Author : Lubna Sufyan Category : African Stories & Novels
maka koda an samu igiya an kulle shi a baka kulki ka jibgeshi bazaka huce ba. Kan gado ta koma ta zauna, zuciyarta na tafasa. Shikam falon ya karasa yana kallon yanda Waheedah take kallon shi cikin sabon tashin hankali. Hakan ya mishi dadi, gara taga da gaske yaranshi zai dauke, saita tashi su koma gida gabaki daya.
Idan rigima takeji zai bata dai-dai wadda zata isheta harda kari idan bukatar hakan ta taso. Waheedah batasan ta mike ba saida taga kallon da Abdulkadir din yake mata. Ta dauka zuciyarta ta bushe, ta dauka babu wani abu dazai sake taba ta, saida taga yarinyarta a hannun shi tukunna takejin yanda yake son rabata da sauran nutsuwar da ta rage mata, muryarta a karye ta soma magana
"Me kake so dani? Sadauki me kake so dani haka? Meye ban baka ba? Lokacin da sukazo saura suka samu daga zuciyata, saboda kaso mafi girma na tare dakai..."
Shiru tayi tana mayar da numfashin daya taso mata mai hade da kukan da yasa ta kasa karasa maganar data fara
"Ki biyoni mu tafi gida, koma menene zamu gyara shi mu biyu..."
Abdulkadir ya fadi yana rokonta da duka zuciyarshi da ta amince, saidai a fuskarta yake ganin hijabin da baisan daga inda ta samota ta saka a tsakaninsu ba, hannu tasa ta share hawayenta tana girgiza mishi kai, yanayin daya kara mishi zafin da kirjin shi yakeyi. Kai ya jinjina yana fadin
"Kiyi abinda kike so Waheedah..."
Ganin ya juya yana shirin barin dakin ya sata furta
"Takardata Sadauki..."
AbdulKadir bai nuna alamun yajita ba ya fice daga dakin. Aurenta a hannun shi yake, yara nashi ne, zai dauka duk sanda yaga dama. Ya dauka idan yayi amfani dasu zata hakura ta dawo hayyacinta daga rashin hankalin da take ciki. Hakan bai faru ba, zai dauki yaran yanzun, zai tafi dasu. Zai kuma ga wanda ya isa yasa shi sakinta, tonon asirine ta gama yi mishi, abinda bai taba tunanin zata tabayi ba, sosai ta girgiza shi, dan harya shiga bangaren Mami yana mamakinta, yana kuma duba cikin kanshi ko zai tuna asalin laifin dayai mata banda na ranar amman ya rasa.
Bai samu Mami a falon ba, Aminu ne zaune da Fajr da hankalin shi gabaki daya akan tom and jerry din da yake kallo a babbar talabijin din dakin. Batare da yayi magana ba ya karasa yana saka hannun shi daya ya dago da Fajr din da a shagwabe yace
"Paapi..."
Gyara mishi tsayuwa Abdulkadir din yayi yana fadin
"Wuce mu tafi..."
Da rashin fahimta yaron yake kallon shi da idanuwan shi irin na Waheedah din
"Omma fa?"
Saida Abdulkadir ya sauke numfashi tukunna yace
"Banda ita..."
Maqale kafada Fajr yayi, yana shagwabe fuskarshi sosai
"Zan zaneka Fajr... Ka wuce nace"
Wucewar Fajr yayi dan duk karancin shekarun shi yasan cewa Abdulkadir din zane shi zaiyi kamar yanda ya fadi, kukan shi ma bai bari ya fito ba, dan yana bala'in tsoron duka, ko tsintsiyar kwakwa yaga Waheedah ta fito da ita ta ajiye waje daya zai nutsu. Abdulkadir kuwa ya taba saka charge ya zane shi, sosai yake tsoron yin wani abu a gaban shi. Sai lokacin Aminu yace
"Tunda ba zashi ba ka kyaleshi"
Kallon shi Abdulkadir yayi yana kafe shi da idanuwa, bai manta maganganun daya fada mishi a asibiti ba dazun, kawai ya kyalene baice komai ba saboda a lokacin yana cikin jin kunyar Mami
"Ka mantani ko? Aminu ka manta wanene ni"
Kai Aminu ya sauke kasa yana jin zuciyarshi na dokawa cike da tsoro. Bai manta ko waye Abdulkadir ba, haushin shi da yakeji dinma a yanzun ya nemeshi ya rasa
"Zan dakeka, zan fasa maka bakin da saikayi sati magana da kowa na maka wahala balle kayi tunanin mun rashin kunya..."
Abdulkadir ya karasa yana directing bacin ran nashi kan Aminu. Sosai yake jiran yaron yai motsin da bai mishi ba, ya ajiye Ikram kan kujera ya dake shi kamar ganga. Zuciyarshi zatai mishi sanyi ko yaya ne idan ya zane wani, tunda bazai iya zane Waheedah da ta bata mishi ran ba. Amman Aminu ko dago dakai baiyi ba ballantana yai kokarin cewa wani abu. Kai Abdulkadir din ya jinjina ya juya ya kama hannun Fajr yana janshi suka nufi hanyar da zata kaisu harabar gidan inda motarshi take a ajiye.
*
Yassar ya hango ya bude motar shi ya fito, cikin shigar manya kaya da hula da suka kara mishi wani irin kwarjini. Tsaye Abdulkadir din yayi batare daya san dalili ba, yana nan har Yassar din ya karaso ya same shi
"Ina kuma zakaje da yara?"
Yassar ya bukata, yana kai hannu ya dafa kan Fajr daya fada jikin shi yana fadin
"Uncle..."
Yana gidan shi a kwance yaga wayar Hajja. Saida zuciyar shi ta doka, dan yasan ba lafiya ba, indai Hajja zata daga waya ta kirashi sai da wani babban dalili. Baiyi mamakin jin dalilin Abdulkadir bane ba.
"Bakaimun sallama ba Hamma..."
Abdulkadir ya fadi yana kankance idanuwan shi, dan yaga yanayin Yassar din shima yasan abinda yake faruwa. Wani irin kallo Yassar ya watsa mishi
"Yaran ka dauko? Ka sake tan?"
Kai Abdulkadir ya girgiza mishi, hannu Yassar ya mika yana karbar Fajr da Abdulkadir din ya kasa hanashi
"Nasan baka da hankali ko kadan, amman banyi tunanin yakai haka ba. Gidan ubanka zakaje da jaririya? Ko Nuriyyar ce zata shayar maka da ita?"
Sosai Abdulkadir ya dakuna fuskarshi
"Karkai mun fada Hamma, idan zaka dauki sides saika tsaya kaji nawa bangaren tukunna"
Tsaki Yassar yaja, da yace bazai sake shiga matsalar Abdulkadir din ba, yanzun ma dan Hajja ta kirashi shisa ya dauko kafarshi yazo. Hannun Fajr ya kama yana shirin raba Abdulkadir din da nufin wucewa
"Hamma ina zakaje mun da yara?"
Kallon shi Yassar yayi
"Idan ka biyoni saina watsa maka mari, mahaukacin banza..."
Murya can kasa Abdulkadir yace
"Yarana, a gaban yarana Hamma..."
Tsakin Yassar ya sake ja yana wucewa abin shi, yanajin Abdulkadir din na biye dashi. Baiko juya ba harya karasa bangaren Anty, tunda Hajja tace mishi suna can data kira. Waheedah ya samu ta hada kanta da kujera, yanayin ta nasa wani abu tsaya mishi a rai, dagowa tayi fuskarta harta tara jini saboda kuka. Sosai Yassar yaji kirjinshi yayi nauyi. Karasawa yayi ya zauna kan kujerar yana mika mata Ikram. Da sauri ta karbi yarinyar tana riketa a jikinta, duminta na saukar mata da wata irin nutsuwa taban mamaki
"Nagode Hamma..."
Ta fadi cikin wata irin murya da tasa Yassar sake kallon Abdulkadir din yana watsa mishi wani kallo. Kankance mishi idanuwa Abdulkadir din yayi, ya dauka Yassar na bayanshi, kamar ko yaushe akan abubuwa da dama. Tun a watanni baya yagane cewa shima bayan Waheedah yake, bashida matsala dan Yassar yaso Waheedah, ko bakomai kanwarshi ce, amman shima kaninshi ne, kuma yana da kishin da bayaso a fifita soyayyarshi akan ta kowa. Ko Hajja bayason yaga tana nuna ma su Yazid soyayya fiye da wadda take nuna mishi.
"Kiyi hakuri Waheedah..."
Kai Waheedah ta girgiza ma Yassar da takejin maganar shi kamar ya watsa mata ruwan zafi. Shima kan yake girgiza mata yana saurin dorawa da
"Ba ina nufin kiyi hakuri da koma menene yai miki ba..."
Da mamaki Abdulkadir yake kallon Yassar
"Hamma?"
Ya kira, ko kallon shi Yassar baiba, asalima maganar da yakeyi yaci gaba
"Idan nan din zasu dameki ki tashi mu tafi gidana..."
Wani murmushi mai sauti Abdulkadir yayi da bashida alaqa da nishadi
"Kana magana kamar izinin fitarta yana hannun ka"
Zama Waheedah ta gyara tana daga Ikram ta mike, towel dinta ta zame ta sakata a bayanta. Goya yarinyar tayi a bayanta. Kamar yanda Yassar din ya fadi, tana bukatar hutu, bataso kowa ya dameta ko yayi kokarin bata hakuri, tana kuma da tabbacin Yassar bazai bar kowa yazo ya dameta ba. Zata jira takardarta a gidan shi. In yaso daga baya ta dawo gida. Dan daman batayi niyyar zama bangarensu ba, balle Mami ta tambayeta meya faru. Batasan ta inda zata fara ba, ya saukake mata shine abinda tafi bukata.
"Ina zakije?"
Abdulkadir ya bukata yana kallon ta cike da sabon mamaki
"Ka aikomun takarda ta gidan Hamma, ko kabama Abba, duk wanda yafi maka sauki dai"
Tai maganar tana kallon Yassar da fadin
"Hamma muje..."
Ta kama hannun Fajr, bai cika yawan magana ba, amman bai taba tunanin zai rasa abin cewa gabaki daya ba sai yanzun, dan ba kalaman shi bane kadai suka kubce mishi, harda abinda ya kamata yai tunanin da ya wuce tsananin mamaki.
"Waheedah tsinuwar mala'iku da duk takun da zakiyi batare da izinina ba..."
Ya tsinci kanshi da furtawa ganin ta saka kafarta daya wajen dakin. Juyowa tayi da wani irin yanayi a fuskarta
"Tunda safiyar yau nake zubar da hawaye, kuma kaine sila, tsinuwar zatai balance Sadauki... Ina jiran takardata"
Ta karasa tana ficewa daga dakin. Wani murmushi Yassar yayi, tunda ya san yarinyar bai tana tunanin tana da kwarin gwiwar karbarma kanta 'yanci ba sai yau. Lokutta da dama yakanji kamar harda laifin shi a abinda take fuskata na zama da Abdulkadir, yakanji a kaso dari ma aurenta da Abdulkadir yana da hannu cikin kashi tamanin harda doriya. Musamman watannin baya haka yakejin duk laifin shine, amman yanzun ta fara rage mishi nauyi. Duk da can kasan zuciyarshi bazaiso mutuwar aurenta ba, amman hakan bazai hanashi goyon bayan gaskiya ba. Wannan karin son Abdulkadir baizai rufe mishi idanuwa ba. Batare dayace komai ba yabi bayanta.
**
Bazai ce ga yanda yakai gida ba, nutsuwar shi bata taba kwacewa akan tuqi ba sai wannan karin. Bangaren Waheedah ya wuce yana shiga har dakin baccin su, wannan karin takalman shi ya cire bayan ya zauna kan gadon tukunna ya kwanta. Pillow dinta ya dauka yana rikewa a jikin shi, kamshin turarukan ta ya shaka yana lumshe idanuwan shi. Yakanyi kewarta duk idan yazo ya koma wajen aikin shi. Bai taba tunanin zai kewarta yana gida ba, amman ya fara, cikin kasa da awa biyu komai ya birkice musu.
'Sadauki zaka karyani...'
Yaji muryarta cikin kanshi data saka shi bude kananun idanuwan shi, kafin ya sake mayarwa ya rufe su yana kara matse pillow din a jikin shi, sanyin shi na sake tunasar dashi cewa ba ita bace ba
"Ba zakimun haka ba, Waheedah ba zakimun haka ba..."
Ya furta a hankali yanajin an kwankwasa kofar dakin, wata irin dirowa yayi daga kan gadon
"Nasani, nasan ba zaki iya nisa dani ba... Nasani"
Yake fadi yana karasawa ya bude kofar, Nuriyya yagani, a karo na farko da yaji baiso ta kasance a bakin kofar ba. Rigarshi ce a jikinta sai wandon da ko cinyoyinta bai rufe ba. Ta kama gashinta da yake a kwance ta kulle shi a tsakiyar kan nata. Kwalliya ce a fuskarta sosai, da alama tayi wanka bayan fitar shi. Sosai yake kallonta yana neman samun nutsuwa koya take daga hakan.
"Naji motar ka..."
Nuriyya ta fadi, tana jin zuciyarta tayo tsalle zuwa wuyanta da yanayin dake fuskar shi, zatai karya idan tace bataji tsoro ba daya bude kofar, saboda taga wani abu kamar disappointment shimfide kan fuskar shi, kamar ba ita ya tsammaci gani a tsaye a gaban shi ba, sosai hakan ya tsoratata. Ganin ya kankance idanuwan shi yana kallonta har lokacin yasata fadin
"Ya jikin Waheedah din?"
Tanajin dacin dora sunan nata kan harshenta, wani irin tuquqin kishi na danne kirjinta da yanda zai kasance sunan Waheedah zatai amfani dashi yau dan tai nasara kanshi
"Da sauqi"
Ya furta can kasan makoshi, kai tadan jinjina tana shagwabe mishi fuska
"Abinci fa?"
Saida ta kira abinci tukunna yaji cikin shi ya murda mishi da yunwar da yakeji, numfashi ya sauke, duk ranar baici komai ba, Waheedah ko damuwa da cikin shi batayi ba. Yanda baya jure yunwa idan yana tare da ita har mamaki yake bashi.
"Ki dafa koma menene"
Yai maganar yana shirin rufe kofar a fuskarta, kallon shi Nuriyya takeyi tanajin cikinta ya murda mata da yunwar da takeji itama. Ba zatace ga rana daya datai wani girki kwakkwara ba tunda tazo gidan. Da tace mishi
'Abinci fa?'
Batana nufin me zata dafa bane, tana nufin me zasuci ya fita ya siyo musu dan ita yunwa takeji ta fitar hankali, biscuit ne kawai a cikinta duk yinin ranar. Saurin dafe kofar tayi
"Masoyi..."
Ta fadi tana tattaro duk wata kissa da zata iya ta nade muryarta da ita. Numfashi Abdulkadir ya sauke, bacin ran da yakeji a kusa yake. Da Waheedah ce data gane gab yake da fashewa, ko bata bashi space din da yake bukata ba zata kama hannun shi ta zaunar dashi, zata dora kanta a kafadarshi su zauna shiru har sai yadan nutsu. Amman da alama Nuriyya bata karanci ranshi a bace yake ba.
"Naga yamma tayi, na dauka ma ka siyo mana..."
Tai maganar tana kallen shi fuskarta a shagwabe. Numfashi ya sake saukewa yana dorawa da
"Idan ba zaki dafa ba ki barshi..."
Da mamaki a fuskarta take kallon Abdulkadir, bai taba mata magana cikin yanayin dayai mata ba yanzun
"Masoyi..."
Ta kira
"Kinjini ai"
Ya fadi yana rufe kofar a fuskarta ya koma kan gadon ya kwanta. Wani bacin ran na sake danne shi. Dan yasan ba laifinta bane ba, ba ita ta bata mishi rai ba, bai kuma kamata ace ya sauke akanta ba. Yagani a fuskarta yanda hakan ya tabata, ba Waheedah bace ba, ita kadai ce a duniyar shi yake saukewa bacin ranshi ko da ba tada alaqa da hakan, saboda tabarshi, saboda ta nuna mishi bakomai dan yayi hakan, ta fahimta yana son saukewa a wani waje, dan ya zabeta bai dameta ba. Karamin tsaki yaja. Ko kadan bayason yawan tunane-tunane, Waheedah tasan hakan ta zabi ta sakashi cikin tunani.
Nuriyya ta kai mintina biyar a tsaye a bakin kofar, ranta idan yayi dubu a bace kowanne yake. A rayuwarta batason wulakanci koya yake, idan akai matashi takanji kamar an mata hakanne dan a nuna mata ita din bakomai bace, amman tunda can idan wulakancin ya kasance daga bangaren shine takanji kamar zata hadiye zuciya ta mutu. Yanzun ma haka takeji, kirjinta har zafi yake mata. Batasan me akai mishi a waje ya bato mishi rai ba, dan ita tasan batai mishi komai ba. Yunwar da takeji na karasa bacin ran ya hade mata, wucewa tayi ta koma bangarenta tana nufar kitchen.
Fridge ta bude tana rasa abinda zata dafa, akwai kaza a ciki danya. Abdulkadir na kokari sosai wajen kula dasu tasani, kajine da yawa a nata fridge din, Waheedah kanzo har bangarenta ta kawo mata, bata cika amfani dasu bane shisa suka taru, randa taji kwadayi ya kamatane take daukowa ta soya. Yanzun ma kulli daya ta fito da ita duk tayi kankara, ta rufe fridge din tana sakata cikin abin wanke-wanke ta bude fanfo. Tukunya ta fito da ita tana ajiye, kazar da take a yayyanke ta kwashe ta zuba cikin tukunyar, ruwa ta zuba a ciki ta dora kan gas tana kunnawa.
Wajen fridge din ta karasa tana dubawa taga ko tana da cefane. Gani tayi babu, tunda ba girkin takeyi ba, bata kula ba. Fita tayi zuwa bangaren Waheedah ta shiga kitchen din nata tana bude fridge, akwai kayan miya a cikin robobi a ajiye wajen roba biyar. Na farkon ta fara dauka ta wuce ta koma, diba tayi ta zuba cikin kazar, sosai take ganin ya mata yawa, dan robar nada girma,a fridge dinta ta saka dan ba mayarwa zatai ba, koda zata sake amfani dashi. Maggi tazo ta bare ta watsa, taliya zatayi jalof. Tana gama zuba maggin taji kiran sallar la'asar. Daki ta koma tayi alwala, zani kawai ta daura saman kayan jikinta ta saka hijab ta gabatar da sallar.
Ko dardumar bata linke ba ta cire hijab din da zanin tana watsa su kan gado ta koma kitchen din, yunwa takeji ta fitar hankali, budewa tayi taga ya tafaso, amman wani karni ya daki hancinta dan kazar ko wankuwa batai ba, kuma kayan miyar babu albasar kirki a markaden su. Dauka tayi ko dan bata karasa dahuwa bane ba, ludayi tasa taji ko kazar tadan yi laushi, rufewa tayi ta tsaya kamar minti biyar a kitchen din, har lokacin ranta a bace yake, tukunna ta bude daya daga cikin locker din dakin ta dauko taliya guda daya. Kakkaryawa tayi ya zuba cikin tukunyar tana jujjuyawa tukunna ta koma falo ta zauna. Gara ko kallo ne tayi ta rage zafi.
Tana kunnawa ta dauki remote suna dauke wutar su, wani dogon tsaki taja
"Tsinannu..."
Ta furta a fili tana mikewa. Kitchen din ta koma taga tsaliyar harta fara laushi dan kanana ce, da tana gidan su takan jima bataci taliyar turawa ba, filawa Babansu yakan siyo a kado musu taliyar Hausa, ita ko lokacin sai tayi sati biyu bata dora tukunya ba, tun Mama na mata fada harta gaji ta hakura, idan ta matsa mata abincin ba za'a ga dai-dai ba, garama idan da mai da yaji ne, ko wake da shinkafa ce wani lokacin waken a tsai-tsaye za'aci shi. Bai gama dahuwa ba, shisa ta daina sakata, tunda ba wadatar abincin suke dashi ba da za'a dinga barnar shi.
Taga alamar taliyar ta kusan dahuwa, amman sosai ruwan yayi yawa. Abin kama tukunya da bangaren Waheedah ta dauko shi bata mayar mata ba ta saka tana dauke tukunyar daga kan gas din, rage ruwan tayi cikin abin wanke-wanke tukunna ta sake mayar da tukunyar kan gas. Tunawa tayi bata zuba mai ba, shisa taga taliyar ta mata wani iri, dubawa tayi ta dauko man a cikin roba, da yake na 'ya'yan itatuwa ne suke amfani dashi. Tana ma da man gyada da Waheedah ta bata yakai kwalba biyu, a cewarta kanwar babanta ce ta kawo mata da tazo gidan. A ludayi ta tara man tana zuba ludayi biyu ta cakuda, gani tayi kamar bazai wadata ba, ta kara ludayi daya tukunna ta rufe tana mayarwa.
Jujjuya taliyar ta sakeyi, ta daddaga ludayin a hannunta ta dan-dana. Gishiri ta dauko ta zazzaga dan taji kamar bai mata ba, hannunta ya kubce kuwa, cikin hanzari tai kokarin saka ludayi ta kwashe amman duk ya narke dan abincin nata tafasa, tsaki ta sake ja, komai baya tafar mata dai-dai. Dabara ce tazo mata, ta dinga kwaso romon da ludayi tana zubawa cikin wajen wanke-wanke tukunna tadan dibi ruwa ta kara ciki, gani tayi cefanen naso yai mata kadan, ta zaro taliya daya ta saka a bakinta, duk da hakan gishirin nason mata yawa, kuma bataji cefane kamar yanda ta Waheedah kanyi ba. Robar ta dauko ta kara dibar wani ta zuba