Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
ko dacan ma bayaso balle yanzun da ba yaro bane shi, sai dai baiga laifin su ba, Waheedah ce, duk laifin nata ne da tai mishi wannan tonon sililin, tafi kowa sanin yanda yake son sirri a rayuwar shi, abinda ya faru yau din tsautsayine da zasu iya magance shi tsakanin su, baisan me yake damunta da ta kwaso matsalarsu tana fadama su Abba da baiga ta inda abin ya shafe su ba.
"Ka kyauta Abdulkadir... Ka ji... Ka kyauta"
Hajja ta karasa muryarta na karyewa, idan ranta yai dubu a bace yake. Abba ya sake kallo
"Dan Allah Abba me tace nayi mata?"
Kai Abba ya girgiza mishi
"Batace kai mata wani abu, aurenka ne kawai ta gaji dashi"
Cikin wani irin tashin hankali Abdulkadir ya kalli Waheedah da ta sauke mishi rinannun idanuwanta. Da nashi idanuwan yake tambayarya me take? Me take yi musu haka?
"Abba zanyi magana da ita... Kaji... Hajja kunji..."
Ganin suna kallon shi yasa shi dorawa da
"Dan Allah..."
Abba ya fara miqewa, shikam batun yanzun ya sallama da lamurran Abdulkadir ba, tsakanin shi da yaron idone da addu'a, amman shikam yace yayi ko kar yayi bakin shi ya daina wannan asarar. Ganin da gaske bar musu dakin zasuyi yasa Waheedah fadin
"Abba dakun zauna... Kome zaice bazai canza komai ba... Takardata kawai nake so ku amsar min tunda ni na mishi magana yaki..."
Basu ce komai ba suka fita, ko karasa barin dakin Hajja batai ba, Abdulkadir ya bar inda yake zaune yana dawowa kusa da Waheedah ya tsugunna, hannu yasa yana tallabo fuskarta
"Me nayi miki da zafi haka Waheedah? Dan Allah me nayi miki haka? Hankalina kike son ganin ya tashi? Nutsuwata kike son rabani da ita? Duk kinyi nasara, wallahi kinyi nasara, kibari haka ki tashi mukoma gida... Idan ma kina so raina ya baci ne kamar yanda na bata miki rai duk ya faru..."
Saida hawaye suka zubo mata tukunna tasa hannuwanta tana zame nashi daga fuskarta, kallonta yake yana ganin kamanninta nata ne, amman gabaki daya yanayinta yasa ta zame mishi baquwa, bai taba sanin tana da wannan bangaren bama balle yai tunanin ganin shi wata rana.
"Aurenka nake so ka saukake mun"
Ta furta da wani irin yanayi daya sashi zama. Ko dai Waheedah nada aljanun da baisani bane sai yau, ko kuma watakila batasan yanda kalmanta suke mishi kamar ta watsa mishi garwashin wuta bane shisa
"You are hurting me...Waheedah dan Allah... Kiyi hakuri... Shikenan? Hakuri kike so in baki?"
Kalaman suka kwace mishi batare daya sani bama, kallon shi take, yaune rana ta farko a tsayin shekarun data sanshi da taji kalmar hakuri ta neman afuwa akan labban shi, sai dai zuciyarta kamar dutse take jinta, babu abinda hakurin shi ya motsa a kirjinta balle yai tasiri. Muryarta na rawa tace
"Ka sakeni... Shi nake so"
Ciwon kan da yake ta fama dashi yaji yana karuwa, ya kasa gane kanta, ko kadan ya kasa gane kanta balle yasan ta inda zai bullo ma abinda yake faruwa.
"Kinsan girman kalmar da kike fada? Kinsan babu kyau mace ta furta ma namiji kalaman nan?"
Duk da hawayen dake zubar mata saida murmushi ya kwace mata
"Zakafi kowa bada tabbacin naje islamiyya Sadauki, kaman yanda zan bayar akanka, an halarta mun neman sakina idan bazan iya zama dakai ba... Zan biyaka sadakinka karka damu..."
Ta karasa tana sa wata irin dariya kubce mishi, ya lallabata, yayi duk iya abinda zai iya, baisan me take son samu daga wajen shi haka data zabi wannan hanyar ba, mamakinta yake sosai, ance kana sanin halayen mutum fiye da ko yaushe idan zamantakewa ta aure ta hadaku, Waheedah nason karyata kowaye ya fara fadin kalaman, dan yanzun bazai iya bada shaida akan halayyarta ba, da wani yanayi a muryar shi yace
"Me kike so daga wajena?"
Dan in bayau ba, shi bai mata komai ba, wata rigima bata hadasu da zata zabi daga mishi hankali haka ba. A gajiye ta amsa shi da
"Sau nawa zan maimaita? Ka saukakemun auren ka"
Tashi yayi daga kasa yana komawa kan kujera, yaga alamar tashin hankalin shi take son yi, nata kuma babu yanda za'ai ya kwanta, baisan kalar wasan da takeyi dashi ba, amman zai biye mata harya gane kan wasan, sai yasan hanyar dazai bi yai nasara akanta.
"Ko meye yake fada miki zaki samu abinda kike nema yaudararki yake yi..."
Ya fada mata yana tabbatar da kalaman sun zauna mata, zaiga wanda ya isa yasa shi sakinta tunda igiyoyin a hannun shi suke.
"Abba..."
Waheedah ta kira idanuwanta cike da hawaye, zaman shi Abdulkadir ya gyara kan kujera yana jin shigowar su. Suka zazzauna banda Anty datai tsaye inda take kafin ta fita daga dakin. Kallon su Abba yayi, fuskar Abdulkadir tana tabbatar mishi basu cimma wata matsaya mai kyau ba, duk da yayi wannan addu'ar, bayason Abdulkadir ya rasa Waheedah din, amman ba za'a hadu dashi aci gaba da zaluntar marainiya ba. Baida karfin daukar zunuban nan kam.
"Abba ku fada mata, ni ban shirya rabuwa da ita ba... Ku fada mata"
Abdulkadir ya fadi yana kara gyara zaman shi, karyar hauka Waheedah take, aure yanzun yakejin ya fara yinshi da ita, dan bai amsa karbar aurenta a masallaci ba saida niyyar mutuwa ce kawai abinda zai raba igiyoyin da suka qulle su a ranar. Baiga meye zai canza wannan ba.
"Kaji shi ko Abba? Bazan iya komawa gidan shi ba nikam... Dan Allah ku bashi hakuri ya saukakemun..."
Waheedah ta fadi cikin tashin hankali, cikinta har yamutsawa yake da tunanin komawa gidan shi, karfinta ya gama karewa gabaki daya.
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Anty ta fadi, tana sa Abdulkadir juyawa ya kalleta
"Kifa daina salati tunda auren bai mutu ba, ba kuma mutuwar zaiyi ba"
Idanuwan Hajja a waje tace
"Abdulkadir..."
Ranshi a bace yake, sosai ranshi ya jima bai baci irin na yau ba
"Salatin me take yi to Hajja? Ni banma san me takeyi anan ba wallahi"
Abba ne ya kalle shi yana girgiza kai
"Ai ba zaka taba sake halin ka ba, ba zaka sake halinka ba Abdulkadir...ni bazan bata hakuri ba, Allah kadai yasan me take qunsa a zama dakai...tunda ta nemi ka bata takardata ai shikenan..."
Wata yar gajerar dariya Abdulkadir yayi da bata da alaqa da nishadi, yasan Abba ba sonshi yake wani yiba, ba tun yanzun ba, yanda ya goyi da bayan Waheedah bai bashi mamaki ba, baibi takan Anty ba, ra'ayinta ko abinda take tunani bashida muhimmanci a wajen shi. Hajja ya kalla da yake ganin hawaye cike da idanuwanta
"Abin nan baimun dadi ba sam...ni dai ko meye ya faru dan Allah kuyi hakuri, kuba abin kwana biyu tunda duk kun hau dokin zuciya... Idan kuka sauko sai ayi magana"
Kai Waheedah ta girgiza ma Hajja
"Ko an kwana biyu bazai canza wani abu ba...gara nidai yaban takardata yau, Abba zan mayar mishi da sadakin shi..."
Rai a bace Abdulkadir yake kallon ta
"Zakuma ki bani yarana..."
Wannan karin zuciyarta taji ta motsa, da karfin gaske, idanuwan shi ya tsayar cikin nata
"Ba Fajr kadai ba, har Ikram..."
Da wani irin tashin hankali take kallon shi
"Alhaji kana jinsu, a gabanka suke wannan rashin hankalin..."
Hajja ta karasa maganar wani hawayen bakin ciki na zubo mata.
"Kasan me kake fada Abdulkadir? Jaririyar kake cewa zata baka? Kayi yaya da ita to?"
Abba yake tambaya yana kallon shi
"Wallahi har ita saita bani, Abba kaji ita me take furta mun ai bakai magana ba, saini dan nace taban yarana zai zamana rashin hankali?"
Numfashi Abba ya sauke
"Karka kara batamun rai fiye da wanda nake ciki, banason furta wasu kalamai marassa dadi a kanka Abdulkadir, batun yanzun kake kure hakurina ba..."
Jikin shi Abdulkadir yake ji har bari yake saboda bacin rai, wani irin kallo ya watsa ma Waheedah da duk ita ta ja mishi wannan tijarar, ya kuma kudurta ranshi bazai baci shi kadai ba, tashin hankali take nema ta kuma samu, yaga alamun duka laifin komai suke so su dora mishi, da yayi wani abu mai girma ne ma ranshi bazai baci har haka ba, babu abinda yayi da za'ai saka shi a gaba haka.
"Abba nasan ba wani sona kake ba daman, ba tun yanzun ba nasani, amman duk da haka ya kamata aimun adalci, saika tambayeta idan na mata wani abu"
Da mamaki Abba yake kallon shi, cikin yaran shi zaice daga shi sai Waheedah yafi kula da lamurran su, yake kuma jin shaquwa taban mamaki dasu, Waheedah saboda hakuri da hankalinta, Abdulkadir saboda yawan kawo mishi karar shi da akan yi, da kuma zuciyar da Allah ya halitta mishi ta saurin fushi, yasa babu ranar da yake gidan da baya kiran shi dakin shi dan sulhunta tsakanin shi da wani a cikin gida, ko kuma yi mishi fada kan koyon hakuri, amman shi yau yaron zai kalla yace baya son shi, wanne kalar soyayya ce bai nuna ma Abdulkadir ba.
"Abdulkadir..."
Hajja ta kira, Abba na katse da
"Ki kyale shi Hajiya Furaira....ki kyale shi"
Mikewa Abdulkadir yayi yana kallon su gabaki daya
"Ni dai ku fada mata, zata bani yarana..."
Wannan karin hawayen da Waheedah taji ya zubo mata daga abinda yai saura mai motsi a zuciyarta ya fito, dan saida taja kafafuwanta tana hade su da jikinta ko zata samu sauqin ciwon da fitowarsu ya bar mata, idanuwanta ta sauke cikin nashi da suke fal da kwantanccen rikici, muryarta dauke da wani irin yanayi tace
"Wannan shine sharadin ka? Yarana kake son amfani dasu Sadauki? Shikenan...naji na dauka, ka saukakemun, ga Ikram nan bayan Anty ta baka ita, Fajr na cikin gida nake tunani saika dauke shi, Allahu ya rayasu cikin aminci..."
Anty da take tsaye batasan lokacin data juya tana nufar hanyar dakin baccin ta ba, dan wani kuka ne ya kwace mata, zuciyarta ta gama karyewa da abinda yake faruwa, Hajja ma mikewa tayo tana kallon Abba kamar shine sanadin komai tunda yaki musu magana, ba a gabanta zasuyi wannan rashin hankalin ba. Ficewa tayi daga falon, Abba ma mikewa yayi yana basu waje ganin kallon da suke ma juna da alama sunma manta basu kadai bane a dakin.
Tunda ta fara magana, yanayin muryarta yasa ko numfashin shi a hankali yake zarya, iskar wajen kanta tsaye Abdulkadir yaji tayi, kamar itama tana son tayashi mamakin Waheedah, dan ya tabbatar ba shi kadai yake mamaki ba, bazai hada yanda yake ganin soyayyar shi da ta yaransu a idanuwanta ba, tasha nuna mishi yanda yake da muhimmanci akan komai na rayuwarta, sai dai bai taba tunanin zata iya ce mishi ya dauki yaran dan ya rabata da auren shi ba, girgiza tayi kadan ya dora halin da yake ciki a yanzun, a cikin idanuwanta yake ganin yanda komai ya fara.
TUNA BAYA...!!!
*
Ya kuke ganin salon tafiyar? Sai naji ra'ayoyinku.
*#Abdulkadir*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732: ©️
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
04
Maballan rigar shi ta makaranta yake ballewa, yana saka hannu a aljihu ya ciro links dinshi, kasancewar rigar mai dogon hannu. Hajja ce ta fito daga daki tana kallon shi
"Dogo dan baban shi, sojan gidan Bugaje..."
Ta fadi da alamun zolaya, kayataccen murmushin da bako yaushe ake gani ba Abdulkadir yai mata. Yan gidan Bugaje suna da tsayi babu laifi daga mazan har matan, dan gajerun cikin gidan basu wuce su hudu ba, amman tsayin da Abdulkadir yake dashi har mamaki yake basu, duk manyan yayyen shi tsayinsu daya dashi, gashi lokacin banda ball da yake yi har motsa jiki yake zuwa, gidan kaf babu wanda baisan burin Abdulkadir shine zama soja ba. Tun yana da karancin shekaru yakan ce shi soja zai zama, tun suna daukar abin kuruciya harya fara tasawa yana cigaba da jaddada musu kaunar shi da aikin soja, ko a hanya yagan su sai yaje sun gaisa.
Ganin nasu baya mishi wahala tunda akwai barikin sojoji tanan kofar ruwa, ga abokan shi biyu Imran da Nawaf duka iyayen su sojojine, abinda ya kara danqon zumuntar su kenan da Abdulkadir.
"Hajja..."
Ya kira, sun gaisa daya dawo daga sallar asuba, shi bazai iya wannan wahalar ta sake sabuwar gaisuwa ba kuma.
"Har an shirya?"
Kai ya daga mata yana dorawa da
"Me kika dafa? Wai Mama koko fa tayi mana da safen nan..."
Dariya Hajja tayi, dan ita bata ma jima da tashi ba, ruwan shayi ta dora batajin ko tafasa yayi
"Sai dai in zaka sha shayi...ban jima da tashi ba nima..."
Daga ido yayi yana kallon agogon da yake dakin hadi da girgiza mata kai
"Naci wani abu idan na fita makaranta..."
Zahra ce ta shigo dakin tana saka Hijab dinta, bata kula da Abdulkadir da yake tsaye ba ta kuwa bangaje shi
"Subhanallah..."
Ta fadi tana jan hijab din ta saka ta dakyau, wani irin mari ya dauketa dashi da yasa Hajja karasawa tana riqo Zahra da ta fashe da kuka tana fadin
"Wallahi Hamma banganka ba..."
Kallon shi Hajja tayi
"Me yasa kake da saurin hannu ne haka Abdulkadir? Zata tureka ne idan taganka..."
Zame jikinta Zahra tayi daga rikon da Hajja tayi mata, kuka take sosai dan ta maru yanda ya kamata, Abdulkadir take kallo daya kafe idanuwan shi akanta yana qarasa saka link din dayan hannun rigar shi
"Ina kwana..."
Ta fadi muryarta can kasa, girar shi ya daga duka biyun
"Abdulkadir..."
Hajja ta kira, yi yayi kamar baiji me tace bama, hankalin shi na kan Zahra
"Ki saki ranki ki gaisheni, fada muke?"
Kai ta girgiza tana share hawayen ta, muryarta ta gyara tana sake fadin
"Ina kwana"
Murmushin gefen fuska yayi
"Kin tashi lafiya?"
Dakyar tace
"Lafiya kalau..."
Tukunna ta wuce daki, safa tazo ta dauka daman, dan girkin Mama ne duka suna dakinta zasu karya acan. Alhaji Ahmad Bugaje mutum ne tsayayye, ba zaka rasa rikici a gidanka ba koda mata daya ka ajiye, ballantana har hudu, sai dai suna kokarin duk wani rikici da zai faru a tsakanin su baya karasawa kunnuwan shi sai dole. Duk abinsu suna shakkar bacin ran shi, shisa aka samu wadataccen hadin kai a tsakanin yaran, dan suna son junansu sosai. Ko a makaranta babu wanda yake taba daya daga ciki, su dukan su zaka gani a saman kanka kaman kudan zuma. Girki a hade sukeyi, sai dai ko in kanason dafa wani dan abin ka dafa a dakinka. Amman duk mai girki zaiyi da duka yaran gidan a dakinshi zasuje suci abinci daga safe har zuwa dare.
Zahra na barin wajen, Abdulkadir ya juyo, fuskar shi a daqune yake kallon Hajja
"Kina mun fada a gaban ta, kina so su rainani ne Hajja? Ya zata shigo daki fuskarta lillibe da hijab? Meyasa ba zata tsaya ta saka ba tukunna ta shigo? Shine zakimun fada a gabanta..."
Hararshi Hajja tayi tana fadin
"Kai yanzun me kakeyi?"
Sake daquna fuska yayi
"Nidai bana so..."
Yace yana sa hannu ya dauki jakar shi ya saqalota yana rataya hadi da juyawa ya fice daga dakin. Harabar gidan ya fita inda babbar motar da ake kaisu makaranta gabaki dayansu take, shekara daya dai ta rage mishi ya gama makarantar nan ya huta da saka uniform, duk da ba wasu shekaru ne dashi ba, yana cikin ta goma sha bakwai ne, amman tsayin shi yasa ana tunanin ya girmi shekarun shi. Bakin motar ya tsaya, yasa hannu a aljihu ya ciro agogon shi, bakwai da kwata
"Duk yaran da yasa nayi latti sai naci uban shi wallahi"
Ya fadi a fili yana daura agogon, duk da shi yake rike da muqamin mai horar da dalibai na makarantar bazai hana principal dinsu yarfa shi gaban yara idan ya makara ba, duk da zai huce a kansu bayaso dai, duk wani abu dazai ja a ci mishi mutunci a gaban yara a makarantar yana guje mishi. Danma ba daliban da suke kasan shi ba, har yan ajinsu shakkar Abdulkadir suke, banda Imran da Nawaf babu mai tinkarar inda yake kai tsaye, dan su kadaine abokan shi nahar wajen makaranta, daman abokai hudu kacal gare shi, sauran biyun Anwar da Tijjani, unguwar su daya, islamiyyar su ma daya, duk tare suka tashi.
Amatullah,Nusaiba, Nabila da Kabir ya hango suna karasowa wajen.
"Ke kaman Hamma Abdulkadir ne tsaye fa..."
Nabila ta fadi, tana saka Nusaiba kallon wajen a firgice
"Inalillahi... Karfe nawa?"
Nusaiba ta tambaya, duk da tsiran sati biyune tsakaninta da Abdulkadir din, ajinsu daya ma a makaranta, amman hakan baya hanashi jibgarta. Babu mai agogo a cikinsu balle ya amsata. Sa'adatu kuwa kallon Kabir tayi
"Kabir dan Allah ce duk su fito..."
Juyawa Kabir din yayi da gudu, su kuma suka karaso wajen suna gaishe dashi a tsorace, amsawa yayi, da sauri suka shiga motar suka sami waje suna zama, Zahra ce ta fito itama, fuskarta a kumbure da kukan da tayi, ga shatin yan yatsun shi nan kwance saman fuskarta, ko da ta shiga motar babu wanda ya tambayeta, duk sunsan bazai wuce Abdulkadir ba. Ba kullum yake binsu a tafi makaranta haka ba, ranakun duk da yahau machine yai gaba abinshi ransu wasai, motar kamar zasu tasheta da hira, in kuwa yana ciki ba zakaji bakin kowa ba.
Kabir bangaren Mama ya nufa, duk suna falon nata, wasu na daura takalma, wasu na saka safa
"Wallahi Commander ya fito..."
Ya fadi yana dariya, Commander shine sunan da suka laqaba ma Abdulkadir din, suke kuma kiran shi dashi a bayan idon shi. Basu jira karin bayani ba da gudu suka kwasa, wani takalmi daya a hannu suna fita. Kusan a tare suka karasa suna maida numfashi
"Wanne rashin hankali ne wannan?"
Abdulkadir din ya tambaya yana kare musu kallo
"Ina kwana Hamma..."
Suka fadi kusan su dukan su, madadin tambayar dayai musu, tsaki kawai yaja yana bude gaban motar ya shiga. Suma soma shiga sukayi, tukunna Waheedah ta karaso wajen, hijabinta a hannu ko sakawa bata samu tayi ba. Gabaki dayansu Sheikh Bashir sukeyi. A bangaren Waheedah banda sunanta daya banbanta da nasu ko ita da kanta da ba zata taba sanin ba Alhaji Ahmad bane mahaifinta, balle kuma yan makarantar su, da rana daya bai taba nuna mata cewar bata fito daga jikin shi ba, kuma a cikin gidan ma babu wanda ya taba daga mata kai akan zaman agolancin da takeyi. Sai kuma kalarta ta banbanta data su, fara ce har shiga ido takeyi, sukan tsokaneta da cewar da taku daya ta gujema zuwa duniya a zabiya, duk da suma akwai fararen a cikin su.
Zata iya cewa ta fara sanin labarinta ya canza ne a ranar, lokacin tana aji uku a sakandire, a gaban motar tagan shi a zaune, duk da gefen fuskarshi tagani saida zuciyarta tai wata irin dokawa da batada alaqa da tsoron shi da kusan su dukansu sukeyi. Yanayine