Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
ba.
"Ki koma cikin gida. Idan naganki a wajen nan saina zaneki..."
Wasu sabbin hawayen taji sun zubo mata, duk da basu hanata kin bin umarnin shi ba, tsaye yayi a wajen yana kallonta harta sha kwana, dan dafe kanshi yayi, yana jin ranshi na baci babu dalili, bangaren su ya nufa, ko sallama baiyi ba ya wuce su Yassar da suke cikin abinci
"Ko shi da wa kuma?"
Yazid ya tambaya, Yasir ya amsa shi da
"Indai bakin ran Abdulkadir ya motsa ko babu dalili yin shi yake..."
Dariya sukayi, sai gashi ya fito, karamin tsaki yaja, dan baiga abinda zai basu dariya ba, ranshi yana baci suna dariya
"Ku komai na dariya ne"
Ya fadi yana kara jan tsaki
"Kai da uban wa?"
Yassar ya tambaya, bai samu amsa ba, Abdulkadir din yazo ya wuce yana yin ciki da kafafuwan Yazid da yace
"Ikon Allah...bani na kar zomon ba"
Shima bai samu amsa ba, Abdulkadir din ya fice daga dakin, yana doko musu kofar kamar zai karyata. Haka kawai ya tsinci kanshi da nufar bangaren su Waheedah dan bai yarda cewar ta koma ba, hangota yayi tsaye bakin kofa tana kai hannu tana goge fuskarta
"Yarinyar nan bata da hankali"
Ya furta a hankali, kukan da takeyi ma zai saka mata wani ciwon kan, ga sauro daya gama moreta a wajen da ta zauna. Da alama bata ganshi ba, dan saida ya kure mata tukunna ta ruga da gudu tana shirin komawa cikin dakin, Abdulkadir ya damqo hannunta
"Hamma dan Allah..."
Waheedah ta fadi idanuwanta kamar zasu fado, ga wani lugude da zuciyarta take mata
"Me nace?"
Kai ta girgiza mishi, hawaye na silalowa daga idanuwanta
"Me nace miki?"
Ya tambaya a tsawace
"Kar in fito... Haka kace kar in fito..."
Idanuwa Abdulkadir ya tsura mata, baiyi niyyar dukanta ba, haka kawai yaji yana son ganin ta tsorata haka.
"Wallahi Hamma kafata daya na cikin daki... Dayace kawai a waje... Wallahi"
Waheedah ta fadi, baisan dariya ta kubce mishi ba saida yaji sautinta cikin kunnen shi. Zahra na da wauta, bayajin kuma a cikin gidan akwai wanda yakai Nabila rawar kai, amman Waheedah cikin sanyi take nata rashin hankalin, dariya yake daya kwana biyu baiyi ba, ita kanta Waheedah din kallon shi take da mamaki, bawai baya dariya bane, amman dariya irin haka da sauti ba zata tuna ranar karshe da taga hakan ya faru dashi ba. Dayan hannunta tasa tana share hawayenta, dan karamin murmushi na kwace mata.
Hannunta Abdulkadir yaja zuwa cikin dakin, ya zaunar da ita kan kujera, da murmushi a fuskarshi ya nufi kitchen din, ruwa ya dibo a cup yazo ya kawo mata, karba tayi tana mamakin yanda batasan tana jin kishi haka ba, ta kusan shanye ruwan, ta ajiye kofin hadi da sauke numfashi, mikewa tayi
"Ina zakije?"
Abdulkadir da yake tsaye ta tambaya, muryarta a dishe tace
"Fuskata zan wanke"
Kai ya daga mata, ta zagaya ta bayan kujerar ta wuce, dan gani take inta wuce ta gaban shi zaiji yanda zuciyarta take dokawa. Kofin ruwan ya dauke yana mayarwa kitchen ya fito ya koma kan hannun kujerar dake kusa da kofa ya zauna. Fitowa Waheedah tayi, yabi fuskarta da ta kara mishi ja saboda kukan da tayi, yana tunanin kartai ciwon ido da yanda yaga idanuwan sun kumbura. Wajen data tashi ta koma tana zama, wasa take da hannuwanta, ko zuciyarta zata rage gudun da take, lokaci zuwa lokaci takan dan dago ta saci kallon Abdulkadir din da yake zaune, kananun idanuwan shi na kafe a kanta, duk da alamun shi sun nuna yayi nisa a duniyar tunani.
Hakan ne a bangaren Abdulkadir din, in da zaka tabashi ka tambayeshi tunanin da yakeyi baisani ba, balle kuma azo dalilin daya sashi yake zaune a wajen, kukan da yaga tanayine ya dame shi, shisa ya dawo kota sake fitowa, yanzun din ma yana zaune ne karya tafi ta sake fita, yana kuma so yaga dawowar su Mami din ya duba jikin Amatullah, dalilan duka sun zauna mishi, dan baya tunanin akwai wani dalili baya hakan, numfashi yaja a hankali yana fitarwa, yana jinjina ikon Allah akan Waheedah din, yanda ta kubcewa fitowa a zabaya abin al'ajabine, hannuwanta da take wasa dasu ya tsayar da idanuwan shi akai, har faratan yatsunta farare ne.
'Wannan wanne irin haske ne?'
Ya tambayi kan shi yana sake sauke numfashin dayasa Waheedah kallon shi, duk cikin yayyen nasu shine basa hira dashi, bakama ga wannan fuskar ba, inba gaisuwa ba, saidai in shi da kanshi ya tambayeka abu zaka amsa, amman hira kam bayayi dasu, wani irin gudu taji zuciyarta ta kara, sautin na bugawa har cikin kunnuwanta, da labbanta da ta dagasu dakyar tana fadin
"Gobe In Allah ya kaimu zaka tafi ko?"
Da mamaki Abdulkadir din ya kalleta, yana dan daquna fuskar shi hadi da jinjina mata kai, wani abu Waheedah ta hadiye da takejin shi tsaye a makoshinta, batasan ya akai take son tambayar shi ba
"Hamma sai kayi shekara baka dawo ba ko?"
Kai ya sake jinjina mata, kamar bazaiyi magana ba kafin yace
"Menene? Ba murna kuke zan tafi ba"
Wannan karin ita ta girgiza mishi kai, tana kallo ya sake kankance mata idanuwan shi kafin yace
"Karya ne..."
Yana sakata yin karamin murmushi
"Ki ban ruwa in sha Waheedah..."
Abdulkadir ya fadi yana kara gyara zaman shi akan kujerar, mikewa Waheedah tayi tana zuwa kitchen ta dibo ruwan ta kawo mishi, karba yayi yana shanyewa tas ya mika mata kofin data mayar kitchen, ta kai mintina uku a ciki tsaye batare datasan tunanin me takeyi ba. Kafin ta fito tana komawa kan kujerar ta zauna, wannan karin tana kwantar da kanta a jikin hannun kujerar, agogon dake daure a hannun shi ya duba yana mamakin gudun da lokaci yayi dan har tara da rabi ta gota.
"Kinci abinci?"
Ya tsinci kanshi da tambayarta, dan yanda ta langabar dakai a jikin hannun kujerar yasa shi tunanin ko yunwa take ji, shi kanshi baici abincin ba. A hankali Waheeda ta daga mishi kai, gyara zaman shi ya kara yi kan hannun kujerar. Lumshe idanuwanta Waheedah tayi, batasan iya lokacin da suka dauka a haka ba, balle tasan bacci ya dauketa, cikin bacci taji muryar Abdulkadir din na fadin
"Ya jikin nata yanzun?"
A hankali ta bude idanuwanta tana kallon Mami, da sauri ta mike tana murza fuskarta
"Mami... Ina Amatullah din"
Kallon ta Mami tayi
"Suna asibitin ita da Hajja, bacci takeyi, da sauqi ma sosai, zasu dawo da safe in shaa Allah..."
Numfashi Waheedah ta sauke, Abdulkadir da yake tsaye ya kalli Mami yana fadin
"Me yasa baku tafi da ita ba?"
Ware idanuwa Mami tayi tana kallon Abdulkadir din
"Asibitin sai munyi gayya Abdulkadir?"
Dakuna fuska yayi
"Da kun tafi da ita ai, ta zauna tanata kuka a waje"
Kallon ta Mami tayi, tana sakata sadda kanta kasa, sai yanzun take jin kunya ta lullubeta
"Harabar motoci Mami, ga sauro a wajen...nikam da kun tafi da ita"
Ya sake maimaitawa, yana kokarin tausasa harshen shi saboda Mami ce, dan murmushi Mami tayi, tasan halin yaron sarai, ta kuma san kokari yake kar maganar da yake tayi kamar yana mata fada ne.
"Ai mun dawo yanzun"
Mami ta fasi da murmushi a fuskarta. Kai Abdulkadir ya jinjina mata
"Sai da safen ku. Allah ya kara sauqi"
Yai maganar yana ficewa daga dakin kafin yace komai, kamar hakan Waheedah take jira ta karaso tana kwantar da kanta a jikin Mami data tureta tana fadin
"Ke yanzun meye na kuka? Ke da zakiyi mata addu'a? Ke komai na kuka ne?"
Dariya Waheedah din tayi tana jin hankalinta ya kwanta, bin Mamin tayi suna hira, kafin tai mata sallama ta wuce dakin su. Sai taji dakin yai mata shiru, musamman data kwanta, da yanzun Amatullah din tana mata tsegumin juye-jujen da take inta yi bacci, dan da yawan lokutta tana cikin bacci zataji Amatullah ta dala mata duka, ta kwashe kafafuwanta data jibga mata ta warbar gefe tana fadin
"Adda Wahee ki kasheni saiki huta"
Dariya tayi ita kadai, mikewa tayi ta kashe wutar dakin, tana daukar yar karamar fitila mai batir ta maqala a cikin hular dake saman kanta, tukunna ta kwanta tana janyo littafin ta dan taci gaba da karantawa. Idanuwanta da taji har zafi suke mata yasata lanqwasa shafin data tsaya din, tayi addu'ar bacci tana rufe idanuwanta, soyayyar Asma'u da Jikamshi na mata tsaye, soyayyar tasu na sata tunani kala-kala, kafin bacci yayi awon gaba da ita cike da mafarkin su.
*
Bangarensu ya nufa ya shiga kitchen tunda girkin Hajja ne ranar, tuwon shinkafa ne tayi da miyar taushe data sha albasa mai lawashi sai kamshi take. Yanajin dadin girkin Anty da Mami, amman abincin Hajja daban yake jin shi, a wajen shi duk wani abinci da zaici bayan na Hajja zai biyo, baisan ko kaunar da ke tsakanin su bace ta rufe mishi ido. Anan kitchen din ya tsaya yana dora abincin kan kantar kitchen din, hannun shi ya dauraye jikin famfon dake gurbin wanke-wanke. A tsayen yaci abincin.
'Kaga zaka tafi wani gari da babu idanuwan mu akan ka, dan Allah ka rike addininka, karkai wasa da sallah, in har kana yinta cikin lokaci, kana kokarin yinta yanda ya kamata zata kare maka aikata abubuwan dabai kamata ba. Kuma ka rage zafin zuciya, dan Allah Abdulkadir ka dinga sakama ranka salama'
Nasihar da Abba yai mishi ta dawo mishi, kai yadan jinjina yana karasa cinye abincin ya wanke hannun shi ya fice daga dakin. Bangaren su ya koma, babu kowa a falon sai Yassar daya kalle shi cike da mamaki
"Daga ina kake haka kaikuma?"
Saida ya zauna tukunna ya daquna ma Yassar din fuska
"Hamma kana tsareni da tambaya kamar yaro"
Dariya Yassar yayi
"Nakai shekarun dazan fita in dawo sanda naga dama"
Dare yayi, dan sha daya harda rabi, gashi bayajin yana da karfin biyewa rashin kunyar Abdulkadir din da zuwa yanzun inda sabo ya kamata ace ya saba, in wani yaiwa a waje su Hajja yake jama zagi, mutane naganin bai samu wadatacciyar tarbiya ba. Abin nama Yassar takaici, mutane nabashi mamaki, yanda sukan dora laifin yara akan iyayensu batare da kwakwwarar shaidar cewa laifin na iyayen bane na ci mishi rai. A ganin shi burin kowanne iyaye dansu ya zamo nagartacce, ya zamo abinda zasuyi alfahari dashi.
Baice wasu lokuttan ba'a samun baraka daga bangaren iyayen ba, baice ba'a samun sakacin iyaye a kan tarbiyar yaransu ba, amman hakan baya nufin duk wani abu da yaro zaiyi saiya zamana laifin iyayen shine, kowanne dan Adam yana da zabi a rayuwa, cikin zabin harda fatali da tarbiyar da iyaye kan dora yaransu akai, a bangaren Abdulkadir din kusan zaice hakane, tun yana da karancin shekaru yake da wata irin zuciya, da ko laifi yayi in zaka kasheshi da duka bazai ko motsa ba ballantana yai tunanin gudu, ko wani yazo ya da nufin janye shi zai nuna bayaso.
Yana tuna lokuttan da Hajja ke dukan shi akan abubuwa da dama, kafin Abba yace tana binshi da addu'ar shiriya tunda dukan baya aiki, ga bakin shi bazai shiru ba, inka fadi daya saiya fadi goma, musamman in yana ganin akan gaskiyar shine, komin girmanka baka wuce Abdulkadir ya datsa maka maganar duk da tazo kan shi ba. Kallon shi Yassar yayi yana fadin
"Dan Allah ka kula da kanka, banda fada da mutane, banda rashin kunya..."
Murmushi Abdulkadir din yayi yana sa Yassar tashi daga kishingidar da yayi a jikin kujerar yana gyara zaman shi sosai
"Nasan fada dai sai kayi, dan Allah banda fadan da babu dalili"
Kankance mishi idanuwa Abdulkadir yayi
"Nasiha kake mun?"
Duka Yassar yakai mishi da yasa shi ture Yassar din yana fadin
"Cin zali babu kyau"
Hadi da mikewa dan kan shi yakeji ya mishi nauyi
"Idan nabar gidan saika nemi wanda zakaci zali"
Ya karasa maganar yana wucewa hadi da turo kofar dakin shi, murmushi Yassar din yayi yana komawa kan kujerar ya kwanta yana sauke numfashi. Addu'ar Allah ya tsare da ta neman saukin zafin rai yake nemawa Abdulkadir din, da damuwar yanda kanin nashi zai rayuwa shi kadai a wani gari batare da kulawar wani nashi a kusa ba...!!!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#FWA*
*#AnaTare*[©
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
07
Zaune take gaban mudubi badan zatai kwalliya ba, tunda ta fito daga wanka ta sakama jikinta riga da wando na Pakistan, ta dauko hula ta ajiye kan mudubin, anan ta shafa mai ta zauna batare da tasan asalin abinda take tunani ba. A hankali ta dauki farar hular ta saka a saman kanta, tana gyara zamanta, hasken hular na saka nata hasken kara fitowa. A hankali cikin sanyin yanayinta tayi baya da kujerar da take sama tana mikewa tsaye. Madai-daicin tsayin da take dashi bai hana sirantakarta fitowa ba, duk da girman kayan jikinta.
Falo ta fito tana ganin Mami a tsaye hannunta riqe da hijab
"Ke ba dake za'aje kun shin ba?"
Mami ta bukata, tana kallon Waheedah data girgiza mata kai, girman yarinyar na bata mamaki, yanda shekaru suke gudu na tsoratar da ita, yanzun Waheedah din tace a aji shidda sakandire, Waheedar tace take shirin zana jarabawar gama aji shidda, ko Amatullah ta gitta sai taita kallon su, tana mamakin lokacin da rayuwa ta kawota inda take, da gaske haihuwa kyauta ce mai girma, kyauta ce da take ma fatan duk wani wanda Allah bai nufa da samu ba ya samu ko zaiji abinda ake ji.
"Jikina yamun nauyi Mami, suje abinsu, nace Amatu zata sakamun jan lalle idan zamu kwanta..."
Waheedah tai maganar tana katse wa Mami tunanin da take.
"Allah ya kaimu... Zamu fita kasuwa da Haj. Halima"
Kai Waheedah ta jinjina tana fadin
"Saikun dawo..."
Tsaye tayi har saida taga Mami ta fita daga dakin tukunna, daga nan cikin dakin tana jiyo hayaniyar mutane da yake nuna alamun bikin da zasu sha a cikin gidan, tun da satin ya kama ake hidima, babu kuma ranar da kanta baya mata ciwo, dan bawai tana son hayaniya bane, amman biki yara uku ita kanta tasan saidai suyi hakuri, Muhsin, Khadija da Babangida, da shi Babangida ma za'a daga, dan ginin shi ko rabi baikai ba, sai Kawu Hamisu ya bashi gida mai daki biyu ya zauna har Allah ya hore mishi ya kammala nashi.
Ita duk ba wannan bane a ranta, Abdulkadir ne manne da zuciyarta, zata iya cewa tun tafiyar shi da rana daya bai taba barin tunaninta ba. Lokutta da dama tana tashi daga bacci takanji kirjinta yai mata nauyi da tunanin halin da yake ciki, shekara daya akace zaiyi yazo gida, amman yanzun shekaru biyu kenan. Watannin baya kasa hakuri tayi, batasan lokacin da tambayar ko yana lafiya ta subuce mata a gaban Abba ba, shine ma yace mata yaje ya duba shi sau daya. Yana lafiya, tukunna taji tadan samu nutsuwa ta wasu fannonin.
Kan kujera ta zauna, niyyar kwanciya take, tunanin Suratul-Kahf da bata karanta ba na sauko mata, kasancewar ranar juma'a. Ta rigada ta saba data idar da sallar asuba take karantawa, yau din bata samu wannan lokacin ba, saboda ta taya Mami gyaran gidan da aka bata, dan duk wanda ya kwana, ana sallah suke ficewa su koma sashin Hajja. Tunanin taje ta dauko Qur'an din takeyi, Aminu ya shigo da sallamar data amsa mishi cikin sanyin murya
"Commander an diro..."
Ya fadi yana dariya, hadi da wucewa kitchen, muryar shi Waheedah take ji ta dira kunnuwanta da wani irin yanayi, kafin ma'anar kalaman nashi su zauna mata, zuciyarta taji ta fara tsalle-tsalle da take tunanin kashedi ne, dan yanda ta fara doka mata, in bata miqe ba, tanajin tsaf zata fito daga kirjinta tayi kafafuwan kanta ta fice daga dakin dan neman duk inda Aminu yace Abdulkadir din yake. Mikewa Waheedah tayi tana saka hannu ta dafe kirjinta, inda take jin zuciyarta na kara gudu da duk daqiqa. A bakin kofa ta zira takalman bandaki da batasan ya akai suka zo wajen ba. Manya-manya ne, karamar kafarta na yawo a ciki, amman bata ma kula ba.
Tafiya kawai take kamar wadda aka sakawa batira, kafafuwanta take takawa tana nufar bangarensu, badan sun taba doguwar maganar da tsayinta ya wuce mintina biyar ba, amman tanajin wata irin sanayya da tai mishi da take tunanin sai dai su goga da Hajja in akazo maganar sanin halayen shi. Abdulkadir din data sani bazai shiga cikin gida ba, idan wani ne daban ya shekara biyu baya gida, yana zuwa bangarensu zai wuce yaga mahaifiyar shi, banda Abdulkadir, zai iya jira, daya shiga hayaniyar da take bangaren Hajja gara ya jira. Tana da tabbacin yana bangaren su.
Nan kuwa kafafuwanta suke daukarta, bayan shi ta fara hangowa, zata rantse da Allah ba girma kawai ya kara ba, harda tsayi, jakace rataye kan kafadar shi, rigar jikinshi ta kamashi kamar zata bude, damtsen hannun shi tabi da kallo daya kusa yar siririyar cinyarta. Sosai take takawa, bugun zuciyarta na karuwa, wani irin dumi taje ji jikinta ya dauka kamar zazzabi na shirin kamata. Tsaye tayi a bayan shi tana kasa motsa labbanta, hannunta daya na kan kirjinta kamar maison kare zuciyarta da take tunanin zata iya fitowa kowanne lokaci.
Hannun shi Abdulkadir yakai yana sake kwankwasa kofar, yana jiyo kidan da suka kunna har nan inda yake tsaye. Tsaki yaja yana addu'ar wanda zaizo ya bude kofar ya kasance kasa yake dashi, yanda zai zabga mishi marin tsayuwar da yasha a bakin kofa, in ba wulakanci ba, ya zasu kunna kida su kuma kulle kofa daga ciki. Yana shigowa gidan ya fara dana sanin zuwa. Baisan meye a maganganun Yassar da sukanyi tasiri akan shi haka ba, amman saiya sauke mishi sakashi zuwan da yayi. Bayason hayaniya irin haka, saboda yasan dole sai wani ya bata mishi rai, ga hannun shi yana saurin tashi, yanzun abin harya fi nada.
Yana sane yaqi zuwa hutun sallar da sukan zo na kwana biyu ko uku in yayi tsayi. Bawai dan baiyi kewar gida ba, sosai yake jin kewarsu, musamman Hajja da Zahra, babu wanda yagani tunda ya tafi daga Abba da sai Yassar. Dan shi kusan duk wata biyu sai yaje ya duba shi, kafin ya tafi kuma duk zuwan da zaiyi sau sunyi fada. Saida yaja dogon tsaki tukunna ya kara kwankwasa kofar da karfi wannan karin. Alama yaji ta cewar akwai mutum a bayan shi, kafin ya tsayar da hankalin shi waje daya, yanajin shiga da fitar numfashin Waheedah da takeyin shi a tsorace.
Juyawa yayi gabaki daya, yana tsorata Waheedah da take tsaye, ta kuwa yi baya gabaki daya, cikin zafin nama ya riqo hannunta, saida yaga ta