Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
macen tayi hakuri, cikin masu mata rashin adalcin harda yan uwanta mata, su da ya kamata su fahimci halin da take ciki fiye da kowa. Shisa Hajja take ganin a duniya babu babban munafuncin da mata suke yaudarar kan su da shi sai fadin
'Ciwon 'ya mace na 'ya mace ne'
Dan yanzun da take zaune a gaban AbdulKadir take kara karyata zancen, badan bataji zafin abinda yaiwa Waheedah ba, ta kwatanta kanta da Waheedah ta kuma san ko kusa ba zata dauki abinda Waheedah ta dauka ba, idan bata mutu ba, auren nata zai mutu. Har kasan ranta kuma take jin da Waheedah din Zahra ce da wahalar gaske idan bataje ta dauko 'yarta ba. Amman ba Zahra bace, Waheedah ce, kuma a wannan gabar danta take ji fiye da ita, ciwon 'ya mace kan zama na 'ya mace ne kawai idan akwai samun riba a cikin al'amarin, shisa munafunci ne kawai a fadin hakan.
Waheedah take so tayi hakuri ta yafe ma AbdulKadir, dan kuwa ba zata jure ganin danta a cikin wannan halin ba, hakan yasa ta fadin
"Yassar zaka dan zauna da shi inje in dawo?"
Kai Yassar ya jinjina mata, ya sanar a wajen aikin shi, babu inda zai iya zuwa in ba gani yayi AbdulKadir din yaji sauki ba. Tun farko abinda yake mishi gudu kenan, amman AbdulKadir bayajin magana, taurin kan shi sai Allah, abinda zuciyar shi ta gaya mishi dai-dai ne shi yake aikatawa, bai taba zaton zai kwatanta ba Waheedah hakuri ba sai yanzun, yana kuma jin son kai da rashin son gaskiyar da yake cikin hakan, bai damu bane kawai.
"Kabani mukullin motar ka"
Babu musu Yassar ya dauka ya mika mata, karba Hajja tayi tana mikewa. Yassar yabita da kallo ganin babu takalma a kafarta, baice komai ba, ya koma inda ta tashi yana zama ya saka idanuwan shi a kan AbdulKadir da duk motsin da zaiyi sunan Waheedah ne a bakin shi, Yassar na jinjina ma kaddarar su, ya dauka yasan zafin so a kan Hauwa, yanzun AbdulKadir da Waheedah ke nuna mishi bakomai suka sani ba a soyayya, dan tasu kalarta daban ce.
*
Rabonta da gidan Yassar tun lokacin da matar shi tayi bari, da yake yarinyar ta sha wahala sosai. Bata kuma zata zatazo gidan batare da wani dalili da zai kasance ya shafi Yassar din ko Hauwa ba, bata taba tunanin dalilin AbdulKadir zaisa tazo gidan Yassar din ba, a kofar gida tayi parking din motar, tunda tasan inta gama abinda takeyi sake fita zatayi, bataga wahalar saita shigo da motar ba. Tsakuwoyin da ta taka na tuna mata cewar babu takalma a kafarta, haka ta shiga cikin gidan, maigadin kan shi kallon ta yake dan yana da tabbacin ba lafiya ba.
Har cikin gidan ta shiga, taci karo da Waheedah da take fita daga kitchen din, itama Ikram zata wankema jiki ta sake mata pampers taji ruwan da sanyi, tausayi yarinyar ta bata shisa ta dafa, tana sake mata kuma bacci ta koma, shine ta fito ta kawo kettle din taci karo da Hajja, sai da zuciyarta ta doka, musamman yanayin Hajja din
"Hajja..."
Waheedah ta kira cike da shakku da alamar tambaya, inda take Hajja ta karasa
"Alfarma na zo roka Waheedah"
Hawaye Waheedah taji sun cika mata idanuwan da suke a kumbure suna zubowa a hankali
"Nasan zaki ce na so kai na, zaki ce na duba bukatar 'dana sama da taki, amman banda wani zabi... Wallahi yanzun ma yana asibiti, faduwa yayi Waheedah"
Hajja ta karasa maganar muryarta na karyewa, wasu hawayen Waheedah taji sun kara zubo mata, muryarta a sarqe cike da kuka tace
"Hajja nima naje asibitin gado zasu bani"
Kai Hajja ta jinjina mata
"Nasani, kiyi hakuri, dan Allah kiyi hakuri, ki duba yanda ya koma cikin sati daya... Kina tunanin zai iya rabuwa dake? Bakomai yake raunana AbdulKadir ba, banma taba ganin abinda ya saka shi shiga yanayi haka ba... Shisa na zo in baki hakuri, koma menene yai miki dan Allah kiyi hakuri"
Hannu Waheedah tasa tana goge fuskarta, amman wasu hawayen ke zuba, itakam hakurin ne bataso su bata, saboda zuciyarta harta fara karyewa, musamman da Hajja ta dafa kafadarta fuskarta cike da roko tana fadin
"Ki yafe mishi dan girman Allah, ki duba rokona Waheedah..."
Kuka Waheedah takeyi, hakan yasa Hajja ta riketa a jikinta, kaddarar yaran na tsaya mata, ita kanta Waheedah din a idanuwanta zaka ga rauni, AbdulKadir dinne ya tabata sosai, amman rabuwa dashine karshen abinda take bukata. Cikin kuka tace
"Hajja bansan ya zanyi ba... Ban sani ba nikam"
Riketa Hajja tayi sosai
"Hakuri zakiyi, kiyi hakuri... In yayi abinda ya nuna miki ke din bakida muhimmanci halin daya shiga yanzun ya isa ya karya shi... Ke dince rayuwar shi Wallahi..."
Kai Waheedah ta girgiza tana kin yarda da kalaman Hajja, wani kishi naban mamaki na turnuqe zuciyarta, da itace rayuwar shi da bai hadata kishi da Nuriyya ba, da itace rayuwar shi da bai ci mutuncinta ya auri aminiyarta ba. Dagowa tayi daga jikin Hajja tana saka hannuwanta duka ta share hawayenta
"Waheedah..."
Hajja ta fadi tana rasa da kalaman da zatayi amfani dasu dan rikici take gani shimfide a idanuwan Waheedah din, da gaskiyar mutane ka guji bacin ran mai hakuri
"Jinin shi ya hau"
Hajja tace tana saka Waheedah rausayar da kai, cikin sanyin murya tace
"Nima hawan jinin nake fama da shi Hajja"
Hawaye na zubar mata, duk idan tayi zaton hawayenta sun kare sai wani abin ya sake faruwa da zasuci gaba da zuba kamar an bude fanfo, numfashi Hajja taja tana fitar dashi kafin tace
"Shikenan Waheedah, Allah ya zaba muku abinda yafi alkhairi"
Ta juya tana ficewa daga gidan. Daki Waheedah ta koma ta dauki wayarta, kuka take har bata ganin abinda ke rubuce a screen din wayar sosai, saida ta goge fuskarta tukunna ta lalubo lambar Abba ta kira, bugun farko ya daga da fadin
"Waheedah..."
Wani irin kuka ta rushe dashi da yasa Abba cewa
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un... Waheedah me ya faru? Menene? Me akai miki?"
Ta dayan bangaren, kana jin tashin hankalin dake cikin muryar shi, numfashi take fitarwa kamar zata shide saboda kukan da takeyi
"Ab....Abba..."
Ta iya fadi dakyar tan dorawa da
"Kowa nata bani hakuri... Abba har Hajja hakuri take bani, zuciyata ciwo take mun Wallahi... Dana tuna zuciyata ciwo take mun... Ab...Abba bansan ya zanyi ba"
Tanajin ya sauke numfashi, cikin taushin murya mai cike da lallashi yace
"Kiyi duk abinda zuciyarki zata nutsu da shi, karki bari hakurin da suke baki ya saki yin zabin da zaki cutu, karkuma ki bari fushinki yasa kiyi zabin da ba zakiyi dana sani"
Kai Waheedah take jinjinawa tana goge fuskarta da bayan hannunta
"Kina jina?"
Abba ya fadi yana sa ta sake jinjina mishi kai
"Zan zo in dubaki anjima, ki samu ruwa ki sha, ki daina kuka kinji Waheedah? Komai zaiyi dai-dai"
Kai ta jinjina tana kara goge fuskarta, batace komai ba ta sauke wayar daga kunnenta, bata samu damar sanin mahaifinta ba, amman Abba ya bata kauna da kusancin da ko mahaifinta jinin shi dake yawo a jikinta ne kawai zai nunawa Abba. Abu biyu ta sani, zuciyarta na mata ciwo na gaske na biyun a fili ta fade shi
"Kin yi kadan in bar miki mijina Nuriyya... Nabar miki abubuwa da yawa a rayuwata, ban da shi, banda Sadauki na..."
Ta goge hawayen da suka zubo daga zuciyarta tana jin wani irin karfin gwiwa da bata taba jin irin shi ba...!
#LubnaSufyan
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
30
Hauwa A Usman Jiddarh
Nagode da kauna
Kunshin hannunta da yake rike cikin na farin matashin saurayin ya fara bi da kallo, kirjin shi na zafi kamar zai bude, kafin yaga saurayin ya mika kai saitin kunnen Waheedah yana rada mata wata magana da tasa tayin dariyar nan tata da take kashe mishi jiki. Baisan ya karasa wajen ba saboda wani irin kishi daya turnuqe shi har duhu-duhu yake gani, tsakanin su ya shiga yana huci kamar kububuwa.
"Lafiya?"
Saurayin ya fada yana kallon AbdulKadir din kamar yaga mahaukaci.
"Lafiya kake tambayata? Bakasan matata bace dan ubanka?"
Dariya saurayin yayi data kara bata ma AbdulKadir din rai
"Ka saketa din, na aura kana fadamun matar..."
Bai karasa maganar ba AbdulKadir din yakai mishi wani irin naushi a baki
*
Duka Yassar yakai ma AbdulKadir din da saura kadan ya gabje mishi hanci, duk da haka ya same shi kadan a gefen mummuqe, wani dukan ya kara jibga mishi yana fadin
"Tashi.... Ka warke shisa zaka kwantar dani ba..."
Mikewa AbdulKadir yayi yana dafe kan shi da yake sarawa, a zuciyar shi yake karanto
'Inalillahi wa ina ilaihi raji'un'
Yana neman tsari daga muguwar kaddara, tari ya sarke shi da yasa Yassar din mika hannu ya dauko robar ruwan da take gefe ya mika ma AbdulKadir din, da sauri ya karba yana sha. Kishine yake turnuqe shi har lokacin, kowanne mahaukaci ne yake tunanin zai saki Waheedah ya aura yana fatan yazo da bargo da filo, dan zaici gaba da kwana a wajen ne, in yagaji ya kara gaba. Karin ruwan da yake daure a hannun shi ya kalla yana son tuna lokacin da suka zo asibiti
"Karka kara tsoratani haka AbdulKadir, idan kana so in goyi bayanka ka zamana mai gaskiya, karka kara tsoratani haka"
Yassar ya fadi muryar shi can kasan makoshi, yanajin yanda har lokacin zuciyar shi bata daina rawa ba. Ganin AbdulKadir din a kwance ya tsorata shi fiye da tunani, ya tuna mishi duk wani dalili da yasa bayason uniform din shi, a lokaci daya kuma ya tuna mishi da soja ko ba soja ba, mutuwa babu ruwanta, ba zabe take yi ba, kowa nata ne, lokaci kawai take jira ta cika aikin ta.
"Ashe kana so na"
Cewar AbdulKadir da murmushi a fuskar shi duk da kirjin shi da yake ciwo, hararshi Yassar yayi da yasa ya karayin dariya, sautinta na dirar mishi a kunne da wani irin yanayi
"Zuciyata namun ciwo Hamma"
AbdulKadir ya fadi yana dorawa da
"Kaman zata fito daga kirjina haka nake ji...amman Waheedah tace mun haka ta dinga ji harna wata takwas, Hamma ta ina zan fara bata hakuri? Ta ina? Yau kawai na fara jin hakan amman inajin kamar lokacin mutuwa yazo gab... Wanne irin karfin hali gare ta?"
Kallon shi Yassar yake, yana jin kuncin dake tattare da muryar kanin na shi da yake tabashi sosai da sosai
"Kayi kuskure AbdulKadir... Bance maka nayi dana sanin zama sanadin daka auri Waheedah dan bana son zaman ku ba... A karo na farko kasa naji dana sani nabar Hamma Yazid ya aure ta"
Da mamaki AbdulKadir yake kallon Yassar din yana jin maganganun shi sun dirar mishi kamar saukar ruwan da babu hadari
"Hamma Yazid?"
Ya maimaita cike da alamar tambaya, kai Yassar ya jinjina mata
"Yana son ta, ya sota a lokacin, ni na fada mishi kuna soyayya saiya hakura... Shisa yai nisa da Kano..."
Wannan karin ruwan da yake hannun shi AbdulKadir ya fisge duk yanda Yassar din ya kira sunan shi, kafafuwan shi ya sakko daga kan gadon yana jin shi wani sama-sama. Yazid ya so Waheedah? Ko kadan kwakwalwar shi ta kasa yardar mishi da maganar, muryar shi can nesa cike da tuquqin kishi yace
"Me yasa ta aure ni to? Tunda yana son ta"
Ya karasa maganar yana kallon Yassar din kamar zai rufe shi da duka, numfashi Yassar ya sauke
"Ka taba ganin son wani a idanuwan ta? Bai taba fada mata ba, bata taba son shi ba, kishin banza da wofi zaka nuna yanzun? Kana kishinta amman baka iya kula da damuwar ta ba"
Runtsa idanuwa AbdulKadir yayi yanajin kamar Yassar ya watsa mishi ruwan zafi, kafin ya bude su a kan shi da fadin
"Karka karamun ciwon da nakeji"
Kujerar shi Yassar yaja yana matsawa gab da AbdulKadir din sosai
"Ba Hamma Yazid ya so Waheedah zaka duba ba AbdulKadir, ka duba yanda ya zabi farin cikin ka a kan nashi, ka duba yanda mu duka muke a shirye da dora farin cikin ka akan namu, ka fara yarda da fadanmu ba nuna isa bane a kanka, fadan mu na tare da yanda muke son ka"
Wannan karin kamar AbdulKadir din zaiyi kuka yake kallon Yassar, idanuwan shi sun kara kankancewa
"Sau nawa abinda nayi yai hurting din ku? Rashin tunani da rashin duba abinda halayena suke yiwa na kusa dani, Hamma sau nawa?"
Dan murmushi Yassar yayi
"Ba zai lissafu ba"
Ya amsa a taqaice yana sa AbdulKadir din runtsa idanuwan shi yana bude su, zuciyar shi na wani irin ciwo
"Harda su Hajja ko? Halayena na taba su suma"
Kai Yassar ya daga ma AbdulKadir din da dan murmushin karfin hali a fuskar shi
"Ta ina zan fara? Taya zan fara baku hakuri Hamma? Ban taba tunanin nan ba, ban taba tunanin dan nayi abinda ni ya shafa zai taba mutanen da nafi kusanci da su ba, mutanen da nake kauna da dukkan zuciyata"
Numfashi Yassar ya sauke
"Ka fara da sauraren shawarwarin mu, ko da baka dauka ba, ka nuna mana yanda muka isa ka saurara"
Kai AbdulKadir yake jinjina, kome suke so shikam zaiyi, tunanin yana cutar dasu ba karamin karyar mishi da zuciya yake ba
"Ka bude bakin ka kaba Waheedah hakuri, tana son ka, shisa kishinka yai mata yawa..."
Kai AbdulKadir din ya sake jinjina, muryar shi a karye yace
"Bansan ya akai kuke so na ba har yanzun Hamma, bana tunanin idan nine a matsayin ku zan manta duk abubuwan nan inci gaba da zama daku"
Wannan karin murmushin Yassar daga zuciyar shi ya fito
"Ba zabi aka bamu ba kafin ka kasance dan uwan mu, akwai alakar da bata baka wannan zabin, haka kaunar da muke maka, ba muna tare da kai dan mun manta abubuwan da kayi da bamu so ba, muna tare da kai saboda mun yafe maka hakan tun kafin kagane kuskure ne ka roke mu"
Hannu AbdulKadir din yakai yanajin kamar maiqo a gefe-gefen idanuwan shi, yasa yatsun shi yana dangwalowa, Yassar din naci gaba da fadin
"A kasan duk rashin kunyar ka, dan uwane kai da ko an bani zabi bazan taba daukar irin shi ba, kana da halaye da bana so, halayen da zanso ka sake su, amman shine cikar dan adam din, duk idan zamu fadama kan mu gaskiya akwai halayen da muke dasu da muke son canzawa saboda ba masu kyau bane ba"
Ya dauka zuciyar shi tagama karyewa da maganganun Waheedah, sai yanzun da yakejin hawayen daya dauka sunyi bankwana dashi cike taf da idanuwan shi, kaunar Yassar din na taba shi tana karya sauran abinda ya rage a zuciyar shi, ko yau rayuwa ta kare mishi yana da tabbacin kaunar su zata cigaba da samun shi a kabarin shi, saboda addu'o'in su ba zasu taba yankewa ba. Baisan ya mike daga kan gadon ba saida yaji Yassar yasa hannu yana ture shi ya mayar dashi ya zaunar
"Rungumeni za kai dan ubanka? Meye haka? A india muke ko America? Bana son iskancin banza da wofi fa"
Dariya AbdulKadir yake sosai yana goge idanuwan shi da yakeji cike da hawaye
"Nagode Hamma"
Ya fadi da dukkan zuciyar shi, kai Yassar ya daga mishi, AbdulKadir din na dorawa da
"Kai musu magana su zo su sallameni, ni bazan kwana anan ba"
Kallon shi Yassar yayi
"Faduwa fa kayi AbdulKadir..."
Kafadun shi duka biyun ya maqale ma Yassar
"Wallahi Hamma bazan kwana ba, in basu sallameni ba zan tafi da kaina"
Kai kawai Yassar ya girgiza hadi da sauke numfashi ya mike, mai hali akace baya taba canzawa, akwai halayyar AbdulKadir din da a jinin shi take, bazai iya canza ta ba, taurin kai na cikin wannan
"Kai kam ko Sheikh Mufti aka saka a ruwa aka girgiza aka baka kasha kayi wanka ba zaka canza hali ba Wallahi"
Dakuna mishi fuska AbdulKadir din yayi yana hade girar sama da ta kasa, babu wanda zai saka shi zama a asibiti, banda zazzabi bayajin komai, sai ciwon kai sama-sama, kirjin shi da yakeyi kamar zai bude ba asibiti yake bukata ba, Waheedah yake bukata, in ya riketa a jikin shi zai samu saukin duk wannan abubuwan da yake ji. Da ido yabi Yassar din harya fice daga dakin, kafin ya sauke ajiyar zuciya yana jin tunanin Waheedah daya baibaye shi.
*
Ruwa ta watsa bayan tafiyar Hajja, ta sake kaya. Wata nutsuwa take ji data kwana biyu bataji irin ta ba, WhatsApp dinta ta bude tana shiga sakon da Hauwa ta turo mata na littafin Farin Wata na Zahra Tabi'u.
'An saka mata sunan mace ba dan ana tunanin ita din cikakkiyar mace bace'
Ta karanta layin farko, maganganun na saka ta tunani barkatai, tun daga kan maitafiya take son marubuciyar, saboda tana tabo labaran da bako yaushe ake tabo su ba a cikin duniyar rubutu, tallar kawai ta ja hankalinta sosai. Dari uku batai mata tsada ba, account number din ta dauka tana tura kudin kafin ta dauki lambar marubuciyar 08065156303 dan ta tura mata shaidar biya. Tana karasawa ta mike, tana tunanin shiga kasuwane dan tayi siyayyar azumi tunda yau dinne ake sa ran fara duban fitowar watan, duk da anata gardama kan hakan kamar ko da yaushe.
Abin na daurema Waheedah kai, yanda ake shafe watanni goma cir ana tafiya kai a hade, sai ance watan Ramadan ya gabato sai a fara rikici kan lissafi, yanda aka saki sunnah da Manzo SAW ya doramu a kai na tsoratar da ita, shisa abubuwa sukai mana yawa, wahalhalun mu suka yawaita. Shagon da takanyi siyayyarta guda dayane, dan sun saba sosai, lokutta da dama duk abinda take so ma list takeyi saita tura musu text, wanda sai an shiga kasuwa cikin yaran shagon ake sakawa yaje ya siyo mata, kafin ta shiga duk sun hada mata kayayyakinta, kudin kawa za tayi musu transfer, sai a nemo mata mai napep a saka mata kayan a baya. Wasu lokuttan kuma mai napep din da taje dashi ne bata sallama.
Yanzun ma komawa tayi ta zauna tana tunanin abubuwan da take bukata, list dinsu tayi gabaki dayan su, sai doya da dankali da ta saka na adadin da zasu siyo mata, daya daga cikin yaran shagon Tasi'u ta kira, bazai wuce shekaru sha tara ba, amman hankalin shi har mamaki yake bata, ga girmama mutane, tace ya duba whatsapp din shi ga kayyakin da za'a hada mata nan, yanzun zata shigo kasuwar, ya kuma taimaka inda yakan siyo mata doya da dankali ya siyo mata doya ta dubu biyu sai dankali na dubu uku. Tasan zata kwana biyu bata nema ba.
Kayan su ta