Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
tana kwanciya jikin AbdulKadir din da Waheedah takeyi kamar nata ne ita kadai, sai dai duk yanda bacci bai wadaceta ba, ta kasa samun shi, data rufe ido hoton hannun Waheedah ke mata yawo da sunanta da take da tabbacin ita tayi saving din lamba dinta a haka a wayar AbdulKadir din, saboda rashin aji, ita ba zatai haka ba da ta dauki wayar AbdulKadir din tana sake nata sunan zuwa
'Matar Masoyi'
Da tunani barkatai a ranta, dukkan su suna hadewa sukai mata wani irin zafi lokaci yake ta tafiya, wutar da aka kawo yasata sakkowa daga kan gadon. Chaji ta fara sakawa tukunna ta shiga wanka ta fito, gaban mudubi ta zauna ta tsara kwalliya sosai a fuskarta, bum short ta saka da wata karamar riga, tana samun hula ta saka a kanta. Tayi kyau das da ita, yunwa ta fara addabarta, kitchen ta wuce ta dafa ruwan zafi a kettle tana hada shayi mai kaurin gaske ta duba biscuit ta dauko, shima ya kusan kare mata, gashi babu wasu kudi a hannunta, zatai ma AbdulKadir maganar kudi idan an kwana biyu, tasan bazai hanata ba. A kitchen din ta tsaya ta fara shan shayin dan yunwa take ji sosai.
Takun tafiyar AbdulKadir din taji, kafin ya rungumeta ta baya
"Yunwa nakeji Nuriyya"
Yatsine fuska tayi dan tasan baya ganinta, muryarta ciki-ciki tace
"Me zan baka Masoyi? Nima yunwar ce ta tasheni... In hada maka shayi?"
Sake matseta AbdulKadir yayi yana sauke numfashi
"Shayi da me?"
Ya tambaya
"Da biscuit"
Nuriyya ta amsa, tana sa AbdulKadir din sakinta ya kama hannunta yana juyo da ita, ta mishi wani irin kyau mai ban mamaki
"Ni zaki ba shayi da biscuit Nuriyya? Na miki kama da Fajr"
Shagwabe fuska tayi
"Bansan me zan baka ba wallahi, me kake son ci?"
Kafadu AbdulKadir yadan daga mata, shima baisani ba, Waheedah bata tambayar shi abinda zaici, bashi kawai takeyi
"Ni dai bazan ci biscuit ba, bari inyi wanka. Kimun koma menene"
Ya karasa maganar yana juyawa ya fice daga kitchen din, kamar hakan Nuriyya take jira tayi wani irin juyi tana buga kafarta a kasa, ko kadan wannan wahalar ce ba zata iya ba sam, a gidansu ma ba girki take ba, can da babu kudi, gidan Anas ma sai ranar da tayi ra'ayi tunda in bai bata kudi ba, inya ajiye dauka take, duk bala'in da zasuyi, ko kudin waye. Daya daina ajiyewa kayan abincin shi take diba ta siyar, akwai gidajen da ake abincin siyarwa kala-kala a unguwar, wani lokacin ma danyen take kai musu, sai a dinga aiko mata dafaffe har kudinta ya kare. Ranta a bala'in bace ta karasa shanye shayin nata, kitchen din Waheedah ta wuce tana dauko duka kwalin indomie din da ko rabi ba'ayi amfani dashi ba.
Batasan abinda zata dafa mishi ba banda indomie din, in zaici yaci, in ba zaici ba kam batasan ya zatayi dashi ba ita. Wannan wahalar ko kadan jikinta ba zai dauka ba, tasan Waheedah zata dawo babu dadewa, tunda mayyar AbdulKadir din ce bata iya nisa dashi. Tana ta kwashema Waheedah albarka a ranta tana dora indomie din, ta duba, albasa ma bata da ita sai da ta sake komawa kitchen din Waheedah ta dauko ta dawo. Lokacin da AbdulKadir ya fito harta karasa ta kashe gas din, ta samu plate tana juye mishi ta saka cokali mai yan yatsu a ciki. Ta dauka zaiyi magana, baice komai ba ya saka cokalin ya fara ci, kitchen ta koma dan tayi wanke-wanke, a kasan ranta takejin yanda harta fara gajiya da zaman gidan.
*
Mami da kanta tace mata takoma gidan Yassar ta huta abinta, babu wanda zai dameta a can din, dan tunda yan gidan suka ga tana nan sai hirar ta dawo bangaren Mamin. Ita kanta Waheedah din tana bukatar shirun, tasan in tana nan gidan ba zata same shi ba, duk da sosai taji nauyin da kirjinta yayi ya mata sauki, musamman da aka hadu anata hira, sun rage mata kadaicin data jima tana fama dashi. Sun kuma rage mata zafin zuciyar da take tare dashi, sai gab da Magriba Yassar yazo ya dauketa daya dawo daga wajen aiki ya biyo.
Fajr ma bata ganshi ba, bata kuma bi ta kanshi ba, tunda ba bakon waje yake ba, ballantana yana wajen Hajja inda babu wanda ya isa ko murya ya daga mishi ai bazai nemeta ba. Da suka koma tadan samu taci abinci dakinta ta koma, tana sallar isha'i ta haye gado taci gaba da kallon film din daya rage mata tunani ba kadan ba. Har saida taji dakyar take bude idanuwanta sannan ta hakura ta kwanta. Badan taji kiran sallah ba, kawai sabo da tashin asuba dinne yasa tun kafin lokacinta ya karasa harta tashi. Tana gabatar da sallah Ikram ta dauka tabata tasha sukayi kwanciyarsu suna komawa bacci.
Sanda ta tashi goma tayi, wanka ta shiga, ta fito ta dauki Ikram dan tayi mata itama, da kuka aka gama wankan, daman in dai kana son jin kukanta to wanka ko yunwa, kafin wani lokaci harta shirya kanta cikin riga da zani na atamfa da dinkin ya zauna mata sosai, kwalliya tayi tana saka jambaki a labbanta, Ikram ta shirya tsaf tana kallon yanda kamanninta da AbdulKadir suke kara fitowa
"Ikram ki rufamun asiri mana, dan Allah banda idanuwan"
Waheedah ta fadi tana gyarama Ikram din riga da ta dauka wasa take mata ta dashe mata baki tana dariya, itama dariyar ta tsinci kanta dayi
"Dariya kike ko? Da gaske banda idanuwan..."
Waheedah take fadi tana jijjiga Ikram dake dariya sosai
"Kuma karkiyi irin rigimar shi, macece ke wahala zaki sha"
AbdulKadir da tun daga bakin kofa yakejin dariyar su, hakan yasa shi murza hannun kofar yana shigowa ya tsaya yana kare musu kallo da murmushin daya manta rabon da yayi shi a fuskar shi yace
"Ki daina hure ma yarinyata kunne...Fajr da ya biyo rigimarki me nace?"
Juyawa Waheedah tayi fuskarta dauke da mamakin ganin AbdulKadir din, duk da ya saba shigowa waje bataji shi ba sai dai ta ganshi, kare mishi kallo tayi ya saka gajeran wando iya gwiwarshi na sojoji sai farar riga a jikin shi, kamshin turarukanta yakeyi. Fuskar shi har lokacin da kumburi, kare mishi kallo tayi kafin ta dauke idanuwanta daga kan shi tana janye Ikram ta matsar da ita tsakiyar gadon ita tana zama a bakin gadon, ta dora hannuwan ta daga gefe da gefe. A hankali AbdulKadir yake takawa zuwa inda take, tsintar kan shi yayi da tsugunnawa saboda Waheedah ta sunkuyar da kanta.
Hannun shi yakai yana dago da habarta, agogon dake daure da hannun shi tabi da kallo, shine kyauta ta farko data shiga tsakaninta da shi, duk tarin agogunan shi, wannan din shi yafi daurawa fiye da ko yaushe, lokutta da yawa wanka da alwala duk dashi yakeyi, fatar duk ta koke, in tai mishi magana sai yace agogon na da muhimmanci a wajen shi, har wani ta siya mishi, amman dai yafi son wannan din. Bama aiki yake ba, batasan me yasa yake yawo da shi ba. AbdulKadir idanuwanta yake son gani, so yake yaga ko da giccin tarin soyayyar da take mishi ne.
"Wahee..."
Ya kira yana wani irin sauke murya cikin yanayin da baisan zuciyar shi zata taba iya jin shi ba balle ta fito dashi, idanuwan nata kuwa ta saka cikin na shi, maganganun Mami na dawo mata suna saka wani abu da batasan yana kulle a kirjinta ba budewa. Komai takeji yana dawo mata kamar a lokacin yake faruwa, tana jin wasu irin hawaye da suke fitowa daga wani waje a zuciyarta daya jima yana ciwo kafin su fara zuba kamar an bude su, dumin su ya fara ji a jikin hannun shi da yake kan habarta kafin ta sake sunkuyar da kanta. Da sauri AbdulKadir ya tashi ya zauna gefenta yana kama hannunta ya juyo da ita ta fuskance shi
"Waheedah..."
Ya kira yanajin yanda kukanta ya karasa birkita mishi tunani, wani irin dana sani yana saukar mishi kamar ruwan sama, ba ita ba, yanajin zai jima a rayuwar shi bai dagawa wani hannu ba a yanayin da yakejin shi. Hannu yasa yana kamo fuskarta ta ture shi tana saka nata hannun ta goge hawayen da sunqi daina zubowa, hannu AbdulKadir ya sake kaiwa, kafin ya taba fuskarta ta sake ture shi
"Ka kyaleni....kabar ni"
Ta fadi cike da kashedin da AbdulKadir bai taba tunanin tana da zuciyar fito da shi ba, dan sanyin halinta yayi yawa, wani kuka na sake kwace mata. Gyara zaman shi yayi yana kokarin saka hannuwan shi duka biyun wannan karin, ture su ta sakeyi da dukkan karfinta tana mikewa, wani irin kallo take mishi da yasa shi jin kamar an watsa mishi ruwan kankara
"Ka kyaleni, kaje ka taba fuskar Nuriyya"
Da mamaki AbdulKadir yake kallonta, kafin shima ya mike yana son hade space din dake tsakanin su, baisan abinda ya kamata yace mata ba, kuma lallashinta yake sonyi, taki bari ya tabata, gabaki daya komai ya cunkushe mishi
"Dan Allah kiyi hakuri Waheedah..."
Ya fadi yanajin shima gab yake da nemo kuka duk inda yake, kilan in ya taga hawaye a fuskar shi sai tagane abinda nata hawayen yake mishi, takawa ya sakeyi, ta dago hannuwanta tana kokarin ture shi, kama hannuwan nata yayi yana sa karfi ya rike su
"Karyewa kike son yi shisa zaki tureni ko?"
Kiciniyar kwacewa takeyi zuciyarta na wata irin tafarfasa
"Nace kiyi hakuri...Dan Allah kiyi hakuri, ba zan kara ba wallahi"
AbdulKadir ya karasa maganar muryar shi na karyewa, har lokacin yana rike da hannuwan Waheedah da take kallon shi kamar tana shirin rufe shi da duka, ga hawayen da bayaso sunki daina zubar mata
"I'm sorry"
Ya fadi da harshen turanci yana dorawa da fadi cikin harshen larabci
"Ana Asif..."
Sosai yake kallonta, tunda yake baisan yanda hakuri yake fitowa daga zuciya ba sai yanzun da yake a gabanta, hannunta daya ya dago ya dora shi a kan kirjin shi inda zuciyar shi ke dokawa kamar zata fito waje saboda tashin hankali
"Su kadai ne yarukan da nake ganewa, idan akwai wani kalar hakurin ki fadamun....nace bazan kara ba, idan akwai abinda nayi miki banda mari ki fadamun duk sai in hada in baki hakuri"
AbdulKadir yake fadi yanajin a wannan gabar kome take so shidin zaiyi indai zata hakura ba zata kara furta mishi kalmar ya saukake mata auren shi ba, hannuwanta take kiciniyar kwacewa, sakar mata yayi, yana kallo tasa ka bayan hannu ta goge fuskarta da har ta kara ja saboda kukan da takeyi
"Kinga fuskar ki harta kumbura, kiyi hakuri kar kanki yayi ciwo Wahee..."
Kallon shi take, tanajin wani tuquqin kishi naban mamaki yana taso mata
"Bakayi tunanin kaina zai ciwo ba ka kara aure ban sani ba?"
Maganar ta dirar mishi cikin kunnuwa tana daukar wasu dakika kafin ta karasa cikin kan shi tana rarrabuwa zuwa inda zai fahimta
"Da kayi auren ka ban sani ba kamar na isa in hanaka, sai ka zabi ka dauki wata daya kafin ka gayamun ta text...Text"
Waheedah ta maimaita maganar cikin gunjin kukan da yaji ya samu wajen zama a zuciyar shi yana daskarar dashi tsaye a wajen, wannan karin ita ta taka tana hade space din dake tsakanin su, cikin fuska take kallon shi
"Bakayi tunanin abinda zanji ba ko Sadauki? Banda darajar da zan san ka yanke hukuncin da ba rayuwarka kawai zai canja ba harda tawa.... Bai isheka ba sai da ka sake nuna mun duk abinda zanji a kai ba matsalarka bane, ka fadamun ka kara aure ta text!"
Wannan karin da hargowa ta karasa maganar tana ture AbdulKadir din duk da ko motsi ya kasayi, tsaye yake kamar bishiyar da ta samu dashe mai kyau, kalamanta yake ji na saukar mishi da wani irin yanayi da bashida kalaman dora su, kuka Waheedah takeyi mai sauti, zuciyarta na ciwo kamar zata rabu da kirjinta, numfashi take ja tana fitar dashi a wahalce, sai dai kalaman takeji na tunkudedeniya da juna wajen fito mata, tagaji da rike su, tagaji da rike komai
"Da ka fadamun ta text, ko kadan hankalin ka bai baka ka fadamun kawata ka aura ba ko? Saboda kai ne, AbdulKadir da babu wanda ya isa, darajar kowa a kasan taka take shisa baka fadamun ba sai da ka dauko ta ka kawomun ita cikin gida na....Kawata Sadauki... Kawata ka aura, idan kaso ka kasheni zaka iya..."
Waheedah take fadi numfashin ta har barazanar tsayawa yake saboda kukan da take tana kuma magana a lokaci daya, amman ta kasa shiru, AbdulKadir din take turewa ko motsi ya kasayi
"Bakayi tunanin ya zanji ba ko? Shisa duk matan Kano....matan duk da suke Kano. Me yasa sai ita? Me yasa zaka sa in raba komai naka da ita?"
Ta karasa maganar wannan karin kamar wadda ta sami tabin hankali, jikinta ko ina bari yake da kukan da take, hannun AbdulKadir din guda daya ta kamo da duka nata biyun tana dorawa akan kirjinta
"Kaji?"
Ta tambayeshi wasu sabbin hawayen na wanke mata fuska tana sake ware hannun shi akan kirjinta inda zuciyarta ke mata ciwo kamar zata fado, wannan karin muryarta da rauni ta fito tana kuma sauka can kasa
"Tun bansan menene so ba zuciyata take doka maka, baka bani dalili ba, ban taba bukatar wani dalili na son ka ba, saboda kaunar ka bata bani wannan zabin ba, dan ban taba fada maka ba shisa bakayi tunanin ina kishin ka ba?"
Waheedah ta fadi tana sauke hannun shi daga kirjinta tana saka yatsunta cikin nashi ta dumtsa
"Duk yanda zuciyata take fadamun yanda take son ka kasance nawa ni kadai, kullum sai na fada mata kai ba nawa bane ni kadai, addini baice ka zama nawa ni kadai ba, nasani Sadauki...dan Allah me yasa ka hadani kishi da ita? Me yasa ita? Kawata ce Sadauki? Ka manta kamar Amatu nakejin Nuriyya?"
Hannun shi AbdulKadir ya zame daga cikin nata yana matsawa da baya taku biyu, kafin ya juya ya sake wani taku biyun, tsugunnawa yayi yana neman iskar da yakeji ta mishi kadan kamar mai asthma haka numfashin shi yake barazana, mikewa yayi har lokacin iska yake nema tukunna ya tantance asalin abinda yakeji, abinda kalamanta suke mishi, bin shi Waheedah tayi tana sake kamo hannun shi, tana jin dumin hawayenta wani na tunkudo wani kafin tace mishi
"Ina zaka je?"
Kai AbdulKadir ya girgiza mata yana son samun wadatacciyar iskar da zai iya fito da sauti kowanne irine, zuciyar shi yakeji kamar an sa hannu a kirjin shi an matse ta ana rabata da duk wani jini da yake jikinta
"Baka duba cewar na dauki ido na kyaleka ba, sai ka dinga zuwa mun da ita kamar kana son nuna mun kawata ce ka aura, saboda ka isa, babu kuma yanda zanyi da hakan"
Waheedah ta fadi da wani irin nisantaccen yanayi a fuskar ta, kai AbdulKadir ya sake girgiza mata yana so tayi shiru ko numfashin shi zai dai-daita kan shi ya rage zafin daya dauka, nata kan take girgiza mishi idanuwanta har wani yaji-yaji suke mata, tana hadawa da jijjigawa kamar yana bacci tana so ta tashe shi
"A gabana kake rike ta, tana kwanciya a jikin ka....kana so ka kasheni tana tayaka... Zuciyata na mun ciwo... Sosai zuciyata take mun ciwo... Bazan iya zama da kai ba, zaka kasheni..."
Cewar Waheedah, kafin a gajiye ta karasa da
"Ba soyayyar ka bace farko na, ba zata samo karshe na ba!"
Hannun shi daya AbdulKadir ya dago yana kama na Waheedah ya cire daga jikin dayan nashi yana dafe fuskar shi da tafukan shi, hadi da jan wani irin numfashi a wahalce, ba zai tuna ranar karshe da wani abu ya same shi yasa shi jin yana son ya ruga wajen Hajja ba sai yanzun. So yake ya ruga wajen ta kamar yaro dan shekara uku da aka kwacewa abin wasan shi, wata kila idan ya ruga Hajja ta saka hannu ta tarbe shi in zata iya ta daga shi ta rike shi a jikinta hawaye su zubar mishi ya samu saukin abinda yake ji. A filin duniya, a shekarun shi da Allah ya bashi aron su daga ranar farko zuwa yanzun da yake tsaya baiyi tunanin akwai tashin hankali kalar wanda yake ciki ba.
Tun kafin ya auri Waheedah duk idan ya kalleta akwai raunin da yake tare da ita da yake saka shi jin son yi mata rumfa ya kareta daga duk wani abu da yake a karkashin ikon iyawar shi, lokacin da igiyar aure ta daure su karkashin inuwa daya, bai fito daga masallacin da hakan ta faru ba sai da alkawurra masu tarin yawa, cikin su harda kokarin ganin wani abu bai cutar da ita ba, in har yana da ikon hakan. Sai dai a tsayin zaman su duk yanda yaso kareta daga hakan, baiyi tunanin kareta daga kan shi ba, baiyi tunanin shi zai iya cutar da ita fiye da kowa ba. Da za'a tambaye shi mutane uku da zasuyi komai saboda shi, mutane uku da zasu sadaukar da komai dan farin cikin shi, Waheedah zata zamo ta ukku bayan Hajja da Abba.
Da gaske ne ba zai ce ya bude zuciyar shi da soyayyarta ba, kafin ranar da Yassar yai mishi zancen ta, bai taba ko a mafarki hango aurenta ba. Amman tun kafin hakan ita din bangare ce ta rayuwar shi, ko da bai aureta ba yana da tabbacin labarin rayuwar shi ba zai cika batare da ta fito a shafuka da yawa ba. Daga ranar daya aure ta yasan cewa ba ita ya fara so ba, amman ita din ce duk wani abu da yake bukata. Baya tunani mai tsayi a kan kowanne bangare na rayuwar shi, shisa bai taba tunanin hukuncin daya dauka shi kadai ya shafa, shi kadai zai taba harda ita ba, kuskuren farko da yaji yayi a rayuwar shi. Yake kuma jin shi har cikin kasusuwan shi shine manta duniyar shi gauraye take da tata, manta cewar duk wani mataki da zai taka ko ya taka shi tare da Waheedah ne, abinda duk ya taba shi zai taba ta itama, kamar yanda yake jin duk abinda ya tabata shi ya taba. Shisa yanzun ciwon da takeji ya lullube shi ruf...!
#AbdulKadir
#LubnaSufyan
#Nagode da dukkan kaunar ku.[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
29
Tsugunnawa yayi yana fitar da numfashi a wahale, cikin shi ke ciwo saboda hanjin shi da yakeji sun tattaru sun