Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
tafi. Su duka Allah ya kiyaye sukai mata batare da sun kara wasu kalaman a kai ba. Ita tana cikin nishadin da fushin da suke da itane karshen abinda yake ranta.
Amman yanzun tunanin fuskantar Waheedah ya dawo mata da komai sabo, wani irin tsoro takeji har kafafuwanta na mata rawa. Da AbdulKadir ya zagayo ya bude mata motar sai da ya mika mata hannun shi tukunna ta kama ta fito daga motar, ya mayar ya rufe, yana sakin hannunta ya bude bayan motar ya dauko dayan akwatinta yana soma jan shi zuwa cikin gidan. Da wani irin sanyin jiki na mamaki take bin bayan shi, tana kallo ya tura kofar yana shiga da cikin gidan da sallama.
Amsa shi Waheedah tayi tana mikewa, ta sake kaya zuwa wata atamfa da tafi dazun yin kyau, ga wani irin kwarjini da yaga ta mishi, gidan gabaki daya sai kamshin turarukanta yakeyi da yai mishi dadi.
"Sannu da zuwa..."
Ta fadi, tana ware idanuwanta ganin Nuriyya, harara ta watsa mata
"Sannu Nuriyya"
Ta fadi, dan rabon da ta sakata a idanuwanta harta manta, duk da suna chatting kuma suyi waya. Amman batace mata ta dawo ba, tunda ko shekaranjiya ta kirata sun gaisa. Ita kuwa Nuriyya wani irin ras kirjinta ya doka jin kalaman Waheedah din, da kuma harar datai mata. Maganar tata nasa AbdulKadir yaji nashi kirjin ya doka, cikin wani irin tashin hankali ya taka yana kama hannun Waheedah ya soma janta, juyawa tayi tace ma Nuriyya
"Ina zuwa..."
Kafin ta mayar da hankalinta kan AbdulKadir din cike da mamaki. Har bedroom dinsu, sannan ya saki hannunta tana kallon zufar da goshin shi yakeyi.
"Waheedah..."
Ya kira yana jin sauran kalaman sun makale mishi, kallon shi takeyi da irin zufar da yakeyi, kafin wani abu ya sara mata a tsakiyar kai. Lokacin da tayi ma Nuriyya magana taga ta matsa tana boyewa bayan AbdulKadir din har jikinta na taba nashi, batasan me yasa sai yanzun kwakwalwarta ta zabi tayi processing wannan yanayin ba. Numfashi take ja a hankali tana fitar dashi, a nutse takeyin hakan tana son iskar ta isa inda ya kamata. Kafin ta iya kallon AbdulKadir, muryarta na dukan dodon kunnenta da fadin
"Nuriyya..."
Tayi shiru tana sake jan wani numfashin ta tabbatar da kirjinta ba zai bude zuciyarta ta fito ba, tukunna taci gaba
"Nuriyya ka aura?!"
Kasa magana yayi, zufa yakeji tana tsatsafo mishi a duk wata kafa da zai iyaji, abin har mamaki yake bashi, tunda zazzabine ruf yaji ya rufe shi duk da zufar da yakeyi.
"Ma shaa Allah"
Waheedah ta fadi tana sake kallon shi da fadin
"Kabarta ita kadai"
Ya bude bakin shi yafi sau biyar yana mayarwa ya rufe kafin ya iya furta
"Waheedah..."
Dariya tayi da tasa shi sake kallonta
"Sadauki... Kaje..."
Badan yana son ya tafin ba, sai dan yana so ya fita daga dakin ko zai ji iska na ratsa shi. Fita yayi yana samun Nuriyya a tsaye bakin kofa kamar mai jiran kyat ta bude tayi ta kanta. Da gasken a tsorace take, dan tana da tabbacin AbdulKadir din ya janye Waheedah ne dan karta far mata.
"Muje.."
Ya fadi lokacin daya karasa yana kama akwatinta ya dauki sauran ledojin da baisan ya sake su ba, suka wuce har bangaren da zata iya kira nata yanzun. A falo ya ajiye akwatin ya nufi bedroom din tabi bayan shi, ledar ya ajiye yana shiga bandaki ya dauro alwala, itama yace taje tayi. Sallah yaja su sukayi ta godiya ga Allah, kafin AbdulKadir din ya mike ya dauko ledojin yana cire na Waheedah ya fice daga dakin ya nufi bagarenta, kwankwasawa yayi yana turawa.
A tsaye ya sameta tana dauko kayan bacci
"Sadauki..."
Ta fadi, ya karasa
"Apple na siyo miki"
Hannu ta mika ta karbi ledar
"Aikam ka kyauta, dan banajin cin komai"
Space din dake tsakanin su AbdulKadir ya hade yana zagaya hannuwan shi ya rungumeta a jikin shi. Zuwa yanzun ya kasa gane ko da gaske lafiyarta kalau ba, yasan Waheedahr shi daban take da duk wasu mata daya taba cin karo dasu. A kaf duniyar shi kuma Hajja ce kawai macen da Waheedah bataiwa nisa ba, duk da haka yanajin kamar ya kamata ta nuna mishi ranta ya baci, ko yaga kishi a idanuwanta, amman ya kasa ganin komai, yana kuma jin kamar tana boye mishi asalin abinda takeji ne.
Sosai ya riketa a jikin shi
"Allah ya bani ikon yi muku adalci"
Ya furta a hankali yana lumshe idanuwan shi, badan zuciyar shi bata dokawa Nuriyya ba, sai dan yanajin inda Waheedah take babu wanda ya taba hangowa balle harya zauna. Ita din daban ce a rayuwar shi. Hannuwanta Waheedah ta zagaya ta bayanshi tana sake shigewa jikin shi, ta lumshe idanuwanta da yanda takejin zuciyarta kamar da bulallukan tsokoki aka jerata, yanzun kuma rugujewa take ta ko ina, kurar ce take saka jikinta daukar wani irin dumi. A hankali ta zame jikinta daga nashi tana sauke idanuwanta cikin nashi, rankwafowa yayi ya sumbace ta.
"Sai da safe"
Ya fadi yana juyawa, bata iya ce mishi komai ba, harya fice daga dakin yana komawa ya samu Nuriyya da tunda ya fita takejin kamar ta bi bayan shi ya dawo saboda wani irin azababben kishi daya turnuqeta, gani tayi ya dade, zuciyarta har tafasa takeyi, kwana daya take dashi, yace mata gobe zai wuce, Waheedah ba zata bar mata shi ya dawo ba, zuwa yanzun kishi ya maye gurbin duk wani tsoro data shigo dashi gidan. Murmushi tayi tana ganin ya shigo, jikinta ya mutu ganin bai mayar mata da murmushin ba.
Karasawa yayi ya zauna gefenta yana kallonta, fuskar shi babu alamar wasa yace
"Bana son tashin hankali, bana son rigima badan ban iya ba, bansan yanda zan daina ba idan na fara. Nasan halin matata tun kafin in aureta, nasan abinda Waheedah zatayi da wanda ba zatayi ba tun kafin insan zan aureta, bansan halinki ko daya ba na aureki, idan har naji rigima a gidana daga wajenki hakan zai fara.
Ko baki girmama Waheedah ba idan baki shiga huruminta ba nasan ba zata taba biyema kome zakiyi ba. Zaman lafiyarta na da muhimmanci a wajena, idan har zamana dake zaiyi nisa zaki zauna da ita lafiya..."
Kai Nuriyya ta jinjina mishi a hankali, itama tasan halin Waheedah din, ba saiya jaddada mata ba, wanda duk yake tare da Waheedah yasan halinta, kuma ita bata shigo gidan dan ta nemi rigima da ita ba, duk da tanajin idan Waheedah tai mata ba zataki ramawa ba. Zadai tayi karya in tace idanuwanta basa mata yaji da shirin taruwar hawayen bakin cikin maganganun shi. Wani irin kishi takeji marar misaltuwa, zuciyarta na dan tsahirta mata da hannunta da AbdulKadir din ya kama.
*
Waheedah kuwa AbdulKadir na fita daga dakin ledar apple din ta bude ta dauki guda daya tana shiga bandaki ta wanko ta dawo kan gado ta zauna. Cinye shi tayi batare data gane dandanon shi ko dalilin da yasa takeci ba, kafin taja kafafuwanta zuwa kan gadon ta kwanta akan bayanta, jin kirjinta na shirin budewa yasa ta juya tana kwanciya kan gefen hannunta na dama. Wani abu takeji yana zubar mata, da sauri tasa hannu ta taba fuskarta, amman babu digon hawaye ko daya, kuka take amman daga ciki.
Ranar ne ya zame musu MAFARIN komai daya kawo su inda suke yanzun, ranar ne kuma Waheedah taji ta shiga wata duniya da tai nisa da zubar hawaye, duniyar data bata mukullin waccen data bari tana budewa tana zuba duk wani bacin rai da zai sameta ta rufe har zuwa yanzun...!
#LubnaSufyan
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#AnaTare
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
25
PRESENT
A rayuwar shi bai taba sanin menene asalin ma'anar kalmar wulakanci ba sai da yaje NDA, kamar yanda ba zaice ga tun lokacin da yake son saka uniform din sojoji ba. Sai dai shi mutum ne da idan yasa abu a ranshi, wahala ko makamancin hakan baya hanashi cimma burin shi. Zai iya rantsewa a yan shekararsu babu wanda ya sha wahalar da yasha a NDA, daga horo zuwa jibga, akwai lokutta da dama a shekarar shi ta farko da baiyi tunanin zai gama NDA da ran shi ba. Saboda bai iya tauna magana kafin ya fadeta ba, kuma bai iyayin shiru idan yana tunanin akan gaskiyar shi yake. Abinda ya ja mishi tsana da kauna daga wajen manyan shi.
Zai iya cewa kwana biyar din da yayi bakomai bane akan irin wahalhalun da ya sha a baya. Abinda ya bambanta da sauran loluttan shine, bashi yayi laifin da kan shi ba, kuma yanzun da yake hanyar shi ta zuwa gida zai shiga gidan batare da yaga Waheedah ba, kuma yayi kwanakin biyar da tunaninta cunkushe a kan shi, ranakun da sukayi mishi wani irin tsayi naban mamaki. Sabon da yayi da rashin wanka na tsayin lokaci idan aiki ya kaisu wajajen da babu nutsuwar yin hakan bai hanashi jin wari da karnin jinin da yake ba.
Ko sallama baiyi ba lokacin daya shiga gida, bangaren Nuriyya ya wuce, dan haka ko kadan bata tsammaci shigowar shi ba. Ta dauka auren Anas shine babban tashin hankalin daya faru da rayuwarta, sai kwanaki biyar da suka wuce da ta dawo gida tana rasa inda zata saka rayuwar ta taji sanyi. Da zazzabi ta wuni, ta kuma tashi dashi ganin har an kwana daya AbdulKadir din bai dawo ba, tayi tunanin zuwa gidansu ta sanar dasu halin da ake ciki, amman ta rasa samun karfin gwiwar yin hakan. Wanda duk suke dan son ta a gidan su AbdulKadir din sanadin Waheedah ne daman, tun bayan auren ta da AbdulKadir babu wanda ya sake ko kallon inda take ballantana magana ta hadasu.
Ta gwada zuwa gidansu AbdulKadir din sau daya, tunda Hajja ta amsa mata gaisuwa bata sake ce mata komai ba, ta muzanta fiye da tunani ranar, dan har kuka tayi bayan ta fito, bata kuma sake marmarin komawa ba. Babban tashin hankalin da ta shiga shine tunanin abinda zai biyo baya da fitowar AbdulKadir din, ta kira lambar Waheedah bata san adadi ba, amman a kashe, dan tasan inta fada mata zata gayawa yan gidansu AbdulKadir din ayi wani abu a kai. Hankalinta in yayi dubu a tashe yake da taga kwanaki na tafiya babu alamar AbdulKadir din.
Yaune ta yanke hukuncin ko me su Hajja zasuyi mata zataje ta same su, dan in su basu kasheta ba, zullumi zai kasheta, ko abinci ta dan samu ta dafa, plate daya haka zata wuni tana jagalar shi. Tayi zuru-zuru ta fita hayyacin ta, ko hankalinta a kwance yake sai tayi kwana biyu bata share dakinta ba, shima idan AbdulKadir na gari ne sai tayi shara ta gyara gado. Daya tafi kuma tana hada sati dakinta baiga tsintsiya ba, yanzun kuwa a kwanaki biyar din nan ko wanke-wanke batayi ba, falon a hautsine yake da gwangwanin lemuka da robobin ruwa, dan tunda ta zo gidan shi rabon ta da shan pure water, inya bata kudi ruwan roba take zuwa ta siyo.
Ita kanta rabonta da wanka tun jiya, duniyar take ji ta hade mata waje daya. Yanzun da AbdulKadir din yake a gabanta, wata irin ajiyar zuciya take saukewa da bata san daga inda take fitowa ba, ta dauka hawayenta sun gama karewa, sai yanzun da taji idanuwanta sun ciko taf da hawaye. Bata taba tunanin bakin mutum zai iya kara baki ba sai yau, duk kumburin fuskar shi bai hana idanuwan shi yin zuru-zuru suna kara shigewa ciki ba. Gashi yayi wani irin dukun-dukun. Kallon ta kawai AbdulKadir yayi yana wucewa cikin dakin baccin su, kai tsaye bandaki ya wuce yana cire kayan da yasan sun rigada sun tashi aiki.
Bandakin yake gani yayi mishi kaca-kaca, ga kayan wanki saman injin wanki harda jiqaqqu, wanka yayi, ya saba jikin shi da sabulu yafi sau biyar amman duk da haka jin shi yake kamar akwai sauran dauda a jikin shi. Towel ya dauka yana goge jikin shi ya daura shi a kugun shi ya fito, idan yace ga asalin abinda yakeji karya yake, dan bayajin komai, zafin dukan da yake jikin shi, ko bacin rai, shiru komai yake mishi. A karo na farko da ko ganin Nuriyya din bai saka shi jin komai ba. Banda Waheedah babu abinda yake cikin kan shi. Takawa yayi yana fita daga dakin, a tsaye bakin kofa yaga Nuriyya tana kallon shi
"Masoyi..."
Ta fadi muryarta na rawa, fuskarta da bayanannen tsoro. Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance a kanta yana kara saka tsoro cika zuciyarta
"Dan Allah... Dan Allah kayi hakuri... Kaji... Bazan sake ba.... Dan Allah karka sakeni, kai mun komai karka sakeni, dan Allah..."
Numfashi nai nauyi AbdulKadir ya sauke, da gaske yake bayajin komai, ciki harda magana da ita, wucewa yayi da nufin karasawa bangaren Waheedah ya dauki kayan da zai saka. Bin bayan shi Nuriyya tayi tana kamo hannun shi, gabaki daya shirun shi ya kara rikitata
"Masoyi..."
Tsaye AbdulKadir yayi batare daya juyo ba, hannun shi yake kokarin zamewa daga cikin nata, ta sake kamashi tana matsawa ta zagaya ta fuskance shi, wasu irin hawaye masu zafi na zubo mata, tana saka shi tuna yanda ko kadan batasan shi ba, da ta kyale shi, ta nemi waje ta zauna, da bata tsaya a gaban shi tana mishi kukan da baiga dalilin shi ba. Numfashin ya sake saukewa
"Kaji... Dan Allah kayi hakuri...dan Allah... Wallahi ba zan sake ba"
Nuriyya take fadi kuka mai karfi na kwace mata, hannun shi AbdulKadir ya zare daga cikin nata, yana rabata ya wuce, jin takun tafiyarta yasa shi juyawa
"Bance kin mun wani abu ba, ban miki magana ba saboda bana son yin magana da kowa, ki kyaleni Nuriyya, ki kyaleni kafin mu samu matsala..."
AbdulKadir ya karashe maganar yana juyawa ya wuce, da idanuwa Nuriyya tabi shi, zatace yana da wata irin kula da ko a tunaninta ba tayi zaton zata samu a gidan aure ba, abinda duk ta nuna tana so yana kokarin yi mata, idan kudi ta tambayeshi yana bata, wani lokacin yana ce mata bashi da kudin da zai bata ta kashe, akwai hidimar da zaiyi. Sai dai akwai bangaren shi da takejin bata sani ba, sannan mutum ne shi mai wahalar sha'ani duk da ba sosai zaman su yake tsayi ba, inya dawo kwana biyune, ita daya, Waheedah daya, amman zatai karya idan tace bata takura da kwana dayan.
Bata cika tsawaita tunaninta akan abin bane kawai, amman AbdulKadir din da Waheedah kanyi magana ko da yaushe daban yake da ita wanda take gani. AbdulKadir din Waheedah namiji ne da ko a littafin hausa batajin akwai irin shi, dan mazan littafin hausa miskilai ne, AbdulKadir din Waheedah ba haka yake ba, AbdulKadir din Waheedah kan mata abu batare da ta tambaye shi ba, yana girmamata fiye da yanda take nunawa, dan Nuriyya da idanuwanta taga hakan. AbdulKadir din Waheedah bashi da wani hali marar kyau, ita shine mutumin da take so, mutumin da tayi tunanin ta aura.
Sai bayan auren da ta fara cin karo da kashedi a darenta na farko taji zuciyarta ta tsinke, sai kuma lokutta da dama da zaiyi tunanin tayi mishi abu tayi kokarin bayani ya rufeta da wani irin fada mai cin rai, kananun abubuwa masu tarin takaici da ba zaka gani daga nesa ba, ko kuma take tunanin AbdulKadir din Waheedah ba zai tabayi ba, sannan yana surutai cikin baccin shi, yana firgita sosai, ranar farko da hakan ta faru tsoron shi ta dingaji, musamman da tayi kokarin taba shi bayan ya farka ya hankadeta yana mata wani irin kashedi da har yau bata sake kokarin zuwa kusa dashi in yana surutan shi a bacci ba.
AbdulKadir na da matsalolin da take da tabbacin bata gama gani ba. Sai dai batasan ita kadai yake nunawa ba, ko harda Waheedah. Falonta ta koma ta zauna tana jin wasu hawaye masu dumi na zarya kan kuncinta. Ita dai yanzun koma me zaiyi indai bazai saketa ba da sauqi.
*
AbdulKadir yana sake kaya, dakin Nuriyya ya koma ya shiga bandaki yana daukar wandon daya cire ya zaro wayarshi da wallet, wayar da take a kashe ya kunna yana fitowa. Sakonni ne guda biyar suka shigo tana gama loading, budewa yayi, biyu daga MTN ne, daya bankin shine, yasan albashi ne, biyu kuma Yassar ne, ya shiga na farkon
'Lafiyar ka kuwa? Wayarka a kashe. Duk da ba ina so ka zo ka dame ta bane, lafiyarka ko?'
Fita yayi yana shiga dayan
'Ka kashe wayarka ne, kayi shiru dan in daga hankalina in goyi bayanka ko AbdulKadir? Yayi maka kyau'
Murmushi yadan yi duk da nishadi na daya daga cikin karshen abinda yakeji. Wallet din shi ya saka a aljihun shi. Ya samu waje gefen gadon yana zama, dan dayaga albashin shi bayaso su kwana baiyi hidindumun da zaiyi dasu ba. Waheedah ya fara turama kudin nata hidimar na wata kamar yanda ya saba, sannan ya tura ma Nuriyya ma, saiya tura wasu cikin account din shi na ajiyar kudin tsaron lalura. Ya turana Abba da Hajja. Kati ya tura ma sauran yan gidan kamar yanda ya saba duk watan duniya, ko yayane yakan tura musu. Wata natsuwa yaji ta daban daya sauke wannan nauyin.
Wancen watan daya fita ya karo musu kayan abinci, dan shi yake siyan su shinkafa da su taliya, sai mai. Kananun abubuwa ne yake basu kudin a hannunsu. Haka suke tsarin da Waheedah, Nuriyya ma data shigo bai canza ba. Duk da ita tana tambayar shi kudi, Waheedah kuma bazai tuna ranar karshe da ta tambayeshi kudi ba, inya dauka ya bata tana karba, in baibata ba bata taba tambayarshi. Na Nuriyyar baya damun shi sam, yakan yi mamakin abinda takeyi da kudi ne kawai wasu lokuttan.
Mikewa yayi ya saka wayar a aljihu, mukullin motar shi yagani ajiye akan drawer din kusa da gadon ta, ya dauka ya fito, ko inda take bai kalla ba ya taka yana ficewa daga gidan. Motar ya shiga ya tayar, kan shi tsaye gidan Yassar ya nufa, yana kallon yanda maigadin Yassar din ya kara sauri wajen bude gate din ganin motar tashi. Saurayine matashi, daga yanayin shi AbdulKadir din ya fuskanci yaron tsoron shi yakeji. Har cikin harabar gidan ya shiga da motar yanayin parking, tukunna ya taka yana karasawa cikin gidan. Sallama yake tayi baiji alamar