Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   33 / 51

96K to 99K   out of 152.3K words

yawa da zaice ya taba jin irin yanayin, baisan asalin yanda yake ba sai yanzun da yake a bakin kofar gidan shi amman ya kasa shiga.

"Oh Allah na"

Ya tsinci kan shi da fadi ganin da gaske shine a tsaye bakin kofar gidan shi ya kasa shiga. Lumshe idanuwan shi yayi yana bude su hadi da sauke numfashi, duk wani sauran karfi da yake jin ya rage mishi ya tattaro ya murda hannun kofar dashi. Kafafuwan shi da yakeji kamar itace saboda nauyin da sukai mishi yaja yana shiga cikin gidan dayin sallamar da ta tsaya cikin makoshin shi. Gyaran murya yayi yana sake yin sallama, amman duk da haka a hankali yaji muryar shi ta fito.

Dakyar yaja kafafuwan shi zuwa bedroom din su, ko sallama sai bayan ya tura ya shiga yayi ta. Amsawa Waheedah tayi, tana jera kaya a wardrobe din dakin da take cikin bango.

"Takalma Sadauki... Saboda kai bana sallah a tsakar daki saina saka darduma, ko ina shigarmun kake da takalma..."

Nan inda yake ya tsaya ya kwance igiyar takalman da suke kafarshi yana zame su tukunna ya karasa cikin dakin ya zauna kan gado.

"Sannu da aiki..."

Ya furta da wani irin sanyin murya da yasata barin abinda takeyi ta juyo tana kallon shi.

"Sadauki?"

Waheedah ta kira cike da alamun tambaya, dan yanayin shi gabaki daya ya bata tsoro, ganin bai dago ba, asalima sake sukunyar da kan shi yayi, yasa ta rufe wardrobe din tana karasawa ta zauna kusa dashi. Kafadar shi ta dafa tana fadin

"Lafiya? Me ya faru? Menene? Wani bashida lafiya a gida?"

Kai AbdulKadir yake girgizawa da duk tambayarta, amman ya kasa dagowa ya sauke idanuwan shi cikin nata. A karo na farko da yake tir da gaggawa kan al'amura batare da tunani ba. Saboda bai taba tunanin zaiji abinda yakeji din ba yanzun, ya rasa karfin gwiwar fuskantar Waheedah ya fada mata yayi aure, an daura mishi aure, matsalar shi ba gaya mata da wa aka daura mishi auren bace a yanzun, ta inda ma zai fara mata maganar auren.

Kan shi ya dora a kafadarta yana sauke wani irin numfashi

"Waheedah...."

Ya fadi cikin wani irin yanayi, hannunta ya kamo ya rike yana rasa kalaman da zaiyi amfani dasu. Da Hajja bata mishi fushi sai ya kirata tazo ta taimaka mishi ta fadama Waheedah din, ko Yassar ma, wani dai ya fara fada mata dan shikam har wani zazzabin tashin hankali yakeji ya fara rufar mishi.

"Kana bani tsoro Sadauki... Na kasa yarda komai lafiya"

Waheedah tace tana dumtsa hannun shi da yake cikin nata. Idanuwan shi ya lumshe da maganganunta yanajin komai yai mishi tsaye cik. Waheedah ce, Waheedahr shi. Ta ina zai fara fada mata ya kara aure batare da saninta ba, sai yanzun tunanin ita ya kamata ta fara sani kafin kowa yazo mishi. Dagowa yayi daga jikinta ya ja Kafafuwan shi kan gadon yana lankwashe su. Numfashi ta sauke, tunda ya shigo gidan sai yanzun ya hada idanuwa da ita, duk da akwai wani abu da take gani tattare da yanayin fuskar shi da yasa zuciyarta yin rawa.

Fuskarta ya tallafa cikin hannuwan shi yana fadin

"Karki barni Waheedah, ki tabbatar mun da ba zaki barni ba"

Nata hannuwan ta dora kan nashi dake fuskarta

"Dan Allah ka gayamun me yake faruwa"

Ta karasa maganar idanuwanta na cikowa da hawaye dan gabaki daya ya tsoratata

"Wani waje mai hatsari zasu sake turamun kai ko? Ka fadamun dan Allah..."

Cewar Waheedah muryarta na karyewa. Wannan na cikin bangaren da tafi tsana a aikin shi, in duk aka turasu wajen da ake hatsaniya, tare da kwanciyar hankalinta yake tafiya, wayar duk da zataji sai gabanta yai wata irin faduwa, idan tayi sati daya bataji shi ba, ko baccin kirki batayi. Tana da tabbacin matan sojoji tare suke raba duk wani tashin hankali dake cikin aikin mazajen su. Mata da yawa nason auren sojoji, ita AbdulKadir take so, in da tana da yanda zatayi da baizo mata a soja ba. Tashin hankalin dake cikin aikin shi yana da yawa.

Kai ya girgiza mata, muryarshi can kasan makoshi yace

"Babu inda aka turani, kawai ina son jin ba zaki barni ba"

Murmushin karfin hali tayi badan zuciyarta ta nutsu ba, amman shi dinma bata ganin nutsuwa a tattare dashi, bata so ya koma wajen aiki a haka.

"Ka taba ganin mata tabar mijinta? Ina zanje nikam...ina tare da kai daga yanzun har sauran kwanakin da Allah ya aramun"

Numfashi AbdulKadir ya sauke yana barin kalamanta na samun wajen zama a kasan zuciyarshi. Yakai mintina biyu tukunna ya saki fuskarta yana mikewa, bandaki ya shiga ya watsa ruwa, amman ko kadan baiji wani sauki ba, hankalin shi yakeji yaki kwanciya, ga wani bangare na zuciyarshi da yake azalzalar shi ya fadama Waheedah din kawai ya huta, amman ya kasa samun karfin gwiwar fada mata, baisan ta inda zai fara ba.

Kwanciya sukayi, Waheedah na jikin shi, ko kadan bacci ya kaurace ma idanuwan shi, ya rasa abinda yake mishi dadi a duniya, karfe hudu ya mike ya karayin wanka, shiya hada kayanshi, ya rasa karfin zuciyar tashin Waheedah din, kai kawon da yakeyi da motsin shi da yai yawa shiya tasheta. Fuskarta kawai ta wanke tayi brush ta wuce kitchen tana fara fere dankalin turawa, iya wanda AbdulKadir din zaici ta soya. Kafin biyar harta gama komai yaci, tana kula da yanda yake komai da wani irin sanyi da yake taba mata zuciya.

Kafin asuba yake fita daman, Yassar ne yake zuwa yana sauke shi tasha. Amman yau kwata-kwatsa AbdulKadir din bai tsammaci zai zo ba, har saida yaji karar shigowar mota tukunna. Jakarshi ya rataya Waheedah na rakashi har bakin kofa, ta kasa sabawa har yanzun, duk randa zai tafi sai tayi kuka. Yanzun ma idanuwan ta cike suke da hawaye, muryarta na rawa tace

"Allah ya tsare mun kai a duk inda zaka shiga. Ka kula da kanka dan Allah..."

Kai AbdulKadir din ya daga mata yana rungumeta a jikin shi, saman kanta ya sumbata da gefen fuskarta, tukunna ya dago ta daga jikin shi

"Zanyi kokari in dawo wata na gaba in shaa Allah. Ki kulamun da kanku..."

Sake rungumeshi tayi tanajin kamar karya tafi. Dakyar ta iya raba jikinta da nashi, tana sa hannunta ta share kwallar data tarar mata. Shi kanshi yanajin barin nata, da son samun shine duk inda zaije da ita zai tafi. Amman ya fahimce ta data fada mishi Fajr na bukatar samun ilimin addini mai inganci, zaman Lagos ba nata bane da yara, tafiso ta natsu waje daya. Shisa ma ya dawo da ita Kanon, tunda shima wani lokaci aiki na dauke shi watanni, duk inda yakaita in hakan ya faru ita kadai zata zauna. Gara a gida inda yasan tana zagaye da yan uwa.

Sai da ya sake sumbatarta tukunna ya fice daga gidan yanajin yau ba wani bangaren shi ya bari ba, harda wani irin nauyi mai girman gaske da rashin gaya mata maganar auren shi, tunda ta tashi yake motsa bakin shi, kalamai ne sukaqi fitowa. Abba ya kamata ya tambaya ta inda zai fara tunda shi yayi hakan har sau uku. Zaifi kowa sanin kalaman daya dace yayi amfani dasu, amman Abba fushi yake mishi, tunda bai kirashi yau ya mishi Allah ya tsare ba.

Wajen motar Yassar din ya karasa ya bude ya shiga yana fadin

"Hamma ina kwana..."

Inda yake Yassar bai kalla ba yaja motar yana fita daga gidan. Numfashi AbdulKadir ya sauke

"Kai ma fushin kakeyi kenan har yau... Ni banyi fushi na Hamma kaine kakeyi... Ok"

AbdulKadir ya karasa maganar yana sauke wani numfashin

"Da Kawu Ali mukaje jiya... An daura auren tun jiya... Ban fadama Waheedah ba, Hamma na kasa fada mata, tunanin bai zo mun ba sam sai bayan an daura auren. Ya kamata in fada mata..."

Katse shi Yassar yayi da cewa

"Wallahi, Wallahi idan kaci gaba da magana zan saukeka ka nemi abinda zai kaika tasha ko ka taka da kafa bai dameni ba. Allah kadai yasan yanda nakai zuciyata nesa na fito... Kayi abinda kake so, wannan matsalarka ce, tun jiya ka rigada ka nuna mun banda matsala da aurenka. Kabar shi a haka kawai, bana son jin duk wani abu daya shafi tsakanin ka da Nuriyya, yanzun, anjima, gobe, kai har iya zaman rayuwar aurenku idan kana son zaman lafiya dani ba zaka kawomun zancen ta ba"

Muryar Yassar din ta tabbatar ma da AbdulKadir yana nufin dukkan kalaman daya fada, daga zuciyarshi yai maganar. A karo na farko da yaji bayason kure hakurin Yassar din. Shiru yayi, yana kara jin komai ya hade mishi waje daya. Wayarshi ya laluba yana ganin text din Nuriyya. Mayar da ita yayi ya ajiye, itama baisan me zaice mata din ba, baisan me zaicewa kowa ba. A bakin tashar unguwa uku Yassar ya sauke AbdulKadir din yana fadin

"Allah ya tsare..."

Yaja motar shi ya wuce, da gaske fushi Yassar yake mishi, dan yakan samu waje yai parking, baya tafiya sai yaga AbdulKadir din ya shiga mota suna shirin tashi tukunna. Wani irin numfashi AbdulKadir yaja yana fitar dashi a wahalce, zai karya idan yace ranshi bai sosu ba, amman Waheedah ta danne duk wani abu da yakeji yau. Zai bi takan sauran al'amura idan ya samu hanyar fada mata ya kara aure.

*

Inda Baba ya fita yabarta, nan ya dawo ya sameta, badan bataso ta tashin ba, sai dan tanajin tsoron tashi ta farka daga mafarkin da takeyi na cewar AbdulKadir yazo neman aurenta wajen Baba. Magana ce da takejin ta kamar almara. Sallamar da Baba yayi yana kiran Mama ya katse mata tunanin da takeyi, duk da hakan baisa ta daina jinta kamar a mafarki ba. Mama ta fito tana kallon Baba da farin cikin dake fuskar shi.

"Auren Nuriyya aka daura yanzun a masallaci"

Cike da mamaki Mama take kallon Baba, tasan kullum zancen shi baya wuce na Nuriyyar duk sanda zasu kebe, amman bai mata zancen ya samo mata miji ko kuma akwai wanda ya same shi da maganar aurenta ba.

"Ban fahimta ba, aure fa kace Baban Nuriyya..."

Kai Baba ya jinjina mata

"Fitar da nayi dazun da maganar suka zo, to a shirye suke ashe"

Har lokacin da mamaki a fuskar Mama tace

"Duk da a shirye suke, kuma ba auren farko bane abin da mamaki, badan baya faruwa ba har a auren budurwar, amman gaggawa na daga shaidan fa, wanene yaron? A musulunce ya kamata ayi bincike kafin a daura"

Murmushi Baba yayi

"Nasani, nima nayi tunanin, amman ganin dan gidan Alhaji Ahmad ne shisa ma banki ba"

Da wani sabon mamakin karara a fuskar Mama take kallon Baba

"Dan gidan Alhaji Ahmad kuma? Wanne daga ciki?"

Gyaran murya Baba yayi tukunna yace

"AbdulKadir"

Wannan karin da tashin hankali bayananne Mama take kallon shi, cike da yanayin da yasa yaji gabanshi ya fadi

"Lafiya kuwa? Me ya faru?"

Kai Mama take girgizawa

"AbdulKadir naji kace, AbdulKadir dan gidan Alhaji Ahmad"

Da sauri Baba yake jinjina mata kai.

"Eh shi nace"

Bango Mama ta laluba tana samun kujera ta katako ta zauna akai tana wani irin mayar da numfashi hadi da fadin

"Nuriyya me kikayi? Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Sosai Baba yake kallon Mama

"Kimun bayani yanda zan gane... Me yake faruwa wai"

Kai Mama ta daga tana kallon Baba da idanuwan da suke cike da hawaye, ko da fada mishi tayi ba lallai bane ya fahimta, abune da 'ya mace kawai zata fahimci ciwon shi, dan ita zuciyarta wani irin zugi take mata, batajin zata dauki abinda akai ma Waheedah din, batasan hawayen ta sun zubo ba sai da taji su kan kuncinta, muryarta na sarqewa tace

"AbdulKadir dinne baka sani ba? Baban Nuriyya AbdulKadir dinne baka gane ba kafin ka biyewa son zuciyar 'yarka ka wakilci daurin auren nan ko me?"

Kafafuwan shi Baba yaji sunyi sanyi, tsugunnawa yayi, yasan matarshi farin sani, a tsayin zamansu, abinda zai sakata zubar kwalla babba ne.

"Maryama na kasa fahimtar ki, kimun magana yanda zan gane, kaina ya daure"

Wani irin kallo Mama take mishi da duk ya kara dagula mishi lissafi

"Kasan yana da aure ko?"

Kai Baba ya jinjina yana kallonta cikin kaguwa da jin sauran zancen

"Kana so kace mun baka san wacece matar shi ba"

Kai Baba yake girgiza mata, zai iya tuna lokacin da akai auren AbdulKadir din, su uku ne ko fiye da haka aka daurama aure ranar in zai tuna, dan a makare yaje, ko cikin masallacin bai samu shiga ba saboda cikowar mutane, ya tsayane har Alhaji Ahmad ya fito yai mishi Allah yasa alkhairi ya wuce. Wani irin daci Mama takeji har kasan zuciyarta, bata shiga harkar Nuriyya ne saboda batason rainin yarinyar, shisa a lokutta da dama take binta da ido, tasan tana da halaye marassa kyau, amman bata taba zaton ko zata nunawa kowa zai fada kan Waheedah ba.

"Amman kasan Waheedah ai"

Kan dai Baba ya sake daga mata

"Ya zakice nasan Waheedah... Waheedah fa"

Baba ya maimaita, yarinyar da aminiyar 'yar shi ce, kaunar dake tsakaninta da Nuriyyar ta kara karfin zumunci shi da Alhaji Ahmad din har yake samun alkhairai da dama daga shi har 'yar tashi. Hankali da nutsuwar yarinyar yasa duk shekarun shi yana ganin girmanta ba kadan ba. Kuma ko da Nuriyya tayi aure duk idan Waheedah tazo gida saita biyo ta gaishe dasu ko baya nan, yakan dawo ya samu sakon abin alkhairin da ta kawo musu.

"Hmm..."

Mama ta fadi zuciyarta kamar zata baro kirjinta, sai da ta hadiye wani abu dayai mata tsaye a makoshi tukunna tace

"Mijinta ne ka aura ma 'yarka"

Cikin tashin hankali Baba yake kallon Mama, yana son tace mishi abinda yaji ba gaskiya bane ba. Yasan Nuriyya daya daga cikin yaran Alhaji Ahmad ta aura, amman harga Allah bazai ce wanne bane a cikinsu, kuma bai taba kawo ma ranshi AbdulKadir din bane ba, tunda da kan shi yazo neman auren Nuriyyar, kuma itama Nuriyyar tasani, ko a mugun mafarki kuma bai hango cewar zasu hadu su biyun suyi wannan cin amanar da addini bai haramta ba, amman kunya da kara ta haramtashi ta kowacce fuska.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Baba yake fadi yana maimaitawa, idan hankalin shi yayi dubu gabaki daya yagama tashi. Ya rasa abinda zaice, mikewa Mama tayi tana kara share kwalla kafin tace

"Bansan abinda kikayi ba Nuriyya, bansan da idon da zaki kalli Waheedah a matsayin kishiya bayan duk halarcin da taimiki da zumuncin dake tsakanin ku ba, wallahi bansani ba. Nikam nasan bazan iya kallon idanuwan yarinyar nan ba.... Duk da ina son tasan bada sa hannuna kikai mata wannan cin amanar ba"

Mama ta karashe maganar tana barin wajen, Baba kuwa har lokacin ya kasa magana, hannu yasa cikin aljihunshi ya zaro sadakin Nuriyya da tunda aka fara maganar kanta yake a kasa, hawaye kawai suke zubar mata badan zata iya cewa ga asalin dalilin zubar tasu ba. Duk da ta daina jin duk wata magana da ta biyo bayan an daura aurenta da AbdulKadir, sai yanzun da tabi kudin da Baba ya ajiye mata da kallo.

"Wallahi da nasan mijin Waheedah ne sai dai ku nemi wanda zai daura muku auren nan Nuriyya... Bansan me kikayi ba, daga ke har shi, ban kuma san dalilinku nayin abinda kukayi ba. Amman in kunyi da son zuciya amana ba zata taba barinku ba..."

Baba ya fadi yana tashi shima. Dakin shi ya wuce yana jinjina al'amarin da kuma daukar da Waheedah zatayi musu ta mutanen da basu san darajar zaman tare da girman alkhairi ba, kuma bazai ga laifinta ba. Da gaske ne gaggawa a komai daga shaidan take, yanda ya kaqu ya rabu da Nuriyya yasa shi amincewa auren batare da tunanin komai ba. A karo na farko da yabi son zuciyarshi gashi tun ba'a je ko ina ba ya fara dana sani. Nuriyya kuwa kudin ta dauka tana komawa daki ta kwanta, har lokacin bata daina jinta kamar a mafarki ba.

Wayarta ta dauko, duk da tana shakkar ta kira AbdulKadir din, text ta tura mishi

'Nagode Masoyi, duk da na kasa yarda na zaka matarka, wallahi ina jina kamar a mafarki'

Sai da taga sakon ya shiga tukunna ta sauke wayar kan kirjinta tana jin wani irin nishadi da bata tabaji ba a rayuwarta yana lullubeta, kafin bacci ya kwasheta cike da mafarkin rayuwar da zatayi a matsayin matar AbdulKadir.

*

Komai bai sake hade mishi waje daya ba sai bayan komawar shi Lagos. Duk wani wanda yake sama dashi a gidansu saida ya kira yai mishi tas kan maganar auren, gabaki daya babu wanda ko Allah yasa alkhairi yai mishi, ya manta rabon da yayi kwanaki da bacin rai haka. Har kannen nashi ma Zahra sai da tayi mishi text

'Hamma baka kyauta mana ba, zaka zageni nasani, amman bai dameni ba wallahi. Abinda kayi baka kyauta ba'

Ya kuwa kira din ya sauke mata masifa kamar zai cinyeta, kukan ta daya ishe shine yasa shi kashe wayar shi, daman wanda zai huce akan shi yake nema. Gabaki daya ya rasa yanda zaiyi ko inda zai saka ranshi yaji sanyi, ga Waheedah duk waya ko video call din da zasuyi sai yaga ta kara mishi wani irin kwarjini da ko maganar kirki sai yayi da gaske yake iya hadata balle har yai mata zancen auren. Nuriyya ma kullum suna waya a gajarce, a satika biyun da yayi a Lagos doguwar waya daya sukayi, shima bayan ya kira Anty Talatu da tunda yake a rayuwarshi bai taba tunanin akwai ranar da zai bukaci wani abu daga wajenta ba.

Amman babu yanda zaiyi, babu wanda zai tambaya tunda duka yan gidansu basa magana dashi dan ya kara aure, itace ta fara zuwa kan shi. Ko ita din ma mamakine bayyane a muryarta da ta daga wayar, suka gaisa tana dorawa da

"Lafiya dai ko AbdulKadir? Kowa lafiyar shi kalau?"

Kai ya daga kamar tana ganin shi

"Lafiya kalau Anty, zan tambayeki ne daman"

Yanajin sauke numfashin da tayi kafin ya dora da

"Idan ka auri bazawara zakayi akwatuna duka ko?"

Dariya Anty tayi daga dayan bangaren

"In kana da halin hakan, ai kyautatawa ce, amman bakowa yakeyi ba gaskiya. Zaka iya magana da ita kaji, wasu sunfi son a basu kudin ma akan a sai musu kayan, kai ma kuma zaifi maka sauqi"

Jinjina kai AbdulKadir yayi, dan bai fahimci maganar Kawu Ali kan lefen ba, ita kuma Nuriyya batayi mishi zancen ba. Shisa ya kira Antyn dan yaji in sai yayine sai yasan

33 / 51