Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
yanda take dakuna mishi fuska tana tambayar shi
"Muna da abinci a kitchen, me yasa zaka siyo?"
Kafadu yadan daga mata
"Sai an dafa..."
Ya amsa a taqaice
"Nasani, amman akwai"
Kai ya girgiza
"Amarya bata girki"
Murmushi tai mishi tana mikewa ta nufi kitchen din, binta yayi. Tare sukaita bude-buden abubuwa a kitchen din harta gama dauko wanda take bukata, da wani gari daya gani kamar yaji, sai dai yafi yaji ja yaga ta jiqa a ruwa, sai tumatir na leda, macaroni tayi musu jalof da sauran kajin da aka kawo musu da su Anty basu cinye ba suka saka mata a fridge. Sosai yaci abincin dan ya mishi dadi.
*
"Masoyi..."
Nuriyya ta fadi tana riko hannun shi, ganin yayi shiru kamar yana tunani
"Ki soya mana ko dankali saiki mana sauce"
Ya fadi da wani nisantaccen yanayi a muryarshi, ranta taji ya baci saboda zaman fere dankalin da zatayi
"Banda dankali fa, sai dai in siyowa zakayi"
Kai ya girgiza mata, bayajin fita sam
"Ki duba kitchen din Wahee... Tana dashi"
Mikewa tayi tana nufar bangaren Waheedah din da tunanin yaushe zata dawo gidan. Dan ita ba zata iya wannan bautar ba sam-sam, rabonta da wani girki harta manta. Gashi ta kula da AbdulKadir din nada mugun cin abinci, kuma tana da tabbacin Waheedah ta lalata shi haka. Kwando ta samu ta kwashi dankalin da take tunanin zai ishe su ta koma nata bangaren. Ta wuce AbdulKadir zaune inda ta same shi, wayar Waheedah ya kira a kashe, hakan yasa shi ajiye tashi yana jin ranshi a jagule.
"Masoyi ba zaka zo ka tayani ba? Da yawa fa dankalin..."
Nuriyya ta fadi daga bakin kofar kitchen din kamar zata fashe da kuka, gashi bata iya saka peeler ba, dole sai dai da wuqa.
"Ban iya ferewa ba nikam"
Yai maganar da iya gaskiyar shi, yakan dami Waheedah da zai tayata aiki in tanayi, amman banda Maggi bata bashi komai, sau daya ta bashi yankan albasa, yajin daya cika mishi ido yasa har ya yanke hannu, bata kara ba, da yayi magana zatace ya rufa mata asiri, kafin azo a kamata taba soja aiki ya yanke hannu. Sai dai yakan miqo mata su cokali ko kwano. Jin Nuriyya bata kara mishi magana ba yasa shi zamewa ya kwanta kan kujerar, ya dora hannun shi saman goshin shi yana lumshe idanuwan shi.
Baifi minti biyar ba ya bude idanuwan shi, sai dai me, yanda tunanin Waheedah ya addabeshi da ya rufe idanuwan hakan ma daya bude su. Tashi zaune yayi, tunani bakon abune a tare dashi, babu abinda ya isa ya saka shi tunani haka, Waheedah tasani, bazai iya kwana baisan matsayar matsalarsu ba. Wayar shi ya dauka ya wuce ya dauko mukullin mota tukunna ya dawo yana fadin
"Nuriyya bari in dubo Waheedah, zanyi sallah a hanya..."
Kai ta daga mishi daya saka shi dakuna mata fuska, babu shiri tace
"Tam a dawo lafiya, kayi mata sannu"
Nashi kan ya jinjina mata, ita bata isa tai mishi ba, tana kuma lura da Waheedah na amsa shi da kai baya ce mata komai, amman ranar farko data kwatanta magana yai mata, data gwada yi mishi shiru ma saida ya sauke mata masifarshi har kuka tayi ranar. Akwai abubuwa da yawa da take lura Waheedah kawai take yinsu yana dauka, hakan kuma na mata quna har kasan ranta. Tana jin takun tafiyar shi har ya bace mata.
*
Kamar yanda ya fada, a hanys ya tsaya yai sallar magriba, sannan ya karasa gidan Yassar. Ya gwada kiran wayar Waheedah bai samu ba, hakan yasa shi shiga gidan kanshi tsaye hadi dayin sallama. Hauwa ta amsa mishi suna gaisawa, AbdulKadir din ya dora da
"Waheedah fa?"
Dan jim tayi na minti daya, batasan me yake faruwa ba, ba kuma tason shiga koma menene, idan akwai abinda zama da Yassar ya koya mata bai wuce kin shiga abinda babu ruwanta a ciki ba. Dan haka ta nuna mishi hanyar dakin da Waheedah din take ciki, tana ci gaba da hidimar da takeyi ta fito musu da abincin dare. Sauri AbdulKadir yakeyi yana godema Allah da baiga Yassar ba, dan zai iya cewa bazai ga Waheedah din ba. Dakin ya tura ko sallama baiyi ba yana mayarwa ya rufe.
Tsaye yaganta ta goya Ikram tana jijjigata, kallon mamaki take mishi, dan ta dauka ma Fajr ne ya shigo mata daki babu sallama haka, juyowa tayi tai mishi fada taga AbdulKadir a tsaye. Lumshe idanuwanta tayi ta bude su akan shi tana jiran soyayyar shi da takanji ta taso mata duk lokacin da zai bayyana a gabanta, amman shiru, babu abinda takeji banda son kara yin nisa dashi.
"Waheedah..."
Ya kira muryar shi na fitowa a karye da ganin nisan da tayi mishi cikin idanuwanta duk da tana tsaye a gaban shi
"Ba zan iya bacci bansan me kike so dani ba..."
Murmushi tayi, kallon ta yake, da gaske murmushi tayi, shi kam ko kadan baiga abin nishadi a yanayin da suke ciki ba
"Da wanne yare kake so in fada maka? Na maka da Hausa, in maka da turanci ko da larabci? Su kadai nasan kana fahimta... Sakina nake so kayi Sadauki, ka fadamun idan akwai abu mai wahala cikin gane hakan"
Tabbas ranar tazo mishi da abubuwa naban mamaki, Waheedah yake kallo yana son ganin ko da gaske matar shi ce a gabanshi, da gaske Waheedahr shi ce da ko murya bata taba daga mishi ba, balle ta tsaya idanuwanta cikin nashi tana gaya mishi magana irin hakan. Ji yake kamar an watsa mishi ruwan sanyi an kunna mishi AC. Jikin shi ba la'asar kawai yai ba, isha'i yayi makararriya.
"Waheedah?"
Ya iya furtawa yana kallonta, ganin taki sauke idanuwanta, kuma bata da alamar amsa shi yasaka shi fadin
"Nine fa, Waheedah ni ne?"
Kai ta jinjina
"Naganka ai... Kaga na nuna alamar bakai bane?"
Wannan karin dariyar takaici mai sauti ta kubce mishi
"Yaushe kika koyi rashin kunya?"
Maganar da yai zaton cikin kanshi yayi ta fito fili, sautin muryar shi na dukan kunnen shi da wani yanayi. Kafadu tadan daga mishi
"Zama da madaukin kanwa..."
Waheedah ta fadi tana zama gefen gadon
"Me kike nufi?"
Cewar AbdulKadir cikin bacin rai, kallon shi tayi wannan karin tana ganin yanda yake gab da birkice mata.
"Karka tasar mun da yarinya, Sadauki bazan iya hayaniya ba, dan Allah inba takarda zaka bani ba ka fita...sanda ka shirya bani kasan inda nake"
Kai kawai ya iya jinjinawa, yana juyawa ya bude kofar ya fice daga dakin, a falo ya samu Yassar da alama lokacin ya shigo
"AbdulKadir..."
Ya kira cike da mamaki, ko inda yake AbdulKadir bai kalla ba, hanyar da zata fitar dashi daga dakin kawai yake nema, saboda yanajin yanda wani agogo yake harbawa cikin kanshi yana mishi kashedin saura kiris ya cika, bayaso lokacin da koma meye ya dibar mishi ya cika a cikin mutane, kar a samu matsala. Rabon da ranshi ya baci irin haka harya manta, dan har wani duhu-duhu yake gani. Ganin hakan yasa Yassar kara kiran shi
"AbdulKadir..."
Gani yai ya fice daga dakin, babu shiri Yassar yabi bayanshi, ko takalma bai tsaya ya saka ba. Kafadar shi ya dafa yana juyo dashi
"Magana nake maka"
Ya fadi yana yawata idanuwan shi kan fuskar AbdulKadir din, bakuma yason abinda yake gani shimfide akai.
"A haka zaka shiga mota kai tuqi? Saboda baka da hankali"
Numfashi AbdulKadir ya sauke yana jan hancin shi da yake ji kamar yaji-yaji a ciki, muryar shi can kasan makoshi yace
"Me yasa igiyar aure ta shiga tsakanina da Waheedah? Hamma me yasa?"
Runtsa idanuwa Yassar yayi, cikin alamar rarrashi ya ce
"AbdulKadir..."
Kai AbdulKadir din ya girgiza mishi yana jin kaman zai kama da wuta da yanda jikin shi ya dauki dumi saboda bacin rai.
"Na mareta da safe, bansan ya akai ba Hamma, wallahi ban sani ba, amman cikin idona ta kalla tai mun rashin kunya... Yanzun ta kara... Bansan meya faru ba, bansan me nai mata haka ba....amman a karo na farko inajin igiyar auren da ta hadamu batai mun adalci ba. Da ta bani damar da zan daketa yanda raina yake so da ta dawo hayyacin ta ta fadamun me nai mata sai in san yanda zanyi in gyara..."
Dafe kai Yassar yayi, baisan abinda ya kamata yayi ba, a yini daya yana ganin AbdulKadir din na shirin susucewa, baisan me zai faru in aka dauki kwanaki a haka ba, tsintar kanshi yayi da musu addu'ar samun maslaha su duka biyun, dan sun saka shi a tsakiya ta yanda bazai iya zaben bangare ba. Motar shi AbdulKadir ya bude tukunna ya sake juyowa
"Ka fada mata, wallahi bata isa ba...wallahi bata isa ta birkitamun lissafi ina zaune lafiya ba...idan rigima take so Hamma ka fada mata AbdulKadir ne...taga wajen kwanana shisa ta rainani haka..."
Da idanuwa yake bin AbdulKadir din da kallo, murmushin da baisan ta inda ya taho ba yana shirin kwace mishi. AbdulKadir na kiran Waheedah bata isa ta birkita mishi tunani ba, amman hauka yake tuburan, tsaye yayi saida yaga yanda AbdulKadir din ya birka mota kamar zai takashi tukunna ya matsa da sauri. Numfashi Yassar ya sauke, yana hango AbdulKadir din ya ziro kai ta window din motar ya kalli maigadin da bai bude mishi kofa da wuri ba, da sauri Yassar ya taka ya karasa kafin ya jibgi yaron mutane a banza.
"Dan kanwar uwarka bakaji karar mota bane halan?"
AbdulKadir din ya tambaya yana kallon yaron da yake a tsorace, da hannu Yassar yai mishi alamar ya matsa, da kanshi ya bude ma AbdulKadir din mota yana fadin
"Allah ya tsare Samarin Hajja..."
Tsaki AbdulKadir yaja
"Idan na zageka a fili yanzun zakace na maka rashin kunya"
Wata irin dariya ta kubce ma Yassar din, har AbdulKadir din ya figi mota, Yassar na tsaye ya rike gate din yana kwasar dariya, dakyar ya samu ya shiga cikin gida, har lokacin da murmushi a fuskar shi, a rayuwar shi bai taba hango abinda zai saka AbdulKadir susucewa a yini daya haka ba, har Waheedah din da kanta kuwa...!
#AnaTare
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedahFacebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
19
TAQABALALLAHU MINNA WA MINKUM
Tana kitchen din har aka kira sallar Magriba, bata mike ba saida ta karasa yanka dankalin tukunna, wanke shi tayi ta tace a kwando, tana ganin kamar yankan yayi girma, amman ta riga ta gaji, ko bata gaji bama ba zata sake tsayawa yankawa ba, ranta a bace take jin shi. Gas ta kunna ta dora kasko ta zuba mai a ciki, tunanin ta barbadama dankalin gishiri bai zo mata ba, man ma ko dumi baiyi ba, balle yayi zafi, ta dibi rabin dankalin ta zuba a ciki tukunna ta fice daga kitchen din. Dakinta ta wuce tana shigewa bandaki ta dauro alwala ta fito, sallah ta gabatar a nutse, bata tsaya addu'a ba ta tashi ta nufi kitchen din dan ganin halin da dankalin ta yake ciki.
Danqare ta same shi, kasancewar man da yasha yayi luntsum, haka ta cigaba da cakuda shi, duk ya kakkarye ya dame cikin man, yana kara jagula mata lissafi gabaki daya. Batajin a cikin abubuwan da mata sukeyi na zaman aure akwai wanda yakai girki bata lokaci da wahala. Bata taba tunanin suyar dankalin zatai mata wannan rashin mutuncin ba, barin shi tayi yadan karayi, tukunna ta kwashe, bata jira man ya tsane ba ta juye a wani kwano da ta dauko. Sauran dankalin ta zuba, tana komawa falo ta zauna. Da fitilar wayarta take ta amfani, kasancewar har lokacin basu dawo da wuta ba. Ga AbdulKadir ya jima, balle yazo ya kunna musu generator, ko kallo tayi ta rage zafi.
Shima sauran dankalin haka taita juya shi duk ya dagargaje mata, ta kwashe tana kallon yanda a ido ma baiyi kyawun gani ba. Gashi sai tayi wata sauce kuma. Badan tana tsoron fadan AbdulKadir din ba, kwai zata soya su hada dashi. Sauran kayan miyar da ta dauko kitchen din Waheedah ta fito dashi ta juye a tukunya tana dorawa kan gas. Tukunna ta dauko albasa ta fara yankawa, ga yajin albasar daya cika mata ido, ga kayan miyar daya fara kamawa, banda tsakinta bakajin komai na tashi a kitchen din, sai kuma kauri. Albasar ta zuba ciki, tukunna ta zuba mai wajen ludayi takwas, dan kusan na kaskon da tayi suyane ta kusa juyewa, cakudawa tayi, taga kamar ta mata yawa, ta fara saka ludayi tana rage man.
Ganin miyar na kara konewa yasa ta kashe gas din
"Wanne irin bala'i ne wannan?"
Tai maganar kamar zata saka kuka, tunawar da tayi bata saka maggi ba, guda takwas ta dibo ta bare, dandanqa shi tayi ta zuba a ciki tana cakudawa, sai taga kamar miyar ta kara baqi. Tabe baki tayi, dan kanta harya fara daukar alamar ciwo. Sanda ta fito daga kitchen din ana Isha'i, tana da alwalar ta, hakan yasa ta wuce daki, tana idarwa ta fara kiran lambar AbdulKadir, sau hudu tana kira bai daga ba. Na biyar dinne ta ji ringing din wayar a cikin gidan ta bangarenta. Hakan yasa ta fito tana dora murmushi a fuskarta
"Sannu da zuwa..."
Kai kawai AbdulKadir ya iya daga mata yana zama kan kujera, wayar shi ya ajiye a gefe.
"In zubo mana abinci?"
Da kai ya sake amsata, ta wuce kitchen din, plate ta samu ta juye dankalin a ciki, tana samun karamun wajen zuba miya ta zuba, ta hado ta fito, a kan kafet ta ajiye. Tana kallon AbdulKadir da gabaki daya hankalin shi ba'a kanta yake ba. Kafarshi ta taba, ya sauke wani numfashi mai nauyi. Waheedah ba zata saka shi kin cin abinci ba, bata isa ta daga mishi hankali yana zaune lafiya ba.
"Meye wannan Nuriyya?"
Ya bukata yana kallon dankalin da ya koma kamar dambu a cikin plate. Zuciyarta taji ta doka a cikin kirjinta, nan take idanuwanta suka ciko da hawaye. Ranshi AbdulKadir yaji ya kara baci, inda Waheedah ce ya shigo tana kallon shi zata gane halin da yake ciki, kuma kome zaice mata ba zata nuna ranta ya baci ba dan tasan nashi a bace yake, balle tayi shirin mishi kuka.
"Bana son Kukan banza da bashida dalili, tambayarki nayi, ki bani amsa, meye wannan?"
Hawayen take kokarin dannewa, amman sosai suke mata barazana. Muryarta can kasan makoshi tace
"Wallahi bansan ya akayi yai haka ba nima..."
Kai AbdulKadir ya jinjina, yasan ana samun akasi wajen girki, a ranakun da ranshi ba a bace yake ba, zai mata uzuri da cewar dan Adam baya wuce kuskure, amman yau haushin shi yake son hucewa akan kowa ya samu, ita kadai ce kuma a gaban shi.
"Hannu zan saka?"
Ya sake bukata yana kankance mata ido, kai ta girgiza mishi da sauri, tana mikewa ta wuce kitchen din, sai da ta matse kwallar da ta taru cikin idanuwanta, tukunna ta dauko cokula guda biyu ta dawo, mika mishi tayi ya karba, yana sakawa cikin miyar daya rasa gane wace iri ce, ga man da yake kwance a miyar zai iya ganin fuskar shi in ya leqa cikinta.
"Me yasa baki saka mana nama ba? Wacce irin miya ce wannan?"
AbdulKadir ya karasa tambayar yana jujjuya cokalin shi cikin miyar, kafin Nuriyya ta amsa ya sake fadin
"Ni sauce nace kiyi mana, ita Waheedah takeyi idan ta soya mana dankali"
Yau ne karo na farko da Nuriyya taji takaicin rashin iya girki a rayuwarta, dan shine karo na biyu a rana daya da AbdulKadir ya hada girkin ta dana Waheedah, kishin da takeji kuwa kirjinta har zafi yake mata. Shikuwa sunan Waheedah daya fadi yasa ranshi kara baci, babu shiri ya dibo miyar ya zuba akan dankalin daga gefe yana cakudashi kamar shinkafa ya dibo da cokalin yakai baki, yana jin kaurin daya cika mishi hanci daga cikin bakin nashi. Hadiyewa yayi batare daya tauna ba, dakyar ya iya cokali hudu, yunwar da yake tunanin yanaji ya nemeta ya rasa. Mikewa yayi kawai, Nuriyya na binshi da ido harya fice daga falon.
Tsoron kar yai mata fada yasa bata tambaye shi inda zaije ba. Ita kanta a dole takecin dankalin, sai da taji cikinta ya cika tukunna ta kwashe kwanukan ta mayar kitchen, ta dawo ta zauna, jin har lokacin AbdulKadir bai tashi generator yasa tayi tunanin ko ta kira wayar shi, sai taganta ajiye akan kujera. Salama ta sakama ranta taci gaba da danne-danne wayar da rashin abin kallo ya sakata. Dan ita ba ma'abociyar chatting bace ba, daman karatu ne, nan tafi kwarewa, to duk litattafan da take bi, ba'a dora sabon cigaba ba.
AbdulKadir kuwa waje ya fita yana samun waje kan matattakalar shiga gidan ya zauna. Yana kallon farin watan da ya haske harabar gidan, yana kuma daukar tunanin shi ya watsa satin su na biyu da tarewa a gidan shi da Waheedah.
*
Tunda sukaje gida ta samo fina-finai wajen Nabila, data gama aiki bata komai sai kallo, daya tambayeta wanne irin film ne tace mishi Korean, jiya daya farka yaganta tana kallo, da kan shi ya kashe system din, sai da ya zare mata ido da gaske tukunna ta hakura ta kwanta, da ta shagwabe fuska zatai mishi kuka. Yau ma aikin kallon takeyi da gab yake da haramta shi saiya bar gidan, tunda ta rage samun lokacin shi. Hidimar shi ya gama yi ya fita sallar isha'i. Fajr na dakin shi yana bacci, dan shi da anyi Magriba cikin shi ya dauka sai bacci, inba yanajin rigima ba.
A matattakalar shiga gidan ya sameta zaune, jikinta sanye da rigar sanyin shi da ba hannun bane kawai yai mata yawa, har da rigar gabaki daya, sai dai Waheedah ce, haka take mishi, sai dai yaga rigunan shi a jikinta, inyai magana zata ce kamshin turarukan shi take so, kuma gasu a ajiye. Yakan ce ta fesa ta ajiye mishi rigar shi, dariya takeyi kawai
"Kamshin ai ya hadu da naka...."
Shine amsarta lokutta da yawa. Murmushi kawai yakanyi, a duniyar shi gabaki daya, ita kadai take mishi abinda take so, ita kadai yake cewa tayi abu ta maqale mishi kafada alamar ba zatayi ba, kuma ya hakura, wani lokacin ma kai kawai zata girgiza, idanuwanta na cikowa da hawaye, sai yaji gabaki daya gwiwoyin shi sunyi sanyi.
"Me kike a waje?"
Ya bukata yana karasowa ya zauna kusa da ita. Hancinta da sanyi ya cika ta ja, tukunna ta amsa shi
"Wata nake kallo"
Murmushi ya kwace mishi mai sauti
"Wata?"
Ya maimaita cike da alamar tambaya, yana kallon ta, kai ta daga mishi. Gabaki daya film din da ta gama kallo ya tafi da imaninta, duk wani