Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   26 / 51

75K to 78K   out of 152.3K words

dakin, karar ruwa ya tabbatar mata da wanka yakeyi, ya jima kafin ya fito. Tanajin wayarshi na kara, bata ko motsa daga inda take ba ballantana tai kokarin daga wayar.

Harya fito daure da towel a kugun shi dayasata dauke idanuwanta daga kanshi, wayar ya karaso ya dauka. Anty Talatu ce, hidimar bikin yasaka shi samun lambarta. Dagawa yayi yana fadin

"Hello..."

Daga dayan bangaren yaji tace

"Ina kukaje AbdulKadir? Kasan dai kowa ya kwaso gajiya ko? Kwanciya zamuyi ka dawo da ita haka"

Kankance idanuwan shi yayi

"Kuyi kwanciyarku kawai, zamu kwana a hotel"

Ya fadi

"Hotel?"

Anty Talatu ta maimaita da matuqar mamaki a muryarta

"Hotel fa AbdulKadir..."

Dakuna fuska yayi yana fadin

"Saida safe"

Ya kashe wayar tashi gabaki daya. In ba zasu kwanta ba su nemi motar Kano su juya a daren. Bayason wani dogon surutu shisa ya kashe wayar gabaki daya. Towel din ya kwance yana barin gajeran wandon dake jikinshi ya koma bandaki ya ajiye. Kan gadon ya karasa yana shirin kwanciya kenan yaji ana kwankwasa mishi daki, tashi yayi yaje ya bude kofar yana tsayawa a bakinta ganin Yassar na sauke waya daga kunnen shi

"Daukota kayi ka kawo nan? Saurin me kake AbdulKadir?"

Dakuna ma Yassar fuska yayi

"Ina da ikon dauko matata in kaita duk inda yaimun"

Ya ba Yassar din daya dafe kai amsa

"AbdulKadir... Oh Allah na, ka tashi ka mayar da ita... Meyasa zaka daukota? Kasan surutun da zaka jama Hajja kuwa? Me yasa baka da kunya ne"

Hamma AbdulKadir yayi dan bacci ne a idanun shi

"Wallahi bazan mayar da ita ba, ai nace ma Hajja karsu zo, kar suzo saboda za'a takurani, za'a shiga rayuwata, bata fada musu ba. Ni kabarni..."

Baki a bude Yassar yake kallon shi kafin yace

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Kallon shi AbdulKadir yakeyi

"Ka daina yi kamar anyi mutuwa fa... Ba zaisa in mayar da ita ba. Da ka wuce ka kwanta zaifi maka alkhairi..."

Ya karasa maganar yana rufe kofar a fuskar Yassar da yake tsaye. Cikin dakin ya shigo inda ya samu Waheedah a zaune tanajin duk wata kunyar duniya ta tattarar mata waje daya, batajin zata iya komawa gidan nan ta hada idanuwa dasu Anty. Amman batasan ya zatayi da AbdulKadir bane ba. Yanzun ma hannunta ya kama yana mikarwa ya dora kan gadon. Hawa yayi shima yana kai hannu ya kashe musu kwan dakin, kwanciya yayi yana jan Waheedah ya kwantar da ita kan kirjin shi yanajin wata irin nutsuwa na saukar mishi.

Yanda yakejin bugun zuciyarta a kirjinshi yasa murmushi kwace mishi

"Baki da hankali Waheedah... Kiyi bacci nima bacci zanyi..."

Yai maganar yana kara gyara mata kwanciya a jikin shi, da gaske yake mata baccin zasuyi. Bayajin yin bacci shi kadai ne shisa yaje ya dauko ta, addu'a yayi tana jinshi ya tofa musu, amman ta kasa koda runtsa idanuwanta ne balle bacci ya dauketa, saida taji numfashin shi ya canza alamar bacci yake da gaske tukunna ta sauke wata irin ajiyar zuciya da batasan tana rike da ita ba. Hannunta daya ta dora kan kirjinshi tana gyara kwanciyar ta, tana godema Allah daya nuna mata zama matar shi.

Kanta ta gyara kan kirjinshi, bugun zuciyar shi na nutsar da wani abu a cikin nata kirjin har baccin gajiya yai gaba da ita...!

*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#AnaTare*
*#SonSo*
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43

*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*

18

"Waheedah..."

AbdulKadir ya sake kira a karo na hudu, fuskar shi dauke da murmushi, baisan kalar gajiyar da tayi ba, sallar asuba ma daya tasheta kallon shi ta dingayi kamar ya kwace mata wani abu, daya jasu sallar suka idar, yana kallonta taja jiki takoma kan gado, ko hijab bata cire ba. Yanzun ma hannun shi da yake kan kafadarta take turewa tana shagwabe mishi fuska

"Me zanyi?"

Ta tambaya muryarta cike da bacci, har lokacin idanuwanta a rufe suke, murmushi yayi har hakoranshi suka fito. Gyara zaman shi yayi gefenta yana saka hannuwan shi duka biyun ya dagota hadi da girgizata

"Ki tashi Waheedah.... Hamma zai kasheni inya dawo bamu shirya ba, idan mukaje gida sai kiyi baccin..."

A hankali take bude idanuwan ta, tanajin kanta kamar an dora buhun siminti, duk wata gaba da take jikinta ciwo take mata, bata taba gajiya irin wadda tai daga satin bikin zuwa wayewar garin ranar ba. Kallon fuskar AbdulKadir da yake mata dariya tayi, tana tunanin inda take kafin komai ya dawo mata.

"Hamma..."

Ta kira tanajin kunyar duniya ta tattaru ta rufe ta. Dariya yayi

"Ki tashi ki watsa ruwa mu tafi..."

Kai ta daga mishi tana bin hannuwan shi da suke rike da ita da kallo, hakan yasa AbdulKadir sakinta, ta dayan bangaren ta ja jikinta ta sauka, kanta a kasa ta wuce shi zuwa bandakin tana rufo kofar, wani numfashi da batasan tana rike dashi ba ta sauke. Ruwa ta watsa tana mayar da gabaki daya kayan da ta shiga dasu, tukunna ta fito. AbdulKadir na zaune inda tabarshi yana danna wayar shi, sai lokacin ta tuno da tata wayar tana gida cikin jaka. Hakan kuma na tuna mata da su Anty Talatu da suka bari da yanda zata fara hada ido dasu yanzun.

"Hamma..."

Ta kira cikin tashin hankali, dago da idanuwan shi yayi yana kankance su akanta

"Ina zamuje?"

Ta bukata, da mamaki yake kallonta

"Gida..."

Ya amsa a taqaice, kai ta girgiza mishi, tana sashi daga mata gira cikin alamar tambaya

"Su Anty na nan, ban san me zance musu ba..."

Bude baki yai da niyyar amsata, kwankwasa kofar da akayi ya hanashi.

"Wallahi badan Waheedah ba da tuni mun tafi...yanzun ma bazan sake magana ba..."

Yassar ya fadi daga wajen dakin, da alamun ranshi a bace yake, mikewa yayi yana daukar hijab din Waheedah ya karasa inda take tsaye, juya hijab din yayi zuwa dai-dai tukunna ya juyo da wajen kan yana saka mata, damtsen hannunta daya ya rike yana jinshi kamar kara a cikin hannun shi, gyara mata zaman hijab din yayi sosai, ya juya ya koma ya dauko dankwalin kayan nata, hannunta ya sake kamowa ya saka a ciki, kallon shi kawai takeyi

"Sadauki su Anty na nan.... Dan Allah... Bansan me zance musu ba"

Waheedah take fadi muryarta a karye, ko inda take AbdulKadir bai kalla ba, wayarshi da wallet ya dauka ya saka a aljihu, yazo ta gabanta ya wuce, saida ya zira takalman shi tukunna ya dauko mata nata yana ajiyewa a gabanta.

"Hamma..."

Idanuwanshi ya kankance mata

"Ki zabi abinda zaki cemun guda daya..."

Da sauri ta amsa shi

"Sadauki..."

Kai ya jinjina mata yana dorawa da

"Kisa takalmanki, idan Hamma yaimun fada raina zai baci, naki zai baci kema saboda na shirya tun dazun ke kike batamun lokaci"

Takalman ta saka, idanuwanta na cika da hawayen da batasan dalilinsu ba. Gaba AbdulKadir yayi tana bin bayanshi suka fita daga dakin, tsaye tayi ya kulle kofar, kanta a kasa yake, koda ya kama hannunta binshi kawai takeyi, inda duk ya cire kafarshi nan takw saka tata, daya tsaya bada mukulli ma a reception, tsayawa tayi batare data amsa gaisuwar da matar tayi mata ba, asalima ko dagowa batai ba balle taga kalarta, tana tunanin da idanuwan da zata kalli su Anty Talatu ne.

Har bakin motar Yassar suka karasa, yana tsaye daga waje, addu'a Waheedah takeyi kar Yassar yai mata magana, shima ganin kanta a kasa yasa shi kin ce mara komai, Allah ya hadata da wani irin miji da sukai hannun riga shida kunya. Shi kanshi Yassar din tayata jin kunyar abinda AbdulKadir yakeyi. Wata irin harara Yassar ya watsa ma AbdulKadir yana f

"Wallahi da ka kara minti biyar da saidai ku nemi abin hawa..."

Dakuna fuska AbdulKadir yayi yana amsawa da

"Na tashi lafiya Hamma, thank you, fatan kaima ka tashi lafiya?"

Wata hararar Yassar ya watsa mishi dan yasan gatse yai mishi, zagayawa yayi ya bude motar ya shiga. Saida AbdulKadir ya bude ma Waheedah bayan motar ta shiga, ya mayar da murfin ya rufe sannan ya shiga gaban, Yassar yaja motar yana fita daga hotel din zuwa hanyar da yake tunanin zata mayar dashi barikin su AbdulKadir din, yana addu'a ya gane hanyar ba sai yayi magana da AbdulKadir ba.

*

Bayan AbdulKadir take bi har cikin gidan, kanta a kasa cike da wata irin kunya da bata taba tsintar kanta ciki ba. Jikinta taji ya soma bari jin AbdulKadir yayi Sallama, kuma Anty Talatu ta amsa mishi muryata dauke da wani irin yanayi

"Anty. Sannunku da gida... Ya gajiya?"

Kallon shi Anty Talatu takeyi, murmushin takaici mai sauti na kwace mata, ba tun yanzun tasan AbdulKadir bashida kunya ba, tun randa tazo gidan akace ya mayar da ita, tai mishi fada kan ya zagi wani saurayi daya kusan bigewa ya gaya mata maganganu, tace ya tsaya ya sauketa, ya kuma yi parking gefe yana jira ta fita. Amman jiya ne ta tabbatar da gaske bashida kunya. Yanzun ma yanda yake hada idanuwa da ita ya kara tabbatar mata da hakan

"Waheedah ina son magana dake kafin mu wuce"

Anty Talatu ta fadi, tana saka Waheedah dago da manyan idanuwanta tana kallonta cike da tsoro, tukunna ta kalli AbdulKadir da yake gefenta, dan daga mata kafadu yayi, yana kallon Anty Talatu data juya

"Anty gaisheki fa nayi, baki amsani ba kika wuce"

AbdulKadir yace cike da takaici, dan ba kullum yake bata gaisuwar shi ba, yau ma dan yana cikin nishadi ne shisa ya gaisheta, amman ta wuce bata amsa ba kamar ya mata wani abu. Ko juyowa batai ba, hakan yasa shi kankance idanuwan shi, yanajin yanda ranshi yake gab da baci. Cikin sanyin jiki Waheedah ta wuce ta bayan AbdulKadir zuwa dakin da Anty ta shiga. A tsaye ta sameta, daga bakin kofa ta tsaya tana jin idanuwanta sun fara tara hawaye, batason fada, ko kadan batason tayima kowa laifi a rayuwarta. Hankalinta gabaki daya a tashe yake.

"Waheedah idan kika biyema soyayyar namiji zaki sha wahala wallahi, bance karki bi mijinki ba, amman ba'a kowanne yanayi ba, yanzun ke mutuncinki ne ace darenki na farko a gidan miji kin dauki kafa kin bishi hotel?"

Kai Waheedah ta girgiza, hawayen da suke cike da idanuwanta suna zubowa, ci gaba da magana Anty zatayi aka turo kofar. Idanuwan shi AbdulKadir ya sauke kan Anty, ranshi ya gama baci.

"Ki fadamun Hadith daya ko aya data ce kar matata tabini hotel..."

Ya karasa maganar yana cigaba da kallonta, shisa bayason mutane, saboda irin wannan ra'ayoyin nasu ya sha banban da nashi, idan kuma ana maganar ranshi zai iya baci, baisan matsalar hausawan mu da hotel ba, yawancin su suna tunanin babu wanda yake ziyartar wajen sai mazinata, basa tuna cewa akwai matafiya da halin kwana ya kama a hanya suka tsaya, akwai wanda aiki ko kasuwancin yan kwanaki yakai shi, bashida zabin daya wuce kama hotel din dan ya zame mishi masauki.

Ranshi na kara baci da amfi ma duk macen da za'a gani a hotel kallon marar tarbiyya, musamman idan aka gansu tare da namijin da zai iya zamowa Yayanta ne tafiyar ta kamasu, dakunan da zasu kwana mabanbanta ne, ko kuma mijinta ne, kowa zaka gani a hotel yana da dalilin shi na zuwa wajen, ba kuma duka dalilan bane suke zama na banza.

"Kar kaimun rashin kunya AbdulKadir..."

Anty Talatu tayi maganar ranta a bace

"Saboda na nemi ki bani hujja kan dalilin da yasa rashin mutuncine kwanan da mukai a hotel?"

Mikewa Anty Talatu tayi daga zaman da take bakin gadon tana fadin

"Allah ya shirya ya bada zaman lafiya"

AbdulKadir din ya amsata da

"Amin..."

Yana matsa mata ta rabashi dan ta wuce, kafin ta fita ya dora da

"Mungode Allah ya saka da alkhairi ya mayar daku gida lafiya"

Bata amsa shiba ta fice daga dakin, ya mayar da kofar ya kulle a bayanta, yana mayar da hankalin shi kan Waheedah da take faman hawaye. Kuka baya damun shi sam, yasha zane Zahra ya zauna ya jirata ta gama kukan da zatayi suyi magana, kuka marar dalili ne bayaso, amman wannan da Waheedah takeyi har kasan zuciyarshi yake jinshi.

"Banaso Waheedah, banason kuka marar dalili"

Kallon shi tayi, wasu hawayen na kara zubo mata, tsoro takeji kar Anty Talatu ta fadama Mami ta mata wani abu, Mami zatai mata fada tasani

"Karta fadama Mami"

Dariya AbdulKadir yayi yana girgiza mata kai

"Baki da hankali ke kam..."

Ya karasa maganar yana kama hannun kofar

"Bari inyi sallama dasu Hamma..."

Kai ta daga mishi tana sa hannu ta goge fuskarta, yana fita ta karasa gefen gadon ta zauna. Har lokacin hankalinta yaki kwanciya, ko kadan batason tashin hankali.

**

PRESENT DAY

Kwankwasa kofar da taji anyi ya katse mata tunanin da take, sallama Hauwa tayi da Waheedah ta amsa mata cikin sanyin murya, turo kofar tayi tana fadin

"Na dauka kinyi bacci, Yassar nason magana dake daman"

Kai Waheedah ta girgiza mata, tana dafa gado ta mike, juyawa Hauwa tayi, tabi bayanta, a bakin kofar ta samu Yassar din a tsaye

"Waheedah yanzun Anty ta kirani, tace za'a mayar dake asibiti ashe..."

Numfashi Waheedah ta sauke

"Dan Allah Hamma kubarni da asibitin nan, hutawa suke so inyi kuma zan huta..."

Kallonta Yassar yake, a yanayin da yake ganinta bayaso ya takura mata, amman kuma lafiyarta nada muhimmanci

"Da gaske zan huta... Allah kuwa, idan naji banajin dadi sosai saimu koma"

Tayi maganar cikin son tabbatar mishi, a hankali ya jinjina mata kai

"Dan Allah koya kikeji kiyi magana mu koma, nasan ba shiri kuke da AbdulKadir a yanzun ba, amman zai kasheni idan wani abu ya sameki karkashin kulawata"

Murmushin karfin hali tayi tana rasa abinda zatace mishi.

"Allah ya sauqaqa"

Yassar yai maganar cikin sanyin murya, saida ta amsa shi da

"Amin..."

Tukunna ta juya ta shiga dakin tana turo kofar, data bude da sauri tana  fadin

"Hamma wayata... Tana can, sai kayan su Ikram..."

Kai Yassar ya jinjina mata, ta sake mayar da kofar ta rufe. Shikam hanyar da zata fita dashi daga gidan ya nufa yana ce ma Hauwa

"Bari in dawo ba dadewa zanyi ba..."

Cike da damuwa take kallon shi

"Bakaci abinci ba har yanzun..."

Murmushi yai mata

"Zanci da na dawo... Kici ke dai..."

Kai ta girgiza mishi

"Nidai zan jiraka... Karka dade kaji?"

Numfashi ya sauke yana jinjina mata kai ya wuce, har wajen motar shi ya karasa ya shiga yana nufar gidan AbdulKadir.

*

A harabar gidan yayi parking din motar shi, batare daya fito daga ciki ba ya kira wayar AbdulKadir din ya fada mishi yana cikin gidan. Ko mintina biyar ba aiba saiga AbdulKadir din ya fito. Da murmushi a fuskar shi yake takawa zuwa wajen motar dan a zaton shi Waheedah Yassar ya dawo mishi da ita, yasani daman, a jikin shi yakeji Waheedah ba zata iya kwana wani waje yana gari ba, bata taba ba, ba kuma zata fara ba yau. Yana karasawa wajen motar ya kama murfin bayan yana kikiniyar budewa, kasancewar gilasan baqaqe ne baka ganin waye a ciki daga waje.

Qasa da gilashin gefen shi Yassar yayi, ya ziro kai yana fadin

"Ka maida hankali ka karyamun murfin mota AbdulKadir..."

Sakin kofar yayi yana matsowa saitin Yassar din

"Tana ina?"

Cike da rashin fahimta Yassar yace

"Ita wa?"

Dakuna mishi fuska AbdulKadir yayi, yanayin da yasa Yassar din jan karamin tsaki

"Malam ka wuce ka dauko mun kayanta dana yara, sai wayarta tace tana nan in hado mata dasu"

Lokaci daya murnar da AbdulKadir din yakeyi ta bace, wani tuquqin bacin rai na maye gurbinta, ga yunwar dake cinshi na kara taimakawa wajen rura mishi bacin ran.

"Kace mata tazo ta diba da kanta"

Bude motar Yassar yayi ya fito, shima nashi ran yake ji a bace

"Kalleni..."

Ya fadi yana dorawa da

"Ka kalleni dan ubanka. Nayi maka kama da abokin wasan ka? Ko na maka kama da dan aike... Karka kara batamun rai fiye da yanda yake a bace..."

Juyawa AbdulKadir yayi yana nufar hanyar gidan, Yassar bazai kara bata mishi rai ba, Waheedah ta gama hada mishi zafi. Bin bayan shi Yassar din yayi yana tsayawa cikin falon, dai-dai fitowar Nuriyya da wandone a jikinta ko cinyoyinta bai rufe ba tana fadin

"Masoyi..."

Da sauri tayi baya babu shiri ganin Yassar din, AbdulKadir ko inda take ma bai kalla ba ya wuce hanyar da zata kaishi dakin baccin Waheedah din. Batama yi tunanin sako abaya ta dawo ta gaishe da Yassar din ba, tasan ya tsaneta kamar sauran yan uwan AbdulKadir din, gara kannen shi suna gaishe da ita ciki-ciki. Amman ko wacce irin gaisuwa taima Yassar din yakan amsata ne da

'Sannunki'

Ya mayar da girar kasa da ta sama ya hade. Yanzun dinma ganinta ya kara bata mishi rai, ko lokacin da take kawance da Waheedah batai mishi ba sam, yanzun tsanar dayai mata ta kara linkuwa, yakan so ko yayane ya dinga mata fara'a saboda AbdulKadir din, amman ya kasa. Yakai mintina goma a tsaye a wajen kafin AbdulKadir din ya fito da wata yar jaka da kaya a ciki, kan kujera ya ajiye yana dora mishi wayar Waheedah da charger a kai ya juya batare da yace komai ba. Shima dauka yai ya fice daga gidan.

Bangaren Nuriyya inda yabar tashi wayar ya nufa yana daukar ta ya rike tukunna ya samy waje ya zauna kan kujera, kirga mintunan da yake tunanin zasu kai Yassar din gida, gara yakai ma Waheedah wayar, saiya kirata ko zai samu ta fada mishi dalilin da yasa take son tarwatsa mishi zaman lafiya haka. Nuriyya ce ta fito daga bedroom dinta, dan taji motsin shi, tasan Yassar ya tafi. Kan kujerar ta karasa ta zauna tana jingina jikinta dashi, hannun shi ya zagaya yana rikota, sauqi yake nema koya yake, so yake ta dauke mishi hankali daga tunanin da yake dan bayaso.

Gefen fuskarta ya sumbata, ta sake narke mishi

"Jikina namun ciwo..."

Muryar shi can kasan makoshi yace

"Me kikayi?"

Sake kwanciya tayi a jikinshi, hanyar da zata gujema yin girki take nema

"Me zamu ci da dare? Ko musha Tea?"

Tun kafin ta karasa kalmar Tea din yake girgiza mata kai, ana zaune lafiya bazai sha shayi ya kwanta ba, yunwar da yakeji ma tafi karfin shayi.

"Wani abu dai banda shayi"

Shagwabe fuska tayi tana sauke muryarta cike da kissa

"Kamar me? Ka zabi wani abu mai sauqi"

Dakuna fuska AbdulKadir yayi, yanayin na mishi baqunta, shifa sam bai saba fadar abinda zaici ba, dafawa Waheedah takeyi ta kawo mishi

"Ki dafa komai ma, ni ban saba zabar abincin ba, kome kika bani zanci, amman banda shayi"

Numfashi taja tana saukewa

"Ko mu fita muci a waje?"

Kallonta yayi yana kankance mata idanuwan shi

"Saboda me?"

Ya bukata yana jiran jin dalilin da zaisa su fita waje suci abinci. Haka kawai tunani ya watsa shi washegarin auren su da Waheedah.

*

"Me zakici in siyo mana?"

Ya bukata bayan tafiyar su Anty, yana kallon

26 / 51