Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
yana yin tsaye, sanyin ruwan na nutsar da wani abu a tattare dashi, idanuwan shi ya kankance saboda bayason rufe su gabaki daya, baisan meya faru ba, baisan ya akai ba, yana da wata irin zuciya ta fitar hankali da bata da alaka da aikin shi, tun kafin shigar shi aikin soja yake da wannan zuciyar da har Abban shi yakan mishi addu'ar samun saukin ta a can baya, bayason rufe idanuwan shi ballantana yaga me zuciya ta saka shi aikata ma Waheedah yau a karo na farko tun auren su. Bazai bata lokacin shi tunanin abinda ya rigada ya wuce ba, wannan ba halayyar shi bace sam, yau bazai zama na farko ba, idan abu ya wuce mishi ya riga ya wuce tunda ba zai iya komawa ya sake ba, gaba kawai zai duba ya kiyaye. Da wannan tunanin a ranshi ya karasa wankan ya fito.
Baibi takan Nuriyya ba, kamar yanda bata bi ta kan shi ba, da towel din daure a jikin shi ya fito daga bangaren ta yana nufar bangaren Waheedah, dan nan yake da tabbacin zai sami kayan shi a nutse, dakin baccinsu ya shiga, kamshin ta na cika mishi hanci, tana son amfani da turarukan larabawa, sai dai bazaice ga wannne da wanne takan hada kamshin su ya bada kalar da yake bayarwa ba. Kan gadon ta ya hango kayan shi data fito mishi dasu, ya karasa ya dauka, riga ce fara qal, sai wando iya gwiwa baki mai wasu igiyoyi. Sai da ya fara saka singlet din da take ta zabga kamshi tukunna ya saka sauran kayan yana daukar towel din ya koma bangaren Nuriyya dashi.
Idan yace ga asalin abinda yakeji karya yake, kan shi dai yayi mishi wani irin nauyi.
'Ka saukakemun auren ka'
Maganar Waheedah ta dawo mishi tana saka shi kai hannu dai-dai kirjin shi inda yake jin wani abu na mishi kaikayi ya murza. Bandaki ya koma ya mayar da towel din ya rataye, tukunna ya karasa kan gadon yana kwanciya gefen Nuriyya da ko inda yake bata kalla ba. Hannun shi ya mika yana zare earpiece din kunnenta, ya sake miqawa ya zare dayan, juyowa tayi fuskarta babu walwala
"Kallo fa nake..."
Idanuwan shi ya kankance mata, yana sa ta fadin
"Dan Allah mana Masoyi, kuma wallahi yunwa nakeji, nace me matarka ta dafa muku kayi banza dani"
Runtsa idanuwan shi Abdulkadir yayi, duk idan yana tare da ita yakan sha wahala, komai saiya fito fili yayi magana tukunna zata gane, ba surutu yake so ba.
"Bata da lafiya... Tana asibiti"
Sai yanzun tagane dalilin dayasa ya shigo mata, inda Waheedah din nan bata tunanin jarabar nacin ta zai sa tabari Abdulkadir ya shigo bangarenta haka kawai batare da wani dalili ba. Tabe baki tadan yi
"Allah ya bada lafiya..."
Ta fadi da wani yanayi a muryar ta da tasa Abdulkadir mikewa
"Me kikayi yanzun?"
Ya bukata muryar shi can kasan makoshi, ware mishi idanuwa Nuriyya tayi
"Me nayi nikuma?"
Hannun ta ya damqo yana janta kamar bata da wani nauyi zuwa gab dashi
"Abinda kikayi da bakin ki yanzun nake nufi"
Wani irin yawu Nuriyya ta hadiya, tasan halin shi, tun kafin dan zaman nan na auratayya ya hadasu, tunda kusan fiye da rabin rayuwarta a gidan su tayi ta, ta kuma san raini na daya daga cikin abinda baya dauka ko daga wajen yayyen shi, iyaye ne kawai Abdulkadir yake dagama kafa, sai dai ita din takan mishi abubuwa da yawa sai dai ya kalleta ya wuce, sosai ta shagwabe mishi fuska tana matsawa hadi da shigewa jikin shi.
"Yunwa nake ji Masoyi...dan Allah karkai mun fada... Ni banyi komai ba, addu'a nai mata"
Yanda ta narke mishi yasa shi sauke numfashi, a hankali ya janye ta daga jikin nashi, yana dafe kan shi da hannu.
'Karka fita baka saukemun auren ka ba'
Maganganun Waheedah ne suke ta dawo mishi. Tsintar kan shi yayi da saukowa daga kan gadon, asibitin yake son komawa ya tabbatar da bata samu matsala a kwakwalwar ta ba, bayajin zai samu wata nutsuwa in bai tabbatar ba
"Ina zaka je?"
Nuriyya ta bukata
"Zan koma asibitin ne"
Ya amsa ta, yana jiran yaji ko zata ce mishi su tafi tare ta duba jikin Waheedah din. Baisan wani abu taji ya taso mata tun daga kirjinta har cikin wuyanta yana mata tsaye ba. Bata son nuna mishi kishin da taji, dan haka tace
"Zaka dawo da wuri? Kayo mun take away dan Allah..."
Kallon ta Abdulkadir yakeyi
"Me yake damun ki Nuriyya?"
Itama kallon shi takeyi
"Bangane me yake damuna ba, kar ince ka taho mun da take away idan zaka dawo da wuri? Jikina yamun nauyi bazan iya girki bane shisa, kuma laifinka ne daka qi dauko mun yar aiki..."
Kai Abdulkadir yake girgizawa
"She was your BestFriend (Aminiyarki ce a baya)..."
Ya furta a hankali, yana mamakin Nuriyya din, yanda yake kallon ta yasa ta cire earpiece din daga kunnuwanta tana ture system din, saukowa tayi daga kan gadon tana takawa ta karasa inda take, ba zaka kirata gajerar mace ba, amman tsayin Abdulkadir na kwatance ne, ga girman da yake dashi kasancewar baya wasa da motsa jiki, sai ta ganta yar karama a gaban shi, matsawa tayi tana riko hannun shi, hadi da daga kanta tana sauke idanuwan ta cikin nashi.
"Masoyi yau kam laifina kake ta gani, bansan me nai maka ba"
Ta karasa maganar tana tattaro hawaye dakyar ta cika idanuwan ta dashi
"Karki mun kuka Nuriyya... Karki mun kuka"
Dayan hannunta ta saka tana share kwallar data taru a gefen idanuwan ta
"Bansan me nayi maka ba..."
Yanda tai maganar cike da rauni ya taba shi, numfashi ya sauke, baisan me yake damun shi ba yau. Ganin ya fara saukowa a fuskar shi kawai yasa Nuriyya dora kanta a kirjin shi tana sakin wani guntun murmushin da take da tabbacin baya gani, batasan meya faru ba yau, idan zatai fada dashi Waheedah ba zata zama sanadin hakan ba, yaune karo na farko daya jefeta da kalmar alaqar dake tsakaninta da Waheedah a baya, ba zata bari hakan ya faru ba, tana sane sarai saboda ba tace zataje duba Waheedah din bane.
"Kome nayi kaina a kasa Masoyi...kar a sauke sojan a kaina yau... Umm?"
Tai maganar tana kara narkewa a jikin shi, dagota yayi yana sumbatar gefen fuskarta batare da yace komai ba ya juya yana ficewa daga dakin, bin bayan shi tayi tana leqawa ta tabbatar da yayi nisa tukunna ta dawo dakin tana turawa hadi da fadin
"Ni na dora mata ciwon... Yanzun haka karya take... Bansan yaushe Waheedah ta koyi munafunci da bakin hali ba..."
Da kan gadon zata koma taci gaba da kallon da take, sai kuma ta fasa saboda cikin ta dayai wata irin murdawa da yunwa. Babu shiri ta koma tana ficewa daga dakin, kitchen din ta ta nufa, a dispenser ta dibi ruwan zafi ta hada shayi, kwalin biscuit ta dauka tana wucewa ta koma daki, ta kasa daina zagin Waheedah a cikin zuciyar ta, yau da safe Abdulkadir din ya koma bangaren ta, shisa ta zauna tana kallon film din ta a system dan kartai tunanin yanda Waheedah take manne dashi kamar mayya, yanzun ma ba zata bari tunanin Waheedah ya bata mata rai ba, hakan take maimaitawa kanta harta samu wajen zama tana gyara system din ta dauki earpiece din ta mayar a kunnuwanta ta kunna film din, tukunna ta dauki kofin shayin data ajiye tana janyo biscuit din gabanta.
**
A hanyar shi na zuwa asibitin yaga Apple, dan harya wuce yayi parking yana fita daga motar ya taka da kafar shi zuwa wajen masu Apple din, hannu ya saka a aljihunshi duk da yasan bai zuba kudi ba, amman Waheedah ta dauko mishi wandon, yana da tabbacin duk wani abu dazai bukata tasa a ciki, akwai kudin kuwa, biya yayi ya karbi ledar yana komawa mota. Zai iya rantsewa da Allah duk idan ya dawo gida ya ganta, yakan manta yanda yake iya yin komai batare da ita a kusa dashi ba. Dayan aljihun yakai hannu ya laluba yaji I.D cards din shi na ciki yana kuma da tabbacin har da ATMs din shi duk suna ciki.
Sai da ya sauke wani numfashi da baisan yana rike dashi ba tukunna yaja motar yana nufar asibitin. Parking din motar shi yayi a inda akeyi yana takawa zuwa cikin asibitin, hannun shi rike da ledar Apple din daya siya, indan tashi ba za'a ci Apple ba, dan yana cikin kayan marmarin da baya kan shi sam-sam. Zama da Waheedah ya sashi koyan ci, duk da haka badan yana jin dadin shi ba, duk idan ta yayyanka yanda takan yi ta miqo mishi bayaqin dauka, ko idan tana ci, data gutsura take miqa mishi shima ya gutsura saita sake karba, ko ruwa zata sha saita bashi shima. Baya tunanin Waheedah na iya cin wani abin yana zaune ko yaci nashi bata bashi ba.
Sosai yake shiga cikin asibitin harya karasa bangaren da Waheedah din take, dan sun kama dakin da ita kadai ce, kan shi tsaye ya nufi dakin da yake lamba ta sha biyu, kwankwasawa yayi hadi da murza hannun kofar ya shiga batare daya jira an bashi izinin ba. Baiga kowa a dakin ba sai Anty, da sallama ya karasa ta amsa shi a sanyaye. Ledar Apple din ya ajiye a gefe kan abinda akan ajiye kayayyaki, tukunna ya kalli Anty da take zaune tana goye da Ikram yana fadin
"Ke kadai? Ya jikin nata?"
Cikin sanyin murya ta amsa shi da
"Sun koma gida, ba'a son hayaniya ne ko kadan, saboda jininta yayi wani irin hawa. Abdulkadir me yake faruwa?"
Kujera ya janyo yana samun waje ya zauna, fuskar shi da bata cika fara'a ba ya sake hadewa waje daya. Tambaya na daya daga cikin abubuwan da bayaso, musamman wadda ta shafi matsalar iyalin shi.
"Tambayar ka nake, me yake faruwa?"
A daqile yace
"Tsakanin mune... Komai zaiyi dai-dai..."
Sakin baki Anty tayi, na dan lokaci ta manta waye Abdulkadir, yanzun yake tuna mata.
"Tsakanin kune take rokon mu da mu karbar mata takardar saki a hannun ka?"
Dago da kan shi yayi yana kallon Anty
"Kaman yanda nace, tsakanin mune. Anty karki wuce hurumin ki dan Allah"
Ya karasa yana mayar da kallon shi kan Waheedah da take bacci, hannun ta da yake daure da ruwa ya kama yana gyara mata zaman shi, baibi takan Anty da take kallon shi ba, rashin kunya ce Abdulkadir ya saba batun yanzun ba, batasan me yasa tai tunanin iyalin daya fara tarawa zasu saka halayyar shi canzawa ba. Bata sake cewa komai ba, tasan halin rashin hakurin ta, kaca-kaca zasuyi ita dashi a asibitin nan, dan bakinta bazai shiru ba, Abdulkadir kuma ba zaiqi datsa mata duk maganar data fito daga bakin shi ba. Yanke hukuncin tashi ta koma wajen dakin tayi, idan ya gama zaman shi ya fita ta dawo.
Yana jin bude kofar ta da rufewa, juya idanuwan shi yayi, yana kara matsawa kusa da Waheedah sosai, sam bayason baqar tambaya, baiga meya shafi Antyn da matsalar gidan shi ba, dayan hannun Waheedah ya kama yana zagayo dashi takan cikin ta hadi da riqewa.
"Wahee kinga me kika ja mana ko?"
Ya furta a hankali, yanzun yake kara samun tabbas akan ba cikin hayyacinta ta furta mishi kalaman dazun ba. Numfashi ya sake saukewa, sosai ya ja kujerar yana kwantar da kan shi a cikinta, kan kuncin shi haggu ya kwanta yanda zai iya kallon fuskarta, har lokacin dayan hannun shi na cikin nata. Wani numfashin mai nauyi ya sake ja yana fitarwa hadi da lumshe idanuwan shi. Babu tunanin komai cikin kan shi, kallon ta yake wata irin nutsuwa na saukar mishi, a hakan bacci mai karfi ya dauke shi shima.
*
Kan ta takejin kamar an dora mata katon dutse, idanuwan ta dakyar ta iya daga su, nauyi taji saman cikin ta, a zaton ta Fajr ne, dan haka yakanyi mata, komin baccin da takeyi zata jishi yazo ya kwanta a jikin ta, bazai taba kwanciya kan katifa ba, ko ta sauke shi daya farka yake sake koma kan jikin ta ya kwanta. Hannu takai tana dorawa kan cikin ta inda take jin nauyin, zata rantse dumin shi ya banbanta dana sauran mutane. Dan dago kanta tayi, shi dinne ba magagin bacci takeyi ba. Hannu takai tana murza kirjinta inda take jin yana mata wani irin ciwo.
A hankali komai yake dawo mata, hannu takai da nufin tashin shi ya furta mata abinda take son ji, saita tsinci kanta da kasa yanke mishi baccin nashi, tunda tasan bako da yaushe yake samu ba, duk da yazo hutune bayan shekara biyu sai yanzun ya sami hutu mai dan tsayi. Kallon shi take, zuciyarta a dunqule waje daya take jinta, shisa bata motsa mata da duk wata kaunar Abdulkadir din. Zufa taga yana yi, a hankali jikin shi ke bari, tasan yana cikin duniyar mugayen mafarkan dakan hana mishi samun wadataccen bacci. Ganin yanda yake zabura yasa takai hannun ta kan fuskar shi tana shafawa a hankali.
"Sadauki..."
Ta kira a tausashe, hannunta taji ya damqa kamar zai karyata kafin ya bude idanuwan shi yana sake matse riqon dayai ma hannunta da saida ta runtsa idanuwan ta saboda azaba, sosai ta dauka ya karyata yau dai.
"Sadauki hannu na..."
Ta fadi, tana saka shi dago fuskar shi daga kan cikin ta yana karema dakin kallo, kafin da sauri ya saki hannunta yana fadin
"Bansan sau nawa zance ki daina yo kusa dani inkin ganni a yanayin nan ba..."
Dayan hannun ta mai daure da ruwa ta dago tana murza wannan din, idanuwanta harsun tara hawaye
"Yau dai ka karyani, kayi maganarka ta karshe a bakin yan Amin, an amsa, ka karyani Sadauki..."
Karamin murmushi yayi yana kamo hannun nata data fisge, karfi yadan saka ya riko hannun
"Kokawa zakiyi dani?"
Ya tambaya yana daga mata girar shi guda daya. Turo mishi labbanta tayi, hannun yake dubawa, farar fatarta tasa hannun ya fara tara jini, shafa mata wajen yayi
"Ban karyaki ba, in kina tabani ina bacci dai zai faru wata rana, na fada miki bakyajin magana"
Fisge hannun ta tayi tana murzawa.
"Ina yarana?"
Ta buqata a hankali, tana jin kewarsu na danneta
"Fajr na tare dasu Mami nake tunani, Ikram na wajen Anty...bari in karbo miki ita..."
A hankali ta girgiza mishi kai duk da hakan take so, batasan lokacin data dauka a kwance ba, tasan yarinyar taji yunwa ba kadan ba, amman a karbota daga wajen Anty, abin ya mata nauyi. Abdulkadir bai saurareta ba ya miqe yana nufar kofar dakin ya bude ya fita, Anty yagani zaune tana danna waya, da alamar game ne daya kalli screen din.
"Ta tashi Anty, ki bata Ikram wai..."
Batare da tace mishi komai ba ta ajiye wayarta a gefe tanaa kama goyon yarinyar ta kwance ta mika mishi ita, karbarta yayi yana kallon ta, idonta biyu, ta tsoma hannuwanta guda biyu a bakinta tana tsotsa. Gyara mata zama yayi a hannun shi daya tukunna ya bude kofar yana shiga yana mayar wa ya rufe, sai da ya saka Ikram a hannun Waheedah din tukunna ya zauna inda ya tashi, yana kallo ta miqe zaune tana jingina bayanta da abin gadon, tukunna ta gyarama Ikram din zama sosai tana soma shayar da ita.
Dago kanta tayi tana kallon shi, zuciyar shi yaji ta doka ganin yanayin nan baibar idanuwan ta ba.
"Kai nake jira..."
Ta furta a hankali, kallon ta yake yana son fahimtar ma'anar kalaman da ta furta mishi.
"Abinda na fada maka dazun, bana ce ka saukake mun auren ka ba? Ko baka jini ba in sake maimaitawa?"
Yanzun ya gama tunanin ta dawo hayyacin ta, ashe bata dawo ba har yanzun, wacce irin buguwa tayi haka. Dole zai magana da likitocin nan, inma barin kasar ya kama Allah ya mishi rufin asirin da baya tunanin zai gagare shi.
"Kayi shiru..."
Waheedah ta fadi tana sake tallabo Ikram din jikin ta, wani irin yanayi taje ji da batasan yanda zata misalta shi ba, har wani kaikayi take ji a jikinta da son jin ya furta mata kalaman da zasu datse igiyar da ta qulleta dashi.
"Kin buga kanki da yawa..."
Abdulkadir ya fadi can kasan makoshi, shine kawai bayanin dazai fassara abinda yake faruwa yanzun. Idan ba kanta ta buga ba Waheedah ba zata nemi saki a wajen shi ba, karma azo maganar saki ba zata kalle shi cikin ido tana mishi magana da yanayin rashin kunya haka ba.
"Ban buga kaina ba, sakina nake son kayi..."
Ta fara bata mishi rai, yana jin yanayin na barazana da hakurin shi.
"Kibar mun maganar nan, ki bari, nace kin buga kanki da yawa ne..."
Ya karasa yana jan kujerar shi baya ya miqe tsaye
"Ina zaka je?"
Dan dafe kanshi yayi yana sauke hannun shi
"Zan magana da likita..."
Wani murmushi Waheedah tayi, tana rasa meyasa kalamanta suke mishi wahalar fahimta haka.
"Kayi magana dashi, idan ya tabbatar maka lafiyata kalau, saika dawo ka saurareni"
Kallon ta Abdulkadir yake yi, maganganunta na zauna mishi, a hankali ya girgiza kai, idan ya zaman bata buga kanta ba, idan ya zamana tana cikin hayyacinta baisan me zaiyi ba, baisa ina take so ya ajiye kalaman ta ba. Babu shiri ya koma ya zauna yana kiran sunan ta
"Waheedah..."
Kallon shi kawai tayi batare data amsa ba, wani abu daya zo wuyan shi ya tsaya yake kokarin hadiyewa amman hakan ya gagara.
"Saboda hakurina ya kwace a karo na farko a zaman mu yasa kike furta mun kalaman nan?"
Kai ta girgiza mishi a hankali
"Kamun abinda yafi nayau, kasani kuma, nayau dinne dai zai zamana na karshe In shaa Allah..."
Wata gajeriyar dariya yaji ta kubce mishi
"Kin san girman kalaman da kike furta mun?"
Ikram ta janye daga jikinta dan hartayi bacci, tana gyarawa tukunna ta jinjina mishi kai.
"Ba zai yiwu ba to, idan ma da gaske baki buga kanki ba, ba zai yiwu ba Waheedah..."
Ya fada da wani yanayi a muryar shi da yasa ta tambayar
"Meye bazai yiwu ba? Sakin nawa?"
A hasale Abdulkadir yace
"Waheedah...kina son sake gwada hakurina ba?"
Cikin idanuwa ta kalle shi
"Meye zai faru? Zaka sake dagamun hannu ne yanda kayi? Nace idan na gwada hakurin ka zaka sake dagamun hannu ne Abdulkadir?"
Yanda taja sunan shin kamar ta kafa abin gurza kwakwa a zuciyarshi taja haka yaji ta karce wajaje da yawa a cikin kirjin shi. Ko a mugun tunani bai taba hango Waheedah zata taba yi mishi rashin kunya ba, mamaki yake har kasan ranshi daya