Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   51 / 51

150K to 152.3K   out of 152.3K words

sana'ata ni direban babban mota ne, kudin duk da nayi miki hidima dasu, kudin da kikai tunanin ina dasu tsintar su nayi. Sai bayan na tsince sune tunanin inzo miki a matsayin attajirin me kudi yazo mun saboda kin manne mun a zuciya. Ko kadan bakiyi wahalar siyewa ba saboda abin duniya ne a gabanki, nan dinne gidan dana samu na gina a cikin sana'ar da nake... Kar kuma kiyi tunanin akwai wani tashin hankali da zakiyi da zaisa in sakeki saboda wallahi nasha banban da duk wasu maza da kika aura a baya, babu kalar tashancin da banci karo dashi ba, banje wajenki ba sai da nayi shirin zama dake a duk yanda kika so mu zauna"

Mayafinta Nuriyya ta sauke daga kafada tana wulwula shi cikin son fifita fuskarta da iska ta daina kai mata, bata taba sanin menene tashin hankali ba sai yau. Tunda Saminu ya fara magana take jin wasu notika na kwancewa a jikinta, cigaba yai da fadin

"Duk motocin da kikaga ina zuwa wajenki dasu cikin ragowar kudin da suka ragemun nake arowa, gidan dana kaiku na ubangidan wani abokin wasana ne da yake gadi na roke shi alfarma naje daku kika gani, naso inji babu dadi na yaudararki da nayi, sai naga mu dukan mu badan Allah muka gina dangantakar ba, ni dan son mallakarki, ke kuma dan son abinda nake dashi, zaki iya taimaka mun mu gyara zaman mu daga yau mu nemi yafiyar Allah"

Wannan karin dariya Nuriyya tayi da bata da alaka da nishadi, tana son wani yazo ya tasheta daga wannan mugun mafarki, dan a mugun mafarkine kawai zata auri direba, direban ma na babbar mota.

"Da gaske ina kasuwanci, tunda idan nakai timatiri legas ina dauko gawayi in dawo dashi nan in siyar"

Da kuka dariyar ta kwace mata, kafin tasa hannu tana goge hawayen ta ajiye mayafinta a kasa ta kalli Saminu tana fadin

"Wallahi karyar iskanci kakeyi, ni zaka yaudara? Saminu ni zaka yaudara? Sakina zakayi yanzun nan dan bazan taba zama da kai ba. Kaga na maka kalar matar da zata zauna a wannan akurkin kajin?"

Dariya Saminu yayi

"Saki? Ai wallahi gara ki fara sakawa a zuciyarki mutuwa ce abinda zata gifta ta rabani da aurenki"

Mayafinta Nuriyya ta tsugunna ta dauka tana jin yanda duniyar take jujjuya mata, shirin fita takeyi daga dakin, cikin zafin nama Saminu ya taso yana riko hannunta, juyowa tayi tana daga dayan da niyar sharara mishi marin da zaisa ya saketa a daren nan ta koma inda ta fito ya rike hannun yana hadawa da dayan yai mata rikon da takeji kamar zai karyata tukunna yasa dayan hannun nashi ya sharara mata wani irin mari da yasa ta jin wani gishiri-gishiri a cikin bakinta

"Na gaya miki duk kalar zaman da kike so muyi dake shi zamuyi, idan mutunci kike so zamu lallaba rayuwar mu, idan rashin mutunci kike so zan zauna dake dashi"

Kiciniyar kwacewa take tana auna mishi kalar zagin da in sun kwana a tafa yakanji karuwai nayiwa masu neman su. Shisa yasha alwashin kudin goron da akewa direbobi nabin mata bazai zamana cikin su ba, koba dan komai ba yana tsoron lahirar shi, duk tangaririya da wahalar rayuwar daya sha da saken daya samu sanadin mutuwar iyaye bai saka shi ya lalace ba. Iskanci zabine a kowanne yanayi duk da yakan zo da kaddara, amman akwai zabi a cikin al'amuran rayuwa. Wani marin ya sake dauketa dashi yana wurgi da ita kan katifar dakin ya fita yana kulle dakin daga waje, yanajin yanda take dukan kofar tana cigaba da auna mishi zagin dako a jikin shi.

Mota yake ya fito da kayayyakin Nuriyyar da suke ciki ya shigo dasu tsakar gidan, sai da ya dawo kofar gidan ya tsaya abokin shi daya roka alfarma yazo ya dauki motar mutane ya mayar musu ya iso, yabashi mukullin tukunna ya koma gidan ya kulle. Ya shiga ciki ya bude dakin Nuriyyar da ta fito, ya nuna mata karfi yana daukarta ya mayar da ita cikin dakin, bala'i ne take gani irin wanda take jin labarin shi, dan Saminu bai jira ya saka abin duka ba, da hannun shi yaci gaba da mata wani irin duka da ko lokacin da AbdulKadir yake tashen zane su a islamiyya bai taba mata irin shi ba. Tun tana samun bakin zagin shi tana kai mishi yakushi har ta galabaita, nishin kuka ma bata iya fitarwa, a haka Saminu yabi ta yana raya daren.

Zuwa safiya kallo daya zakai mata kasan tagama fita daga hayyacinta, a gida yai sallar asuba. Ko kazar daya siyo sai da safen yace mata tazo suci, kai kawai ta iya girgiza mishi dan dakyar ta iya samu tai wanka tayi sallah saboda ciwon da ko ina na jikinta yake mata, shine kawai abin daya tabbar mata da cewar ba mafarkin auren Saminu takeyi ba, da gaske ne auren shi tayi.

"Kalar duk zaman da kika zabar mana shi zamuyi Nuriyya"

Ya kara tabbatar mata lokacin daya fice daga dakin, kanta kawai ta hade da gwiwa wasu irin hawaye masu zafi na silalo mata, hausawa sunce babu inda son zuciya baya kai mutum, ko da wasa bata taba hango nata zai kawota cikin wannan bala'in ba, ko kadan idan sama da kasa zasu hade ba zatayi zaman aure da Saminu ba...!

#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#LubnaSufyan
[7/16, 9:57 PM] +234 802 111 7692: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
YouTube: https://youtu.be/WwocHslDAYk

*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*

Epilogue

Hannu hijab take gyarama Ikram, ta kasa rankwafawa saboda tsohon cikin dake jikinta. AbdulKadir sai kiranta yake, yace shi bazai shiga cikin gida ba, saida ta fito harabar gidan ma tagan ko motar bai shigo da ita ba, kofar gidan ta fito ita da Ikram tana tsammanin ganin motar shi. Amman ko alamarta babu, dan baima karaso ba duk yabi ya daga mata hankali kamar wani wajen tazo ba gida ba.

A shekaru uku zatace babu abinda ya canza musu banda samuwar karin cikin da yake jikinta, rayuwa suke a nutse da ba zatace a kullum cike take da farin ciki ba, suna samun matsalolin da basu fi karfin yin sulhu tsakanin su ita da AbdulKadir ba. Sai dai zuwa yanzun ta fahimci rayuwar haka take tafiya a ko ina, ta koyar da ita babu wani abu waishi dawamammen farin ciki, sai dai akwai farin cikin da kake samu ko yayane a cikin kowacce rana tunda zaka tashi da tarin dalilan da zaka godema Allah domin su.

"Waheedah..."

Taji muryar Nuriyya ta dirar mata cikin kunnuwa, daga ranar da ta kwashe kayanta rabon da ta sakata a idanuwanta, duk da lokutta da dama takanyi tunanin kotana wacce duniyar, juyawa tayi tana kallon Nuriyyar da rayuwa tasa tayi wani irin sanyi. Da hijab doguwa a jikinta, duk. Da ba wata shigar azo a gani bace a jikinta, ba'a wulakance take ba, dan har kasan ran Waheedah din taji dadin ganinta a nutse. Haka zuciyarta take, wanda suke nufinta da sharri ma da fatan alkhairi take binsu, dan a wajenta duka duniyar bata da wani yawa. Mu duka kuma yan cirani ne da muke haduwa da mutane mabanbanta a hanyar mu, burin kowa shine samun ribar da zai alfahari da ita idan lokacin shi ya cika. Shisa bataga dalilin da zaisa bata lokacinta akan abubuwan da ba zasu amfaneta ba.

Sosai Nuriyya taji dadin ganin Waheedah din, tun tana ganin auren Saminu kamar abu na wasa, kamar abinda ba zata tana yarda dashi ba, tun tana mishi rashin mutunci yana jibgarta harta fara saduda da lamurran duniya, dan taje gida Abba ya rantse wannan karin idan harta kaso auren Saminu ba zata zauna mishi a gida ba, Mama kuma tace ba zata bashi hakuri ba. Haka ta hakura ta koma, kullum rana sai Mama ta kirata a waya tayi mata nasihar da saida ya dauketa shekaru biyu bata jita ba, shima shekarun satar fita tayi batare da ta fadama Saminu ba, akai mummunan hatsari a gaban idanuwanta mota ta take mace da goyonta ko numfasawa basuyi ba.

Motar kuma ta kama da wuta haka direban ya fito yana ihu yanaci da wuta mutane na kokarin kawo mishi dauki, bata tunanin ta taba tsorota kamar yanda ta tsorata a wannan yanayin dan a gigice ta karasa gidansu da kafafuwanta kamar zararriya, tana shiga gida jikin Mama ta fada tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, gabaki daya duniyar bakomai bace ba, kana aikin banza kake cinye kwanakinka, sosai hatsarin ya tuna mata da kwanciyar kabarin da take jiranta, tarin tashin hankalin da yake cikin kwananta na farko ita kadai batare da taimakon kowa ba.

Ranar a gida ta kwana, duk da washegari Saminu zai dawo daga Legas. Samun shi tayi ta bashi hakuri kan irin zaman da suke, sosai kuma suka fahimci juna suka kuma nemi juna gafara. Data nutsu saita sami farin ciki a zama da direban data raina, direban da take ganin tafi karfin tayi rayuwar aure dashi a duniyar da bakomai bace, data nemi tana son ta gwada neman aiki da takardun NCE dinta bai musa mata ba, ca yayi ma akwai wani ubangidan shi zai mishi magana yaji. Cikin ikon Allah aka samo mata aikin koyarwa a wata primary ta mata da ke nan dan dinshen. Dai-dai karfin shi Saminu yake mata hidima.

Duk da matsala dayace take fama da ita yanzun, itace rashin haihuwa, banda wannan rayuwa take data sa tagane farin ciki bako yaushe yake zuwa da kudi ba, farin ciki kanzo idan ka samu wadatar zuciya da iya inda Allah ya zaunar dakai. Tayi nasarar ganin Anas sau daya tun bayan rabuwar su, ta kuma roki daya yafe mata, duk da har yanzun takanyi juyi da amsar daya bata

'Na jima da yafe miki Nuriyya saboda bana son wani abu ya sake hadani dake, ciki kuwa harda tsayuwa gaban Ubangiji a filin tashin kiyama, wallahi na jima da yafe miki karki damu'

Sosai takanyi tunani akan kalar rayuwar da tayi a baya, da mutane biyun da suka nuna mata kauna fiye da kowa a rayuwarta da yanda tayi amfani da wannan kaunar ta cutar dasu

"Nuriyya"

Waheedah ta fadi tana katse mata tunanin da takeyi

"Ki yafemun dan Allah, na cutar dake da yawa, wanda kika sani da wanda baki sani ba, ki yafemun Waheedah..."

Numfashi Waheedah ta sauke

"Babu komai, Allah ya yafe mana"

Wannan karin ajiyar zuciya Nuriyya ta sauke tana dorawa da

"Ki rokar mun AbdulKadir da ya yafemun shima"

Kai Waheedah ta daga mata tana hango motar AbdulKadir din

"Sai anjima..."

Tace ma Nuriyyar tana kama hannun Ikram din

"Ina Fajr?"

Nuriyya ta tsinci kanta da tambaya tana saka Waheedah juyowa ta kalleta cikin idanuwanta

"Na yafe miki Nuriyya, tun kafin ki tambaya, amman hakan baya nufin ina son sake kasancewa dake a rayuwata, babu wani abu da zai sake hadani kawance dake"

Kai Nuriyya ta jinjina ma Waheedah din, bata koji zafin maganganunta ba, ko itace a matsayinta abinda zatayi kenan.

"Nagode..."

Nuriyya ta fadi da wani irin yanayi a fuskarta

"Ina miki fatan alkhairi a duk inda rayuwa zata kaiki"

Waheedah ta fadi tana jan Ikram suka tsallaka inda AbdulKadir yayi parking din motar, Nuriyya kuma ta shiga gida. Bayan motar ta budema Ikram ta sakata a ciki, tukunna ta bude gaban ta shiga

"Kinsan sarai gobe zan tafi, shine zaki zo ki barni ni kadai"

Murmushi kawai tayi

"Nuriyya nagani yanzun ta shiga gida, tace ince ka yafe mata"

Shiru AbdulKadir din yayi badan baiji me tace ba, sai dan a shekaru uku yaune rana ta farko da maganar Nuriyya ta gifta a tsakanin su. Motar shi ya tayar yana wucewa dasu gida, bashida abin cewa yanzun ma, shisa ya zabi yin shiru, wanda duk zaiji labarin shi da Nuriyya zai san kaddarar zaman aure ce kawai ta gifta a tsakanin su, yanzun ta zama bayan shi, bayan da baya dubawa idan harya wuce, ya gama yafe mata duk wani kuskure da tayi mishi a dan gajeran zaman da sukayi. Shima fatan shi idan ya kuskure mata ya zamana ta yafe mishi.

Dan da Abbba ya kira shi yai sake mishi nasiha kan abinda ya faru din daya kira mishi ko da gaba zai tunanin kara aure saida hanjin cikin shi ya murda, yana addu'ar Allah yasa kaddarar shi ta zama da mata biyu ta kare daga kan Nuriyya, Waheedah ta ishe shi rayuwar duniya yana kuma fatan ta zama matar farko da zai nema idan ya tsallake duk wani mataki yayi nasarar shiga aljanna.

Suna karasawa gida an kawo wuta, Ikram nata tsalle ganin tv a kunne da tashar cartoon network da suka saka shun the sheep. Nan falon suka barta suna shigewa dakin su. Waheedah na cire hijabin dake jikinta, AbdulKadir ya taka ya hade space din dake tsakanin su, sai nishi take kamar tayi wani aikin karfin.

Hannun shi daya ya dora kan cikinta kamar abinda yake ciki hakan yake jira yayi motsin da taji har bayanta ya amsa tana runtsa idanuwanta ta bude su akan AbdulKadir da yake mata dariya

"Ke kam kamar ba matar soja ba"

Harar shi tayi

"Da zan iya dana cire cikin nan ka dauke shi kona kwana biyune"

Tsinin cikin bazai barshi ya rungumeta yanda yake so ba, hakan yasaka shi sakin hannunta ya zagaya yana rungumeta ta baya hadi da rada mata maganganun da sirrine a tsakanin su, hannu tasa tana dan ture shi hadi dayin dariya kafin ta dora hannunta saman nashi da ya ke kan cikinta tana lumshe idanuwan shi. ABDULKADIR din ta, sojan ta, Sadaukin ta. Bata same shi da sauki ba, kaddarar zaman su bata kawosu inda suke da sauki ba, bata da wani tabbaci akan yanda rayuwa zata kare musu, amman tana da yakinin indai suna tare da juna koya rayuwa zata hankade su koda sun fadi dayansu zai daga daya...!

DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH.

51 / 51