Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
kai karshe wajen baci, ya mata kuskure bawai bai mata ba, amman hakan bashi bane dalilin dazai sa ta kalli kwayar idanuwan shi tana fada mishi son ranta, bai tsaya kalmar neman saki ba, harda rashin kunya tana daga mishi murya.
"Saukake miki a hannuna yake ko? Ba zai faru ba to, kina jina bazai faru ba"
Wasu hawaye taji masu zafin gaske suna zubo mata, ji take wani abu yana yamutsawa cikin kanta, rashin hankalin da yake mata tunanin take ji yana gab da cimmata idan bai saukake mata auren shi ta huta ba yau.
"Wallahi baka isa ba"
Ta fadi muryarta na karyewa da kukan da takeyi, kujerar shi yaja baya yana mikewa, wani irin tuquqin bacin rai yake ji har idanuwan shi ke lumshewa
"Ki kalleni..."
Ya furta ta tsakanin hakoran shi, kukan ta taci gaba dayi
"Ki kalleni Waheedah!"
Ya fadi cikin wata irin murya data sata sauke idanuwanta da suka fara rinewa da kuka cikin nashi
"Na isa...Ni Abdulkadir Ahmad Bugaje na isa har nayi yawa. Bansan me yake damunki ba, ki kwanta kiyi bacci, bana bata lokacina akan abinda ya riga da ya wuce ke kin sani, zanyi kamar komai bai faru ba..."
Ya karasa maganar yana juyawa dan jikin shi ya soma bari da bacin ran da yake ciki
"Sadauki karka fita baka saukake mun ba..."
Waheedah ta furta kamar baiyi magana ba, kamar bata ji abinda yace ba, bai juyo ba, saboda baida tabbas kan abinda zai iya faruwa idan baibar dakin ba, yanda ya doko kofar saida ya firgita Ikram data zabura tana fashewa da wani irin kuka, riketa Waheedah tayi tana jijjigata cikin alamar lallashi dan itama kukan takeyi. Yana fita Anty ta shigo tana kallon Waheedah dake faman share hawaye. Dan haka ta karasa tana karbar Ikram din daga hannunta ta goya yarinyar da dakyar ta samu tayi shiru.
"Dan Allah kubi komai a hankali, kinji Waheedah? Kinga baki da lafiya..."
Saida ta share hawayen da sunqi daina zubar mata, da wani daci a makoshin ta tace
"Ni bance wani abu ba Anty, ko a musulunci an bani damar neman saki idan naga bazan iya zama dashi ba... Me yasa bazai mun abinda nake so ba?"
Yanayin karayar dake muryarta yasa Anty karasowa ta dafa ta, itama tana jin idanuwan nata sun ciko da hawaye dan Allah yai mata wata irin zuciya da ko bata sanka ba taga kana kuka itama tayaka takeyi, balle kuma Waheedah da hankalin yarinyar yasa take jinta har ranta. A raunane tace
"Ku dai bi komai a hankali, karki yanke hukunci cikin fushi..."
Wasu sabbin hawayen na zubar ma Waheedah tace
"Anty ki aramun wayarki dan Allah"
Batare da wata gargada ba Anty ta cire lambobin sirrin data rufe wayar dashi ta mika mata, wajen kira ta shiga tana fara saka lambobin mutum dayan da take da yakinin shi kadaine zai iya saka Abdulkadir yai mata abinda take so, shi kadaine kuma bazai ce tayi hakuri ko abi abun a hankali ba. Danna kira tayi tana kara wayar a kunnenta, ringing daya tayi a na biyun ya daga da sallamar data kasa amsawa sai ma wani sabon kukan da taji ya kwace mata. Dakyar ta iya cewa
"Abbah..."
Tana jin muryar shi daga dayan bangaren ya amsa da
"Waheedah?"
Cikin son tabbatar da ita dince, kai take daga mishi kamar yana ganin ta, wasu hawayen na zubar mata
"Abbah..."
Ta sake kira cikin kukan ta
"Subhanallah... Waheedah me yake faruwa ne? Lafiya dai ko?"
Kai ta girgiza mishi
"Abbah kai ma Abdulkadir magana ya sauwaqe mun... Dan Allah Abbah"
Ta karasa maganar kuka mai sauti na kwace mata, jim yayi daga dayan bangaren da alama yana juya zancen tane, kafin yace
"Hajiya Halima na kusa dake?"
Dakyar ta iya cewa
"Eh..."
"Ki bata wayar..."
Anty dake tsaye Waheedah ta miqa ma wayar, tana jan kafafuwanta ta hade su da jikinta hadi da dora kanta saman gwiwoyinta hawayenta naci gaba da zuba...!
*#Abdulkadir*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732: ©️
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
03
Tunda ya shiga gida bangaren Waheedah ya wuce, dakin baccin su ya shiga, yana zama gefen gadon. Kan shi sarawa yake tunda ya fito daga asibitin, baisan ta inda zai fara tarar matsalar da Waheedah take son janyowa rayuwar su ba, dan baisan meya shiga kanta ba, kafafuwan shi ya janyo da nufin dorasu kan gadon yaga takalman shi dabai kwance ba.
"Bazan cire ba..."
Ya fadi a fili, da Waheedah yake, dan ita ce bataso yana shigo mata da takalma har daki, abinda take so shi take mishi yau, shima abinda yake so zaiyi, hannu yasa ya dafe kan shi, yana kuma saukewa hadi da ajiye numfashi mai nauyi. Idan matsalar kwakwalwa ce ta samu Waheedah, yaga alama harshi takw son gogawa tunda ya fara magana shi kadai. Hoton su dake durowar gefen gadon ta ya dauka yana tsayar da idanuwan shi akai. So yake yagane wanne kalar kayane a jikin Waheedah din, yadai ga farare ne, dankwalin da ta nade kanta dashi ma farine, zai iya tuna da wayarta ta dauke su hoton, tana lafe a jikin shi, ya zagayo da hannunshi daya kan cikinta data dora nata hannun akan nashi, ya kankance mata idanuwan shi daba girman kirki ne dasu ba daman, da dariyar nan tata a fuskar shi.
Dan yatsan shi ya saka ya shafi dai-dai fuskarta, yasha ganin hoton a ajiye a gurin, hade da sauran hotunan shi da bazaice ga lokacin data dauke su ba, amman zai karya idan yace ya taba tsayawa ya kula da hoton da yake hannun shi, balle ya tambayeta lokacin data kai aka wanko hoton har aka saka shi a frame hakan, baisan meyasa sai yanzun yake son tambayarta ba. Sake shafar fuskarta yayi
"Me yake damunki yau? Me kike son janyo mana Wahee? Me kike son janyo mana haka?"
Ya tsinci kan shi da tambaya, shirun dakin na saukar mishi da wani irin yanayi daya saka shi ajiye hoton inda ya dauka. Baisan abinda ya kamata yayi ba, wani abu makamancin wannan bai taba faruwa da shi ba, asali yau ce rana ta farko da rikici ya soma hadashi da Waheedah, shisa yake jin komai ya kwance mishi, ba zaice baya fada da ita ba, ita dince dai bata taba biye mishi, komin fadan dazai sauke mata hakuri kawai zata bashi, baisan me yake damunta ba yau.
Aljihun shi ya taba, wayarshi bata ciki, waige-waige ya fara yana neman inda ya ajiye ta, babu shiri ya mike, duka inda tunanin shi zai iya kaiwa cikin dakin saida ya duba amman bai ganta ba, takawa yayi zuwa falon su, zuciyar shi na wani irin dokawa da ya sauke idanuwan shi kan table din da Waheedah ta fada kai, ga jini da harya fara bushewa kan kafet din, kafafuwan shi da yake ji sun soma rawa yaja zuwa hanyar kitchen, wani karamin bokiti yagani ya dauka ya tara ruwa a ciki, kan window din kitchen din ya dauki omo ya zazzaga a ciki. Abin goge-goge yake nema, bai gani ba sai wani towel karami.
Shi ya dauka ya saka cikin bokitin yana daukowa ya fito daga kitchen din, gefen da jinin yake akan kafet ya ajiye bokitin yana tsugunnawa, towel din ya fiddo ya matse yana soma gogawa a wajen, sosai jikin shi ya dauki dumi da alamar zazzabin da yake da alaqa da dana sanin da ya lullube shi, yana mayar da towel din cikin bokitin yaga yanda ruwan ya sake launi yaji wani abu na tattarowa daga zuciyar shi ya hadu a wuyan shi ya shaqe shi, a hankali kuma shige da ficen numfashin shi ya fara canzawa. Towel din yake gogawa a wajen da dukkan karfin shi.
'Jinin Waheedah ne duka anan'
Wata karamar murya ta furta cikin kunnuwan shi, numfashin shi na fita da sauri-sauri kamar wanda yai gudu.
'Bana bata lokaci akan abinda ya riga ya wuce, bana tunani akai saboda bazan iya komawa in canza ba'
Yake fadi cikin kwakwalwar shi ko zuciyar shi zata taimaka ta bashi hadin kai. Iya abinda zai iya gogewa daga jikin kafet din ya goge yana daukar bokitin ya mayar kitchen, wajen wanke-wanke ya juye ruwan, kalar shi nasa cikin shi yamutsawa, baisan lokacin da jini ya fara daga mishi hankali haka ba, fanfo ya bude kan ruwan dan ya wuce da wuri, bayason ganin shi, ya tara hannuwan shi a jiki ya wanke, har fuskar shi ya wanke ko zata rage mishi zafin da yaji tanayi, ya kashe fanfon ya fito. Tunawa yayi wayar shi yake nema, yaci gaba da duddubawa, baisan lokacin da yace
"Waheedah! Ina wayata?"
Idanuwan shi ya runtsa, bai gama tunanin yanda shima yake gab da samun tabin hankali ba yaji karar wayar. Hakan na sashi bude idanuwan shi babu shiri, inda yake jin karar wayar yake bi, harkan kujera daga gefe, hannu ya saka ya janyo wayar da rabin ta ya fara shigewa cikin lokon kujerar, sai dai kiran harya yanke, dangwala jikin gilashin wayar yayi tunda babu wani mukulli a jiki ta kuwa bude, mamakine bayyane a fuskar shi ganin Abba ne ya kira, bawai dan baya kira ba, lokacin daya kira dinne yaji ya mishi wani iri.
Yana shirin bin kiran sai gashi ya sake shigowa, amsawa yayi yana kai wayar kunnen shi da fadin
"Abba..."
Daga dayan bangaren Abba ya amsa
"Abdulkadir, kome kake kazo gida yanzun"
Zuciyar shi yaji tai wata irin dokawa
"Abba lafiya?"
Ya bukata yanajin sautin muryarshi daya fito a tsorace
"Ka dai zo..."
Kai ya girgiza
"Ni dai ka fara fadamun ko menene a waya tukunna"
Abdulkadir ya fadi, dan yanda zuciyar shi take bugawa sam bai aminta da kiran Abban ba.
"Abdulkadir..."
Abba ya kira cike da kashedi
"Ba zanyi tuqi a nutse bane idan bansan meye dalilin kiran ba Abba, ni dai ka fadamun dan Allah. Kaji"
Ya sake fadi
"Bari in aiko a dauke ka to"
Cewar Abba da alamun ranshi ya fara baci, kai Abdulkadir ya girgiza yana jin komeye yake shaqe da wuyan shi yana kara shaqe shi.
"Akan Waheedah ne ko?"
Ya tambaya muryar shi can kasa, yana kuma jin bugun zuciyar shi har cikin kunnuwan shi, idanuwa ya runtse yana jiran amsar Abba, a ranshi kuwa rokon Waheedah yake
'A'a Waheedah, bakimun wannan tonon asirin ba, baki mun haka ba, ba zaki taba mun haka ba'
Bude idanuwan shi yayi dajin Abba yace
"Akan ta ne, kazo yanzun ina jiran ka"
Kafin ya furta wani abu Abba ya kashe wayar, tayi yar karar alamun an kashe daga dayan bangaren cikin kunnen shi, sauke wayar yayi yana fadin
"Abba mana, Abba banaso ana kashe mun waya cikin kunne, da gaske bana so..."
Ya karasa maganar da furta
"Yaa Ilahee..."
Komai yake ji ya kwance mishi, takawa yayi yana fita daga dakin, gurin motar shi ya nufa, budewa yayi yana jefa wayar a ciki, harya daga kafarshi daya ya saka cikin motar yaji an kira sallah
"Ni sai nayi Sallah wallahi"
Ya furta kamar wani yace kar yayi sallah, cikin gida ya koma ya daura alwala, sai dai bayajin yana da nutsuwar da zai iya zuwa masallaci, anan dakin baccin su ya nemi darduma ya shimfida yana tayar da sallah. Sai dai ga mamakin shi kokawa ya soma yi sosai da nutsuwar shi, dakyar ya samu yai sallar tunani fal cikin ranshi, ko addu'a baiyi ba ya mike yana barin dardumar anan. Fita yayi ya shiga motar yana kunnuwa hadi da janta ya juya, maigadin kofar nashi ya bude mishi gate ya fice ya nufi hanyar da zata kaishi da gidan nasu da yake a kofar ruwa.
**
Dakyar Anty ta samu likitan yabar su suka taho gida, shima da alkawarin cewa zata dawo da Waheedah a ranar, komai a asibitin suka baro shi. Ita kanta Antyn taso koma menene abar shi sai Waheedah ta samu sauqi sai ayi, amman ita da Abbanta sunki yarda da hakan. Har suka shigo gida addu'ar Allah ya kawo musu sauqi takeyi. Waheedah da kanta ta fara jan Anty zuwa bangarenta, badan bata son ganin Mami ba, bata son kowa yace tayi hakuri ko tabi komai a hankali, batason jin duk wannan.
Kujera ta samu tai zamanta a dakin Anty, lokaci zuwa lokaci take saka hannu ta share hawayen dake biyo fuskarta, Ikram ma data qara bata tasha Anty ta miqama yarinyar. Tana nan zaune Abba ya shigo da sallama, tana sauke idanuwan ta cikin nashi wani irin kuka ya kwace mata, a hankali Abba ya karaso cikin falon yana neman waje ya zauna.
"Waheedah..."
Abba ya kira sunanta muryar shi cike da rauni, kanta da yake nade da bandeji ya fara bi da kallo, tukunna ya tsayar da idanuwan shi kan fuskarta da duk kumburin da tayi da alamun kukan da tasha bai hana yanda ta rame matuqa nunawa ba. Kukan da take yasa ta kasa amsa shi
"Waheedah kiyi hakuri kinji..."
Abba ya furta yana jin yanda zuciyar shi take a jagule, muryar Waheedah a dishe ta dago jajayen idanuwanta tana kallon Abba, kai take girgiza mishi tana sauke ajiyar zuciya a hankali
"Dan Allah Abba..."
Ta soma fadi tana jin zuciyarta kamar zata fado
"Dan Allah... Karkace in koma... Karka ce inyi hakuri Abba... Wallahi nagaji... Inajin idan na koma zuciya ta Abba..."
Tai maganar tana kai hannunta a kirji inda take jin zuciyarta kamar zata fashe, numfashi take ja tana fitarwa amman iskar bata kai mata inda take so, dakyar take iya magana
"Abba zuciyata ina jin kamar zata fado, dan Allah karkace inyi hakuri, karka tambayeni me ya faru... Bansan ta inda zan fara maka bayani ba, kawai nagaji ne, nagaji sosai"
Anty dake tsaye hannu tasa tana share hawayen da taji suna shirin zubo mata, a muryar Waheedah take karantar kuncin da Allah kadai yasan tun yaushe take danne shi, a muryat Waheedah take jin ciwon da take ciki, ya kuma taba zuciyarta ba kadan ba, sosai tayi niyyar lallaba yarinyar takoma dakin mijinta domin shi aure dan hakuri ne, kowa kaganshi zaune a gidan mijin shi komin dadin zaman su akwai hakurin da suke da juna ta fannin da bazai bayyanu ba.
Sai dai kuma batasan har yaushe za'a dinga labewa a bayan hakuri ana cutar mata a zamantakewa ta auratayya ba, batasan sai yaushe mutane zasu fahimta shi kan shi hakurin yana da qa'ida ba, a al'adance ma hakuri na da iyaka, balle addini daya sauqaqa matakin komai, batasan lokacin da mutane zasu fahimci duk da hakuri jigone na zaman aure bai sa ya zama ibadar auren gabaki dayan ta ba.
"Dan Allah Abba..."
Roqon da Waheedah tayi ya katse ma Anty dogon tunanin da takeyi, wani radadi takeji zuciyarta nayi, kuncin Waheedah na tuna mata da duk hakurin da tayi a nata gidan auren, yana sa tana tuna rashin sauqin da yake tattare da hakuri, sai mai matuqar karfin zuciya ake yiwa ya kauda kai. Abba kan shi numfashi ya sauke yana furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un... Abdulkadir...Halima kinga yaron nan saida ya kure hakurin ta ko?"
Abba ya karasa maganar yana jinjina kanshi, a raunane Anty ta amsa shi da
"Ai shikenan, ya kyauta, ya kuma yima kan shi wallahi"
Hajja ce ta shigo dakin da sallama, tana kare musu kallo, dan sallah take lokacin da Abba ya aika a kirata. Mami daman da Anty taje da kanta catai duk suna wajen ita kam bataga zuwan me zatayi ba, ta san zasuyi yanke duk abinda ya kamata akan Waheedah din. Duk kawaicin Mami, Anty tasan Waheedah ta ninka ta, yau kam tura takai bango.
"Allah dai yasa lafiya..."
Hajja ta fadi bayan Anty ta amsa mata sallamarta, kafin ta zagayo ta samu waje gefen Abba ta zauna, sai lokacin ta kula da Waheedah da tun shigowar Abba ta sauko daga kujerar da take ta zauna kan kafet din dakin
"Subhanallah, Waheedah? Ashe dai ciwon da yawa haka... Zainab tazo tana fadamun, yanzun nake shirin in idar da sallah saimu koma asibitin gabaki daya. Amman kamar bai kamata su baki sallama da wuri haka ba..."
Anty ce ta amsa Hajja da
"Basu bayar da sallama ba suma, zamu koma zuwa anjima..."
Da mamaki Hajja tace
"Ikon Allah... Lafiya dai ko?"
Tai tambayar tana kallon Abba daya girgiza mata kai
"Abdulkadir ne..."
Zuciyarta Hajja taji tayi wata irin dokawa jin sunan dan nata
"Yau kam dai ya kure hakurin yarinyar nan. Saki take nema..."
Cikin tashin hankali Hajja tace
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...saki kuma Alhaji? Meya faru? Me yai mata?"
Dan rausayar dakai Abba yayi, dan baida wannan amsar, ba kuma shi da karfin zuciyar da zai tambayi Waheedah din tunda har roqon shi tayi dakar ya tambaya. Waheedah dake share kwalla Hajja ta kalla
"Waheedah me ya faru?"
Batare data dago ba ko hawayenta ya daina zuba tace
"Dan Allah Hajja karki tambayeni meya faru, kiyi hakuri, duk kuyi hakuri, takardata kawai nake son a karbar mun a wajen shi..."
Maganar daga zuciyar ta takejin tana fitowa, ta dauka rashin Abdulkadir a kusa da ita zai barazana da rayuwarta, bata taba tunanin zama dashi ne abinda zai haifar da hakan ba, in baya kusa da ita ko numfashi batajin tana fitarwa dai-dai, amman yanzun tunanin kusanci dashine yake barazana da dai-daiton numfashin ta. Ba tasan lokacin da rayuwa ta bude musu wannan shafin ba, sai dai ko ba zata iya wuce shi ba, zatai duk wani kokari da zata iya ko dansu Fajr. Salati Hajja take tana kara wani
"Ke kam Waheedah kiyi hakuri mana, kinji tunda duk muna nan kibari a kira shi in shaa Allah koma menene yake faruwa zamuji sai a dai-daita ku...tunda haihuwa ta shiga tsakani ko dan yara sai a duba lamarin..."
Kai Abba ya girgiza ma Hajja
"Karkuyi amfani da yaranta ku danne ta..."
Rai a jagule Hajja ta kalle shi
"Karka cemun kana tunanin yin abinda take so ne batare daka duba lamarin ba?"
Kafin ya amsa Abdulkadir ya shigo dakin, kallo daya zakai mishi kasan babu nutsuwa a tattare dashi ballantana ai maganar kwanciyar hankali. Ko sallama baiyi ba, zagayowa yayi yana zama kan hannun kujera, zuciyar shi kamar zata fito daga kirjin shi saboda tsallen da takeyi
"Abba me tace na mata?"
Ya tambaya, rashin gaskiya shimfide a fuskar shi. Kallon shi kawai Abba yakeyi, Hajja ce ta watsa mishi harara
"Me kai mata Abdulkadir? Me ka sake yi mata?"
Cike da rashin fahimta yace
"Bangane me na sake mata ba Hajja? Na mata wani abune banda nayau?"
Girgiza kai Anty tayi tana fadin
"Hmm..."
Dan batason tayi magana, Abdulkadir rashin kunya zai mata tasan shi sarai
"Dan ubanka baka san me kai mata ba?"
Fuskar shi babu walwala yace
"Hajja mana..."
Ko kadan bayaso a saka shi a gaba ana mishi fada,