Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 51

18K to 21K   out of 152.3K words

kiran duk wani sunan Allah dazai zo bakinta ko zuciyarta zata daina rage gudun da takeyi. Tana sake damke hannun Waheedah hadi da janta dan su kara sauri...!

*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732: ©️
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com

*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*

05

Da yawan lokutta idan aka tashe su daga makaranta sukan fi mintina sha biyar suna jira kafin azo a dauke su. Yazid yafi kawo su yazo ya dauke su, amman kowa in za'a tambaye shi zaice yafi son Mubarak yazo, dan duk gidan babu dan raha irin shi, kudin duk da yake aljihun shi kuma ranar akan su zai karar, duk abinda zasu nuna suna so sai an tsaya an siya. Yanzun basa komawa lokaci daya da Abdulkadir, saboda yana tsayawa extra lesson din da zai taimaka mishi wajen zana jarabawar aji shidda.

Yau din kuwa sa'a sukaci Mubarak ne yazo daukar su, kowa ka duba fuskar shi kar take

"Ina Commander din naku?"

Ya bukata yana sa Amatullah jan wani numfashi a tsorace

"Hamma..."

Suka kira kusan gabaki daya, dariya Mubarak yayi

"Bansan ya akai baiji sunan nan ba har yanzun"

Jinjina kai Zahra tayi, tana hasaso kalar drama din da za'ayi duk randa yaji suna kiran shi da Commander din nan. Mubarak ya rigada ya juya motar ya hango mai yalo a tsallaken titi

"Wazai siyo mana yalo?"

Ya bukata yana kallon Waheedah dake zaune a gaba, dan kafin ma ta ja kafarta cikin sanyin tafiyarta da mutane da yawa zasu iya kuskurewa da yanga sun gaggama shiga motar, gaba kadai ya rage. Jakarta ta ajiye tana cewa

"Kawo a siyo.... Wanne iri? Farin?"

Daga baya Nazir yace

"Nidai bana cin fari..."

Yana sa Mubarak juya ya harare shi

"Kaji mun yaron nan fa, nace zan siyo dakai ne?"

Yana zaro dari biyu ya miqama Waheedah

"Kowanne na dari..."

Motar ta bude ta sauko, baya tadan yi tana tsayawa daga bayan motar, abubuwan da take tsoro a rayuwarta basu da yawa, tsallaka titi na daya daga cikinsu, bataso tai magana ne su isheta da tsokanar su da bata karewa shisa ta karba, amman zuciyarta dukan uku-uku kawai take. Dakyar ta iya tsallaka hannu daya, tana tsaye a tsakiya, ganin motocin da mashina take suna wucewa da gudun da take tunanin ko suna da niyyar tashi sama ne. Banda zare idanuwa babu abinda takeyi, juyawa tayi dan ta tsallaka ta koma, amman abin ya gagara, data sani tace wani yaje, yanzun take jin gara tsokanar su da wannan tashin hankalin da take ciki.

Yana daga dayan bangaren shida Imran da Nawaf da suka jashi suna fitowa dashi, kasancewar basa fara extra lesson din sai biyu da rabi cif, ana nada rabin awar dan sallah da cin abinci.

"Lokaci yana tafiya, wanne iskanci ne wannan wai? Ku siyi kome zaku siya mu koma dan Allah"

Cewar Abdulkadir yana duba agogon dake manne a hannun shi. Imran ne ya kalle shi, dan Nawaf bai niyyar asarar bakin shi ba

"Karka daga mana hankali Malan, ka koma abinka mana"

Wani kallo Abdulkadir ya watsa ma Imran din

"Ai kuma karya kake, ku biyun, yanda kuka janyoni na fito haka zamu koma tare..."

Ya karashe maganar yana gyara tsayuwar shi, kamar ance ya daga idanuwan shi, ya kuwa sauke su kan Waheedah, duk da tana juyawa zuwa dayan bangaren hadi da bashi baya bai hanashi ganeta ba, akwai farare a makarantar sosai, harda yaran kwarori da suke makarantar, yana tunanin da kalar farin sune kawai zai iya kwatanta na Waheedah, yanzun ma yanda ya shigar mishi idone yagane itace, sai kuma yanayin sirantakar. Sake kankance kananun idanuwan shi yayi ganin ta sake juyowa ta fuskanto inda yake tsaye, da alama a rikice take. Apple din dake hannun shi ya juya yana tunanin abinda ya tsallako da ita titi.

Bai amsa Imran da yake tambayar shi ya sake shawarar tafiya babu su ne, dan abarba suka siya ana fere musu. Titin ya tsallaka yana takawa harya karasa inda take. Saboda a daburce Waheedah take ko kula batayi dashi ba

"Uban me ya tsallako dake?"

Muryar shi ta daki kunnuwanta tana tsoratata, baya tayi saboda yanda zuciyarta tai wani irin tsalle, da zafin nama Abdulkadir ya riko hannunta daya yana mata wata irin damqa kamar zai karyata, bakin shi da take ganin yana motsi ya tabbatar mata da ba magana kawai yakeyi ba, fadan shi yake mata da baya karewa, amman batajin shi, ta tsorata har cikin ranta, da bai riketa ba da labarin ya banbanta, tana jin yajata suna tsallakawa bangaren titin daya baro. Hannunta ya saki yana kai nashi hannun ya dan goge wani abu a goshin shi da yake jin ya taru.

Badan yanda zuciyar shi take dokawa ba daya dauke ta da mari

"Me zakiyi a tsallaken titi?"

Ya bukata yana kafeta da idanuwan shi da suka saukar mata da wata irin nutsuwa

"Ya... Yalo zan siya"

Numfashi Abdulkadir yaja yana saukewa, wani irin yanayi yakeji da bayason alaqanta shi da tsoron da yaji, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su, sam bayason tuna yanda ta kusan fadawa titi

"Hamma Mubarak yace in siyo..."

Waheedah ta fadi a tsorace, ba tsoron titin data kusa fadawa ba, tsoron yanayin da take ganin Abdulkadir din a ciki, yanda ya dago da idanuwan shi yasata kai hannuwanta duka biyun tana rufe kuncinta dasu, wani irin dogon kallo yai mata yana kai hannun shi wajen fuskarta, matsawa tadanyi a tsorace tana rufe idanuwanta gam, cikin yanayi biyu zuciyarta take dokawa, yanda take cike da tsoron shi, da kuma yanda takanyi duk idan yana kusa da ita haka. Dari biyun da ke cikin hannunta yakai yan yatsun shi yana fisgewa hadi da nufar inda mai yalon yake, baisan me take tunanin zaiyi ba, dukanta ne karshen abinda yazo mishi.

Mai yalon ya mika ma kudin yana tsayawa

"Na nawa?"

Mai yalon ya tambaya

"Na duka..."

Kai ya jinjina ma Abdulkadir ya dauko leda hadi da sake fadin

"Wanne iri"

Wani irin kallo Abdulkadir ya watsa mishi, yalo duk ba yalo bane da zai tsare shi da tambayar banza

"Malan ka sakamun yalo, karka isheni da tambaya dan Allah..."

Ya karasa maganar da jan karamin tsaki, daya miko mishi ma a hasale ya karba, ranshi a bace yake jin shi. Waheedah na tsaye inda ya barta, ta sauke hannuwan ta daga kuncinta saboda bataji marin da tai tsammani ba. Batare da yace komai ba yasa dayan hannun shi ya damqi nata dashi yana janta batare da yace komai ba, hannun nashi tabi da kallo, wani irin yanayi na lullubeta, kafin ta kalli fuskar shi da take a nutse, yanda wani abu ke motsi a kuncin shi dake nuna alamar ciza hakoran shi yake ta cikin bakin shi tasan ranshi a bace yake. Yan gidan duka sukan ce kullum ma ran Abdulkadir a bace yake.

Tasan ba dariya yakanyi ba, in kuwa yayi takan ga baquntar yanayin akan fuskar shi, amman ita tana gane idan ranshi a bace yake ko ba'a bace yake ba, batasan ya akai take ganewa ba, tunda ta taba gwada yi musu bayani sau daya suka sakata a gaba da dariya bata sake kwatantawa ba. Fuskar shi take kallo tana binshi duk inda ya jata, batasan sun tsallaka duka titin biyu ba saida ya saka ledar yalon a hannunta yana sakin hannun tukunna.

"Idan na sake ganin ko da wasa kin nufo kusa da titi saina zane jikin ki Waheedah, Allah saina zane ki, kina jina ko?"

Kai ta daga mishi a hankali, bai jira amsarta ba, duk cikinsu ita kadaice baya damuwa da saita mishi magana da bakinta, inta ware mishi idanuwanta haka tana kallon shi da farar fuskarta yasan ko kasheta zaiyi ba iya magana zatai ba. Dan haka ya juya yana zagaya wa inda Mubarak ya fito daga motar ya tare mai yoghurt yana zaba yana sakawa a mota

"Hamma idan kasan zaka siyi wani abu tsallaken titi ka daina aiken yara, in ba zaka tsallaka da kanka ba ka hakura"

Dago kai Mubarak yayi yana kallon Abdulkadir din da in zasu gwada tsayi a kafadar shi kan shi zai tsaya. Duk da ba wani nisa bane a tsakanin su ta bangaren shekaru, amman ya girmi Abdulkadir din, yanda yai tsaye yana bashi umarni yasa shi yin dariya da fadin

"To Abba..."

Cikin ido Abdulkadir ya kalle shi

"Da gaske nake, karka sake aiken su tsallaka titi, bana so..."

Kai Mubarak ya daga mishi, dan bazai iya masifar Abdulkadir din ba, juyawa yake da shirin tafiya, Mubarak yace

"Kazo ka dauki yoghurt"

"Bana sha..."

Kallon shi Mubarak yayi

"Daga abin arziqi?"

Daquna fuska Abdulkadir yayi

"Nima bance wani abu ba, bana sha kawai nace"

Hannu Mubarak ya daga mishi

"Naji, sai anjima, jeka abinka"

Tafiyar kuwa yayi yana nufar hanyar da zata mayar dashi cikin makarantar. Waheedah kuwa dakyar ta iya jan kafafuwanta ta shiga cikin motar. Kan sit din da Mubarak ya tashi ta dora mishi ledar yalon, hannunta take murzawa inda take jin na Abdulkadir har lokacin, zuciyarta na mata wani irin yanayi da ta kasa fahimta. Har Mubarak ya shigo ya bama kowa yoghurt din shi, tata karba tayi tana zage aljihun jaka ta jefa a ciki, haka yalon ma, dan ji take sun takura yanayin ta, kanta ta jingina da jikin motar tana lumshe ido, kafin ta daina jin hayaniyar da suke a cikin motar dan ta bace cikin duniyar tunani.

Jikinta gabaki daya a sanyaye take jin shi, banda yanayin fuskar Abdulkadir din lokacin daya rikota babu abinda take hasasowa, so take taji ta a kwance a daki, ta janyo bargo ta rufe jikinta gabaki daya har hakanta, ba zataki bacci ya dauketa cike da tunanin shi ba, dan a dakine kawai take da tabbacin babu wanda zai uzzura mata balle ya katse mata tunanin ta.

"Waheedah..."

Taji an kira ana tabota, juyawa tayi fuskarta babu walwala

"Dallah anata miki magana, mu kwance kai yau, kinga alhamis babu islamiya, gobe in Allah ya kaimu sai muje kitso gabaki dayan mu..."

Da sanyin murya tace amsa Zahra da

"Kuje kitson ku, Nuriyya zatai mun"

Hararta Zahra tayi

"To mai Nuriyya data iya kitso, sai kita zuwa ai"

Tana kallon Amatullah ta tabe baki, juyawa tayi ta gyara zamanta tana kyalesu, batasan me Nuriyya ta tsare musu da basa sonta har haka ba, ko wani abin ake in tace da Nuriyya zatayi takan ga kiyayya shimfide a fuskarsu, musamman Amatullah da takance tama fi son Nuriyya akan ta, bata raba duk wani lokacin da ta samu tare da ita saida Nuriyya, zata iya cewa dukka yan uwan nata kan yi mata wannan mitar, kamar suna kishi da Nuriyya din, dariya takan yi musu kawai, yau kam ko dariyar basu samu ba, dan tunanin Abdulkadir ya addabeta fiye da kowanne lokaci, dashi manne a kasan zuciyarta kuma suka karasa gida.

**

Bai shigo gidan ba sai gab da Magriba, bangaren su ya wuce yana tura kofar dakin da sallama ya shiga, kafafuwan shi da jikin shi cikin shigar kayan ball. Bangaren da gabaki daya mazan gidan suke daban yake, daka shiga falo zaka samu da kujeru a ciki, sai kofofin dakuna a zagaye, dakin bacci hudune a cikin wajen manya-manya, sai karamin nashi da yake tunanin anyi shi na baki. Da shi da Mubarak suke kwana, kafin ya tattara yana bar mishi dakin, bai damu da kwana shi kadai ba, asalima hakan na mishi dadi, da dakin ya kasance nashi ne shi kadai, amman baisan dalilin da yasa kowa yake gudun hada daki dashi ba, abin na bata mishi rai wani lokacin, ko kujera mai zaman mutum biyu ya zauna da wahala kaga wani ya zauna kusa dashi.

Kusan su hudu yagani a falon suna kallo, baibi takan su ba, kitchen ya fara wucewa ya bude fridge din da yake kitchen din ya dauki ruwa, ba wani amfani suke da kitchen din ba, banda kwanonin da in suka shiga cikin gidan sukan zo su jibge, sai ya gaji da ganin su yake sa wani ya kwashe ya mayar cikin gidan. Dakin shi ya wuce yana cire kayan jikin shi ya shiga bandaki, ruwa ya watsa cikin hanzari dan yasan ana gab da kiran sallah ya dauro alwala ya fito, kananun kaya ya saka, dan Hajja harta gane shi, in ya saka manyan kaya to sallar juma'a zashi, kayan duk da za'a dinka musu manya da sallah, yana dawowa idi yake zare su daga jikin shi.

Fitowa yayi yana jin ana kiran sallah, har yakai kofa ya juyo yaga su Yasir a zaune.

"Kuna ji ana kiran sallah, kuna kara gyara zama"

Yassar ne ya dago daga cikin kujera yana kallon Abdulkadir din

"Ka wuce abinka kai dai..."

"Badai kyau wallahi"

Cewar Abdulkadir din, dan yagane Yassar ne a yanayin shi, kusan duk gidan zai iya kwantanta zafin ranshi dana Yassar ne, baya tunanin ko Mama tana iya banbance su in bada hakan ba, kamannin su ya baci, gashi ya rasa jarabar da tasa komai iri daya sukeyi, har askin kansu, in suna tare ka kira daya su dukan su suke juyowa. Da zafin ransu ne kawai ake ganewa.

"Karka bari in taso Abdulkadir..."

Yassar ya fada, amman ko motsi Abdulkadir baiyi ba

"Hamma Yasir kaima biye mishi zakayi? Dan kun fito a yan biyu bazai sa a rufeku a kabari daya bafa, wallahi jibgar banza zaka sha..."

Mikewa Yassar din yayi yana fara takawa inda Abdulkadir din dayake dariya yake tsaye, sai dai kafin ya karasa harya bude kofar ya fice da gudu

"Dan banzan yaro marar kunya, daka tsaya ai"

Yassar ya fadi, yana sa Yasir yin dariya

"Banda kai a gidan nan, banga wanda Abdulkadir yake wasa dashi haka ba"

Mubarak ne ya jinjina kai yana miqewa

"Halin sune yazo daya shisa, yaron can ko tsokanar shi na gwada yi zaice mun bayaso, zansa yara suji su raina shi"

Dariya kawai Yassar yayi yana wucewa yabar su anan, banda Yasir da suka fito rana daya, bayajin akwai wanda yake ji har kasan ranshi a gidan kaman Abdulkadir, duk da kusancin su baya hana yai mishi rashin kunya sosai, amman kuma shi kadai yake daga ma Abdulkadir hannu ya sauke batare da Abdulkadir din ya gwada ramawa ba, sai dai ya sake fadar maganganu ya wuce, ko rikici akeyi dashi, Yassar din ake kira dan shi kadai yake iya raba rikicin Abdulkadir. Alwala duk sukayi suna fita masallaci tare.

*

Abdulkadir bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i, bai samu kowa a falon ba sai Yassar da yake cin abinci, kamshin da wake da shinkafar da ya hango yaji busashen kifi yake yasa shi sanin girkin Mami ne, dan duk ranar baici abinci a gidan ba, da safe ya rigasu fita makaranta dan shi yake da duty, acan ya siyi abinda ya sakama cikin shi, daya dawo kuma sunje gidansu Imran, acan sukaci abinci rana. Cikin shi yaji ya murda da yunwa, ya karasa yana zama kusa da Yassar din, hannu yakai zai dauki cokalin Yassar ya doke hannun shi

"Tashi ka zubo naka"

Daquna mishi fuska Abdulkadir yayi

"Hamma mana..."

Abincin Yassar ya kara diba ya cika bakin shi yana fadin

"Zanci ubanka wallahi"

Sake daquna fuska Abdulkadir yayi

"Saika dinga zagina, ko a gaban yara saika zageni, salon kasa yara su rainani. Ni kam bana so kana mun irin haka"

Hannu Yassar yasa yana kai mishi duka saboda bakin shi da yake cike da abinci, miqewa Abdulkadir yayi, duk gidan babu wanda yake mishi irin wannan cin mutunci sai Yassar, ya rasa kuma menene tattare da Yassar din da yakan sashi daga mishi kafa tunda ba tsoron shi yake ba, baya tunanin idan fada ya hadasu Yassar zai iya dibar wani abu a jikin shi, amman saiya barshi yana ci mishi mutunci haka, ko Abba bai taba dukan shi ba, balle kuma Hajja, Yassar ne mutum na farko a duniyar shi daya fara dauke shi da mari bai iya ramawa ba, lokacin da fada ya kaure tsakanin shi da Babban Yaya, kan ya mare shi ya rama.

Amman da Yassar din ya kafe shi da idanuwa tsintar kanshi yai da barin wajen, yana mishi kwarjini naban mamaki. Yanzun ma kallon da yake mishi yasa shi fita daga dakin. Kanshi tsaye bangaren Mami ya wuce yana shiga har tsakiyar falon tukunna yai sallama, Mami din data fito daga kitchen ta amsa shi

"Ina wuni"

Ya furta a hankali, duk cikin matan Abba yafi ganin girmanta, ita kadaice bata taba shiga harkar shi ba, asalima banda gaisuwa babu abinda yake hadasu, yanzun ma wucewa tayi hidimar gabanta, shi kuma ya taka yana karasawa har kitchen din, inda yaga Waheedah a tsaye, juyowa tayi tana kallon shi, kafin a dan daburce tace

"Hamma..."

Ludayin da yake hannunta ya karba, jajayen kayane a jikinta daya kara fito da farin ta yana saka shi daquna fuska

'In shaa Allah babu abinda zai hadani hanya da farar mace'

Ya fadi a kasan ranshi, plate ya dauko batare daya kulata ba, yana kallo ta matsa tana hade bayanta da kantar kitchen din, abincin da yake tunanin zai iya cinyewa ya zuba

"Ina miya?"

Ya tambaya yana kin kallonta dan farinta na shigar mishi ido, da hannu ta nuna mishi tana sake matsawa dan zuciyarta dokawa take sosai, da tunanin shi manne ta yini, har fita tayi harabar gidan ko zata ganshi batare da tasan dalilin hakan ba, ta gaji da leqe-leqenta ta dawo cikin gida, ko sallar isha'i sai yanzun ne tayi alwalarta, a falo ta zauna tana jiran ko zata ga ya shigo dibar abinci, sai yanzun da yake tana da rabon tagan shi din. Cokali yasa hannu ya dauka hadi da wani plate din daya dora kan abincin ya rufe yana ficewa batare daya sake kallon inda take ba. Bangaren su ya koma, abincin ya fara ajiyewa tukunna yaje ya dauko ruwa ya dawo ya zauna. Daga shi sai Yasir da Yassar, Ahmad da suke kira da Babangida, sai Mubarak a falon.

Film din da lokacin ake rubuta sunaye alamun farawa ya tsayar da idanuwan shi akai.

'Paheli'

Ya karanta sunan film din da tun daga kidan daman yagane indiya ne. Abinci yake ci yana nutsar da hankalin shi kan film din, dan sosai yake jin dadin shi, kafin yaji an harbar mishi baya da kafa, ya kuma san Yassar ne

"Sojan gobe ne yake kallon soyayya haka?"

Yassar yai maganar yana dariya

"Babu abinda zai hana insa a rufemun kai ko kwana biyune, saboda babu wanda ya rainani a gidan nan kamar ka"

Dariya Yassar ya sake yi

"Lallai ma yaron nan. Ka zama sojan tukunna"

Juyawa Abdulkadir yayi yana kankance mishi idanuwa

"Na kusan applying NDA ai, in shaa Allah. Kuma wayaki soyayya?"

Wannan karin

7 / 51