Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABDDULKADIR Soyayya Da Ta Zama Rauni by Lubna Sufyan

Author :  Lubna Sufyan Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 51

3K to 6K   out of 152.3K words

shiga rigimar su kaine zaka sha kunya.

"Ikram ce kika goya haka?"

Anty ta tambaya tana daga hijab din Mami, taga yarinyar ta farka tana ta kalle-kalle.

"Idon ta biyu ma..."

Cewar Anty

"Ikon Allah..."

Mami ta fadi tana mikewa ta kwance goyon tana sauko Ikram

"Ke baiwar Allah babu magana..."

Inji Mami tana gyarama Ikram din zama, da alamu hakurin mahaifiyarta ta biyo, sam yarinyar bata da rigima, ruwa ta karba ta zuba a murfin tana ba Ikram din

"In kuma basa ba yar su ruwa fa?"

Anty ta bukata

"Nidai ai na bata, wannan shirmen nasu na zamani ba dani za'ayi shi ba, cikin su babu wanda ba'a bama ruwa ba, meya same su?"

Dariya Anty tayi

"Ni kaina bazan iya ba wallahi, gani nake daukar alhaki ne..."

Hira suke a hankali a hankali, Anty ita tasa Mami dan tsakurar abinci, dan damuwa ce fal ranta.

"Ba za'a zuba a mika ma Abdulkadir ba kuwa? Yana wajen nan"

Mami ta fadi tana sa Anty kallon ta

"Ni rabani da wannan dan Allah, ya koma gida yaci wajen dayar matar shi, ban zubo abincina da shi ba nikam"

Shiru Mami tayi, sai dai duk yanda taso ta nuna halin ko in kula da Abdulkadir din sai ta kasa, Ikram ta mikama Anty tana mikewa ta taka zuwa kofa tasa hannu ta bude dakin tana leqa kai, yana zaune kuwa ya hade kanshi cikin hannayen shi.

"Abdulkadir..."

Ta kira a hankali tana kallon yanda ya dago kai, idanuwan shi sun sauya launi. Yanayin kaddarar su na mata nauyi

"Ba zaka shigo kaganta ba?"

Abinda yake son yi kenan, amman ya kasa, yanzun dinma kunyar Mami tasa shi sadda kanshi kasa yana kasa cewa komai.

"Ka shigo ka ganta..."

Mami ta umarta, sai da taga ya mike tsaye tukunna ta dawo da kanta cikin dakin, a hankali ya tako yana shigowa, daga bangon kusa da kofar ya tsaya yana jingina bayan shi a jiki, inda Mami take zaune ta koma tana zama, idanuwan shi ya tsayar kan Waheedah da nata suke a rufe da alamun bacci, duk da haka yana jin gabaki daya idanuwan su na yawo a jikin shi, ya zabi yaki kallon sune kawai dan bayason yaga kallon tuhumar da suke mishi.

Zuciyar shi yaji tayi tsalle tana shirin dawowa cikin makoshin shi, kafin ta koma mazauninta tana ci gaba da wata irin dokawa da yake ji ba cikin kunnuwan shi kawai ba, har a ko ina na jikin shi, bai tsammaci Waheedah zata bude idanuwan ta data sauke cikin nashi ba.

"Waheedah... Alhamdulillah..."

Yaji muryar Anty ta fadi, yana kuma jin motsin kannen shi da suke mikewa suna tahowa sukai ma gadon Waheedah din rumfa, yadai daina gane me suke ta fada, saboda har lokacin idanuwan Waheedah na cikin nashi, kallon shi take da wani irin yanayi da yasa zuciyar shi rawa. Yasha ganin yanayi da dama cikin idanuwanta, kaunar shi na daya daga cikin yanayoyin da suka rinjayi sauran, suka rinjayi lokuttan da ko a kasan bata mata ran da yakan gani akwai kaunar shi. Wannan yanayin bakone, kuma bazai ma kan shi karya ba, ya soma ganin alamun shi wajen kwana hudu da suka wuce. Sai dai duk idan yaga giccin yanayin yakan ga alamun kaunar shi da yake son rinjayar ko meye din yake gani.

Yau kam kallon ta yake, duba idanuwanta yakeyi sosai yana neman alamar kaunar shi a cikin su ya rasa, a hankali yake girgiza mata kai, akwai inda ta boye soyayyar shi, ba zatai mishi haka ba, Waheedah ce yasani, kaunar shi bangare ce na rayuwarta da bata boye mishi, ba zata fara ba yau, bakin ta yaga ya fara motsawa kafin yaji dirar muryarta cikin kunnuwan shi da fadin

"Mami dan Allah ku ban waje inyi magana dashi..."

Bazai ce ga asalin abinda yake ji ba, amman yasan bayason subar dakin, bayason fuskantar ta, a karo na farko da yake son gujema fuskantar wani abu, bai taba hango zuwan ranar nan ko a mafarkin shi ba.

"Ko ruwa ki sha..."

Anty ta fadi, yana kallo Waheedah ta girgiza mata kai, har lokacin shi take kallo da yanayin nan cikin idanuwan ta.

"Ina son magana da shi dan Allah..."

Ta sake furtawa, yana kallon daga Mami har Anty suna mikewa, su Salim suka fara wucewa suna fita daga dakin. Anty ce karshe, bata fita ba sai da ta dan tsaya tana mai wani irin kallo kamar tana son yawo da idanuwanta cikin zuciyar shi ne taga abinda yake boyewa kowa, tukunna ta fice tana turo musu kofar.

"Ka zo ka zauna..."

Waheedah ta fadi, daga inda yake taga ya girgiza mata kai. Zuciyarta take jin ta daskare a kirjinta, ta dunqule waje daya kamar dutse, ta dauka datai hakan ba zatai mata ciwo ba, ba zata ji yanda take dukan kirjinta da wani yanayi da yake barazana da numfashin ta ba.

"Magana zamuyi Abdulkadir..."

Ita kanta saida taji sunan ya dira cikin kunnuwanta da wata murya da tasa jikinta bari, balle Abdulkadir da yake jin kafafuwan shi na rawa, yaune karo na farko a tsayin rayuwar shi data furta sunan shi kai tsaye haka.

"Waheedah..."

Ya kira da bayanannen mamaki a fuskar shi da muryar shi.

"Idan ba zaka zauna ba shikenan"

Cewar Waheedah cikin sanyin muryarta din nan, da yau yake taba shi a wajajen da baisan akwai su a jikin shi ba.

"Waheedah..."

Ya sake kira yana jiran hakan yai tasiri a kanta kamar ko da yaushe. Sai dai cikin idanuwanta yake ganin katangar daya kasa ko motsi balle yayi wani abu akanta tana ginuwa a tsakanin su, kai yake girgiza mata a hankali, kamar hakan kadai ya isa ya hana abinda yake faruwa ya faru.

"Aurenka zaka saukake mun!"

Maganar ta jima tana mishi yawo kafin ta samu wajen zama tana sa shi kokawa da shaqar numfashin da yakeyi ta hanci, bude baki yayi yana soma shaqar iskar ta bakin shi ko zata wadace shi, yakai mintina biyu a haka kafin yaja wani irin numfashi, budaddiyar muryar shi na sake budewa da wani yanayi yace

"Karki sake mun irin wasan nan, bana so, karki sake"

Wata dariya tayi da sautin ta yai mata wani iri har a cikin kunnuwanta, kafin wasu hawaye masu dumi da bata da iko dasu suka zubo mata

"Ba wasa nake ba, Sadauki ba wasa nake ba"

Lumshe idanuwan shi yayi yana bude su, Sadaukin da ta kira shi na rage bugun da zuciyar shi take yi, yana kuma bashi karfin raba jikin shi da bangon wajen yana karasawa inda take yaja kujerar ya zauna gab da gadon nata, hucin numfashin shi da taji kan fuskarta na sata runtse idanuwan ta, wani irin abu na tsirga mata har kasan zuciyarta, sanannen yanayin da takan ji duk idan yai kusa da ita haka take jira ya dirar mata, amman shiru, babu ko alamar shi, hakan yasa ta bude idanuwan nata tana jan jikinta ta mike zaune, bayanta ta jigina da gadon da take kai tana kallon shi.

A duk jikin ta take jin lokacin da take jira yayi, lokacin da batasan ta dibarma zama dashi ba sai yanzun take ji har a kasusuwanta ya cika

"Ka saukakemun auren ka"

Ta sake maimaitawa, wannan karin shi yai wata yar dariya yana kallon ta kamar ta samu tabin hankali

"Doctor din nan yace babu wata matsala, haka yace baki samu wata matsala ba..."

Abdulkadir yake fadi, maganganun Waheedah din na tabbatar mishi ta samu matsala a kwakwalwar ta, da hankalinta ba zata furta mishi wannan kalaman ba, bazai kusa da ita haka ta sake maimaita kalaman ya saukake mata auren shi ba.

"Ki kwanta ki huta sosai kina jina?"

Yai maganar yana daga mata girar shi, cikin yanayin da take jira hannunta da taji ya motsa ya sauka akan fuskar shi, sai taji shi akan tata fuskar tana shafa kuncin ta, cikin yanayin daya sashi saurin fadin

"Waheedah..."

Wasu hawayen taji da suka fi na dazun dumi sun sake zubo mata.

"A gaban yarana, Sadauki a gaban yarana..."

Take fadi tana jin wani daci na taso mata daga kirjinta, kalmar hakuri na daya daga cikin kalaman da baya amfani dasu, shisa yanzun da yake neman ta inda zai fara furtawa ya kasa, indai abinda take son ji kenan zai kokarin furta mata ko zata dawo cikin hayyacinta.

"Ka saukakemun auren ka, dan Allah ka saukakemun auren ka"

Take fadi tana kamo hannun shi, da sauri ya rike hannun nata yana dumtse wa, yanajin siraran yatsunta da suke barazanar ballewa kowanne lokaci cikin nashi, suna saka shi sassauta rikon dayai mata

"Bakisan me kike fadamun ba ko? Baki san kalaman da suke fitowa daga bakin ki ba"

Abdulkadir yake maganar yana yawata idanuwan shi kan fuskarta, yana so tagan shi, yana so taga shine Abdulkadir. Kamar tasan hakan yake nufi ta furta

"Nagan ka...ka yarda dani naganka, na kuma san me nake fadi. Ka saukakemun auren ka nace, kuma wallahi da gaske nake... Dan Allah sadauki"

Waheedah ta karasa maganar wani irin kuka na kwace mata, ji take in ta kara kwana daya da igiyar auren shi a kanta hauka zatayi.

"Kaji dan Allah..."

Hannun ta ya saki yana jan kujerar shi baya, kai yake girgiza mata, baisan akwai wani waje mai laushi daya rage a zuciyar shi ba sai yanzun da Waheedah tasa kalaman ta dai-dai wajen tana dannawa. Yana alaqanta wannan hargitsin da yake ji da yanda ya jima baiji tashin hankali ba. A gaban shi abokan aikin shi babu adadi suka tarwatse, wasu daga sassan jikin su na dukan jikin shi harda fuskar shi, a gaban shi harsashin bindiga yasha fasa kan abokan aikin shi, mutanen daya yarda dasu da rayuwar shi, mutanen daya kwashi shekaru yana kwana waje daya dasu a karkashin kasa ko a samanta. Bayajin akwai sauran tashin hankalin dazai gani ya taba shi, asalima ya dauka ya jima da katange zuciyarshi da faruwar hakan.

Sai yanzun da Waheedah take karyata shi, take nuna mishi raunin katangun daya gina.

"Dan Allah Waheedah...kinji... Dan Allah ki daina mun wasan nan"

Da mamaki take kallon shi, take hango raunin da bai taba bari tagani ba, da sati daya daya wuce ne taji taushi irin wannan a muryar shi, ta hango rauni haka a cikin idanuwan shi, da tana da tabbacin zuciyarta ta gama narke mata da soyayyarshi da ta jima tana dawainiya da ita, da yanzun tana jikin shi ta rike shi cike da tsoron kar tabar kofar da wani abu zai sake shiga tsakanin su fiye da yanda ya riga da ya faru, amman yau babu abinda hakan ya kara banda sa zuciyarta yin wani taurin fiye da yanda takejin ta a kirjin ta.

Ganin da gaske bai dauka cikin hankalinta take magana ba yasa ta fadin

"Mami..."

Cikin wani sabon hargitsin Abdulkadir yake kallon Waheedah da take hawaye kamar an bude wani abu.

"Mami!"

Ta sake fadi da karfin da yasa Mami turo kofar babu shiri, ganin kukan da Waheedah take yasa Mami fadin

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un....Waheedah? Me yake faruwa haka?"

Salatin da Mami tayi yasa Anty biyo bayanta tana ma su Salim alamar dasu tsaya nan inda suke karsu biyo su, ita ta karasa da sauri gefen Waheedah din ta zauna tana rikota jikinta. Kuka Waheedah take kamar numfashin ta zai dauke, kallon ta Abdulkadir dake zaune yake yana jin shi kamar a mafarki, yana jin shi shirun da yaji lokacin da bomb ya fara tashi da abokan aikin shi a karo na farko a gaban shi, shiru ne da bai taba fatan ya sake jin irin shi ba, bai dauka akwai abinda ya isa ya sake saka shi jin irin shi din bane bama, sai yanzun.

"An...Anty..."

Waheedah take fadi tana jin numfashin ta na mata wani sama-sama.

"Waheedah dan Allah ki daina kukan nan... Kinji...duk gamu nan, ko ma menene, muna nan tare dake, kina jina?"

Kai Waheedah take girgiza ma Anty tana ci gaba da wani irin kuka da yasa jikin Mami yin sanyi, dan ita kam tana tsaye ta rasa abinda ya kamata tayi

"Anty kuce ya saukake mun, dan Allah kuce Sadauki ya sakeni!"

Ba Abdulkadir din ba, har su Mami saida suka girgiza da kalaman da Waheedah din ta furta

"Kunji, kuce karya fita daga dakin nan bai rabani da auren shi ba..."

Wannan karin Anty nata idanuwan cike yake da hawaye, fuskar Waheedah din ta dago tana kallon ta

"Waheedah kinsan me kike fada?"

Anty ta tambaya cike da tashin hankali, tasan auren Waheedah da Abdulkadir wani irin aurene da yake cike da hargitsi, ta hango mutuwar shi a watannin kusan takwas da suka wuce, amman bai mutu ba, batasan dalilin da yasa sai yanzun ba. Duk da zatai karya idan tace a watannin baya bataso mutuwar auren ba, ko dan kwanciyar hankalin Waheedah din, amman yanzun da take ganin abin na shirin faruwa a gaban idanuwanta, tashin hankalin da take ciki bazai misaltu ba.

Mikewa Abdulkadir yayi

"Ina zaka je? Ka dawo fa, karka fita baka rabani da auren ka ba... Ka dawo"

Waheedah take fadi tana kai hannu ta fisge karin ruwan dake jikin dayan hannun nata. Mami kallon ta take tana da tabbacin ba a cikin hayyacinta take ba. Hannu Abdulkadir yadan daga yana kasa magana, kafin dakyar yace

"Iskar dake dakin tamun kadan... Zan fita in shaqi iska ne"

Yai maganar muryar shi can kasan makoshin shi.

"Ka saukake mun saika fita kasha iskar..."

Waheedah ta fadi tana sa hannu ta share hawayen dake fuskar ta, tana tsayar da idanuwan ta akan fuskar shi da wani irin yanayi da yasa bugun zuciyar shi karuwa. Juyawa yayi

"Sadauki... Sadauki!!"

Baiko juya ba, tafiya yaci gaba dayi yana ganin kofar dakin ta mishi nisa, kafin ya samu ya fice, ko kofar bai ja musu ba, Anty ta rike Waheedah gam, dan shirin sauke take daga kan gadon tabi Abdulkadir

"Anty ki sakeni, kuna kallo fa ya fita, Mami ki bishi ki karbomun takardata, idan bazai rubuta ba ya fada miki da bakin shi ki dawo ki fadamun..."

Kallon ta Mami takeyi

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Ta furta a hankali tana ci gaba da maimaitawa, dan batasan wani abu daya kamata ta fadi ba. Wannan tashin hankalin da yake faruwa a gaban idanuwanta yafi karfinta.

"Anty dan Allah ku kira shi, kinji... Ku kiraa sh..."

Bata karasa maganar ba, ta sulale jikin Anty data saki wani irin sakati a firgice, cikin tashin hankali ta ke girgiza Waheedah

"Haj Sakina ba kallona zakiyi ba,ku kira likita mana..."

Da sauri Mami ta fita tana ma su Aminu magana dasu kira likitan, kafin kace meye saiga likitan da gudu, wani ma yana biyo bayan shi, dayan ne yace ma su Anty su fita daga dakin, ya rakasu har bakin kofa yaja kofar.

"Me yake faruwa wai? Anty me yake faruwa?"

Zainab ta tambaya cike da damuwa.

"Meya sameta? Naga Hamma ya fita a hargitse shima... Dan Allah kuyi mana magana"

Cewar Nabila muryarta na karyewa. Hamma da ta fadi yasa Anty kallon su Aminu da fadin

"Ku bishi dan Allah, kar yace zaiyi tuqi a yanayin da yake ciki..."

Tsayawa sukai suna kallon ta cike da rashin fahimta, tsaki ta saki tana kama hanya cikin sauri ta fita daga wajen, sai dai bata ga Abdulkadir din ba, ko alamun shi bata gani ba, har wajen asibitin ta duba amman bata ganshi ba, wajen da taga an ajiye motoci ta nufa tana duddubawa, duk da batajin tasan wacce irin mota Abdulkadir din yake da ita, kawai dai ta duba ne ko Allah zaisa tagan shi. Dan dafe kai Anty tayi tana fadin

"Oh Allah na..."

Kasan zuciyarta take addu'ar Allah ya kaishi gida lafiya idan can din ya nufa, kafin ta juya tana nufar hanyar da zata mayar da ita cikin asibitin Aminu Kano din, a duk jikinta take jin wannan abin bana lafiya bane...!

*

#Abdulkadir
#FWA
#AnaTare[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732: ©️
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com

*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*

02

A nutse yake tuqin shi, dan ba ranar bane karo na farko daya taka mota cikin rashin kwanciyar hankali, yana dai kula da yanda ake kauce mishi saboda katon tambarin bajon sojoji da yake manne jikin gefen motar, sai kuma sticker dinsu a gaban motar, ko babu kayan da suke jikin shi, kallo daya zakai ma motar kasan cewa ta soja ce. A haka harya kara gidan shi da yake Rijiyar Zaki, kasancewar shi muqamin shi First lieutenant, akwai sojoji guda biyu masu tsaron shi a gida. Daya daga cikin sune ma ya bude mishi gate, bai damu da ya tsaya ya gyara parking din ba, kawai kashe ta yai ana harabar gidan yana fitowa, mukullin ma a jiki yabar shi bai cire ba.

Cikin gidan ya karasa, har saida ya wuce tsakiyar falon da takalman shi, kaman daga sama yaji muryarta na fadin

'Babu sallama Sadauki? Takalmi har tsakiyar daki, ina sallah a wajen fa'

Bai kokarin cire takalman nashi ba, sallamar dai ya tsinci kan shi dayi. Jin shiru babu wanda ya amsa yasa shi takawa cikin gidan yana karasawa bangaren Nuriyya, hadi da sake yin wata sallamar, yasan tana can tana bacci, idan akace batai sallar Azahar ba bazai musu ba, ranar girkinta ma tana bacci, balle yau da tasan ba itace dashi ba. Karasawa yayi bangaren dakin baccin ta yana kwankwasawa, tukunna ya tura ya shiga, tana zaune kan gado, kunnenta liqe da earpiece, ta tusa system a gaba, da alama kallo takeyi.

Jin shigar shi yasa ta zare earpiece din guda daya tana kallon shi a kasalance da idanuwanta da suka fi komai a tattare da ita jan hankalin shi. Miqa tayi hadi dayin hamma tukunna tace

"Masoyi..."

Kamar yanda take kiran shi ko a gaban waye. Ganin yayi tsaye yasa ta mika hannunta tana mishi alama daya karasa, tana sakeyin wata hammar

"Bacci nake ji Allah, jikina namun ciwo"

Tsintar kan shi yayi da tambayar

"Me kikayi?"

Daquna mishi fuska tayi

"Kallo nayi... Me Waheedah ta dafa dan Allah?"

Zuciyar shi yaji tayi wata irin dokawa da sunan Waheedah din da Nuriyya ta kira. Bai iya amsa ta ba ya wuce kan shi tsaye yana nufar bandaki. Da ido Nuriyya ta bishi tukunna ta tabe baki tana mayar da earpiece din data cire daga kunnen ta daya taci gaba da kallon da shigowar shi ta katse mata. Rigar jikin shi ya fara cirewa yana mamakin yanda akai Nuriyya bata kula da jinin da yake jikin kayan shi ba, bata ma kula da damuwar da take shimfide a fuskar shi ba. Kan washing machine din da yake cikin bandakin ya ajiye kayan daya cire.

Ruwa ya bude ma kanshi

2 / 51