Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 51

66K to 69K   out of 152.3K words

karantawa tana lumshe idanuwanta ta adana su wajen da tasan ba zasu taba bace mata ba koda ta farka tukunna ta bude idanuwan nata.

'Tara...'

Ta karanta

"Bansan yazan ci gaba da rayuwa bayan abin nan ba Hamma, idan mafarkine ka tabani ta fannin da banajin zan koma dai-dai wannan karin... Ka fifitamun wutar burina ka dawomun da komai baya..."

Ta karasa maganar da wani irin sanyin murya, sosai take jin in har mafarki take a gefen soyayyarshi da take wahalar da ita, burin samun shi zai zauna, zata dinga kallon shi tana jiran ya sama mata wajen zama a rayuwarshi ko da bata samu a zuciyarshi ba.

'Ina son ka, ina son ka da aure Hamma AbdulKadir'

Ta tura mishi tana jiran taji ta farka daga baccin da take, alama tagani na cewar ya karanta sakon, kafin taga ya sauka daga kan WhatsApp din, wani irin numfashi da batasan tana rike dashi ba ta saki, itama kashe data din tayi ta ajiye wayar hadi da mikewa. Bandaki ta shiga ta tara ruwa tana wanke fuskarta, har lokacin numfashi take mayarwa kamar wadda tayi gudu. Zuwa yanzun bata da kalaman da zata fassara abinda takeji. Takai mintina goma tsaye a bandakin ta dafe sink, amman idan ka tambayeta ba zatace ga asalin abinda take ji ko take tunani ba.

Alwala ta daura ta fito daga bandakin, doguwar hijab din da take sallah da ita ta dauko ta saka jikinta. Dardumar da tayi sallar isha'i tana shimfide bata nade ba, kai tahau ta fara jero salloli tana rokon tabbatar alkhairi a koma menene yake shirin faruwa tsakaninta da AbdulKadir din, dan tun daga yanda take son shi tasan abin yafi karfinta, yanzun ma ba zata iya ba, ba kuma zata bata darenta tana tunanin abinda baya karkashin ikonta ba, gara ta bude ma Allah zuciyarta, sosai kuma ta samu nutsuwar da take jin ta kwace mata, akan dardumar bacci mai nutsuwa ya dauketa.

*

Tana da darasin safe, gashi ta tashi da wani irin sanyin jiki, har iskar da take shaqa daban take jinta yau din, bata sake shiga wani yanayi ba saida taci karo da sakon Abba

'Aslm. Waheedah ki sameni kafin ki wuce makaranta'

Haka kawai taji zuciyarta na mata rawa, duk da ba yau bane ranar farko da Abban yakan mata irin sakon ko idan zasuyi magana ko kuma zai bata wani abin. Yau dinne dai takejin kiran kamar zai zamana daban. Sanda tagama shiryawa saida ta biya dakin Mami tai mata sallama tukunna ta fita zuwa bangaren Abba. A bakin kofa ta tsaya ta kwankwasa, saida taji yai magana tukunna ta tura dakin da sallama tana shiga. Waje ta samu kan kafet din ta zauna dan shima anan yake zaune ya miqe kafafuwan shi.

"Ina kwana Abba..."

Ta gaishe dashi cikin sanyin muryarta

"Waheedah..."

Ya kira yana dorawa da

"Kin tashi lafiya? Ya makarantar?"

Hijab dinta da taji ta danne ta dan daga tana gyara zamanta sosai

"Alhamdulillah..."

Wani numfashi Abba yaja yana kallon yanda take komai nata cikin sanyi. Da tunaninta ya kwana a ranshi, har zuwa safiyar ranar yana jinjina ma kaddarar data hadata da AbdulKadir, dan ko a tunaninshi ya kasa dai-daita dacewarsu. Idan zabi za'a bashi na ya aurar da ita cikin yaranshi, yanajin Yazid kadai zai iya aura ma ita hankalin shi a kwance, yana da tabbaci akan Yazid zai riketa da amana, dan bazaice ga rana daya da yaji anyi wata hayaniya dashi ba tun yarintar shi. Muryarshi dauke da nauyin da yake jin dukkan jikin shi yai mishi ya soma magana

"AbdulKadir ya sameni jiya. Nasan halin shi, nasan bazai sameni batare da amincewarki ba, amman ina so in tabbatar daga bakinki Waheedah, amana ceke a wajena kamar yanda suma suke amana, banma kowa maganar ba tukunna, ki fadamun idan kin amince da auren shi..."

Kanta a kasa yake tunda ya fara magana, bata taba tsintar kanta cikin kunya irin wadda takeji ba, wasu zasuce kamar kasa ta tsage su shige, a irin kunyar da take ciki ba tajin zata iya jiran kasar ta tsage, ita take so ta narke ta sulale tabi kasar ta shige cikinta. Ga zuciyarta da take wata irin dokawa kamar zata fito daga kirjinta

"Kimun magana Waheedah, karkiji nauyina, idan har baki amince dashi ba yazo ya sameni ki fadamun, wallahi indai ina numfashi babu wanda zai miki dole akan komai na rayuwa..."

Shirun ta sakeyi tana kara sadda kanta kasa, numfashi Abba ya sauke

"Aure ba abu bane da akanyi dan kowa nayi, ba kuma abu bane da ake fatan idan anyi a fito, aure abune da ake fatan idan har anyi ya zamana har muddin rai, shisa ba'a son gaggawa a cikin duk wani abu daya shafe shi, ba'a kuma son tursasawa, da fahimtar juna ma dole sai an hada da hakuri a zamantakewar da za'a tashi a kwana karkashin inuwa daya. Kimun magana Waheedah, bazan samu nutsuwa akan maganar nan ba..."

Kanta da takejin yaima siririn wuyanta nauyi naban mamaki yau ta samu ta motsa tana dagashi a hankali, da ace nutsuwar Abba bata kanta da bazai ga daga kan ba

"Kin amince da auren shi?"

Abba ya tambaya yana son tabbatar wa, kan ta sake daga mishi a hankali. Wani numfashin ya sauke, yana jinjina ma karfin kaddara da take zuwa karkashin ikon Allah. Kai ya jinjina

"To Alhamdulillah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi..."

Kafafuwanta Waheedah ta tattara, har lokacin ta kasa dago fuskarta, jikinta gabaki daya ya dauki dumi da kunyar Abba da takeji, mikewa tayi dakyar tana juyawa cikin sauri da nufin barin dakin

"Kizo ki karbi kudin makaranta..."

Abba ya fadi yana saka hannu a aljihun shi, amman kamar maganarshi ta kara tunzurata, da gudu ta fice daga dakin tana ja mishi kofar. Murmushi Abba yake

"Oh Allah mai iko..."

Ya fadi, ya jima wani abu bai bashi mamaki ba irin na daren jiya zuwa safiyar yau. Da gaske AbdulKadir da Waheedah sukeyi, yanda yake jinshi zai kwana biyu yana jinjina al'amarin. Wayarshi ya dauka ya kira Mami dan ya sanar da ita kafin ya samu dangin Baban Waheedah din da maganar, duk da sun jima da nuna mishi yana da damar yanke hukunci akan rayuwar Waheedah din bazai hanashi nuna musu godiya da halaccin da sukai mishi ba, zai samesu da maganar duk da yasan ba zasuki kowa yake son hadata dashi ba, balle kuma idan sunji jinin shi ne.

*

"Ina zaki je?"

Muryarshi ta sauka cikin kunnuwanta, tana sakata gyara zaman jakar dake kafadarta tukunna ta juya tana sauke idanuwanta akan shi. Jikin shi sanye da riga fara kal, sai wandon sojoji gajere da silipas din wanka a Kafafuwan shi.

"Hamma..."

Ta kira da wani yanayi a muryarta, wani irin son shi taji ya taso mata har yana ma numfashinta barazana. Tasan ya kamata ta sauke idanuwanta daga kanshi, ta daina kallon shi, amman zuciyarta ce da iko kan idanuwanta wannan karin, ta kuma nuna mata bata gaji da kallon shi ba. Shima idanuwan shi ya kankance akanta da dakyar take ganin kwayar cikin su, fuskarshi a kumbure take har idanuwan da alamar rashin wadataccen bacci.

"Ina zaki je?"

Ya maimaita tambayar yana kallonta, tsaye yake ya hango hijabinta da yake share harabar gidan, blue ne mai hasken da yai mishi kyau sosai. Badan baya ganin masu saka hijab ba, amman kowa zai gani da hijab itace mace ta farko da take zuwa mishi a rai, kuma bai taba ganin wanda hijab yake ma kyau kamarta ba, zai rantse yanayin tafiyarta a cikin hijabanta daban yake. Kamar hijab din na bata wani asirtaccen confidence da idanuwa basa iya gani, sai yaga kamar ba Waheedah mai sanyin halin nan ba, kwarjininta daban yake mishi in tana cikin hijabanta.

Idanuwanta take raba mishi, wannan karin cike da wani yanayi da ya saka jikinshi daukar dumi, kalar hijabin ta kara mata farin da yasa shi furta

"Wanne irin mai kike shafawa?"

Da mamaki bayyane a fuskarta tace

"Vaseline..."

Kankance mata idanuwa ya karayi

"Yana kara haske?"

Dariya tayi tana girgiza mishi kai

"Hamma Vaseline fa"

Kafadunshi yadan daga mata, bazai sani ba, tunda haske take kara mishi a duk ganin dazai mata.

"Ina zaki je?"

Ya sake tambaya a karo na uku. Da murmushi a fuskarta har lokacin tace

"Makaranta..."

Ta dauka wani abu zai canza tsakaninsu da maganar auren, amman bataji komai ba ita kam, banda soyayyar shi da duk lokacin da zata dauka babu wani waje a jikinta daya rage wanda baya dokawa da soyayyarshi, sai ta sake jinshi a wani wajen da batasan yana motsi ba. Babu abinda ya canza, shidinne dai, Hammanta, Sadaukinta, ko babu maganar auren batajin akwai inda zatakai soyayyar shi.

"Da sassafen nan? Waye zai kaiki?"

AbdulKadir ya fadi yana katse mata tunanin da takeyi

"Ina da class, nama makara, napep zan hau..."

Kai ya fara girgiza mata yana sata dorawa da

"Ina zuwa Hamma, ba kullum ake kaini ba"

Kan AbdulKadir yake girgizawa har lokacin, yaushe Waheedah din tai girman da zataje makaranta, ta tafi ita kadai bai zauna mishi ba sam

"Na iya zuwa Allah"

Ta fadi ganin shakkun dake cikin idanuwan shi

"Ki jirani ina zuwa..."

Cewar AbdulKadir din yana juyawa da sauri. Binshi tayi da kallo harya shige bangarensu, idanuwanta akan kofar tana jiran fitowarshi da dukkan zuciyarta. Baifi mintina biyar ba taga ya fito yana takowa zuwa inda take, tari tadanyi da yanda zuciyarta ta matse cikin kirjinta kamar akanta yake tafiyar.

"Muje..."

Yai maganar yana yin gaba, tabishi a baya har wajen motar Yassar, mukullin yasa yana bude kofar, ita kuma ta zagaya, saida ya zaro wayarshi daga aljihun bayan wandon tukunna ya shiga ya zauna, hannu ya mika ya bude ma Waheedah dayar kofar ta shigo itama. Wayarshi ya dora kan cinyarta kamar babu inda zai iya ajiyewa a cikin motar gabaki daya. Daukar wayar tayi ta rike a hannunta, tanajin shi ya tayar da motar yana jansu suka fice daga gidan.

"BUK, old site..."

Tace mishi

"Nace miki bansani ba?"

Kai ta girgiza mishi

"Me yasa kike fadamun to?"

Ya sake maganar yana dan kallonta kafin ya mayar da hankalin shi kan tuqin da yakeyi. Har malamansu gabaki daya yasani, bazai ce ga course din da take dashi ba a ranar, amman idan ya duba wayarshi zai iya fada mata, a cikin labaranta gabaki daya yasan hakan, me yasa take tunanin bai rike ba? Dan bai amsa ba baya nufin bai karanta ba, baya nufin hankalin shi baya kai. Shiru tayi bata amsa shi ba, tunda tasan halin shi.

"Bakici abinci ba...bakici komai ba kika fito"

Yai maganar kamar tunanin ya fado mishi. Girkin Mama ne har ranar, da yunwa ya tashi ya kuma je bangarenta bata gama ba, lokacin daya shiga ma ake fere doya. Ko da yayi maganar da alamar tambaya ne, Waheedah batajin zata amsa shi, bazai sauke mata fadanshi da sassafe ba.

"Kinsan yanda abincin safe yake da muhimmanci?"

Murmushi taji ya kwace mata, ba abincin safe bane kadai yake da muhimmanci a wajen AbdulKadir, duka abinci nada muhimmanci dan baya wasa da cikinshi ko kadan. Wani shago ya hango hakan yasa shi tsayawa, batare dayace mata komai ba ya fice daga motar. Wayarshi dake hannunta ta latsa dan taga ko karfe nawa, zuciyarta nayo tsalle zuwa makoshinta ganin hoton dake kan wayar. Hannuwanta ne babu tantama, da kunshinta da bata manta ranar daya dauka ba.

"Hamma..."

Ta fadi da wani irin yanayi a muryarta tana shafa screen din wayar. Dai-dai lokacin da AbdulKadir ya bude motar ya shigo yana dora mata leda akan jikinta da kashedin

"Karki sake fitowa bakici wani abu ba"

Bata abinci takeyi ba, kallon shi take tanajin wani irin yanayi da bazai fassaru ba, har suka karasa makarantar babu wanda ya sake cewa wani abu. Har department dinsu ya kaita yana zaune cikin motar saida yaga ta shiga aji tukunna ya sauke numfashin da baisan yana rike dashi ba, kafin yai wata irin hamma, ba wani bacci ya samu ba jiya, yana kwance yana tunanin yanda akai rayuwa ta kawo shi inda yake yanzun. Sai dai zuwa safiyar yau komai ya mishi dai-dai. Tana son shi, zai aureta, ya rigada ya gama duk wani tunani da zaiyi akan hakan. Yanzun yaga garin da aka kaishi ne abinda yake ranshi, sai yai magana da Hajja dan yaji ko nawa ne zai tara. Juya motar yayi yana nufar gida.

*

Sallar azahar ya dawo, yana kwance a daki yaji an turo kofar kamar za'a karyata

"AbdulKadir me kayi?"

Yaji muryar Yassar din ranshi da alamun a bace yake. Sai dai a iya tunanin AbdulKadir din baisan ya mishi wani abu da zai bata mishi rai ba. A nutse ya tashi daga kwanciyar shi ya zauna yana dakuna ma Yassar din fuskarshi cike da rashin fahimta.

"Kajini ai, me kayi?"

Yassar ya sake fadi yanajin yanda yake gab da kwashe AbdulKadir din da mari. Aiki ya fita, yau da wuri yake tashi, yana dawowa yakejin ana maganar auren AbdulKadir din da Waheedah cikin wata shidda tare za'a hada da nasu Yazid. Maganar yake ji kamar wasa, saida ya tambayi Mama tace mishi da gaske ne, Abba da kanshi ya fada musu. Yasan halin AbdulKadir zai iya cewa fiye da kowa a gidan, yasan yanda yake son kanshi fiye da tunani, amman bai dauka yakai haka ba. Bai dauka yakai yai amfani da soyayyar da Waheedah din take mishi ta wannan fannin ba.

"Kaimun magana yanda zan gane Hamma..."

AbdulKadir ya fadi a kasalance, bacci yakeji, kuma da niyyar yin baccin ya kwanta

"Waheedah... Me kayi AbdulKadir..."

Dan dafe kai AbdulKadir yayi yana fadin

"Oh... Aurenta zanyi..."

Numfashi Yassar yaja ta baki yana fitar dashi ta hancin shi

"Baka son ta AbdulKadir, me kayi haka?"

Kafadu AbdulKadir din yadan daga mishi

"Tana sona..."

Wata dariya Yassar yayi batare da yasani bama

"Wai ma meya faru ka sameni kanata hure-huren hanci kamar dragon... Ba jiya kake mun maganar yanda take sona ba?"

Kai Yassar ya dafe yana sauke numfashi, sosai yakejin yanda ya kusa kwada ma AbdulKadir mari

"Da nace tana sonka bance kaje kace zaka aureta baka shirya ba"

Gyara zaman shi AbdulKadir din yayi

"Eh haka Abba yace ba'a aure babu shiri, shisa ba za'ayi nan da sati biyu ba, tare da nasu Hamma Mubarak za'a hada, wai za'ayi su lefe... Zanje inma Hajja maganar ma... Zan tara kudin in shaa Allah, albashina da dan yawa... Zai isa idan na tara..."

Ciwon kai Yassar yaji ya saukar mishi, abinda yake nufi daban, abinda AbdulKadir yake fahimta daban, ba shiri na hidimar aure yake mishi magana ba, shiri na zaman aure da yake bukatar fiye da soyayya.

"AbdulKadir... Baka son ta"

Dakuna fuska AbdulKadir yayi

"Tana sona Hamma.. Me yasa bazai ishe mu ba?"

Ya karasa maganar yanajin ranshi ya soma baci, baiga dalilin da zaisa Yassar ya dinga maimaita mishi magana daya kamar itace abu mai muhimmanci a maganar auren, ya tambayi Waheedah tace tana son shi da aure, shima kuma a shirye yake yai zaman aure da ita, bai kuma san meye yafi wannan muhimmanci ba.

"Bacci nake ji... Dan Allah kabarni nikam. Na rigada nagama magana da Abba, auren nan zai faru... Maganganun duk da muke din nan basu da wani muhimmanci tunda ba zasu canza komai ba"

AbdulKadir yai maganar yana komawa ya kwanta hadi dajan mayafi ya rufe jikin shi. Kai Yassar yake girgiza mishi yana dana sanin furta mishi cewar Waheedah nasan shi, har ga Allah bai taba tunanin ba soyayya suke ba, da yasani da bazai taba tayar ma fa AbdulKadir da maganar ba, amman lokaci ya kure. Kamar yanda AbdulKadir din ya fadane, maganganun shi ba zasu canza komai ba.

"Dan Allah karka cutar da ita, karkai amfani da soyayyar da take maka ka cutar da ita AbdulKadir, marainiyace, karka cutar da ita..."

Yassar yai maganar da wani irin yanayi a muryarshi, a kasan zuciyarshi yana addu'ar kar AbdulKadir din ya taba dana sanin auren Waheedah din, dan yanajin ya yanke hukuncin aurenta cikin gaggawa, ko da ya shirya zaman aure da ita, yayi gaggawa yagane hakan a jiya kawai. A wani bangaren yana fatan akwai wani bangare a kirjin AbdulKadir din da yake dokama Waheedah batare daya sani ba.

"Ka jamun kofar inka fita"

AbdulKadir ya amsa kamar baiji maganganun da Yassar din yayi ba.

"Allah ya tabbatar da alkhairi..."

Cewar Yassar yana ficewa yajama AbdulKadir din kofa, idanuwan shi ya lumshe, dan bashi Yassar zai saka tunani ba, bacci mai karfi ya dauke shi.

*

Ba zatace ga yanda satika biyu suka wuce mata ba, tasan dai a cikinsu abubuwa da dama sun faru, harda maganar da Mami tai mata kan auren AbdulKadir din itama kamar Abba tana son karin tabbaci ne. Data samu din kuma addu'a tai musu

"Allah yasa alkhairin juna ne ku, Allah yasa muku albarka a tafiyar dake gabanku Waheedah, Allah ya yafe ma mahaifinka ta kyautata makwancin shi"

Ko ita kadai ta zauna addu'ar Mami kan sanyaya wajejen da batasan suna mata zafi ba. Tun yan gidan na mamakin maganar auren suma har sun daina, dan Zahra ma saida tace mata

"Lallai ma, ki rasa wa zaki aura a duniyar nan sai Hamma AbdulKadir? Ya gama zaneki ya lallabo kuma zaki aure shi...Tafdin..."

Dariya kawai takanyi, Mubarak ma da yakai ta makaranta a cikin satikan saida yai zancen

"Zuciyarki bata kyauta miki ba Waheedah... Ta rasa wa zata janyo muku sai masifaffen nan. A kafa aka dauramun AbdulKadir saina tsinke nayi takaina..."

Shima dariyar tai mishi a kunyace. Ba zasu taba fahimtar yanda take son AbdulKadir din ba, ita kanta ba zatacr ga yawan soyayyar da take mishi ba, halayenshi kaf babu wanda ya taba damunta balle ya daga mata hankali, fadanshi kan tsaya mata a rai duk idan yai matashi wasu lokuttan, tana kuma tsoron fadan nashi, sai dai bai taba zama dalilin da zai hanata tunkararshi da kowacce irin magana ba, kuma bai taba sa taji soyayyarshi ta yi ko alamar dishewa ba. Tana son shi da duk wani abu da yake tattare dashi.

Kwata-kwata tun satin farko take neman wayar Nuriyya bata samu ba, sau biyu ta biya ta makarantarsu bata samunta, sai a sati na biyune ta sameta a waya ashe batajin dadine, har gida taje ta dubata take kuma fada mata sa ranarta da AbdulKadir, tayi mamakin da

'Allah yasa alkhairi'

Kawai Nuriyya ta furta, saidai Waheedah tai mata uzurin cewar dan batada lafiya ne, tadai gyara mata gidan da yai kamar yayi wata baiga tsintsiya ba, ga tarin wanke wanke, kusan duk wani abu da yake kitchen din bashida kyau. Ko ina ta gyara mata tsaf, har girki tai mata tukunna sukai sallama tabar gidan. A satin

23 / 51