Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
nan ya kula da idan ya ajiye kudi a wallet tana kwashewa ba, ko yazo yin kwana biyu, indai zai mata nata kwana dayan saita dibar mishi kudi. Idanuwa ya dauka ya saka mata yaga gudun ruwanta, yanzun ne ta gama kawo mishi wuya.
"Mu me zamu ci?"
Nuriyya ta bukata muryarta a sanyaye, dan sosai ta saka ranta a abinda Waheedah din ta girka. Sai takejin da wahala ta iya cin taliyar da ta dafa
"Ke ba mace bace? Baki dafa naki bane?"
AbdulKadir din ya bukata yana tsareta da idanuwa, duk da maganganun shi sun mata zafi, murmushi ta danyi
"Na dafa mana taliya"
Baice mata komai ba, ganin hakan yasata mikewa ta samu plate ta zubo musu taliyar, har miyar ta hade. Tare sukaci, AbdulKadir na rasa ranshi da yake a bace ne, ko taliya ce da bai cika so ba, ko kuma girkin ne bashida gabas, dan ko gishiri-gishiri na miyar ma baiji ba, sai wani daci-daci. Turawa kawai yayi, ita kanta Nuriyya da tana da wani zabi sam ba zata ci taliyar nan ba, sa ma ranta cin girkin Waheedah da tayi yasa taliyar kara fitar mata daga rai. Tana kai kwanon kitchen dakin baccinta ta wuce, ta dauki wayar ta. Tallar littafin Hauwa A Usman Jiddarh tagani na Saki Reshe, tana tunanin sarkakkiyar da take ciki na yanda za'ayi jarumin ya kasance gagarumin dan fashi.
Ba'a kai da fara shi ba, hakan yasata jan dan karamin tsaki, daman jiya littafin Fadime na Bingel ta maimaita dan sosai takejin dadin littafin, soyayyar da aka shimfida ciki na tuna mata dalilin da yasa ta auri AbdulKadir tun da farko, amman yanzun ta fara gajiya dan taci karo da abinda bashi take tsammani ba. Ganin babu abinda zata karanta yasa ta dauko system din ta, daman tana lallaba fina-finan da take dasune, tana budewa sai ga AbdulKadir ya shigo dakin, karasawa yayi kan gadon yahau yana saka hannu yaja system din
"Masoyi..."
Ta fadi tana kallon shi, bai mata magana ba yasa hannu yana kashe system din dauketa daga kan gadon gabaki daya ya dora kan drawer din da take gefen shi ya juyo yana tsura mata kananun idanuwan shi da suka sata yin shiru
"Ki kashe mana wuta"
Ya fadi, dan makunnin ba'ayi shi a kusa da gado ba, mikewa Nuriyya tayi tana zuwa ta kashe wutar ta dawo ta kwanta itama, sai dai ga mamakinta, juya mata baya AbdulKadir yayi da alamun bacci zaiyi. Wani abu taji yai mata tsaye a makoshi, batason ya sauke mata fadan shi, shisa ta hakura bata dauki system din ba, wayarta taci gaba da dannawa, tana ganin yanda status din kowa ya gauraye da maganar ganin wata
"Anga wata"
Ta fadi, AbdulKadir ya jita, surutunne ba zaiyi da ita ba yau, asalima niyyar azumi ya daura a zuciyar shi, sake gyara kwanciya yayi yana fuskarta, wayar da take hannunta ya fisge yana sakata a key ya ajiye a tsakiyarsu tare da fadin
"Ki kwanta Nuriyya"
Muryarta can kasan makoshi tace
"Banajin bacci wallahi, bakasan baccin da na sha ba yau daka fita"
Shisa bata neme shi ba, baccin ta yafi jin inda yake muhimmanci. AbdulKadir ya fadi a ran shi, zuciyar shi na kara jagulewa
"Bazan sake magana ba..."
Cewar AbdulKadir din cikin iko da gadarar shi da take bata mata rai. Gyara kwanciya tayi, ranta in yayi dubu a bace yake, batasan iya lokacin data dauka a haka ba har bacci ya dauketa itama. Su dukkan su baccin suke, shi AbdulKadir baccin daya kwana biyu baiyi bane ba, ita kuma Nuriyya baccin da batayi da wuri bane, ko ma da wurin ta kwanta shi yake tashinta sallar asuba, inba haka ba sai dai ta makara, dan in baya gari makara takeyi. Hakan yasa ko kiran sallar farko basuji ba, sunata bacci har karfe shidda saura.
Haske AbdulKadir yagani cikin idanuwan shi, kasancewar window din dakin baccin Nuriyya din daga waje yake, duk da wanda yake waje ba zai iya hango su ba, su da suke ciki zasu iya hango shi, haka gilashin window din yake. Amman bai hana hasken da yake nuna alamar gari ya waye shigowa ba. Murza idanuwanshi yayi da hannu yana kara runtsa su, kafin ya bude su cikin tashin hankali yana mikewa zaune babu shiri, hasken da yagani cikin dakin bai saka shi ya yarda ba, saida ya dauki wayar Nuriyya da take gefen shi ya danna, yana ganin shidda saura minti goma.
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
AbdulKadir ya furta yana kai hannu ya jijjiga Nuriyya
"Ki tashi mun makara"
Ya fadi yana hasaso kalar yunwar da zaiji a yinin yau, dan shi azumi baiyi suhoor ba rayuwar shi na cikin tashin hankali.
"Nuriyya..."
AbdulKadir ya kira yana bubbugata, idanuwanta ta bude dakyar tanayin mika
"Dilla ki tashi karfe shidda fa"
Wata irin mikewa Nuriyya tayi tana kallon shi
"Karfe shidda? Shidda fa? Bamuyi Suhoor ba, baka tasheni ba"
Wani irin kallo AbdulKadir ya watsa mata yana jan tsaki
"Ban tasheki ba? Bake ya kamata ki tashi ba, ki dafa mana abinda zamuci, nine zan tasheki?"
Shagwabe fuska tayi, tanajin idanuwanta na cika da hawayen bakin ciki, duk yanda sukai zaman rashin mutunci da Anas yana tashinta lokacin azumi, tunda yaga randa batai suhoor ba ta zama abin tausayi, a kwance ta wuni shame-shame. Shine AbdulKadir zai sauke mata fada kamar akwai inda aka rubuta cewar ita ya kamata ta tashe shi dole dole.
"Kaima idan ka tasheni ai ba wani abu bane Masoyi"
Ta fadi wani abu na tokare mata wuya, kankance idanuwan shi AbdulKadir yayi
"Magana zaki fadamun?"
Ya bukata cike da neman ta furta wani abu ya sauke mata fadan shi, kai ta girgiza a hankali, hawayenta na kara taruwa, qwafa yayi yana sauka daga kan gadon ya wuce bandaki, abin na hade mishi waje daya, ga bakin cikin rashin suhoor ga asuba daya rasa, ga Nuriyya da zatai mishi kukan rashin dalili. Saida yadan watsa ruwa a gaggauce tukunna yayi alwala ya fito, bama shida kaya a dakin nata, dole sai yaje bangaren Waheedah. Nuriyya ya kalla da bata ko nuna alamar tashi ba
"Ke ba zakiyi sallah ba?"
Kafafuwanta ta sauko daga kan gadon
"Ba zakiyi wanki ba kuma? Bandakin ki baya shigar miki ido, me yasa bakya wankewa ne? Dakyar nayi wanka a ciki"
AbdulKadir ya karasa yana wucewa ta fice daga dakin. Wannan karin hawayen ta taji sun zubo. Wani malolon bakin ciki na tokare mata kirji, a haka ta dauro alwala ta dawo ta gabatar da sallar asuba. Tana idarwa ta koma bandakin, tasa tsintsiyar da take a ciki ta wanke shi sama-sama, ko omo bata saka ba. Ba zata fara karar da karfinta a bandaki tun yanzun ba, dan wani sharri ma, cikinta harya fara murdawa da alamar yunwa. Wani zaninta ta dauka ta hada duka kayan wankin da suke cikin bandakin ta kulle su, ta dawo ta cire zanin gadonta dan yayi dauda sosai shima takai bandaki ta ajiye akan wancen kayan wankin, zata fitar dasu tunda Waheedah ta dawo.
*
AbdulKadir kuwa dakin Waheedah ya wuce yana turawa wani kamshi ya cika mishi hanci, dakin a gyare yake tsaf. Ta sake zanin gado, ko ina tsaf tsaf, tana zaune kan gado ta mike kafafuwanta, ta goya Ikram ta gaba tana kwance akan kirjinta, hannunta daye rike da Qur'ani. Ba zaice ga kalar dinkin jikinta ta yanda take zaune ba, amman atamfa ce, ta daura dankwalin atamfar, fuskarta fayau babu kwalliya. Amman ta mishi kyau har zuciyar shi dokawa take. Sai da ta idar da ayar da take kan karantawa, tukunna ta dago idanuwa ta sauke su kan AbdulKadir din
"Ina kwana"
Ta furta cikin sanyin muryarta tana dan mishi murmushin da yaji zuciyar shi ta dan nutsu
"Wahee... Ya kuka tashi?"
Dan langabar da kai tayi
"Alhamdulillah..."
Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance mata
"Shine baki tashe mu ba? Mun makara, yanzun fa muka tashi, ko sallah banyi ba"
Ware mishi idanuwa Waheedah tayi, ita ba Suhoor takeyi ba, sai dai inta tashi tayi brush tasha ruwa, in tana da kankana ta dan sha dan samun ladan suhoor din, ko taci dabino wasu lokuttan, yau dinma hakan tayi. Zatai karya idan tace batayi tunanin duba ko AbdulKadir din ya tashi ba, tunda tasan yanda yake wahala idan baiyi suhoor ba, kawai dai ta tsinci kanta da share koma meye yake son yin tasiri a kanta
"Na dauka kun tashi, kasan ni ba Suhoor nake ba"
Kai kawai AbdulKadir din ya iya jinjina mata, ba sai ta fada mishi ba, yasan fushin da takeyi dashi ne, koya tashi Waheedah zata kara kiran wayar shi ta tabbatar da hakan, wahala take son yasha, kuma zai shata din yau ya sani. Kaya ya wuce ya dauka, yana ganin yanda Waheedah batace ya bari ta dauko mishi ba
"Ka dauki na kwana biyu ka wuce dasu Sadauki, inka dauki kaya kaje dasu bangarenta ka cire acan kabar mata acan, karka dawo mun dasu nan dan Allah"
Ta karashe maganar da rokon shi kamar yana da wani zabi
"Ki zo ki dauko mun to"
AbdulKadir yace kamar karamin yaro, Qur'anin ta ajiye tana tallabe Ikram ta sauko daga kan gado, kaya ta dauko mishi, riguna da gajerun wanduna, harda na ciki kala bibbiyu, tunda shi ba manyan kaya yake sakawa ba, yana dasu, in tayi magana kan ya saka bakinta ne zai tsini, ba zaisa ba, bayason manyan kaya. Hannun shi ta dago tana saka kayan a ciki, tayi mishi murmushi har hakoranta suka fito, idanuwa AbdulKadir ya kankance mata
"Ko turare baki fesa mun ba"
Kallon shi tayi
"Bafa kayi sallah ba, lokaci na wucewa kuma"
Wani irin shagwabe mata fuska yayi, ta wuce tana komawa tayi zamanta, tana daukar Qur'ani taci gaba da karantawa a bayyane da muryar data tsaya dai-dai kunnuwanta. Da kan shi yaje wajen mudubinta yana daukar turaruka ya feshe kayan dashi, ko inda yake ma Waheedah bata kalla ba, balle yai tunanin zatai mishi magana. Harya gama ya fice daga dakin, ta sauke numfashi tana cigaba da karatunta. Ko da ta idar, bata fita ba sai wajen karfe goma, da Ikram ta fita karta ajiyeta ta farka taita kuka dan wanki zatayi kafin su dauke wutar su.
Sai da ta fara share dakin wankin tukunna ta koma dakinta ta dauko jakar da suka dawo da ita da. Tana cikin firfito da kayyakin wankin sai ganin Nuriyya tayi kamar mikiya, ta diro dakin wankin, da katon zanin gado da alamar kayan wankine a ciki
"Lafiya?"
Waheedah ta tambaya tana tsare Nuriyya da idanuwa cikin yanayin da yasa Nuriyyar jin duk ta daburce, Waheedah din na mata wani irin kwarjini naban mamaki, dan ko babu fara'a a fuskarta bata hade girar sama da ta kasa haka.
"Ina kwana"
Nuriyya ta fadi saboda ta rasa abinda zatace kafin tayi saurin dorawa da
"Ya jiki?"
Sai da Waheedah ta kalleta na wasu dakika, tana sata jin duk ta tsargu, kafin ta amsa da
"Lafiya"
Tana cigaba da hidimarta, tsaye Nuriyya tayi mamaki duk ya gama cikata. Kayan wankin ta ajiye tana juyawa ta fice daga dakin. Wankin ta Waheedah tayi dan bashida yawa, ta kwashe ta zuba a wata babbar roba, Ikram tazo ta kwantar akan doguwar kujera tana saka pillow din ta tareta, dan yarinyar ta cika juye-juye, karta fado. Tukunna ta koma ta dauki robar ta fita bayan gidan inda igiyoyin shanya suke, ta shaya kayan ta dawo. Wanda Nuriyya ta ajiye ta kwashe tanajin nauyin shi, bangaren Nuriyyan da tunda ta shigo gidan zata kirga lokacin da kafafuwanta suka taka ta nufa, a tsakiyar falo ta ajiye mata kayan tana juyawa, dakin wankinta ta janyo ta saka mukulli ta rufe ta dauki Ikram suna shigewa ciki.
Nuriyya kuwa fitowa tayi dan ta kawo wata hijab da tagani da datti, taci karo da jibgin kaya ajiye a falo. Tsaye tayi turus tana kallon kayan cike da mamaki, ba rashin lafiya bace take damun Waheedah, wani hali na banza ne ta dauka da ba nata ba, dan bata santa dashi ba. Ranta a bala'in bace ta dibi kayan wankin tana komawa dasu ciki ta ajiye a tsakiyar bandakin, itama tana da injin wankin ai, bawai bata dashi bane ba, kitchen ta koma ta dauko ledar omo ta dawo tana kallon AbdulKadir da yake a kwance yana danna waya
"Masoyi..."
Ta kira shi muryarta na fitowa a karye, hakan yasa shi dago idanuwan shi ya kalleta
"Ya ake amfanin da abin nan?"
Dakuna mata fuskar shi yayi
"Wanne abu?"
Ya tambaya, yana sa kunya ta rufeta, dan ta tsani ace duk irin wannan abubuwan na gayu ita bata iya ba, muryarta can kasan makoshi tace
"Na wanki"
Mikewa zaune AbdulKadir yayi yana kallonta cike da rashin fahimta, hakan na sata sake fadin
"Injin wankin, ya ake amfani da shi"
Har lokacin kallon ta AbdulKadir yakeyi
"Da ina kikaje da kayan? Ba naga kin fita dasu ba"
Maganar shi nasa ranta kara baci
"Bangaren Waheedah..."
Ta amsa a taqaice tana kin mishi bayani, wannan karin fuskar shi ce dauke da tsantsar mamaki
"Me kike nufi da bangaren Waheedah?"
Kanta ta saddar kasa ganin irin kallon da AbdulKadir din yake mata
"Ita kika kai tayi miki wankin saboda baki da hankali?"
AbdulKadir yake fadi yanajin ranshi na kara baci fiye da yanda yake a bace, dan bai taba ganin irin wannan rashin hankalin ba, shisa ya sai mata nata injin wankin itama, yanda ma ba sai taje bangaren Waheedah din ba gabaki daya akan maganar wanki. Yana daukar abubuwa da yawa a rayuwar shi amman bayason raini
"Ajiyeta kikai da zaki kai mata wanki Nuriyya?"
Kanta ta kara saddarwa, hawaye na tarar mata cikin idanuwa a karo na biyu daga wayewar garin yau, ko kadan bata saba a sakata a gaba ana mata fada ba, ko a gida daman Baba ne yake mata fada in tayi wani abin, to sai tayi abu goma, Mama bata fada mishi ba. Ranta baci yake yi duk idan akai mata fada, balle kuma yanzun da take jin tayi girman da duk wannan abubuwan bai kamata ana mata su ba, ranta a bace tace
"Karka ce haka..."
Tunda shi ba zama yake gidan ba, kuma Waheedah din na wanke mata da, bai sani bane ba
"Dama can nake kaiwa, yaune kawai ta dawo dashi"
Sosai AbdulKadir yake kallon ta
"Wankin kike dauka daga nan, sai ki kai bangaren ta, sai ta wanke miki?"
Yayi tambayar yana saka Nuriyya jin kamar tayi wani laifine, wata yar dariya AbdulKadir yayi da ko kadan batada alaka da nishadi kafin ya sauko daga kan gado yana ficewa daga dakin ya doko kofar kamar zai karyata. Bangaren Waheedah ya nufa ko sallama baiyi ba yanda ya tura dakin yasa ta bude idanuwanta daga baccin daya soma fisgarta
"Wanki kike ma Nuriyya? Akan wanne dalili?"
Ya bukata yanajin yanda ranshi yakai koluluwa wajen baci
"Baka taba kula ba sai yanzun?"
Waheedah ta bukata a sanyaye, dan yana gidan Nuriyya take kwaso wankin ta kawo mata bangarenta, shisa ta dauka yasani.
"Karki amsa mun tambaya da tambaya, karki kara batamun rai Wallahi"
Yanda yai maganar da yanayin fuskar shi yasata sauke idanuwanta daga cikin nashi, akwai yanayin da tasan ba zata fara gwada hakurin shi a cikin su ba, yanzun na daya daga cikin su
"Ko ban sai mata engine wanki ba, akan wanne dalili zakiyi mata wanki? Ajiyeki tayi?"
Numfashi Waheedah ta sauke
"Ina azumi nikam"
Kankance mata idanuwa tayi
"Ni nace miki bana azumin ne?"
Kai ta girgiza mishi a hankali, tana jin murmushin da yake shirin kwace mata, tayi kewar rikicin shi
"Allah ya baka hakuri Sadauki, yanzun ai zata wanke abinta kaga, kuma menene dan na hada na wanke?"
Kallon da yai mata yasa ta yin murmushi
"Yi hakuri"
Tsaki kawai AbdulKadir yaja yana ficewa daga dakin, su duka biyun haukata shi suke sonyi yaga alama. Akwai halayen Nuriyya da yawa da yake kula dasu yanzun da baya ganin su da, dakin ya koma yana samunta inda yabarta, bandakin ya wuce ran shi a bace har lokacin, tsayen da Nuriyya taga yayi ne yasata bin shi, nuna mata yanda zatayi amfani da injin wankin yayi, bama komai tagane ba saboda a masife yake nuna mata komai, yana gamawa ya fice daga dakin, falo ya koma ya kwanta kan doguwar kujera yana huci shi kadai. Ga hanjin shi daya tattaru ya kulle waje daya. Bacci yake son yi, rana na karawa kuma, yana so yadan shiga kasuwa, dan ba zai ba Nuriyya kudin shi ba. Komawa dakin yayi ya dauko wallet da mukullin mota sai wayar shi ya fita daga gidan.
*
Dakyar ya dawo gida, har wani haske-haske yake gani yana gilmawa ta cikin idanuwan shi saboda yunwa. Ga makoshin shi kamar sahara, a bushe da kishi, a hanya ya tsaya yai azahar, kayan ma dakyar ya fito da su daga mota, daga dankali sai doya da cefane ya siyo, sai kuma kwai da dakyar ya samo shi. Ga kasuwar a shaqare, darajar watan azumi shisa duk wanda ya take mishi kafa in ya bashi hakuri ko amsa baya samu, amman da mutanen da zai mara Allah kadai yasan yawan su, duk da haka saida ya watsa ma wani me napep zagi, baiko juyo ba illa kara gudun napep din ganin wandon sojoji a jikin AbdulKadir din.
Yana shiga ya wuce bangaren Nuriyya ya ajiye kayayyakin a bangarenta, tukunna ya koma mota ya dauko apple din daya gani yana shiga dakin Nuriyya, a falo ya sameta zaune, ta kwantar da Ikram a kujera tana mata wasa, sallamar shi tasa ta amsa tana dago da kanta, fuskar shi ta kalla taga gajiyar da take tattare da shi, ledar ya mika mata tasa hannu tana fadin
"Sannu da gajiya..."
Kai AbdulKadir ya jinjina mata, yana kallonta, jira yake tace mishi zata hada mishi ruwan wanka ya watsa ruwa, ko batace haka ba, ta fada mishi wani abin, ta nuna mishi damuwarta kamar yanda ta saba, amman ta ajiye ledar apple din tana mayar da hankalinta kan Ikram
"Wahee nagaji sosai, kuma yau ana rana"
Hancinta ta hada dana Ikram din da take wangale bakinta da babu hakora, suna saka zuciyar shi cika fam da kaunar su, hankalinta na kan Ikram din tace
"Sannu, akwai rana kam, ni da nake cikin gidama inajin zafi"
Kallonta yayi, muryar shi da wani irin sanyi yace
"Nasan nayi laifi, nasani Wahee, ki horani ta kowanne fanni zan dauka. Amman wannan rashin kulawar banda ita, zuciyata ba zata dauka ba Wallahi"
Yanda ya karasa maganar ya sata yin shiru batace komai ba, tanajin shi ya juya ya fice daga dakin. Numfashi ta sauke me nauyi, sai taji wani irin kadaici ya danneta, kewar Fajr takeji, da yana nan da ya dameta da