Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
zasu siya. Tana kuma da tabbacin masu kyaune, za'a saka mata kayanta a gidan da bai cancanta ba. Gyara zama Nuriyya ta sake yi, sosai takejin abin kamar a mafarki. Waheedah da take ta hira da kawayenta suna dariya take kallo, tana jin wani nauyi a kirjinta.
Yanda kawayenta na FCE da basu taba ganin Waheedah ba suke zancenta yai mata zafi, yanda take shiga zuciyar duk wanda yaganta lokaci daya na tsayama Nuriyya a makoshi. Yanzun yanda take dariya na kara hada mata zafi, babu abinda take tunani sai kanta, da za'a daureta a auren Anas cikin kwanaki biyu, Waheedah zata ci gaba da hidimarta babu nauyin auren kowanne talaka akanta. Zata iya samun maikudi ta aura, karshen abinda take si ya faru kenan. Zata karasa mutuwa idan Waheedah ta samu Abdulkadir, shisa take addu'ar karya taba kallon Waheedah din da wannan niyyar.
Bazai taba yiwuwa a liqa mata auren Anas, Waheedah kuma ta samu Abdulkadir ba. Sai dai ko bata same shiba, tasan zata samu wani wanda yafi Anas din kudi, zata samu abinda ita bata samu ba kamar koda yaushe. Hakan kadai idan tayi tunani tanajin kamar zatayi hauka. Ko kadan rayuwa batai mata adalci, Waheedah ta zama kamar kaddara ta shigo da su rayuwar junan su dan ta nuna ma Nuriyya abinda duk take son zama amman yai mata nisa. Idanuwanta ta lumshe, alkawari taima kanta ta gama zubda hawaye akan abinda yake faruwa, tunda Anas yace yaji yagani, zata ga ko zai iya jure zaman aure da ita. Dan ta gama shirya mishi wulakancin da zaisaka shi dana sanin aurenta.
*
NDA KADUNA
Wanka ya fito, daga shi sai gajeran wando, da towel rataye a wuyan shi. Ahmad da shi kadaine abokin shi a zaman shi makarantar horar da sojojin tunda yazo ta shekaru hudu da wani abu, har yana shirin fita kuma, dan watannin daya rage musu bashida yawa. Suna shekararsu ta karshe kenan. Babu ruwan shi da kowa, in baka shiga lamarin shiba, sai abinda bazai iya kaucewa bane kawai zai hadaku. Ko wajen motsa jiki, ko training, ko a aji, wani abu dai daya zama mishi dole, saboda akwai masu saurin daukar zafi irin shi. Saidai bakowa yake jurewa hukuncin manyansu idan fada ya kaure ba.
Tun suna mamakin taurin zuciya irin na Abdulkadir harsun bari, shisa zuwa yanzun babu mai shiga sabgarshi sai ta kama, a yan Terma five kenan, balle kuma wanda suke kasan shi, har basaso wani abu ya hadasu da Abdulkadir din. Zai dakeka kamar ya samu ganga, musamman idan ya tashi yana jin bacin rai, in ya samu wani ya huce a kan shi yakanji ya dawowa dai-dai.
"A. Bugaje"
Ahmad yace kamar yanda kowa yake kiranshi a NDA din.
"Baka gyara wayar nan ba ashe?"
Screen dinshi ya fashe, a kwana biyu yana dan samu ya amsa kira idan ya shigo, saita kara faduwa, yaje ya gyara dinne baije ba. Yassar ma a wayar Ahmad din yake kira su gaisa.
"Zan gyara"
Ya fadi a takaici yana karasawa kan gadon ya kwanta. System dinshi ya janyo da take ajiye kan tebir din da yake dakin, budewa yayi, hannuwan Waheedah da kunshinta na cika screen din. Har yau baiga kunshin da yai mishi kyau kamarshi ba
"Hannuwan nan namun kyau wallahi, ina ma in gano yarinyar da take da shi"
Ahmad ya fadi yana miqa kanshi dan yaga hango sosai. AbdulKadir yakai hannu ya latse system din yana kasheta gabaki daya.
"Au dan bakin ciki kar ingani?"
Yai maganar yana dariya. Har duba system din yayi baiga hoton ba, ya rasa kalar boyan da Abdulkadir yai ma hoton, idan zai mutu yana tambaya ko yasan mai hannun ne, ko yana da alaqa da ita kamar yanda yai zato da farko bazai kulashi ba ballantana ya samu amsa. Kamar yanda yanzun ma bai kulashi ba. A gidansu Abdulkadir banda Yassar baisan kowa ba, sai Hajja dan sukan gaisa idan ta kira Abdulkadir din koshi ya kira, sai Zahra da itama suna waya, itace ma daya tambayi AbdulKadir din ko kanwarshi ce ya samu amsar
"Ban damu da ka kusa zama cikakken soja ba, zan karyaka Ahmad, da gaske zan karyaka..."
Yayi dariya sosai, kuma hakan ya tabbatar mishi da cewa kanwar Abdulkadir din ce. Akwai yarinyar da yake yawo da hotonta a wallet din shi. Wasu lokuttan kuma yakan cire hoton ya saka a aljihun shi, duk idan aka bata mishi rai Ahmad na kula yakan saka hannun shi a aljihun shi, kamar hoton nada wani sihiri da zai hutar da fushin shi. Duk yanda yake so ya tambayeshi alaqar shi da yarinyar hoton saiya kasa, saboda a bayyane yake. Tana da muhimmanci na gaske a rayuwar shi. Bai dai taba nuna alamar yana da budurwa ko yana son wata ba. Idan har hirarsu ta tsawaita to ta dangancin aikin da suke gab da fuskanta ne na kare kasarsu.
Sai dai watanni kusan bakwai da suka wuce, yakanga Abdulkadir din manne da wayarshi duk dare, ba daddanawa yake ba, da alama dai yana karanta wani abinne, yakan kuma ga yana murmushi shi kadai inya zauna da wayar a hannun shi. Gashi ya bude whatsapp din da babu yanda baiyi dashi ya bude ba, yaki. In kuma ya dauki wayar Abdulkadir din dan yai kira ko wani abu, banda yan gidansu da zaiga Hamma wanne, ko Adda wance, sai su Zahra, baya ganin kiranshi da kowa sai lambar daya sakama 'Wahee'. Yakan kuma ga saqoninta na shigowa wasu lokuttan. Baida tabbas, amman yana alaqanta hotonta ne Abdulkadir yake yawo dashi.
Juya mishi baya Abdulkadir yayi, yana jan pillow ya dora hannuwan shi akai, dan baya sakawa a kanshi, koya kwanta yasa pillow daya fara bacci yake zarowa ya dora hannunshi akai. Gashi har yanzun kwanciyar jarirai yake, jikin shi a dunqule haka yake bacci. Idanuwan shi ya lumshe, hoton Nuriyya na mishi yawo kamar koda yaushe, tun yana kokarin danne shi harya haqura yabarshi. Ya daina kokawa da zuciyarshi akanta, zuwa yanzun ya fahimci zuciyar shi na doka mata. Zai wani abu akai, saiya fita daga NDA ya dan samu nutsuwa, yanzun koma menene yake ji dole ya jirashi ya nutsuwa tukunna.
Lokaci irin wannan hirar Waheedah yakan karanta, har tai mishi saida safe, yakan koma baya yaita sake karantawa har saiya fara jin bacci. Amman kwana biyu hakan baya samuwa saboda bai gyaro wayarba. Yana kewar hirarrakinta, dan takan hana mishi tunanin Nuriyya irin haka, takan debe mishi kewar gida da gujema ganin Nuriyya ya hanashi zuwa. Sosai surutun ta yake mishi dadi
'Hamma kasan me ya faru yau'
Yakan karanta sakkoninta da sanyin muryarta, har yanayin idanuwanta yakan gani, kamar tana cikin dakin tare dashi. Idan an bata mishi rai yakan lumshe idanuwan shi yaji muryarta cikin kanshi
'Banda saurin fushi Hamma, dan Allah banda saurin fushi kaji'
Takan fada mishi haka a sakkoninta, tana saka murmushi kwace mishi. Inba ita ba, babu wanda ya isa yana bashi umarni haka, ko abinci takan mishi magana yaci, karya zauna da yunwa, wata rana sunanta kawai zai rubuta, zata ce mishi ya ajiye wayar ya kwanta. Yanda take karantarshi har mamaki yake bashi, tashi yayi ya dauko wallet dinshi ya ajiyeta gefen kanshi yana gyara kwanciyarshi. Hotonta yai amfani dashi ya danne na Nuriyya da zai sakashi tunanin abubuwan da zasu addabeshi. Baccin ya fara jin yana fisgarshi
'Hamma kayi addu'a'
Yaji muryar Waheedah na fadi cikin kanshi, batare daya bude idanuwanshi ba yayi addu'a, ko tofawa baiyi ba, bacci ya dauke shi.
*
Washegari da yake ya fada asabar, Ahmad ya dame shi, suka shiga kasuwar wayoyi ya gyara screen din wayarshi tukunna suka dawo. Suna dawowa charge ya saka wayar dan yaga yayi kasa sosai. Yai sallar azahar yazo ya zauna ya fara cin abinci, wayar ya ciro daga chargy ya bude data dinshi yana ci gaba dacin abincin, text dinshi ya shiga ganin wajen sakonnin ashirin, ya kuma san Waheedah ce. Dubawa yayi duka na jin ko yana lafiyane. Zuciyar shi na daukar wani irin dumi da sakonninta ne kadai kan haifar. Tana bashi kulawar da yake so, kulawar da babu wanda yake bashi ita sai Hajja, itama bakowanne lokaci ba.
Whatsapp din ya shiga, sakkoninta ne da yawa, zaice ita kadai take turo mishi sakkoni haka, su Nawaf gaisuwace, sai kuma zagi idan ya karanta bai amsa ba. Yassar ma hakan ne, yafi jin dadin nata fiye da nakowa, ita kadaice bata taba magana akan halayyarshi ba, asalima tana saka shi jin babu wani abu marar kyau a abinda yakeyi din. Bata damu dako ya amsata ko bai amsata ba, idan tazo takan sake mishi magana ta kuma bashi labari, Waheedah daban take da kowa na rayuwar shi.
Daga farko ya fara karanta sakon, da gaisuwa ce, hirar makaranta. Sai kuma ta fara bashi labarin suna hidimar biki. Karanta sakkonin yake yana cin abinci, kafin yaji shinkafar ta bimishi ta hanyar da bai kamata ba, tari ya kuwa sarqe shi, ruwa ya dauka babu shiri yana kwankwada, amman tarin bai daina ba, ga kirjinshi da yakeji kamar an fara hada wuta a ciki, idanuwan shi harsun kawo ruwan wahalar shaqewar da yayi, hakan yasa shi kankance su yana sake duba sakon Waheedah
'Nikam nagaji sosai Hamma, daman haka hidimar bikin kawa yake? Allah nafi Nuriyya gajiya'
Kasa yayi babu shiri yana isa sakonta na karshe
'Hamma har an daura auren Nuriyya fa'
Karanta sakon yake yana son fahimtar asalin ma'anar shi, kafin yaji numfashin shi na barazanar daukewa. Kanshi yake girgizawa yana sake danna wayar ko zaiga wani sabon sakon Waheedah din da zai karyata na karshe.
"No... No... Wasa ne wannan"
Ya furta yana jin zuciyarshi kamar tana rabewa biyu, kullum Waheedah na mishi hira, me yasa bata taba ce mishi Nuriyya zatayi aure ba, sai yanzun ne zata fada mishi an daura mata aure.
"Haka nace ki jirani, in nutsuwa waje daya Nuriyya. Nace ki jirani"
Yake fadi kamar wanda ya samu tabin kwakwalwa, ji yake gabaki daya duniyar ta hade mishi waje daya. Wayar ya cilla kan gado yana ture abincin, mikewa yayi ya fice daga dakin kwanan nasu. Wajen motsa jiki ya nufa, yana addu'ar kar wani ya tare mishi hanya, dan ko gani bayayi sosai, wani abu yake son duka, idan ba punching bag ba, to fuskar duk wanda tsautsayi ta gifto dashi. Allah ya taimake shi harya karasa wajen motsa jikin baici karo da kowa ba, bai kuma kula ko ana kaucewa bane idan an hangoshi
"A. Bugaje..."
Ahmad dake wajen ya kira ganin yanayin Abdulkadir din
"Ka matsamun Ahmad..."
Abdulkadir ya fadi yana karasawa ya dauki abin nade hannu ya fara nannadawa a hannun shi. Ahmad na karasawa wajen shi
"Me ya faru? Lafiya? Kaimun magana dan Allah..."
Dayan hannun Abdulkadir yake nadewa
'Hamma har an daura auren Nuriyya fa'
Shine maganar dake mishi yawo a ko ina na jikin shi tana kara saka kirjinshi wani irin radadi, yasan bacin rai, yasan fushi, yasan abubuwa da dama. Amman yanayin da yakeji yanzun daban ne a rayuwarshi, yanayine da baya fatan ya sake jin shi har abada, dan haka bazai bari ya dame shi ba, zai daki wani abu har saiya daina jin kirjinshi na mishi kamar zai bude.
"A. Bugaje..."
Ahmad ya kira cike da damuwa a muryarshi, Allah ne shaida yana jin Abdulkadir din kamar dan uwanshi. Bai kuma taba ganin yanayin da yake gani a fuskarshi ba, bai kula shi ba, punching bag din ya soma duka kamar zai jijjigota, da dukkan karfin shi yake dukanta, amman ji yake kamar yanayin da yakeji na karuwa da duk dukan, kamar da tunanin Nuriyya a matsayin matar wani zuciyarshi na kara budewa. Saida yaji numfashin shi na barazanar daukewa tukunna ya daina dukan yana dora hannuwan shi gwiwoyin shi hadi da wani irin sauke numfashi, tukunna ya dago ya hada wata irin zufa.
Kankance idanuwan shi yayi yana kallon Ahmad, muryarshi can kasan makoshi yace
"Tayi aure. Ahmad tayi aure..."
Kai Ahmad ya jinjina mishi yana fahimtar dalilin da yasa Abdulkadir din shiga yanayi, bai magana na ba, dan yaune karo na farko da Abdulkadir din yake fada mishi wani abu mai girma haka
"Ta jirani fa in nutsu ne... Shine tayi aure. Ni nace banyi tunanin aurenta bane? Me yasa zatayi aure?"
Ya karasa yana sauke numfashi, hannu Ahmad yakai ya taba kafadar shi cikin son nuna mishi yana tare dashi, ya fahimta. Abdulkadir din ya kauce yana fadin
"Don't... Kabarni"
Ya juya yana ficewa daga wajen motsa jikin, dan iskar da take wajen ta mishi kadan, kanshi kamar zai bude saboda bacin ran da yakeji a cike dashi. Har wani ja-ja yake gani yana gilmawa ta cikin idanuwan shi. Tayi aure bata jira shi ba, shine tunanin da yake cike dashi, yana jin wani yanayi na maye gurbin koma meye yake ji akan Nuriyya...!
#TeamAbdulKadir
#TeamYassarDinAntyFati
#TeamWaheedah
#FWA
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
14
"Sadauki dan Allah... Ka saukake mun auren nan"
Muryar Waheedah ta daki kunnuwan shi tana dawo dashi daga dogon tunanin daya tafi, runtsa idanuwan shi yayi yana sake budesu akanta. Dubawa yake ko zaiga alamar wasa a tata fuskar, ko zaiga hijabin da ta saka tsakanin su ta yaye. Kan hannun kujerar dake kusa dashi ya zauna yana maida numfashi, sosai ya girgiza, bazai tuna ranar karshe da wani abu ya girgiza shi haka ba. Kallon Waheedah ya sake yi da yaji kamar kafafuwan shi na rawa saboda tashin hankali. Hannu yaga tasa tana share kwallar da ta tsiyayo kan kuncinta. Kirjin shi yaji yana zafi, gani yake yau din gabaki daya duk wani abu da tasan bayaso takeyi, kamar kuma tana yi dinne dan ta bata mishi rai.
"Wahee..."
Ya kira muryarshi can kasan makoshi, bata dago ba, taji shi, ta saurara ne ko tsikar jikinta zata tashi kamar ko da yaushe, tsayin shekaru baisa ta daina jin yanayin soyayyar shi ta daban da take taso mata duk idan ya kira sunanta. Wannan karin babu abinda taji banda gajiya da komai, duniyar take ji ta hade da ita a waje daya, kamar tana cikin dakin da babu ko da window ballantana kofa, ji take fitarta daga dakin zata zo da saukake mata auren shi da zaiyi.
"Wahee magana nake miki"
Abdulkadir ya fadi, yana kokarin danne bacin ran da yake ciki, yanayin da yazo mishi a wahalce, saboda Waheedah ce, bai taba boye wani yanayi nashi ba a tare dashi. Bai taba tsoron bude mata komai nashi ba, tare da ita bai taba jin akwai wannan bukatar ba, idan ranshi a bace yake yana nuna mata saboda tasan yanda zatayi dashi, idan farin ciki yake takan gani. A gabanta yake dariya sosai dan yasan bazata taba raina shi ba, a yar karamar duniyar shi daga ita sai Yassar yake tsokana sosai. Ita fiye da kowa, ko Yassar kanyi shakkar mishi wani wasan, amman cikin ido Waheedah kan kalle shi ta tsokane shi.
Ganin tayi shiru har lokacin yasa shi saukowa daga kan kujerar yana tsugunnawa kusa da ita. Hannuwanta ya kamo duka yana rikewa cikin nashi. Kusancin shi bai taba kinyin tasiri akanta ba, yasani, lokutta da dama ko damun shi tayi da surutunta, matsawa zai ya rike hannunta bakinta zai shiru. Idan wani abu yai mata daya riketa a jikin shi yaji ta zagaya hannuwanta a bayanshi yasan ta karbi hakurin shi batare daya furta ba. Yanzun ma hakan yake so yayi amfani dashi kafin komai ya karasa kubce mishi.
Ita kanta Waheedah mamaki takeyi, dan tasan abinda yake kokarin yi din, lokuttan duk da yayi tasani, amman hakan bai taba hanashi tasiri akanta ba, wannan karin zuciyarta ta gama bushewa. Hawayen da ke shirin zubo mata taji sun tsaye cik, kamar tabatan da yayi ya kara busar mata da zuciya. Hannuwanta ta zame daga cikin nashi, tana yawata idanuwanta akan fuskar Abdulkadir din
"Ka kwashi yaranka, ka bani takardata..."
Tai maganar muryarta na mata baqunta cikin kunnuwanta, balle Abdulkadir da yake kallonta idanuwanshi na kankancewa da bacin rai. Kallon shi take, yanayin da take gani a fuskarshi a da zai tsoratata, sosai zuciyarta zata fara rawa da abinda zai faru, amman yau ko a jikinta take ji. Itama ranta a bacen yake, karo na farko da takejin son dora bukatarta sama da tashi. Wani murmushi yayi mai sauti yana mikewa, bin shi da kallo Waheedah tayi ganin ya soma tafiya, amman ba kofa ya nufa ba, hanyar da zata kaishi dakin Anty. Wani sabon zazzabi take ji yana lullubeta, da gaske Abdulkadir yakeyi yaranta zai dauka. Hawayen da suka bushe mata take jin sun fara farfadowa.
Tana kallon shi harya bace mata, dakin Anty ya nufa kanshi tsaye. Ko kwankwasawa baiyi ba ya tura kofar yana samunta a tsaye.
"Ikram zaki bani"
Kallon shi Anty takeyi, tasan taurin kanshi tun yarinta, amman nayau da take gani daban ne, musamman Waheedah, bata taba ganin ran yarinyar a bace irin nayau ba, ko menene Abdulkadir din yai mata mai girma ne. Amman hakan baya nufin tana son ganin mutuwar auren nasu, kodan yara dake tsakani
"Abdulkadir karkayi haka, karka yanke hukunci cikin fushi dan Allah. Ka duba yarinyar nan duka watanta nawa a duniyar? Idan zaka tafin ne ma, ka dauki Fajr shi. Kabarta ta huta idan an kwana biyu saika dawo kuyi magana, itama tahau dokin zuciya ne"
Kankance idanuwan shi Abdulkadir yayi, yana wani irin sauke numfashin bacin rai, Waheedah ita taja mishi tonon sililin nan. Da ta saka kowa yazo yana tsoma mishi baki a cikin maganar iyalin shi
"Kiban yarinyata Anty..."
Abdulkadir din ya fadi yana kokarin danne sauran maganganun da suke kan harshen shi. Itama Antyn ranta take ji yana kara baci
"Ba zakaji magana ba kenan ko? Ba zaka ji ba ko Abdulkadir..."
Runtsa idanuwan shi yayi yana budesu
"Idan da naso jin ra'ayinki kan abinda yake faruwa ina da bakin dazan bukaci hakan...kiban yarinyata"
Hannu Anty ta saka tana kwance goyon Ikram din, mika mishi ita tayi tana furta
"Allah ya shirya"
Karbar yarinyar yayi da taketa bacci kamar komai bai faru ba, nutsuwar da take ciki na sakashi sauke numfashi, saida ya gyarata cikin hannun shi tukunna ya kalli Anty
"Amin"
Ya juya yana ficewa daga dakin, yanda ya doko kofar na saka Anty yin dana sanin marin da taki daukeshi dashi. Sai dai tasan Abdulkadir idan bai rama ba, sai ya gaya mata maganganun da zatayi satika tana juyi dan kunar rai. Wani abin da zai