Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   17 / 51

48K to 51K   out of 152.3K words

hoton tane a jikin wallet din shi shekara daya kenan..."

Wannan karin da duk hannayen shi Yazid ya dafe kan shi yana wani irin sauke numfashi kamar wanda yasha gudu. Zazzabin da yake ji na saukar mishi gabaki daya. Dago fuskar shi yayi yana saka hannu ya dauki hular shi dake ajiye akan gadon ya soma fifita dashi, dan sosai iskar dakin ta mishi kadan har bayajin tana kai mishi inda ya kamata ballantana ya iya tunanin wani abu. Shi kanshi Yassar din wani irin nauyi yake ji yana danne shi da bazai ce ga daga inda yake tasowa ba, amman Yazid din ya kamata yasan abinda yasani shima.

"Koni ba kullum nake kallon fuskar Abdulkadir in fada mishi magana ba, badon ina tsoron shi ba, sai dan ina gudun ya fada mun maganar da zan dake shi saina karya shi.

Ina kula dasu Hamma, cikin ido Waheedah take kallon shi tai mishi magana..."

Sosai Yazid yake fifita fuskar shi, muryar shi can kasan makoshi yace

"Kadan bani waje..."

Cike da wani irin yanayi Yassar yake kallon shi

"Hamma..."

Kai Yazid ya girgiza mishi, zuciyarshi yake ji ta kumbura ta cika kirjin shi taf, bayason ta tarwatse a gaban Yassar, bayason ta tarwatse a gaban kowa

"Dan Allah Yassar... Bana son in breaking a gabanka... Abin zaimun yawa..."

Numfashi Yassar din ya sauke yana kallon Yazid sosai, cike da son tabbatar da koma meye zai biyo baya, koya Yazid din zai karye, zai iya komawa dai-dai. Kamar Yazid yasan me Yassar din yake tunani yadan tattaro sauran karfin da yake ji yana mishi murmushi hadi da jinjina mishi ka cike da son tabbatar mishi cewar wannan abin bazai kashe shi ba, tukunna Yassar ya juya ya fita daga dakin. Kofar na rufewa Yazid ya kwanta kan gadon yana dunkule jikin shi. Wani irin ciwo yake ji da bai taba tunanin akwai kalar shi ba.

Numfashin shi har tsai-tsayawa yake da yanda kirjin shi yake zafi, yana jin yanda da duk dakika wani abu a zuciyar shi yana karyewa hadi da faduwa a cikin kirjin shi da wani irin ciwo da bashida kalaman dazai dora shi. Baisan tunanin me ya kamata yayi ba, asalima tunani daya yake cike da kan shi da zuciyar shi dake karyewa.

'Bazai hada soyayya da kanin shi ba'

Ko rana aka saka mishi da Waheedah yagane Abdulkadir din najin ta a zuciyar shi fiye da matsayin kanwa zai hakura yabar mishi, idan ma Allah bai nufa zai aureta ba, su biyun zasu hakura ta samu wani. Amman soyayyarta zata kashe shi kafin ya hadata waje daya data kanin shi. Yanzun yake kara godema Allah da bai furta mata ba, yana kuma tabbatar da wannan ne dalilin daya rike shi harya kasa furta mata. Yafi minti goma a kwance yana son ciwon da yake ji ya lafa mishi ya tashi ya saka kayan shi dan masallacin idi zasu tafi su duka gidan.

*

Tana fitowa wanka, mai ta shafa ta zura doguwar rigar sabuwar atamfarta, dankwalin ta daura yanda zata iya dora hijab akai batare daya dameta ba. Fuskarta ta duba a mudubi, atamfar yellow ce da ja, tayi matukar karbar hasken fatarta, maikon fuskarta taga kamar yai yawa. Farar hodar da take shafawa ta dauka ta zazzaga a jikin soson hodar Amatullah dan ba zata tuna ko tana da soson hoda ko bata dashi bama. Murzawa tayi a fuskarta ta ajiye tana sake dubawa. Kayan kwalliyar da banda farar hodar da wasu cikin turarukan dukan su sauran na Amatullah ne take dubawa.

Rasa wani abu da zata dauka tayi amfani dashi tai. Ko a gida zata zauna bata tunanin zatayi wata kwalliya fiye da wadda take fuskarta, ballantana fita zasuyi, su dukan su suke zuwa masallacin idi a gabatar da sunnar da take cikin zuwa sallar idi. Fuskar mace kan shiga cikin al'aura, wato abinda ya kamata ya zama a rufe duk lokacin da ta tsara mata kwalliya, sharadin saka niqab ya fada akanta koda batada kyawun dazai karya alwalar maza. Tana yawan tunasar da Amatullah da Nuriyya, amman biris suke da ita, wasu lokuttan ma Nuriyya kan ce mata ita ta cika tsawwala lamurran addini.

Sai dai tasan zunuban da yawancin mutane kan dauka kanana, sune suke taruwa a hankali har suyi girman da mutum bazai iya dauka ba. kwalli ta hango ta dauka ta sakama idonta, tana ganin yanda fuskarta ta sake fitowa. Da gaskiyar Mami, kwalli na mata kyau. Mikewa tayi ta dauki turare ta tuna fita zatayi, ta mayar ta ajiye. Hijab dinta da take a linke ta dauka ta warware tana sakawa a jikinta. Doguwa ce har kasa, sai dai babu hannu a jiki, tana kuma sane ta dauko dan kunshin da yake hannuwanta.

Kafafunta ma safa ta saka musu, batai kunshi dan mazan da ba muharramanta ba, tayine dan kwalliya. Dogayen takalmanta da suke ajiye ta saka. Amatullah kan mata tsiya cewar tana saka dogayen takalma ne dan bata da nauyin da zata dinga gurdewa. Dariya kawai Waheedah kan yi, ta riga ta sabane da dogayen takalman tun yarinta, gashi kuma hijabanta wani lokaci suna dan jan kasa, idan ta saka dogayen takalman sai taga sunfi kyau. Bata ga Mami a gidan ba, har dakinta ta leqa bayan ta fito, tana da tabbacin suna bangaren Hajja danyin hidimar bikin sallar da suke haduwa su duka hudun suyi.

Dan haka ta fice daga gidan itama, yau dai ta shirya da wuri, badan gugar da taima Yazid bama da tuni ta jima da shiryawa. Babu mai mata mita ta cika sanyin jiki. Takawa tayi har inda ake ajiye motocin gidan tana samun guda daya ta tsaya a jikinta, saitin da zata iya hango bangaren su Abdulkadir, dan shi take so tagani tunda ta tashi. Tafi minti biyar a tsaye kafin ta hango shi ya fito, jikin shi sanye da farin yadi da hula rike a hannun shi cikin yanayin da yasa bugun zuciyarta karuwa. Dago kai taga yayi yana tsayar dashi akanta. Bata hango idanuwan shi daga inda take, murmushi ya kwace mata.

Sosai take murmushi da yanda mazaunin idon AbdulKadir din kawai take iya hangowa daga inda yake. Hakan yasata sauke kallonta daga kan shi, zata rantse idanuwanta kawai ta sauke tana kallon takalmanta, ta sake dago su taga Abdulkadir din tsaye a gabanta yana kankance mata idanuwan shi, zuciyarta taji cikin makoshinta inda tai tsaye tana ci gaba da dokawa.

"Murmushin me kike?"

Ya tambaya yana tsare ta da idanuwa, dan shi baiga abin nishadi a safiyar ranar ba, kan shi ciwo yake. Gashi komai baya mishi dadi, kai ta girgiza mishi tana saka shi fadin

"Taqabbal Allaahu minna wa minkum"

Ya dora da

"Ba'aimun dinkin sallah ba"

Cikin yanayin da ya saka wani murmushin kwace mata, dan yanda yai maganar kamar karamin yaron da akaima gagarumin laifi ya sakata jin tamkar tana kan lilo. Komai nashi ya mata, komai a tattare dashi. Amsa gaisuwar sallar da yai mata tayi a hankali har lokacin tana murmushi

"Ba abin murmushi bane ba, kayan Hamma Yassar na saka, basumin dinkin sallah ba, kowa an mishi banda ni"

Abdulkadir din ya fadi yana rasa dalilin da yasa yake gaya mata. Kawai ya tsinci kanshi da son gaya mata ba'ai mishi dinkin sallar ba, yana kuma jin son gaya mata duniyar ma bata mishi dadi, baisan ta inda zai fara ba. Idan tana kusa dashi yakan tsinci kanshi dayin abubuwan da baisan dalilinsu ba. Abu daya yake gani a fuskarta, zai iya yin komai a gabanta, ba zata taba raina shi ba, bai taba ganin hakan a fuskar kowa ba sai tata, ko Yassar bakomai yake iyayi a gaban shi ba, a hakan ma ya raina shi dan yana ganin ya bashi wasu yan shekaru, shisa yake kokarin ganin ya kama girmanshi a gaban Yassar din.

Dayan hannun shi ya dago ya bude mata shi, links ne a cikin tafin hannun nashi. Hakan yasata tattaro hijab din jikinta ta fito da hannayenta da Abdulkadir din yabi da kallo, zuciyarshi na fada mishi bai taba ganin hannuwa masu kyau irinsu ba. Links din ta saka hannu ta dauka, Abdulkadir na rike hannun nata

"Kunshi kikayi"

Maganar ta fito daga kasan makoshin shi lokacin da ya dago dayan hannun shi yana kamo dayan hannun nata dashi hadi da duba kunshin nata da yakejin na kwance wasu kusoshi cikin kanshi. Wani irin yanayi yake ji da bazai fadu ba. Motsi yaji a bayan shi, amman bai juya ba, asalima bayason ya dauke idanuwan shi daga hannuwan Waheedah din, a karo na farko da ko kadan tunanin hasken fatarta baizo mishi ba, baya ganin komai sai jan lallen dayai wata irin fitowa a hannunta.

Tun daga nesa Yazid ya hango su, yana jin zuciyar shi kamar zata fito waje, dan zazzabi ne a jikin shi ruf, dakyar ya iya fitowar ma, baisan kafafuwan shi sun motsa ba lokacin dayaga Abdulkadir din ya rike hannun Waheedah sai da yagan shi tsaye a bayan shi, amman daga Waheedah din har Abdulkadir sunyi kamar basu san yana wajen ba. Musamman Waheedah da yake ganin tsayuwar duniyarta akan Abdulkadir din ta cikin idanuwanta, tana saka shi tuna duka lokuttan da yake ganin hakan a idanuwanta idan Abdulkadir na wajen, yana sakashi tunanin kalar sakarcin shi wajen kasa fahimtar abinda yake faruwa a tsakaninta da AbdulKadir din, dan yana tunanin tayi yarinta ta fahimci wani So ballantana harta fada cikin shi.

"Waheedah..."

Yazid din ya kira yana saka zame hannuwanta daga cikin na Abdulkadir tadan kalli bayan shi inda Yazid yake tsaye

"Hamma..."

Ta fadi tana saka Abdulkadir din juyawa ya kalli Yazid din shima

"Taqabbal Allaahu minna wa minkum"

Abdulkadir ya fadi yana mikama Yazid din hannu, karba yayi ya amsa yana kuma yi musu murnar sallah a bisa tsarin addinin musulunci tukunna ya zagaya ta bayan motar ya tsaya, dan kirjinshi yake ji kamar zai bude. Juyawa Abdulkadir yayi yana mikama Waheedah hannuwan shi. Dai-dai lokacin da Yazid din ya juyo yana kallon su, links din Waheedah ta daura mishi, idanuwan shi nakan hannayenta da yake jin kamar ya yanke ya koma Kaduna dasu, ya manna a jikin bangon dakin shi, duk lokacin dayai ra'ayi ya juya ya kalla. Hakan dayai tunani ya saka shi laluba aljihun shi ya zaro wayarshi daga ciki.

Waheedah na kallon shi, zuciyarta kamar zata fito waje. Tana kuma kallon shi yana danna wayar, kafin ya kamo hannunta yana mikar dashi, ya kuma kamo dayan ya dora a kan dayan cikin yanayin yanda yake son yagan su, ita kam a gabanshi takan koma kamar yar tsana mai batir da remote, remote din kuma yana hannun Abdulkadir, yanda duk yake so tayi hakan yake juyata. Idanuwanta tsaye yake kan fuskar shi, tana jin yanda yake rike da yan yatsunta, kafin ya saki yana duba wayarshi hadi da dan daga mata kai cikin yanayin da yasata sauke hannuwanta tana murza su cikin hijab, har lokacin tana jin nashi hannuwan manne a jiki.

Kanshi Abdulkadir yadan dafe daga gefe yana runtsa idanuwa, tukunna ya bude su akan Waheedah yana fadin

"Kaina na ciwo..."

Bata ce mishi komai ba yaga ta juya da sauri, yana bin takalman kafarta da kallo, ko tunanin ta fadi cikin dogayen takalman nan batayi. Yana kuma kula da yanda kusan duka takalmanta dogayene. Bayan shi ya jingina da motar yana duba hoton hannuwanta a cikin wayar tashi, blackberry badai camera ba, sosai hoton ya dauku, shiya mayar kan wallpaper din shi daman hoton wani lallen ne, wannan dai yafi mishi kyau. Baisan lokacin da yasa hannu ya shafi screen din wayar ba, yana karama Yazid zazzabin da yake ji. Dan yana kallon duk abinda yake faruwa, bai daisan haka zai mishi zafi na gaske ba.

"Abdulkadir..."

Ya kira a hankali yana saka Abdulkadir din juyawa ta bangaren da yake ya kalle shi

"Karka sake rike Waheedah, akwai haramci a hakan, kasani ba saina fada maka ba, ba muharramarka bace ba"

Dakuna fuska Abdulkadir din yayi

"Kunshi tayi Hamma..."

Ya fadi kamar hakan zai zama dalilin da zaisa ya rike hannuwanta

"Na dai fada maka, ranka zai mugun baci idan na sake gani"

Yazid ya fadi cikin yanayin da AbdulKadir din bai taba gani a tare dashi ba. Hakan yasaka shi daga kai a hankali kawai tukunna ya juya yana hada bayanshi da motar wajen. Ranshi bai baci ba yau, bashida wannan wajen, kunshin Waheedah ya dauke mishi wannan yau kam, bashida lokacin fada da Yazid din, duk da ya tsoma mishi baki cikin lamurran da baiga ta inda ya shafe shi ba. Waheedah ce ta dawo da robar ruwa a hannunta, dayan hannun a dumtse, tana sake goge mishi komai da yake cikin kan shi. Robar ruwan ta mika mishi, ya karba, idanuwan shi kafe kan hannuwanta, dan yaji suna danna mishi tunanin Nuriyya inda yake son boye shi dan karya sake dawo mishi.

Dayan hannun Waheedah ta ware mishi yana ganin Panadol guda biyu, kai yake girgiza mata, a duniya babu abinda ya tsana irin magani, ko rashin lafiya yake bayasha. Yassar ya taba tura mishi cikin ayaba yana ce mishi ko itace yaci zaiji karfin jikin shi, kawai yana gutsura ya tauna magani a ciki, kuma ya tsare shi da saiya hadiye, har amai yayi.

"Bazan sha wani panadol ba"

Ya fadi yana kankance mata idanuwa. Kallon shi Waheedah takeyi

"Kanka na ciwo fa Hamma..."

Dakuna mata fuska Abdulkadir yayi

"Nifa bazan sha wani magani ba"

Yazid Waheedah ta kalla da yake tsaye yana kallon su, shima Panadol din yake bukata, ji yake kamar yai ihu ko zata ga yana bukata fiye da AbdulKadir din ta bashi

"Hamma kai mishi magana. Kan shi yana ciwo wai bazai sha magani ba"

Kallonta Abdulkadir yayi yana tunanin idan Zainab ce da yanzun ya kwada mata marin da bakinta bazai sake gigin kai karar shi ba, amman Waheedah ce, batayi hakan dan ta raina shi ba, yana ganin damuwa tattare da muryarta.

"Ki kyale shi tunda bazai sha ba"

Yazid ya fadi, yana kuma jin tun maganar ta fito daga zuciyar shi dake wani irin ciwo.

"Hamma..."

Waheedah ta kira cikin sanyin muryarta da yasaka Yazid din juyawa yana dana sanin fitowar da yayi. Bazai yiwu yanajin azababben kishin Abdulkadir ba, AbdulKadir ne, kanin shi, dan uwan shi ciki daya. Amman zuciyarshi batasan wannan ba, kishi yakeji har idanuwan shi na lumshewa

"Me yake faruwa ne?"

Yassar daya karaso wajen ya tambaya

"Bakomai..."

Abdulkadir ya fadi a lokacin da Waheedah tace

"Kanshi ne yake ciwo kuma wai bazai sha magani ba, har na ballo kuma"

Kallonta Abdulkadir yayi ciwon kan da yake ji na karuwa

"Bazan sha ba, ni babu maganin dazan sha. Nace ki ballo mun?"

Yake fadi cike da masifar shi

"Karbi maganin nan kafin inci ubanka, tunda ta ballo sai kasha wallahi. Kaji na rantse"

Hannu Abdulkadir ya mikama Waheedah da take murmushi tana sakashi kankance ido cikin son watsa mata harara.

"Mincika..."

Yassar ya fadi yana kwashewa da dariya hadi da dorawa da

"Anya ba'aima Hajja musayarka a asibiti ba? Abdulkadir wanne irin idone wannan?"

Maganin Abdulkadir ya saka a bakin shi ya bude robar ruwan ya hadiye tukunna ya watsama Waheedah da Yassar din harara, yana saka Yassar sake kwashewa da dariya, mukullin motar shi ya saka a jiki ya bude. Bayan motar Abdulkadir ya bude ya shiga, yana dakuna fuska, tsakanin shi da Allah fushi yake an sakashi shan magani. Yazid ma bayan ya bude ya shiga ta bangaren shi. Hakan yasa Waheedah bude gaban motar zata shiga, hango Nuriyya tayi ta shigo gidan, dan tare da ita sukan tafi tunda Babansu bazai taba jerawa ya tafi idi da ita ba.

Irin atamfar jikin Waheedah ce ta saka itama, dan tare Abba yai musu da duka sauran matan gidan. Hijab ce dako gwiwarta bata kai ba, daga inda Waheedah take tana hango kwalliyar da take fuskar Nuriyya, musamman jambakinta. Tana kuma hango yanda kugunta ya fito cikin skirt din da take sanye dashi, dan ita riga da skirt tayi. Kai kawai Waheedah ta girgiza dan in tai mata magana kan cewa hijab din tayi karama fada zasuyi da safen nan. Daman sunyi wani kan Anas. Karasowa Nuriyyar tayi

"Wallahi na dauka kun tafi, inata sauri"

Kai Waheedah ta girgiza mata

"Yanzun dai zamu tafi. Na dauka ba zakije ba"

Hararata Nuriyya tayi, tana ganin ta mata wani irin kyau naban mamaki. Dariya Waheedah tayi ta bude gaban motar ta shiga. Zagayo Nuriyya tayi ta bude bayan motar ta bangaren Abdulkadir da tunda yaji muryarta ya runtsa idanuwan shi yana budesu da wani irin bugawa da zuciyarshi tayi. Har addu'a yayi karya ganta harya tafi, yanzun ma kokarin kin juyawa yake yaji ta bude kofar, baisan lokacin daya juya ba, yana nasarar sauke idanuwan shi cikin nata. Janbakin ta na saka wani abu cikin kanshi yamutsawa. Tsarin kwalliyar da take fuskarta na samun wajen zama cikin kanshi.

Kallon shi Nuriyya tayi, bugun zuciyarta nayin dai-dai da nashi. Yayi mata wani irin kyau cikin farin yadin shi, ga wani irin kamshi da yake, yau kam sosai take jin kasancewarta sallah. Murmushi tayi tana zama cikin motar ta rufe murfin tukunna tace

"Ina kwananku"

Yassar ne ya amsa yana dorawa da

"Nuriyya anyi sallah lafiya?"

Amsa shi tayi, turarenta na cika hancin Abdulkadir din, yana saka shi sauke numfashi a wahalce da yanayin da yakeji. Dan matsawa ya sakeyi jin yanda tayi kusa dashi da yawa, amman hakan bai rage mishi komai ba, saima hannunta daya kalla da take gyara hijabinta dashi, itama kunshine, ja da baqin lalle daya saka shi runtse idanuwan shi yana kirga daya zuwa hamsin, har yaji Yassar ya tayar da motar ya juyata suna ficewa daga gidan.

Idanuwan shi ya bude yana gyara zaman hannun shi daya dauke babu shiri jin ya taba na Nuriyya, ta gefen idanuwan shi yaga ta kalle shi da idanuwanta da taja da eyeliner suna kara fitowa. Wani abu Abdulkadir yake ji tun daga dan yatsan kafarshi zuwa tsakiyar kanshi da kusancin da Nuriyya tayi dashi. Ita kam yau ranta kal ta zauna kusa da Abdulkadir, ta kuma lura da a takure yake, zataji dadi idan ya zamana itace tai affecting dinshi haka, yana nufin koyayane ya damu da zamanta. Inda idanuwan shi suke kallo take nema kafin ta kula da hannunta ne, dayan hannu ta zaro tana ci gaba da wasa da yatsunta.

Abdulkadir na kula da yanda har cikin tafukan hannuwanta itama kunshine, sai dai nata da ratsin baqi, na Waheedah kuma gabaki

17 / 51