Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   42 / 51

123K to 126K   out of 152.3K words

kulle a gefe daya. Ko ina na jikin shi ciwo yake, har wajajen da bai taba sanin zasuyi mishi ciwo batare da zubar jini ba. Waheedah na tsaye tana kallon shi, yanda yakeyi kamar shi yayi watanni da ciwon da tayi fama da shi, a karo na farko halin da yake ciki bai taba zuciyarta ba, tana jin dadin yanda yake jin kadan cikin quncin da zuciyarta take fama dashi

"Kirjin ka kamar zai bude ko Sadauki?"

Ta bukata cikin wani irin sanyi murya da yasa AbdulKadir daga idanuwan shi da har sun canza launi yana kallon ta, rausayar da kai tayi

"Haka nake ji duk idan naganka tare da Nuriyya..."

Mikewa AbdulKadir yayi yana karasa inda Waheedah take, hannuwan shi yasa ya kama kafadunta yana dan dannawa cikin alamun ta zauna, batayi mishi musu ba tayi kasa tana zama kan kafet din dakin, shima zaman yayi a gefenta, dan dakin ya fara jujjuya mishi da jirin tashin hankali. Idan taci gaba da magana baisan inda zai saka rayuwar shi ba, ya bude bakin shi ya kai sau biyar amman ya kasa furta komai. Sai da yaja numfashi yana fitar dashi, kafin ya iya cewa

"Waheedah..."

Kalmar na fitowa daga wani sashi na zuciyar shi da yau dinne ranar farko daya san da zaman shi, runtsa idanuwan shi yayi yana bude su, cikin kan shi yake ji babu komai, baisan ko yanajin alamun kwakwalwa ba a baya, amman a yanzun bayajin komai sai kokon kan, balle yayi tunanin kwakwalwar shi zata taimaka mishi da wasu kalamai, amman kirjin shi ciwo yake kamar zai bude, da gaskiyar zancen Waheedah, bai gane yanda zai fassara abinda yakeji ba sai da ta fada, kan shi babu komai, amman zuciyar shi cike take fam da yanayoyi daban-daban, bude bakin shi yayi yana barin zuciyar shi ta mulki abin zai fito daga bakin shi

"Ina da son kai, ban taba sanin ina da son kai ba sai yau, kina da rashin adalci..."

AbdulKadir ya karasa maganar cikin muryar da ta dira kunnuwanshi kamar ta wanda yasha gudu, yana saka kwayar idanuwan shi cikin na Waheedah da take ware mishi nata cike da maiqon hawaye, kai ya daga mata a hankali

"Me yasa baki fadamun ba? Me yasa baki fadamun ba Wahee? Kince kina sona, ni nagani kina sona, me yasa kika boyemun?"

Kai Waheedah take girgiza mishi, idanuwan ta na tsiyayo wasu hawaye masu dumi, ba zai mata haka ba, ba zata bar shi ya dora mata laifin da bata da shi ba

"Me yasa ka boyemun za kai aure? Ka boyemun kayi aure har wata daya? Ka boyemun Kawata ka aura sai da ka shigomun da ita cikin gida?"

Jinjina kai AbdulKadir yayi, kalamanta duka suna dirar mishi kamar zubar ruwan gishiri a sabbin ciwukan da kalamanta na baya sukai mishi, yasan tana da muhimmancin a rayuwar shi fiye da yanda zai misalta da kalamai, bai dai san a tattare da muhimmanci akwai iko akan abubuwa da yawa da suka shafe shi ba, ciki harda zaman lafiyar shi, kwanciyar hankalin shi, nutsuwar shi gabaki dayan ta

"Hakane..."

AbdulKadir ya iya furtawa yana kallonta da wani nisantaccen yanayi, muryar shi yakeji na fitowa da wani sauti da baida fasali

"Ba uzurin da ya sani yin abinda nayi nake so in baki a kurarren lokaci irin yanzun ba..."

Ya fadi yana maida numfashi kafin yace

"Banda komai, ko kalaman ban hakuri bani dasu, wallahi banda kalaman baki hakuri"

Dan har zuciyar shi yakejin hakuri yayi kadan ya wanke girman laifin da yayi mata

"Shisa zan baki wani abu daban, zan baki dukkan gaskiyata, ban san zanyi aure ba, lokaci daya tunanin ya zo mun..."

Kai Waheedah take girgiza mishi, bata son ji, bata son jin yanda yayi aure, tunda ya rigada yayi, shima kan yake girgiza mata

"Za kijini, ba zaki yanke mun hukunci gabaki daya ba, kimun adalcin da ban miki ba dan Allah, na rokeki"

Cikin rawar murya data fito cike da sautin kuka Waheedah take girgiza mishi kai

"Son kai Sadauki, son kai ne wannan"

Kafada yadan daga mata, ita hawayenta sun zuba, ance kana samun sauki duk idan ka zubar da su, shi bai samu wannan zabin ba

"Nasani, halina ne daman..."

Cewar AbdulKadir din yana dorawa da

"Da sanin zanyi auren da auren duka a kwana biyu ya faru, na samu awanni 48 da zan dauki mintina talatin in fada miki zanyi auren, banyi ba, kuskurena ne wannan da zai zauna dani har karshen rayuwata..."

Hannunta ya kamo yana hada yatsunsu waje daya, yanajin yanda ta dumtse nashi cike da neman alfarmar da ba zai iya mata ba, idan bai fada mata na shi bangaren ba, yana da tabbacin kirjin shi budewa zaiyi

"Amman ni ne, bana tunani, ban fara tunani ba sai bayan nayi auren, na kasa fada miki, banji maganar su Hajja da suka fadamun akwai rashin kyautawa a abinda nayi ba saboda ina ganin addini ya halarta mun, banyi tunanin ke yanda zakiji ba har lokacin, nayi tunanin ban kyauta ba da ban fada miki ba, kin san me yasa?"

Kai ta girgiza mishi a hankali, akwai yanayin da yake tattare da muryar shi da bai hana gwiwoyinta yin sanyi ba duk da a zaune take

"Saboda ban saba boye miki abu ba, lokacin ya kamata in san ban kyauta ba..."

Wannan karin ajiyar zuciya mai nauyin gaske ya sauke

"Ina miki maganar Nuriyya ne saboda kece, badan na raina ki ba Wahee, ba dan in nuna miki na isa ba, Wallahi babu ko daya a ciki, ki yarda dani..."

Ya karasa maganar muryar shi na karyewa, kafin ya ci gaba da fadin

"Ina fada miki ne saboda ke ce"

Ya sake maimaitawa kamar 'Ke ce' din ta isa ta fassara mata abinda yake nufi, shi kuma kalaman da zaiyi amfani dasu dan ta fahimta yake nema

"Tun ban san zan aureki ba kike sanin abubuwa a kaina da ba kowa ne yake sani ba, saboda ke ce, ke kadai kikejin maganata idan raina yana bace, saboda ke ce, su Hajja na so na, amman basa son da yawa cikin halayena, suna magana a kai, baki taba ba, kina so na da komai nawa, shisa nabari kika sanni yanda kowa bai sanni ba"

Idanuwanta Waheedah ta runtsa tana kokarin hadiye yawu ko zai wuce mata da abinda take jin ya tsaya mata a kirji, shagwabe mata fuska AbdulKadir yayi cikin yanayin da bata taba gani ba, sai da taji zuciyarta ta doka da tunanin ko kuka zaiyi

"Ban miki maganarta dan in sosa ranki ba, na miki maganarta saboda komai nawa ina fada miki, banyi tunanin kishin da zakiji ba, saboda ina son kai na da yawa, wannan ma kuskurena ne... Auren kawar ki"

AbdulKadir ya karashe maganar yana runtsa ido kamar kalaman nashi sun raunani shi, kafin ya bude su yana ci gaba da fadin

"Wahee ina so ince ki yafe mun, amman ina jin hakan ma zai kara zama rashin adalci..."

Kai ta daga mishi tana tabbatar mishi da ta yarda da kalaman shi, hawayen da suka zubo mata na kara tafasa shi, numfashi ya sauke yana dago hannun su da yake hade yakai kan goshin shi, ya lumshe idanuwan shi yana kara sauke numfashi mai nauyi, duniyar ta mishi tsaye waje daya, yakai mintina biyu a haka, kafin ya iya dago da kan shi

"Son kai halina ne, shisa zan fada miki ba zan iya rabuwa da ke ba....Wallahi ba zan iya ba, da tunanin aikina zaiyi sanadiyyar mutuwata nake kwana nake tashi kullum, cikin sati daya kin nuna mun kinfi aikina wannan hadarin, Wahee zaki kasheni in kika barni...."

AbdulKadir yake fadi a susuce, babu komai cikin kan shi har lokacin, ba lallai bane kalaman da yake fadi suna da wata ma'ana tunda bayajin taimakon kwakwalwar shi a fitarsu, zuciyar shi ce kawai take haukanta

"Idan lokaci kike bukata zan baki... Komin tsayin lokacin da kike so ki huce zan baki..."

Kallon shi Waheedah take tana girgiza mishi kai cikin rashin yarda da cewar zai bata duk lokacin da take so, shi kuma yana fahimtar hakan da cewa tana nufin bata yarda ba, ya saukake mata auren shi, hakan yasa shi kara rikicewa da fadin

"Ba zan dinga zuwa ba, ba zan dame ki ba, duk lokacin da kike bukata..."

Dayan hannunta tasa tana goge fuskarta, taja hancinta da takeji yana mata radadi kamar ta shaqi barkono

"Shekara daya..."

Ta furta cikin dakusasshiyar murya, wannan karin dokawar da yaji zuciyar shi tayi da a kasar wajene ya tabbatar likitoci zasuji mishi tsoro bugun zuciya na farat daya

"Shekara biyu"

Waheedah ta sake fadi da wani nisantaccen yanayi a muryarta

"Uku... Hudu... Biyar...."

Taci gaba, ba iska kadai yakeji ta mishi kadan ba, hasken dakin yaga yana raguwa, ga zuciyar shi da take cigaba da dokawa tana mishi barazanar tsayawa, hannun Waheedah ya saki yana dafa gadon dake kusa da shi ya mike dakyar. Batace mishi komai ba, asalima da idanuwa take bin shi harya fice daga dakin, baiko ja mata kofar ba, bai taba ganin nisan daga cikin gidan Yassar ba zuwa harabar gidan inda ya ajiye motar shi. Wannan tashin hankalin bakon abune a wajen shi, kamar yanda tunanin da yai mishi daurin goro yake bako a wajen shi.

Dakyar yakai wajen motar shi, dishi-dishi yake gani lokacin daya bude ya shiga, bakomai na cikin tuqi yake iya tunawa ba, ya taka motar ne ta baya ya fita daga gidan, yana jin yanda ya daki gefen gate din dako gama budewa maigadin baiyi ba, haka yahau titi yana nufar hanyar gida, a ran shi yake karanto duk wani sunan Allah da yazo mishi, cike da yabo saboda yanda yake jinjina ikon Allah, yasan ba hankalin shi ya kai shi gida ba.

Lokacin da yayi parking din motar cikin gidan lumshe idanuwan shi yayi yana girgiza kan shi, ya sake bude su yana ganin duhun da yake son lullube mishi su ruf, dakyar ya fito daga cikin motar yana wani irin mayar da numfashi. Dishi-dishi yake gani duk yanda yake kara ware idanuwan shi, ga jiri da yakeji yana dibar shi. Ganin kamar Khalid yake hangowa yasaka shi kara ware idanuwan shi sosai, amman sai yake ganin Khalid din na rabe mishi gida wajen hudu. Da hannu yai ma yaron alama da yazo, yana sake runtsa idanuwan shi, can sama-sama yaji muryar Khalid din na fadin

"Hamma...Hamma lafiyar ka kuwa?"

Ko kai AbdulKadir ya kasa girgiza mishi, dan iskar wajen ta sake mishi kadan, Khalid kuwa a karo na farko da ya kai hannu yana kama na AbdulKadir din da tsoro daban, dan yanda yakeyi kokawa da numfashin shi kamar mai asthma

"Hamma..."

Khalid ya kira cike da tsoro, kafin AbdulKadir din ya lumshe idanuwan shi yana wata irin faduwa da ta saka Khalid sakin wani ihu daya fito daga kirjin shi da yake cike fal da tsoro

"Hamma AbdulKadir!"

Yake fadi yana tsugunnawa hadi da girgiza AbdulKadir din da baisan a wacce duniya yake ba, da gudu Khalid ya tashi yana nufar bangaren Mami da shine yafi kusa dashi, a falo yake kiran

"Mami, Hamma.... Hamma Mami"

Cikin tashin hankali Mami ta kama Khalid din, zatace a yaran gidan yana daga cikin wanda basu da hayaniya, baya shiga harkar kowa, daga gaisuwa sai kayi da gaske zaka sake jin maganar shi, duk cikin yaran Mama yafi kowa fita daban, bata taba ganin shi a hargitse ba, shisa lokaci daya hankalin ta ya tashi

"Wanne Hamman? Me ya faru Khalid?"

Ya kasa magana, da hannu kawai yake nuna mata alamar waje, bin bayan shi kawai tayi, daga nesa ta hango AbdulKadir din, da gudu ta karasa, cikin bayanannen tashin hankali tace

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un.... AbdulKadir... Khalid kira Hajiya Safiyya..."

Juyawa yaran yayi zuwa bangaren Hajja da ko mintina biyu ba'a cika ba ta karaso wajen tana tsugunnawa ta kama AbdulKadir din ta dago shi jikinta tana kasa yarda yaronta ne a kwance kamar gawa

"AbdulKadir..."

Ta kira tana dora hannunta a kan kirjin shi, bugun zuciyarshi shi a cikin tafin hannunta na nutsar da wasu bangarori a tare da ita da batasan a tashe suke ba sai lokacin, wani irin numfashi take saukewa, Mami da take tsaye cikin tashin hankali itama tace

"Mu tafi asibiti..."

Kai Hajja take girgiza mata, su biyun duka tana da tabbacin ba zasu iya daga AbdulKadir din ba, balle su saka shi a mota

"Ki kiramun Yassar"

Hajja ta fadi, badan babu wasu manyan yaran gidan da in aka kirasu zasu zo ba, sai dai duk wani abu da ya shafi AbdulKadir din Yassar ne yake fara sani, wani lokaci yana ma rigan su sani, kuma shine mutum na farko da ya fara zuwa ma Hajja a kai. Har Mami tabar wajen ta kuma sake dawowa Hajja na zaune rike da AbdulKadir, zata kirga lokuttan da taga bashida lafiya a tsayin rayuwar shi, rashin lafiya dai wadda zata kwantar dashi. Shisa yanzun bata ma san asalin abinda take ji ba, lokacin take gani baya mata sauri duk da ba agogo bane a gabanta, sai taga kamar tayi awanni zaune a wajen kafin motar Yassar ta shigo cikin gidan.

Ko kasheta baiyi ba ya fito, kallo daya za kai mishi kasan a hargitse yake, baiko bi ta kan su Hajja ba ya tsugunna yana dago AbdulKadir din hadi da girgiza shi

"AbdulKadir ba za kai mun haka ba fa"

Yassar yake fadi muryar shi dauke da wani yanayi na karaya da tsantsar tashin hankali, baya tunanin ko su Hajja suna shiga tashin hankalin da yake shiga duk lokacin da aikin AbdulKadir zai kai shi wani waje mai hatsari, yana da Yasir, amman a duniya ji yake idan ya rasa AbdulKadir yayi rashin da har nashi numfashin ya tsaya ba zai taba komawa dai-dai ba. Su Hajja nada wasu yaran, shi kam ji yake bashi da wani dan uwan, shisa yanzun ma yake da tabbacin basa cikin tashin hankalin da yake ciki. A kafadar shi ya saka AbdulKadir din yana mikewa da shi, bayan motar shi ya bude ya saka shi a ciki, ya rufe murfin.

Harya zagaya bangaren direba ya shiga yana jin nauyin AbdulKadir din a tare dashi, baibi ta kansu Hajja ba, baima kula da ta shigo motar ba, ja kawai yayi yana nufar hanyar da zata kaishi wani asibitin kudi da yake yan albasa na rijiyar lemo, dan abokin shi yana aiki a wajen shisa har yasan da asibitin, tunda a cikin lungu yake. Gudu yake yanajin kamar yabi takan motocin da suke gaban shi saboda saurin da yakeyi, a haka suka karasa asibitin, a kafadar shi ya sake daukar AbdulKadir yana shiga asibitin da gudu, wasu nurses na hango su suka taho dan su taimaka musu, ko ba mata bane Yassar bayajin zai mika musu AbdulKadir, wani daki suka nuna mishi, ya nufa da AbdulKadir ya shimfide shi kan gadon dakin, ana kiran likitan daya shigo a rikice shima.

Ya gane Yassar din, dan yana zuwa wajen Dr Isa sosai

"Kadan fita..."

Yace mishi, yanda Yassar ya daga ido ya kalle shi cikin yanayin dake fassara 'Wasa kake amman ko?' yasa likitan mayar da hankalin shi kan AbdulKadir da ko motsi bayayi har lokacin, bugun zuciyar AbdulKadir din na tabbatar mishi da a sume yake. Duk wata allura da akai mishi da ruwan da suka daura mishi a kan idon Yassar akayi shi. Da suka gama ma, baibi ta kan su ba, likitan ma da yayi mishi magana yaga alamar hankalin shi ba'a kan su yake ba, shisa ya fita yana samun Hajja dake tsaye bakin kofar, ko takalma babu a kafarta, Hijab din jikinta ma sallar azahar zatayi da a haka zata fito, ita sukai ma tambayoyin da suke bukata wajen bude ma AbdulKadir din kati, lokacin Dr Isa ya fito wajen, Dr Aminu na kallon shi da fadin

"Mahaifiyar Yassar ce abokin ka, sun kawo marar lafiya ne"

Gaishe da Hajja, Dr Isa yayi yana mata kallon sani daman tunda ya zo wajen, amman shi yasan ba Mama bace ba, sai dai ko cikin matan Baban Yassar din. Mai jiki yake tambayarta, yana cewa taje kawai zai karasa sauran, har kudin bude katin shi ya biya. Tukunna ya karasa dakin da AbdulKadir din yake suna gaisawa da Yassar daya dora da

"Me ya same shi wai?"

Dan sai lokacin yaji ya samu natsuwar bukatar hakan, Hajja likitan yadan kalla da take zaune kan farar kujerar roba, tana share kwallar da taji ta tarar mata a gefen idanuwanta

"Kayi mun magana Isa, dole zata sani tunda Maman shi ce"

Kai Dr Isa ya jinjina dan yayi magana da Dr Aminu shisa yace

"Jinin shine ya hau sosai, Allah ya rufa asiri daya samu matsala, dan Allah a gujema daga mishi hankali. Idan ya kara faduwa haka zai iya samun matsala sosai..."

Wani abu Yassar yaji ya kulle a cikin shi

"Hawan jini?"

Ya maimaita cike da shakku a muryar shi, yana ganin kai da Dr Isa ya daga mishi

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...oh Allah na"

Cewar Yassar da yakejin wata sabuwar damuwa ta lullube shi, ganin halin daya shiga yasa Dr Isa yi mishi sallama hadi da yiwa AbdulKadir din fatan samun sauki. Yassar din idanuwan shi ya tsayar kan AbdulKadir da sai lokacin ya motsa yana saka Hajja fadin

"AbdulKadir..."

Fuskar shi ya dakuna batare daya bude ido ba yace

"Wahee..."

Kunne daga Hajja har Yassar din suka kasa, can kasan makoshi AbdulKadir yake ci gaba da sambatun da baisan yanayi bama

"Waheedah kiyi hakuri... Bazan iya ba, Wallahi ba zan iya ba"

Numfashi Hajja ta ja tana fitar dashi, idanuwanta na cikowa da hawayen tausayin dan nata, sosai maza suke tunanin suna da iko akan mace, saboda musulunci da al'ada sun saka matan a karkashin su, sai dai yawa cikin mazan sun ma abin juyayyar fahimta, musulunci bai saka mace a kasan namiji saboda ta kasance mai rauni ba kawai, sai dan wani karfin zuciya da Allah ya dasa mata da bakowane yake fahimta ba, mace na da juriyar daukar laulayin ciki da yafi kowanne yanayi wuyar sha'ani, tana da juriyar naquda da duk wani kashi da yake bayanta sai ya motsa, a lokaci daya kuma tana da juriyar daukar hakuri da kaddarar wahalar da namiji.

Mace zata iya hakurin shekaru da bakin cikin da namiji ba lallai ko a fuskarta a fahimci hakan ba, amman rana daya zata ware ta kwatanta rama kadan cikin wulakancin, harshen da namiji sai yayi tashin da duk wani makusancin shi zai fahimci yana cikin yanayin damuwa, karshe sai yaba mutane tausayi saboda ya kasa jurewa har a juyar da al'amarin ana ganin ita

42 / 51