙirji alamar Barka da fitowa.
Cike da girmamawa ɗaya daga cikin su yace.
“Ranka ya daɗe ga abinci”.
Numfashi ya fesar kana ya tsira musu ido na second biyu tare da cewa.
“Shin meyesa aka tsareni anan?”.
Cike da ladabi da kuma Mutuntawa suke sake sunkuyar da kansu ɗaya daga cikinsu yace.
“Kayi haƙuri Ranka ya daɗe Umarni ne daga mai martaba yace kada mu bari a buɗe maka ƙofa dukkan abinda kake buƙata akwai shi anan basai ka fita ba”.
Cike da mmki ya kallesa kana ya lumshe idanunsa tare da fesar da iska mai zafi yace.
“Akan me za'a rufeni a hanani fita bayan ina da abubuwanyi”.
Cike da ladabi Hadimin ya sake sunkuyar da kansa wanda da alama shine babban su kana yace.
“Kayi haƙuri In Sha Allah Mai martaba yana nan zai zo wajenka”.
Batare daya sake furta komai ba ya koma ya zauna akan kujeran.
Allah ya sani shi yama rasa shin wani irin tunani zaiyi abu ɗaya dai yana jin wata nitsuwa ta musamman a jikinshi da zuciyarsa.
Anutse Hadimin ya sake biyo sa tare da cewa.
“Bismillah ka matso ga abinci”.
Kai ya girgiza duk da kuwa yunwa da yake ji amma yanayin da yake ciki bazai iya bari yaci abinci ba.
Ganin haka yasa ɗaya daga cikin hadiman ya nufi jikin Frigde kana ya kawo masa Fruits tare da ajiyewa akan stool agabansa.
Sanyayyar iska ya fesar daga bakinsa kasancewar sa mai son ƴaƴan itatuwa yasa ya miƙa hannu ya ɗauki apple ya ɗan fara ci ahankali...
Yayin da hadiman suka koma baya suka ci-gaba da tsayuwar anutse ya ɗago manyan idanunsa dake lumshe ya kallesu kana yace.
“Ku zauna mana”.
Murmushi sukayi tare da faɗin.
“A'a yallaɓai babu matsala kada ka damu wannan ai aikin mune”.
Da mamaki yake kallonsu kana yashiga tunanin wannan al'amarin ya yake.
Yana zaune yaga wani Hadimin ya turo ƙofa ya shigo yayin da wasu hadimai uku mata ke biye dashi hannunsu riƙe da manya-manyan Trolley suna shiga suka gaishesa cike da girmamawa kana suka nufi bedroom ɗin suka buɗe Weldrop suka shirya masa kayan kana suka fito Hadimai matan suka tafi suka bar namijin.
Shi kuwa namijin cike da ladabi ya durƙusa gabansa tare da faɗin.
“Mai martaba yace ayi maka sannu da zuwa, sannan yace afaɗa maka ka kwantar da hankalin ka ka shiga kayi wanka ga kaya an kawo maka ka huta zuwa anjima zai zo kugana”.
Tunda ya fara magana Moddibo ke kallonsa jin ya dasa aya yasa shi faɗin.
“Ina buƙatar wayoyina suna cikin mota akawo min ko kuma suzo muyi duk maganar da zamuyi zan tafi ina da abubuwan yi”.
Cike da girmamawa Hadimin ya furta.
“Kayi haƙuri In Sha Allah zan isar masa da saƙonka”.
Kana ya miƙe ya fita...
Acan cikin gida Side ɗin mai Martaba kuwa Didi ce ke tafiya cikin sasarfa yayin da hadimai biyu ke biye da ita hannu ta sanya ta buɗe ƙofar falon yayin dasu kuma suka tsaya daga gefe.
Cikin Sassarfa ta ƙarasa shiga cikin falon Idanunta suka sauƙa akan Mahaifinta Sheikh Jabeer, Mijinta Sarki Youssef Muhammad Mouley, Waziri, Jakadiyar Sarki, Galadima cikin sauri da girmamawa Jakadiyar Sarki ta miƙa mata hannu alamar tazo ta zauna
Kai ta gyaɗa kana ta zauna tare da kallon Mahaifinta wato Sheiykh Jabeer cikin sanyi da yanayin damuwa ta furta.
“Abiey meke faruwa? Me nakeji? Kufahimtar dani na kasa fahimtar abinda Dr Jameel da Hakim ke faɗa min shin gaskiya ne”.
Cikin sauri Jabeer bin Jabeer ya matsa kusa da ita tare da riƙe hannunta cikin ƙauna da shaƙuwa ta Yah da ƙani yace.
“Didi ina ji ajikina ɗankine kuma tsatsonkine, ina ji ajikina wannan mutumin dana gani ɗankine wallahi domin babu abinda ya raba shi da Ibraahim kamanninsa da Ibraahim da kuma Mahaifinsa har ya ƙazanta.
Didi dai-dai da faratunsa irin na ƴaƴan kine”...
Aƙage ta matse hannunsa dake cikin nata kana idanunta cike da ruwan hawaye tace.
“Toh waye shi? A ina yake? kununa min shi?, dan Allah kuyi gaggawan kaini garesa domin idanuwa sun ƙagu suyi tozali dashi haka zalika kunnuwana su ƙagu suji sautin Muryansa”.
Gyaran murya da Sheiykh Jabeer yayi yasa ta dawo cikin nutsuwarta cike da kamala da tarin nutsuwa ya furta.
“Fatima ki nutsu mana, ai komai yazo da sauƙi Bi'iznillahi ta'ala ɗan da muka rasa tsawon shekaru, in Sha Allahu yazo garemu nima kaina na gamsu wannan ɗankine tsatsonkine”.
Numfashi mai martaba ya fesar tare da muskutawa kana ya furta.
“Nima inaji ajika babu haufi babu shakka ko tsoro wannan ɗana ne jini nane Abeey yaron nan Aliyu nane babu haufi jikina da jinina da zuciyata sun shaida min”.
Sai kuma ya maida kallonsa kan Sheykh Jabeer kana yace.
“Tabbas wannan al'amari ya girmama sai dai kuma yanzu saboda idon Fada da kuma yadda al'amarin yaja hankalin mutane yana buƙatar sirri”.
Kai Jabeer bin Jabeer ya jinjina tare da sake tuno kamannin Moddibo da kuma Ibraahim Sarki Youseep Muhammad Mouleey kuwa numfashi ya fesar kana ya cigaba da faɗin.
“Ga kuma yanda ya shigo ya iya sarrafa *Rinƙas* yaja hankalin mutane gaba ɗaya sannan kuma muna buƙatar tabbatarwa da shi kan al'adun masarautar da sanar dashi dukkan abinda ya dace, dan haka sai zuwa tsakiyar dare yanda hankalin mutane duk ya kau zamu shiga wajensa dan bincike da tabbatar wa”.
Kai suka jinjina cike da gamsuwa da kalamansa sai kuma ya maida idanunsa kan Sheykh Jabeer tare da faɗin.
“Abeey Wallahi wannan yaron ɗanane babu ma wani batun tabbarwa inaji ajikina ɗanane tsatsonane ɗanane da muka rasa tsawon lokaci”.
Cikin fesar da numfashi Sheikh Jabeer yace.
“Ka kwantar hankalinka Youseep na sani amma akwai buƙatar bincike akwai buƙatar mu san wani abu”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Toh shikenan”. Kasancewar Sheykh Jabeer abokin Mahaifinsa Muhammad Mouley ne yasa baya iya yi masa musu.
Galadima da tunda aka fara magana bai ce komai ba, sai yanzu ya fesar da numfashi kana yace.
“Tabbas nima inaji ajikina wannan tsatson mune saboda inba haka ba bai isa ya sarrafa *Rinƙas* ba sannan kamannin nan yayi yawa kana ku kalli yanda yake bin taswiran gidan nan tamkar yasan wuraren, wannan yasa nakeda tabbacin da wuya ace akwai wani abinda bai saniba na al'adunmu sai dai abin tambayar shin taya hakan yakasance”.
Kai suka jinjina cike da gamsuwa kana suka cigaba da tattauna maganar daga haka suka tashi daga taron.
Yayin da Didi kam daren wannan ranan haka ta suku-ku baki ɗaya zuciyarta da nutsuwarta ya tafi izuwa ga ɗouki da kuma mararin son ganin yaron da akece yana tsananin kama da Ibrahim ɗin ta koda kuwa abincine ta kasa ci.
Acan ɓangaren Moddibo kuwa yana zaune a inda yake batare daya motsa ba bare kuma yaci abinci baki ɗaya abin duniya ya ishesa abubuwa goma da ashirin sun haɗe masa, tarin tambayoyin a kansa sama da dozin wanda innayi kaɗai yakeson ji da ganin yayi mata su, ahaka ya cigaba da zama kafin daga bisani wata zuciyar ta yanke shawarar ya tashi koda zai iya samun wata ƙofa ta baya da zai fice.
Ahankali ya miƙe tare da kallon gefen daman sa inda ya shiga yayi alwala kana ya kalli falon daga gefe ya hango wata ƙofa ahankali ya fita idanunsa suka sauƙa akan wani falo na daban shima still yana ɗauke da ƙofa hagu da dama murɗa ƙofar yayi ya fita anan yaga wani ƙofa hagu da dama sai kuma wani step daga tsakiyarsu daga can sama shima kofa ce hagu da dama...
Hadimansa kuwa ganin ya fita yasa suka shiga taka masa baya tunda basu da ikon hanasa cikin tsuke fuska ya kallesu, su kuwa cike da girmamawa ɗayansu yace.
“Ranka ya daɗe ko akwai abinda kake buƙata?”.
Girgiza kai kana yace.
“Um-um babu abinda nake buƙata”.
Kai suka gyaɗa tare da faɗin.
“Toh”.
Tunda basu da ikon hanashi tafiya.
Cike da a nitsuwa yake tafiya har ya haura step ɗin yanda ƙasan yake haka zalika saman yake komai na ginin iri ɗaya ne sai dai tsarin Furnitures ɗin ne suka banbanta.
Kasancewar suna saman daga gefen dama komai White & Sky blue kalar Sararin samaniya sai kuma daga can gefen Hagu komai na cikinsa ya kasance Jane da ratsin fari haka nan yakeji kamar anayi ma shi jagorane.
Cikin fesar da numfashi ya koma kan step ɗin ya tsaya a Balcony yana mai cigaba da kallon tsananin kyau da tsaruwan wajen tun da yake a iya tsawon rayuwarsa bai taɓa kallon falo mai masifar girma da kyau irin wannan ba.
Ahankali ya ɗaga idanunsa sama anan ya hango ainihin tsakiyar Fadan.
Babbar Fadace mai masifar kyau da girma akwai wurare daban-daban yayin da Part-part sunfi aƙirga iya inda idanunsa ke iya hangowa Part-part ne ashimfiɗe sai kuma hadimai da yake hangowa suna zirga-zirga wanda bazai iya ƙiyasta yawansu ba, ga wani irin wuta mai haske da ƙyalli daya haske ko ina na cikin fadar tamkar rana kana ga bishiyoyin dabino da mijin gwanda wanda duk ta inda ka cilla ido suke rausayawa sai zurga-zurga Hadimai keyi.
Ahankali ya juya bayansa daga gefe nan idanunsa suka hango wani garden Mai azabebben kyau daga can bayan Garden ɗin kuwa wani Swimming pool ne dake ɗauke da ruwa Sky blue ga wasu fararen kujeru kaman resting Chair dake gewaye da wajen kana daga ƙasa su kuwa Grass Carpet ne da yayi dark blue Mai azabar kyau yayin da wasu irin tsuntsaye masu kyan gani da daɗin sautin murya ke shawagi awajen wanda da alama saboda ƙayatarwa aka ajiye su...
Ya ɗauki tsawon lokaci yana kallon wajen haka nan ya tsinci kansa da son ganin wajen domin kallon wajen yatuno masa da Gembilan sak yanayin tsarin gidansu haka wajen yake sai dai tsarin wannan ba suda yalwan Furanni haka kawai aransa yaji da ace za'a bashi dama zai ƙawata Ilahirin Fadar da Furanni saboda arayuwar duniya babu abinda ke sashi farin ciki kamar yai ta kallon Furanni har misalin 11:30 yana tsaye awajen kafin ahankali ya motsa ƙafafunsa jin sun gaji da tsayuwa kana ya gangaro ya dawo cikin ainihin falon da aka kawo sa...
Yana shiga falon ya zauna akan kujera tare da lumshe manyan idanunsa dake lumshe yana mai sakin ajiyar zuciya akai-akai.
Zaman sa babu daɗe wa kamar misalin 12:00 yaji ƙaran ƙofa an buɗe.
Jin ƙaran buɗe ƙofa yasa ya buɗe Idanunsa dake lumshe kana yabi wajen da kallo...
Da mamaki yake kallon Jabeer bin Jabeer da suka haɗu ajirgi kasancewar shine agaba.
Jabeer bin Jabeer kuwa cikin ƙaguwa ya maida idanunsa kan Didi da Lalla Khadijah da Hafsat ke gefenta, tare da cewa.
“Didi shigo kiganifa, Didi dan Allah ki ganshi da kyau fa”.
Sheikh Jabeer, Sarki Youseep Muhammad Mouleey, Waziri Galadima, Sarkin Dawakai, Jakadiya, Mahaifiyar Sarki Niyna Lalla Khadijah da Lalla Hafsat sai kuma Rahama dake can biya tana biyosu da sassarfa tare da faɗin.
“Didi ku jirani mana”.
Su kuwa cikin nutsuwa suka shiga cikin falon.
Suna shiga Moddibo ya zuba musu ido cike da mamaki yake bin Didi da Abualeey da wani irin amintaccen kallo yana mai jin wani irin yanayi na ratsa mishi zuciya a kansu haka nan ya gaza janye idanushi a kansu sai bugun da zuciyarsa keyi.
Lalla Khadijah da Hafsat kuwa ruggumeshi sukayi tare da sakin wani sassayyan kuka, wannan na gefen dama wannan na gefen hagu,
Rahama kuma na isa, sai kawai ta kifen kanta bisa guiwowinsa tare da faɗin.
“Yah Aleey laisa leeh misluka abadan, ana uhubbuki hubban azeeman”.
wani irin amintaccen nitsuwa ne yaji yana ratsashi, wanda yasa baisan lokacin da yasa tafukan hannunsa yana sharewa Lalla Khadijah da Hafsat hawayeba.
Su kuwa Khadijah da Hafsat sai kuma suka ɗan janye jikinsu tare da ruggume juna cike da tsananin farin cikin.
Ita kuwa Rahama cikin yanayin shogwaɓar ƴan auta take ɗan kuka tare da cewa.
“Yah Ibraahim ina kake kazo kaga Yah Aleey na ya fika kyau daga yauma niba ruwana da kai”.
Dan fesar da numfashi Modibbo yayi tare da sa hannushi yana ɗan shafa bayan Rahama alamun tayi shiru.
Sarki Youseep Mouleey kuwa cikin kamala ya zauna bisa kujera kana Sheikh Jabeer ma ya zauna gefensa yayin da Galadima, Waziri, Sarkin Dawakai, suka zauna a ƙasa.
Amintattun Hadiman dake biye dasu kuwa daga can baya dasu suka zauna.
Jakadiya kuwa idanunta akan Moddibo ta saki yalwataccen murmushi mai cike da zallan farin ciki kana tace.
“Masha Allah nesa ta matso kusa abin nema ya samu”.
Moddibo kuwa idanu ya zuba musu baya ko ƙyaftawa ganin Jabeer bin Jabeer ya zauna aƙasa gasu Galadima sai shima ya zamo daga kan kushin ɗin ya zauna akan Carpet tare dasa hannunsa yana sharewa rahama hawaye.
Yayin da yake kallon Sheikh Jabeer cike da mamaki kasancewar ya masa farin sani domin yasha zuwa wajensa a Adamawa sai dai baya samun haɗuwa dashi cikin tsananin mamaki ya motsa laɓɓansa tare da faɗin.
“Sheikh Jabeer”.
Sheikh Jabeer na kallonsa tare da mamakin kiran sunan sa ya furta.
“Na'am. Ka Sanni ne?”.
Ware idanu Moddibo yayi kana ya jinjina masa kai cikin sanyi Murya da yanayin nutsuwarsa yace.
“Farin sani ma kuwa shekaran Kur'anin dana rubuta na farko kusan uku awajenka wanda na rubuta daga baya kuma yayi cika shekara ɗaya awajenka amma har yanzu ban samu an dubasuba.
Batare da Sheikh Jabeer ya janye idanunsa daga kansa ba yace.
“Menene sunan ka”.
Moddibo kuwa ahankali yace.
“Sunana Moddibo daga Taraba nake tura maka wanda aminina Jameel Bashir Mai Dala yake kai maka”.
Baki ɗaya falon ya sake yin shiru baka jin muryan kowa sai na Moddibo da Sheikh Jabeer yayin da Didi da Sarki Youseep Mouleey kuwa jikinsu ke wani irin tsuma aduk lokacin da Muryan