Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
Kofar gidansu babur din ya ajiye shi, ya sallame shi, yana saka canjin a wallet zai mayar aljihu ya hango Nuriyya tsaye ita da wani a bakin motar shi. Ko babu fitilar kofar gidan su AbdulKadir din da ta haska mishi ita, yana da tabbacin zai gane ita din ce.
Wani irin tuquqin kishi da yajine idanuwan shi har lumshewa suke ne abinda bai tsammata ba. Baisan kafafuwan shi na takawa ba sai da yagan shi tsaye a gabanta. Ita kanta ta girgiza dan bata tsammaci ganin shi ba, tun da safe take kiran wayarshi a kashe, ga sakonnin duk da ta tura basu nuna alamar sun shiga ba, ya kirata jiya da dare ya dorata kan tsanin buri, da safen nan ya girgizata ta fado. Har kuka tayi, tunanin shine yai mata yawa shisa ma ta fito zancen ko bakomai zata rage dare, inta koma ta sake kiran shi in bata samu ba ta hakura ta gwada kwanciya ko bacci zai saceta, shine tunaninta lokacin data fito
"Masoyi..."
Ta fadi murmushi na kwace mata, kallo daya AbdulKadir yai ma yaron da yake tsaye ya zagaya ya shiga motar shi yajata yana barin wajen.
"Me kike tsaye da wancan yaron Nuriyya?"
Ya bukata ranshi a matukar bace, saboda baiga dalilin da zaisa ta addabi rayuwar shi idan tasan zata dinga kula wannan yaran ba, baisan me yasa zata ce tana son shi ta fito tana kula kananun yara ba. Kafin ta bashi amsa ya dora da
"Me kike so da ni? Me yasa zaki dameni kuma ki fito kina kula wannan yaron? Da wannan yaron zaki hadamun soyayya Nuriyya? Raini kike son ja mun?"
Kai take girgiza mishi, gabaki daya yanayin shi ya tsoratata, muryarta a karye tace
"Ka aureni, ka aureni....in baka son ganina da kananan yara ka aureni"
Murmushi AbdulKadir yayi mai sauti da ko kadan bashida alaka da nishadi, tana maganar aure kamar abune mai sauqi, shisa ta zabi tayi auren tabarshi tun daga farko. Magana zaiyi yaga ta matsa da sauri tana boyewa a inuwar shi. Hakan yasa shi juyawa ya kalli inda idanuwanta suka bari, baisan waye ya shiga gidan su ba, amman bazai wuce wani cikin kannen shi ba. Hankalin shi ya mayar kanta
"Me kike boyewa?"
Idanuwanta cike taf da hawayen da batasan ta inda suka taso ba ta tsinci kanta da fadin
"Naziru ne ya wuce..."
Lokacin da tace tana son shi, bata hango girman hakan ba, asalima idanuwanta a rufe suke da tunanin samun shi, ta manta alakar da take tsakaninta da Waheedah da zata iya saka auren shi ya zame mata abu mai matuqar wahala.
"Me yasa zaki boye?"
AbdulKadir ya sake tambaya, Nazirun ba bakonta bane, baiga dalilin da zaisa ta boye ba.
"Zai ganmu a tsaye"
Ta amsa a sanyaye, tana saka hannu ta share kwallar data taru a gefen idanuwanta, wata irin soyayyar AbdulKadir din na dafa ruhinta
"Me yasa kika ce kina sona idan kananun abubuwa irin wannan zasu dameki?"
Idanuwanta ta sauke cikin nashi tana rasa abinda zata ce mishi, numfashi AbdulKadir ya sauke, gabaki daya kanshi yayi nauyi, bayaso abu ya dame shi, yaga alama kuma Nuriyya zata dame shi
"Kina sona da gaske?"
Kai ta daga mishi, inta ce kalamai zatayi amfani dasu ba zasu isheta ba, kalar son da take mishi har mamaki yake bata. Kai ya jinjina mata
"Zai zo karshe in na sake ganinki tsaye da wani, bana so, raina zai baci idan naganki da wani"
Kan ta sake daga mishi
"Bana so ana mun magana da kai, ki bude bakinki insan kin fahimci abinda nake fadi"
Wani abu dayai mata tsaye a wuya ta hadiye tana kallon fuskar AbdulKadir din
"Ba zaka sake ganina da kowa ba"
.
Wannan karin shiya jinjina mata kai, ya juya yana barinta a tsaye a wajen, sai da taga ya shiga gida tukunna itama ta wuce, zuciyarta na wata irin dokawa taban mamaki. AbdulKadir kuwa wani irin yanayi yakeji da bai taba tunanin zaiji ba, cikin gida ya shiga yana wucewa bangarensu. A daki ya samu Hajja da ko gaisheta baiyi ba, sallamar da yayi ma bai jira ta amsa shi ba yace
"Hajja ina Abba?"
Cike da mamaki take kallon AbdulKadir din
"Lafiya? Me ya faru?"
Kai AbdulKadir ya girgiza mata
"Lafiya kalau Hajja, ina son magana dashi ne, yana ina?"
Ita ba girkinta bane ba, Mami ke da girki, dan haka tace ma AbdulKadir din
"Yana bangaren shi..."
Kai ya jinjina mata ya fice zuwa bangaren Abba, da sallama ta shiga, ya samu Mami tana hada kwanonin abincin da alama Abba ya gama ci.
"AbdulKadir.... An iso kenan"
Abba ya fadi da fara'a a fuskar shi. Murmushi AbdulKadir din yayi shima yana gaishe da Mami da ta amsa shi cike da fara'a, kunya irin tata bata iya tambayarshi ya Waheedah ba, ta fice daga dakin tana barinsu. Kan hannun kujera AbdulKadir ya zauna
"Abba..."
Ya kira yana dorawa da
"Ina wuni"
Gyara zama Abba ya sakeyi kan kafet din
"Lafiya kalau, ya aikin? Ka samu kowa lafiya dai ko?"
Kai AbdulKadir ya jinjina yana tsintar kanshi da daburcewa a karo na farko a rayuwar shi
"Abba.. Daman zanyi magana dakai ne... Zamuyi magana..."
Ya rasa kalaman daya kamata yayi amfani dasu. Cike da kulawa Abba yace
"Allah yasa lafiya"
Numfashi AbdulKadir ya fitar da baisan yana rike da shi ba, sakkowa yai daga kan kujerar yana zama a kasa a gaban Abba din, muryarshi can kasan makoshi yace
"Aure zanyi Abba..."
Maganar Abba yaji kamar daga sama, yanda yajita yafi yanda maganar auren AbdulKadir din daga farko ta dirar mishi.
"Aure AbdulKadir?"
Abba ya tambaya cike da shakku, duk da matan shi hudu, hakan bai hanashi jinjina maganar AbdulKadir din ba, dan yasan yan zamanin su da zamanin su AbdulKadir din akwai banbanci, adalci nama yaran yanzun wahala, kuma da yawa sukanyi auren ne badan ra'ayin hakan ba, sukanyi ne saboda dalilai da kala-kala, da yawa dan suna samun matsala da matan su na gidane. Maimakon su tsaya su fuskanci matsalar su shawo kanta, sai a dinga basu shawarar su kara aure, kamar hakan zai zama sanadin batan matsalar da suke fama da ita.
Wasu kanyi dan su huce haushin wani abin da matarsu ta gida tayi ko take musu, wanda duk dalilai ne da basu kamata a dubasu wajen karin aure ba, shisa ga sunan, yara kanana suna fama da mata biyu da basu san yanda zasuyi dasu ba, tunda ta farkon ma tana neman fin karfinsu. Bayaso AbdulKadir ya kasance cikin mazan da zasu duba wannan dalilin wajen kara aure. Duk a cikin yaran shi babu wanda yake da mata biyu, a matan dai akwai wanda suke da abokan zama. Jin AbdulKadir din yayi shiru yasa shi dora tambayar tashi da
"Me yasa kake son kara aure? Kuna samun wata matsala da Waheedah ne?"
Kai AbdulKadir din ya girgiza mishi da sauri, bazai ce a zamansu da Waheedah basu taba samun matsala ba, amman inzai fadi gaskiya yafi bata mata rai fiye da yanda take bata mishi rai, dan ko abu yai mata bata taba daga mishi murya ba, in tai mishi maganar ya balbaleta da fadan shi sai dai ta bashi hakuri ta wuce daki, da duk idan ya bita kuka yake samun tanayi. Waheedah macece da yasan maza da yawa zasu so samun irinta, bata taba bashi wani dalili na dana sanin aurenta ba, asalima hukuncin aurenta na daya daga cikin abubuwa mafi girma na alkhairi daya sami rayuwar shi.
"Kawai ina son kara auren ne, babu wani dalili bayan haka Abba..."
AbdulKadir ya karasa maganar da yakeji tana fitowa daga zuciyar shi. Kai Abba ya jinjina,haka kawai yakejin maganar ta kasa zauna mishi. Har ga Allah duk lokacin da zai ga Waheedah a gidan sai yaji gabanshi ya fadi, dan yana tunanin ko AbdulKadir din yayi mata wani abu, amman har gashi aurensu na dosarma shekaru biyar ko a fuskar yarinyar bai taba ganin damuwa ba. Yafi kowa murna, dan baiyi tunanin akwai macen da zatai hakuri da baudadden halin AbdulKadir na tsayin lokacin ba. Shisa yaji auren bai zauna mishi ba, yana jin yaron har kasan zuciyarshi, bayason yana zaune lafiya ya jajibo abinda zai zame mishi matsala. Numfashi mai nauyi Abba ya sauke
"Kayi tunani akan maganar nan dai AbdulKadir, aure ba abu bane da zaka tashi kaji kana sonyi, yana bukatar natsuwa a cikin shi"
Kai AbdulKadir yake girgizawa, bayason abu ya dame shi, gudun tunanin ne yasa shi yanke hukuncin yin auren. Baiga dalilin da Abba zaice mishi ya kara yin wani nazari ba
"Nagama duk tunanin da zanyi... Auren kawai nake sonyi, shisa nazo na fada maka"
Shiru Abba yayi kafin yace
"Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi, yar gidan wacece? Wacce unguwa take? In yaso sai kayi mata magana su saka mana rana, ni da Alhaji Hamisu da Alhaji Hadi sai muje ayi magana"
Goshin shi AbdulKadir ya tana yana share zufar da yaji alamar tana tarar mishi. Bai taba tunanin muryarshi zatayi saukar da tayi yanzun da yake furta
"Nuriyya ce Abba?"
Kallon shi Abba yayi yana jiran ya tabbatar mishi da rashin hankalin da Hajja kance yana tattare dashi. Wani abu da yaji ya tokare mishi wuya AbdulKadir yake hadiyewa, ko kadan bayason kallon da Abba yake mishi
"Abba ita Nuriyyar...Dan Allah karkace wani abu...ita nake so in aura"
Abba bai taba tunanin akwai ranar da zai so wanke fuskar AbdulKadir da mari haka ba, da auren shi harda yaro.
"Ban taba yarda da baka da hankali ba sai yau AbdulKadir, wallahi yau ka tabbatar mun da cewar baka da hanlali. Nuriyya kake magana, kawar Waheedah, Nuriyya aminiyar matarka, ita kazo kana fadamun kana so ka aura"
Kallon Abba AbdulKadir din yake yana rokon shi daya fahimce shi, yasan lokutta da daman mutane na barin abinda addini ya halarta musu dan al'ada na ganin hakan bai kamata ba, kuma tun da ya fara tako kafarshi da niyyar furta maganar auren Nuriyya yasan zai fuskanci wannan matsalar, amman shi mutum ne da surutu irin wannan basa damun shi sam, bayajin akwai wani abu da addini zai halarta mishi kunya ta hanashi yi.
"Bafa haramun bane Abba"
AbdulKadir din ya fadi yanajin yanda ranshi ya soma baci, Hajja ce ya tsammaci zatai mishi wannan maganar ba Abba ba, tunda shi namiji me zai fahimta.
"Idan baka fitar mun daga daki ba, wallahi saina wanke ka da mari, marar kunyar banza da wofi..."
Mikewa AbdulKadir yayi yana fadin
"Babu abinda nayi da ba dai-dai ba Abba, nikam zan aureta..."
Dafe kai Abba yayi, yanajin zagin da bai taba tunani ba na mishi yawo a cikin kai, da yana da tsohon hawan jini bacin ran da yake ciki yanzun zai taso mishi dashi. Yanajin AbdulKadir din na sake cewa
"Zan mata magana sai a ta fadi ranar da zakuje din"
Kafin yaja mishi kofar yana ficewa daga dakin...!!!
#Teamwaheedah
#TeamAbdulKadir
#LubnaSufyan[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
22
INA GODIYA DA ADDU'O'IN KU DA DUKKAN SAKKONIN KU. KEEP THE COMMENTS FLOWING, NAGODE, NAGODE, NAGODE.
Har ya shiga gida ran shi a bace yake jin shi. Yana jin Waheedah tun da ta amsa mishi sallama tai mishi sannu da zuwa tana bin shi da ido. Yasan ta fahimci ran shi a bace yake. Kitchen ta shiga ta samu babban plate ta zuba musu abinci a ciki, manja ta zuba musu ta saka cokulla guda biyu a cikin abincin, maggi ta dauka da robar yaji ta fita falon. AbdulKadir na zaune inda tabar shi akan kujera, so take ta tambaye shi waya bata mishi rai, amman batajin dadin jikinta, ba tajin zata iya da fadan shi da daren, shisa tayi shiru. A kasa ta ajiye abinci da robar yajin ta dora maggin a sama.
Kitchen ta koma ta dauko wani plate din da kofuna guda biyu, ta bude fridge ta dauko pure water guda biyu, sai robar da cittarta take a ciki, in dai an kawo ruwan roba gidan AbdulKadir ne yazo ya fita ya siyo shi, barnar kudin nan bada ita akeyinta ba, akwai gidan ruwa a unguwarsu, maigadi take ba ya siyo mata leda goma ta zuba a fridge din, sai ta kwana biyu bata nemi ruwa ba. Danma Fajr na mata barnar shi, idan yagan shi a roba kuma bakinta baya hutawa da surutu, babu qishin da yake ji, zai dauko ne kawai dan yasata magana.
A kasa ta samu AbdulKadir ya sakko, itama ta ajiye ruwan ta samu waje ta zauna. Maggin ta barbada ta bude robar yaji ta zuba, duka ta cakuda, tasan AbdulKadir zai tsaya kallonta sai ta cakuda inda zataci suci wajen tare, ko ta cakuda mishi na gaban shi, in sunje gidan su har mamakin yanda yake komai da kan shi take, amman da sun dawo yaga su kadai ne zai shagwabe mata. Badan batason hakan ba, wani lokaci abin kanyi mata yawa, gashi, ga Fajr. Abincin suke ci, bakajin komai na tashi a dakin sai karar cokulla. Sun gama kenan ta zuba mishi ruwa ta mika mishi kofin sukaji sallamar Yassar.
Ita ta amsa mishi sallamar tana kallon yanayin shi ko zata fahimci dalilin zuwan shi da dare haka. Murmushi yai mata yana amsa gaisuwar ta hadi da dorawa da
"Duk suna lafiya. Ya jikin ki?"
Sunkuyar da kanta tayi kasa a kunyace, tana amsawa can kasan makoshi, idanuwa Yassar ya sauke kan AbdulKadir, hakan da Waheedah ta kula da shi yasa ta mikewa ta dibi kwanonin ta wuce kitchen, acan tasha ruwa tukunna ta fito tana ma Yassar sallama ta wuce daki. Kowa ya batama AbdulKadir din rai tasan bazai wuce a gida bane, tunda taga Yassar yazo. Shisa tabasu waje, in AbdulKadir yana so taji da kanshi zai fada mata, ita kam kaya zata sake ta kwanta abinta.
Yassar mikewa yayi, baisan yanda akayi ya iya dora murmushi a fuskar shi ba, bayan abinda yake so yayi daya shigo shine wanke fuskar AbdulKadir din da mari. Abinci zaici Abba ya kirashi rai a bace yake fada mishi abinda AbdulKadir din yake shirin yi da ko a mugun mafarki Yassar bai taba hango faruwar lamarin ba.
"Magana nake son yi da kai"
Kallon shi AbdulKadir yayi yana kankance idanuwan shi, ran shi ya kara baci, Abba kiran Yassar yayi ya fada mishi kenan, kuma baiga dalilin yin hakan ba, tunda zai fadama Yassar din da kan shi, magana ce da ba boyuwa zatayi ba, dan baiga abinda zaisa shi ya fasa ba, ya rigada ya furta.
"Ina jin ka ai"
Ya amsa, mikewa Yassar yayi, idan AbdulKadir bashida hankali, shi yana dashi, da alama Waheedah bata sani ba, ba zaiso ta faraji daga bakin shi ba.
"A waje zamuyi magana ba anan ba"
Cewar Yassar yana ficewa daga dakin, tashi AbdulKadir yayi yabi bayan shi har wajen motar shi, suka tsaya. Sun kai mintina biyu Yassar nason hadiye abinda yakeji yana taso mishi ko zai samu nutsuwar yima AbdulKadir din magana batare daya dura mishi ashar ba.
"Abba ya kirani...."
Shiru AbdulKadir din yayi, yana jira Yassar ya fada mishi wani abu da bai sani ba, wannan tsohon zance ne tunda gashi tsaye a gefen shi yana huci kamar sabon biredi.
"Ka ce mun wasa kake AbdulKadir, dan wallahi na kasa wrapping din kaina akan maganar nan"
Kallon shi AbdulKadir yayi
"Yaushe Abba ya zama abokin wasana? Meye wahala a fahimtar maganganun da nayi? Auren da zan kara ne yake maka wahalar fahimta?"
Numfashi Yassar yake ja yana fitarwa a hankali, da alama idan bai kai zuciyarshi nesa ba, mota zai koma yajata ya take AbdulKadir din duk su huta.
"Bansan me kake so ince maka ba Hamma... Bansan me yasa kazo kana kallona kamar akwai haramci a cikin abinda nake so inyi ba"
AbdulKadir yake fadi ranshi inyai dubu kowanne a bace yake, tun a hanya yake jin maganganun daya fadama Abba suna dawo mishi, abin na mishi kamar mafarki, yana kasa yarda da abinda yake shirin faruwa din. Amman zuwan Yassar ya kara tabbatar mishi da cewa auren zaiyi babu fashi. Dan baiga dalilin da zaisa Yassar ya dinga mishi kallon da yake mishi ba. Kai Yassar yake girgizawa, muryarshi a gajiye yace
"Bani da matsala da auren ka, wadda zaka aura din ce damuwata, me yasa sai ita? Kawarta ce AbdulKadir..."
Kankance mishi idanuwa AbdulKadir yayi
"Sai me ya faru dan kawarta ce? Haramun ne in auri kawar ta?"
Dafe kai Yassar yayi da yakejin wani irin ciwon kai ya dirar mishi. Ga zuciyar shi dake zafi, in har yanajin haka da abinda AbdulKadir yake shirinyi, baisan ya Waheedah zataji ba
"Ka daina yin kaman mai asthma Hamma, bazai sa in fasa auren nan ba. Bansan me yasa Abba zai fada maka ba, tunda ai zan gaya maka da kaina daman"
Da hannuwa biyu wannan karin Yassar ya tallafe fuskar shi. Da ance mishi akwai ranar da zata zo da zaiji bayason ganin AbdulKadir zai karyata, amman abinda yake ji yanzun, maganganun AbdulKadir din ko kadan bayason gani. Dashi ake jinjina maganar matan da suke cakawa mazajen su wuka duk idan hakan ya faru, AbdulKadir yasa shi fahimtar kadan daga cikin dalilin da maza suke ba matansu har shaidan yai galaba akan su, su hau dokin zuciya su aikata abinda zaisa ka su dana sani daga doron duniyar har lahira.
Idan akwai mazaje dari irin AbdulKadir, yana da tabbas lahirar mata da yawa zata raunana, zasu zama barazana da kwanciyar kabarin mata da dama. Fuskar shi Yassar ya bude yana jan wani irin numfashi ya fitar dashi rai a bace
"Babban kuskuren rayuwar Waheedah shine amince ma auren ka"
Wannan karin AbdulKadir ne yaja wani irin numfashi, kai yake girgizawa
"Baka fadamun maganar nan ba Hamma, ka janye kalamanka..."
Mukullin shi Yassar yake lalubawa cikin aljihu, ya kuwa yi nasarar ciro shi yasa a jikin murfin mota ya bude. AbdulKadir ya mayar da murfin yana rufewa, ya kuma rike hannun kofar gam. Muryarshi can kasan makoshi yake cewa
"Hamma ka janye kalaman ka, dan Allah ka janye ko zasu rage mun zafin da sukeyi..."
Tsaki Yassar yaja
"Ka matsamun daga jikin mota kafin in kwada maka mari AbdulKadir.... Wallahi yanda nake ji komai zai iya faruwa..."
Kallon shi AbdulKadir din yakeyi, a tsayin rayuwar shi yaune rana ta farko da Yassar ya fada mishi maganganun da yakejin ciwon su har cikin kasusuwan shi, akan maganar abinda addini ya halarta mishi ta kowacce fuska. Yasha ganin ya ta mutu, kanwarta ta auri mijin, baisan me yasa nashi zai banbanta ba.
"Me yasa zaka fadamun haka? Hamma me yasa? Saboda nace zan auri Nuriyya? Dan zanyi abinda