Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKAWARIN ALLAH Bayan Hawaye by HUGUMA

Author :  HUGUMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 53

18K to 21K   out of 156.9K words

sanarwa anty husaina,tun yana jin babu komai harya soma shiga damuwa,ganin lokaci yana quracewa,sannu a hankali ya soma yanke tsammanin samun kudin ma gaba daya,wanda hakan ya jefashi cikin damuwa mai tsanani,damuwar da tasa anty husaina ta gane halin da ake ciki,ta kirashi tayi masa fada sosai,ta kuma saida dan abinda ke gareta na kudi,saidai kudin basu cika ba,kaso d'aya aka samu cikin biyu,a lokacin ya rage saura kwanaki makarantar su rufe registration.

A hankali take takowa zuwa cikin soron nasu,niyyarta ta tsoratashi kaman yadda yayi mata shekaran jiya ya tsoratata,taji tsoro sosai ya koma gefe yana mata dariya yana fadin
"Ashe farar kura ce ke bansani ba?".

Yau da yazo kan dakalin qofar gidan nasu yaci burki,hakanan yake jin ranshi babu dadi,wanda hakan ya bayyana har gangar jiki da fuskarshi,saidai duk sanda ya tuna yanzu zaiga sanyin idaniyarsa sai yaji yanayin da yake ciki din ba komai bane,wayarshi dage aljihun wandonshi ta dauki qara,ya zura hannunshi a hankali ya zaro wayar,anty husaina ce ke kiranshi,yasan kuma kiran bai rasa nasaba da cikon kudin registration dinsa ba,zayaso kunnuwanta su jiye masa ya samu,saidai ba mai yiwuwa bane yayi mata qarya,abokin kuka shi ake gayawa mutuwa,sannan uwa uba bayaso wani abu ya kawowa karatunshi tsaiko,babban burinsa a yanzu shine ya kammala karatunsa ya samu aiki,ya auri shahidansa ya kuma kula da anty husaina,itama ta huta taji dadinsa
"Yaya dai muhammadu an samu cikon kuwa?" Ta tambayeshi bayan ya gama gaidata,cikin nuna kasawa da sarewa yace
"Anty ina ganin saidai nayi haquri....wannan karon duk wani qoqarina na samun cikon kudin na gaza,kudin sunqi samuwa....ina tsoron asarar karatuna..." Tausayinsa ya kama anty husaina,tasan abune mai wuya ganin karayar anwar
"Kaci gaba da addu'a,ina nan ina nawa qoqarin mu zubawa sarautar Allah ido,in sha Allahu yana tare da mu"
"A'ah anty.....karki takurawa kanki karki damu,nima zanci gaba da nawa qoqarin...".

A hankali ta koma da baya cikin tsananin mutuwar jiki,ba labe tayi musu ba amma ta kasa tafiya sanda yake wayar da anty husaina,cikin mutuwar jiki da karaya take juyawa zuwa cikin gidan,qirjinta ya quntata qwalla ta cika mata idanunta,dama akwai wani abu da anwar zai iya boye mata game dashi?,da wannan tunanin ta isa dakinta,gefan katifarta ta samu ta zauna tallafe da kumatunta,batasan adadin lokacin data dauka a haka ba har ya tarawa wayarta miscal bata gani ba,saida ummanta ta daga labulen dakin
"Wanne shashanci ne kike haka shahida?,kinsan ba zaki samu fita ba kikabar anwar qofar gida yana jiranki?" Hannayenta ta sauke tana cewa
"Yanzu zan fita umma" sakin labulen tayi ta juya ta fice tana mita
"To ke kuma ya isa haka malamar mita,tunda ta baki uzuri basai kija bakinki ki shuru ba?" Ta jiyo abbanta yana fada
"Kaga kar kace zakamin fada,don na mata magana laifi nayi?"
"Ba laifi bane,mitar ne ni banason ji karki cikamana kunne"
"Wai yau cin mutuncin naka ne ya motsa baban shahida?" Ta saki abinda take ta zuba masa idanu tana tambayarsa,saiyayi banza da ita ya zubda ruwan daya kurkure bakinsa ya dauki hularsa ya fice,ajiyar zuciya shahida dake tsaye bakin window ta saki,ta godewa Alla daya taqaita cecekucen nasu baiyi tsaho ba har yaja hankalin anwar ko yajisu.

Katifarta taje ta daga,kudaden da uncle hisham ya bata ta dauko,ta zauna ta qirgasu a nutse sannan ta shiryasu,koda batasan nawa anwar ke buqata ba tasan cikon kudin bazaikai yawan kudaden dake hannunta ba,don kudaden da uncle anwar din ya bata suna da yawa,don taji ma anty amina na cewa mama su aje a karba a siyawa shahidan tukunya mai sha biyu a aje mata,lanqwashesu tayi sannan ta miqe ta gyara mayafinta ta fice.

Sanda ta koma yana zaune kan dakalin,ya zubawa qasa idanu wanda hasken farin wata ya haske jikinsa yake bashi hoton inuwarsa,a hankali ya dago kai idanunsu suka hadu da juna,wani sanyi yaji har cikin rai da zuciyarsa,saiya sakar mata murmushi yana jin kaso tamanin na quncin da zuciyarsa ke ciki ya tafi,kallon farko ana biyu ya karanci lallai akwai abinda yake damunta,duk sai yaji wani iri,yaji babu dadi,duk wata walwala da karsashinsa ya shiga yin nashi guri,shi ya amshi daddumar hannunta ya shimfida ya kuma yi mata nuni data zauna,batayi musu ba ta zauna din,yana tsaye qyam a kanta yana qare mata kallo,ya samu kanshi da kasa zama
"Mene ne yayi kutse cikin farincikin gimbiyata?"
"Kaine...." Ta fada kanta tsaye,cikin sanyin jiki ya samu dan wani dutse dake daura da ita ya zauna samanshi
"Bana fatan kasancewar wannan ranar....wane kuskure na tafka haka harya zama tarnaqi wa farincikin zuciyata?" Hawaye ta soma zubarwa,bana komai bane saina tausayinsa,zurfin cikinsa yayi yawa,kara da kawaicinsa sun baci,amma ko daya bata son ya sake boye mata wani abu daya danganceshi,tana ganin kaman hakan wani naqasu ne tattare da dangantakarsu,zai zama tamkar bai bata muhimmancin da take tsammanin ya bata ba
"Ashe dukan inda nake tunanin nakai bankai can ba a zuciyarka?"
"Ya salam" ya furta fuskarshi na nuna tsantsar tashin hankalin daya shiga,wanda har cikin zuciyarshi haka ne,wanda har yanajin ya zarce na rashin kudin registration da bai samu ba
"Shah......"
"Kar ka sake cemin komai....na kamaka da laifuka guda biyu kawo yanzu,ban taba boye maka komai daya danganceni ba....amma kai ka boyemin abubuwa har biyu,ban sani ba ko.matsayina baikai nasan wannan fannin ba...." Sanyi ya dinga ji yana ratsa qasan zuciyarshi,duk da bai fuskanci me yayi mata ba,dubanta yake cike da qaina soyayya sa shauqi mai yawa,ta damu da lamuransa fiye da tunanin mai tunani kamar yadda ya damu da nata,bai tsammaci zata soshi kamar yadda yakesonta ba,ya zaci zata soshi ne irin son da baikai ya kawo ba,kodon kyau da Allah ya bata,kodon gata data d'arashi,ko don saboda farinjini da Allah yayi mata
"Yanzu karatunka ba nawa bane?" Ta fada maganar quruciyarta na fitowa fili,hakanan ta b'ata rai sosai ta kuma tsareshi da ido,murmushi ya saki wanda ya bayyana fararen haqoranshi
"Nakine my shahida"
"Don me baka gayamin halin da kake ciki ba?" Dan shuru yayi yana tauna amsar da zai bata,tsahon minti guda kafin yace
"Shahida....kin wuce duk inda kike zato kike tsammani a wajena,tunda Allah ya busan numfashi ban taba qaunar wata d'iya mace ba saike,nine namiji,ni nake nema,kuma nine sama dake,bai cancanci ace dukkan wata wahalata tana wuyanki ba"
"Koda bani da abun da zan taimaka dashi ai na sanyaka cikin addu'o'ina ko?" Idanunsa ya lumshe idanunsa yayi yana sakin murmushi
"Ni na sani shahidana koda banda damuwa ba zata daina sakani a addu'arta ba"
"Ta yaya zan aminta cewar mun zama daya kana boyemin ire iren wadan nan abubuwan?"
"Shahidaa...karki sake tunanin bamu zama daya ba,kin zama muhammad anwar,na zama rahamatulshahida" sunan ya bata dariya har sai data murmusa,tafin hannunta ta bude sannan ta miqa masa kudin hannunta
"Ungo qirgamin" amsa yayi yana zolayarta,sannan ya soma qirgawa yana cewa
"Shahidana ta zama hajjaju" sai daya gama qirgawa sannan ya dago ya dubeta yana gaya mata nawa ne,kai ta gyada duk da tasan nawa ne dama
"Kayi amfani dasu" sak ya tsaya yana dubanta kafin yace
"Shahida...." Idanunta ta ware masa tana dubansa itama,ya gane me take nufiSai ya saki murmushi
"Aro na baka,amma kayi duk amfanin da kakeson yi dasu"
"Kai amma wannan yarinya kin iya bada rance....to na gode Allah ya bani ikon biya" daga haka sukaci gaba da hirarsu,saidai rabin hankalinsa dukka yana kan halayen shahidan,yana sake godewa Allah tabbas baiyi zaben tumun dare ba,hakanan ya tabbatar bai miqa zuciyarshi inda bai cancanta ba.

Wannan abu da shahidan ta yiwa anwar ba qaramin qara mata qima yayi a idanun anty husaina ba,wata qauna take mata tamkar diyar cikinta tun kafin ma ta yiwa anwar hakan,ta yadda ta kuma yi amanna cewa anwar yayi dace da matar aure,ta kuma shiga sahun masu masa addu'ar Allah yasa shahidan ta zama mallakinsa.

Ta gefan anwar dinma tuni ya shiga bakunan 'yan uwan shahidan musamman 'yan gidansu da anty amina wadda sukafi dasawa da shahida duk cikin 'yan uwan mamanta,kasancewar tasu tafi zuwa daya da mamanta,kuma ita daya ke gaya mata magana itama maman da ita take shawara.

Cikin ikon Allah anwar yayi registration dinsa,komai yaci gaba da tafiya dai dai,rayuwarsu da shahida kuwa ta zama abar kwatance ga duk wanda ya sansu,kowa najin jinin danuwansa na yawo a nasa jikin,tun mutane na mamakin yadda sukeson juna har abun ma ya zame musu jiki,su kansu yadda suke nunawa kansu qauna basusan sunayi har haka ba saidai a gaya musu.

Sannu a hankali rayuwa taci gaba da juyawa,ta wanni fannin ana samun ci gaba yayin da wani bangaren yake zamowa koma baya da babban naqasu wajen bawa.

Zuwa sannan shahida sun shiga ss 3 term din farko,a sannan ne Allah ya yiwa mahaifin zunnurah rasuwa,hakan ya zama silar barinsu garin kano sukayi qaura suka koma katsina cikin danginsu,dalilin kenan daya sanya kusancin shahida da firdausi ya sake samun tagomashi mai yawa,ta maye mata gurbin zunnurah,yayin da ita da zunnurah ya zama sai a waya,lokaci lokaci idan sukayi waya tana sako mata zancan fiddausin tare da sake ja mata kunne kan tayi hankali da ita,murmushi shahida keyi yawancin lokaci,ta sake yarda Allah ne kadai.ya isa ya hada zukatan bayinsa,har yau bata tana ganin wani abu mai kama da abinda zunnurah ke tuhumar fiddausi dangane da ita ba.

Anwar ya samu ya kammala karatunsa cikin wahala da dagiya da kuma taimakom anty husaina wadda ta sadaukar da dukkan wani abu nata don ci gabanshi,yayin da shahida ta zamo mutum na biyu data sadaukar da dukkan wani abu da take ganin ta mallaka saboda anwar din.

Bayan fitowar sakamakonsa wani yayan abokinsa ya kirasu yayi musu tallar aikin d'an sanda da za'a soma dauka,rimi rimi sukayi komai da karime karime da qarfafawar gwiwar shahida data dage kan sai yaje,sai kuma batun tafiya training ya taso,a nan ne ya sare saboda lissafen lissafen abubuwan da za'a buqata daga garesu,wanda kusan duka harka ce ta kudi,koda wasa bazai doshi anty husaina da wannan batun ba saboda yasan cewa wahala ce da nauyi kawai zai dora mata,saiya shiga neman kudi babu ji babu gani,sai lokacin da tafiyar ta matso sannan ya shaidawa anty usaina,ta masa addu'a sosai,ranar da zaiyi sallama da shahida ta dauko baqar ledar viva ta dire masa.

Sai daya gama kalla sannan ya dago yana dubanta,baisan ma da wanne baki zai mata magana ba,da wanne harshe zai gaya mata yadda take a wajensa?,kaya ne da tasan cewa zai iya buqata a ciki,wanda ko bata fada ba yasan a qalla zata kashe dubu biyar,Da hannu ta masa nuni dole yayi shuru,tamkar ba zasu rabu ba ranar,ji yake kaman idan yaje zaiyi shekara ne bai dawo ba.

Kwanansa uku acan shida wasu mutum biyar suna cin wuya saboda ance sam babu sunansu cikin list din,bawai kuma babu dinba,yanayin qasarmu ne kawai,an suba wadanda sukafi kowa rashin galihu an cire sunayensu daga list din an maida gurbinsu dana wasu,hakanan suka tattara suka dawo gida.

Randa shahida ta ganshi ya dawo ba qaramin jin takaici tayi ba,har kuka ta kusa yi,shi ya dinga lallabata yana bata haquri
"Duk randa Allah ya horemin abu na farko da zan fara ginawa shahida shine makaranta,zanyi irin makarantar da yaran masu kudi suke zuwa,irin makarantar da suke karatuna zuba yaran masu qaramin qarfi,su samu irin ilimin da yaran masu hannu da shuni suke samu,su samu gata da kulawa irin na yaran masu dashi"shuru shahida tayi tana karantarsa,har cikin zuciyarsa maganar take fitowa saboda yadda hakan ya bayyana saman fuskarsa
"Yaran marasa shi suna shan wahala,suna shan wahala matuqa wajen neman ilimi,bayan sun samu karatun da qyar ya zamana karatun ya kusa zama na banza,sakamakon yadda aiki ke musu wahala,wanda wasunsu daga qarshe sakamakon karatun nasu kusan dai dai yake da takardar tsire" nan ma dan shuru yayi yana hadiyar yawu,sosai lamarin ke sukar zuciyarshi,sun jima suna tattaunawa game da halin rayuwa sannan daga bisani sukayi sallama.

Anwar bai gajiya ba bai kuma sare ba yaci gaba da neman aiki baji ba gani,burikansa din nan guda biyu su yake fafutukar ganin ya cimmawa,yana tsoron shahida ta kammala secondry ba tare daya samu aiki ba,babban burinsa a duniya suyi aure sanda zata kammala makaranta,ya kuma tsaya mata tayi karatu kaman yadda takeso harsai tace ya isheta,yana da burin yi mata halacci kwatankwaci koma fiye da yadda tayi masa.


*BAYAN WATA HUDU*

Kallonshi take tamkar ta zabga masa mari haka takeji,saidai hakan ba maiyuwuwa bane tunda ba tarbiyyarta bace,dawowarta kenan daga gidan anty amina ya tsaidata,sam batasan yana biye da ita tun daga qofar gidan anty amina ba cikin motarsa saida ta iso layin nasu,ta shiga gida da niyyar ba zata saurareshi ba yadda yaketa zabga aike yasa umma tace ta fita ta saurareshi.

Hakanan cikin jikinta takeji kamar akwai wanda yake kallonta,kamar anwar na wajen tare dasu,a hankali ta kalli damanta,shine kuwa sanye cikin jibgegiyar rigar sanyi da wandon jeans,kasancewar ana cikin yanayin sanyi,yayi kyau matuqa,kai kace wani ne ko dan gidan wani,kyansa ya sake fitowa,fitilun motar daya bari a kunne sun haskeshi sosai kaman yadda suka haskesu,idanunta cikin nashi saiya ja da baya ya juya ya soma barin wajen.

Wani tashin hankali ya ziyarceta,da wanne baki zata yi masa bayani?,ganin yadda hankalinta ya wajen ya sanya saurayin shima juyawa yana kallon wajen saidai baiga komai ba,bata sake bi ta kanshi ba ta shige gida da hanzari,wayarta ta laluba ta soma kiran layin anwar din,saidai harta qaraci ringing dinta ta gama bai daga ba,hakan ba qaramin daga mata hankali yayi ba,ba zata manta ba shekaran jiya suna hira yake ce mata
"Shahida tsoro nakeji,gani nake kaman zan rasaki,kaman kinfi qarfina" cikin mamaki tace
"Me kake fada anwar?" Murmushi yayi saidai ya taba har zuciyarsa
"Shahida...kina kallon kanki a mudubi kuwa?,irinki ba qananun mutane ke aurenki ba....ina tsoron kada wani mai motar yasha gaba na" sosai taji haushi harma ta shige gida ta barshi ko sallama basuyi ba,da qyar yasha kanta ya waya,to jiya bai samu zuwa ba kasancewar ya samu dan wani aiki yana kulawa wani da provision dinsa cikin anguwarsu,ladan da yake bashi ba wani mai yawa bane kasancewar kanti ba wani girma gareshi ba,amma ya karba yana yi saboda ba mutum ne shi mai raina sana'a ba komai qanqantarta.

Kusan ranar kwana tayi tana kiran layin nashi amma ko sau daya bai daga ba,daga nashi bangaren hankalinsa a tashe yake,hakanan zuciyarsa ke wani irin tafasa,kishi ne ki cinsa sosai,fargaba ta lullubeshi,fargabar kada ace zancansa ne zai tabbata zai rasa shahidansa,duk sanda ta kirashin bai daga ba sai yaji wani qunci na sake ziyartar zuciyarsa,bai iya daurewa yana jin kiranta na shigowa amma ya kasa dagawa,daga bisani tilas ya kashe wayar duka yana fatar ta haqura tayi bacci.

Kwana biyu ba anwar din ba dalilinsa,hakan ya daga hankalinta don har wajen kai sadaka bata ganinsa,da yammacin kwana na ukun bayan ta dawo daga kai abinci wanda yanzu ajewa kawai take wajen baba ado dake wajen ya raba a aiko da botikin don fir anwar yace ta daina kaiwa,shiryawa tayi ta tadda ummanta zaune tana jan carbi bayan ta idar sallar la'asar
"Umma....zanje gidan anty amina"kai ta daga ta dubeta sannan ta shafa addu'arta
"gidan amina kuma?,makarantar fa?"kanta tadan sunkuyar tana wasa da farcenta
"hadda ake karba,kuma ni na bada tawa tun jiya" dan jim tayi sannan tace
"Shikenan,ki gaisheta....yauwa....kice mata yaushe za'a fitar da ankon umaiman,ki gaya mata lokaci yana qurewa fa"
"Tohm umma....saina dawo"
"Zan rakaki yayaa" cewar mubina wada ke shirin islamiyya ta fada bayan ta watsar da hijabinta wajen
"Babu inda zaki,makaranta zakije" cewar ummanta,tana jiyo ihunta ta saka kai zata fice tana dariyar rikici irin na mubinan,dai dai lokacin abbanta ya shigo,saita koma da baya tana masa sannu da zuwa yayin da yake tambayar abinda aka yiwa mubinan
"Wai gidan anty amina tace zata bini,kuma islamiyya zata"
"Ke ina taki islamiyyar?"
"Hadda ake amsa abba kuma na bada tawa tuni..."
"To ma sha Allahu,dama inason ganinki"
"To abba gani" ta dawo tana dawowa saman kujera 'yar tsuguno ta zauna,
"Shahida....ina fatan ba wani abune ya shiga tsakaninki da yaron nan ba anwar?"
"Abba meka gani?" Ta tambaya a sanyaye
"Kwana biyu bana ganinsa yana zuwa" shuru tayi tana tunanin amsar da zata bashi,dukkaninsu ummanta da abbanta wani irinso sukewa anwar din,halayen anwar abun sone,nagarta gareshi wadda ta zama tilas ko waye kai ya burgeka
"Uhmmm...bakice komai ba"
"Abba in gaya maka?" Mubina dake goge hawayenta ta fada,harararta shahida tayi amma hakan baisa ta fasa magana ba
"Wanine mai mota yazo...umma tace taje ta sallameshi,shine yaya anwar ya ganshi ya tafi"
"Ubanki mai shegiyar magana" umman ta fada tana kai mata duka
"A'ah hadiza barta ta fada....kice kawai kin soma shanshano wani ne....ke shahida tashi ki tafi,kema zamu gamu dake"
"Duk abinda kaga dama ka fada,tunda dai ba zuciyata ka shiga ka hangi haka ba shikenan na gode Allah" tun kan ta fice daga soron nasu ranta ya soma baci,saboda taji suna gab da kaurewa da halayyar tasu da suka saba,saitayi maza maza ta ficema don kada ta jiyo abinda wunin yau zai sa ta kasa walwala,sam bata iya daurewa duk sanda wani sabani ya hasu tafi kowa jin zafin abun,tqfi kowa shiga qunci,ta rasa me yasa dukkansu basu haquri da juna,kowa kaman jiran kowa yake,kamar wadanda aka sakawa hannu cikin mu'amalarsu.

Ba dadewa ta isa gidan anty amina,ta taddata tana wanki ta saka mata hannu suka gama tare,tanata tambayarta anwar kwana biyu bai leqo ba batace komai ba,har sai da suka gama suka zauna dakinta suna ninke wasu kayan da suka soma bushewa
"Anty....nifa zuwa nayi ki mana sasanci da anwar"
"Sasanci kuma,me ya hadaku kenan?,yau kwana uku kuwa da zuwanshi ya gaidani"ana ya gobe abun zai faru kenan?,shahida ta raya a ranta,batasan ma yazo din ba,jininsu ya hadu da anty amina,gashi kuma ba wani nisa sosai tsakanin gidanta dana anty usaina,don har zumunci ma suke yanzu ta sanadinsu,tsaf ta kwashe komai ta gayawa anty aminan,a take tasa shahidan ta

7 / 53