Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 51

45K to 48K   out of 152.3K words

a duka kafafuwa da hannuwanta, ita ta taimaka mata tahau kan gado ta kwanta, gabaki daya duniyar take ji ta tattaru a hannuwanta da kafafuwanta da suke a daure da ledoji. Ita kam bataga komai a cikin kunshi banda wahala ba. Batajin zata iya bacci da wannan ledojin a jikinta, da wannan tunanin bacci ya dauketa cike da mafarkin Abdulkadir.

*

Washegari kasancewar safiyar sallah, yanayin garin kanshi yayi sanyin da safiyar sallah ce kadai kan haifar. Tunda suka tashi suke hidimar su, Waheedah bata ga kunshin taba sosai saida gari ya fara wayewa tunda babu wutar lantarki. Kyau yai mata sosai, gashi ya kama har wani ruwan kasa-kasa mai cizawa yake. Da gudu ta taho tana rungume Amatullah da take tsaye ta baya

"Kinsan ina son ki ba?"

Ta fadi, Amatullah din na tureta

"Soyayya da sokamun kasusuwa?"

Dariya Waheedah tayi tana sake komawa ta riqe Amatullah din dake kiciniyar kwacewa gam

"Adda Wahee mana"

Amatullah ta fadi tana samu ta ture Waheedah din, da murmushi a fuskarta, Mami ce ta fito ta gansu

"Mami kalli kunshina"

Cewar Waheedah tana daga ma Mami hannuwanta, jinjina kai Mami tayi

"Ma shaa Allah. Yayi kyau sosai kuwa, yanzun kika zama yan mata"

Shagwabe fuska Waheedah tayi

"Me kike nufi Mami?"

Amatullah ta karbe zancen da amsa ta

"Kinfi kowa sanin me take nufi"

Numfashi Mami ta sauke

"Nikam ku matsamun ina da aikin yi"

Matsawar sukai ta wuce, suna rufa mata baya zuwa kitchen din. Wanke-wanke sukayi ita da Amatullah din. Sun gama kenan, Amatullah ta fice daga kitchen din, Nuriyya tai sallamar da Mami ta amsa mata tana dorawa da

"Nuriyya idonki kenan?"

Dariya Nuriyya tayi, dan kwana biyu bata shigo gidan ba, itama sunata hidimar sallah

"Wallahi Mami inata kitso ne fa. Ina kwana"

Murmushi Mami tayi

"Lafiya kalau, ya kowa da kowa?"

Da murmushi a fuskar Nuriyya take amsa Mami data fice daga kitchen din bayan sun gama gaisawa. Hijab dinta Nuriyya ta cire tana dorawa kan window din kitchen din, yanayin da yasa Waheedah kallon ta

"Naga kin cire hijab"

Kai Nuriyya ta jinjina

"Bazan cire in sha iska ba?"

Yar dariya Waheedah tayi, idan wani yaga Nuriyya ta cire hijabin zaiyi zaton aiki zata tayata, ita da yake tasan hali bata saka a rai ba, dan Allah ya zubama Nuriyya qwiya, ko aikin gida aka sakata sai ta zuba ha'inci a ciki, wani lokaci Maman su na kallonta zata tsallaketa tayi aikinta, a cewarta ko wanke-wanken Nuriyya ba fita suke ba, haka zakaga maiqo cikin kofuna.

"Ke jiya Anas yazo da daddare, saima bayan isha'i tukunna"

Nuriyya ta fadi wani tattausan murmushi na bayyana a fuskarta da yake nuna alamun Anas din ba karamar hidimta mata yayi ba. Sun hadu ne lokacin da suka kai mishi dinkin uniform din Nuriyya na Green Olive, Yazid ne ya hadasu dashi a cewar shi yakan mishi dinki wasu lokuttan, basu da nisa dashi sosai tunda suna kofar ruwa ne, shikuma yana Kurna babban layi ta wajen yan doya. Kusan tun lokacin ya manne ma Nuriyya, da yake ana barinta fita zance, sukam gidansu saika gama sakandire tukunna. Anas ya gama diploma dinshi a yanda Nuriyya take fadama Waheedah, sai dai baici gaba ba, shine babba a gidansu, kuma Allah yaima mahaifinshi rasuwa, hakan yasa yai tsaye kan sana'arshi ta dinki da take kawo mishi rufin asiri dai-dai gwargwado.

Dan a cikin sana'ar yake ma kanshi da mahafiyarshi harma da yan uwanshi duk wata hidima, duk a yanda Nuriyya take sanar da ita, yana da gidanshi na gado mai daki falle-falle guda biyu, sai bandaki da kitchen, dan in yanzun Nuriyya ta bashi dama a shirye yake daya turo a tsayar da magana. Abinda baisani ba shine ko kadan Nuriyya bata jinshi a ranta, duk da Anas bashida wata makusa a matsayinshi na matashi, yana da kyau na misali da cikar zarrah, ga nutsuwa da kamala shimfide a fuskar shi. Ko kadan Anas ba tsarin aurenta bane ba, bashi bane mijin da take buri.

Tana kulashi ne saboda hidimar da yake mata, hannun shi a bude yake, ko yaushe cikin mata hidima yake, sau biyu yakanzo a sati, duk zuwan da zaiyi da kalar kayan ciye-ciyen da zai kawo mata. Da sallar nan kaya yai mata kala uku, mayafi harda jaka da takalmi, shi yai mata dinkunan, ya kuma kawo dubu biyu ya bata tayi kitso da kunshi. Sosai Waheedah take son Nuriyya da Anas din saboda yanda yake da nutsuwa da kuma son Nuriyyan da take gani a tattare da yanayin shi.

"Turarenki yana gida..."

Nuriyya ta sake fadi tana yar dariya. Tana kara jin dadin yanda haduwa da Anas take bata damar yima Waheedah kyauta irin haka.

"Dan Allah fa... Turare ya kawo miki?"

Waheedah ta tambaya cike da jin dadi itama, kai Nuriyya ta daga mata

"Har guda uku ma"

Dan bude baki Waheedah tayi

"Aikam baki isa ba saina zaba... Mai kamshin cikin nake so"

Yar dariya Nuriyya tayi

"Banza in munje gidan duk wanda kike so saiki ta dauka. Ina da wasu ai"

Karasa share kitchen din Waheedah tayi suna hirar Anas din da Nuriyya

"A fara poly Anas ya turo musha biki"

Hade fuska Nuriyya tai waje daya

"A'a kin manta, uwar biki zaku sha"

Dariya Waheedah takeyi

"Ki daina mun wannan wasan, nace miki ina son shine?"

Kai Waheedah take girgiza mata

"A'a amman kina karbe mishi kaya ai, wallahi Nuriyya kar Allah ya kamaki"

Tsaki Nuriyya taja tana daukar hijab dinta daga kan kofa tana sa Waheedah tambayar ta

"Ina zakije?"

Ko kulata Nuriyya batai ba, ta saka hijab dinta, dan ta gama bata mata rai, wato fatan ta auri Anas take mata, dan karta huta. Ko a hanya aka ganta ansan batai kalar auren tela ba, diplomar da yake da ita ya fada mata bashida niyyar cigaba, tunda yana da tsayayyar sana'a, ita kam sai wanda yake zuwa office, babu abinda zatai da tela.

"Hamma yazo..."

Waheedah ta fadi cikin sanyin muryar da yasa zuciyar Nuriyya wani irin dokawa, da sauri ta juyo

"Haba dai..."

Kai Waheedah ta girgiza mata

"A'a ki tafi, ba tafiya zakiyi ba?"

Dan murmushi Nuriyya ta dora kan fuskarta

"Dallah ai kece kike son batamun rai. Ban labari yaushe Hamma din yazo?"

Wannan karin wani tsadadden murmushine ya bayyana kan fuskar Waheedah

"Allah Nuriyya ina son shi fa..."

Wani zafi Nuriyya taji kirjinta ya dauka, ta fada mata kwanaki, bata kulata bane, saboda tayi kamar sai lokacin tasan tana son Abdulkadir, batasan meyasa take maimaita mata ba yanzun

'In shaa Allah ba zaki taba samun shi ba'

Nuriyya ta fadi a cikin ranta, a fili kuma tabe baki tayi tace

"Kina da hankali kuwa?"

Narai-narai Waheedah tayi da idanuwa, ita kanta tasan batada hankali, ta kuma san ta rungumowa kanta dala ba gammo

"Bansan yazan ba Nuriyya. Nasan banda hankali, shisama ban taba tunanin samun shi ba, kawai dai nasan ina son shi"

Ta karasa maganar muryarta cike da rauni

"Yafi miki alkhairi..."

Nuriyya ta fadi a taqaice tana dorawa da

"Bari inje gida... Zan dawo anjima"

Dan batasan Abdulkadir ya dawoba da ba zata shigo gidan haka ba, sauri zatayi taje gida tai wanka ta tsara kwalliya tukunna ta dawo, batasan me yasa ba, haka kawai taji bataso yaganta batare da tayi kwalliya ba. Kai kawai Waheedah ta iya daga mata dan batajin zata iya wata magana, tunanin Abdulkadir ya cika zuciyarta fal.

*

Yassar na kula da yanayin Abdulkadir din tun jiya da yaje dauko shi, dayake sunyi waya a bakin gate ya same shi tsaye da jakar shi, batare da yace ma Yassar din komai ba ya zagaya ya shiga mota. Hannu ya saka ya kunna radio din motar cikin nuna ma Yassar din alamar bayason yin magana. Haka daren jiya duk wanda yazo dan su gaisa da masifa Abdulkadir din yake amsa su, kamar sannu da zuwan nasu na kara mishi bacin ran da Yassar ya kula yazo dashi. To yau ma da alama da yanayin ya tashi, shisa tun asuba bai koma dakin nashi ba, duk da zai karya idan yace abin bai dame shi ba.

Maballan kayansu da tela bai saka musu ba Yassar din yake sassaka musu a jikin riguna, daga shi sai Aminu a falon, dan duk yawanci sun faffara shiga wanka. Abdulkadir ne ya fito daga shi sai singlet da gajeran wando

"Ina kwana Hamma..."

Aminu ya gaishe dashi sanin halin shi, shiru Abdulkadir din yayi, hakan yasa Aminu sake gaishe dashi dan a zaton shi ko baiji bane, daquna fuska Abdulkadir yayi

"Karka dameni Aminu, meyasa zaka fara gaisheni tunda sassafe"

Numfashi Aminu ya sauke yana jinjina kanshi kawai, da idanuwa Yassar yai mishi alama da yabar falon, bai musu ba ya miqe ya nufi dakinsu, saida ya shiga ya turo kofar tukunna Yassar da bai dago daga maballin da yake sakawa ba yace

"Me yake damunka?"

Zagayawa Abdulkadir yayi ya zauna inda Aminu ya tashi, bayason yin magana, bayaso ai mishi magana, komai baya mishi dadi

"Da kai nake, me yake damunka?"

Yassar ya sake tambaya wannan karin yana sauke idanuwanshi kan fuskar Abdulkadir da babu alamar walwala a tare da ita

"Karka dameni Hamma, dan Allah. Gidane ban niyyar zuwa ba"

Rigar dake hannun shi Yassar ya ajiye yana mayar da hankalin shi kan Abdulkadir din

"Ubanwa yace ka daga waya ka kirani inzo in daukeka to? Idan kasan bakai niyyar zuwa ba saikai zamanka...meyasa zaka zo kana ma mutane bakin rai, ubanka akai maka?"

Yassar yake fadi dan shima ranshi ya fara baci, hakan Abdulkadir ya kula dashi yasa shi fara shirin mikewa dan yabar wajen

"Wallahi idan ka tashi ranka saiya baci, ka zauna ban gama maganar da nake ba..."

Komawa Abdulkadir yayi ya zauna, karshen abinda zaiso a yanayin da yake ciki shine bacin ran Yassar din, yana da zuciya yasani, abinda yake bata mishi rai a kusa yake, amman yana sauka da wuri, wasu lokuttan idan yai duka ko yai fada shikenan. Amman na Yassar daban ne, yakan jima ranshi bai baci ba, amman idan ya baci duka gidan sai hankalin kowa ya tashi

"Meke damunka? Bazan sake maimaitawa ba"

Numfashi Abdulkadir ya sauke yana rasa amsar dazai ba Yassar din, bashida wata kwakkwarar amsa, me zaice mishi? Ranshi a bace yake saboda zuciyarshi nason ja mishi abinda su dukansu bazai musu dadi ba? Ko kuma fada mishi zaiyi yanda yake ta kokarin ciro Nuriyya daga duk inda take a cikin jikinshi kafin ta zame mishi matsala amman ya kasa? Wanne daga ciki zai fada mishi da bazai mishi kallon marar hankali ba, ko zai fada mishi yanda Waheedah ta saka shi zuwa gida bai niyya ba, yanda alkawarin dayai mata yai mishi tsaye a wuya saida ya janyoshi garin kano. Amsar da tafi mishi sauki yaba ma Yassar din

"Bansani ba, komai bayamun dadi"

Numfashi Yassar ya sauke, yanayin da Abdulkadir din yai maganar na saka bacin ran da yake ji soma dishewa.

"Kayita istigfar, tana yaye damuwa"

Kai Abdulkadir ya jinjina mishi yana mikewa tsaye

"Bari inyi wanka... Kayana fa? An dinkamun?"

Dan kallon shi Yassar yayi

"Da bikin su Hamma ai masifa kaimun, na maka dinkin da bai maka ba...."

Daquna fuska Abdulkadir yayi

"Da wanne kayan zanje sallar idi?"

Dan daga mishi kafadu Yassar yayi

"Bakazo da kaya ba?"

Idanuwa ya kankance ma Yassar

"Gajerun wanduna ne fa..."

Maballan shi Yassar yaci gaba da sakawa, ganin AbdulKadir din na tsaye har lokacin yasa shi fadin

"Kamun tsaye a kai"

Da mamaki Abdulkadir yace

"Hamma da gaske baka dinka mun ba?"

Wani kallo Yassar ya watsa mishi daya tabbatar mishi da gaske yai maganar. Kuma da gangan yaki dinka ma Abdulkadir din kaya, saboda rashin kunyar dayai mishi wancen karin, har cayai shi bazai saka wasu manyan kaya ba. Ya fadama kanshi bazai sake dagama Abdulkadir din hannu ba, tunda ba yaro bane yanzun, amman hakan baya nufin bazai nuna mishi kuskuren shi ba. Yana jin Abdulkadir din ya wuce, danko dagowa baiyi ba, ya saka daya daga cikin nashi kayan, idan zasuyi mishi kenan, dan yaga ya kara budewa...!

*#TeamAbdulkadir*
*#TeamYazid*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: ©️
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com

*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*

12

Da kayan shi rungume a kirji ya shiga dakin hadi dayin sallama, bai samu kowa a falon ba sai Yassar daya amsa mishi sallamar yana kuma binshi da kallo yana fadin

"Meye a jikin kayan daka rungumosu kamar sabon jariri?"

Murmushin shi Yazid ya kara fadadawa, Waheedah ta goge mishi kayan, akwai kalar kamshin da ya kula tana yi duk idan ta gifta shi a cikin gida, idan zata fitane kawai bayajin yana kamshin, sosai kuma yake jinjina ma kokarinta na wajen ganin ta gujema abubuwan da addini ya haramta mata da mata kan dauka kananun zunubi a zamanin da ake ciki. Haka kawai yau da ita ya tashi manne a ranshi fiye da kowanne lokaci, shisa yakai mata kayan yace ta danne mishi ta kuma shafa mishi turare. Tunda ya amso yake jin kayan har kasan zuciyar shi.

"Hamma..."

Yassar ya fadi ganin yanda murmushin Yazid din yake kara fadada da duk dakika.

"Karka dameni Yassar"

Yar dariya Yassar yayi, harda shi cikin yan gidan wajen yima Yazid surutun kin nemo matar aure, amman yanayin da yake nunawa yanzun kamar na sabon kamu a soyayya

"Anya Hamma? Baka kamu ba kuwa?"

Dakuwa Yazid din yai mishi, yana tsintar kanshi da jin wata irin kunyar kanin nashi da ta bashi mamaki. Sosai Yassar yake dariya yanzun kam

"Yaa Rabb... Hamma da gaske soyayya kake? Wace mai sa"ar ce?"

Ya karasa tambayar da farin ciki nannade a muryarshi, a kasan ranshi harya fara addu'a da fatan ta gari ce, akance ba'a shaidar mutum, amman zai tashi tsaye yai shaidar dan uwan shi, duk a cikin gidan Yazid ne kawai zai bada shaida akan shi batare da wani shakku ba, ya yarda da nagartar shi dari bisa dari. Yana da tabbacin matar da duk zata kasance karkashin kulawar shi ba zata taba samun dalilin yin koke ba. Yazid mutum ne mai hakuri da kauda kai akan al'amuran duniya.

"Wacece Hamma? Kaji? Dan Allah wacece?"

Yassar ya sake jero mishi tambayoyin yana saka shi sauke numfashi mai nauyi. Bai taba fadama kowa sirrin da yake zuciyarshi ba, har ita Waheedah din da sirrin ya shafa, amman yau yana jin ya fada ma wani, yana kuma jin son raba sirrin da wani, watakila ya samu karfin gwiwar fadama Waheedah din itama. Ya kuma san Yassar na da sirri ba kadan ba, idan bashi yace ya fadama wasu ba, maganar ba zata taba wuce tsakaninsu ba. Cikin sanyin murya Yazid yace

"Bata sani ba har yanzun ai"

Dan ware idanuwa Yassar yayi

"Jiran me kake to? Meyasa baka fada mata ba?"

Kafadun shi duka biyun Yazid yadan daga cikin yanayin dake fassara shima baisan dalili ba

"Ina ganin kamar tayi yarinta ne, hakan nake fadama kaina saboda banason tabbatar da na rasa karfin gwiwa ne"

Fuskar Yassar dauke da murmushin fahimta yace

"Ba'a yarinta da sanin 'So' Hamma, saboda abune mai wahalar sha'ani..."

Kai Yazid ya iya jinjina ma Yassar din, yanajin jikin shi yayi wani irin sanyi, da gaskene ya kamata Waheedah tasan yanda yagama tsara musu sauran rayuwar shi idan yana da rabon gani, bai taba hango komai na rayuwar aure da wata idan ba ita ba. Ko a titi yaga budurwa da saurayi, ita ce take fado mishi a rai. Idan kallo yake yaga wani abu daya burgeshi, da ita yake hasaso aiwatar dashi. Yana mata kyauta lokaci zuwa lokaci, amman yana jin tamkar ya janyo ranar dazai kashe mata duka kudin da suke cikin aljihun shi, ranar da zai siyo duk rigar daya gani yake tunanin zatai mata kyau ya kawo ta saka mishi yagani.

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskarta na mishi yawo a cikin kwanyar shi, wucewa yayi da niyyar shiga daki ya sake kaya, Yassar dakatar dashi da fadin

"Ka fadamun sunanta idan ban santa ba"

Saida ya murza hannun kofar dakinsu tukunna yace

"Waheedah... Waheedah ce Yassar"

Wani dum Yassar yaji cikin kanshi, kafin hanjin cikin shi su hautsina suna saka shi mikewa babu shiri ya rufa ma Yazid din baya. Yanda ya tura dakin na saka Yazid din tsorata, wani irin yanayi yake gani a fuskar Yassar daya saka zuciyarshi soma dokawa yana fadin

"Yassar?"

Cike da shakku da alamar tambaya, kai Yassar yake girgiza ma Yazid din yana son ya tabbatar mishi ba Waheedah bace yake so, yana son ya gaya mishi bai hada soyayya da Abdulkadir ba, kallon Yazid din yake da idanuwan shi yana rokon shi da cewar zuciyar shi batai mishi haka ba.

"Yassar..."

Yazid ya sake kira wannan karin muryar shi na rawa cike da tsoro, ko kadan bayason abinda tunanin shi yake shirin hasaso mishi, hannu yadan daga ma Yassar din yana saukewa, kafafuwan shi har rawa yake jin sunayi dan shi mutum ne mai raunanniyar zuciya. Gadon da yake dakin ya laluba ya zauna a gefe, yanajin yanda zuciyarshi ke dokawa har cikin kunnnuwan shi. Yanayin shi kawai da Yassar yake gani na kara tabbatar mishi da yanda ya dade da soyayyar Waheedah adane a cikin kirjin shi batare da kowa yasani ba. Wani abu Yassar din yaji yana danne shi, yanda akai bai kula ba na bashi mamaki, dan shi mutum ne mai kula da al'amuran yan uwan shi. Cikin wani yanayi yace

"Hamma..."

Yana tsintar bakin shi da yi mishi nauyi wajen karasa maganar da yake sonyi. Halin da Yazid din zai shiga yake tunani. Amman ko jiya da yana neman canji, bayan Abdulkadir din yazo ya dauki wallet din shi ya bude hoton Waheedah na jiki a manne, ya kuma ga ya sake wallet din, amman hoton na manne. Yasan kanin shi, yasan kanin shi fiye da kowa a gidan. Idan har ya cire hoton Waheedah daga dayar wallet din ya mayar a sabuwa tana da muhimmanci a wajen shi, idan har zai ajiye hoton daga farko to yana da tabbacin wani abu na faruwa a tsakaninsu. Idan har zai iya bazai bari su hada yarinya daya da Yazid ba, yana numfashi bazai taba bari wannan rikicin ya faru ba.

"Dan Allah Yassar kace wani abu, a tsorace nake wallah"

Yazid din yace yana sa wani abu tsagewa biyu a kirjin Yassar din, da yake tsaye yana tattaro duk wani karfin halin dazai iya

"Ba Waheedah ba Hamma, kowacce yarinya banda ita"

Kai Yazid din yake girgiza mishi yana jin iskar dake dakin na fara yi mishi kadan, cikin sabon tashin hankali yace

"Yassar..."

Da sauri Yassar din ya girgiza mishi kai, ganin yanayin da yake fuskar shi, ya tabbatar Yazid na tunanin shine yake son Waheedah

"Bani bane, Hamma bani bane ba"

Kan shi Yazid yadan dafe da ya fara ciwo, yanajin alamar zazzabi nason rufe shi

"Abdulkadir ne, ba zance soyayya suke ba kai tsaye, amman

16 / 51