Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
hada a jakar da Yassar ya kawo musu. Ta kara gyara dakin tsaf tukunna ta saka Ikram a jakar goyanta, tasa hijab tana goya yarinyar ta gaba, ta dauki jakar da mukulli ta wuce, a falo suka ci karo da Hauwa, da mamakin ganin ta dawo da wuri a tattare da Waheedah tace
"Yau da wuri haka?"
Dariya Hauwa tayi
"Nagaji fa, gudowa nayi nace banda lafiya"
Murmushi Waheedah tayi, daman tayi niyyar karbar kayanta a kasuwa ta sauke a gida ta dawo, sai tayi musu sallama tukunna ta wuce. Cikin sanyin murya tace
"Ina son zuwa kasuwa ne, sai in biya gida in kai kayan nan"
Hauwa batasan lokacin data hade space din dake tsakanin su da Waheedah ta rungumeta ta gefe ba, saboda Ikram da take rike da ita, tukunna ta dago tace
"Inata kokari kar in miki magana Wallahi, inakuma kokari kar in wuce gidanki daga wajen aiki in jibgi Nuriyya ko zan huce haushina... In kika bar mata gidan harni kin cuceni, bata isa kibar mata gidanki ba wallahi"
Dariyar karfin hali Waheedah tayi, Yassar yasa ta sami kawa a tare da Hauwa.
"Nagode Hauwa"
Ta fadi a sanyaye, kai Hauwa ta jinjina mata
"Muje in kaiki, ba abinda zanyi sai kwanciya ko na zauna gidan daman"
Tare suka fita da Hauwa din, har kasuwa sukaje tare tana ta tsegumin yanda motarta take bukatar ganin bakanike saboda tana mata wata kara da Waheedah bataji ba, tunda ba sanin kan mota tayi ba. Da suka dauki kayan gidan Waheedah din suka wuce ta kai, bataga Nuriyya ba, bata kuma damu da hakan ba, har bedroom dinta ta wuce ta ajiye jakar kayansu, ta dauki mukullan data manta ranar karshe da tayi amfani dasu, ta kulle dakin baccin nata da sauran dakunan da suke bangarenta, dawowa tayi ta rufe kitchen dinta ma, dan siyayyar duk da tayi a tsakiyar kitchen din ta ajiye su, inta dawo ta shirya komai. Suka sake ficewa da Hauwa din.
Saloon tace zataje ta wanke kai, tare sukaje, itama Waheedah kan aka wanke mata akayi mata kitso, yanda suka dameta da a saka mata bakin lalle akan jan da yake hannunta zaiyi kyau, harda Hauwa din yasa ta bari, da yake babban saloon ne, har su gyaran jiki anayi. Lokacin da suka gama, wani yawon Hauwa ta sake janta, wai zata kai dinki. Gidansu Waheedah tace ta sauketa, lokacin gab da magriba, dan anan Hauwa tayi magriba tana ta sauri
"Yau zan sha fada nasani Wallahi"
Hauwa ta fadi hankalinta a tashe, bakomai Yassar yake magana a kai ba, amman Allah yai mata son yawo, shikuma ya tsani taje unguwa tayo dare, tasani kawai taurin kaine irin na mata, dariya Waheedah ta dinga mata, har bakin mota ta rakata tukunna ta koma ciki tana samun Mami a dakinta, gefen gado ta zauna tana fadin
"Mami zan koma"
Numfashi mai nauyi Mami ta sauke
"Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, karkiyi wasa da addu'a, kinsan in kina da matsala waya kawai zaki dauka ki kirani ko?"
Kai Waheedah ta jinjina mata, addu'o'inta Mami ta sakeyi musu tana kara binta da nasiha mai ratsa jiki, tukunna ta dauki Hijab dinta tana barin Ikram ta wuce bangaren Abba, shisa ta kirashi kar yaje gidan Yassar zata taho gida itama. Da sallama ta tura kofar tana shiga falon Abban da murmushin dake fuskar shi ya nutsa wani abu a zuciyarta
"Abba..."
Waheedah ta fadi cike da farin ciki, bata taba tunanin zata kaunaci wani da jinin shi baya yawo a jikinta da yawa haka ba, tana son Abba da dukkan zuciyarta. Babu jinin shi a jikinta, amman kaunar shi na ciki ta gauraye, karasawa tayi ta zauna a gefen shi kan kafet bayan sun gaisa
"Kina lafiya ko?"
Abba ya bukata, yana jin dadin ganin murmushin da yake kan fuskarta
"Ina lafiya Abba..."
Numfashi mai nauyi Abba ya sauke
"Kin yi magana da AbdulKadir din?"
Kai ta jinjina ma Abba a kunyace, murmushi yayi ba saita fada mishi ba, yasan sun shirya da AbdulKadir din, tsakanin mata da miji daman ance sai Allah.
"Babu inda hakuri ya tashi a banza Waheedah, kar wani ya taba sa kiji hakurin ki yayi yawa. Karki bari halayen kowa ya canza naki masu kyau. Da yawan lokaci rashin kirkin mutane na gurbata na masu kirki....karki bari hakan ya faru dake kinji?"
Kai ta sake jinjina wa tana furta
"In shaa Allah"
Numfashi Abba ya sauke yana cigaba da fadin
"A lokaci daya kuma karki bari hakurin ki yaja miki raini, ko da zaki yafe in an miki kuskure ki nuna hakan, ba saikin yi da hayaniya ba, tunda ba halinki bane, kiyi a nutse, karki barshi a cikin ki zai cutar dake. Allah yai miki albarka, Allah ya shirya miki zuri'arki"
Da wani yanayi a muryarta tace
"Amin Abba, Allah ya bamu aron rayuwa mai tsayi tare da kai"
Da murmushi a fuskar shi ya amsa ta da
"Amin..."
Yana dorawa da
"Ba gidan ki zaki koma ba?"
Kai ta sake sunkuyar wa cike da kunyar shi data lullube ta, hakan yasa Abba fadin
"Kije ki shirya ki fito in kai ki"
Mikewa tayi dan ji take kamar zata nutse a wajen saboda kunya. Babu abinda zata dauka banda Ikram, Fajr na wajen Hajja, kunyar Hajja din takeji dan dazun batasan bakinta ya subuce ta mayar mata da magana ba. Duk gidan itace ta farko da ta sameta har gidanta bayan taji Nuriyya ta tare ta bata hakuri, ita ta fara nuna mata ko kadan bada son ranta akai auren AbdulKadir din da Nuriyya ba, duk da a lokacin ta nuna ma Hajjan babu komai, bata kwana uku bata kirata taji lafiyarta ba, matar bata nuna mata komai banda kauna ba. Sallama tayi da Mami tana goya Ikram, ta samu Abba harya fito ma yana motar shi a zaune. Budewa tayi ta shiga gaba ta zauna tana mayar da murfin ta rufe.
*
A kofar gida Abba yayi parking yana kiran wayar AbdulKadir din, da ya fito ko takalma babu a kafafuwan shi, kamar baiga Abba a tsaye ba yace
"Waheedah..."
Yana kasa boye farin cikin shi, kunya tasa Waheedah raba AbdulKadir din ta wuce cikin gidan da sauri. Sai lokacin AbdulKadir ya kalli Abba yana fadin
"Abba... Ina wuni"
Harar shi Abba yayi
"Sai yanzun kaganni?"
Dan sosa kai AbdulKadir yayi yana karasawa wajen motar Abban ya jingina, yanajin tsakuwoyin da yake takawa da suke tunasar dashi bai ko saka takalma ba.
"Ba yaro bane kai da zan zauna ina maka fada akan duk wani abu na rayuwa, ya kamata ace ka hutar dani haka AbdulKadir, kasan wasu abubuwan sun kamata ko basu kamata ba, bansan me kai mata ba wannan karin, ban kuma san inda ta sami karfin zuciyar yafe maka ba. Amman banajin ni zan yafe maka idan ka sake taba ta haka, Hajiya Safiyya tace mun Fajr ya fada mata ka ture Waheedah harta fadi, ya kuma yi kankanta ya shirya karyar da baigani ba haka"
Kan shi AbdulKadir ya sadda kasa yanajin maganganun Abban na shigar shi sosai
"Bansan inda ka sami tarbiyar dagama matar aurenka hannu ba, nikam badaga wajena ka dauka ba..."
Abba ya karashe maganar cikin sanyin murya kafin yace
"AbdulKadir..."
Yana saka AbdulKadir din dagowa ya kalli Abba
"Ranar da duk ka sake dagama yarinyata hannu, ka kalli fuskata ba wasa nake da kai ba, wallahi ka daki aurenka"
Rufe fuskar shi AbdulKadir yayi da hannuwan shi biyu yana budeta, kirjin shi na daukar dumi kamar ana gobara a cikin shi, muryar shi a karye yace
"Abba nima dan ka ne... Itama kace mata idan nayi mata abu ta dinga fadamun ina bata hakuri, kace mata ta daina bari a ranta babu kyau. Abba ka kalli yanda duk ka tsoratani"
Ya karasa yana goge zufar da take tsatssafo mishi a goshi, amman fuskar Abban babu wani alamar wasa, shikam yanzun kowa yagane raunin shi, rabuwa da Waheedah ne raunin shi, shisa suke son kashe shi duk su huta, yasan da yayi abu zasu dinga mishi barazanar rabashi da Waheedah din tunda sun san hankalin shi tashi zaiyi
"Itama in kirata kace mata a bakin aurena idan tana qullata ta"
Mota Abba ya bude ya shiga yana mayar da murfin ya wuce, ya yarda akwai mutanen da duk shekarun da zasuyi a duniya rashin hankali bazai taba barin su ba, ciki harda AbdulKadir.
"Kaji Abba..."
Baiko kalle shi ba, ya tayar da motar, murmushi AbdulKadir din yayi
"Nagode Abba... Zan kiyaye in shaa Allah, zan kiyaye"
Ya sake jaddadama Abban, kafin yaja motar shi ya wuce. Numfashi AbdulKadir ya sauke yana wucewa cikin gidan. Shima da magriba Yassar ya dawo dashi, dan asibitin kin sallamar shi sukayi sai da suka karasa mishi wani ruwan da allurar da ta sakashi bacci har kusan magribar, bai jima da dawowa ba, wanka kawai yayi tunda sunyi sallah a hanya. Har haushin Yassar yaji da yace
'Matar ka bata da hankalin da zaka wuni baka koma gida ta nemeka ba ko?'
Duk da gaskiya ce ya fada, Nuriyya din ko flashing batayi mishi ba, ya kuma ji haushi sosai, dan shi mutum ne mai bala'in son kulawa, shisa tunda ya dawo yake shashareta, ya kuma ga bata damu ba, hidimarta kawai takeyi, yayi alkawarin zai dafata a ruwan sanyi, dan bazai dauki wannan halin ko in kula din nata ba, inma ba da gangan takeyi ba, bangaren Waheedah ya shiga yana samun ta ta fito daga bandaki, da alama alwala tayi, bata ce mishi komai ba ta dauki hijab dinta, shima bandakin ya shiga ya daura alwala yana fita masallaci, zuciyar shi a nutse yake jinta har aka idar da sallah. Ko azkar bai tsaya yiba ya dawo gida, dan so yake yagan shi a kusa da ita.
Ita kam Waheedah zafi taji ya isheta ta sake watsa ruwa tana idar da sallah, doguwar riga ta saka ta material dinki bubu, yadin blue mai haske, ta dauki hula kalar shi mai cizawa ta saka a kanta, tana jin dadin wutar da suka dawo da ita, dan fitilar waya take ta amfani da ita a dakin, torchlight dinta babu caji a jiki. Duk da darene jambaki ta tsinci kanta da shafawa a labbanta, tana dan murza mai a hannuwanta, ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin kamshi. Sanda AbdulKadir ya shigo ta sauke ikram kan katifarta, tana kara gyara gadon da yake a hargitse. Tsaye yayi a tsakiyar dakin, kamshin ta na saka shi lumshe ido, wata irin kewarta na dabaibaye shi.
Har inda take ya taka yana rungumeta ta baya ya sumbaci kuncinta, cikin kunnenta yace
"Ki yafemun Waheedah, dan Allah ki yafemun"
Tanajin yanda maganar ta fito daga zuciyar shi, zame jikinta tayi daga nashi, tana juyowa ta fuskance shi, fuskar shi take kallo sosai, tana saka hannuwanta ta rike kuncin shi, tanajin yanda sai da tadan daga kafafuwanta, girman shi harya daina bata mamaki, kallon shi tayi na wasu dakika kafin ta sauke hannunta batare da tace mishi komai ba, a shirunta yake karantar yafiya, duk yanda idanuwanta suke tabbatar mishi yana da sauran lokaci kafin ta sauka daga fushin da take, zaiyi komai, indai tana kusa dashi duk mai sauki ne.
Gadon ta karasa gyarawa, ta dauki Ikram dake ta bacci ta mayar da ita kan gadon tana ficewa daga dakin zuwa kitchen, tanajin AbdulKadir na biye da ita, mukulli tasa ta bude kitchen din tana turawa, tabar mukullin a jiki, tsugunnawa tayi tana bude kwalaye da ledojin siyayyarta, AbdulKadir na tsaye yanata binta da idanuwa kamar bai taba ganinta ba, ta mishi kyau sosai. Da ance mishi lokaci zaizo da zaiji shakkarta zai karyata, amman yanayin dake fuskarta yasa shi hakura da duk yanda yake son sumbatarta. Yanzun ma kasa hakura yayi ya tsugunna kamar zai tayata fiffito da kayayyakin da take ya kamo hannunta da yasha lalle yana dago shi ya sumbata.
Kallon shi Waheedah tayi tanajin yanda ko meye tasa ta lullube kaunar shi dashi yana soma budewa, hakan yasata zame hannunta daga cikin nashi
"Aiki nake Sadauki"
Ta fadi tana dauke idanuwanta daga kan shi, ta dauki ledojin maggi tana dorawa kan kantar kitchen din ta dauko robobinsu ta bude kowane tana juye shi a mazaunin shi. Baice mata komai ba, kayan ya tayata shiryawa, suna cikin aikin Nuriyya ta karaso wajen da murmushi a fuskarta, wutar da aka kawo yasa ta fitowa falon sai taji motsin yayi yawa shisa ta fito, sosai taji sanyi a ranta na ganin Waheedah din, taliya ce ta samu ta dafa fara, tanayin miyar da ko a ido batai mata kyau ba.
Tunanin abinda zasuyi suhoor dashi takeyi da yanda zata kaya musu washegari, ranta duk baya mata dadi, amman yanzun tasan indai girki ne ta kare, fadansu da ta hango ita da AbdulKadir kan hakan ya wuce. Sosai hankalinta ya kwanta
"Waheedah... Ashe kin dawo"
Ta fadi tana saka Waheedah din da AbdulKadir juyawa a tare, Waheedah najin wani abu ya taso mata daga dan yatsan kafarta zuwa tsakiyar kanta yana dawowa kirjinta ya tokare, AbdulKadir kuwa wani irin tsoro da baiyi tsammani ba yaji ya lullube shi, kar Nuriyya din tayi kokarin rike shi a gaban Waheedah, da sauri yazo ya rabata ya fice daga kitchen din yana wucewa bedroom din Waheedah ya turo kofar, jikin shi yakeji har bari yake mai, dan baisan ya zaiyi ba, a karo na farko a rayuwar shi da komai ya kwance mishi.
Waheedah kuwa wani kallo tayi ma Nuriyya din da yasa taji gwiwoyinta sunyi sanyi. Ba zatace tun zuwanta gidan suna hira da Waheedah din ba, ko kuma sunci gaba da zama kawaye, amman suna gaisawa kullum, kuma tana shigowa bangaren Waheedah din ta zauna a falo, har remote take dauka tayi kallo, musamman in tajiyo kamshin girki, data kula ko batazo ba tana bata abinci saita rage zuwa sai AbdulKadir na nan. Amman Waheedah daman ta daina fara'a a gabanta, sai dai bata mata irin wannan kallon, bata mata kowanne kallo ma.
"Sannun ki"
Waheedah ta fadi tana juyawa taci gaba da abinda takeyi, watakila ko dan batajin dadine, Nuriyyar tayi tunani, hakan yasa ta wuce ta koma bangarenta dan bata kula da sanda AbdulKadir ya fice ba. Tsaf Waheedah ta karasa gyara kitchen din tana share shi, fridge dinta ta bude taga an dibar mata robobin kayan miya, ta kuma san Nuriyya ce, daga yau kuma ta kare, can gidan kasa ta tsugunna, tana janyo kwami ta ciro roba fara mai murfi, dakyar ma ta fito da ita dan tayi kankara. Farfesun kayan cikine a ciki, tukunya ta dauko ta saka robar a sink tana sakar mata ruwa dan yadan saki.
Doya ta yanka da zata isheta iya cikinta, ta fere tana zuba dan mai a abin suya, ta soyata fararta, tana kwashewa a plate. Lokacin farfesun ya saki, iya wanda zai isheta ta diba ta zuba a tukunya tana mayar da sauran a fridge. Ta dora, da yake yasha kayan kamshi, kafin kace wani abu gidan ya budade da kamshin daya fito da AbdulKadir yazo kitchen din yana fadin
"Me kike dafa mana?"
Juyowa tayi tana kallon shi
"Daga dawowata zan karbi girki? Banda lafiya ko ka manta, sai jibi nikam"
Da mamaki AbdulKadir yake kallonta
"A'a ba abin tashin hankali bane ba, sai in koma gida, jibin in dawo"
Kai ya girgiza mata da sauri, shi bashida karfin fada koyin gaddama da ita. Duk da yaso jinta a jikin shi daren yau, kwana biyu bazai canza wani abu ba, sanin tana cikin gidan ya ishe shi, ran shi ya biya da abincin sosai, wata yunwa da baisan yanajin taba ta taso mishi. Dan waje ta samu ta juye farfesun a ciki, AbdulKadir din yakai hannu zai dauki guda daya ta doke hannun shi
"Ni ban dafa da kai ba Wallahi"
Tana janye kwanon ta ajiye gefe, kallonta yake, yayi mata laifi yasani, ya bata hakuri kuma
"Ba kyau horon yunwa"
Ya fadi can kasan makoshi, Waheedah nayin kamar bataji shi ba, duk abin ya mishi wani iri sosai dan bai saba ba, sau nawa take hakura da abu tabar mishi, amman yau itace take cewa tayi girki banda shi, zuciyar shi batai mishi dadi ba sam, tukunyar data bata take wankewa. Sai ga Nuriyya ta shigo kitchen din tana ta washe baki, dan tana sallar isha'i take jiyo kamshin, yawunta sai tsinkewa yake, kwana biyu bataci abu mai galmi-galmi ba.
"Kamshi duk ya cika gidan, me ake dafa mana ne"
Ta fadi kamar yanda ta saba, AbdulKadir na kallonta a karo na farko yaga kwadayi a fuskarta, baisan ko dan shima an hanashi bane yasa shi jin haushin kwadayin nata. Ga mamakinta ko inda take Waheedah bata kalla ba, asalima plate din doyar ta dauka da kwanon farfesun tana zuwa ta gabansu,
"Kudan fita zan rufe kitchen din"
Ta fadi tana ganin suka fita bakin kitchen din suna ta kallonta, sai da ta janyo kitchen din tasa mukulli ta rufe tukunna ta wuce da fadin
"Sai da safen ku"
Su biyun suna binta da kallo cike da mamaki
"Ina namu?"
Nuriyya ta fadi bayan Waheedah ta shige lungun da zai kaita dakin baccin ta, dakuna fuska AbdulKadir yayi
"Nima bata bani ba"
Ya amsa ranshi a jagule yana wucewa bangaren Nuriyya din, da duk da mamakin da take bai hanata jijjiga kitchen din ba taji da gaske a kulle yake, dan Waheedah bata taba rufe kitchen dinta ba. Tsaye tayi a wajen ta kasa yarda da abinda ya faru...!
#LubnaSufyan
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
31
Da wani irin sanyin gwiwa ta karasa bangaren ta, watakila har yanzun Waheedah batajin dadi, in baka da lafiya daman komai fita ranka yake shisa. Ko kuma taji haushine dan batai mata ya jiki ba, ita kuma sai lokacin tunanin yazo mata. A haka ta karasa bangarenta, ta samu AbdulKadir kan doguwar kujera a zaune. Karasawa tayi ta zauna a gefen shi, yanajin shigowarta, ran shi a bace yake, ga yunwa da yakeji kuma. Baisan me yasa sai yanzun yake jin haushin ta ba, dana kudin shi da ta kashe, da kuma na yau da ko kadan bata neme shi ba ballantana tasan bashida lafiya harya yini a asibiti.
Har yanzun yaga alama batasan waye shi ba, ko dan rashin Waheedah a kusa dashine yasa yake ganin komai ma bashida muhimmanci, yanzun da yasan ba zata barshi ba, ya samu natsuwar da zai fuskanci sauran matsalolin shi. Bayason kashe kudin da bashida dalili, komai nashi a kan tsari yake, sosai yakan yi tunanin abinda takeyi da kudi, kuma ba a dan zaman sun