Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   38 / 51

111K to 114K   out of 152.3K words

yanda ya kamata. Ranta kal take jin shi, ko kadan bataji shigowar AbdulKadir daya nutsar da hankalin shi kanta ba, ya dauka ma wani abinne ya sameta harta dora girki yai wannan kamun ko kaurin shi bataji ba.

"Nuriyya..."

AbdulKadir ya kira ranshi a matukar bace, da alama batama jishi ba, dan tayi rufda cikine da waya rike a hannunta

"Nuriyya!"

Ya sake kira da karfi wannan karin yana sakata juyowa a tsorace, ganin shine yasa ta tashi zaune tana ajiye wayar hadi da fadin

"Sannu da zuwa"

Da idanuwa AbdulKadir ya kafeta

"Bakida hankali ko? Baki da hankali zaki dora girki ki dawo daki ki zauna kina danna waya. Gobara kike son ki hadamun a gida Nuriyya?"

Gabanta ne yai wata irin mummunar faduwa tana mikewa tsaye

"Ina zakije?"

AbdulKadir ya bukata

"Wallahi na manta ne"

Ta amsa tana wani irin sauke murya da ya kara bata mishi rai

"Saboda girkin bashi bane a gabanki, ya zaki dora girki har yai wannan konewar kina fadamun kin manta"

Idanuwanta Nuriyya taji sun ciko da hawaye, ta manta ranar karshe da aka tusata gaba ana mata fada haka, daman shine in yana nan baya rasa abinda zatayi da zai mata fada.

"Masoyi mantuwa ce, kowa nayi kuma"

Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance a kanta, yanajin yanda ranshi yake kara baci, bazai dauki wata rashin kunyar bayan wadda Waheedah ta gama sauke mishi ba. Karasawa yayi ya kama hannunta yana fara janta zuwa hanyar da zata fita dasu daga dakin, binshi kawai Nuriyya take har kitchen din tana ganin hayakin da har lokacin bai gama fita ba

"Meye a hancinki? Danna waya yafi miki muhimmanci, ki kalli kitchen dinki, yaushe rabonki da shara Nuriyya? Wanke-wanke fa?"

Hannunta daya damka take murzawa da dayan, tana jin wani hawaye mai dumi ya zubo mata

"Karki mun kukan banza da bashida dalili wallahi..."

AbdulKadir din ya fada, dan bayason kukan banza. Rabata yayi ya wuce yana fita daga kitchen din, daki ya koma ya shiga bandaki, yana ganin yanda farin tiles din yai duqun-duqun, bangon har wani dallakin daudar da baisan ko tun ta yaushe bace ba, ga kayan wanki kaca-kaca. Tsintar kanshi yayi da kasa amfani da bandakin, ya fito yana ganin bedroom dinma a hargitse. Kai kawai ya girgiza yana tunanin kalar Nuriyya, inda zaman kallone ko danna waya babu wanda zai nuna mata.

Bangaren Waheedah ya wuce yana shiga bandakin ya gama abinda zaiyi ya fito. Bangaren Nuriyyan ya koma ya zauna a falo yana dora kafafuwan shi kan kujera dan jin kasar da yake takawa kan kafet din. Yanajin kacafniyar kwanoninta a kitchen din. Da alama wanke-wanke take, aikam abinda takeyi kenan, ranta a bace yake, batasan yanda zata sake mishi maganar yar aiki ba, idan azumi yazo mata Waheedah bata dawo ba ta gama yawo tasani. Kugunta taji ya gaji lokacin data gama tana share kitchen din, fitowa tayi ta samu AbdulKadir din a zaune

"Yunwa nakeji nikam"

Ya fadi yana kallonta, dan zaman da yayi waje daya yasa yunwar taso mishi. Nuriyya kamar zatayi kuka tace

"Nikam me zan baka? Kaga abincin ne na dora ya kama, ko zaka yo mana takeaway?"

Kai ya girgiza mata, yanda yakeji bazai iya fita ba

"Ko indomie ki dafa mun, bazan iya fita ba Nuriyya"

Robobin lemukan ta karasa tsincewa dana ruwa tan komawa kitchen din, ranta inyai dubu ya gama baci. Ita har ranta batayi niyyar cin indomie ba, batama tunanin tana da indomie din, dubawa tayi, sauran data rage matace ta dafa jiya. Fitowa tayi tana kallon AbdulKadir din, muryarta can kasan makoshi tace

"Babu indomie"

Juyawa yayi yana kallonta da mamaki

"Baki siya bane wancen watan?"

Kai Nuriyya ta girgiza mishi, ita wancen watan kudin da ya batane gabaki daya ta tattara ta siyi zobon gwal karami, dubu biyu kawai ta cika. Babu abinda ta siya, ta dauka ma shi zai siyo musu.

"Ki duba kitchen din Waheedah"

AbdulKadir din ya fadi da alamar gajiya a muryarshi. Wucewa tayi ta dibo indomie din guda hudu ta dawo

"Masoyi"

Ta kira tana dorawa da

"Yaushe Waheedah zata dawo? Jikinne har yanzun?"

Kai AbdulKadir ya jinjina mata

"Zata dawo, tana gida....data kara warwarewa"

Wucewa Nuriyya tayi batare da tace mishi komai ba. Ranta ya kara baci ba kadan ba, ashe gida Waheedah ta wuce abinta saboda bakin hali. Nan da nan ta dafa indomie din, dan zatace duk a abinci ita kadai take dafawa babu wata matsala, a plate ta zubo musu ta saka cokula tana fitowa da ita ta ajiye, cokalin AbdulKadir ya dauka, duk yunwar da yakeji bata hanashi fadin

"Baki dafa mana kwai ba? Haka zamu ci?"

Batare da Nuriyya ta kalle shi ba tace

"Banda kwai ni"

Da alamar kosawa a muryarta, ta kula ba a iyama AbdulKadir din, ta samu waje ta zauna

"In zakiyi mana siyayyar azumi ki siyo mana, ina so ni fa"

Cewar AbdulKadir din yana fara dibo indomie din da tai mishi zafi yana jira ta huce, kallon shi Nuriyya take cike da rashin fahimta

"Bakai zaka siyo ba?"

Kai AbdulKadir ya girgiza mata

"Me yasa zan tura miki kudin idan ni zan siyo"

Hanjin cikinta Nuriyya taji sun tattaru sun kulle waje daya

"Wanne kudin?"

Ta tambaya cikin bayanannen tashin hankali, indomie din daya dibo yakai bakin shi ya tauna yana hadiye tukunna ya kalli Nuriyya

"Na tura miki dubu arba'in dazun, baki gani bane?"

Kai Nuriyya ta daga dan dakyar ta hadiye indomie din dake bakinta

"Na siyayya ne daman?"

Cikin rashin fahimta AbdulKadir yake kallonta kafin yace

"Nuriyya..."

Saboda yanayinta daya gani duk ta daburce, ya kirata ne yana tambayar ko lafiyarta, amman ita bata fahimce shi ba, ta dauka koya gane bata da gaskiya ne

"Wallahi bansan na siyayyar azumi bane Masoyi, nasan kana bani kyautar kudi"

Kallon nata AbdulKadir yakeyi, yana son fahimtar inda kalamanta suka dosa, kallon ne takejin yana kara rikitata

"Na siyi takalma a ciki, daman wancen watan akwai atamfofin dana dauka, shine na cika kudin.... Saina biya kudin dinki kuma"

Cokalin AbdulKadir ya ajiye cikin abincin yana kallon Nuriyya

"Bangane me kike cemun ba, kudin dana tura miki dazun dinne kika siyi su takalma da atamfofi?"

Kai Nuriyya ta daga mishi, cikin tashin hankali take fadin

"Dan Allah kayi hakuri, wallahi bansan na siyayya bane"

Kallonta AbdulKadir yake yana rasa abinda ya kamata yayi, ranshi da yake kokarin kwantarwa ne Nuriyya take ta batawa tunda ya shigo. Tsaye yake akan gidan shi, indai kayan sawa ne duk bayan wata biyu ko uku yake ba Waheedah kudi ko zata siya, itama Nuriyyar ya fara bayan watanta biyu da zuwa, to tana yawan tambayar shi kudi, ko zatayi ankon suna kona bikin kawayenta, ko zata siyi wani abin, shisa ya daina bata. Akwai kudin daya ware na siyayyar kayan sallar su daman.

"Kudin kayan abincinne kika siyi takalma dasu Nuriyya? Abinda duk nake miki bai isheki ba saikin tabamun wannan kudin?"

Kai Nuriyya ta girgiza mishi

"Baki da takalma? Baki da kayan sawa? Kin tambayeni kudin takalma na hanaki ne?"

AbdulKadir yake tambaya yana kallonta, kai kawai take girgiza mishi, mikewa AbdulKadir yayi abincin gabaki daya ya fita daga ranshi, itama Nuriyyar mikewa tayi tana dana sanin fada mishi, hannun shi zata kama yace

"In kika tabani saina mareki Nuriyya..."

Tsaye tayi tana zare idanuwanta da suke cike da rashin gaskiya

"Yau ya zama ranar karshe da zakimun amfani da kudin hidimar gida kan wani abu daban, wallahi ranki zai mugun baci tunda naga alama ke baki da hankali"

AbdulKadir ya karasa maganar ranshi a bace

"Dan Allah kayi hakuri"

Nuriyya ta fadi, wani irin kallo AbdulKadir din ya watsa mata, hakurin da take bashi ne yakejin yana kara bata mishi rai, wucewa yayi yana komawa bangaren Waheedah, dan idan yana ganin Nuriyya komai zai iya faruwa. Kan kujera ya kwanta yana lumshe idanuwan shi. Da Waheedah na nan ma koyayane zuciyarshi zatai sanyi, amman tayi tafiyarta saboda ta daina damuwa dashi, abinda yafi tsana fiye da komai ya tsinci kanshi tsundum a ciki, tunanin safiyar ranar da sukayi fada da ita.

*

Kwanan shi biyu da zuwa, yana kula da yanayinta tunda yazo. Shirunta ya mishi yawa, bai dai tambaya ba sai safiyar ranar tana kitchen tana soya musu fanke ya shiga yai tsaye yana jingina bayan shi da kantar kitchen din

"Wahee me yake damun ki?"

Ya tambaya, da wani nisantaccen yanayi a fuskarta ta girgiza mishi kai

"Lafiya ta kalau"

Ta fadi tana cigaba da aikinta, da idanuwa AbdulKadir din yake binta harta gama ta dauki kulolin tana wucewa falo. Har suka karya idanuwan shi na kanta, shirun nata tabashi yake har kasan zuciyarshi, ranar ta karbi girki, tunda hutu zaiyi kwanan shi biyu a wajen Nuriyya. Sake binta kitchen yayi ya samu tana wanke-wanke

"Shirunki yamun yawa"

Batare da ta kalle shi ba ta amsa a takaice

"Babu komai"

Kasa fita yayi daga kitchen din harta gama wanke-wanke tana goge kitchen din, ta dauki karamin towel na goge-goge ta sake fitowa falo, AbdulKadir din na binta. Tana jin shi, batada abinda zatace mishi, bata kuma jin yin surutun, yana tsaye Nuriyya ta fito tana fadin

"Masoyi..."

Goge-gogenta Waheedah ta cigaba dayi duk da zuciyarta da takejin kamar zata bude kirjinta ta fito, ta gefen idanuwanta taga Nuriyyar ta karaso ta kama hannun AbdulKadir din tana saka wani irin tukukin kishi taso mata. Batasan me suke cewa ba saboda zafin da kirjinta yakeyi ya dauke mata hankali daga kan su. Bayau ta fara gani ba, wani lokaci suna zaune a kujera Nuriyyar zata fito daga bangarenta tazo ta zauna gefen AbdulKadir din, ko ta kwantar da kanta a jikin shi, ko ta rike hannun shi, duk wani abu da jikinsu zai hadu a gaban Waheedah din ta kula shi takeyi.

Bata taba daga kai ta kalle su ba, ballantana tayi magana, tasan idan aka tsaya tambayarta kalar soyayyar da take yiwa AbdulKadir ba zata iya misaltata ba. Sai dai koda wasa batayi tunanin tana da zafin kishi ba sai da taga Nuriyya a kusa da shi. Bata kara sanin zafin kishinta ya girmama ba sai lokacin da AbdulKadir din ya fara mata hirar Nuriyya da batason ji, baya kuma kula da bata tanka mishi duk idan yanayi. Ko film take kallo in sun kalla da Nuriyya saiya fara bata labari har abinda Nuriyya din ta fada kan film din.

Babu abinda tagaji dashi sai yanda ran girkinta ko ba ranar girkinta ba sai dai tagansu a bangarenta zaune suna jira tagama girki suci, idan girkin Nuriyya dinne ma inta zuba musu tare suke ci mata abinci a falo. Bata taba jin tagaji dasu biyun ba irin wannan karin, daga Nuriyyar har shi AbdulKadir din daya kwaso mata ita ya ajiye mata a gida tagaji dasu, ko ganin su bata son yi. Ji take idan bata dan fita tasha iska koyaya ba komai zai iya faruwa.

Tanajin kamar daga randa Nuriyya ta shigo gidan wani abu mai kama da bomb ya kunnu a cikin jikinta, abinda ganin Nuriyyar da AbdulKadir ke karama gudun lokacin fashewa, yanzun tanajin yana gab da tarwatsewa kuma ba zaiyi kyau ba. Muryar AbdulKadir din taji yana fadin

"Wai zata fitane da, kuma ta fasa"

Dagowa Waheedah tayi tana kallon shi, kafin taji Fajr ya riko mata hannu

"Omma banga socks ba, nasa uniform din"

Kai ta jinjina mishi

"Zan duba idan na shiga daki Fajr"

Sakin hannunta yaron yayi yana komawa kan kujera inda ta kwantar da Ikram

"Karka tasar mun yarinya bangama aikina ba"

Tace mishi, hakan yasa shi matsawa gefe ya zauna. Hankalinta ta mayar kan AbdulKadir

"Zanje gida anjima..."

Tana kallon yanda yake girgiza mata kai tun kafin ta karasa maganar

"Zaki barni ni kadai... A'a kam, ba yau ba Wahee"

Cikin idanuwa ta kalle shi wannan karin

"Ni ina so inje, dan Allah kabarni"

Ta karasa maganar wani abu na mata tsaye a makoshi, kai AbdulKadir ya kara girgiza mata

"Karma mu fara jan maganar nan, ba zakije ba"

Hawaye taji sun cika mata idanuwa da take da tabbacin basu da alaka da hanata fita da yayi, kawai tagajine har cikin kasusuwan jikinta

"Gaskiya Sadauki sai naje... Ina so inje gida nikam"

Da bayanannen mamaki a fuskar shi AbdulKadir yake kallon ta, bata taba mishi magana da wannan yanayin ba, baya kuma son ta fara

"Ba zakije ba to"

Ya fadi yana kankance mata idanuwanshi, sai dai rikicin da yake cikin nata yafi nashi

"Zamu gani"

Ta fadi tana juyawa da nufin komawa kitchen ta wanke towel din da yake hannunta

"Me kika ce?"

AbdulKadir din ya tambaya ranshi a bace, juyowa tayi tana saka idanuwanta cikin nashi

"Kajini ai, ca nayi zamu gani"

Murmushi AbdulKadir yayi me sauti

"Zamu ga me?"

Ya tambaya, wuce shi Waheedah tayi ta ajiye towel din tana fitowa, bataso kome takeji ya tarwatse mata cikin gidan. Ta gaban AbdulKadir din tazo wucewa

"Bafa inda zakije Waheedah...kinjini ai"

Ikram ta gyarama kwanciya, ganin kamar zata fado tana cewa

"Sai kai tayi kuma"

Sosai AbdulKadir yake kallonta

"Rashin kunya zakimun Waheedah?"

Ya tambaya yanajin kanshi har dumi yake dauka saboda bacin rai, dagowa tayi tana matsowa kusa dashi

"Idan rashin kunya nai maka me zai faru?"

Mamakin da yakeji ne yake kokarin danne yanda ranshi yake tafasa, da za'a tambayeshi zaice babu rana daya da Waheedah zata iya daga mishi murya balle harta kalli cikin idanuwan shi tana fada mishi magana. Murmushin takaici ya sake kwace mishi, juyawa yayi da nufin yabar mata dakin, dan komai zai iya faruwa yaji tace

"Na dauka wani abin zakayi ai..."

Baisan me ya shiga kanta haka ba, har tambayarta yayi da yaga kamar wani abin yana damunta tace mishi bakomai

"Waheedah ki kiyayeni, Allah ki kiyayeni, karkice zaki fara mun rashin kunya. Gidane ba zakije ba, duk kwanan nan ma babu inda zakije, ba gida kawai ba ko ina ne ma"

Dariya Waheedah tayi da take nuna mishi shidin bai isa ba, tana kara bata mishi rai

"Lallai..."

Ta fadi tana sakeyin wata dariyar, runtsa idanuwan shi yayi yana budesu a kanta, ranshi in yayi dubu a bace yake, ya manta ranar karshe da wani abu ya bata mishi rai irin hakan, bayajin ma a duniyar shi gabaki daya akwai wanda ya isa ya bata mishi rai har haka, sai dai ita din.

"Ban isa ba kenan ko me kike son ce mun?"

Ganin kallon da take mishi ya tabbatar mishi da abinda take nufi kenan

"Waheedah..."

Ya fadi cike da kashedi

"Meye Sadauki? Nifa sai na fita, kaji na fada maka ma"

Juyawar yayi yana soma tafiya, gidan zai bar mata gabaki daya, idan ya daina jin bazai dauke ta da mari ba sai ya dawo yaji ta inda rashin kunyar nan da ba halinta bane take fitowa. Bin shi Waheedah tayi tana riko hannun shi, in bata fita ta shaki wata iska daban da ta gidan ba tanajin matsala zata samu, kirjinta zafi yake

"Kace mun inje ni dai, kaji... Dan Allah"

Hannun shi ya zame daga cikin nata

"Ki sakeni kafin in mareki"

Wannan karin mamakine karara fuskar ta

"Saboda zan fita shine zaka mareni? To ka mareni dan Allah... Ka mareni kaga in zai hanani fita"

Hannun shi AbdulKadir ya zame yana ci gaba da tafiya, sake riko shi tayi, ko kadan baisan ya akai hannun shi ya sauka kan fuskarta ba yana hadawa da tureta, ya manta yanda ko kadan bata da kwarin kirki, kafin ya rikota takai kasa kanta na buguwa da table din da yake ajiye a wajen, lokacin dayai kasa yana rikota har jini ya fara taruwa inda da alama ta fasa kanta ne. A rikice yake girgizata

"Waheedah...Waheedah..."

Tunda yake a duniya bai tunanin zaiga tashin hankali kalar wanda yake gani yanzun da take rike a hannun shi kamar bata numfashi ba. Baiyi tunanin akwai abinda zai gigita shi kamar wannan gigitar ba, sai yanzun da yakejin duniyar ta hade mishi waje daya.

*

Gyara kwanciya yayi yana sauke wani irin numfashi, kuskurene yayi da baisan ta inda zai fara gyarashi ba, na lokacin ya manta yanda Waheedah matarshi ba kanwarshi ba, da tana kanwar shi har lokacin zai dauketa ya kaita asibiti, in taji sauki suka dawo gida zaisa cable ya zani rashin kunyar da tai mishi, ya kuma zane wadda takejin zatayi mishi a gaba. Amman matarshi ce, baisan da wanne ido zai kalli Abba idan ta fada mishi ya mareta ba, dan a gaban shi Abba kan fadi duk namijin daya daga ma yarinyar shi hannu ya sani sai dai kaddara amman ya daki auren shi.

Sai dai ya bata hakuri, ya kamata ta hakura, ta sake bashi wata damar, kome zata ce mishi, duk rashin kunyar da zatayi mishi ba zaima kulata ba ballantana ya daga mata hannu. Tashi zaune AbdulKadir yayi yana dafe kan shi da hannuwan shi biyun, komai yakeji ya hade mishi waje daya, baisan dame zaiji ba, ranshi dayake bace da Nuriyya da ko kadan bata kula hankalin shi ba'a kwance yake ba ta kara bata mishi rai, ko da Waheedah da ta hargitsa duk wani kwanciyar hankalin shi.

Yasan da baiyi rashin kunya lokacin da aka bashi damar yin bayanin karar shi da Major yakai ba, da wahala ma ya kwana, tunda bayani kawai zaiyi suce mishi yaja ma matar shi kunne, sai yaba Major hakuri, amman bazai iya wannan ba. Rashin kunya ya tsula har Major din ya sa mishi hannu, da sukayi detaining din shi kuma ya sake jibgar wani a cikin cell din. Shisa yai kwanakin da yayi, gashi sai yanzun yakejin ciwon da jikin shi yake mishi.

Waheedah ko wannan bata duba ba take kara kallon idanuwan shi tana cewa ya rabu da ita, shikam bashi da wannan zuciyar, hakuri zatayi ta yafe mishi ta dawo suyi zaman su. Dan shi bazai taba iya rabuwa da ita ba. Yanzun ma ji yake yanda ranshi yake a bace in bai ganta ba akwai matsala, wata irin kewarta yakeji tana danne shi kamar bai ganta awanni kadan da suka wuce ba, a gigice yakejin rayuwar shi da wata irin rashin nutsuwa da kusancin Waheedah kawai yake samar mishi. Tashi yayi yana laluba aljihun shi yaji mukullan motar shi suna ciki. Ficewa yayi daga gidan ya shiga mota, wajen Abba zashi, in Waheedah bata dawo gidan shi yajita a kusa dashi ba yau baisan yanda zaiyi da tunani ba.

*

Tsintar kan shi yayi da kasa nufar bangaren Abba kai tsaye, dan haka ya wuce wajen Hajja, a falo ya sameta zaune da remote a hannunta, Zainab da itace Autarta kuma tana aji daya a jami'a a yanzun tana zaune gefen Hajja din

"Hamma ina wuni"

Ta fadi bayan Hajja ta amsa sallamar AbdulKadir din, kai kawai yadan daga ma Zainab din data mike tabar musu falon. Inda ta tashi AbdulKadir ya koma ya zauna, yana dafe kan shi cikin hannuwan shi dan ya rasa abinda zaice. Kallon shi

38 / 51