Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   40 / 51

117K to 120K   out of 152.3K words

ce ikon Allah ne kawai zaisa ba zata kashe aurenta da na AbdulKadir ba, tunda farko ma bataga dalilin da zaisa ta dauki yarinya ta bashi ba, musamman mai sanyin hali irin na Waheedah. Numfashi Anty ta sauke

"Bansan me kikai ta bari a ranki har zuwa lokacin nan ba, ni bazan baki hakuri ba Waheedah, amman kije gida kiyi magana da Maminki, nasan kawaici ba zai barta furta komai ba, kije taga kina lafiya ba wai a waya ba"

Hannu Waheedah takai tana share hawayen da taji sun zubo mata. Cikin sanyin murya tace

"Idan gidan zaki koma bari mu wuce tare"

Kai Anty ta jinjina mata, ba gida zata koma ba, amman hidimarta zata jira, inta sauke Waheedah din saita sake fitowa. Hijab dinta ta dauko, sai jakar goyon Ikram din ta sakata a ciki tana goyata ta gaba ta tallabe, Fajr zata tasa Anty ta hanata, sabar yaron tayi a kafadarta, wayarta kawai Waheedah ta saka a jaka ta rike a hannu, mukullin da Hauwa ta bata na gidan guda daya, ko da zata fita ta dauka, sannan tabi bayan Anty. Kulle gidan tayin suka nufi motar Antyn, a cunkushe Waheedah takejin kanta da zuciyarta gabaki daya. Da tunani fal a kanta suka nufi gida.

Har suka karasa gida Waheedah batama sani ba, sai da taji Anty ta bude mata kofar motar ta bangarenta, saukowa tayi da Ikram tallabe a kirjinta. Fajr ya tashi bata ma sani ba, jakarta ta dauka tana ratayawa ta kama hannun shi, ko sallama bataiwa Anty ba ta wuce tana nufar bangaren su, Antyn ma mota ta koma ta fice daga gidan, zuciyarta cike da tunanin Waheedah din. Da sanyin jikinta ta karasa gida tana shiga da sallama, a falo ta samu Mami a zaune, Fajr kam bai bita ciki ba ya wuce bangaren Hajja, ita ma batabi ta kan shi ba. Sallama tayi tana cire takalmanta ta karasa, tunda Mami ta amsa ta taji idanuwan ta sun cika da hawaye.

Kan kujera ta zauna kusa da Mami tana sauko Ikram ta kwantar da ita a gefe, hijabinta ta cire, tana saka dan yatsa ta share kwallar da ta taru a gefen idanta, kallon ramar dake kasan idanuwanta Mami tayi, zatai karya idan tace bata kwana da yarinyar tana tashi da ita a rai, kwanakin nan yinsu kawai take badan suna mata dadi ba, duk da Yassar kullum da safe saiya kira ya hadata da Waheedah din sun gaisa, baccin kirki ma ba sosai take samun shi ba, haka takan raya daren da salloli tana yima Waheedahr addu'a.

"Waheedah..."

Mami ta kira tana rasa ta inda zata fara mata magana, maganar cewar bata taya Waheedah jin abinda Nuriyya tai mata ba baima taso ba, har kasan zuciyarta taji zafin abin, musamman ita da tafi kowa sanin yanda Waheedah ta dauki Nuriyyar, amman rayuwar haka take tafiya, wanda yafi kusa dakai shi yafi kowa samun damar cutar ka, yanzun mutanen kirki basu bane wanda zasu dauki abu su baka, mutanen kirki sune wanda zakuyi tarayya tare dasu basu cutar da kai ba. Auren da AbdulKadir din yayi bai saba addini ba, ya taka matakai da yawa na rashin kyautawa ne kawai a al'adance.

Taso yima Waheedah maganar sai tace mata

'Babu komai Mami, ya rigada ya faru, ki mana addu'a Allah yasa hakan alkhairi ne'

Duk da tabar zancen, wani abu a kasan ranta saida ya fada mata Waheedah na boye kishin da tasan yana damunta ne, ta kuma jima tana tsoron rana irin wannan. Tana kallon yanda Waheedah take kai hannu tana share kwallar da take tarar mata lokaci zuwa lokaci, numfashi Mami ta sauke

"Waheedah..."

Ta sake kira a tausashe, wannan karin kamar hakan Waheedah take jira wani irin kuka mai sauti ya kwace mata, jikin Mami ta kwanta tana kukan da takeji yana fitowa daga kasan zuciyarta inda yake mata ciwo na gaske. Kuka take da bata tabayin irin shi ba a rayuwarta, kukan ranar da AbdulKadir ya fada mata ya kara aure ta text saboda bai darajata ba, kukan ranar da ya shigo mata da kawarta, Nuriyya da ta dauka yar uwa a matsayin kishiya, kuka take da duk ranar da Nuriyya ta rike AbdulKadir din a gabanta, kuka take daya kamata tayi shi watanni takwas da suka wuce, ta jima tana rike da shi a ranta, yanzun da ta fara bata san ya zata daina ba, muryarta a karye cikin wani irin kuka ta dago daga jikin Mami tana fadin

"Ma... Mami duk mata... Duk matan garin Kano da inda aiki yake kai shi... Mami baiga kowa ba sai Nuriyya....me yasa Nuriyya?"

Waheedah ta karasa maganar tana kai hannu ta dafe kirjinta da yake wani irin ciwo kamar zai tsage. Kishi takeji har wani duhu-duhu take gani. Riketa kawai Mami tayi, tasan kukan ma Rahma ne, amman har ranta take jin shi, duk karfin hali irin nata hawaye takeji cike taf da idanuwanta, yanzun tagane kishi ne yake cin 'yar tata

"Kuma Nuriyya ta aure shi, ni bazan taba mata haka ba, bai haramta ba, amman bazan auri mijinta ba...me yasa zata auri nawa? Mijina Mami, Sadauki ta gani duk fadin Kano...."

Waheedah take fadi batare data sani ba, dan yanda take maganar tana wani irin kuka kasan ba a cikin hayyacinta take ba, sosai take kuka tana sambatun da ba zatace ga daga inda suke fitowa ba, riketa kawai Mami tayi tana jijjigata kamar karamar yarinya. A jikin Mamin tayi kuka har bacci ya dauketa, banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, a hankali Mami ta zame Waheedah kan kujerar tana dauke mata Ikram. Bacci tayi har azahar, lokacin da ta tashi wani irin zazzabi ya rufe ta ruf, dakyar taja jiki ta wuce dakin Mami tayi alwala, sai da taba Ikram tasha dan duk hakurin yarinyar harta fara kuka, tukunna ta samu tayi sallah.

Duk yanda Mami ta lallabata kasa cin abinci tayi, shayi ta hada ta samu tasha rabin kofi, da idanuwa Mami take binta duk inda tayi, har saida ta gama jijjiga Ikram tayi bacci, Mami ta karbeta ta saka zani ta goyata. Waheedah din na zaune kan kujera, tanajin kamar ta shige ciki dan gujema magana da Mami din. Cikin sanyin murya Mami tace

"Na dauki ido na saka miki ne tun farko saboda nayi tunanin in har kina da matsala ina da kusancin da zaki sameni da ita. Bazance miki hakuri ba abu bane me kyau, duk da akan ce idan yayi yawa yana zama cuta. Babu inda hakuri yake yawa, a zamantakewa ta yau da kullum, ko a zamantakewa ta aure, musamman ma ta aure..."

Gyara zama Waheedah tayi, tanajin yanda hawaye suka cika mata idanuwa, magana Mami ta cigaba dayi

"Ba hakuri bane yake yawa ya zama cuta, rashin yafiya ne, akwai banbanci tsakanin ai maka abu ka hakura bakace komai ba, da ai maka abu ka hakura ka yafe. Yafiyar itace take saka duk yawan lokuttan da kai hakuri kake samun riba, idan har zaka hakura ba zakayi magana ba kabar abin a ranka bashida wani amfani, gara ka fito da shi kawai..."

Mami ta karasa maganar tana sake sauke muryarta da fadin

"AbdulKadir halin shine ya fito fili, shisa babu wanda ya tambayeshi me ya faru, babu ma wanda yai tunanin yaji nashi uzurin, kowa laifi ya dauka ya dora mishi. A karo na farko koya dace ko bai dace ba Waheedah, ko da za'a ce nayi son kai zan fadi raina ya sosu da auren Nuriyya da AbdulKadir yayi, bai taka addini ba, amman banji dadi ba ko kadan, saboda halin da zaki shiga nayi tunani"

Wannan karin Waheedah bata koyi kokarin share hawayen dake zubar mata ba, yanda muryar Mami take a karye kawai na kara taba zuciyarta, ita kanta Mamin kokarin tarbe hawayen da suke ta mata barazana take, yanayin Waheedah din na gwada karfin zuciyar ta fiye da yanda ta zata.

"Mutuwar aure tafi yin shi wahala, duk yanda ake ganin da kalamai kawai za'a yita. Ban taba ganin inda uwa taso mutuwar auren yarta ba Waheedah, ko ya kaddara ta rubuto hakan, ni shawara kawai zan baki a wannan matakin, bazanyi kokarin haramta miki abinda addini ya halarta miki ba, abu daya zance miki, kiyi magana da AbdulKadir..."

Kai Waheedah take girgiza ma Mami wasu sabbin hawayen na zubar mata, har ranta tagaji da auren shi, tanajin idan ta koma komai zai iya faruwa, ciki harda tarwatsewar zuciyarta, ba zata iya daukar wani ciwon bayan wanda taita dauka ba

"Wallahi Mami nagaji, nagaji har raina..."

Waheedah ta fadi cikin kuka, kai Mami ta jinjina mata

"Bance wani abu ba nima, kiyi magana da shi, magana ta fahimta, lokutta da dama aure kan samu tangarda ne saboda rashin tattauna matsala har a samu maslaha, kowa naganin laifin dan uwan shine, babu kuma wanda yake kokarin sauke girman kai ya saurari dayan har a gano bakin zaren, ki fada mishi matsalar ki, ki saurari uzurin shi"

Shiru Waheedah tayi tana share kwalla

"Kina jina?"

Mami ta fadi, kai kawai Waheedah ta iya daga mata, tana sake shigewa cikin kujera. Numfashi Mami ta sauke, komai baya mata dadi sam, kitchen ta wuce badan tana da wani abu mai muhimmanci da zatayi a ciki ba, sai dan inta ci gaba da kallon Waheedah din hawayen da take ta boyewa ne zasu zubo. Duk wannan kishin da yake nuqurqusarta, da gajiyar da take fadin tayi, zaka fahimci yanda rabuwa da AbdulKadir shine karshen abinda take son yi...!

#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#LubnaSufyan
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43

*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*

28

Cikin baccin da baisan lokacin daya dauke shi ba yaji wayar shi na ruri, idanuwan shi a rufe ya lalubota, har kiran ya yanke, numfashi ya sauke yana dora wayar a kirjin shi hadi da gyara kwanciya. Wani rurin yaji wayar ta sake dauka, dakyar ya bude idanuwan shi yana ganin Nuriyya ce, dagawa yayi ya kara a kunne batare da yace komai ba

"Masoyi..."

Ta kira ta dayan bangaren, shirun AbdulKadir ya sakeyi, sosai ta bata mishi rai, Waheedah ce a tunanin shi da komai shisa baiyi lokacinta ba har yanzun

"Hello..."

Ta sake fadi, muryar shi can kasan makoshi cike da bacci yace

"Ina jin ki"

Ya lumshe idanuwan shi da suke mishi yaji saboda bacci

"Naga baka dawo ba har yanzun... Dan Allah kayi hakuri..."

Ta karasa maganar muryar ta na karyewa

"Ina gida ni tun dazun"

Cewar AbdulKadir din yana ganin rashin hankalin Nuriyya da zatayi tunanin dan ta bata mishi rai zai tafi wani wajen, a lokaci daya kuma yana ganin yanda har yanzun bata san wa take aure ba, jin tayi shiru yasa shi fadin

"Kiyi bacci, sai da safe"

Kafin tace wani abu ya kashe wayar shi. Bai taba zaton akwai ranar da matar shi zata bata mishi rai harya raba shimfida da ita ba, duk fadan da zaiyi da Waheedah in dai suna gida daya a jikin shi take bacci, ko baya mata magana kuwa. Numfashi yaja yana sauke shi, kirjin shi zafi yake sosai, tunanin Waheedah din yanzun ya kara taso mishi da wata irin kewarta. Wayar shi ya duba yana ganin karfe sha daya na dare, karamin tsaki yaja, dare ma baiyi ba sosai, ga baccin gabaki daya yabar idanuwan shi.

Lambar Waheedah ya kira a kashe

"Dan Allah ki kunna wayarki, ba sai kin daga ba Wahee, ko ringing din naji a kunne na zan dan samu nutsuwa"

AbdulKadir ya fadi yana sake gwada kiran wayar, a kashen dai ya sake ji, tashi zaune yayi ya jingina bayan shi da jikin gadon. Dayan pillow din ya dauka yana dora shi kan cinyar shi. Bude wajen text yayi yana rasa abinda zaice mata, ko da can kalaman shi taqaitattu ne, balle yanzun kuma. Fasa tura mata yayi yana scrolling can sama, tsofin sakunanta ya dinga karantawa, duk yawan da suke dashi sai yaga sun kare mishi da wuri, WhatsApp ya koma yana jin dadin yanda baya goge chat, dan lokutta da dama ita take goge mishi in ta dauki wayar, sai tace yana cika waje.

Danma ya hanata goge mishi nasu, tunda idan yana wajen da babu network su din yake karantawa suna rage mishi kewarta. Lokacin da yabi duk wani text dinsu ya gama karantawa karfe biyu saura. Duniyar yakeji ta mishi wani irin fadi, ga kadaici naban mamaki daya lullubeshi, da yanajin nutsuwa sallah zaiyi har gari ya waye, amman bashida wannan nutsuwar. Saukowa yayi daga kan gadon yana fita daga dakin zuwa bangaren Nuriyya. Bacci ya samu tanayi hankalinta a kwance, shi yace tayi bacci da kan shi, baisan me yasa baccin ya bata mishi rai ba

'Kin batamun rai, bana tare dake shine kikayi bacci kika barni'

AbdulKadir ya fadi a ran shi yana girgiza kai, bandaki ya wuce ya watsa ruwa. A rayuwar shi baya hada wani da wani, hakan na cikin abinda bayaso sam, ko fada Hajja take mishi ran shi yana baci yaji tana kwatanta shi da wani. A wajen shi Allah ya halicci mutane daban-daban mabanbanta halaye da ra'ayoyi, har kamanni ma, wanda Allah ya halitta yan biyu sukazo da kamanni daya, suka kwanta a ciki daya ma saika sami halayensu daban.

Sai gashi yanzun daya fito ya tsinci kan shi da hada halin Nuriyya da na Waheedah a waje daya yana aunawa, Waheedah ba zata taba bacci tabarshi ba, ko da shi ya bata mata rai, a yanda zata dinga kallon shi da idanuwanta kawai zaka gane babu nutsuwa a tattare da ita.

'Na baka hakuri fa Sadauki, kai mun magana dan Allah, wallahi a takure nake jina, ni banason yin fada da kai'

Kalamanta suka dawo mishi

'Hamma har yanzu fushi kake mun? Babba da hakuri aka san shi'

Takance, duk idan tayi amfani da Hamma to ya kwana yana mata fushi, ko tana son tambayar shi unguwa, zatace shifa Yayanta ne. Murmushi yaji ya kwace mishi, kafin kirjin shi ya sake amsawa kamar zai bude, har zazzabin rashinta a kusa dashi yake ji. Sai da ya sake komawa bangarenta ya sakko gajeran wando da singlet tukunna ya dawo dakin Nuriyya din, baccin da take zai hana mata, tunda shi ya kasa, kuma bayajin tunanin Waheedah zai barshi ya samu.

*

Da safe dakyar Nuriyya ta tashi sallar asuba, tana ta turo baki saboda baccin dake idanuwanta, bata kwanta da wuri ba, idan tace dan bai dawo bane karya take, kallo takeyi a system dinta suka dauke wuta, bata tuna dashi ba sai da chargyn system din ya kare, kudine ta riga ta kashe, fada ne zaiyi ya gama. Ita ko kadan batama hango zai mata fada akan dubu arba'in ba, yanda take ganin kudin shi, yafi karfin dubu arba'in, idan nashi ran ya baci itama natan a bace yake.

Data kirama yace tayi bacci tana kashe wayar guntun tsaki taja ta ajiye ta kwanta, daman ko baice ba baccinta zatayi. Dan tunda harya dawo daga ko ina Major ya kaishi bai mata fada ba wani abu ya nutsu a ranta. Batajin akwai wani babban abu da zatayi mishi kuma da zai kai wannan, iya kacin shi fada, duk da fadan na tsaya mata a rai, in yayi yagama shikenan. Ta kula bashida riko, da wahala ya kwana yana fushi kan abu daya. Tana idar da sallah ta janyo wayarta, chajin taga saura goma, dan ta manta ta saka sanda aka kawo wuta. Haka kawai tunanin azumi da saura kwana biyu ya diro mata, wayar AbdulKadir din da take kan drawer din gado ta janyo, ta saka sunan Waheedah a cike taga bai bude ba.

Tasan dai duk password din shi baya wuce sunanta, dan waccen wayar daya sake haka password din yake, har wani daci-daci take ji duk idan ta dauki wayar shi, shisa yanzun taji zuciyarta tayi wani tsalle da tunanin ko sunanta ya saka, jikinta har bari yake lokacin da ta saka sunanta, sai taga wayar bata bude ba, kamar daga sama taji sallamar shi yana dorawa da

"Me kike mun da waya?"

A dan tsorace ta daga kai tana sauke idanuwanta cikin nashi daya kankance mata

"Bakomai, zan duba abune, nama kasa budewa kuma"

Gira daya AbdulKadir ya daga mata dan baiga abinda ta ajiye a wayar shi da zata duba ba, hakan ta kula dashi yasa ta dora da fadin

"Hotuna zan kalla fa, wayata babu chaji, ban saka ba na manta"

Karasawa AbdulKadir yayi yana hawa gadon

"Ko gaisheni bakiyi ba kike son cinyemun chajin waya"

Murmushi Nuriyya tayi mishi tana matsawa sosai ta kama hannun shi

"Ina kwana"

Kankance mata idanuwa AbdulKadir yayi

"Waheena"

Ya fadi yana zare hannun shi daga cikin nata yaja kafafuwan shi ya hau dasu kan gadon, cike da rashin fahimta

"Password din"

Ya fadi yana kwanciya ya lumshe idanuwan shi, Nuriyya tabi shi da kallo yanda yake shirin komawa bacci kamar bai fada mata abinda taji dacin shi ya taso daga kasan zuciyarta zuwa makoshinta ba. Har wani hucin bacin rai takeji kamar kububuwa, AbdulKadir kuwa baccin shi ya koma, yana barin Nuriyya nan zaune ranta in yai dubu a bace yake. Dan kamar ba zata bude wayar ba, kafin ta yanke hukuncin Waheedah ba zata hanata latsa wayar AbdulKadir din ba, tunda yanda takejin mijinta ne itama haka takeji. Kuma tana so ta shiga messages din shi harna whatsapp taga ko yaushe Waheedah zata dawo.

Wani malolon takaici ya sake taso mata, ganin saita kara saka wani password din tukunna zata iya gani, gashi lambobine wannan karin, hakura tayi tana shiga wajen kira taga ko yayi magana da Waheedah.

'Matar Sadauki'

Sunan farko data fara cin karo dashi a jerin wajen kiran wayar AbdulKadir yaso wanke mata bacin ran da takeji, kafin ta kula da kiran fita yayi ba shigowa ba, tana kuma ganin

'Nuri'

Daga kasa, wannan karin wani irin tsakine ya kwace mata, fita tayi tana kara kula da wallpaper din AbdulKadir din, hoton Fajr ne daya sata jin son samun nata yaron taso mata yana zuwa mata wuya, ba sosai takanyi tunanin samun ciki ba, amman duk idan taga giccin Fajr tanajin kamar ace yaron nata ne. Kulle wayar tayi zata ajiye taga hoton dake fitowa idan an kulle waya kunshine, daga yatsun ta gane hannun Waheedah ne. A gefen AbdulKadir ta ajiye wayar tana addu'ar ya mirgino ya dora mata nauyi screen din ya samu matsala ko zai rage mata takaicin da take ciki.

Mikewa tayi ta cire hijabinta, kan gadon tahau daga can karshe ta kwanta, banda tafasa babu abinda ranta yake, kafin ta matso

40 / 51