Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
zan koma ba wani wajen ba"
Numfashi Yassar ya sauke, Yazid na girgiza kai
"Ba za'a taba maka abin arziqi ba kai kam. Allah ya tsare hanya, a kula, banda rashin kunya"
Idanuwa kawai Abdulkadir ya kankance mishi, baice komai ba harya fice daga dakin. Hankalin shi ya mayar kan Yassar
"Wai shafa mai ne haka tun dazun. Ka shiga uku kaikam, sai kace mace"
Murfin man Yassar ya jefa mishi yana fadin
"Fita daga dakin nan dan ubanka..."
Dariya Abdulkadir yayi
"Ba inda zanje, ni da dakina"
Ganin Yassar na ajiye robar man dake hannun shi yasa Abdulkadir din mikewa babu shiri, ya fice daga dakin yana dariya. Daman yana da niyyar zuwa ya gaisa da Hajja kuma yai mata sallama, tunda inya koma baisan lokacin da zai sake dawowa ba kuma, sai dai ta waya. Da sallama ya shiga dakin Hajja, yana samun wasu cikin dangin Abba da suma duk ranar zasu tattafi, yawancin su baya tunanin a garin Kano suke da zama, bai tabbatar ba, saboda ko taron dangi da akanyi duk karshen shekara zai iya qirga guda nawa ya taba zuwa, suma idan Yassar ya jashi.
"Sannun ku"
Ya fadi yana soma wucewa cikin dakin sosai, kamun wata mata da yasan yar uwar Abba ce, amman bazai tuna ya alaqar take ba, ko abokiyar wasan shi bai sani ba, tace
"Abdulkadir baka iya gaishe da mutane ba?"
Juyawa yayi yana kare mata kallo, kafin ya amsa da
"Sannun kun da nace bai miki ba?"
Daya daga cikin matan ta watsa mishi daquwa tana fadin
"Karbi wannan Abdulkadir, marar kunyar banza. Yayar gyatumin naka kake mayarwa magana haka"
Kankance idanuwa Abdulkadir yayi yana fara bude baki ya tambayeta meta hada da Abban nasu da zatai mishi zagin yara, Hajja ta katse shi da fadin
"Abdulkadir..."
Juyawa yayi ya kalli Hajja, ranshi ya gama baci
"Me yasa zatai mun zagin yara Hajja? Wacce gaisuwa suke so in musu? Bayan ta musulunci daya wajaba akaina har sannu na musu"
Runtsa idanuwa Hajja tayi, tana gujema Abdulkadir bakin mutane
"Abdulkadir..."
Ta sake fadi, wannan karin ranta a bace, da gajiya da halayenshi, ba zatace batayi kewarshi a shekarun nan ba, amman bakinta ya huta kwana biyu. Kuma babu wanda yazo gidan yagan shi ballantana wani abu ya hadasu har yai musu rashin kunya. Juyawa Abdulkadir din yayi yana ficewa daga dakin. Hajja tabi bayan shi, sauri ta kara tana wuce shi, ganin ta nufi sashin Abba yasa ran Abdulkadir din kara baci, yasan kararshi zata kai wajen Abba, shi ba karamin yaro ba.
Bayanta yabi har dakin Abban data shiga da sallama, yana zaune akan kafet da alama karyawa yagama yi. Hajja najin shi yana biye da ita, dan haka bata tsaya bata lokaci ba tace
"nagaji da halin yaron nan Alhaji. Yanzun su Hajiya Salamatu ya samu a falo yai musu rashin kunya..."
Numfashi Abba yaja ya fitar yana kallon Abdulkadir din da yake tsaye. Hakan yasa shi fadin
"Ni ba rashin kunya nai musu ba Abba"
Juyawa Hajja tai tana kallon shi
"Na maka ta kudin ka, kasan tambarin gidan muce"
Kai Abdulkadir ya sauke kasa, shisa daya tafi ya shekara biyu baizo gidan ba, sai angan shine za'a saka shi a gaba ana mai fada kamar karamin yaro. Juyawa Hajja tayi tana ficewa daga dakin
"Ni ban musu rashin kunya ba Abba. Nayi sallama fa, har sannu nayi musu. Shine zasuyi mun surutu ban gaishe dasu ba"
Numfashin dai Abba ya sauke da maganganun Abdulkadir din, addu'a itace abinda yake bin yaron da ita, dan idan yace zai saka bacin rai da halayenshi matsala za'a samu. Tunda haka Allah yayi shi da baudadden hali, idan zagin shi akai, ko akai mishi fada ba amfani yake ba, dukan ma ko sanda ake mishi baji yake ba. Addu'a ita kadai ce abinda zai tausasa zuciyar Abdulkadir. Hakan yake yawan kwatantama Hajiya Safiyya.
"Ka kyauta ai. Inace tun jiya da daddare kaimun sallama cewar yau da sassafe zaka wuce"
Abba ya fadi, kallon shi Abdulkadir yayi yanajin wani sabon bacin rai, dan yaga alama, Abban nason nuna harya gaji dashi.
"Yanzun ma sallama naje in mata..."
Kai Abba ya jinjina
"Allah ya tsare ya kaiku lafiya. A dinga tausar zuciya dai"
Sai da ya amsa da Amin tukunna ya fice daga dakin. Sosai ranshi a bace yake, amman bazai tafi baima Hajja sallama ba. Dakin ya sake komawa, yana buga kafafunshi cikin son sanar dasu Hajiya Salamatu baiyi niyyar gaishe su ba, babu kuma wanda ya isa yasa shi yin hakan, ba kuma yanda zasuyi dashi tunda ba haihuwarshi sukai ba. Dakin Hajja ya fara shiga ya samu bata nan, fitowa yayi yana nufar kitchen. Acan kuwa ya sameta tana hada shayi
"Hajja..."
Ya kira, inda yake bata kalla ba, aikin da takeyi taci gaba, dan sosai ya bata mata rai.
"Hajja mana... Banaso fa..."
Abdulkadir ya sake fadi, ganin bata da shirin kulashi yasa shi kama hannunta
"Zan watsa maka ruwan shayi idan baka bace mun dagani ba"
Wani guntun murmushi ya kwace ma Abdulkadir din
"Nine fa Hajja..."
Harara ta watsa mishi, yanayin yanda ya kankance mata idanuwan shi nasa murmushin da batayi niyya ba kwace mata, tana son yaranta fiye da yanda zata iya fadi, amman Abdulkadir daban take jin shi, tun yana karami jin shi take har ranta, ko dukan shi tayi tana da tabbacin yanda hakan yake mata zafi a zuciya yafi yanda yake mishi a jiki. Wasu yaran kan zama karfin ka, Abdulkadir rauninta ne.
"Hajja hanya zan hau, bana so in tafi kina mun fushi, bayan banyi komai ba"
Duka Hajja takai kishi a kafada tana yarfe yatsunta da suka amsa, dariya Abdulkadir yayi yana kama hannun nata data fisge tana hararshi, yasan ta huce dan yana ganin murmushi a idanuwanta
"Saura aita kiran wayarka a kashe"
Yar dariya Abdulkadir yayi
"Zan kunna in shaa Allah"
Kai Hajja ta jinjina mishi
"Dan Allah ka kula...kaga girma kake, banda rashin kunya"
Daquna mata fuska Abdulkadir yayi
"Nifa bana rashin kunya"
Rausayar dakai Hajja tayi
"Hmm..."
Kawai ta iya fadi, Abdulkadir din yai mata murmushi yana dorawa da
"Sai munyi waya..."
Kai ta jinjina mishi
"Allah ya tsare ya bada sa'a..."
"Amin. Zahra fa? Hamma Mubarak ma ni sau daya nagan shi tun da nazo"
Kofin shayi Hajja ta dauka tukunna tace
"Kasan wannan hidimarshi tafi karfin shi, nima da muke kwana gida daya, sai in yini ban saka shi a ido ba. Zahra kuma tana bangaren Hajiya Halima nake ji..."
Kai Abdulkadir ya daga mata kawai, saida ya samu plate ya zuba soyayyar doya da kwai da tayi, ya dauki shayin da ta hada mishi, tukunna ya sake yi mata sallama yana ficewa daga dakin ya nufi bangaren su.
*
Tare suka fito da Yassar, jakar Abdulkadir din riqe a hannun shi, sai wallet dinshi a dayan hannun, gaban mota ya bude yana jefa jakar tashi kujerar baya ta gaban. Ya fito da jikin shi kenan daga motar yaji ance
"Hamma..."
Sanyin muryarta yasa shi sanin itace tun kafin ya juya yana sauke kananun idanuwan shi akan Waheedah da take tsaye, jikinta sanye da doguwar riga ta atamfa, ta saka farar hular sanyi saman kanta, sai yaga fuskarta tai mishi fayau. Kallon shi Waheedah take tana jin zuciyarta dake dokawa ta matse waje daya a kirjinta. Yanayine da bata da kalaman da zatayi amfani dasu wajen fassara shi, bata taba jin kewar wani a rayuwarta yanda take jin kewar shi tun kafin ya tafi din ba. Gaishe shi ya kamata ace tayi tasani
"Tafiya zakai?"
Ta bukata, bata bari ya amsa ba tace
"Hamma bakai mun sallama ba, tafiya zakai bakai mun sallama ba..."
Ta karasa maganar muryarta na karyewa tana jin hawayen da suke tahowa daga zuciyarta sun cika mata idanuwa taf. Kallonta Abdulkadir yakeyi, banda Hajja da Abba, babu wanda yaima sallama a gidan. Su kadaine yake jin ya zama dole yai musu sallama idan zai tafi, wanda yagani yanzun dazai fito dai sunyi sallama, baisan meye a yanayinta da yake son saka shi jin kamar bai kyauta ba da bai mata sallama ba. Tsintar kan shi yayi da fadin
"Zan zo hutun sallah..."
Saida ta ware mishi manyan idanuwanta tukunna maganganun dayai suka zauna mishi
"Da gaske zaka zo? Dan Allah kazo Hamma, kaji... Kazo dan Allah"
Kai Abdulkadir din yadan daga mata, yana ciza fatar bakin shi daga ciki, baisan meyasa yace mata zaizo din ba, amman hawayen da yake gani cike da idanuwanta ne bayason su zubo. Murmushi tai mishi da yasa fuskarta qara mishi haske. Su duka biyun basu kula da Yassar ba harya wuce ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya zauna yana jiran Abdulkadir din.
"Sai na dawo..."
Abdulkadir din ya furta muryar shi can kasan makoshi. Wani irin yanayi kalmomin nashi suka jefata, ji take kamar zai tafi da wani bangare na zuciyar ta, lokaci daya ta nemi tsallen da zuciyarta take mata najin zaizo hutun sallah ta rasa. Sai kewar shi da ta kara danneta
"Kamar karka tafi"
Ta furta muryarta a karye, tana saka shi runtsa idanuwan shi ya bude su hadi da kankance su akanta. Hannun shi daya yasa ya laluba aljihun shi duka biyun, da alama baiji abinda yake nema ba, juyawa yayi sai lokacin yaga Yassar, kanshi ya zira ta jikin murfin motar yana fadin
"Dan bani biro..."
Cike da mamaki Yassar yace
"Biro kuma?"
Daquna fuska Abdulkadir yayi
"Idan zaka bani kabani kawai Hamma, meye namun tambaya kamar na maka wani yare?"
Kallon shi Yassar yayi
"Bazan bayar ba to"
Da alamun gajiya Abdulkadir yace
"Hamma mana... Kabani nikam"
Kallon shi Yassar ya sakeyi, baisan me zai da biro ba, amman saboda Waheedah da take tsaye yasa shi dudduba cikin motar, yako samo wani baqi ya miqama Abdulkadir din, karba yayi yana takawa inda Waheedah take tsaye. Bashida takarda, bashida kuma lokacin zuwa nemo wata. Hannunta ya kamo, yana share yanda ta ware mishi manyan idanuwanta cike da mamaki, zuciyarta nayin wani irin tsalle ta dawo cikin hannun nata daya riqe, bin shi tayi da kallo tana mamakin yanda akai baya kyarma, dan tana jin yana kyarmar daga ciki. Rubutu Abdulkadir din yai mata a hannun tukunna ya saki yana juyawa batare daya ce komai ba.
Kallo Waheedah tabi shi dashi harya shiga mota yaja murfin ya rufe, da ido ta rakasu har gate suka fice, ko sau daya Abdulkadir din bai juyo ba balle tayi tunanin ko hannu zai dan daga mata cikin alamar bankwana, jikinta take jin kamar an mata allurar rashin kuzari, saida taga mai gadi yaja gate din gidan ya rufe tukunna ta dago hannunta da take jin har zufa-zufa yake ta bude tafin hannun tana juyo dashi saboda taga meya rubuta. Lambar wayar shi ce da adireshin shi na email, dayan hannunta tasa tana shafar rubutun hadi dayin yar dariya, sosai Abdulkadir yana da kokari ko da suke islamiyya da boko, a ajinsu kaf babu wanda yake kamo shi, amman baida rubutu me kyau, zaka rantse dan firamare ne yayi duk idan kagani.
Hannunta ta sake dubawa tana kallon lambobin hadi da rufe idanuwanta ta karanta su cikin kanta inda suka samu wajen zama daram. Adireshin email din ta duba 'Abugaje@yahoo.com' ta hada da lambar wayar tana samar musu waje me kyau ta adana, hannun dake da rubutun ta daga tana dorawa a kirjinta inda zuciyarta take dokawa da wata irin nutsuwa tukunna ta juya tana nufar bangaren su, tana jin tafiyar da take kamar akan gajimare.
*
Idanuwan shi kofar gidansu Nuriyya ya sauka suna fita, saiya tsinci kan shi da sauke wani numfashi da baisan yana rike dashi ba, bazai ce ga asalin abinda yake ji ba, amman idan da Nuriyya zata kasance tsaye a kofar gidan hakan zai mishi dadi, gyara zama yayi cikin kujerar yana lumshe idanuwan shi, numfashi ya sake ja, kafin ya fitar dashi Yassar yace
"Meke damunka?"
Idanuwan shi ya bude yana juya kanshi bangaren Yassar din daya dan juyo ya kalle shi yana sake mayar da hankalin shi kan tuqin da yake
"Kai ido kaman an saka ma sakwara dan yatsa, kaita qara kankance su..."
Dakuna mishi fuska Abdulkadir yayi
"Kana cewa Ma shaa Allah Hamma, kyawun idanuna yasa kuka cinye mun tun ina karami..."
Dariya Yassar yayi
"Banza. To har kai shekara wajen hudu in za'ai hoto idanuwanka basa fitowa"
Murmushi Abdulkadir yayi yana fadin
"Allah ya yafe maka..."
Dariya Yassar ya sake yi, muryar shi wannan karin babu alamun wasa yace
"Da gaske, me yake damun ka?"
Dan daga kafadu Abdulkadir din yayi, baisan me yake damun shi ba shi kanshi, kawai dai wani sanyin jiki yake ji naban mamaki, kuma ba zai cema Yassar yaso yaga Nuriyya a tsaye a kofar gidan ba, saboda bashida dalilin da zaiji hakan, bai kuma san abinda yasa yake jin hakan ba. Shiru Yassar yayi, dan ta gefen idon shi yaga Abdulkadir din ya daga mishi kafadu, ya kuma san ba sake wata magana zaiyi ba, idan wani abin ma yana damun shi sai yaga dama zai fada mishi.
"Kardai kabari koma menene ya dameka"
Yassar yace, wallet din shi Abdulkadir din yake wasa da ita, maballin yake ballewa yana mayarwa, kafin ya sauke idanuwan shi akan wallet din lokacin daya balle maballin, karamin hoto yagani a jiki, bayan shi a juye, daquna fuska yayi, a hankali yake furta
"Ba duka na bata ba?"
Dan kallon shi Yassar yayi
"Magana kake?"
Dagowa Abdulkadir yayi yana girgiza ma Yassar kai, kafin yasa dan yatsan shi ya zaro hoton yana juya shi, daquna fuska ya sakeyi ganin hoton Waheedah, kafin dariyar da baisan daga inda ta fito ba ta kwace mishi. Yana da tabbacin ko gawayi aka shafama Waheedah a fuska sai idanuwanta sun nuna alamun farinta, yanda akai ta kubcema zama zabiya abin jinjina ma Ikon Allah ne. Juya hoton yayi yasaka shi dai-dai a cikin wallet din, haka kawai ya tsinci kanshi da saka dan yatsa ya shafi fuskarta dake jikin hoton, kamar zaiga tsoron shi ya cika manyan idanuwanta.
Jiyai an fisge wallet din, da sauri ya bita da shirin kamowa, Yassar ya mayar da ita dayan bangaren yana daga cinyar shi ya saka wallet din
"Tuqi nake Abdulkadir..."
Harararshi Abdulkadir yayi
"Hamma bana so, bana so, kabani wallet dina"
Murmushi Yassar yake yi
"Meye kake shafawa da dan yatsa? Dariyar me kake kuma?"
Kankance idanuwa Abdulkadir yayi
"Ina ruwanka? Karka bude, kabani wallet dina..."
Gudun motar Yassar ya rage yana zaro wallet din daga karkashin cinyar shi ya bude, dan kallo yayi tukunna ya mayar da idanuwan shi kan titi, wannan karin shi ya daquna fuskar shi da take dauke da bayanannen mamaki ganin hoton Waheedah din
"Kabani Hamma, ni banason irin wannan. Ai zubda girma ne kana daukar abin kaninka. Ba saika ja in rainaka ba"
Abdulkadir din yake fadi yana miqa jikin shi ya fisge wallet din daga hannun Yassar ya balleta yana dan daga jikin shi ya saka a aljihu. Kallon shi Yassar yayi yana rasa abinda zai fada, sosai mamaki yakeyi.
"Karka fara abinda ba zaka iya karasawa ba Abdulkadir, karka fara"
Yassar yace da wani yanayi a muryar shi da yasa Abdulkadir din kallon shi cike da rudani
"Kar in fara me?"
Wannan karin sosai Yassar ya rage gudun motar, yana jin wanda suke bayan shi suna danna mishi hon, alamun idan shi baida gurin zuwa su suna dashi, amman bai damu dasu ba, Abdulkadir ya kalla sosai yana son karantar gaskiyar abinda yake tunanin, amman banda confusion babu abinda yake fuskar Abdulkadir din. Murmushi Yassar yayi yana girgiza mishi kai. Idan soyayya ce take shirin qulluwa a tsakanin Abdulkadir din da Waheedah bazai kara mata gudu ba tun kafin Abdulkadir din ya fahimci akwaita.
"Ni banaso a fara mun maganar da bangane ba, kasani kuma"
Gudun motar Yassar ya kara, tukunna ya amsa Abdulkadir din da
"A shaqeni a fito da sauran mana"
Wani kallo Abdulkadir din yai mishi, tukunna yakai hannu yana kunna radio din cikin motar, maganar yake qurewa da yasa Yassar bugar mishi hannun daya janye babu shiri, maganar ya rage yana fadin
"Ka qarata sai naci ubanka wallahi, ba zaka cika mun kunne ba"
Daquna fuska Abdulkadir din yayi kasa-kasa yace
"Matsala kake da ita Hamma"
Murmushi Yassar yayi
"Idan ma zagine bazan zagu a fili ba, kuma bazan daku ba..."
Gyara zaman shi Abdulkadir din yayi cikin kujerar, yana jingina kanshi da jikin kujerar. Idanuwan shi ya lumshe, hoton Nuriyya na tasowa daga inda ya samu wajen zama cikin kan shi yana bayyana a bayan idanuwan shi cikin yanayin daya sashi bude idon shi babu shiri, kallon hanya yaci gaba dayi zuciyar shi ta mishi nauyi naban mamaki.
*
A kasan zuciyarta take jin wani irin fili da tafiyar Abdulkadir tabar mata, zata rantse da Allah akwai wani bangare nata da ya tafi dashi, sai dai ba zata iya dora dan yatsa akan bangaren ba, da duk kwanakin da yake karawa da yanda take jin filin na qara mata girma. Yanzun ma hakan take ji, komai baya mata dadi, har littafin da ta fara karantawa na Biebee Isa (ke Alheri ce) tana kwasar dariyar Nenne da dinkum dinta, yau ta kasa karasawa. Sosai take jin kewar shi na danne ta. Ga ranar Alhamis ce babu islamiyya balle taje ta rage zafi. Nuriyya kuma bata nan, taje wajen dangin mamanta sada zumunci.
Kujera ta dauko ta saka a harabar gidan ta zauna, tunanin ya hadar mata biyu. Gana Abdulkadir, gana Nuriyya da takeyi, dan ta jima tana mata maganar tsoron faduwa jarabawar aji shidda, kasancewar makarantar gwamnatin ba wani tabbacin kirki gareta ba, duk da Nuriyya na da kokari, gashi tunda suka shiga aji hudu su biyun, banda darasin ingilishi da lissafi, babu abinda suke iya samu suyi ita da Nuriyyan, tunda ita Waheedah bangaren Art take, Nuriyyar kuma commerce, a cewarta tana son karantar bangaren kasuwanci dan tayi aiki da wani kamfani babba. Ita kuwa Waheedah turanci take son karanta, ta kuma koyar in ta samu hakan.
To satin aka fara biyan jarabawar aji shiddan ta Waec, batasan ta inda zata fara yima Abba maganar Nuriyyan ba, saboda batason dora mishi nauyi fiye da wanda yake kan shi, amman ta tambayo wata makaranta da babu nisa dasu, Green olive, kudin jarabawar kuma kadan zai cika a wanda zai biya mata ita kadai a Sheikh Bashir su zana anan Green Olive din ita da Nuriyya. Kamar daga sama taji an tafa hannuwa a saitin fuskarta daya katse mata tunanin datai zurfi a ciki, tana sauke idanuwanta kan fuskar Yazid dake mata murmushi har dimple din gefen fuskar shi ya bayyana.
Kaf dakin Hajja, har matan babu mai kyawun Yazid, ga sumar dake fuskar shi ta kara mishi wani kwarjini naban mamaki, abinka da wanda yake da haske fata
"Hamma Yazid..."
Waheedah ta fadi tana mayar mishi da murmushin