Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
dokawa har lokacin cikin bakon yanayin daya kasa fahimta yasa bayason ya zauna shi kadai. Ganin ta Waheedah ta koma ta zauna yasa Nuriyya din fara shirin zama itama.
"Ki wuce inda zakije"
Abdulkadir ya fadi yana watsa mata wani kallo dayasa ta barin wajen batare data ko yima Waheedah sallama ba, ta tsorata sosai, ranta kuma inyai dubu ya gama baci, meyasa zaima Waheedah magana kamar tana da muhimmanci a wajen shi, ita kuma yai mata magana kamar ita din bakomai bace, yana nuna kamar Waheedah yar uwarshi ce, bayan babu wanda baisan agola bace a gidan nasu, itama din bakomai bace a wajen shi. Harta koma inda ta fito ta zauna ranta a bace take jinshi, bikin gabaki daya yagama fita daga ranta.
*
Numfashi Abdulkadir ya sauke da barin Nuriyya wajen, gabaki daya abinda yakeji baqone a wajen shi, bakuma zai yiwu yar mitsitsiyar yarinya kamar Nuriyya ta saka zuciyarshi wannan gudun ba, kawai dan tana da kyau. Baya son raini, komai tattare da Nuriyya na nuna mishi idan ta samu fuska zata raina shi.
"Sai muzo tare ki tafi kibarni..."
Yai maganar yana kallonta, a lokaci daya yana rasa yanda akai ita kadai take ganin bangaren shi haka, yanda yakejin ita kadai zai iya nuna ma bangaren shi haka batare da tunanin zata raina shi ba. Dan kallon shi Waheedah tayi tana sauke idanuwan ta dan akwai wani abu tattare da nashi idanuwan da yake karya duk wata garkuwa ta jikinta, komai tattare da Abdulkadir daban take ganin shi. Batasan me zatace mishi ba, dan haka shiru tayi kawai tana lafewa cikin kujerar da take zaune a wajen.
Abinci aka kawo aka ajiye kan teburin da suke zaune, abincine wajen kala uku a cikin faranti daya, sai tsire a tsinke, harda hadin salad a gefe, a koshe Abdulkadir yake jin shi dan yaci abinci kafin ya fito, tsiren kawai ya dauka yana ci, kallon shi Waheedah takeyi harya cinye, nata tsiren ta dauka daga cikin plate dinta ta sake dorawa a nashi batare da tace komai ba, kallonta Abdulkadir yayi, ba dokawa zuciyar shi tayi ba, dumi yaji ta dauka wannan karin, hannu yasa ya dauki tsiren baice komai ba ya fara ci.
Lemo Waheedah ta dauka na roba da aka ajiye musu guda biyu, bata taba ganin shi da coca-cola ba tunda take, hakan yasa ta sanin ba zabin shi bane, dan haka ta bude mishi sprite din tana daukar abin zuqa ta saka a ciki tana turawa gaban shi. Dauka Abdulkadir yayi, banda Hajja da Yassar, babu wanda ya taba mishi abinda Waheedah din take mishi yanzun. Kowa a gida yana daukar baya bukatar kulawa, ko Hajja takan yi wannan tunanin wasu lokuttan. Sosai zuciyar shi ta sake daukar dumi, baice komai ba. Tsiren ya cinye, yana ganin Waheedah ta dauki abin goge hannu tana mika mishi, karba yayi ya goge hannun shi tukunna ya dauki robar lemon yasha kusan rabi ya ajiye
"Ruwa fa?"
Ta bukata, kai ya girgiza mata a hankali, yana kallon ta gyara zamanta kamar shi din dayaci wani abu kawai ya isheta, ita ba saitaci ba, numfashi ya sauke, yana kallon yanda fitilar wajen ta karama fuskarta haske. Haka suka zauna shiru, ita tunanin shine fal cikin ranta, shikuma bazaice ga abinda yake tunani ba har mutane suka fara hada-hadar fita, da alamu anyi abinda za'ayi an fara shirin tashi. Yazid ne yazo yana jansu biyun a cewar shi za'ayi hotuna, binshi sukayi akayi hotuna sosai dasu tukunna Abdulkadir din ya damqi hannunta yana fara janta. Binshi take tana kallon hannun shi da yake rike da nata, zuciyarta kamar zata fito waje take jinta.
Su duka biyun basu kula da Nuriyya da take bin bayansu tanajin kamar zuciyarta zata fado, karshen abinda zai faru shine Waheedah ta samu abinda take so, fuskar Abdulkadir din take kallo ko zata ga alamun so, kamar yanda yake bayyane a fuskar Waheedah, amman bataga komai ba, asalima kamar ranshi a bace yake. Ita dai komai zai faru kar Waheedah ta taba samun Abdulkadir din. Tana jin zatayi komai dan kar hakan ya faru. Wajen motar shi suka karasa tukunna ya saki hannun Waheedah din, yana bude motar da mukullin, har lokacin basu ga Nuriyya da take tsaye a gefe ba.
Zagayawa Abdulkadir yayi ya shiga motar, ya miqa hannu ya budema Waheedah daga ciki, jikinta babu karfi ta shiga cikin motar tana rufe murfin, su dukansu juyawa sukayi ita da Abdulkadir din ganin an bude murfin bayan motar.
"Nuriyya..."
Waheedah ta fadi cike da mamaki tana dorawa
"Banganki ba"
Cikin takaici Nuriyya tace
"Ya zakiyi kiganni daman"
Saida taji sautin muryarta tukunna tasan a fili tayi maganar da tayi. Yanayin muryarta Abdulkadir yaji bayaso, yanda tai maganar kamar Waheedah ta mata wani laifi ya mishi wani iri, saboda yana tare da Waheedah din bai kuma ga abinda tai mata ba. Baisan dalilin da yasa ta bude mishi mota tana shirin shigowa ba, shisa yake da tabbacin idan ta samu fuska zata raina shi, ga zuciyar shi da yaji tana shirin ci gaba da dokawa.
"Ki rufe mun mota..."
Ya fadi a tsawace, yana saka Nuriyya mayar da kafarta data dago, tana jin wasu hawayen bakin ciki sun tarar mata lokacin data rufe mishi kofar tana matsawa gefe ganin ya fisgi motar kamar zai bigeta. Cike da rashin jin dadi Waheedah tace
"Hamma..."
Saida yai baya da motar sosai yai kwana tukunna ya kalli Waheedah din idanuwan shi cike da rikici
"Tare nazo da ita? Meyasa zata budemun mota? Sa'anta ne ni?"
Kai Waheedah take girgiza mishi idanuwanta cike da tsoro, batason fada, musamman nashi
"Meyasa zaki kirani kamar ban kyauta ba then? Sa'ankine ni da zaki kira sunana kina tsareni da idanuwa kamar ban kyauta miki ba?"
Kai Waheedah ta sake girgiza mishi, yanda take jin ranshi ya baci nasa idanuwanta cika da hawaye. Tsaki Abdulkadir yaja, shi kanshi idan za'a tambaye shi asalin abinda ya bata mishi rai bazai ce gashi ba. Yasan Nuriyya na da hannu a cikin bacin ran nashi, baisan tayaya bane kawai. Tunda Waheedah ta lafe cikin kujerar motar ko motsin kirki batayi, ta gefen idanuwan shi yake kallon tana goge fuska, yasan kuka take. Inyai magana ta amsa yaji kuka take tabbas zai watsa mata mari ya bata dalilin da zata saka shi a gaba tana mishi kuka, shisa baice mata komai ha har suka karasa gida.
Ita ta fara fita daga motar, tukunna ya fito shima, zagayawa yayi ta gefen da take, cikin sanyinta ta dago da hannu tana mika mishi wallet din shi, karba yayi yanajin shi wani iri. Bude wallet din yayi tukunna ya sa hannu yana zaro duka kananun hotunan da suke cikinta, sosai ya matsa daf da Waheedah din ya kamo hannunta yana ware tafin ya saka mata hotunan a ciki tukunna yasa dayan hannun shi yana rufe yatsunta akan hotunan ya saki hannunta yana juyawa abinshi...!
*#TeamAbdulkadir*
*#TeamWaheedah*
*#TeamNuriyya*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732: ©️
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
09
Washegarin ranar a kwance ya wuni, tunda yai wanka, karin safe ma baiyi ba sai wajen karfe sha daya na safe. Ko daya fita yai sallah a masallaci wajen karfe daya, yana dawowa daki ya cire dogon wandon ya mayar da iya gwiwar shi, kwanciya ya koma yayi. Idan abu ya riga ya wuce baya tunanin shi, baya wannan asarar, shisa baisan dalilin da Nuriyya zata manne mishi cikin kai haka ba, ko idanuwan shi ya rufe ita yake gani, ta addabe shi, ta hanashi sakat, ya riga da ya fadama kanshi tana da kyau, baiyi ma kanshi karya ba tun farko, amman taki barin shi, wani in yagani saiya rantse da Allah hotonta ya dauka ya samu waje ya rataye cikin kanshi.
A hankali yaja karamin tsaki yana juya kwanciyar shi, yunwa yaji ta fara mishi sallama, duk da bai karya da wuri ba, saboda shi mutum ne da baya wasa da abincin kwata-kwata. In har baici ba, to damar hakan ne bai samu ba. Ya mike yasa wani ya kawo mishi dinne yake mishi wahala yau, lumshe kananun idanuwan shi yayi, har lokacin Nuriyya na manne cikin kanshi, bacci ne ya fara fisgarshi a hankali. Cikin kunnen shi yaji an turo kofar hadi dayin sallama a hankali
"Hamma..."
Muryar dayai tunanin Nazir ne ta dirar mishi. Shiru yayi bai amsa ba, yana fatan shirun tasa kowaye ya tafi.
"Hamma kazo inji Hajja..."
Nazir ya fadi yana riqe da kofar ko da almatsutsan Abdulkadir din zasu tashi. Bazai tsaya ya sauke su akan shi ba
"Kaina namun ciwo"
Abdulkadir ya fadi batare daya bude idanuwan shi ba, baisan kiran me Hajjon take mishi ba, bangaren ta yasan a cike yake da mutane, ta kuma san bason hayaniyar yake ba, zata fara sakawa a kira shi. Ba kanshi yake ciwo ba, jikin shine bayajin dadin shi. Turo baki Nazir yayi dan saida Hajja ta balbale shi da fada tukunna yazo kiran Abdulkadir din
"Tace kazo..."
Sake runtsa idanuwan shi Abdulkadir yayi
"Zanci ubanka idan na bude idanuwana kana cikin dakin nan"
Yanajin karar rufe kofa, batare daya bude idanuwan shi ba ya gyara kwanciyar shi yana kwantawa kan bayan shi hadi da dora hannuwan shi duka biyun kan cikin shi, bacci ne mai karfi ya dauke shi wannan karin duk da yunwar da yake ji. Ba zaice ga lokacin daya dauka ba, baccin kuma yau yayi karfin da baiji turo kofar ba sai bubbuga mishi kafa da yaji anayi, a tunanin shi Nazir dinne ya sake dawowa, raini yasa shi harda bubbuga mishi kafa wannan karin.
Cikin zafin nama yai amfani da inda yake jin hannun na bubbuga shi ya hasaso inda fuskar yake tunanin fuskar Nazir din zata kasance yakai mishi wani barin makauniya.
"Umm um um umm..."
Yassar ya fadi yanajin wani yawu da yake tunanin jinine na tattarowa yana cika mishi baki, dan a mummuke Abdulkadir ya same shi
"Ba zaka fita ba kenan dan uban ka?"
Abdulkadir ya fadi jin gurnanin da Yassar din yayi yana bude idanuwan shi hadi da mikewa ta sauke su kan Yassar dake dangwalo mummuken shi yana dubawa, ware kananun idanuwan shi Abdulkadir yayi
"Inalillahi... Hamma... Wallahi na dauka Nazir ne..."
Hannu Yassar ya daga mishi kawai yana wucewa bandaki ya kuskure bakin shi yana zuwa saitin mudubi, wajen harya tara jini daga waje, bude bakin shi yayi yana zira dan yatsa ya tana hakorin shi na sama da yaji kamar ya fara girgidi, sosai ya tattaba hakoran duk da yake tunanin sun fara girgidi yaji suna zaune dam, dubawa ya sakeyi yaga babu jini tukunna ya fito daga bandakin yana samu waje gefen gadon ya zauna, bazai karya ba, ya maku yanda ya kamata.
"Hamma..."
Abdulkadir ya kira da alamun dariya a muryarshi ganin yanda Yassar din ya nutsu. Gabaki daya fuskar shi Yassar yake ji ta dauki dumi kamar tana zazzabi ita kadai. Saida ya tabbatar idan yai magana muryarshi ba zatai rawa ba tukunna yace
"Dan ubanka ba zaka bude idon ka ba? Daka cire mun hakori me zaka fadamun?"
Sosai Abdulkadir yake son danne dariyar shi amman ya kasa, sauka yayi daga kan gadon yana mikewa tsaye, sosai yake dariya
"Inda Nazir dinne haka zaka kai mishi wannan dukan? Saboda kai baka da tausayi?"
Dariya Abdulkadir yakeyi
"Wallahi bansan kai bane ba"
Kai Yassar ya jinjina yana yin qwafa kawai. Gabaki daya duk wani karfin gwiwa daya shigo dashi dakin ya gama sacewa. Bandaki Abdulkadir ya wuce yana wanko fuskar shi ya fito, nesa da Yassar din ya zauna, dan yasan in ya yanke hukuncin rama dukan shi zaiji jiki. Tukunna yace
"Menene kake tashi na?"
Sai da Yassar ya watsa mishi wani kallo tukunna yace
"Hajja tace zaka dauki mutanen da zasu kai Khadija, saika tabbatar ka tattaro su Zahra dan kar suce zasu kwana..."
Dakuna fuska Abdulkadir din yayi
"Gaskiya babu inda zance...bari in kira su Zahra din in musu kashedi kawai"
Tsare shi da idanuwa Yassar yayi cikin yanayin daya sashi qara daquna fuska yana fadin
"An shiga rayuwa ta wallahi... An takurani gaskiya"
Kallon shi dai Yassar yaci gaba dayi batare da yace komai ba. Abdulkadir din bayason yana kallon shi haka, bayaso yana kallon shi kamar yayi wani laifi. Meyasa za'ace ya fara kai mutane wani waje, Hajja tasan a gidan in ba ita ba sai Abba, ko yara ba'a sakawa yakai makaranta. Balle yazo ya fara dibar wasu mutane kamar direba.
"Ba zaka je ba kace Abdulkadir? Kai tsaye ba zakaje ba? Ince maka Hajja tace kayi abu kana fadamun ba zakaje ba? Dan Ubanka ba zaka shiryu ba, ba zaka gane girma kakeyi ba ko?"
Yassar yake fadi ranshi a bace, baisan lokacin da Abdulkadir din zai gyara wannan muguwar dabi'ar ta rashin ganin kan kowa da gashi ba. Kicin-kicin Abdulkadir din yayi da fuska
"Nidai an shiga rayuwata gaskiya"
Ya sake maimaitawa yana saka Yassar fadin
"Yayi kyau..."
Yaja kafafuwan shi yana dorawa kan gadon, wayar shi kirar blackberry curve 2 ya zaro daga aljihu yana ci gaba da dannawa. Sake daquna fuska Abdulkadir yayi yana kallon Yassar din, yasan ranshi ne ya baci, bayan Abba a gidan babu wanda yake kokarin gujema fushin shi irin Yassar, fiye da Hajja dan yasan ita da wuri take sakkowa
"Wanne unguwa ne?"
Ya bukata muryar shi can kasan makoshi, inda yake Yassar bai kalla ba, ballantana yai kokarin kula shi.
"Hamma kaji... Wacce unguwa? Karfe nawa za'a tafi?
Shirun Yassar ya sake mishi
"Bana so ina magana ana mun shiru, kasani kuma, ina tambayarka kayi banza ka kyaleni"
Yanayin yanda yai maganar yana sa Yassar fadin
"Fada zakai mun Abdulkadir?"
Kankance idanuwa Abdulkadir ya sakeyi
"Magana nake maka kai shiru ka kyaleni"
Kai kawai Yassar ya jinjina
"Ya maka kyau"
Ya karasa maganar yana mikewa ya fice daga dakin, Abdulkadir nabin shi da fadin
"Kaifa kaqi bani amsa, banyi fushi nabar maka dakin ba kaine zaka fita? Hamma bana son irin haka... Hamma... Ok ya maka kyau"
Wucewa Yassar yayi, yana jin 'Ya maka kyau' din da Abdulkadir din ya fadi da tasa shi jin son komawa yasa belt ya zane jikin Abdulkadir din, sai dai alkawari yaima kanshi bazai biyema Abdulkadir din ba, dan idan akwai mashi a kusa, tsaf takaicin dazai qunsa maka zai saka soka mishi batare daka sani ba. Idan ya biyema Abdulkadir zai dake shi saiya karya shi, yana kuma da tabbacin duk da bazai rama ba, bakin shi bazai shiru ba. Addu'ar shiriya yai mishi kamar ko da yaushe.
*
Saida ya dauro alwala tukunna ya fito daga dakin da nufin zuwa masallaci dan yaga la'asar ta kusan qarasawa, yana da tabbacin ana gab da kiran sallah.
"Zahra..."
Ya kira daya hango ta taho, tun jiya yake mamakin girman yarinyar, wai har ta gama sakandire, Yassar ne yake fada mishi ta nemi gurbin karatu a jami'ar Bayero dake nan Kano din ma da yake mishi zancen girmanta. Duk da ta tsallake aji uku, kasancewar tana da kokari sosai. Takowa take a hankali tana nufo inda Abdulkadir din yake
"Yanga zaki tsaya mun?"
Ya fadi yana kallon ta, kai ta girgiza mishi tana saurin fadin
"A'a..."
Ta karasa inda yake tsaye da sauri. Kallon ta Abdulkadir yayi, dankwalin lace din dake jikinta ne ta dora saman kanta batare data daura ba, indai Zahra ce ba zata taba yin abu irin na mutane ba yasani, ko makaranta zataje hijab dinta in baya hannu lokacin zakaga tana saka shi.
"Ki kawomun abinci...da ruwa, kikai mun dakina a bude yake..."
Amsa shi tayi tana shirin juyawa Abdulkadir yace
"Ki fada musu ni zan dawo daku daga wajen kai Adda... Duk wanda na nema sai yaji a jikin shi"
Ware idanuwa Zahra tayi, gabanta yana faduwa, kafin ta dakuna fuska
"Baki jini ba saina watsa miki mari"
Sake dakuna fuska tayi, da gaske Hajja take ba zasu kwana ba din dai, bayan Adda Khadee din da kanta tace musu zasu kwana tun kafin bikin.
"Zan fada musu"
Zahra ta amsa tana wucewa, yana kallonta tasha kwana, tunawa yayi baima tambayeta wacce unguwa ko kuma karfe nawa ba, bin bayanta yayi tunda ta rigada tasha kwana ko kwala mata kira yayi ba lallai taji shi ba, gashi yau bayajin hayaniya kwata-kwata. Zahra kuwa tana shan kwana taci karo da Amatullah
"Kinsan Hajja tasa Commander ne yakai mu?"
Dafe kirji Amatullah tayi
"Kice mun wasa kike? Haba dai Commander... Ina ce Hamma Yazid zamu bi"
Kai Zahra ta girgiza ma Amatullah din
"Yanzun yaimun magana da kanshi, wai karma mu bari ya neme mu idan an kaita din"
Buga kafafuwa Amatullah tayi cike da rashin jin dadi
"Allah dai ya hadamu da jarabu da qwai..."
Turo baki Amatullah tayi tana fadin
"Ai gara Jarabu da qwai akan Hamma A..."
Hadiye maganar tayi ganin Abdulkadir din a tsaye ya diro musu kamar mikiya. Yanda ya tsareta da idanuwa yana tabbatar mata da maganar yake so ta karasa, wani abu da taji ya tsaya mata a wuya ta hadiye, a daburce tace
"Hamma A... Hamma Aminu"
Zahra da yanayin Amatullah din ya tabbatar mata da Abdulkadir din ne ya karaso wajen yasa ta juyawa ta kuma matsa kamar zata hade da bangon wajen, da yanayin fuskarshi ya tabbatar mata da yajita.
"Yaushe Aminun ya zama Hamman ki?"
Abdulkadir ya fadi yana tsare su da idanuwa. Alamun motsi yayi su biyun suka kwasa da gudu, kai ya girgiza murmushi na kwace mishi
'Jarabu da qwai'
Ya maimaita cikin zuciyar shi wani murmushin mai sauti na kwace mishi
"Sai naci uban yaran nan Allah..."
Yai maganar a fili yana juyawa. Masallaci ya fita abin shi. Sanda ya dawo hanjin shi har nadewa suke waje daya. Dakin shi ya nufa kai tsaye yana tunanin ganin abinci baiga komai ba, tabbas saiya zane jikin Zahra. Fita yake shirin yi yaji an kwankwasa kofar hadi dayin sallama cikin sanyin muryar daya tabbatar mishi da Waheedah ce.
"Shigo..."
Ya fadi
Da kafa ta tura kofar saboda farantin da yake hannunta, tukunna ta shiga dakin. Zahra ta sameta tace Commander yace ta kai mishi abinci. Hakan yai mata dadi, tun safe take jin ganin shi, ta fito yafi a qirga amman bataga giccin shi ba, batason fito da hotunan daya bata jiya daga inda ta adana su, saboda gidan cike yake da mutane. Farantin ta ajiye mishi a kasa tana mayar da hannunta daya baya kamar mai boye wani abu
"Ina wuni"
Ta gaishe dashi
"Lafiya..."
Ya amsata a taqaice yana jan farantin gaban shi
"Akwai wainar shinkafa, ban saka maka ba saboda nasan baka ci"
Da mamaki Abdulkadir ya dago yana sauke mata kananun idanuwan shi. Baya tunanin ko Hajja tasan bayacin wainar shinkafa, dan da bakin shi bai