Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
surutun shi, addu'a take a kasan ranta, Allah yasa AbdulKadir din yaje ya taho dashi, tunda ita ba zata iya kira tace a dawo dashi ba. Tana nan zauna aka kira sallah, ta tashi ta dauki Ikram suka koma daki.
AbdulKadir yana shiga dakin Nuriyya a kwance ya sameta kamar gawa, har saida ta tsorata shi ganin ko motsin kirki batayi
"Nuriyya..."
Ya kira, tana dago kanta dakyar ta kalle shi, dariya yaji ta kubce mishi
"Duk azumin ne?"
Ya tambaya yana zama gefen gadon, ta matsa mishi can, duniyar takeji ta hade mata waje daya, ga baqar yunwa da take addabarta, ga wankin da tayi akwai kayan da suke zuba, duk ta hade su da masu haske. Harta zanin gadonta yayi kampala-kampala, zaman gidan takejin ya gundureta, ga kuma fadan AbdulKadir din. Zama tayi tana tunanin rayuwar da ta tsarama kanta kafin shigowa gidan shi, da wannan da takeyi yanzun. Ga kuma Waheedah ta kara sawa komai ya kwance mata, mamaki takeyi tana karawa, babu kalar tunanin da batayi ba, ko wasu kawaye Waheedah tayi masu mugun hali da suka bata shawarar canza mata haka.
"Wallahi bakaji cikina ba, kamar an mun sata"
Murmushi AbdulKadir yayi, zuciyar shi yakeji tayi nauyi a kirjin shi. Kan gadon sosai yahau ya kwanta, idanuwan shi ya rufe yanajin gajiya sosai. Bacci yayi har la'asar dan saida Nuriyya ta tashe shi tukunna yai alwala ya fita masallaci. Sanda ya dawo sun kawo wuta, yai zaman shi a falo yana kallon namun daji a tashar discovery. Har wajen biyar kafin yaga Nuriyya ya fito daga dakin tana bin bango, shima yunwar yakeji. Kitchen ta shiga tana rasa abinda zata farayi, batama san abinda zata dafa ba, tunda bataga alamar Waheedah zatayi girki dasu ba. Ita yau ma ba zataje bangarenta ba, alkawari taiwa kanta.
Zama tayi ta yanki doya ta fere tana samu ta dora, tunda taga kwai, gara ta soya musu doya da kwai kawai. Bude fridge tayi taga babu lemo ko daya sai ruwa, falo tazo tana samun AbdulKadir din tace
"Masoyi bamu da abin sha fa a dakin nan, ko fanta ka siyo mana"
Yana rike da remote, hankalin shi nakan tv ya amsa ta da
"Banda kudi"
Yana cigaba da kallon shi, abinda ya zame mishi dole yayi shi zaiyi, tunda tai mishi barnar kudi zata gane kuskurenta. Tsaye tayi tana kallon shi cike da mamakin fadin bashida kudi da yayi, ranta a jagule takejin shi
"Me zamuyi buda baki da shi to?"
Har lokacin bai kalli inda take ba ya amsa da
"Nima ban sani ba"
Yana cigaba da kallon shi. Kitchen Nuriyya ta koma, ta cika kamar zata fashe, dan ta kashe dubu arba'in shisa yake mata wannan wulakancin, wayarta ta dauka tana duba account dinta taga babu abin arziqi a ciki. Kudin hannunta kuma bai wuce dubu hudu ba, shisa take karajin kamar batada lafiya, dan ta tsani taji babu kudin kirki a jikinta, in ba zai bata ba tasan zai ajiye, zata kuma diba idan ya ajiye. Dan tana bukatar abubuwa na ciye-ciye. Doyar ta sauke da tafasa daya tayi ta tace ta. Ko gishiri ta manta ana zubawa balle dan sikari tunda sabuwar doyace, ko ba sabuwa bama taste din nayin dadi na daban inka dan saka sikari.
Ruwa ta maka mata, ta dauki cefanen ta juye wajen wanke wanke ta gyara shi, jiri ma takeji saboda yunwa. Markadawa tayi duka ta juye shi a tukunya. Tana da danyar kaza a fridge ta daukota, ba zata iya wata wahala ba, itama ruwa ta saka mata ta wanketa, da kankara a jiki har lokacin ta dauketa tana zundumawa cikin kayan miyar tunda a yayyanke take, kankara ce tayi, zata narke in taji wuta, ta zuba ruwa kofi biyu, duk su hadu su tafaso tare sai tayi miyar da yawa ta saka a fridge, diba kawai zata dingayi. Mai ta dauko ta bulbula a kai, ta bare maggi ta zuba ta rufe tana komawa daki ta kwanta.
Mintina talatin ta ba miyar ta fito tana ganin ruwan ya tsane, jujjuyawa tayi ta sauketa tana kashe gas din. Doyar ta yayyanka ganin yamma tayi sosai, ta kada kwai ta zuba maggi, ta dora mai. Yar albasa ta dauka ta yanka cikin kwan tana tuna cewar bata zuba a cikin miya bama. Karamin tsaki taja tana kara dauko wata albasar ta yayyanka a plate ta bude miyar ta zuba a ciki ta mayar ta rufe, tukunna ta zuba doyar cikin kwan ta cakuda ta juye ta gabaki daya a cikin mai tana komawa gefe ta tsaya. Aikam ya fara tasowa yana zuba har kasa, gabanta yai wata irin mummunar faduwa, zuwa tai kashe gas din mai ya zubo mata ta saki ihun da yasa AbdulKadir shiga kitchen din da gudu.
Hannu yakai yana kashe gas din ya kama na Nuriyya zuwa wajen famfo ya sakar mata ruwa
"Mahaukaciya ce ke? Me kikeyi haka?"
Hannunta ta cire daga cikin ruwan tana yarfewa saboda azaba. Turo baki tayi kawai dan tanayin magana fashewa zatayi da kuka, batasan me yasa komai yake jagule mata ba haka. Shi kanshi AbdulKadir din ranshi yaji ya kara baci, kananun fada haka ba halayyar shi bane ba, amman a kwanakin nan jin shi yake komai ma na fada ne, ganin idan ya tsaya a kitchen din fada zai mata yasa shi fita kawai ya koma ya zauna inda ya tashi. Nuriyya doyar ta samu wani waje ta rage, tana rage man ma, ta sake kunna gas din, ta soya ta ciki da kwan jiki duk ya nadi mai, ta kwashe ta saka wadda ta rage din itama ta soyata, doyar nayin wajenta kwan ma yanayin wajen shi. Zuwa lokacin shidda harda kwata.
Dan AbdulKadir ya wuce daki dan ya daura alwala, yana so ana kiran sallah ya fara saka wani abu a cikin shi tukunna ya fita masallaci ko zai samu natsuwar yin sallah. Nuriyya kettle ta dauka da nufin dora ruwan zafi su sha shayi, shaf ta manta da man da ya zube a kitchen din, ga kuma ruwan da ta zubar dan ta cika kettle din, ta kuma takashi tana nufar inda socket zaiyi, ta taka man tana wata irin zamewa, sai da tai sama, kettle din ma tayi sama tukunna su duka suka sauka kusan a tare, kettle din a gefe da ruwan ciki daya mungule gabaki dayan shi, ita kuma aka mazaunanta tayi warwas a kasa. Ta dauki wasu dakikai tana sauke numfashin wahala kafin taja kafafuwanta ta mike.
Jikinta take kakkabewa duk ta nade ruwan a doguwar rigar dake jikinta, kettle din ta dauka ta tari wani ruwan, tana kokarin mayar da hawayen da suka cika mata idanuwa taf. Gabaki daya duniyar ta hautsine mata a cikin kankanin lokaci. Kettle din ta jona tana kunnawa. Sannan ta sa abin goge-goge na tsaye ta fara aikin goge kitchen din, tanajin kiris take jira ta fashe da kuka. Tana gama gogewa ta sake mayar da miyar kan wuta ta bata mintina biyar tukunna ta kashe, ko tayi ko batayi ba a haka zataci.
Tana nan tsaye ruwan ya tafasa, kettle din ta kashe kanta, ta dauko flask tana juyewa taji kiran sallah. Ta karasa ta rufe, ruwa ta dauko a fridge sai ga AbdulKadir ya shigo kitchen din, ya karbe robar daga hannunta yana budewa yai Bismillah ya kafa bakin shi, Nuriyya na bin shi da kallo harya sauke robar hadi da wani irin numfashi, ruwan ya mika mata ta karba itama tasha, yana dirar mata ciki da wani yanayi mai sanyi.
"Kibani wani abu inci in fita masallaci"
AbdulKadir ya fadi yunwa yakeji har kan shi na mishi ciwo. Kular doyar ta bude mishi, a tsaye ya saka hannu yana dauka ya saka a bakin shi duk da ta mishi zafi, yanajin ta kamar babu gishiri, kuma kwan bai kama ba, Waheedah harda tattasai take saka musu in zata soya. Baiyi magana ba, saboda yau daya ga azumi, bazai dora alhakin fadansu akan shaidan ba, asalin halayen sune zasu bayyana. Ficewa yayi daga kitchen din zuwa masallaci, jikin shi har kyarma yake sanda aka idar ya taho gida. Bangaren Waheedah ya wuce yana jin kamshin daya hade waje daya baisan kona menene ba, amman ya kara mishi yunwa. Kan darduma ya sameta a daki tana azkar ne da alama.
"Sannu da shan ruwa"
Ya fadi yana kallon yanda fuskarta tai wani sanyi. Murmushi tayi mishi tana idar da addu'ar ta
"Sannun mu"
Ta amsa shi tana mikewa ta ninke dardumar da take kai. Kallon ta AbdulKadir yake tayi yana kallo ta fita daga dakin, tana dawowa da apple a hannunta ta gutsura tana taunawa, Ikram ta dauka a gefen shi tana samun waje ta zauna, yarinyar ta gyarama zama itama a jikinta dan ta bata tasha, taci gaba da cin apple dinta, cikin shi da yaji yayi wata irin murdawa yasa shi mikewa, dan da alama Waheedah ba zata bashi abinci ba, ta daina son shi yanzun...!
*
Please, biko, dan Allah show me love, subscribe to my YouTube channel. Ina bukatar aqallah subscribers dubu daya. Nagode
https://youtu.be/WwocHslDAYk
#LubnaSufyan
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#AnaTare[7/16, 9:56 PM] +234 802 111 7692: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
32
Kan kafet ya zauna yana jiran Nuriyya ta fito daga daki ta dauko musu kular doya. Ko yaji bata dashi, ta ajiye tana samun waje ta zauna tare da fadin
"Masoyi ko yaji bamu da shi, in karbo mana wajen Waheedah?"
Tun kafin ta karasa AbdulKadir yake girgiza mata kai. Bada shi za'ayi wannan danyen aikin ba, ba zata ja mishi jangwam daga dan samun natsuwar shi ba. Kai Nuriyya ta rausayar tana sake mikewa, kofina ta samu guda biyu, a kitchen din ta hada musu tea ta fito dashi tana ajiyewa AbdulKadir na shi, dauka yayi ya kurba dan ya kora doyar da tai mishi tsayuwar mashi a makoshi. Yana dan bata rai jin kamar akwai abinda ya kamata ya kasance cikin shayin da babu, ya saba da Waheedah na saka kayan kamshi a shayinta, yanzun kam ruwan zafine sai madara da milo, ko lipton din ma bai samu a ciki ba.
"Wacce irin doyace wannan Nuriyya? Babu kwai fa"
AbdulKadir ya fadi yana saka Nuriyya hadiye doyar dakyar, gashi tayi mata wani irin salaf, shi baiga kokarin da tayi ba, ko da bata soyu kamar yanda ya kamata ba, sai ya duba kokarin da tayi yai shiru
"Na saka kwai ni dai"
Tai maganar tana saka AbdulKadir din kankance idanuwan shi a kanta
"Bana gani ne? Ya zaki cemun kin saka kwai? Kafafuwa yayi ya rabu da doyar kenan"
Yai maganar a fadace saboda yanda yaji zuciyarshi na tafasa, ga yunwa yanaji ta fitar hankali, amman rabon shi da abinci makamancin mai munin wannan tun wani aiki da yaje Makodi, shima wajen abinda duk ka samu shi zaka aunawa cikinka. Amman ko wannan din zakaji alamun gishiri a jikin shi. Ganin tayi shiru yasa shi jinjina kai kawai, bazai karar da dan karfin shi akan doya da kwai ba. Haka ya dauka yana turawa sai ya danna da shayin ya hadiye. Iya inda yaji cikin shi ya cika ya tsaya yana karasa kurbe ruwan shayin ya mike, dai-dai lokacin da yan nepa suka zabi su dauke wutar su.
Dogon tsaki AbdulKadir yaja, yayi niyyar ya biya ya siyo mai dazun, kwana biyune bai damu daya kunna gen din ba shisa. Daman indai ya biyewa Waheedah ba kunnawar zai dingayi ba, zatace ita babu abinda zatayi da wutar tana da charge, kuma tama fitilar ta ma, sai dai in ana zafine dan su kunna fankoki. Da fitilar wayar shi yayi amfani zuwa daki ya dauko ma Nuriyya tata wayar yana kunna maya fitilar ya ajiye kan kujera ya kama hanya yana ficewa daga gidan batare da yace mata komai ba. Tana jin shi harya fita bata dai dago bane ba, wani irin kunci naban mamaki ya cika zuciyarta fam, ba zata tuna ranar karshe da wani abu yazo wuyanta yai tsaye ba haka.
Har yunwar da takeji ta nemeta ta rasa, kwashe kwanonin tayi tana mayarwa kitchen, acan ta tsaya dakyar ta shanye ruwan shayin tanaji kamar zata kama da wuta saboda bacin rai. Shinkafarta data dora ta duba taga ruwan ya tsane, ta kashe gas din tana barinta a cikin tukunyar ta wuce dakin bacci, alwala ta sakeyi jin har ana kiran isha'i. A daddafe tayi sallah tana idarwa ta janyo wayarta tana bude whatsapp ta lalubo chat dinsu da Asma, ita kadai ce kawarta da zatace suna maganar komai a yanzun, kuma bazawara ce, a FCE suka hadu. Ita Nuriyyar ma ce ta manne mata saboda ganin yanda tafi kowa wayewa da kudi a ajin. Har suka zama kawaye, dan Nuriyya na bala'in so ace tana tare da manyan mutane.
'Asma mutumin nan bashi da kirki wallahi, kinsan dai yanda azumi yake bani wahala ko da nayi sahur balle yau da muka makara, dakyar na soya doya kinji masifar da ya sauke mun'
Kafin kace meye Asma harta karanta sakon
'Ya dauko miki yar aiki kema, kina auren mutum kamar wannan zaki zauna kina shiga Kitchen, ke banzar ina ce, narkewa zakiyi saiya dauko miki yar aiki"
Numfashi Nuriyya ta sauke, duk yanda zata misaltama Asma halin AbdulKadir din ba zata fahimta ba
'Kika san magana nawa nai mishi? Taurin kan shi yafi karfina, yace ba zai dauko ba fa, kuma nasan ba zai dauko din ba'
Kawunan mamaki Asma ta turo mata tana dorawa da rubuto
'Lallai ma, saiki zauna kina kwasar bakin ciki ai, shisa kinganni, auren nan ya gama fita kaina wallahi, tunda na tungule aurena na biyu naji ko zanyi wani ba nan kusa ba, bazan zauna wani katon banza na batamun rai ba. Ga mutane nan kaca-kaca suna lallabani, sha'anina kawai nakeyi. Kudi na shigomun ta ko ina'
Shiru Nuriyya tayi tana tauna maganar, da gaskiyar Asma, kafin igiyar aure ta daureta da AbdulKadir free take jinta, babu nauyi ko tunanin kowa, inda take so nan take zuwa, amman yanzun tana iya tambayar AbdulKadir zataje waje ko baya gari yace ba zata ba, iya wannan ta kasa sabawa dashi, dan auren Anas mayafi take dauka in yana nan tace mishi ta fita, idan baya nan tayi gaba abinta. Balle kuma yanzun ga maganar girkin nan da sauran ayyuka, ta shiga wani irin matsatsi cikin kwanaki kadan da bata taba hangowa ba, ko kafin kwanakin nan, zasuyi waya da AbdulKadir, zasuyi chatting ko yayane, zaizo suyi hira tana kwance a jikin shi. Amman tanajin wani abu can kasan ranta da ta rasa menene.
Sai yanzun takejin farin cikine cikakke bata dashi, ba zatace ma ga asalin yanda yake ba, dan inta taba shigar shi a bayama ta manta. Yanzun ne kuncinta ya karu, rayuwar a cunkushe take jinta. Data dinta ta kashe batare da ta amsa Asma ba. Ta ja jiki ta haye gado ta kwanta, gara ko bacci ta samu tayi watakila zuciyarta zatayi mata sanyi-sanyi. Tana nan kwance taji shigowar AbdulKadir din ya wuce bandaki kan shi tsaye, ruwa ya watso ya fito ya saka gajeran wando dan baiga towel din shi ba
"Nuriyya ina towel dina?"
Ya bukata, kai ta dan dago, bata ganin shi sosai saboda ta kashe fitilar wayarta, tashi kuma ya ajiye a bandaki, tadan hasko dakin kadan. Sai da taji zuciyarta ta doka, dan tunda ta kwaso kayan daga wajen shanya, kulle su tayi a cikin zanin gado ta ajiye can gefe
"Magana nake dake fa"
AbdulKadir ta fadi a kule, saukowa tayi daga kan gadon tana kunna fitilar wayarta ta taka zuwa inda ta ajiye kullin kayan ta kama su taba kwancewa
"Ki mikomun gajeran wando da singlet"
Daukowa tayi, duk sun zama kamfala, musamman gajeran wandon da yake ruwan madara, mayar dashi tayi ta dauko mishi na kakin sojoji shima duk yayi rodi-rodi. Tana dunkule su waje daya ta karasa ta mika mishi, kamar hakan yan nepa suke jira da bugun agogo na alamun cikar karfe tara na dare suka kawo wuta, haske ya gauraye dakin, yana dai-dai da sauke idanuwan AbdulKadir akan kayan ya kuwa ware su yana bude kayan sosai.
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ya fadi yana jujjuya wandon shi
"Bansan akwai kaya masu zuba ba, na hada duka"
Kai AbdulKadir yake girgizawa
"Aikin ki kenan, kullum bakisan abu ba, ko yaushe uzurinki baki sani ba. Hankalin ki bai baki ba'a hade gabaki daya kaya wajen wanki ba? Idan kin hada wandon nan da sauran kaya, me yasa zaki hada farare da masu kala? Ke mahaukaciya ce?"
Ya karasa maganar yana kallon ta
"Kuskure ne kowa nayi"
Nuriyya ta fadi cike da gajiya
"Karki fara mun rashin kunya, wallahi karki fara cewa zaki fadamun magana Nuriyya, baki sanni ba ko? Bakisan halina ba har yanzun, shisa nake magana kina kokarin mayar mun"
Shiru tayi idanuwanta na cika da hawaye, gefen gado ta koma ta zauna, ta dauka yayi shiru, ai kamar lokacin ya fara fada, sai da yayi mai isar shi tukunna ya koma bandakin, ranta inyai dubu a bace yake, kwanciya tayi tana tsiyayar hawaye masu zafin gaske, ko kadan ba wannan rayuwar ta hango ba, bata saba ana mata fada ba, duk bala'in Anas ba koyaushe yake kulata ba, sai ta kaishi karshe, shima in yaga ta hayayyaqo mishi sai yayi shiru ya kyaleta koya fice daga gidan. Amman yanda AbdulKadir ya nuna yana gab da kwada mata mari shisa tayi shiru, ba sai kowa ya gaya mata ba zai dauki kaso daya cikin abinda Anas ya dauka ba.
Fitowa yayi har lokacin ran shi a bace yake ji shisa ya karayin wanka. Ya zagaya kan gadon ya hau yana kwanciya, baya Nuriyya ta juya mishi, tsintar kan shi yai da bai damu da hakan ba, Waheedah ce dai bata isa ta juya mishi baya ba kome yai mata, ko gajiya tayi da kwanciyar zata juya hannu sai dai suyi musayar waje. Ko a jikin shi take kuwa, sai dai in bacci yayi, daya tashi ya ganta saiya kamata ya juyata.
"Ki kashe mana fitila"
Ya fadi yana juya kwanciyar shi, yana jinta ta sauka daga kan gadon ta kaso fitilar ta dawo. Alarm ya saka a wayar shi ya ajiyeta gefe, Addu'ar bacci ya tofa a jikin shi yana lumshe idanuwan shi duk da alamun yunwa da yakeji.
*
Karfe uku da rabi alarm din daya saka ya tashe shi, sai da yayo brush da alwala tukunna ya tashi Nuriyya. Rigar