Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
tsaya da kafafuwanta tana ware mishi idanuwanta da suke cike da tsoro tukunna ya saki hannunta, yana mamakin yarinyar daya bari ce a gaban shi, komai ya canza tattare da ita banda farinta, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su akanta, tayi wani irin girma naban mamaki, farin da rashin kibar yana nan, sai dai za'a iya kiranta da budurwa, duk da a idanuwan shi tana nan a yar yarinyarta.
Waheedah kuwa dayan hannunta ta saka tana kama wanda Abdulkadir ya saki, zuciyarta naci gaba da lugude a cikin kirjinta, numfashinta ma kokawa take dashi cikin yanayin da kusanci dashi haka kadai yake bayyanawa, sosai ya canza mata, kuma ba askin kanshi kadai bane yasa fuskar shi canza mata, dan ya aske shi qasa sosai, Abdulkadir da yake tara suma, fuskar shi tai mata fayau da askin da akan kira buzz a turance. Ga tabbai qananu a fuskar da batasan yanda akai yaji su ba. Tabon da yake gefen goshin shine kawai tsohon abu a fuskar shi, dan tasan dashi tun kafin ya tashi.
Idanuwanta ta sauke zuwa wuyan shi, inda yake da wani dogon tabo daga gefen mummuqen shi zuwa wuyan, yana bace ma ganinta daga inda rigarshi ta lullube, wani abu na matsewa a zuciyarta, hannunta takejin yana mata kaikayi haka kawai, so take ta kaishi kan tabon da alamu suka nuna sabone sosai, ta kuma kirga duka qananun da take gani kan fuskarshi, yanda inya sake dawowa zata ga ko yaji wani sabon ciwon ko baiji ba. Kofar da Abdulkadir yaji an bude yasa shi dan juyawa, kafin ya sake juyowa yana mayar da hankalin shi kan Waheedah.
Yana mamakin yanda ta tsaya tana kallon shi, kamar tana son bude har tsokar jikin shi taga ko yana boye wani abu cikin kasusuwan shi, yana kuma mamakin tsoron da yake cikin idanuwanta bai hanata kare mishi kallo haka kamar ta aike shi ba, batun yanzun yake kula da ita ba. Ko abu su Zahra suke son tambayar shi ita din suke sakawa, haka zata kalle shi cike da tsoron shi da baya hanata yi mishi tambayar, karfin halinta bazai gaji da bashi mamaki ba. Baisan dariya mai sauti ta kubce mishi ba, saida yaga yanda ta hadiye wani abu da yafi karfin yawu
"Hamma..."
Ta furta, muryarta can kasan makoshi, idanuwa Abdulkadir ya kafeta dasu, yana sata sake hadiye wani abu da take ji tokare da makoshin ta. Zata rantse tanajin zuciyarta ta yunkuro mata da tambayar da ta jima tana ma iska a dakin su, tunda shidin da take son tambaya baya nan.
"Shekara daya akace Hamma.... Shekara daya akace zakayi kazo... Me yasa ka dade?"
Wata gajerar dariyar Abdulkadir ya tsinci kanshi da sakeyi
"Shine gaisuwar?"
Ya bukata, muryar shi na nutsar da gudun zuciyarta. Ta dauka girman shi zaisa muryar shi ta canza ko ta kara budewa, tana nan yanda tasanta, shidinne kawai ya canza a bayyane. Dan murmushi taji ya kwace mata
"Ina wuni..."
Kai Abdulkadir ya girgiza kawai
"Ki kawomun abinci"
Ya fadi maimakon amsa gaisuwarta, ya juya yana sa hannu ya tura kofar, akan ce idan ka girma, rana da abubuwa nasa haskenka yadan dishe. Bayajin ko wahala zatasa Waheedah dishewa, da tunanin farinta da yakeji cikin idanuwan shi har lokacin ya shiga dakin yana fadin
"Uban waye ya kunna kida ya kuma kulle kofa daga ciki?"
Ya karasa maganar yana kare musu kallo, dakin kusan cike yake da mutane, bakin fuskar da bazai wuce dukan su ahalin Bugaje bane ba, dan ga kamannin nan yana gani, wasu kuma ya gane su.
"Ubanka ne, nace ubanka ne ya kunna"
Abdulkadir yaji muryar Yassar cikin kunnuwan shi, kafin yaji hannun Yassar din kan wuyan shi dayai ma wani irin riqo da yasa Abdulkadir din riqo hannun Yassar daya kasa banbarewa
"Hamma zaka kasheni...me yasa kakemun hakane a gaban yara... Ka sakeni dan Allah"
Abdulkadir yake fadi, yana raina karfin shi da yake tunanin ya karu saboda yanayin horon daya samu a makaranta.
"Daga zuwan ka, shisa babu wanda yai kewar ka"
Cewar Yassar daya saki wuyan Abdulkadir din yana tallabe mishi bayan kai
"Dan banzan yaro kawai"
Idanuwa Abdulkadir ya sauke kan Salim da yake kallon shi yana murmushi
"Idan na karaso saina tabbatar labbanka sunyi kumburin da zaka kwana biyu bakai murmushi dasu ba"
Mikewa Salim yayi yana wucewa dakinsu, ba akan shi Abdulkadir zai fara sauke kurar NDA daya kwaso ya shigo da ita ba. Dariya Yassar yakeyi, Abdulkadir din ya wuce bayan ya watsama duk wani da suka hada ido dashi a cikin dakin harara. Dakin shi ya wuce yana murda kofar yaga ta bude. Shiga yayi da takalman shi, dakin a share yake, sai dai akwai kaya kan gadon, juyowa Abdulkadir yayi da nufin zuro kai yaji wanda ya shigo mishi daki ya zuba mishi kaya akan gado.
"Nine, ni nake kwana a dakin da aka fara hidimar biki..."
Yassar ya fadi muryar shi dauke da gajiya da rikicin Abdulkadir da baya karewa. Yana yawan zuwa dubo shi a makarantane, tun ranar farko da yaje yaga halin da yake ciki, yasha wani irin duka ga zazzabin da yake da tabbacin dukanne yasa mishi shi, gashi ya rame sosai, daya dawo gida har kuka yaima Abba da fadin yaje ya dawo da Abdulkadir din, tunda zama sojan ba wahayin shi aka saukar mishi ba. Dan yana da tabbacin rashin kunya da bakin shi zaisa su mishi dukan da zai ajalin shi wata rana. Abba yace shi yaji zai iya, abar shi, kilan sanadin sojan yasashi fara ganin kan mutane da gashi.
Amman hankalin Yassar din ba'a kwance yake ba, bazaiki ace kullum yaje ya duba halin da yake ciki ba, yaji dadi ma yanzun da wayar hannu ya yawaita, ko bakaje kaga mutum ba, zakaji muryar shi, amman zai karya idan yace baya addu'ar kar Abdulkadir yai abinda zasuyi mishi dukan mutuwa a NDA din nan, dan yaga alama abin babu sauqi.
"Kaine mutum na farko da zan kulle ko kwana biyune Hamma, saboda kana mun abinda kake so a gaban yara"
Abdulkadir ya fada babu alamar wasa a muryarshi, hannu yaga Yassar ya kawo, da sauri ya rufe kofar yana dariyar daya manta rabon da yayi irin ta. Kan gadon ya karasa yana kwanciya, kafafuwan shi a kasa, duk da ba takalman bane suka hana shi dora kafafuwan kan gadon, ra'ayin kwanciyar a haka kawai yake ji. Iskar gida kanta daban take data NDA, gyara kanshi ya sakeyi, farar rigar Yassar dake gefe nasa Waheedah fado mishi, badan kalar nata farin iri dayane da rigar ba, ko kusa basuda alaqa, kawai ya tsinceta a ranshi ne, yafi alaqanta hakan da jiran da yake ta kawo mishi abinci, dan yunwa yake ji ta fitar hankali.
**
Kitchen ta koma, tana jinta kamar akan iska take tafiya, tanajin yanda zuciyarta ta lullube mata wani nishadi da idan tabari ya fito fili tsalle-tsalle zata fara kamar karamar yarinya, ba tana cikin kunci bane a shekaru biyun nan, sosai take zagaye da yan uwanta da suke sakata farin ciki, amman nishadin da take ji yanzun ganin Abdulkadir dinne kawai yake bayyana shi. A litattafan Hausar data karanta taga soyayya kala daban-daban, shisa ta sakama kusancin da takeji da Abdulkadir ayar tambaya, dan har yanzun batajin yana da suna a zuciyarta. Dan abinda takeji akan shi yasha banban da duk wata soyayya da take gani a litattafai.
Abinda takeji akan Abdulkadir batasan tun yaushe ya fara ba, kawai bude idanuwa tayi a kusa dashi taji zuciyarta na wata irin dokawa, idan sone ya kamata ta fara tunanin koshi yanajin kalar kusancin da takeji akan shi, amman har kasan zuciyarta bata damu dako yanaji ko bayaji ba, asalima tanajin yanda nata ya ishesu su biyun. Kuma tana jin tsoron shi kamar yanda su Zahra suke jin tsoron shi. sai dai akwai wani karfi da yake tasowa daga zuciyarta koda yaushe yana danne tsoron in tana son magana dashi.
Da murmushin daya kasa barin fuskarta take zuba mishi shinkafa da miyar da Mami ta girka, ta kuma san saboda Amatullah ta dafa, dan ba zataci abincin da batasan waya dafa ba, haka zata wuni tana shan shayi, kyankyamin da yarinyar take dashi har mamaki yake bama Waheedah. Salak ta zuba mishi a gefe da su tumatiri da ta yayyanka harda kokomba. Batasan waye da waye baici abinci ba, amman naman dake miyar kusan fiye da rabi ta zuba ma Abdulkadir din.
"Tunda shi baqone..."
Ta furta ma kanta, Allah kadai yasan kalar abincin da suke ci acan, gara yau yasan yazo gida. Babban faranti ta samu ta dora karamin a ciki tana rufewa, tukunna tasa cokali a gefe. Ruwa ta daukar mishi da kofi duk tasa cikin farantin tukunna ta dauka tana ficewa zuwa bangaren su Abdulkadir din, saida ta kwankwasa suka ce ta shiga tukunna ta cire takalmanta a wajen ta shiga.
"Ina Hamma Abdulkadir?"
Tai tambayar tana kallon Naziru daya nuna mata dakin Abdulkadir din da dan yatsan shi, yana mayar da hankalin shi kan kallon da yake, dan shi kadai ta samu a falon ma, da alama kowa ya fice hidimar gaban shi. Abinda bata sani ba shine Abdulkadir ya fito ya zare wayoyin speakers din da suka kunna kidan dashi, da yaji bai hana kidan yi ba, yaje ya raba extension din da kayayyakin suke jone da socket din dakin gabaki daya yana zubarwa a kasa ya juya ya koma daki baice ma kowa komai ba. Yassar ne yace su hakura kawai su kyale shi, shisa kowa ya fice daga dakin, shi kanshi Nazir din sai gaban tv din ya koma sosai dan ya rage maganar tayi kasa yanda kunnuwan shine kawai zasuji.
Wucewa Waheedah tayi, tana kwankwasa dakin
"Shigo..."
Abdulkadir din ya fadi, a hankali ta tura kofar tana shiga hadi dayin sallama, tashi zaune Abdulkadir yayi yana kasa hakuri data ajiye mishi farantin, yasa hannu ya karba, a kan cinyar shi ya dora yana budewa hadi da saka cokali a ciki ya fara cakuda gefe, tukunna ya diba yana zubawa a bakin shi. Yanda ya sauke numfashi nasa Waheedah jin da tana da iko kullum saita aika mishi abinci Kaduna. Tasan ya kamata ta tafi, amman kafafuwanta kamar an dasasu a wajen, bayanta ma ta jingina da bangon dakin tana kallon yanda yake cin abincin da sauri-sauri. Abinci ya mishi dadi sosai, bai damu da tsayuwar da Waheedah din tayi ba, ko kofar dakin data bar mishi a hangame. Haka kawai yaji ya kasa ce mata tsayuwar me take mishi a dakin har lokacin.
Batasan meyasa takejin son mishi magana haka ba, jikinta har dumi yake dauka da yanayin son mishi maganar
"Dame kaji ciwo Hamma?"
Ta tambaya, yanda yadan tsaya, kafin yakai cokalin abincin bakin shi yana juyowa ya sauke mata kananun idanuwan shi yasa zuciyarta dokawa cike da tsoron shi da bai hanata sake fadin
"Yaushe zaka tafi?"
Abincin Abdulkadir yake taunawa a nutse, inda wani ne ba ita ba, zaiji kamar ya raina shi da yawa da har zai tsaye yana jero mishi tambayoyi, amman a muryarta yake jin yanda tsakaninta da Allah tayi tambayar, babu raini kowani abu, kawai tana son sani din, amman daga haka raini yake farawa, shiru yayi ya kyaleta yana cigaba da cin abincin shi
"Sune basa barin ku zuwa? Ko kaine kawai kaqi zuwa? Hamma kaga wani tabon fa har a gefen kuncinka... Dame kaji ciwuka haka dan Allah?"
Waheedah taci gaba da jero mishi tambayoyin da take jin suna fito mata a sauqaqe, kamar sun shekaru masu yawa a tare dashi, kamar tayi sabon da zatayi labari dashi mai tsayi batare da fargabar komai ba haka take jinta, duk da a kasan zuciyarta wani abu yake fada mata ba amsa zata samu ba, itama ba tana tambayar shin bane dan ya amsata, tana tambayar ne kawai saboda tana son magana dashi ko da bazai amsa ba, indai yana jinta ya isheta.
"Ko kun fara fita aikin soja ne?"
Ta bukata, tana ware idanuwanta, zuciyarta cike da wani sabon tsoro da tunanin abinda hakan yake nufi
"Hamma kun fara zuwa yaqi ko? Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...oh Allah na... Ko harbine tabon wuyanka? Oh Allah na"
Cokalin Abdulkadir ya ajiye cikin abincin shi yana fadin
"Fitar mun daga daki Waheedah..."
A daburce tace
"Na'am..."
Dan tunaninta yayi nisa cikin kalar tashin hankalin da take gani a fina-finan sojojin da take cikin kallo yanzun duk idan ta samu lokaci. Yazid kanbar mata laptop dinshi inya samo, saita kalla a ciki.
"Ki fitar mun daga daki kafin in watsa miki mari"
Abdulkadir ya fadi can kasan makoshi, saboda dariya na gab da kwace mishi, yana kallon tsoron da ya cika idanuwanta kafin ta fice da sauri kamar zata fadi, saida ya tura kofar tukunna wata irin dariya ta kwace mishi, yana mamakin yanda Waheedah ta kasance mai hankali kuma marar hankali duk a lokaci daya. Hannu yasa ya shafi tabon da haukanta yake mata tunanin na bindiga ne.
"Wai yaqi..."
Ya fadi yana karayin dariya
"Wallahi Waheedah bata da hankali... Yaqi fa"
Abdulkadir din yake maimaitawa har lokacin yana dariyar da yakejin fitowarta tun daga zuciyar shi. Abincin shi ya karasa cinyewa tas yasha ruwa, tukunna ya ajiye farantin a kasa, gani yai uku da kusan rabi, hakan yasa shi mikewa ya kwance takalman kafar shi, tukunna ya shiga bandaki dan ya dauro alwala, fuskar shi ya kalla a mudubi, murmushin da yake bayyane a jikinta nasa shi janye idanuwan shi daga kan mudubin, dan yanayine da ya zame mishi baqo, ya kwana biyu baiyi nishadi irin nayau ba. Tsintar kanshi yai da murmushin har ya idar da alwala ya fito, waje ya samu ya zauna yana jira a kira sallah dan ya wuce masallaci.
*
Dinner zasuyi da daren ranar, duk da Abba ya nuna duk wannan bidi'ar bason ta yakeyi ba, haka ya hakura ya kyalesu ganin sun kafe. Dogayen riguna ne sukai anko iya su yan cikin gidan, material din wine color, yayi matuqar kyau. Mami tai ma Nuriyya ankon da duk sauran dinkunan da taima Waheedah. Yanzun ma tare duk suka fito da za'a tafi, yanayin dinkin ya zauna ma Nuriyya sosai, da wahala ta gitta baka sake kallonta ba, ko dan kwalliyat data sha, kusan duka yan gidansu Waheedah din Nuriyya tai musu kwalliyar su, ga kunshi ansha, kamar sune amaren. Nuriyya ta rataya mayafinta a kafada, yanda su Zahra ma sukayi.
Itakam Waheedah fuskarta fayau take, banda hoda data murza sai Vaseline data shafa ma labbanta, daurin dankwalinta ma mai sauqi tayi, saidai kalar kayan ta amshi farar fatarta, ta yafa qaton mayafinta a kafadunta duka biyun, duk da haka wani iri takeji, wuyanta da yake a bude, itakam wannan mayafin asarar kudine, dan tasan ana gama bikin zata ajiye shi, tafi gane hijabanta. Motar da za'a dauke su ciki ta cika tsaf, bata samu waje ba.
"Yanzun dan Allah saiku tafi kubarni?"
Waheedah ta fadi cikin sanyin murya, tana dorawa da
"Nuriyya dan Allah ki rungumeni..."
Dariya Nuriyya tayi
"Ki yamutsemun riga? Wallahi bazai yiwu ba"
Sake marairaicewa Waheedah tayi
"Toni ki tashi in rungumeki"
Maryam, yar yayan Abba dake zaune gefen Nuriyya ta kwashe da dariya.
"A wacce cinyar zaki rungumeta? Mansur muje dan Allah..."
Maryam ta karashe maganar tana miqa hannu ta ja murfin motar dan taga alamar in suka biyema Waheedah zasu kara bata lokaci, ba zata rasa wanda zata biyo ya kawota ba. Kuma za'a daddawo daukar sauran mutane dole daman. Waheedah din kanta tasan hakan, kawai dai taso ta bisu dinne tunda duk sa'anninta na cikin motar, ga Nuriyya kuma, kafin dai ta gama sanyin jiki duk sun shige, tsaye tayi a wajen tana jin idanuwanta sun cika da hawaye.
"Waheedah ke baki tafi ba?"
Taji muryar Yazid, juyowa tayi, kwalla cike da idanuwanta
"Wai ba waje..."
Dariya Yazid yayi, yarinyar bata da wahalar kuka ya kula, sai dai akwai wani abu tattare da sanyin halinta da yake ji har kasan zuciyar shi.
"Yanzun Abdulkadir zai fito, saiku wuce tare...ina zuwa zanyi abu"
Yazid ya karasa yana wucewa da sauri, aikam Abdulkadir dinne ya fito, jikin shi da shadda ruwan toka mai cizawa, ta manta ranar karshe data ganshi da manyan kaya, sosai taga yai mata kyawun da taji yasa zuciyarta ta matse waje daya. Sai kamshi yake zabgawa, hular da take hannun shi ya saka saman kan shi yana karasowa inda take, ya miqa mata wallet din shi da agogo yana da links din hannuwan rigar
"Riqe mun..."
Hannuwanta biyu ta ware mishi ya saka a ciki, yana daukar link guda daya ya fara sakawa a jikin hannun rigar yana zabga tsaki
"Meyasa Hamma zaimun wannan hannun shirmen?"
Da sauri Waheedah tace
"Kawo in sa maka?"
Kananun idanuwan shi ya kara kankance mata
"Kin iya?"
Kai ta daga mishi, kayan hannunta ya karba, yana miqa mata dayan hannun shi, kamawa tayi tana dan rausayar da kanta gefe
"Saika dago hannun ka"
Ta fadi a hankali, gyara mata hannun Abdulkadir yayi yana kallon yanda ta nutsu tana saka mishi link din, sai yaga kamar tafi dazun yi mishi haske, ko dan kwan fitilar da ya haske mata fuskane, bai sani ba.
"Dayan hannun..."
Cewar Waheedah tana jin wani gajimare na mata yawo a kanta. Miqa mata Abdulkadir yayi yana ware mata tafin hannun shi ta dauki link din. Saka mishi tayi, sai ya tsinci kanshi da miqa mata agogon, karba tayi ta daura mishi, wallet din ya miqa mata, yasan yana da aljihu a wando da rigar kayan da suke jikin shi, kawai yanajin bata ta riqe mishi ne.
"Kin shirya? Muje?"
Ya tambaya, tana daga mishi kai, harya numfasa yai mata maganar ta bude bakinta ta amsa shi, saiya tuna Waheedah ce, ta saba amsa mishi magana da kai, saboda shiya saba kyaleta duk idan tayi. Wucewa kawai yayi tana bin bayan shi, saida suka karasa tukunna taga dayar motar Abba ce zasu fita a ciki, zagayawa Abdulkadir yayi yana bude motar ya shiga, harya kunna baiga alamar Waheedah zata shigo ba, numfashi ya sauke yana rasa kalar Waheedah, kafin ya miqa hannu ta ciki ya bude kofar, yana ganin tayi baya tana murza hannunta da alamar ya bugeta.
"Sai nace ki shigo?"
Ya bukata a fadace, yanajin gajiyar da baisan daga inda ta fito ba. Idanuwanta take ware mishi, dan taji ba cayai ta shiga din ba, tambayar ta yayi, kai ta girgiza mishi a hankali, da alama tana jiran ya bata umarni ta shiga din tukunna, numfashi ya sake saukewa a karo na farko, bayajin zai iya masifa
"Shigo Waheedah..."
Ya