Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   37 / 51

108K to 111K   out of 152.3K words

akwai mutane ba.

Ranar aiki ce yasani, Yassar din zai yiwu yana wajen aiki, matar shi ma tana aiki a asibiti, bangaren accounting tunda abinda ta karanta kenan. Sai dai yasan Waheedah na nan, dan haka ya taka zuwa bangaren da ya sameta zuwan karshe da yayi. Kwankwasa dakin yayi tukunna ya tura hadi dayin sallama, kamshi na dukan hancin shi, duk da bana turarukanta bane ba, kamshin yai mishi dadi sosai. Wani irin tsalle zuciyar shi tayi naban mamaki ganin Waheedah a zaune, doguwar rigace ta atamfa a jikinta wani irin dinki da bazaice ga yanda yake ba, ta saka Ikram cikin jakar goyo ta goyata ta gaba tana tallabe da yarinyar da take bacci.

Kwalliya ce a fuskarta da ba koda yaushe takeyi ba, ta daura dankwalinta ya zauna das a saman kanta kamar a jiki akayi. Tana zaune gefen gado ta dora kafa daya kan daya, da plate din soyayyen dankali a gefenta da cokali mai yatsu a ciki, ta dora system din da yake zaton ta Yassar ce akan wani dan tebir tana kallo. Kafafuwanta yake kallo da suka sha zanen flower tayi wani irin ja mai duhu, kafin ya yawata da idanuwan shi yana tsayarwa kan hannunta daya dake tallafe da Ikram da shima yasha kunshin.

Kai ta dago tana kallon AbdulKadir din, zuciyarta na wata irin dokawa da wani sabon tashin hankalin da ta kwana biyar bataji shi ba, duk wani abu da su Yassar suka san zai dauke mata hankali ya rage mata tunani shi sukeyi mata. Har system din Hauwa dake cike da fina-finai daga American zuwa na indiya harda na korea da tafi so ta kawo mata, ta manta lokacin karshe data huta haka. Ji takeyi kamar tayi wata takwas rabonta da samun bacci mai nutsuwa, wata takwas rabon da ta zauna ta huta ma rayuwarta, rabon da tayi wani abu don kanta kawai.

Taji dadi da AbdulKadir din bai dameta ba, shisa ta kashe wayarta ta ajiye. Bashi kadai ba, har yan gidan su batason kowa yayi mata maganar, kuma kowa ya kyaleta. Yanzun ganin AbdulKadir din na mata barazana da dan kwanciyar hankalin da ta samu, dan jiya da akazo yiwa Hauwa kunshi itama yi mata akayi, jinta takeyi daban, kamar tabaro waccen Waheedahr a gidan AbdulKadir, yanzun kuma watace daban da batasan akwaita bama.

"Wahee..."

AbdulKadir ya kira da wani irin sanyin murya mai tattare da mamakin ganin hankalinta a kwance yake. Dan ganinta yasa komai dawo mishi, dukan da yasha a barikin sojoji da yake nan garin Kano, yunwar da yake tattare da ita ta kwanaki na rashin samun wadataccen abinci, rashin bacci, da duk wani rauni da baya iya nunawa a gaban kowa. Itama Waheedah kallon shi takeyi, tana kallon kumburin dake kasan idanuwan shi da tasan rashin bacci ne, da kuma wasu kumburin na alamun duka. A karo na farko a rayuwarta da taji halin da yake ciki bai dameta ba, ballantana harta tambaye shi ya akai ya shiga ciki.

Dauke idanuwanta tayi daga kan shi tana mayar da hankalinta kan kallon da takeyi, tana kai hannu ta dauki plate din dankalinta tana cigaba daci

"Waheedah..."

AbdulKadir din ya kira wannan karin cike da rashin yarda cewa ita din ce ta nuna mishi halin ko in kula, ita din ce ya shigo waje ta kalle shi taci gaba da wata hidimar kamar baya nan. Takawa yayi yana karasawa inda take ya zauna gefenta yana son ta sake ganin shi dinne

"Baki ganni bane?"

Ya tambaya yana kallon fuskarta da babu kowanne irin yanayi akai, dankalin data tauna ta hadiye tana tsayar da film dinta dan batason komai ya wuce ta.

"Naganka... Menene? Takardata ka kawomun?"

Wata irin dariya mai sauti AbdulKadir yaji ta subuce mishi, tabbas Waheedah na da aljanu, yana mamakin yanda akai basu taba tashi ba sai yanzun, film dinta ta dannama play tana mayar da hankalinta a kai. Hannuwan shi AbdulKadir ya saka fuskar shi a ciki yana fitar da wani irin numfashi, bashi da karfin yin ko hayaniyar kirki, duk wani kashi da yake jikin shi ciwo yake, yasan yanda ake dukan ma'aikata in na horo ne, sun san inda suke duka da zai shigeka batare daya ji maka ciwon da zai hanaka zuwa aiki washegari ba. Lokutta da dama ko fuskarka ba zata gwada alamun dukan da kaci ba.

Suna dukan inda uniform zai kare shatikan ko ciwukan. Sauke hannayen shi yayi yana rutsa idanuwan shi da yanda hakarkarin shi ya amsa, yasan ba karaya ko daya a jiki, amman wajen ya tara jini saboda dukan da yasha, bashi bane na farko, Waheedah kan sa towel da ruwa mai zafi ta gasa mishi ta bashi panadol ko da bayason sha.

"Kwanana biyar a barikin sojoji..."

AbdulKadir ya tsinci kanshi da fadi da wani irin sanyin murya, Waheedah batama ji shi ba, dan gabaki daya hankalinta ya tattaru kan kallon da takeyi, hannu AbdulKadir yakai yana rufe system, hakan yasa ta kalle shi

"Bana so, banma ga dalilin da zaka shigomun daki ka nemi dagamun hankali ba"

Murmushi AbdulKadir yayi

"Ina da duk wani dalili da zan shigo dakin nan, hankalina ba'a kwance yake ba, banga dalilin da zai sa naki ya kwanta ba Wahee, ke kika zabar mana wannan rayuwar...sannan ba dakinki bane wannan... Dakinki yana gidana"

Da kalar rigimar dake cikin idanuwan shi take kallon shi tana jin dai-dai take da duk wani abu daya shirya tarar ta dashi, gabaki daya yagama fita daga ranta, ko ganin shi batason yi, auren shi takeji kamar wata igiya data shake mata wuya tana hana mata yin numfashi a walwale, shisa take so ya datseta ya warware mata ko zata samu ta shaqi iska mai nutsuwa.

"Bani da daki a gidanka, bani da komai a gidan ka sai kayan da nake gab da zuwa in kwashe dan takardata zaka bani tunda babu inda aka taba aure dole"

Mikewa AbdulKadir yayi, ya dauka bashida karfin yin hayaniya, amman tunda can Waheedah tafi kowa damar bata mishi rai, bata amfani da wannan damar ne sai yanzun.

"Igiyar aurenki a hannuna take, yanzun kuma na fara rikon ta, kaya kuma Allah ya baki iko, kina jina? Allah ya baki iko dake da duk wanda yake da tsautsayin shigomun gida da nufin tayaki kwashe su... Aljanu ne kike dasu da bansani ba sai yanzun, to wallahi ko su ubansu yayi karya....ke da kanki ma kinyi karya kisani yin abinda banyi niyya ba"

Kallon shi Waheedah takeyi itama tana tsintar kanta da mikewa tsaye

"Ana dole ne? Nagaji... Nagaji da aurenka"

Cikin hargowa yace

"Ni bangaji ba, gajiyarki bata da wani muhimmanci"

Dariya Waheedah tayi tana jin duk wani kwanciyar hankali data samu a kwanakin nan na bace mata

"Abubuwa da yawa da suka shafeni basu da muhimmanci a wajenka daman, saboda haka banyi mamaki ba"

Cike da rashin fahimta AbdulKadir yake kallon ta

"Bangane abubuwa da suka shafeki ba suda muhimmanci a wajena ba"

Gyarama Ikram zama ta sakeyi a jikinta tana kara tallabeta

"Kwakwalwa ce a kanka duk da bako yaushe kake amfani da ita ba, sai kayi tunani ai"

Kallon ta AbdulKadir yakeyi, ya dauka ya gama shan mamakinta tunda ta iya bude baki ta nemi ya saketa, amman da duk wani gani da zai mata bayan haka da yanda take kara shayar dashi mamaki

"Zagina zakiyi Waheedah?"

Kai ta girgiza mishi, zagi ba dabi'arta bane tunda can, ko Fajr ma zata kirga lokuttan da ta zage shi balle shi AbdulKadir din

"Idan ba zagi ba, me maganganun ki suke nufi? Rashin kunya kike neman yimun da bansan lokacin da kika koyeta ba"

Yake karasa maganar da wani irin bacin rai marar misaltuwa

"Nifa ban zageka ba, rashin kunya kuma in dai koya nayi bai kamata kayi mamaki ba tunda nayi rayuwar aure da kai"

Da hannu yake nunata

"Gashi nan... Yanzun me kikayi.. Wani zagin ne wannan ai... Wallahi Waheedah ki kiyayeni, kina gwada hakurina... Kuma tashi zakiyi mu koma gida"

AbdulKadir yayi maganar yana son ture alamun da yakeji kamar na tsoro na son taso mishi, ga hankalin shi da yake a tashe kasan bacin ran da yake fama dashi, musamman da Waheedah tayi mishi wani irin kallo tana komawa ta zauna tare da fadin

"Saika daukeni ka dora saman kai ka mayar dani ai"

Kai AbdulKadir yake jinjina mata, inda take ya karasa, rashin hankali take nuna mishi karara, zai nuna mata duk abinda takeji dai-dai yake da ita. Belt din da yake kafadunta na jakar goyon yake kokarin ballewa, ta ture hannun shi

"Me kakeyi?"

Ta tambaya muryata cike da tsoro, hannuwanta AbdulKadir ya kama duka biyun yana saka karfi ya rike su, belt din ya kwance duk ihun da Waheedah take mishi, da hannu daya ya zame Ikram yana sauketa daga jikin Waheedah din

"Sadauki ka sakeni, dan Allah ka kyaleni, kaga Ikram na kuka"

Waheedah ta karasa tanajin idanuwanta sun ciko da hawaye duk yanda ta fadama kanta ta gama yi mishi kuka

"Ashe muryarki na sauka haka, harna manta saboda yanda kike dagamun ita a kwanakin nan"

Cewar AbdulKadir din yana kama hannuwanta da yake rike dasu ya dagota ya mikar tsaye, zuwa lokacin ta daina kiciniyar kwacewa, dagata yayi yana sabata a kafadar shi kamar ya dibi kayan wanki, yasa hannuwan shi yana mata rikon da tasan ko da wasa ba zata iya kwacewa ba, ikon Allah take saurare kawai tana tabbar da AbdulKadir na da tabin hankali, bata sani bane tuntuni sai yanzun.

"Wallahi ka saukeni, wannan kidnapping ne, shekara goma sha biyar zakayi a gidan yari"

Dariya AbdulKadir yayi, wannan karin tana fitowa daga bangaren zuciyarshi daya kwana biyu baiji ya buga mishi ba.

"Ka saukeni, bana son haka, ka saukeni...ko ka kaini ba zama zanyi ba Sadauki...na fada maka nagama aurenka"

Hanyar da zata fitar dashi daga dakin ya nufa yana bude kofar yaci karo da Yassar da ya miko hannu da alama yana shirin kwankwasa kofar ne koya bude. Dan tunda ta shigo gidan yakejin kamar maganganu shisa ya nufo bangaren Waheedah din, muryarta na tabbatar mishi da AbdulKadir na ciki. Yanayin maganganunta ne ya hanashi bankada kofar kar yaga abinda bai kamata ba, tunda yasan AbdulKadir ba hankali gare shi ba ballantana kunya. Sai dai baki a bude yake kallon AbdulKadir din

"Ka matsamun Hamma..."

Ya fadi yana gyara ma Waheedah zama a kafadar shi

"Me kakeyi AbdulKadir? Me kakeyi?"

Yassar yake tambaya yana kallon AbdulKadir din kamar a film, dan bai taba ganin abinda yakeyi a zahiri ba, cikin kuka Waheedah take fadin

"Hamma kace ya saukeni, dan Allah kayi mishi magana, ni bazan koma gidan shi ba..."

Muryar Yassar har lokacin da mamaki yace

"Ka sauketa AbdulKadir.... Ka sauketa tun kafin ranka ya baci"

Kankance idanuwa AbdulKadir yayi

"Ita tace in dauketa a kai in tafi da ita..."

Waheedah najin hawayen dake digar mata, ga kanta daya fara tara jini saboda yanayin yanda AbdulKadir din ya riketa

"Ni bance mai ba Hamma... Dan Allah kace ya saukeni"

Kokari Yassar yakeyi kar murmushi ya kwace mishi, idan AbdulKadir yaga alamar wasa koya take tattare da Yassar din bazai sauke Waheedah ba

"Ka sauketa nace maka AbdulKadir..."

Baisan ya akayi maganar Yassar din tayi tasiri akan shi ba. Sauketa yayi tana dafa kofar wajen jin zata fadi, tana tsayuwa sosai tasa hannu tana goge fuskarta, dankwalinta batasan ma lokacin daya fadi ba, ga wata irin matsananciyar kunyar Yassar din da ta kamata. Wani irin kallo ta watsa ma AbdulKadir din

"Aurenka ko na zobe ne sai ka rabu dani... Kuma wallahi saina fadama Abba"

Ta karashe maganar wasu hawayen takaici masu zafi na zubo mata. AbdulKadir kuwa Yassar ya kalla

"Kagani ko? Hamma kanajin irin rashin kunyar da take mun"

Hannu Yassar ya daga mishi

"Ka wuce ka tafi"

Kafada AbdulKadir ya makale

"Ni bangama magana da ita ba"

Kai Yassar ya girgiza yana sauke numfashi, so yake yabar wajen kafin dariya ta kwace mishi.

"Ka tabbata zakai mata magana kamar mai hankali?"

Kai AbdulKadir din ya daga mishi, saida Yassar din yadan tsaya tukunna ya juya. Kofar AbdulKadir ya tura yana mayar da hankalin shi kan Waheedah data dauki Ikram tana kokarin lallashin ta

"Babu ribar da zakici a fada dani Waheedah... Ki taho mu koma gida, na baki hakuri.. Kiyi hakuri dan Allah. Kizo mu koma... Kinga ni bana son yin fada dake"

Ya karasa maganar yana sauke muryarshi, amman a idanuwanta yake ganin yanda maganganun shi ko kadan basuyi tasiri ba, ci gaba yai da fadin

"Kinji Wahee... Kina ta dagamun hankali akan magana karama, Wallahi kwanana biyar a barikin sojojin garin nan, ki kalli fuskata, na manta rabona da wadataccen bacci balle abincin kirki..."

Yayi maganar yana kama rigar jikin shi ya daga mata, jinine yayi baqiqirin a gefen cikin shi da duka hakarkarin shi, tana kallo ya juya mata har bayan shi da nan ma jinin ne a kwance, kowanne irin duka akai mishi ba karami bane ba, zuciyarta takeji a bushe babu wani abu da take sonyi banda shakar numfashi batare da igiyar auren shi ta daure mata wuya ba. Sakin rigar shi AbdulKadir yayi

"Ban shigo da nufin yin fada dake ba, har kudin hidimar gida na tura miki dazun..."

Kalamai yake nema da zai lallasheta dasu, amman ya rasa, saboda basu taba fada ya wuce yini daya ba, koyace bata taba fada dashi ya wuce yini daya ba, tunda ba biye mishu takeyi ba, ita ta saba lallashin shi, shisa komai ya kwance mishi. Takawa yayi ya karasa yana kamo dayan hannunta da yake jikin Ikram yana sakata sake rike yarinyar sosai

"Kinga azumi ya kusa, saura kwanaki kadan, ana yafewa juna kafin azumi, bama kyau fada kafin azumi"

Cikin idanuwan shi Waheedah ta kalla

"Ka saukake mun kafin azumin...dan Allah Sadauki...kaji...ka sakeni in huta nima. Nagaji da auren ka"

Ta karasa maganar tana zame hannunta daga cikin nashi ta share kwallar data zubo mata. Wani irin numfashi AbdulKadir ya sauke yana juyawa ya fice daga dakin, bai tsaya ko ina ba sai cikin motar shi, tayar da ita yayi ya fita daga gidan Yassar, a gefen hanya yayi parking yana hade kan shi da abin tuqin motar. Kan shi ciwo yake da bashida alaka da yunwa ko rashin bacci. Wani irin tsoro yakeji da bai taba sanin akwai shi ba. Kalaman Waheedah ke mishi yawo da wani yanayi naban mamaki.

Batayi mishi maganar da hayaniya ba, asalima idanuwanta cike suke taf da hawaye, da neman alfarma, bata taba rokon wani abu a wajen shi ba, yaune yake ganin alamar tana rokon shi, kuma rokon farko daya shiga tsakanin su shine na ya rabata da auren shi, si take ya bude bakin shi ya furta mata kalaman da zasu warware igiyar da bai yarda an kullata tsakanin su ba saida nufin mutuwa ce kawai zata raba. Bai taba tunanin cewa zata roke shi wani abu da zai kasayi mata ba, kodan girman matsayinta a wajen shi, amman sai ta tambayeshi abinda yakejin duk duniya babu wanda ya isa ya sakashi yin shi.

Wani irin tsoro yakeji daya danne duk wani abu da yake damun shi. Lumshe idanuwan shi yayi yana hango yin rayuwa babu Waheedah, da sauri ya bude su yana dagowa daga jikin motar, dan jin shi yayi duniyar tai mishi wani irin girma, ga kadaici naban mamaki daya lullubeshi. Da aurenta yasan akwai abinda babu a rayuwar shi sai bayan ta shigota, daga randa igiyar aure ta hadasu zama a karkashin inuwa daya bai kara hasko wani lokaci a rayuwar shi da babu ita a ciki ba. Ko tunanin mutuwa yake bai taba hango zata riga shi ba, abu ne da tunanin shi ma baya hasaso mishi.

Film idan yana kallo indai za ai mutuwa, yafi son yaga mijinne ya mutu yabar matar, dan baisan yanda zaiyi da sauran rayuwar shi idan babu ita a ciki ba.

"Bazan iya sakinki ba Waheedah... Ko meye nai miki me zafi haka hakuri zakiyi ki dawo. Inke zaki iya barina ni bazan iya barinki ba wallahi... Bazan iya ba"

Ya karasa maganar yana dafa fuskarshi da duka hannuwan shi biyu. Yafi mintina talatin a cikin motar kafin ya tayar da ita yana nufar gida...!

#TeamAbdulkadir
#TeamWaheedah
#LubnaSufyan
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43

*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*

26

To UMMU ABDUL, Hajjan AbdulKadir, Chairlady ta yan Fikra, Tauraruwar MSU. Thank you, SonSo a ko da yaushe.

Tun daya tunkari kofar yake jin kauri ya cika mishi hanci, yana bude kofar ya saka kafafuwan shi cikin falon Waheedah yakejin kaurin na karuwa, bangaren Nuriyya ya karasa yana ganin hayakin dayake fitowa daga kitchen din ya turnuqe falon, gaban shi yaji yayi wata irin mummunar faduwa, da gudu ya shiga kitchen din, hayakin na shaqe mishi kafofin shige da ficen iska, yana soma tari, ta inda kaurin yake fitowa AbdulKadir ke nema. Kafin idanuwan shi sukai kan tukunyar da tayi wani irin baki. Hannu yakai yana kashe gas din ya fito daga kitchen din yana takawa zuwa dakin baccin Nuriyya.

Tunda AbdulKadir din ya fita, ta tashi tana dora ruwa ta zuba shinkafa a ciki dan ita ba tsayawa zatayi sai ruwan yayi zafi ba. Dawowa tayi ta dauki wayarta tana ganin text, dubawa tayi taga dubu arba'in, murmushi tayi hankalinta da yake a tashe taji ya kwanta. Daman ko da AbdulKadir din bai dawo ba ita ba tunanin abinda ya same shi ko abinda ake mishi ne a gabanta ba, tunanin abinda zai mata idan ya dawo shine matsalarta, tunda kuma ya tura mata kudi kamar yanda yakanyi duk wata, hakan na nuna alamar babu abinda zai faru. Ko fadama bai mata ba, shisa ta wuce dakin baccin.

Akwai wasu takalma da aka turo a group dinsu na mata da kawarta Safara'u ta sakata ciki, takalman sun mata kyau, har ta private Safara'u tai mata magana ko zata siya, sai dai ta kashe kudin hannunta tas, tayi niyyar ta nunama AbdulKadir din daman inya kwana biyu ya huta, sai ga Waheedah tazo tana asibiti ita kuma. Batasan cutar da har yanzun take damunta da bata warke bama, takalmin tace tana so dubu bakwai da dari biyar, ta tura kudin, saita turama Safara'u balance din atamfofin da ta dauka wancen watan dubu goma, ta kuma turama mai dinkinta shima dubu goma. Kafin wani lokaci dubu hudu ce ta rage mata a banki.

Kwanciya tayi kan gadon da yake a hargitse tana manta cewar ta dora wani girki tunda ba sabawa tayi ba. Hankalinta ya nutsu kan littafin DAN ADAM na Rufaida Omar da take karantawa, dan littafin saika nutsu zaka fahimce shi

37 / 51