Author : Aisha Aliyu Garkuwa Category : Free Novels Online (Read & Download)
rakata”.
Miƙewa Dije tayi sannan suka fita bayan Asma'u ta yiwa Mommy da Hajja Nana sallama har bakin hanya suka rakata saida ta samu adaidaita ta hau sannan suka koma.
Asma'u na isa gidan direct Sashen Innayi ta nufa zaune ta hango Innayi kan barandar ta tayi tagumi da hannunta na dama jin anɓude ƙofa yasa tayi saurin ɗaga kanta ganin Asma'u yasa ta saki Ajiyar zuciya.
Cikin sanyi Asma'u ta ƙarasa tare da zama agefenta cikin sanyin murya tace.
“Innayi”.
Numfashi Innayi ta fesar tare da tsira mata ido cikin alamun damuwa tace.
“Na'am Asma'u kin zo ya jikin Umminki!?”.
Kanta aƙasa tace.
“Innayi da sauƙi Ina Yah Moddibo fa?”.
Ajiyar zuciya me nauyi Innayi taja kafin ta sauƙe cike da damuwa tace.
“Asma'u bansan wani irin yanayi Moddibo yake ƙoƙarin shiga ba baki ɗaya ya zama wani iri ya dawo tamkar mara lafiya ya zama abin tausayi koda fitowa bayayi”.
Sai kuma ta runtse Idanunta cike da damuwa kana ta buɗe su tare da cewa.
“Ko abinci idan bana nuna masa ɓacin raina ba baya ci banda ruwan tea Babu abinda yake sha baki ɗaya ya sauya duk hankalina ya tashi na rasa yanda zanyi.
Gaba daya ƙasar nan tafi raina duniyar ta isheni”.
Sunkuyar da kai Asma'u tayi tana jin hawaye na cika kwarmin Idanunta.
Cikin raunin murya Innayi ta kalli Asma'u tare da cewa.
“Na rasa yanda zanyi da Moddibo ɗazun nan ma Abban Jameel ya fita dalilin zuwansa da yayi masa.
Nasiyya da kwantar masa da hankali shine ma muka samu ɗazun yasha kunu”.
Numfashi mai zafi Asma'u ta fesar tare da kallon Innayi tace.
“Ummi ma tace tana som ganinsa baki ɗaya ta damu da rashin zuwansa kuma koda ta kira wayarsa baya shiga bare taji muryarsa, Innayi barin shiga wajensa”.
Kai Innayi ta gyaɗa kana tace.
“Shikenan ba matsala muje”.
Miƙewa Asma'u tayi tare da nufar Sashen sa Innayi na biye da ita.
Innayin ce ta tura ƙofar falon suka shiga ahankali Idanun Asma'u suka sauƙa akan Moddibo dake zaune kan 1sitter Ƙirjinsa Rungume da Alkur'ani yayinda idanunsa ke lumshe suna tsiyayar da hawaye kana dashash-shiyar muryarsa na rera karatun Alkur'ani.
Cikin mutuwar jiki Asma'u ta zauna daga gefen ƙafafunsa Innayi kuma ta zauna daga saman kujeran.
Ganin yanda hawaye ke fita Shar-shar-shar a idanunsa yasa Asma'u fashewa da kuka mai gunji hadda sheshsheƙa.
Jin sheshsheƙan Kukan Asma'u yasa Moddibo da idanunsa ke lumshe saurin buɗewa ganin yanda Asma'u ke kuka da sheshsheƙa yasa yayi saurin sanya tafin hannunsa yashiga goge hawayen dake saman kuncinsa.
Cikin sanyi Innayi ta kallesa tare da cewa.
“Moddibo!, Moddibo!!, Moddibo!!!”.
Ahankali ya ɗago kumburarrun Idanun sa da suka jiƙe da hawaye kana Eyelashes ɗinsa sun kwanta cikin sanyi ya kalleta.
Innayi kuwa cikin tsaresa da Ido tace.
“Moddibo za kayi fushi da hukuncin Ubangiji ne?”.
Cikin sauri ya girgiza mata kai tare da cewa.
“Astagafirullah³”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta tsira masa Ido tace.
“Toh Meyesa Moddibo baka fita, baka cin abinci sannan baka walwala, kenan fushi kake da Ubangijin daya bamu Jameelu sannan ya ɗaukesa!?”.
Kai ya girgiza mata batare da yace Uffan ba!.
Cikin sanyi da rauni Innayi ta zuba masa Ido baki ɗaya Garin Jahar Taraba da maƙasar Nigeria yafi ta ranta, fesar da numfashi kana tace.
“Toh Meyesa sai dai ka ɗauki Kur'ani ka rungume kana karatu kana kuka”.
Cikin wata dashash-shiyar murya me cike da rauni da tashin hankali yace.
“Innayi mai zan fita nayi acikin garin Gembulan? Innayi da waye zan fita? Innayi baki ɗaya garin nan ya fita raina bana son garin nan na tsani garin nan garin nan ya fita min araina”.
Sai kuma ya runtse Idanunsa da ƙarfi yayin da jijiyoyin kansa suka tashi ruɗu ruɗu dasu kana zuciyarsa ta shiga bugawa da masifar ƙarfi cikin dauriya ya buɗe idanunsa da suka yi masifar Ja yace.
“Innayi duk inda na wulga acikin garin Gembulan zanga kamar J ɗina na akusa dani, shin Innayi taya zan fara fita da waye zanyi yawo da waye zanje masallaci da waye zanyi dariya da wa zan dawo gida da wa zan zauna inci abinci!?”.
Asma'u kuwa kife kanta jikin kushin ɗin da yake zaune tayi tare da fashewa da wani irin kuka tabbas sunyi rashin da baza su sake samun kwatankwacin saba sannan kuma anzalince su zalinci mai muni da raɗaɗi.
Jin yanda Asma'u ke kuka kamar ranta zai fita yasa Moddibo juyawa ya kalleta cikin sanyi da tausayinta yace.
“Asma'u ki daina kuka ki yiwa J addu'a domin shine abinda yake buƙata atare damu”.
Innayi kuwa kallonsa tayi har zuwa lokacin hawaye na zuba daga idanunsa ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Toh Moddibo kaima fa kukan kake ya za ayi Asma'u ba zatayi kuka ba”.
Kallon Innayi yayi tare da lumshe idanunsa wasu hawaye masu masifar zafi suka zubo masa.
Anutse ya goge tare da cewa.
“Innayi idan har bana samu na rungume Kur'ani ina karatu ba bana samun damar hawaye suna zubo min, sannan aduk lokacin da hawayena ke zuba inaji kamar ana zare min wani abu mai nauyi ne acikin ƙoƙon raina, shiyasa nake rufe kaina ni kaɗai nayi ta kuka”.
A tausashe ya kalli Innayi data tsaresa da ido ya cije Lip ɗinsa kana yace.
“Innayi idan har banyi kuka ba menene amfanin Idanuna da hawayena? idan ban zubar dasu arashin J ba J fa Innayi J ɗina”.
Numfashi Innayi ta fesar cikin sanyi tace.
“To ai addu'a zaka yi masa Moddibo”.
Cikin dashash-shiyar muryarsa daya dishe da kuka da tashin hankali yace.
“Innayi to ai ina masa addu'a”.
Asma'u kuwa ahankali ta ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kallesa cikin sanyi tace.
“Yah Moddibo Meyesa ka daina zuwa wajen Ummi?.
Baki ɗaya hankalinta ya tashi ta dawo kamar mara lafiya?”.
Girgiza kai yayi tare da kallonta kana cikin sanyi yace.
“Asma'u ki cewa Ummi tayi haƙuri insha Allah zan zo amma ina jin wanin irin yanayi ne taya zan kalli al'amarin tayaya zan iya zuwa wajen Ummi ba tare da J na kusa dani ba?”.
Numfashi mai zafi ya fesar da karfi kana yace.
“Baki ɗaya rayuwa tayi min ƙunci na rasa madafa, komai ya min duhu acikin duniyar nan na rasa yanda zanyi da kaina baki ɗaya na rasa yanda zan fuskanci al'amarin”.
Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe tare da fesar da nunfashi ta kallesa tare da faɗin.
“Ni dai Yah Moddibo mu tafi, idan har baka jeba Ummi na cikin tashin hankali da damuwar rashinka, koda magana da Ummi ba tayi idan ba mun matsa mata ba amma sai ta zauna shiru ita kadai afalo baki ɗaya gidan ya daina yi mana daɗi”.
Ahankali Moddibo ya taune Lip ɗinsa kana yace.
“Insha Allah zan zo ki cewa Ummi tayi haƙuri”.
Girgiza kai Asma'u tayi kana tace.
“A'a Yah Moddibo nidai gaskiya Ummi tace sai dai muje tare”.
Gyara zama Innayi tayi tare da fuskantar Moddibo cike da kulawa tace.
“Toh ka tashi kuje matuƙar kana son farin ciki da kwanciyar hankalin Ummin ka, kada ka haɗa mata ciwo biyu Moddibo kasan rashin ka awajen Ummi babban matsala ne”.
Cikin sauri Asma'u tace.
“Wallahi kuwa Yah Moddibo baki daya ƙuncin ya mana yawa, ba kai babu Yah Jameel. Baki ɗaya zuciyarmu acunkushe yake da damuwa amma ganinka zai ɗebe mana kewa”.
Cikin sanyi da rarrashi Innayi tace.
“Ka daure kaje ko hankalinsu zai kwanta kuma kaima za kaji sauki acikin ranka”.
Ta ida Maganar tare da miƙa masa key tsohuwar motar data fara saya mishi.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da karɓa kana ya miƙe cikin sanyi ya Murɗa handle din ƙofar
tare da fitowa wajen, cikin sauri ya lumshe idanunsa rabonsa da ganin haske irin haka ko kuma ya taka kofar falon yau tsawon kwana biyar kenan ko da sallah agida yake baya fita jam'i kai tsaye inda Motarsa yake ya nufa ya shiga sannan yaja suka tafi.
Innayi kuwa na ganin tafiyarsu ta kira Number Malam Arɗo bayan ya ɗaga tace.
“Dan Allah Malam Arɗo idan babu damuwa kazo ina da magana da kai”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Toh badamuwa Insha Allah zan zo”.
Modibbo kuwa suna isa memory sa ya shiga tariyo masa hoton fuskar J ɗin sa cikin sauri ya juya gefen damansa jin kamar sautin murya J ɗinsa cikin dariya yana cewa A.J tsayuwar me kakeyi Please kazo mu shiga inga Ummina kasan dai nayi missing dinta da yawa.
afili ya furta.
“J kai ko nima ainayi kewarta kuma dan na tsaya jiranka ne da tuni na taho”.
Murmushi yaga M Jameel ya sakar masa sannan ya janye hannunsa daga cikin nasa ya juya ya fara tafiya yana jujjuya masa hannu alamar Byebye.
Da sauri Moddibo ya juya tare da cewa.
“J ina kuma zaka je ba kace ka matsu kaga Ummi ba?”.
Cikin sauri Asma'u dake Kallonsa ta tashare hawayen dake kwaranya a Idanunta kana tace.
“Yah Moddibo Yah Jameel fa baya nan sannan bazai taɓa zuwa inda muke ba”.
Moddibo kuwa ido ya tsirawa Asma'u kamar mai son fahimtar abinda take faɗa sai kuma yayi saurin dafe kansa tare da maimaita Kalmar Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n shi kansa yasan zuwa zuwa yanzu dai kamar zautacce yake.
Numfashin ya fesar sannan ya nufi falon bakinsa ɗauke da Sallama Asma'u na biye dashi.
Ahankali idanunsa suka sauƙa akan Ummi dake zaune kan 3sitter ta daura guiwar hannunta duka biyu akan cinyarta tayi tagumi tare ta tsirawa waje ɗaya Ido baki ɗaya ta rame fuskarta yayi fayau.
Cikin sauri Moddibo ya ƙarasa shiga falon tare da zama agefenta kana ya janye tagumin da tayi ya maida hannunta kan gwiwoyinta.
Ummi kuwa cikin sauri ta sunkuyar da kanta nan take hawaye suka fara zuba Shar-shar-shar cikin sanyin murya ya kalleta kana yace.
“Ummi dan Allah kiyafemin. Insha Allahu bazan sake nesa dake ba, kinji Ummina ki daina zubar da hawayenki, dan baza mu iya juran. Kallon hawayen ki na zuba ba”.
Kallonsa Ummi tayi cikin wata raunan'niyar murya tace.
“Babana idan har baka zuwa wajena ya zanyi?Kana so ka haɗa min zafi biyu alokaci ɗaya ne?
Babu Jameeluna sannan kaima baka kusa dani mekake tunanin zanji arayuwata, kana so inshiga wani hali ne?”.
Cikin sauri ya girgiza mata kai kana muryarsa na rawa yace.
“Insha Allahu bazan sake nesa da keba, zan kasance atare daku tamkar yanda J ke kasancewa atare daku, zan sanya ku farin ciki tamkar yanda J ɗina ke saku insha Allah zan kiyaye”.
Ya kalli Ummi da har zuwa lokacin hawaye ke zuba a Idanunta ya ɗaura tafin hannunsa akan nata cikin rawan murya yace.
“Insha Allah zan zame muku farin ciki kuma Garkuwa kamar yanda J ɗina ya kasance agareku Ummi. Asma'u Bashir Insha Allah bazan bari hawayenku ya zuba ba tamkar yanda J ɗina baya bari su zubo ba nayi al'ƙawarin zan zame muku farin ciki zan maye muku gurbin J ɗina”.
Ya ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka kasa rarrashin sa Ummi tayi kawai itama hawaye ya cigaba da zuba daga idanunta haka Asma'u da Bashir suka riƙa kuka harda sheshsheƙa baki daya Moddibo baya jin zai iya hana kansa kuka bare kuma ya samu kuzarin rarrashinsu hakan yasa aka rasa wanda zai rarrashi wani acikinsu.
Malam Ahmad da dawowansa kenan ya zuba musu ido cike da tausayinsu ganin yanda suke kukan kasan daga ainihin zuciyarsu yake fitowa.
Cikin sanyi malam Ahmad ya zauna gefen Ummi ya zamana yana fuskantar Moddibo, Asma'u da Bashir dake ƙasa cike da tausayawa da kuma rinƙa rarrashisu da basu baki.
Ahankali Ummi ta maida bayanta da jikin kushin ɗin ta jingina hawaye na cigaba da zubo mata Moddibo kuwa kasa yayi da kansa yana jin wani irin yanayi azuciyarsa shikenan J ya tafi ya barsa bari na har abada.
Kallonsu Malam Ahmad yayi kana ya cigaba da cewa.
“Insha Allahu da yardan Ubangiji Jameelu yana cikin rahama, salama nutsuwa da kwanciyar hankali domin Jameelu ya kasance bawa mai tsananin Biyayya ga dokokin ubangiji sannan Jameelu yaro ne me biyayya ga Iyayensa akullum burinsa yaga ya sanya Iyayensa da shalinsa acikin farin ciki”.
Jinjina kai sukayi Atare cike da gamsuwa da maganarsa tabbas ta ko wanni fanni Jameel bashi da makusa.
Ajiyar zuciya Malam Ahmad ya sauƙe kana yace.
“Jameel ya kasance mutum mai tsananin tausayi da temakon al'umma Jameel baya taɓa kallon mutum acikin halin neman temako sannan ya wuce batare daya temakesa ba, duk wanda yasan Jameel da addu'a yake binsa na Ubangiji ya jiƙansa dama mutane masu Kirki da karamci Ubangiji bai fiye barinsu tagayyaraba sam Jameelu bai cancanci kuka agare kuba, addu'a ya cancanci ku masa domin da izinin Ubangiji yana can cikin rahmar Allah da yardan sa”.
Kai Bashir ya gyaɗa tare da share hawayen saman fuskarsa kana cikin sauri yace.
“Hakane ma Abba abinda kake faɗa yanzu shine abinda.
Yah Jameel ya faɗa min acikin Mafarkina jiya da daddare yace. in faɗawa Ummi ta daina yi masa kuka domin duniyar da yake ayanzu tafi wannan duniyar da muke ciki daɗi, nutsuwa, salama, da kuma aminci”.
Cikin sharce hawaye ya gyara zamansa tare da fuskantar Ummi kana yace.
“Sannan yace bayason wannan kukan da Ummi ke masa, shikam addu'a yake buƙata duk wannan koke koken bayaso adaina yi masa.”
Kallonsa ya mayar kan Moddibo tare da cewa.
“Sannan kaima Yah Moddibo acikin mafarkin da nayi da Yah Jameel yace in Faɗa maka ka cigaba da yimasa addu'a sannan kayi ƙoƙari ka cika masa wasiyyar da yayi maka ta gefen Innayi ya jadda min kuma ka taya Abbansa kula da lamuran kasuwancinsa”.
Saurin ɗago kai Moddibo yayi tare da cewa.
“Ummi wani wasiyya kuma J ɗina ya bari akaina??”.
Girgiza kai Ummi tayi tare da fashewa da matsanancin kuka batare da tace Uffan ba.
Ajiyar zuciya Malam Ahmad ya sauƙe tare da kallon Ummi dake sheshsheƙa kana yace.
“Fatima yanzu kuka za kiyiwa Jameelu? shin kinsan Rahman da Ubangiji ya tanadar wa da duk wa'anda aka zalunta da rabasu da rayuwarsu?
Kada fa ki manta Ubangiji ya tana dar da rahma wa duk rayukan da aka kashe batare da hakkinsa ba”.
Ahankali Ummi ta ɗago kanta kana ta sanya tafin hannunta ta share hawayen ta Numfashi malam Ahmad ya fesar kana yace.
“ki tuna ni'imomin da Allah yayiwa muminai tanadin su.”
Lokaci ɗaya Ummi ta saki murmushi wanda tun bayan sace M Jameel ba tayi irinsa ba wani irin nutsuwa da salama taji yashigeta lokaci ɗaya tabbas tana ji ajikinta Jameelun ta na cikin rahmar Ubangiji.
Moddibo ma murmushi yayi wanda ya fito daga ainihin zuciyarsa in sha Allah J dinsa yana cikin kwanciyar hankali da salama da izinin Ubangiji addu'a kawai J dinsa ke buƙata atare dashi Insha Allah kuwa zai cigaba da masa hakan yasa suka cigaba da hirar rahmar da M Jameel zai kasance da izinin Ubangiji cikin sakin fuska suka cigaba da hira.
Acan gidan Lamiɗo kuwa ƙarfe biyar dai-dai Hajja Nana ta mike tare da kallon Dije dake zaune gefen Khausar suna hira tace.
“Ke Dije tashi mu tafi”.
Kai Dije ta gyaɗa tare da miƙewa cike da girmamawa Mommy ta haɗa mata tsaraba sannan ta bawa Khausar ta riƙe suka fito.
Suna fita coumpund ɗin Hajja Nana ta kalli Khausar tare da cewa.
“Insha Allah idan Baffa Jimeta yazo zamu zo tare”.
Ko uffan Khausar bata ce da ita ba haka zalika Mommy, bayan Khausar sun koma falon ta kalli Mommy cikin sanyin murya tace.
“Mommy yanzu dan Allah biye mata zakiyi?”.
Ahankali Mommy ta zauna tare da kallon Khausar cikin sanyi tace.
“Yanzu Khausar idan ban biye mataba wa kika tsayar? sannan tsohuwar nan tunda ta rantse akan dole sai anmiki aure tofa babu makawa, sannan babu yanda zanyi dole sai an Aurar dake ke dai kiyi fatan Allah ya miki zaɓin alkhairi, sannan ya baki mijin da zai barki ki cigaba da karatunki ki kuma cika burin ki”.
Wani abu mai masifar ɗaci Khausar ta haɗiye cikin raunin murya tace.
“Mommy nifa Banason sa”.
Kallonta Mommy tayi kana cikin tsareta da ido tace.
“To idan bakya sonsa wakike dashi ko kuma wa kika tsayar babu wani saurayi dake zuwa wajenki Naseer da ake maganar sa yanzu ya fita sabgarki kuma hakama yafi min.
Ni yanzu abinda na fahimta ma kamar soyayya suke da Amina”.
Khausar kuwa kallon Mommy tayi tare da tura baki kana tace.
“Eh Mommy soyayya suke to amma.
Ni me ruwana dasu ni dai bazan Auri Yah Aliyu ba Naseer kuwa bana sauraron maganarsa bare insa shi araina”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da gyara zaman ta cikin sanyin murya tace.
“Toh Allah ya mana zaɓin alkhairi”.
ta faɗa tare da miƙewa tashiga Bedroom ɗin ta Khausar kuwa jingina bayanta da jikin kushin tayi tare da lumshe Idanunta.
Da yammaci Misalin ƙarfe biyar da rabi Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce zaune agaban Boka Kar'uzu.
Cikin farin ciki Hajiya Lami ta gyara zamanta tare da kallon Boka Kar'uzu dake taune laɓɓansa na ƙasa duk yayi muni ba kyan gani cikin sassauta murya tace.
“Na gaishe ka Boka Kar'uzu Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu ina mai farin cikin sanar da kai shekaran jiya Alhj ya tafi Saudia kaga yanzu sai ka shirya ka koma gidana kaje kayi sati ba matsala”.
Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar'uzu ya fashe dashi wanda yasa ganyen bishiyar dake wajen suka soma zubowa yana mai ƙara wangale wawakeken bakinsa yace.
“Anjima da daddare zanzo, maza ku tashi ku tafi da ƙafar hagu yanzu zanyi manyan baƙi da kukar bulikiya Ɗan Jaƙunana mai ƙaho Atsakiyar kai da da jela zai ƙaraso”.
Ai cikin sauri suka miƙe suka fita daga wajen kamar yanda ya faɗa.
Acan gidan Innayi kuwa zaune suke da Malam Arɗo asaman baranda Moddibo.
Cikin nitsuwa Innayi ta kalli Malam Arɗo cikin sanyin murya tace.
“Toh kaji yanda mukayi dashi, yanzu abinda nake so idan Allah ya nufa zaka je kasamu Abban Jameelu kayi masa bayani idan yaso sai mu isar da manufarmu ga mahaifin yarinyar”.
Jinina kai Malam Arɗo yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.
“Insha Allahu idan Allah ya yarda zan shiga wannan maganar da iyakacin ƙarfina zan shigeta da izinin Ubangiji”.
Kai Innayi ta jinjina tare da cewa.
“Toh ba matsala Insha Allah Nagode matuka”.
Acan gidan Ummi kuwa bayan fitar Malam Ahmad Moddibo ya kalli Ummi cikin sanyin murya da damuwa yace.
“Ummi nayi al'ƙawari da izinin Ubangiji da yardan Allah sainayi duk yanda zanyi sai an gano waɗanda sukayi mana wannan cuta.
“Domin duniya tasan irin baƙin zunubin da suka aikata, sannan akamasu ayi musu hukunci dai-dai da zunubinsu, domin wasu su tsira agaba kada su sake cutar da wasu kamar yanda suka cutar damu, da zukatanmu da kuma ahalinmu”.
Numfashi Ummi ta fesar tare da sauƙe ajiyar zuciya kana tace.
“Hummmm?".
Cikin sauƙe numfashi Asma'u tace.
“Toh ammn ta ina zamu fara Yah Modibbo!?”.
Ahankali Ummi ta kalleta kana ta kalli Moddibo ta sauke ajiyar zuciya mai sanyi tace.
“Nima abinda nake tunani kenan, ta ina zaku fara wannan ba ƙaramin case bane dole yakasance mutum nada ƙwararan hujjoji