Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   13 / 51

36K to 39K   out of 152.3K words

taba cewa kowa yana cin abu kaza ko bayaci ba, idan yaje ya duba yaga ita akayi ficewa yake ya nemi wani abin daban yaci. Ganin kallon da yake mata yasa tajin zuciyarta na bugawa, tana mamakin yanda idanuwan shi suke birkita mata lissafi, duk kankantar su.

"Ban taba gani kaci ba, idan ka shigo anyi baka diba kake fita"

Waheedah tai mishi bayani, Idanuwan shi ya dauke daga kanta, yana jin jikin shi ya dauki dumi na daban. Abune da bai taba tunanin wani yai damuwar dazai kula ba. Plate din shinkafa da miya harda lettuce data zubo mishi ya dago yana dora shi kan cinyar shi, yanda yake motsa abincin a nutse take bi da kallo, kafin ya diba abincin yana fara kaiwa bakin shi. Idanuwanta Waheedah ta dauke daga kanshi, tana dan sa hannu ta dafe kirjinta da yake dukan uku-uku. Passport dinta ne data gama bincika duk wasu da take dasu tana dauko wanda tai tunanin tayi kyau a ciki ta ke riqe dashi a hannunta.

Tun jiya da tunanin ta bashi yazo mata zuciyarta take dukan uku-uku da tunanin abinda zai iya biyo baya. Tasan babban cikin su bazai wuce tasha mari yace ta raina shi ba, amman son ya tafi da wani abu da nata ne yafi karfin duk wani tunani da takeyi, yanda yabar mata wani abu nashi duk da ko baiyi ba tasan zai kasance manne a zuciyarta harya dawo, haka take so ko yayane itama ya tuna da ita, ta gama tattaro karfin gwiwarta amman ganin shin da tayi ya tuna mata yanda a kasan komai  akwai tsoron shi a shimfide. Kalle-kalle take cikin dakin, a drawer din gefen gadon ta hango wallet din shi, karasawa tayi wajen tana zama.

Sai lokacin Abdulkadir ya dauke idanuwan shi daga kan abincin da yake ci ya kalleta, ganin wallet din shi yayi a hannunta ta bude

"Kin ban ajiya ne?"

Ya bukata yana tsareta da idanuwa, tunda ta shigo yake tunanin ta kara haske, sai lokacin ya kula da lace dinta farine da ratsin ja ko stones din jikine ja bazai tantance ba, shiya kara fito da haskenta dayai mishi yawa a ido. Kai Waheedah ta girgiza mishi zuciyarta take ji ta dawo wuyanta, idanuwan shi ya dauke daga kanta yana ci gaba dacin abincin shi, hakan ya bata damar saka mishi hoton cikin karamin wajen da zaka iya ajiye hoto tukunna ta balle wallet din tana ajiye mishi inda taganta. Sosai zuciyarta take dokawa har wani zazzabin faduwar gaba take ji a jikinta.

Ga zufa da tafukan hannunta sukeyi, mikewa tayi

"Ina zakije?"

Abdulkadir ya tambaya, bai jira amsarta ba ya dora da

"Ki jira in gama ki tafi da kwanonin"

Komawa Waheedah tayi ta zauna, idanuwanta kafe a kasa, shirunta Abdulkadir yaji ya mishi yawa, hakan yasa shi kallon ta, kanta a kasa yake

"Waheedah?"

Ya kira cike da alamun tambaya, ta dago tana sauke mishi manyan idanuwanta da yake da yakinin za'a cire hudun nashi a ciki har a samu ragowa, har mamakin yanda za'a ce idanuwan mutum ne da wannan girman yake, yana son ganin tsoron shi cikin su saboda girman da sukan qara yi mishi.

"Lafiyar ki?"

Ya tambaya, tambayar shi kanshi tana bashi mamaki, haka kawai yana son jin tana lafiya, da bata mishi surutunta yau. Kai Waheedah ta iya daga mishi, yanda ya kira sunanta nasa har lokacin zuciyarta dokawa take har cikin kunnuwanta. Numfashi ya sauke, ita kadai take amsa mishi magana haka, surutun nata yake son ji, tana amsa mishi magana da kai. Abincin shi ya karasa ci yana cire robar ruwan daga kan farantin ya dago dashi ya miqama Waheedah data miqe tsaye, gara ta fita, kan shi yake jin ya mishi nauyi yau din nan, Nuriyya taki ficewa daga cikin shi, bazai kara da tunanin ko lafiyar Waheedah kalau shisa take mishi shiru-shiru ba.

*

Tsaye yake jikin mota Abba yana jiran wanda zaikai din su fito, ance mishi sharada ne, yagane ta wajen dan akwai abokin shi a gurin unguwar. Waheedah ya hango tana takowa inda yake, tafiyarta yake kallo kamar batason taka kasar dakyau karta tsage ta rufta da ita. Hijab ce mai hannuwa a jikinta har kasa. Yana son hijab, dan matar shi ba zata saka mayafi ta fita wani qaton banza na kallonta ba, kwalliyarta a cikin gida zatayi iya idanuwan shi. Kalar hijab din ruwan kasa mai cizawa, a ranshi yake tunanin ko Waheedah batasan tana da gaske bane, duk kayan da zatasa kara mata haske suke suna saka ta shigar mishi ido. Yana son mace mai duhu

'Kamar Nuriyya'

Wata murya cikin kanshi ta furta mishi tana saka shi sauke numfashi, duk da ba karya ta fadi ba, yanayin kalar Nuriyya haka yake son macen shi ta kasance.

'Har yanayin jikinta da komai nata'

Muryar ta sake fada mishi tana saka shi girgiza kai, kamar yana son fada mata kartai musu haka shi da ita, karta ja musu raini. Karasowa Waheedah tayi tana fadin

'Hamma baka shirya ba, yanzun fa za'a tafi, dangin su Angon har sun zo"

Sosai yaji dadin saukar muryarta da ta katse mishi tunanin da yake da yake da tabbacin babu abinda zai ja mishi sai rainin dayafi tsana a rayuwar shi. Kafin maganganub Waheedah din su zauna mishi suna saka shi kallon ta cike da rashin fahimta

"Wanne irin shiri?"

Dan kallon shi Waheedah tayi tana rausayar dakai, tagan shi da wando iya gwiwa sai riga blue mai haske datai mishi kyau naban mamaki a idanuwanta, amman duka cikin abokan angon da suka zo da motocin da kuma yan gidan nasu da zasu taya hidimar daukar amaryar manyan kaya ne a jikin su.

"Baka sa kaya ba"

Ta fadi, tana saka shi kankance mata idanuwan shi. Haka Yassar yai mishi maganar sake kaya dazai fito, itama tazo tana mishi yanzun

"Tsirara kika ganni? Meya sami kayan da suke jikina? Me yasa bazan je da wannan din ba? Su ba kaya bane"

Kallon shi Waheedah take yanda ya kankance ido yana mata masifa kamar jiranta yakeyi daman, ita bada tunanin komai tai mishi magana ba, idanuwanta taji sun cika da hawaye. Batare da tunanin komai ba ta sake cewa

"Allah ya baka hakuri..."

Wani murmushi Abdulkadir yayi mai sautin dake fassara ya kasa yarda shi Waheedah tace ma 'Allah ya baka hakuri'. Duk da baiji raini a muryarta ba, baqar magana ce ta fada mishi saboda yana magana mai tsayi da ita

"Bakar magana zaki fadamun? Saboda kinga hakorina? Maganar da nake dake tasa zaki fara rainani ko?"

Hawayen da take tarbewa ne suka zubowa, yana kara harzuqa Abdulkadir din saboda bayason kuka marar dalili, idan zaka saka shi a gaba kana mishi guga gara ya tabbatar ya baka dalili me karfi nayin kukan

"Me nai miki?"

Kai Waheedah ta girgiza mishi, hawayenta na sake zuba, fadan shi take ji har kasan zuciyarta, inda tasan zai mata fadan ba zata soma mishi maganar kayan da yasa ba.

"Raini ne yasa kike mun kuka?"

Abdulkadir ya sake tambaya yana tsareta da qananun idanuwan shi. Kafin yaja tsaki yana wucewa ya nufi bangaren su, kayan da Yassar din ya fito mishi dashi dan ya saka yaqi ya dauka hadi da jan wani karamin tsakin, dan baisan dalilin da yasa shi yake sake kayan jikin shin ba, tunda baiga abinda sukai ba. Ko motsi Waheedah batayi ba daga inda yabarta, hannu take sakawa tana share kwallar da taqi daina zubar mata har lokacin, fuskarta tayi wani irin ja, abinka da farar fata. Anan Nuriyya da tun jiya da suka dawo ta kwanta batare da tace mata komai ba ta sameta.

Tunda aka fara hidimar a gidansu Waheedah din take kwana, duk da ko babu hidima tana kwana wasu lokuttan, kusan rabin da kwata na rayuwarta tare dasu takeyin ta a gidan. Yau da safe data tashi ma bata kula Waheedah din ba, saboda haushinta take ji, haushin kowa da komai take ji, data isheta catai mata kanta ke mata ciwo, harda bata paracetamol din rainin hankali.

"Ke kuma lafiya? Me akai miki?"

Nuriyyan ta tambaya tana tabe baki, hannu Waheedah tasa tana share kwallarta, muryarta a dishe tace

"Hamma Abdulkadir ne ya sauke mun fadan shi"

Dariya Nuriyya tayi saboda har ranta taji dadi, Abdulkadir din ya tabbatar mata da Waheedah kamar kowa ce a wajen shi, babu wani special treatment da take samu

"Abin dariya ya baki ko?"

Waheedah take fadi tana hararar Nuriyyan data sake yin wata dariya tana riqo Waheedah din hadi da dora kanta kan kafadar Waheedar

"Sorry kawata. Halin Hamma wanne ne baki sani ba?"

Jinjina kai Waheedah tayi, tasan shi fiye da zaton kowa, fadan shine ba zata taba sabawa dashi ba, duk yanda take da tsoron duka gara ya daketa dayai mata fadan shin nan mai tsaya mata a rai.

"Nasani Nuriyya, bana son fadan shine kawai"

Tabe baki Nuriyya tayi

"Nidai muje..."

Ta karasa tana kama hannun Waheedah din dan su samu mota, cikin abokan angon wani ya leqo kai yana ma Nuriyya murmushi

"Ya zaku wuce direban naku?"

Ya fadi yana dan daga mata gira, dariya Nuriyya tayi ganin baiko kalli inda Waheedah take ba. Murfin motar zata bude dan ta shiga, kamar daga sama taji ance

"Ina zaki je?"

Juyawa tayi zuciyar ta na dawowa makoshinta, kamshin turaren shi na cika mata hanci, shaddar jikin shi tayi matuqar amsar shi, jikinta har wani bari yake, kafin ta kula da idanuwan shi tsaye suke kan Waheedah. Wani tuquqi taji ya taso daga dan yatsan kafarta yana samun wajen zama a makoshinta. Yana fitowa bai ganta wajen motar ba, hijab dinta ya hango, ranshi a bace yake har lokacin, baima san wayace tabar wajen ba.

"Nace ki bar wajen ne?"

Ya tambaya, kai Waheedah ta girgiza mishi, kalar fadan da yake ji yau na bata mamaki, tunda daman bashi ya kirata ba, ita ta same shi a wajen, yanda ya kafeta da ido yasa ta wucewa ta gaban shi kamar qwai ta fashe mata. Wani kallo ya watsa mata mukullin motar dake hannun shi na subucewa ya fadi, kafin ya yunkura Nuriyya ta tsugunna ta dauko mishi tana sauke idanuwan shi cikin nata, wani irin abu na tsirga mishi dayasa gashin dake bayan wuyan shi miqewa. Hannu ya miqa mata ta saka mishi mukullin a ciki. Yana duk wani kokari dazai iya karya riqe hannunta ya jujjuya shi yaga kunshin ta dakyau.

Idan akwai abinda yake kara burgeshi bai wuce kunshi ba, ko baisan yarinya ba yaga hannuwanta dauke da kunshi saiya sake kallo, musamman na Nuriyyan da yake baqi da ja. Gashi yan yatsun nata jan lallen ya kama. Wani abu ya hadiye a dakyar yana tsintar kan shi da fadin

"Wa yai miki kunshi?"

Murmushi Nuriyya tayi saboda shine karo na farko da yai mata wata magana da ba amsa gaisuwa bace, banda jiya da yace ta rufe mishi kofa.

"Wata mata ce"

Ta amsa tana saka shi ware kananun idanuwan shi da ya tabbatar a waje yai maganar, kai yadan daga mata yana juyawa. Takun tafiyar da yakeji ya tabbatar mishi da Nuriyyan na biye dashi. Zuciyar shi dokawa take sosai, ga tsikar jikin shi da yake ji tana miqewa, bayaso ya juya ya sake fadin wata maganar da bai niyya ba, shisa ya kyaleta. A tsaye wajen motar ya samu Waheedah. Zagayawa yayi ya bude motar ya shiga, wannan karin baice ma Waheedah ta shigo ba, da kanta ta bude kofar ta shiga. Bata kula da hararar da Nuriyya ta watsa mata ba, dan ita taso ta shiga gaban motar.

Babu yanda zatayi haka ta bude bayan ta shiga, duk da gabanta na faduwa kar ya koreta, baice mata komai ba, zuciyarta har wani tsallen murna take, murmushi yaki barin fuskarta har lokacin. Dan tashi Abdulkadir yayi yana saka hannun shi a aljihu ya ciro links din dake cikin aljihun tukunna ya zauna. Waheedah ya mikama links din, batace komai ba ta karba tana gyara zamanta dan ta saka mishi a hannun da ya miqo mata din. Cikin yanayin dayasa murmushin da Nuriyya take ya bace bat daga fuskarta, kallon su takeyi har Waheedah din ta daura mishi link din, ya janye yana miqa mata dayan hannun nashi, saka mishi tai tukunna ta gyara zamanta batare da tace komai ba.

'links ne kawai, kema dan bazai yiwu ya baki bane kisa mishi shisa ya bata'

Nuriyya take fada ma kanta duk da wata murya na gaya mata

'Ita ma din ai ba kanwar shi bace, babu abinda ta hada dashi, agolar gidan su ce'

A karo na farko da taji daman Waheedah tazo a kanwar Abdulkadir din da hakan zaifi mata, saboda babu wani chance na soyayya a tsakanin su. Kirjinta take jin yana mata zafi da abinda take jin kishi ne na fitar hankali, tasan Abdulkadir ya mata nisan da bazai misaltu ba, shisa duk kyan da yake mata, da yanda yake sak da zabin mijin da take burin samu bata taba daga burinta akan shi ba. Haka take so yaima Waheedah nisa, ko kadan bata son wanni kusanci daya banbanta da wanda yake nunawa tsakanin shi da kowa. Idan ba zata same shi ba, Waheedah din ma ba zata same shi ba.

Abdulkadir kuwa kokawa yake da yanda komai na jikin shi yake son juyawa ya sake kallon Nuriyyan, kafin kanwar Abba ta bude motar ta shigo tana fadin

"Abdulkadir..."

Damar yai amfani da ita ya juyo

"Anty... Ina wuni"

Dan ware idanuwa Anty Maryama tayi, duk da taga Abdulkadir din ya girma, tana tunanin hankali ne yazo mishi har yau take samun arziqin gaisuwa

"Lallai Abdulkadir an girma..."

Ta fadi tana saka shi daquna fuskar shi. Irin abinda bayaso kenan, saika gaishe da mata saita dinga nuna maka kamar an haifeka a gabanta, ko Hajja da ta haifeshi bayaso tana ce mishi yaro a gaban kannen shi. Nuriyya ya dan kalla yana sata sauke idanuwanta daga kanshi babu shiri. Juyawa yayi yana gyara zaman shi. Anty Hafsatu ce ta shigo itama yanajin motar tai qasa saboda nauyin da sukai mata. Tayar da motar Abdulkadir yayi

"Ka tsaya Hajiya Hassana ta karaso, gata can ta taho"

Anty Hafsatu ta fadi tana sa Abdulkadir fadin

"Inba saman motar zata shiga ba nan dai ai ya cika"

Abdulkadir yace yana yin baya da motar, ganin da gaske tafiyar zaiyi yasa Anty Hafsatu rufo murfin motar

"Mutum nawa suke zama a baya? Ka jira tazo Abdulkadir"

Daquna fuska yayi yana fadin

"Gaskiya ta shiga wata motar. Bakiji yanda motar tai kasa ba da kika shigo... Inba so kike muna tafiya muna gurzar titi ba"

Bude baki Anty Hafsatu tayi cike da mamaki

"Kaci uwaka Abdulkadir, kana jina..."

Daquna fuska Abdulkadir din yayi, yana shirin yin magana Waheedah tace

"Hamma..."

Yanda tai maganar cike da roqo yasa shi harararta cike da alkawarin sauke mata wata masifar. Bata damu ba indai zaiyi shiru, bata so su Anty Hafsatu suce ya musu rashin kunya, kuma tasan idan maganar tai tsayi ba a iya rashin kunya zai tsaya ba, Abdulkadir zai iya fita yabarsu a motar ko su su fita subar shi a ciki. Batason hakan ya faru, Nuriyya dake gefe tana kallon su ta tabe baki.

'Allah yai miki baqin shishigi'

Ta fadi a ranta, koma menene din bata ga matsalar Waheedah ba tunda dai su Anty Hafsatun jinin shine, ita kuma bare ce, amman ji yanda tai mishi magana kamar tana da wani muhimmanci a wajen shi. Tun su Anty Hafsat suna mita har sukai shiru, saboda radio din da Abdulkadir ya kunna yana qure maganar, basu ce ya kashe ba, tunda babu wanda inhar yana zuwa gidan baisan halin Abdulkadir ba. A haka suka isa gidan Adda Khadija din, da duk da ba babba bane yanayin ginin yaima Abdulkadir kyau. A cikin motar ya zauna bayan ya fadama Waheedah inta shiga cikin gidan tace ma su Zahra su fito su tafi...!

*#TeamAbdulkadir*
*#TeamWaheedah*
*#TeamAbindaAntyFatiTaHanani*
*#AnaTare*
[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732: ©️
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com

*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*

10

Sai da yai wanka tukunna ya dauro alwalar sallar Asuba, yana kuma dawowa daga masallaci jakarshi ya hada tukunna ya kwanta. Sai lokacin ya kunna wayar shi tunda yazo Kano. Babban Yaya, Muhsin ne ya basu, dan shi harkar da yakeyi kenan, tun yana yaron shago da yake ubangidan nashi bamai baqin ciki bane, Muhsin din kuma akwai ladabi da kwantar dakai, kudaden duk da yake samu saiya tattara in za'a china saro kayayyaki saiya hada da nashi a dan saro mishi abubuwa. A haka har Allah ya saka mishi albarka, duk da ya kammala karatun shi bangaren computer science, bai nemi wani aikin ba, da sana'ar ya dogara, sai babban café daya bude a wajen rijiyar lemo da shima yana kawo mishi rufin asiri.

Shima wayar hannun nashi blackberry din ce, danne-danne yake, yana ma rasa abinda zaiyi da wayar, lokutta da dama hakan yakan faru tunda aka bashi wayar, idan ya gaisa dasu Hajja shikenan, kashewa yake, tana iya kwana biyu a kashe. Yazid ne ya turo dakin da sallamar da Abdulkadir din ya amsa mishi

"Ni banga amfanin wayarka ba"

Yazid ya fadi yana zama gefen gadon da Abdulkadir din yake zaune ya miqe kafar shi akai

"Ina amfani da ita mana..."

Kai Yazid ya girgiza cikin rashin yarda

"Kai dan BBM din nan da kowa yake yi ma bakayi"

Kankance mishi idanuwa Abdulkadir yayi

"Meye BBM din wai? Nawaf ma ya isheni da maganar kwanaki"

Dariya Yazid yayi

"Kafar sada zumunta ce, amman wayar blackberry ce kadai take dashi. Idan kayi register zasu baka wasu lambobi hade da haruffa, to sune zasu zama kamar..."

Hannu Abdulkadir din ya dagama Yazid, alamar baya bukatar karasa ji hadi da cewa

"Bani da ra'ayi..."

Yassar da yake wanka ne ya fito daga bandakij dan yanajin duk hirar da suke

"Ai idan kana son magana da Abdulkadir sai dai kai mishi text kawai, ko ka tura mishi saqo ta email dinshi. Idan ba zaka iya jira ya kunna wayar shi kuyi magana ba"

Yassar ya karasa yana daukar mai dake ajiye a gefen Abdulkadir din ya kwance ya dangwala yana soma shafama hannuwan shi.

"Matar yaron nan tana da aiki"

Yazid ya fadi yana sa Abdulkadir din watsa mishi harara da kananun idanuwan shi

"Bafa naso Hamma, duka shekara baifi shekara hudu kabani ba"

Kai Yazid ya girgiza mishi

"Banma baka ko daya ba, yaro sai shegen son girma..."

Turo labba Abdulkadir yayi

"Kayi na girman ka Hamma, kar kai na ukku"

Mikewa Yazid din yayi

"Sallama nazo muyi, rasa kunya..."

Daquna fuska Abdulkadir ya sakeyi

"Wanne irin sallama sai kace wanda za akai kabari? Ina ce makaranta

13 / 51