Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 51

15K to 18K   out of 152.3K words

da ba zatace ga lokacin daya fara ba, ko muryarshi taji sai zuciyarta ta fara doka mata irin hakan, dan zata rantse wasu lokuttan har wani gashi ne yake miqewa a bayan wuyanta. Jikinta da wani irin yanayi ta saka kafarta a cikin motar, dariya taga sunayi mata kasa-kasa, motar ta cika taf.

"Ku matsamun..."

Ta fadi cikin sanyin maganarta

"Babu waje fa"

Nabila ta amsa ta da murmushi a fuskarta, a raunane Waheedah ke kallon su, tana sauke idanuwanta kan Nazir da yake zaune a gefe, hararata yayi yana fadin

"Tab..."

Yazid da shine zai kaisu ya karaso wajen motar, cikin sanyin halinta ta gaishe dashi, ya zagaya ya bude gaban motar ya shiga yana mayarwa ya rufe

"Wai waye bai fito bane?"

Abdulkadir ya tambaya yana juyowa, Waheedah yagani tsaye

"Uban me kike da ba zaki shigo ba?"

Idanuwanta taji sun ciko da hawaye, ga zuciyarta naci gaba da dokawa da wani irin yanayi da bata da kalaman fassara shi

"Babu wajene anan din..."

Kabir ya amsa mata

"Baga waje anan ba?"

Abdulkadir ya fadi yana kallon su, hannu Nazir ya saka yaja murfin motar ya rufe, dan babu yanda za'ai ya koma gaba, bazai zauna waje daya da Abdulkadir ba. Karma yaga shine a gefe yace ya tashi ya koma, ita Waheedah da bata fito da wuri ba, ita zata zauna kusa dashi, tsaye tayi a wajen tana rasa yanda zatayi. Ba zama waje dayan dashi bane tashin hankalinta, luguden da zuciyarta takeyi duk idan ya wuce ta gabanta ma kawai, balle kuma ta zauna ga kugunta ga nashi tana jin kusancin shi. Tunda take shine namiji na farko da batasan meyasa take jin hakan akan shi ba.

Hannu Abdulkadir yasa ya bude murfin motar

"Idan bakina ya sake magana sai ranki ya baci"

Batasan lokacin da kafafuwan ta suka motsa zuwa gaban motar ba, tana ganin ya kara matsawa, shiga tayi jikinta a sanyaye, kafin ta zauna ta dora hijab dinta kan cinyar shi tana rufo murfin kofar tukunna ta zauna a takure, tasa hannu tana daukar hijab din nata

"Baki ga inda zaki ajiye ba sai a jikina?"

Kai ta girgiza mishi, karamin tsaki yaja yana gyara zama, farinta yake ji yana shigar mishi idanuwa, a dakinsu shida Babban Yayan su Muhsin ne baqaqe, shi yadanfi Muhsin hasken fata ma, amman farin Waheedah na mishi wani iri, duk inya ganta tana kara saka shi yanajin yanda babu abinda zai hada mishi hanya da auren farar mace, ko kadan basa burgeshi. Hijab din ta dayasha guga ta warware tana shirin fara sakawa

"Idan kika bigeni sai na mareki Waheedah, bansan iskancin dazaisa ba zaku saka hijab tun daga gida ba..."

Yazid dake tuqi ya girgiza kanshi yana murmushi

"Wallahi ka cika shegiyar masifa..."

A hasale Abdulkadir yace

"Hamma banaso..."

Waheedah kuwa hannuwanta ta sauke tana rike da Hijab din, numfashin kirkima ba sosai take yinshi ba, kar yaji iskar ta mishi yawa a kusa dashi ya sauke mata wata masifar tashi da bata karewa. A haka suka karasa makarantar babu wanda yake ko motsin kirki.

**

Kitchen din Mama ta shiga, tana bude katuwar kular data zuba abincin a ciki taga ko rabi ba'a diba ba. Jinjina kai tayi

"Kunma kanki Wallahi, gaba takaini"

Ta fadi tana dauko wasu manyan robobi masu murfi guda uku ta soma rage dafadukar shinkafar a ciki. Daman bayan sun tafi makaranta, tunanin abinda zata dafa takeyi, tana bude fridge taga bata da cefane, dubu uku Abba ya bata kafin ya fita, zubin adashi zatayi da dubu biyu, akwai bikin da zasuje na bangaren kishiyar Ummanta, dole a kece raini a nuna banbanci, dan ba tun yau take ma bikin tanadi na gaske ba. Sauran guntayen miya da tagani, wasu ma Allah kadai yasan tun yaushe suke ta dauko ta hade su waje daya ta sheqa ruwa ta kara mai da niqaqqen yaji a ciki, taga wani tsohon crayfish ta watsa a ciki, ko tsincewa bata tsaya tayi ba, tasan baci zatai ba, tai musu dafadukar shinkafa.

Da daddare tuwo zata tuqa, tana da sauran miyar kubewar da suka bar mata wancen girkin nata, ita zata juye ta karama ruwa ta kara kada wata kubewar ta tasheta, dan ita bata zubar da abinci, yanda suka barshi basuci ba, in wani girkin nata ya zagayo shi zataima kwaskwarima suzo su diba. Dubu dayan zata aiki salim yayo mata cefane kona dari ne naman dari biyu tayi yar miya ta dafama Alhaji Ahmad taliya, damam hakan takanyi, dan idan yasan kalar abincin da take dafama yaran tashin hankali zai mata marar misaltuwa. Shinkafar take kwashewa tana fadin

"Haba yara, wannan shinkafar ruwan jakara ce, in kunqi ci yau, kunci gobe"

Abdulkadir ya shigo, ya dan tsoratata dan ganin shi kawai tayi

"Kai dan ubanka baka iya sallama bane?"

Kallonta yayi rai a bace

"Karki sake zagina gaskiya tunda nayi sallama tun daga falo, ba laifina bane in bakiji ba"

Baki a sake Mama take kallon shi, rashin kunyarshi karuwa take duk rana

"Zaka rama zagin ne Abdulkadir?"

Rabata yayi yana dauko plate, ko Hajja inta zage shi ji yake kamar ta watsa mishi ruwan zafi, dan gani yake a shekarun shi ya girmi zagi, in yara sukaji ai saisu raina shi. Balle kuma Mama da baiga dalilin da take dashi na zagin shi ba. Wani ludayin ya dauko yana shirin sakawa cikin kular abincin da ko kadan yanayin shi bai kwanta mishi ba

"Karka batamun wani ludayin, ga wani nan..."

Ta fadi tana miqa mishi, karba yayi ya saka a ciki yana jujjuya abinci

"Meye wannan baqi-baqi a ciki?"

Ya tambaya yana daquna fuska

"Abin crayfish ne..."

Kallonta Abdulkadir yayi

"Crayfish kuma? Meye yasa za'a saka mana a abinci...me yasa ba za'ai mana da nama ba"

Shisa taki fitowa tun dazun, ta dauka duk sun gama dibar abinda zasu diba tunda taga lokacin tafiya islamiyyar su ya kusa, duk a cikin yaran gidan shi kadai yake tsareta da tambaya kan abinda ta dafa musu, bamai mata wannan fitsarar sai Abdulkadir, har bataso yaganta ranar girkinta, tana kuma shakkar yaje ya samu Abba da maganar dan tasan tsaf zai iya. Dan murmushi tayi

"To ai ana sakawa, yama fi nama zaqi..."

Ta fadi a fili a ranta tana

'Dan iska yaro mai baqin hali irin na uwar shi'

Cigaba da jagula abincin yake da ludayi, ranshi yake jin yana kara baci, duk kwana biyun da zatayi a jigashe suke yinshi, har yaranta, saboda kalar abincin da take dafa musu.

"Nikam gaskiya bazanci wannan jagwalgwalon ba"

Ya fadi yana ajiye plate din daya dauka yabar mata ludayin cikin kular ta juya ya fice daga dakin

"Karkaci dan ubanka, in girkina ya zagayo ita din zaka sake dawowa ka samu, shegen iyayin banza da wofi. Yaro ga rashin kunya malam..."

Mama take cewa tana kwashe sauran shinkafar a robobin ta rufe su ta saka a fridge, harta koma daki bata daina kwashe ma Abdulkadir albarka ba. Shikam bangaren su ya koma yana samun Zahra ta dauko uniform din islamiyar ta a hannu

"Sannu Hamma"

Tace mishi, dan baka isa ku hadu ka wuce bakai ma koda sannu bane ba.

"Zahra ki dafamun ko taliya"

Ware mishi idanuwa tayi

"Hamma guga zanyi... Lokacin islamiyya kuma ya kusa, dan Allah kayi hakuri"

Ta karasa maganar idanuwanta na cikowa da hawaye. Agogo ya kalla, uku da rabi harda wasu yan mintina akai

"Tsayuwar me kike? Da yanzun kin kai kitchen, kiyi sauri, wallahi kikai latti ubanki zanci"

Uniform din ta ajiye akan kujera tana nufar kitchen, tasan da gaske yake, zai iya yana gama cin abincin shi ya fita Islamiyyar, tana da tabbacin zai iya riganta zuwa, kuma babu abinda zai hanashi dukan ta, fiye dana kowa ma, dan in ya tare latti su gefe yake sawa su ware, in yaima sauran bulala biyar-biyar nasu sai yakai goma. Wani lokacin zata rantse da Allah yanayin murmushin shi yakan canza duk idan ya kama wani ya zane, kamar akwai nishadi na musamman da duka yake samar mishi. Lokutta da dama ko fada Hajja tai mishi akan su yake huce wa, motsi ma in kayi bai mishi ba zai iya ja maka duka.

Sai dai yana da wani hali daya, babu wanda ya isa ya dake su a waje, babu malamin da baisan rikicin Abdulkadir ba duk Islamiyyar, tun baikai haka ba, hannunsu yake kamawa har inda malamin da ya dake sun yake ya tambayi dalilin da zaisa yai musu kalar dukan dayai musun, tun ana bashi suspension, har suka gaji da halin shi suka kyaleshi, su da kansu basa son a dake su ya sani, basama fara zuwa suyi labarin inda zaiji. Kan kujera ya samu waje ya zauna yana jiran Zahra ta dafa mishi taliyar ta kawo.

*

Yau bata jira kowa a gidan ba, dan ranta kal take jin shi, tunda Mami ta siyo musu sabon takalmin makaranta ita da Amatullah, ta tambayeta ko zata iya bama Nuriyya wancen natan, dan kafar su daya. Kai kawai Mamin ta daga mata, dan tasan ko ta hanata ma a sace zata dauka ta bata. Da takalman da atamfar da wata yar uwar su Mami ta bata, taqi rabawa da Amatullah ta roki Ammi din ta kara siya musu wani yadi aka dinka musu doguwar riga ita da Nuriyya, duka ta hado ta saka a leda tana shiga gidansu Nuriyya da yake liqe jikin nasu, ba wani babban gida bane, daki ukune a cikin gidan, Nuriyya ce babba a gidansu, kuma yarinya kwalli a wajen mahaifiyarta da Allah yai ma rasuwa wajen haihuwarta din, tana da kannai guda hudu yanzun haka da matar babanta ta haifa dashi, ga cikin na biyar a jikinta.

Zakai karya idan kace Mama kamar yanda su Nuriyya suke kiran matar baban nata Maryama tana musguna mata, da zuciya daya matar take rike da ita, wanda abune mai wahalar samu a wannan zamanin, yanda mata suke musguna ma yaran mijin su da zaman kishi sam bai ma hadasu da iyayen yaran ba abune mai matuqar muni daya zama ruwan dare. Sai dai Baban Nuriyya talakane sosai, dan sana'ar kanikanci yake a wani gareji, da kuma kacokan din sana'ar suka dangana, danma mutum ne da yake tsaye kan iyalan shi da dukkan karfin shi.

Waheedah zata iya cewa ta tashine taga Nuriyya a rayuwarta, dan a lissafi da akayi, wata daya Nuriyyan ta bata, kawancen su abune da zai baka mamaki, dan tunda karancin shekarun Waheedah ko abu aka bata saita tambaya ina na Nuriyya din, tun Mami na hanata shiga gidan su Nuriyya dan ita macece da batason tashin hankali a rayuwarta, harta hakura da taga kawancen na yarta da Nuriyya abune da kaddara ta hada. Yanzun ma sallama ta rangada tana gaishe da Mama data amsa tana dorawa da

"Hassanar taki na ciki..."

Dariya kawai Waheedah tayi tana wucewa ta nufi dakin su Nuriyyan. Abba shiya fara musu tsokanar nan ita da Nuriyya gashi kowa ya dauka, duk idan ya siyo mata abu zai bata wani irin shi yace na Hassanarta ne, dan shaquwarsu zaka rantse yan biyune, duk da kamannin su da halayensu ya bambanta, Waheedah fara ce sosai, kuma siririya ce ta gaske, tana da kyau da in zaka tsaya ka kalleta sosai zakaga bashi da alaka da hasken fatarta, sannan komai nata da sanyi takeyin shi, gashi babu wanda zaice ya taba ganin bacin ranta balle kuma fada, shisa tasu tazo daya da Nuriyya din, ita kadai take iya hakuri da halinta. Sannan Waheedah zata iya sati fuskarta bata ga ko hoda ba, dan ma farace, ba zatace bakinta ya taba ganin jambaki ba, kwalliya kwata-kwata ba abu bane da yake gabanta, indai ta saka kaya masu kyau tadan goga turare mai sauqin kamshi, shikenan.

Nuriyya na da fada sosai, ba zaka daga mata dan yatsa ka sauke batare data lankwasa shi ba, ba fara bace, zaka iya saka hasken fatarta a mutanen da ake ma laqabi da masu kalar cakuleti. Kusan kyawun mahaifiyarta ta biyo, dan kowanne irin kaya Nuriyya tasa saikaga sun amshi jikinta, tana da matsakaicin tsayin da mutane da yawa zasu iya kiranta gajera, amman a dire take, tun da yan shekarun tan nan zaka fahimci Allah ya halicci mace a wajen, cikar lokaci kawai take jira ta karasa fitowa. Gashi fuskar nan tana daukar kwalliyar dake kara fito da ita, da wahala ka kalli Nuriyya baka sake kallonta ba. Itama aji ukku take a sakandiren gwamnati ta mata dake nan cikin barikin sojoji, sannan islamiyarsu daya da Waheedah.

"Kardai kice baki shirya ba..."

Waheedah ta fadi ganin Nuriyyan a kwance kan katifar dake tsakar dakin, bayan tayi sallama tana daga labulen, takalman kafarta ta zare a bakin kofa tana shiga dakin sosai. Sai lokacin Nuriyya ta tashi tana fadin

"Nayi wanka, har alwalar la'asar nayi, uniform fa zan tashi in saka..."

Gefen katifa Waheedah ta zauna tana ajiye jakar makarantarta da ledar kayan data kawoma Nuriyya din hadi dabin farantin daya ke ajiye a gefen katifar

"Kai dan Allah Nuriyya, me kuka dafa mai manja baki kawomun ba?"

Waheedah ta bukata dan ita duk abincin mai manja baya wuce ta, ga yan gidan nasu basu cika son manja ba, ko alala sai ace da farin mai za'ayi aci da sauce, itakam tana son abinci mai manja, kallon ta Nuriyya tayi

"Gero da wake ne..."

Bakinta Waheedah taji yana tara yawun kwadayi, dan inba gidansu Nuriyya ba bata taba ganin inda aka dafa gero da wake ba, sai kuwa in sunje Bugaje ne da Abba, akan kawo musu, bamai ci sai ita.

"Zakici ne in zubo miki?"

Nuriyya ta tambaya a daqile, wani lokaci irin rainin wayan nan na Waheedah yana sata jin wani maqaqi a makoshin ta, ta tabbatar abincine mai rai da lafiya aka dafama su Waheedah a nasu gidan, da wahalar gaske in babu naman kaji, amman tana nuna mata kamar su wanda suka dafa din yafi nasu, badan batason mahaifinta ba, tana jin shi har ranta, amman idan akai mata tayin musayar rayuwa da Waheedah da gudu zata amsa, kodan ta dinga zuwa makarantar kudi tana turanci kamar yanda taji sunayi, duk da itama nacin ta yasa tana da kokari naban mamaki, kuma tana kwaba turancin duk yanda yazo mata, Waheedah na gyara mata sosai.

"Kema kinsan zanci ai"

Waheedah ta fadi, daman ba wani abin kirki Waheedah din taci ba, girkin Mama sai godiyar Allah. Mikewa Nuriyya tayi tana nufar karamin kitchen dinsu ta samu faranti ta zubo mata gero da waken ta zuba mata manja da yaji a gefe ta dauki cokali ta saka mata a ciki, dakin ta koma ta ajiye mata plate din a gabanta

"Allah dai yai miki albarka yarinyar nan"

Harararta kawai Nuriyya tayi, ledar dake gefenta Waheedah ta dauka tana miqa ma Nuriyyan da fadin

"Anty Asabe taban atamfa kwanaki, sai Mami ta bayar akai mana doguwar riga nida ke"

Da sauri Nuriyya ta karbi kayan da murmushi a fuskarta tana kasa tsayawa ta kwance ledar, yagawa tayi tana fito da doguwar rigar da dinkin yai matuqar burgeta, kasan rigar ta tsugunna ta tattaro sai lokacin ta kula da takalman da suka fado, kafa daya ta dago, badan tasan Waheedah da takalman ba, zata ce sabone yanda ta wanke shi fes dashi.

"Ke banza harda takalmi kika hado dashi"

Kai Waheedah ta daga mata, dan ta cika bakinta da abinci, saida ta fara hadiye wani daga ciki tukunna tace

"Nakine... Mami ta siyo mana sabo"

Ta karasa maganar tana kara kai wani cokalin bakinta. Takalmin Nuriyya ta mayar ta ajiye kan katifa tana jin wani irin abu a kasan ranta da ta kasa fassara shi. Bawai batai murna da kyautar bane ba, tana tunanin har lokacin da zatakai tana saka kwancen abubuwan Waheedah, tana da wani irin buri a rayuwarta, tana son taga ranar da zatazo ace itace take da damar yima Waheedah irin hidimar da takeyi da ita, ba zataki ace idan damar tazo Waheedah bace a kasanta, hakan zai mata dadi ba kadan ba.

Idan bata samu damar yin karatu ta zama wani abu ba, ba zata taba auren marar hali ba, zata auri mai kudi, irin mijin da takanji a cikin litattafan hausar da bata jima da soma karanta su ba.

"Kisa uniform dan Allah Nuriyya..."

Waheedah ta fadi dan ta kusa cinye abincinta, kayan ta linke ta ajiye su a gefe tana dauko uniform dinta da su kansu tsofin na Waheedah ne ta bata bayan an dinka mata sabo, abinda takeji kasan ranta girma yake karawa, batun yanzun ta jima tana jin yanayin ba, yana kara girma ne duk lokacin da zataga Waheedah da sabon abu, ko kuma Waheedah din ta bata abinda ta rigada tai amfani dashi. Kayan ta zira tana dauko doguwar hijab dinta ta saka, Waheedah ta rigata fita ta nufi randar ruwan su Nuriyyan da take ajiye a tsakar gida tasa cup
din dake sama ta dibi ruwa tasha.

"Nuriyya dan Allah kibar kwalliyar nan ki fito haka, wallahi zamuyi latti"

Daga can cikin dakin Nuriyya ta amsa da

"Dan Allah karki isheni, hoda kawai nake shafawa..."

Dan ana duka kan yawan kwalliya a islamiyar tasu, duk da haka saida ta kara wajen mintina goma bata fito ba. Sallama sukai da Mama, bayan Nuriyyan ta fito suka nufi hanyar kofa tare, suna fitowa kofar gida suna cin karo da Abdulkadir, wani irin dokawa da zuciyarta tayi saida ta riko hannun Nuriyya

"Ina wuni Hamma"

Nuriyya ta fadi a tsorace itama, prefect ne a makarantar, batun anan tasan shi farin sani ba, duk da inba a makarantar su ba, bai taba dukanta ba. Asalima ko gidan ta shiga gaisuwarta ma can kasan makoshi yake amsawa kamar ta mishi dole. Yanzun ma amsa ta yayi da

"Lafiya..."

Yana tsayar da idanuwan shi kan Waheedah da ko ina cikinta bari yake

"Ban hanaku tsayawa wani waje in kun fito islamiyya ba?"

Dagowa idanuwanta da suka tara hawaye tayi tana kallon shi, ko batai wani abuba ya kafeta da idanuwan shin nan masu kama dana yan Japan saboda kankantarsu ji take komai ta kwance mata batare da wani dalili ba.

"Ka...ka hanamu"

Ta fadi a daburce, kai ya jinjina yana wuce su, hannun juna suka kama ita da Nuriyya suna wucewa suma, wani irin sauri suke zumbudawa kamar zasu tashi sama, Waheedah nada tabbacin in ya rigasu isa makaranta zai kirki dalilin dazai mata dukan biyawa gidansu Nuriyya, ita kuma Nuriyya laifin Waheedah din tasan shi zai shafeta, juyawa Nuriyya tayi taga ko yana gab dasu, ta sauke idanuwanta cikin nashi da yasa wani irin yanayi tsirga mata daga dayan tsakiyar kafarta zuwa dan yatsan kafarta, kafin da sauri ta juya tana

6 / 51