Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
kirki ya dauka yasaka a jikin shi, yana ganin yanda ta koma kamar Kampala itama, sallar nafila ya tayar yanayin raka'a hudu. Sai lokacin ma Nuriyya ta sauko daga kan gadon dakyar ta shiga bandaki ta wanko fuskarta, ta wuce kitchen. Mikewa AbdulKadir yayi yana fita shima ya nufi bangaren Waheedah ya tura hadi da sallama ya kuwa same shi a bude, kwan dakin ya kunna yana sakata runtsa idanuwanta sosai alamar hasken ya shigar mata cikin su, kafin ta bude su tana kankancewa akan AbdulKadir
"Nace ki dinga kulle kofa, bakyajin magana ko Wahee?"
Cikin bacci ta turo mishi bakinta da har lokacin da alamun janbaki ja, mika tayi, muryarta cike da bacci tace
"Na manta ne"
Hararta AbdulKadir din yayi yana sakata yin murmushi
"Kinfi so inta surutu kan abu dayane kawai"
Ya karasa ya dauki Qur'ani daman shi yaje dauka, ya tako yana kashe fitilar
"Kabar mun a kunne"
Waheedah ta fadi, sake kunna mata yayi yana jan numfashi kamar yana son zuqar iya kamshin da zai iya da yake cikin dakin kafin ya fita hadi da ja mata kofar. Dakin Nuriyya ya koma ya samu waje ya zauna yana bude Qur'anin shi ya soma karantawa cikin sanyin murya, yana wajen har Nuriyya ta shigo ta ajiye musu plate din shinkafa sai miya data zuba a wani kwanon, sai da AbdulKadir ya karasa shafin da yake karantawa tukunna ya rufe Qur'anin, su Hajja kawai yaiwa Addu'a sai iyalan shi da yan uwan shi, Yassar ne na farko. Janyo jikin shi yayi yana matsowa inda Nuriyya take zaune, yanayin shinkafar a idanuwan shi yaga kamar bata dahu ba, hakan yasa shi dan dibowa da cokali ya saka a bakinshi ya dan tauna yaji ta giri-giri
"Wallahi bazan ci shinkafa a tsai-tsaye haka cikina ya kumbura ba, bata dahu ba"
Ya fadi yana ajiye cokalin, kallon shi Nuriyya tayi
"Kici a bakin ki, da tun jiya kika dafa mana yanzun saiki yi warming kawai"
Plate din Nuriyya ta dauka tana mikewa da sauri ta fice daga dakin, dan duk wani abu na zuciyarta gaya mata yake ta juye mishi shinkafar sannan ta kwantara mishi farantin tangaran din saman kai kowa ma ya huta.
"Kece da asara Waheedah, danni bawai ya dameni bane"
Nuriyyar ta fadi a fili da bala'in bacin rai, da tayi tunanin kwantara mai faranti ya mutu duk su huta. Cikin tukunya ta mayar da shinkafar ta kara ruwa tayi tsaye. Idan ta koma dakin ya sake magana tanajin kome ya fito daga bakinta fada mishi zatayi sai dai in gabas zai saka kanta ya yanka yayi. Tagaji har cikin kasusuwan ta, ya fara fita daga ranta daga shi har auren, a wuya takejin su sun mata tsaye. Takai mintina sha biyar har saida ta fara jin kaurin shinkafar tukunna ta kashe gas din, ko ta dahu ko bata dahu ba haka zai hakura yaci, ko ya fito ya dafa wata.
Sake zubawa tayi ta dauka tana komawa dakin ta ajiye. Dan diba AbdulKadir yayi yana sakawa a bakin shi, tadan rissina ba kamar dazun ba. Duk da bata kai yanda Waheedah take dafa musu laushi ba, kallon shi Nuriyya takeyi tana jiran taji ya sake cewa bata dahu ba, dan tabbas wannan karin zata kwantara mishi farantin tangaran din. Sai taga baice komai ba, miyar ya dibo yana zubawa a gaban shi hadi da cakudawa, ba sosai yake son abinci mai zafi ba, hakan ne yasa shi baiyi saurin kaiwa bakin shi ba, ta riga shi zuba miyar ta juya ta diba ta saka a baki. Wani irin karni taji cikin kofofin da suka hada bakinta da hancinta, sannan miyar ta sauka cikin bakinta da wani dandano marar kan gado, tana taunawa dakyar ta hadiye.
AbdulKadir ta kalla daya ciko cokali tanajin kamar tace mishi karya ci, ya kuwa auna cikin bakin shi, lokaci daya yanayin fuskar shi ya sauya, bai tauna shinkafar ba ya hadiye yana wani irin sauke numfashi har lokacin bakin shi a gauraye yake jin shi. Mama na musu abinci marar dadi, amman yana ciyuwa, bakajin kamar zaka shaqe ka wuce lahira
"Kasheni kike so kiyi Nuriyya... Da raina kike so ki kasheni"
AbdulKadir ya fadi yana dorawa da
"Baki iya abinci ba, bansan ya akai ban taba sani ba sai yanzun... Wacce irin miyace wannan?"
Kai Nuriyya ta saddar kasa tanajin kunyar data shiga ta danne bacin ran da take ciki
"Shisa kike cewa in daukar miki yar aiki?"
Kai tadan daga mishi a hankali, kai AbdulKadir ya jinjina dan abinda ba zai taba yiwuwa bane ba, badan kar a tayata aiki ba, ko dan baya goyon bayan mazan da suke daukar ma matan su yan aiki ba, ko da babbar sallah yana ma Hajja magana a dauko ma Waheedah ta soya mata nama. Baiga dalilin da zaisa shi yaci abincin yar aiki ba
"Ki koya dan ni ba zanci abincin yar aiki ba"
Kallon shi Nuriyya tayi sosai, tana tunanin ta inda yake so ta fara koyon girki, kowa yake so taje ta samu ya koya mata
"Kafin ki kasheni dan Allah ki dinga mana mai da maggi"
AbdulKadir ya karasa maganar da sigar roko yana dorawa da
"Yanzun ma tashi zakiyi ki zubomun da mai..."
Batayi musu ba ta mike, numfashi AbdulKadir ya sauke yana jin komai ya birkice mishi, fada yaso yayi sosai, amman kananun maganganu ba halayyar shi bace ba, bai kuma saba komai sai yayi magana a kai ba, sun sami matsala da yawa yau Da Nuriyyar bayaso su kara samun wata cikin daren nan. Dan yasan halin sune, kome zai faru iya sune, babu shaidan din da zasu labe a bayan shi tunda watan azumi ne. Bai shirya sanin yana da halaye marassa kyau ba, gara tasan yanda zatayi ta koya, ya dai cika da mamaki, ya dauka koyayane mata sun iya girki tunda abune da sukeyi yau da kullum.
Da mai yaci kuwa yana mayarwa da ruwa ya mike, yanajin yanda idanuwan shi sukai zuru-zuru duk da bai kallo mudubi ba. Bacci suka dan koma kafin asuba. Sanda ya dawo masallaci Nuriyya harta sake komawa bacci. Shikam zama yayi yana yin azkar har rana ta fito ya mayar da sallah raka'a biyu ta nafila. Sai daya wuce dakin Waheedah yana samunta tana linke dardumar ta da alama itama sai lokacin ta tashi. Dan ita ta saba mishi da yin nafilar bayan asuba, ko kadan bata wuce ta, ta tunasar dashi tarin ladan da yake cikin hakan.
Yanzun harta zame mishi jiki, cikin sanyin muryarta ta gaishe dashi, ya amsa
"Kun tashi lafiya?"
Sai da ta fara jinjina mishi kai tukunna ta amsa tana dorawa da
"In kaje gida yau ka taho da Fajr"
Kallonta AbdulKadir yayi, sosai take kewar yaron nata
"Ni nace miki zanje gida ne? Ki kirasu a kawo miki shi"
Kai ta girgiza mishi
"Ni kunya nakeji ai"
Dan murmushi yayi
"Lallai yarinyar nan, nine sarkin rashin kunya ko?"
Dariya Waheedah ta tsinci kanta dayi tana girgiza mishi kai
"Haka kike nufi mana, ba zanje ba to, in kina kewar shine ki kirasu da kanki"
Ya karasa maganar yana juyawa dan bacci zaije yayi daman zai duba ya suka tashine.
"Dan Allah ka dauko mun yarona"
Juyawa AbdulKadir din yayi yana harararta ya fice daga dakin yaja mata kofa, dariya take sosai, har ranshi tasan harara ce yake ganin yanayi, amman idanuwan shi basuda girman da zasu juyu har suyi hararar, bata taba gaya mishi bayayi dai-dai ba. Sai dai tasha dariyarta kawai. Ikram ta dauka tana cire mata kaya, dan wanka zatayi mata, itama tayi, sai suzo suyi baccin.
*
Bacci yayi har wajen sha biyu sannan ya tashi, ya watsa ruwa ya fito yana zaune bakin gado, Nuriyya na kai tana danne-danne waya, dan group dinsu an turo wasu laces masu bala'in kyau. Kuma duk wanda yake cikin group din yace yana son guda daya, ita kadai ce batace a ajiye mata ba, dan taji Hajiya Kaltume mai siyar da kayan tace kudi hannu ne, ba zata bayar da bashi ba wannan karin, da sai ta dauka sai karshen wata. Gashi kowa sai magana yakeyi ita ba zata siya ba, tana ta kallon sune batasan me zatace ba, kar a rainata.
"Masoyi"
Ta kira cikin sanyin murya, tana saka AbdulKadir din kallonta
"Kaga wani lace"
Ta fadi tana nuna mishi wayar, kallo yayi yana jinjina mata kai
"Yayi kyau"
Ya amsa a taqaice yana daukar tashi wayar da take ajiye a gefe. Murmushi Nuriyya tayi dan taga alamar zatayi nasara
"Dubu arba'in da biyu"
Kai kawai AbdulKadir ya jinjina mata baice komai ba yaci gaba da danna wayar shi, da sauri tace
"In dauka zaka biya kudin?"
Dago idanuwan shi AbdulKadir yayi yana kallonta kamar bata da hankali
"Wai me kika daukeni ne Nuriyya? A bishiya nake tsinko kudi kome? Kin manta kudina da kika kashemun, kin sani saida na taba wasu dana ajiye dan wani abin, har kina mun maganar in sai miki abin dubu arba'in da biyu. Ina nagan su?"
Kallon shi take dan in jikinta zai zama kunnuwa ba zata taba yarda bashida su ba, da cayai mata ma bazai bayar ba sai yafi mata saukin yarda. Wayar shi AbdulKadir yaci gaba da dannawa yana nemo text din albashin shi ya ajiye wayar kan gadon yana turama Nuriyya data dauka
"Bansan kallon me kike mun ba, amman ni ba wasu kudi gareni ba, kinga albashina nan duk watan duniya, a ciki nake duk hidimata, katon gidan nan kudin allowance ne na wasu ayyuka, haka motata, bawai albashina bane, sukuma sai ayi shekaru ba'a same su ba. Idan ban taba fada miki ba yau kisani, ni bamai kudi bane, cikin layin masu rufin asiri ma a tsakiya za'a sakani"
AbdulKadir ya karasa yana mikewa ya fisge wayar shi daga hannun Nuriyya yana ficewa daga dakin yabarta a zaune gabaki daya jikinta ya gama mutuwa. Tabbas yau kallon kitse ake ma rogo ne ya tabbata a kanta, wannan albashin na AbdulKadir sam-sam bashi bane burinta ma hamshaqin mijin da take son aure
"Tafdin..."
Ta fada ranta a jagule, kwata-kwata yanda ta hango AbdulKadir ba haka yake ba. Daga halayen shi har kudin shi, ita da bata hango ckarta shekara daya a gidan batare da tayi motar kanta ba. Da wannan yagalgalallen albashin yaushe harya tara kudin da zai siya mata mota. Wani kunci takeji yana taso mata tun daga yatsan kafarta yana mata zaune a kirjinta. Harma fada mata yake shi ba kudi yake dasu ba dan karta sa ran zai mata wani abin arziqi. Har ranta take jin babu wanda ya cuceta sai Waheedah, babu babbar makira irinta, ita ta dinga nuna mata kamar tana cikin daular rayuwa, ita kuma ta dinga mata hidima kamar AbdulKadir din wani hamshaqin mai kudine, ita taja mata duk wannan abin da take ciki, dan ita ta haska mata AbdulKadir din taga kyallin shi harta kwadaitu da auren shi, amman da duk mintina take ganin abinda bataso a tattare dashi.
Gani tayi bakin ciki zai mata katutu, ga whatsapp din data bude harta private Hajiya Kaltume ta mata maganar siyan lace din nan, hankalinta ya kara tashi, hakan yasa ta janyo system dinta, drawer din gefen gado ta janyo ko ta saka earpiece dinta a ciki, taga wata leda da batasan ta ajiye ba, dagota tayi taga kudine a ciki, sai da zuciyarta tai wata irin dokawa, warware ledar tayi tana zazzago kudin kan gadon, ganin su tayi da yawa sosai, da sauri ta tashi ta saka mukulli ta kulle kofar ta dawo, kudine masu yawan gaske dan ba'a dauresu ba, hakan ya sata tunanin da alama ana zararsu ne. Tasan AbdulKadir din kan ciro kudi ya ajiye ana diba, dan tasha zara kuma bai taba ganewa ba tunda bai mata maganar ba.
Duk da zuciyarta na dokawa, wani abu kasan ranta na fada mata kar tayi, dubu arba'in da biyu ta kirga ta ware su a gefe, ko kwatar kudin bataga alama sun girgiza ba, tasan ba kirgawa zaiyi ba, da sauri ta gyaggyara su ta mayar cikin ledar tana nannadewa kamar yanda tagani ta mayar ta rufe drawer din. Wanda ta diba din ta mike ta samu jaka ta zuba su a ciki. Kafin ta zauna taji ana kwankwasawa, da yake ta saba dibar kudin Anas ko dar bataji ba, taje ta bude mishi kofa, baice mata komai ba ya rabata ya wuce.
'Namiji munafuki'
Ta fadina ranta, daman akance namiji bazai taba nuna maka samun shi ba, yau ta kara yarda, yanzun ya nuna mata wani alert kamar mai gaskiya, jibi kudin da ta gano. Daman tanata tararrabi anya ace bashida kudin da take tunani. Tana kallo ya bude drawer din ya dauki ledar ya sake zuwa ya fice, dakin ta tura. Ta koma kan gado tana daukar wayarta taba Hajiya Kaltume amsa
'Ni banda kudi a banki, Cash ne bansan ya za'ayi ba, gashi yau bazan fita ba, ni nake da girki'
Ba'ayi mintina biyu ba Hajiya Kaltume ta amsa ta
'Kibani address din zan turo yaro yazo ya karba'
Tura mata tayi kuwa tana komawa kan gado ta zauna. Ko da kirgawa AbdulKadir yayi yagane an diba sai ta bashi hakuri, fadane zaiyi saita toshe kunnuwanta ta kyale shi, in aka kawo lace din ta daura a jikinta zai wanke mata haushin shi da zataji na dan wani lokaci. Ko mintina sha biyar ba aiba, taga kira yaron harya iso kofar gida. Kudin ta dauka ta saka hijabi ta leqa ta kai mishi, saida ya kirga a gabanta tukunna ta dawo gida, tana jin wani abu yadan kwanta cikin bacin ran data shiga.
*
"Hamma kasan fa bani da lafiya, gashi ana rana, ina azumi ka fito dani"
AbdulKadir ya fadi yana mika mishi ledar kudin da sun kai kwana goma a ajiye a wajen shi, dan Yassar din yayi cinikin mota zai sake wata, tashi nata bashi matsala, daya ciro kudin sai cinikin bai yiwuwa ba, yana jin qwiyar komawa bank ya kuma san halin shi, ko Hauwa yaba ta ajiye saiya bi ya karba ya kashe. Amman idan AbdulKadir dinne ba zai bashi ba sai dai ko in lalura. Yanzun ma dan yace ga motar an kawone an gama komai, kudinne kawai zai basu, tashi motar ma har wanda ya siya ya dauka tukunna AbdulKadir din ya fito da kudin.
Ya daukama dakin Waheedah ya ajiye, dan yaje yana nema, ta taya shi basu gani ba, kafin ya tuna dakin Nuriyya ya ajiye.
"Kai kamar ba soja ba"
Kankance mishi idanuwa AbdulKadir yayi
"Ina gida yanzun, kabarni. Kuma ma dan ina soja sai akace duk wahala in dinga jureta"
Kai kawai Yassar ya girgiza mishi yana karbar kudin ya basu. Suna tsaye aka kirga
"Dubu dari hudu ne babu arba'in da biyu"
Da mamaki Yassar yace
"Bangane ba"
Dan yasan kudin shiya ciro su da kan shi
"Eh babu dubu arba'in da biyu"
AbdulKadir ya kalla yana fadin
"Ka taba kudin nan ne AbdulKadir?"
Kai AbdulKadir ya girgiza dan baima ji me suke fada ba, hankalin shi nakan wayar shi da yake duba sako
"Me ya faru?"
Ya bukata yana mayar da hankalin shi kan Yassar din
"Wai basu cika ba, babu dubu arba'in da biyu"
Dagowa AbdulKadir yayi daga jikin motar shi
"A kara kirgawa dai"
Ya fadi saboda bayason abinda ya fara zuwa kan shi ya tabbata, sam bayaso, mutumin kuwa bai musu gardama ba, wannan karin duk a tare suka kirga kudin, babu dubu arba'in da biyun. Wallet din shi AbdulKadir ya zaro yana dauko ATM din shi ya mikama Yassar
"Kasan password din"
Wani irin kallo Yassar ya watsa mishi kafin yace
"Bana son iskancin banza da wofi"
Kai kawai AbdulKadir ya jinjina yana mayar da ATM din inda ya dauko shi, batare da yace komai ba ya bude murfin motar shi, ran shi ya dade bai baci ba irin haka.
"AbdulKadir me ya faru? Ka fito daga motar nan muyi magana"
Yassar ya fadi ganin yanayin fuskar AbdulKadir din, amman mukullin motar shi ya murza yana tayar da ita, duk maganar da Yassar din yake mishi baiji ba ya fisgi motar yana hawa titi...!
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#LubnaSufyan
[7/16, 9:56 PM] +234 802 111 7692: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
YouTube: https://youtu.be/WwocHslDAYk
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
33
To my fav Aunt (Rabi'atu). Allah ya shiga lammuran ki. Amin thumma amin
Tunda ta gama baccin safenta ta gyara bangaren ta tsaf, sannan tayi wanka ta shiga kitchen. Dan wanke-wanken da take dashi tayi. Ikram na kwance cikin kekenta tana bacci. Fridge din ta duba taga tana da naman rago, kawai sai marmarin tuwon semo da miyar dan yar kubewa ya kamata. Fito dashi tayi dan ya huce, yayi kankara, ta dauki Ikram suka fito ta kulle kitchen dinta. Daki ta koma ta kira Naziru a waya tace yaje ya siyo mata danyar kubewa ya kawo mata in yazo sai ta bashi kudin. Hakan kuwa akayi, dadewar da yayi har bayan azahar yasa ta dauka ma ya manta dan tasan shiriritar shi.
Kitchen din ta koma ta samu kwando ta juye kubewar a ciki, tana da yawa, inta ajiyeta ma kafin ta sakeyin wani tuwon zata iya yin yaushi, gara tayi miyar ta saka a fridge. Tasan zata waiwayeta. Ajiyewa tayi ta wuce daki ta dauko wayarta ta dawo, Tafsir din Sheikh Albani ta kunna kan yanda zaka kara gyara ibadunka. Ta rage karar dai-dai kunnenta tunda ba earpiece ta saka ba, duk da ita kadai ce ta riga ta saba. In akwai abinda yake saurin sosa mata rai bai wuce tana zaune waje wani ya kunna waka ko wani abin ya kure sauti ba. Sam mutane basa tunanin ko wanda yake kusa dasu baya jin dadin su abinda suke saurara din, ko baya cikin yanayin son saurarar komai.
Wasu suna ganin ai karatun Qur'ani ne, musamman lokacin azumi, kuma zaka iya shiga hakkin wani, shisa aka saukaka da akai earpiece, ka saka kaji duk abinda kake so dai-dai kunnuwanka batare daka takura kowa ba. Kubewarta ta wanke tana dauko abin gogawa ta dauraye shima ta ajiye su gefe dan taga naman ya saki, gara ta dora shi ta dafa, har cefane ta dauko, lokacin ba wahala gare shi ba, gashi tana son dafa zobo. Aikinta take a nutse taga giccin AbdulKadir da wani irin sauri da ya sakata leqawa, yanayin tafiyar shi ya tabbatar mata da ranshi a bace yake sosai.
"Allah ya rufa asiri"
Ta furta a hankali tana komawa taci gaba da aikinta. AbdulKadir kuwa duk azumin da yake bai hana shi zira kai ta murfin mota yana ma mutane masifa a hanyar shi ta zuwa gida ba, dan gani