Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
yanda zaiyi
"Kaman nawa zai isa"
Ya tambaya
"Gaskiya bazance ba, daga dubu dari in kana da hali har dari biyu ma, ko kasa da hakan. Iya aljihunka iya abinda zaka yi"
Shiru AbdulKadir yayi
"Idan nace banda dubu dari biyu nayi karya, amman akwai hidindimu a gabana nikam, matata nada ciki"
Yar dariya Anty tayi
"Bakayi tunanin akwai wata hidima a gabanka ba kake shirin kara aure, na dauka halin naku na mazane ya motsa ai, aljihunka kaji a cike da kudin da bakasan yanda zakayi dashi ba sai karin aure..."
Dan murmushi AbdulKadir yayi
"Nasan ba zamu gama wayar nan lafiya ba Anty... Dole sai kin fadamun maganar da zanji daman ban kira ba"
Dariya Anty tayi sosai
"Allah ya shirya mana halinka AbdulKadir..."
Sallama yai mata hadi da godiya kafin ya kashe wayar. Da gaske yake da yace mata hidima ce a gabanshi, akwai kudaden da yake ajiye da sai dolece take sakawa ya tabasu, yana ajiyewa ne saboda tsaron lalura. Dan sai da aka haifi Fajr tukunna yasan kula da yara ba abu bane me sauqi. Saima daya fara haqora, ga kyanda. Shisa baya wasa da ajiye kudi dan irin lalura haka. Yanzun kuma Waheedah nada wani cikin, yana son ta samu duk kulawar da take bukata, asibiti me kyau da baifi karfin shi ba. Sannan ga kayan babies da itama kayan da zai mata da sauran hidindimu. Amman auren ma shiya yanke hukuncin yin shi. Dole ne yayi abinda ya dace.
Akan maganar kudin kayan ne sukai doguwar waya da Nuriyya. Ya karbi account number dinta ya tura mata, ta mishi maganar tarewa yace mata saiya koma nan da sati biyu sai suyi maganar. Badan bashida wajen da zai ajiyeta ba, sai dan har zuwa lokacin bai fadama Waheedah ba. Duk wayar da zasuyi sai yaji zuciyarshi ta doka, hankalin shi baya kwanciya sai yaji tana mishi hira, gani yake kamar wani daga cikin yan gidansu zai sameta ya fada mata. Duk da zaiso hakan, zasu hutar dashi, amman kuma dukkan zuciyarshi na fada mishi zai kyautu ya fada mata da kan shi. In da zai samu kwarin gwiwar yin hakan.
Idan yace ga yanda watan ya wuce mishi da sauri haka yayi karya. Bai taba ganin gudun kwanaki ba sai da yagan shi yana hada abinda yake bukata a yar jakar shi da yammacin juma'a, dan ranar zaibi motar dare ya isa Kano da safiyar asabar. Yasan yau dinne ranar karshe da yake da ita da zai fadama Waheedah ya kara aure, idan bata sani yau ba sai yaje gida gobe tukunna, ba kuma yajin zai iya kallon idanuwanta ya fada mata. Bashi da wannan karfin halin, yanzun kuma yake sanin hakan.
Gefen gadon dakin yake zaune, ya mika hannu ya dauko wayar shi. Lambar Waheedah ya lalubo, basu dade da gama magana ba, ita tasa shi ya tashi ya hada kayan shi, tace karya taho da yunwa, yaci wani abu. Amman abinci ne karshen abinda yake ranshi. Sake kira yayi, ta daga da fadin
"Sadauki... Harka shirya kayan?"
Kai ya daga mata batare da yace komai ba, dan a rayuwarshi ita kadaice take fahimtar shirun shi, da yayi magana da baiyi ba Waheedah takan fahimta, abin ya daina bashi mamaki.
"Menene? Shirun nan naka yana mun yawa kwana biyu. Wani abu yana damunka amman kaqi fadamun ko?"
Numfashi ya tsinci kanshi da saukewa da baisan yana rike dashi ba. Muryarshi na rawa yace
"Magana nake so in fada miki, ba tun yau ba, tun ana gobe zan taho, bansan ta ina zan fara bane Wahee...a karo na farko da bansan yazan miki magana ba, ina nufin kece, komai fada miki nake batare da tunani ba, na kasa yanzun.... Ina so in fada miki har raina amman na kasa"
Ya karashe yanajin wani irin tashin hankali da bai taba tunani ba
"Nice kaman yanda kace... Akwai wani abu da zaka boyemun? Ka fadamun dan Allah... Menene?"
Kai AbdulKadir yake girgizawa, yanayin muryarta ya kara sakawa yaji komai ya kwance mishi
"Bansan ya zan fara ba"
Shiru tadanyi na wasu dakika kafin tace
"Sadauki kana tsoratani, cikine a jikina ko ka manta? Ka fadamun dan Allah"
Wannan karin hannu yasa yana dafe kan shi, bugun zuciyarshi na karuwa, sauke wayar yayi daga kunnen shi yana kashewa. Kafin ya rasa kwarin gwiwar da yakeji ya bude shafin tura saqo ya fara rubutu
'Aure nayi ana gobe zan dawo Waheedah, bansan yazan fada miki ba'
Ya tura yana jin kamar yabishi ya kamo, sai dai kamar auren shine, ya riga da ya faru, babu damar komawa baya ya canza komai, sakon ya riga ya shiga dan ya nuna mishi alama Waheedah ta samu, zufa yakeji a duk wata kafa ta jikin shi yana jiran ganin sakonta. Da hasken wayar ya dauke sai ya sake tabawa, bai san ya dauki mintina talatin yana jiran sakonta ba saida ya duba lokaci.
'Dan Allah kice wani abu Waheedah, ki ce wani abu'
Nan ma saida ya kara mintina goma yana zufar da duk iskar fankar dake dakin bata kai mishi kafin yaga wayar shi ta kawo haske. Jikin shi babu inda baya rawa ya daga yana dubawa.
'Ran daren da zaka tafi? Wata daya daya wuce kenan ko?'
Da sauri ya fara bata amsa
'Da gaske Wahee, ki yarda dani tun ranar naso in fada miki, tun ranar'
Wannan karin bata dauki lokaci ba ta turo mishi
'Karka damu. Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, bari inyi alwala naji an fara kiran Magriba'
Wata irin ajiyar zuciya AbdulKadir din ya sauke, kafin ya sake ganin text dinta
'Allah ya tsare ya kawo mana kai lafiya, ka daici abinci karka manta. Zan sa chargy an kawo wuta, saura 2%'
Da murmushi a fuskarshi yace
'Nagode, Nagode sosai. In shaa Allah. Ki kulamun da ku. Zan kiraki dana shiga mota'
Ya sa ran amsa koya take, dayaga bata turo komai ba ya mike yana hakura. Wanka ya shiga yayi ya fito ya sake kayan jikin shi tukunna ya fita masallaci. Saida ya biya ya siya abinci yaci, hankalin shi yakeji ya kwanta sosai. Yasan daman idan kowa bai fahimce shi ba, Waheedah zata fahimce shi, shisa take da matsayin da babu wanda yake dashi a rayuwar shi. Yana dawowa jakar shi ya dauka yayi addu'a a bakin kofa kafin ya fita ya kulle gidan yana takawa zuwa gate da zai samu yaje inda zai hau machine zuwa tasha...!
#TeamWaheedah
#TeamAbdulKadir
#LubnaSufyan[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
24
Wayar tasa a chargy kamar yanda ta fada mishi, sai dai ta kasa dagowa daga tsugunnan da tayi. Wayar take kallo tana gane asalin ma'anar 'Yawo kan gajimare'. Duk da ba zatace ga ranar da wuyanta ya gajiya da daukar nauyin kanta ba, yau kan jinshi take kamar baya jikin ta, gashi yana mata tamkar iska ta cika shi tana fita ta hancinta da kunnuwanta har ma da idanuwanta. Kafin kan nata yai wata irin sarawa cike da fahimtar ma'anar
'Aure nayi ana gobe zan dawo Waheedah, bansan ya zan fada miki ba'
Da kuma abinda hakan yake nufi a rayuwarta, numfashinta takeji yana barazanar kin wuce kirjinta yakai inda zai ba zuciyarta damar cigaba da dokawa yanda ya kamata. Wani irin numfashi take ja a wahalce, a karo na farko a rayuwarta da tashin hankalin da takeji yafi karfin hawayenta.
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ta samu furtawa tana zama sosai kafin taja kafafuwanta ta dora kanta a sama ko zataji saukin zafin da zuciyarta take mata, lokacin da ta fara laulayi jinta take a wata duniya ta daban, duniyar da wanda ya taba shiga halin da ta tsinci kanta ne kawai zai fahimta, bata san akwai duniyar da zata shiga tafi waccen wahalar sha'ani ba sai yanzun. Ciwo take ji daya wuce fatarta da jininta zuwa cikin kasusuwan jikinta. Idan tace ga asalin abinda ya fi mata ciwo karya take.
Auren da yayi da batada darajar da zata sani kafin a daura shi, kallon idanuwanta bayan an daura din dayi mata murmushi kamar babu wani abu mai muhimmanci da yake tunanin ya kamata ya sanar da ita, ko kuma zabar ya fada mata abinda ya canza rayuwarta da ta tashi ta sakon waya.
"Banda daraja har haka a idanuwanka Sadauki? Ban nuna maka farin cikin ka na da muhimmanci a wajena bane da zai isa in baka goyon baya akan kowanne irin al'amari ba?"
Waheedah take maganar kamar zararriya, dan batasan a fili takeyin ta ba, ta dai san daga wani bangare na zuciyarta mai ciwon gaske maganganun suke fitowa. Bata san iya lokacin da ta dauka a zaune tana kallon bango batare da tasan asalin abinda take tunani ba, banda wani irin ciwo da bata tunanin akwai abinda yake da maganin shi batajin komai. Kamar a wata duniya da ta jima da bari take jin wayarta na ruri, dakyar ta iya raba idanuwanta daga bangon da take kallo tana sauke su akan wayar
'Sadauki'
Ta gani rubuce a jiki
"Me kake so dani Sadauki?"
Ta tambaya tana kallon wayar harta yanke, wani sabon kiran ya sake shigowa. Hannu ta mika ta zare wayar daga chargy tana dannawa ta amsa kiran hadi da karawa a kunnenta da wani irin sanyin murya tace
"Hello..."
Tana mike kafafuwanta da sukai mata sanyi, ga abinda ke cikinta da taji ya dunqule waje daya kamar yana tayata daukar ciwon da takeji, hakan nasata fahimtar wani irin ciwon mara da batasan tun yaushe ya fara mata ba.
"Kin fara bacci ne?"
Kai ta girgiza mishi a hankali, a karo na farko da taji muryarshi na kara mata ciwo, taji da magana dashi gara mata kallon bangon da takeyi, shi baya kara mata ciwo, amman muryar AbdulKadir din kamar gishiri a sababbin ciwukan da yaji mata takejinta.
"Na sa chargy ne"
Dan jim yayi ta dayan bangaren kafin yace
"Inata kira tun dazun babu network"
Sama-sama take jinta, komai na mata wani iri
"Har kun taho?"
Ta tsinci kanta da tambaya
"Tun dazun, amman cunkoso har yanzun muna cikin Lagos"
Kai ta jinjina mishi
"Allah ya tsare maka hanya ya kawo ka lafiya"
Amsawa yayi da
"Amin..."
Yana dorawa da
"Ki kula da kanku"
Ita ta jinjina kan tana kasa cewa komai ta sauke wayar daga kunnenta, chargyn ta mayar, dakyar ta iya mikewa, wani irin jiri daya dibeta yasa ta koma tana kiran sunan Allah duk wanda ya zo bakinta. Numfashi take fitarwa a wahalshe, ciwo take ji da bazai misaltu ba, tafi awa daya a zaune kafin ta iya mikewa, Fajr ma bata iya ta matsar dashi gefe ba, ita taja jiki kan katifar ta kwanta gefen shi. Ko sallar isha'i batayi ba, amman ciwon da takeji ba zata iya zuwa bandaki har ta iyayin alwala ba. Daga kwancen ma jiri take ji. Bata san dare yayi ba sai lokacin da ta samu ta sauko daga gadon ta dauki wayar ta taga karfe daya. Ajiyewa tayi har lokacin jiri takeji.
Ga ciwon marar da takeji ya tsanantar mata, ga wasu ciwukan daban da ba zatace ga daga inda suke fitowa ba, amman mararta da zuciyarta su tafi ji. Bango ta dinga bi har takai bandaki, dakyar ta iya daura alwala ta fito. Daga zaune tayi sallah dan ba zata iya tsayuwar ba, azkar ta gabatar na bayan sallah, tana kwanciya anan kan kafet din dan ko addu'a bata iyayi ba. Sunayen Allah duk wanda yazo bakinta fadin shi takeyi ko zata samu saukin azabar da takeji. Akan kunnenta akai kiran sallah na farko, har aka sakeyin wani aka shiga masallaci tukunna ta iya raba jikinta da kafet din. Alwala ta sake zuwa tayi dan batajin ta cikin yanayin da zata tabbatar tana da alwalar.
Ta shiga wata duniya mai wahalar misaltawa. Sallah ta dawo tayi, tana sake komawa ta kwanta kan kafet din. Sai yanzun takejin dama ta kira Yassar jiya ya dauki Fajr, dan ko wanka ba zata iya mishi ba, ballantana abinda zata bashi yaci. Wajen shidda na safe ko motsin kirki bata iyayi, ga wani irin zazzabi mai zafin gaske daya lullubeta. A haka AbdulKadir ya shigo ya sameta, dan shi ya dauka bacci takeyi da yaita sallama yaji shiru.
"Waheedah..."
Ya kira yanajin gabanshi yayi wata irin faduwa, da sauri ya karasa yana tsugunnawa ya dagota, jikinta da yaji kamar garwashin wuta yasa shi fadin
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Yana dorawa da
"Baki da lafiya? Tun yaushe Wahee? Me yasa baki fadamun ba?"
Dakyar ta iya bude idanuwanta ta kalle shi, da gaske kara mata ciwo yakeyi, daga muryarshi har tabatan da yakeyi. Tana ji ya zameta daga jikin shi yaje ya tashi Fajr daya shagwabe fuskarshi cike da bacci zaiyi kuka, ganin AbdulKadir din yasa yaron wartsakewa dukkan shi
"Paapi"
Ya fadi yana riko AbdulKadir din daya kamashi ya sauko dashi daga kan gadon
"Fajr tashi, Omman ka zamu kai asibiti"
AbdulKadir ya karasa maganar yana yin bandaki da Fajr, fuska ya wanke mishi yaga abin bazaiyi ba. Da kanshi yai ma yaron wanka ya goge mishi jiki da towel, kaya yazo ya dauko mishi yanajin dadin yanda komai yake a shirye, baisha wata wahala ba. Yana gama saka ma Fajr kaya da yake ta mishi surutun da hankalin shi baya kai, yaga Waheedah taja jiki dakyar ta mike. Muryarta na rawa tace mishi
"Nikam kabarni da zuwa asibitin nan"
Ko inda take AbdulKadir bai kalla ba, Fajr ya zaunar kusa da ita, ya koma ya dauko wayarshi dake cikin jaka. Yassar ya kira, sai da ta kusa yankewa tukunna ya daga batare da yace komai ba, jin hakan yasa AbdulKadir fadin
"Hamma banzo da mota ba, Waheedah bata da lafiya kuma..."
Da sauri Yassar din yace
"Subhanallahi, ina zuwa yanzun"
Ya kashe kiran daga can bangaren shi, yana saka AbdulKadir din bata rai, bayaso a kashe mishi waya a kunne, ko kadan abin na bata mishi rai, ya kuma rasa dalili. Wayar ya ajiye kan gado yana karasa ya kama hannuwan Waheedah duka biyun, batayi mishi musu ba. Kasa yai da muryarshi sosai saboda Fajr dake zaune a wajen
"In tayaki kiyi wanka?"
Kai ta girgiza mishi
"Zan iyayi... Ka rakani bandakin kawai"
Taimaka mata yayi har cikin bandakin, duk da hankalin shi bai kwanta daya barta ita kadai din ba, fitowa yayi yai tsaye bakin kofar bandakin, duk bayan wasu daqiqa saiya kira sunanta duk da yasan babu kyau tayi magana a bandakin. Badon Fajr ba shikam shiga zaiyi, karta fadi a ciki ya shiga uku. Saida yaga ta fito tukunna hankalin shi yadan kwanta, kama hannunta yayi yana janta zuwa gefen gado ta zauna. Da kan shi ya dauko mata doguwar riga da inners ya ajiye mata akan gado gefenta
"Sannu, Bari in hadama Fajr Tea"
Kai Waheedah ta daga mishi, ya kama hannun Fajr din suna wucewa kitchen. Flask ya fara jijjigawa yaji akwai ruwan zafi a ciki, ya samu kofi ya zuba madara da milo ya hada mishi rabi, ya saka sikari yana juyawa. Hannun yaron ya sake kamawa har falo ya zaunar dashi kan kafet yana ajiye mishi kofin shayin, Fajr na kama kofin yaga yana tiriri ya kalli AbdulKadir din
"Bamai zafi Omma take bani ba"
Kofin AbdulKadir ya dauka ya kurbi shayin, babu wani zafin da bazai iya sha ba
"Wanne irin shayine bamai zafi ba Fajr?"
Shagwabe fuska Fajr yayi
"Na Omma..."
Kai AbdulKadir ya jinjina yana ajiye kofin
"Bata da lafiya, sai kasha nawa yau"
Turo baki Fajr yayi
"Baka bani biscuit ba"
Runtsa idanuwa AbdulKadir din yayi, wajen matar shi yake son zuwa ya dubata, yaron yana da rikici, duk karancin shekarun shi baya hana AbdulKadir din zane shi. Kitchen ya koma ya dudduba, baiga inda Waheedah ta ajiye biscuit ba idan akwai kenan. Ya dawo yana fadin
"Ni banga biscuit ba"
Narai-narai Fajr yayi da idanuwa
"Kasan Allah idan kaimun rigima zaneka zanyi Fajr. Ka zauna kasha Tea din ka kana jina..."
Ya karasa yana juyawa ya koma wajen Waheedah, harta saka kaya, da alama tadanji kwarin jikinta da tayi wanka. Kusa da ita ya zauna yana taba wuyanta, da zazzabi har lokacin
"Shine jiya baki fadamun baki da lafiya ba?"
Idanuwanta ta ware mishi
"Zazzabi ne kawai, zai tafi"
Kai AbdulKadir ya girgiza
"Banaso... Karki karamun wannan, idan baki da lafiya ki fadamun ni dai"
Kai Waheedah ta jinjina mishi, ba zata iya doguwar magana ba, kirjinta yayi nauyi, mararta na ciwo har lokacin. Kiran Yassar yagani, hakan yasa bai daga ba ya mike yana ficewa daga dakin da falon gabaki daya. Fajr na ajiye kofin shayin ya bishi da gudu ko takaa babu a kafarshi, yana kara gudun shi ganin Yassar ne, cike da farin ciki yake fadin
"Uncle..."
Daga shi sama Yassar din yayi yana dariya
"Fajr..."
Ya kira yana rike shi a jikin shi sosai
"Zan bika ni"
Kai Yassar ya jinjina
"Tare zamu tafi aikam"
Tukunna ya kalli AbdulKadir da yake mishi murmushi, hade fuska Yassar yayi kamar bashi ya gama dariya ba
"Ya mai jiki?"
Ya tambaya, kai AbdulKadir ya jinjina
"Yanzun kai ma Fajr dariya kana magana muryarka lafiya kalau..."
Mukullin dake hannun shi Yassar ya mikama AbdulKadir din yana juyawa tare da Fajr din tunda yana da kaya a gidan. Kyaleshi AbdulKadir yayi ya koma cikin gida suna fitowa tare da Waheedah, da kanshi ya bude mata mota ta shiga ta zauna, ya rufe tukunna ya zagaya ta dayan bangaren, ya tayar da motar, yana ja suka fita daga gidan zuwa wani asibitin kudi na masu ciki da bashi da nisa sosai da gidan.
*
Har azahar suna asibitin, dan ruwa suka saka mata leda biyu. Har Hajja ya kira bata daga wayar ba. Sosai ran shi yaji bai mishi dadi ba, daman ya fada mata ne, sai a turo wani cikin yan gidan da zai tayasu aiki, Waheedah din ta huta. Amman zaiyi komai da zai iya, kuma yaga Waheedah din da sauki, duk da ance ta samu wadataccen hutu, kafin a sallamesu su tafi gida. Magunguna kala biyu ne kawai aka basu, duk zuwan da yake asibitin tare da ita, wannan ne karo na hudu magani sai dai yaga guda daya ko biyu, sam basa tila magunguna.
"Nikam kamar in dinga zuwa asibitin nan in bani da lafiya, sam basa bada magunguna masu yawa"
Ya fadi yana kwance takalman kafar shi, sai da Waheedah ta cire hijabinta tukunna ta kalli AbdulKadir din
"Asibitin masu cikin Sadauki?"
Dakuna mata fuska yayi
"Me yasa sai masu cikine kawai zasu je? Basa bada magani da yawa"
Kai Waheedah ta girgiza
"Dan na masu cikine shisa basa bayarwa da yawa, bakowanne magani ake sha ba in ana da ciki"
Kai ya jinjina mata yana fahimta, ita kuwa hannunta take murzawa inda akai mata karin ruwa tanajin yana mata ciwo. Har lokacin ba zatace ga asalin yanda takeji ba, kallon AbdulKadir