Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   48 / 51

141K to 144K   out of 152.3K words

yake sun tare mishi hanya, sun hana shi isowa da wuri, wayar shi ma da Yassar ya ishe shi da kira kasheta yayi. Ba zai tuna ranar karshe da yaji kunyar Yassar irin yanda yaji ba yau. Tunda can ma akan Yassar ne fara sanin yana iya jin nauyin wani dan adam haka, kan shi tsaye zai iya fadama Hajja abu, har Abba ma, koya tambaye su abu, amman Yassar saiya jima yana juya maganar kafin ya samu ya fito da ita. Lokutta da dama yanajin kamar shine ya kamata ya fito ciki daya da Yassar, su kwanta a mahaifa daya saboda kusancin da yake tsakanin su.

Sai dai haka Allah Ya kan tsara lamurra, wani lokacin ma sai kaga shakuwa a tsakanin mutanen da basu hada jini ba, Yassar na daya daga cikin abinda yake godema Allah da samu a duk sallar shi ta duniya tunda ya mallaki hankalin shi. Ta ina Nuriyya take so ya fara hada idanuwa da Yassar din? Me take so yace mishi bayan yau? Ta mishi abubuwa da yawa, kanana da manya da ya dauki idanuwa ya saka mata, abubuwan da duk ya tsarama kan shi ba zai dauke su a wajen macen da yake aure ba. Sai dai ita din ba Waheedah bace ba, yanajin ranar da duk zai waiwayi abinda tayi mishi da wahala alaqarsu ba zata samu tangarda ba, shisa yake kauda kai yana kyaleta.

Yau ne ta kai shi saman kanta ga ba jikin bango bama, da shi ta taba, da kudin shine, watakila ba zai ji abinda yakeji ba yanzun, da kudin ma na wani ne daban da yasan in ya mayar mishi zai karba duk abin zai zo da sauki. Kudin na Yassar ne, kuma ko jiya sai da yai mishi mitar bashi da kudi, yai ma Hawwa gyaran mota, yana so ya kara tara wasu kudin itama ya sake mata wata, zai iyayin abubuwa da dubu arba'in da biyun shi, ko kayan abinci zai siya ya ajiye, ko yayi hidimar sallah da take gaban shi cikin kwanaki kasa da talatin. AbdulKadir na da tabbacin bashi kadai bane yake tsara komai na rayuwar shi. Ciki harda yanda kashe kudin shi yake tafiya.

Bakin kofar dakin Nuriyyar ya tsaya yana rike da handle din kofar, idanuwan shi ya lumshe ko zai tuna wani dalili da yasa zuciyar shi doka mata tun daga farko amman ya rasa, ba halayenta bane, saboda baisan su ba lokacin da ya fara son ta, bai san su ba lokacin da zuciyar shi ta sake doka mata bayan ya rufe shafinta daga rayuwar shi. Baisan ko kadan cikin halayyarta ba lokacin da ya amince ma aurenta, halayenta sun fito mishi ne bayan ya aureta, a kasa da sati daya bayan ya aureta ya fara kula dasu, sun sake fito mishi bayan ta tare a cikin gidan shi, zama ya hada su, tana saka shi fahimtar dalilin da yasa mutane ke cewa zaka iya shafe shekaru da mutum ba kasan ko da kashi ashirin cikin halayen shi ba, saboda akwai boyayyayun halayen da ba mutum bane yake boye su dan kar a sani, basa fitowa ne sai zama na a kwana a tashi karkashin inuwa daya ya kama suke bayyana.

Auren Nuriyya yasa ka shi fahimtar abubuwa da dama duk da ba zama yakan yi yai tunani akan hakan ba. Akwai kuma dalilin da yasa akan auren Nuriyyar bayan ta tare Hajja ta kira shi a waya tana ce mishi

'Soyayya ce take dibarka yanzun AbdulKadir, kuma ita kadai bata isa ta rike aure ba, akwai lokacin da zaku tashi ku duka ku nemi digon soyayyar nan ku rasa, wallahi idan har baku gina zaman ku akan abinda ya girmi soyayya ba, in kuka shiga cikin irin yanayin nan zai muku wahala ku samu dai-dai to. Ba zance maka kacokan zaman aure kan ginu akan halaye bane kawai, amman su din kan zama ginshiqi mai girma na zaman aure. Ga ka ga Nuriyyar nan, itama ga ta ga ka nan, ba baki zan maka ba, amman akwai halayenka da nake da yaqinin Waheedah ce kadai macen da zata iya jurewa'

Bayason ya tsaya tunanin hakanne a baya, dan zai saka tunanin cewa sai da kowa da yake son shi yai mishi magana akan auren Nuriyya din yai biris da su, ko Yasir da ba shiga harkar juna suke ba sai dole sai da yace mishi

'Da yawan lokutta mukan so abinda ba alkhairin mu bane ba, zaka iya son abu ka rayu babu shi, zaka iya kin abu ka rayu dashi AbdulKadir. Dan kana son yarinyar nan baya nufin in baka aureta ba wani abu zai sameka, da yawan lokutta mukan yi hakuri da abinda muke so dan zaman lafiyar mu'

Shima yai watsi da shi, kashe wayar shi ma yayi. Shisa duk wani karamin abu da Nuriyyar zatai mishi baya daga kai, yasan tunanin maganganun da kowa ya fada mishi kan aurenta ne zai danne shi. Ya kuma tsani kalaman dake biyo bayan dana sani na 'Sai a wane ko wance suka fadamun ban ji ba' wani lokuttan kuma sai kaji ana 'Daman ance mun kaza da kaza'.  Duk bayason wannan tunda ba zasu canza abinda ya riga da ya faru ba, shisa yau yake tsaye bakin kofar yana so ya tuna koma menene da zai saka shi yadan sauka daga dokin zuciyar da yake kai, ko da kuwa sharrin shaidan ne, amman azumi akeyi, babu wani shaidan a cikin abinda yake ji sai Nuriyya. Numfashi yaja yana fitar dashi da wani irin bacin rai ya tura kofar, a tsaye ya sameta tana linke hijab. Kan lace din da tayi saurin jefa hijab din sama idanuwan shi ya fara sauka kafin yaji kamar ta watsama wutar da take ci a zuciyar shi galan din fetir..

"Me yasa?"

Ya tambaya muryar shi can kasan makoshi yana kafeta da idanuwa

"Me yasa me?"

Nuriyya ta tambaya tana son yin kamar bata fahimci abinda yake nufi din ba, duk da yanayin shigowar shi yasa ta gane yasan ta dibi kudin, ita tabarmar kunya da hauka akan nadeya. Tana bacci ma wayarta ta fara ihu, ta dauka taga Hajiya Kaltume ce tana fada mata yanzun za'a kawo lace din ma, dan ya iso, ta dauka sai dare. Ta karbo kenan ta shigo ta tsaya waya da Asma, ta manta shaf bata kulle kofar ta dauke lace din ba taji shigowar shi, da yasa zuciyarta yin wani irin tsalle, shisa ta jefa hijabin a sama tana fatan Allah yasa baigani ba. Tana kallon yanda yasa hannun shi ya dafe goshin shi yana runtsa idanuwan shi kafin ya sauke hannun yana ware su a kanta.

Sosai yake kokawa da duk wani abu dake zuciyar shi yana tuna mata da in ta manta akwai igiyar aure a tsakanin su da Nuriyya da ta hana mishi dukan ta saiya fitar mata da yanda ko a gaba ba zatai kokarin raina hankalin wani mai suna irin nashi ba, akwai azumi a bakin shi, watan Ramadan ne, wata mai albarka da yake cike da son yafiya da aikata alkhairai. Amman tafin hannun shi har kaikayi yake ya amsa tambayar rainin hankalin da tayi mishi akan kuncinta, marin da sai taga taurari

"Ki tauna maganar da zaki fadamun Nuriyya, Wallahi gab nake da wanka miki mari. Karki gwada wasan banzar ki a kaina yau, ba zai mana dadi ba. Me yasa kika daukar mun kudi?"

Kallon shi Nuriyya tayi tana jin zuciyarta na ci gaba da dokawa, bata taba ganin shi cikin irin wannan yanayin ba, amman a kasan tsoronta akwai yanda maganganun shi suka bata mata rai, taya zaice zai mareta tana matar shi, ita alkawari taiwa kanta daga ranar da namiji zai tabata ya taba auren shi tunda ita ba jaka bace da zai kamata yana duka.

"Wai wanne kudi?"

Ta tambaya tana karasa kwance sauran hankalin da AbdulKadir yakeji yana rike da kwakwalwar shi ya kuwa dauketa da wani irin mari da yasa tajin kamar idonta daya ya fado, da sauri ta saka hannu ta dafe idon tana lalubawa taji kwayar na cikin shi, wani irin numfashi take ja tana son kukan ya kwace mata ko zai rage mata radadin da takeji, AbdulKadir na kallon ta, wani irin dana sani yake ji yana shirin lullube shi, alkawari yaiwa kan shi da ba zai sake taba wata mace da zata kasance karkashin igiyar auren shi ba, saboda yanda addini ya haramta mishi hakan, yanda al'ada bata yardar mishi da hakan ba, amman Nuriyya ta saka shi ya karya alkawarin nan da azumi a bakin shi.

"Na fada miki ki tauna maganar da zaki fadamun baki jini ba, uban me yasa ni da gidana ba zan ajiye kudi inda nake so ba? Me yasa zaki dauka? Me yasa zaki daukar mun? Rashin hankalin ki bai fada miki kudin zai iya kasancewa ba nawa bane? Ban nuna miki salary dina ba Nuriyya?"

Ba sosai take jin maganganun AbdulKadir din ba duk da hargowar da yakeyi kamar kiris yake jira ya rufeta da duka

"Abinda nake miki bai isheki ba sai kin daukar mun kudi? Kin dauka ban san kina zarar mun ba duk idan na ajiye? Ban miki magana bane saboda ina guje mana zuwa inda muke yanzun. Kinsan kudin wa kika dauka? Kinsan kunyar da kika sakani a ciki? Me kike so in ce mishi? Ni na dauki kudin? Ko ke kika dauka? Me yasa zaki mun haka?"

Zuwa lokacin radadin da take ji ya fara yin kasa, sai hawayen bakin cikin da suke silalo mata suna busar da tsoron shin da takeji, tunda ba mala'ikan mutuwa bane ba, ta dauka yafi karfin dubu arba'in da biyu da har zai zauna yana mata tijara akan su

"Ni na dauka, saboda na tambayeka ka hanani shisa nagani na dauka, me yasa kai baka fadamun ka ajiye kudin ba? Me yasa kai baka fadamun ba naka bane ba?"

Nuriyya ta tambaya cike da tsantsar rashin kunya tana saka wani murmushin takaici kwacema AbdulKadir din

"Akan dubu arba'in da biyune zaka mareni? Ni ba jaka bace da zan zauna kana jibgata"

Kai AbdulKadir ya girgiza, idan yana ganinta a gaban shi, idan taci gaba da magana zai daketa saiya ji wani daga cikin kasusuwan ta yayi kara alamar karyewa, zai daketa sai ta kasa ko nishi balle alamar kuka, ballantana ta sami bakin da zata tsaya tana kallon shi cikin idanuwa tana mishi rashin kunya, zai zabar musu abinda zai fi musu sauki, muryar shi a hankali ta fito kamar yana dandana duka kalaman shi

"Kije gida Nuriyya, kije gidan ku ki dan huta, nima in huta"

Sheqeqe Nuriyya take kallon shi, tana jin auren shi yau kamar sartse a makoshin ta, bambancin su da Anas na bayyanar mata

"Ni babu inda zanje babu wata shaida, sai inje musu saqaqa ince me? Yaji na yo? Ka sakeni mana sai in tafi da Hujja"

Ta karashe maganar tana watsa mishi wani kallo kafin ta dora da

"Ni ba kai bane mijin dana dauka na aura, ba haka Waheedah take fadarka ba, ba haka take nuna ka ba"

Da mamaki AbdulKadir yake kallonta

"Kin aureni akan abinda Waheedah take fada ne daman?"

Dan sosai yake son ya kwantar da bacin rai ya fahimci maganganunta, amman su kansu tunzura shi sukeyi, ba shi ta aura ba, mijin Waheedah ta aura shine abinda take son fada mishi.

"Me zanyi da kai? Wallahi AbdulKadir ba kai bane mijin da nake burin aure, kudinka da halayenka basuyi mun ba, ba zan iya zama da kai da wannan bakaken halayen ba"

Nuriyya ta karasa maganar tana jin zugin da kuncinta yake na marinta da yayi, garama ya saukake mata auren shi, Asma tace mata da kyawunta ta zauna namiji na wahalar da ita, kuma gaskiya ne, in yau ta gama iddarta tana da tabbacin samarine zasu dinga mata layi. Numfashi AbdulKadir yake ja yana fitarwa idan taci gaba da magana tabbas zai datse igiyar dake tsakanin su, maganganun da take fada din na kara tunzura shi sosai da sosai, dan bai kara sanin yanda zuciyar shi take doka mata ba sai yanzun da take fada mishi maganganun da yasa shi jin kamar ita din bata taba son shi ba. Abinda take tunanin auren shi zai samar mata shi take so. Abinda taga kamar auren shine ya samarwa Waheedah shi ta biyo.

Lokutta da dama kuma ba mata kawai ba, har maza na wannan wautar, ba a karin mata ta biyu ba maza kanyi kuskuren nan, a ta farkon ma, da yawa kan dauka auren wata mace shine cikar farin ciki, idan har baka da farin cikin da kaine silar samarwa kanka shi, cikar shi zatayi maka wahala idan wani ya zama sanadin farin cikin ka, ko da zama na yau da gobe bai taba wannan farin cikin naku ba, rabuwa ta kaddarar rayuwa ko mutuwa kan iya giftawa, sai kayi yaya? Aure kan samar da farin ciki, amman baya nufin duka farin cikin naka zai zamana a zagaye da shi auren. Mata sunfi kowa yin wautar nan, musamman a zamanin da muka tsinci kan mu a ciki.

Zamanin da yasa idan mace ta samu jinkirin auren da ba laifinta bane za'a dameta da yawan surutai har ya sata jin yin auren ne kawai hanya daya ta samun farin ciki, a wasu lokuttan kuma idan yarinya bata tashi cikin wadata ba, bata kuma da wadatar zuciya sai ta dora ginshiqin aurenta da samun farin ciki akan auren mai kudi, wasu kuma hange-gange shine yake halakar dasu, kinga mace cikin rufin asiri, kinganta daga sama da mijinta suna cin me kyau su sha me kyau, sai wannan kyallin ya haska miki shi, sai kiga kamar ta samu duk wani abu da shine burinki a zaman aure.

Bakisan yanda zaman aurenta yake tare da mijinta ba, bakisan me take jurewa ba, bakisan shima me yake jurewa a zama da ita ba, zamantakewa ta tsakanin ma'aurata sirrine da yake a lullube, abinda idanuwanki suka gani baya nufi shine komai, zai iya yiwuwa mijin wadda kika kyalla idanuwanki a kai bashi bane abinda burinki yake bukata. Karki so mutum dan abinda kike tunanin kin ga matar shi ta samu a tare dashi, ko da zatonki ya zama gaskiya ba kida tabbas ke zaki samu irin wannan a tare dashi. Duk da wasu matan ma na da laifin ganin mijin su nasu ne su kadai, wasu kance 'Ta auri mijin wata'. Dan kawai ta shiga a ta biyu.

Babu wani abu mijin wata daga lokacin da musulunci ya halarta karin uku bayan ke tun kafin wanzuwarki, mijinki nata ne itama. Wahalhalu da yawa mutane su suke dorama kan su ita, kwanciyar hankali baya zuwa idan baka neme shi ba. AbdulKadir ko kadan bai zaci ta aure shi da wata manufa da ta wuce ta son zama dashi kamar yanda yake son zama da ita ba, shisa ya juya yana ficewa daga dakin. Takawa yake dan ya fita daga gidan ya tafi wani waje, koma ina ne inda ba zaiga Nuriyya na wani lokaci ba kafin ta tunzura shi ya yanke musu hukuncin da su duka ba zai musu dadi ba.

Amman sai ta biyo shi, a falon Waheedah ta sake shi zai wuce ta gaban kitchen din shi tana kama mishi riga ta janyo shi saida ya juyo

"Nuriyyaa"

Ya sake kira cikin wani sabon kashedin, Waheedah taji takun tafiyar shi tun kafin ya fito, ta kuma ji muryar su dan tana hango kafar shi guda daya, da yake kujera ta saka ta zauna a kitchen din ta jingina bayanta da lokar kitchen din ta dora roba kan cinyarta tana gurza kubewa

"Ka dawo ka saukake mun wannan kaddararren naka, dan Wallahi ba zanje gidanmu babu wata shaida ba, ni dama nagaji da zama da kai..."

Numfashi AbdulKadir ya sauke ya kama hannunta yana banbarewa daga rigar shi yana fadin

"Kin gaji da zama dani right? Ki jirani Nuriyya, duk mu huta da rashin albarkar da take bin mu"

AbdulKadir ya karasa dan shi kan shi yanajin yagaji da bala'in nan, yanzun nan kuma yanajin rashin albarkar iyaye ce take bibiyar shi shisa a kasa da sati biyu komai ya jagule musu shida Nuriyyar, shima a gajiyen yake jin shi, maganganun kowa da suka fada mishi sun tabbata, hankalin su ya kwanta, sai su kalli idanuwan shi suyi mishi dariya su fada mishi da yaji maganar su daga farko da baizo inda yake ba yanzun. Dakin Waheedah ya wuce, Nuriyya na tsaye bakin kofar kitchen din Waheedah din tana girgije-girgije, ta wutsiyar ido Waheedah ta ganta, ko dagowa batayi ba, kubewarta take gurzawa a hankali tana bin karatun daya shigo na Suratul-Mulk cikin muryar Qari Sheikh Ghamdi da ke nutsar da abubuwan da batasan a tashe suke a tattare da ita ba.

Bata kalle su bane saboda basu bane a gabanta, saboda fadansu bai shafeta ba, asalima bata da alaka da shi. Nuriyya na nan tsaye AbdulKadir ya dawo da takarda a hannun shi, dayan da biro rike, fuskar shi kawai zaka kalla kasan ran shi a matuqar bace yake

"Gashi nan, na sake ki saki daya"

Runtsa idanuwan ta Waheedah tayi tana jiran taji ko zata girgiza tare da abinda ya girgiza daga kalaman sakin aure da AbdulKadir ya furta, asalima tana bude idanuwanta ji tayi kamar tare da sakin Nuriyyar ya dauke mata wani katon dutse daga saman kai. Nuriyya kuwa bata karbi takardar ba, kallon AbdulKadir din takeyi bata son sake hada wata hanya dashi ko ta wasa ce, wani auren zatayi na mai kudi inda ba za'ai mata tijara kan dubu arba'in da biyu ba

"Daka haifu cikin Hajja da ka karashe biyun ai, kaga duk sai ka hutar damu"

Sosai AbdulKadir yake kallon ta, a duniya babu wanda ya taba zagin shi haka, babu wanda ya taba kallon shi ya zage shi haka, saki daya ko uku, har a bayan zuciyar shi yanajin kamar yanda ya nuna babu wanda ya isa ya hana shi lokacin daya aureta, sai wata kaddarar da baiyi fata ba, haka yakejin yanzun ma babu wanda ya isa ya saka shi sake zaman aure da ita ko da su kadai suka rage a fadin duniya, saboda bayason gauraya yaran shi da matar da ta fada mishi maganganun da Nuriyya ta fada mishi. Takardar ya yaga yana komawa cikin

48 / 51